Kenza eBookz

Mikiya complete Novel - Chapter 14

Mikiya complete Novel - Chapter 14

Mikiya complete Novel Chapter 14: Mikiya complete Novel Chapter 14. 🤍🔥✅✅✔ Wani colourn kyakykyawan murmushi ta saki tana sake janyo kansa tana dorawa…

4,471 words

🤍🔥✅✅✔ Wani colourn kyakykyawan murmushi ta saki tana sake janyo kansa tana dorawa akan kafafunta. Kafin wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata. "Garga me martaba! Lokacin bayyanuwar boyayyiyar gaskiya ne yayi, Alkawarin kare masarautar EMAAR's nake son kamin.... Ta fadi hawaye sosae na balle mata wani irin dauke kansa yayi yana kallon bayansa. Sai kuma ya juwo tamkar wani zaki ya goge mata hawaye ya ce, " You don't have to cry since you have me, i promise Insha ALLAH to be there for you no matter the weather, I promise to you and I promise to be your one and only till the end of time! Na dauki Alkawarin kawar da gurbatattun cikin masarautar nan Insha Allah Oummeyyy!!!" Ya fadi yana me dafa saman kanshi da hannunta yake hade da nashi hannun. Wata nannauyiyar ijiyar zuciya ta sauke tana mikewa tsaye. Ganin dare ne ya sanya oum yi masa sallama ita da jesra suka tafi, har bakin part dinsu ya mikasu da kansa cikin daya daga cikin motocin da suka daukosa. Shima zaid nashi bangaren ya wuce dake jikin ma ak din daga barin damarsa, kayan jikinsa ya zame tare fadawa bathroom wanka yayo duk da kuwa cewar dare ne, Silk kayan barci mara nauyi ya zira bayan ya feshe jikinsa da mayun turarukan. kai tsaye lafiyayyan hadadden gadonsa me kama da alkaki ya nufa. Dakatawa yay daga shirin kwanciyar da yake ya sake dora idanunaa akan yar karamar cctv footage din dake sakale tsakanin wasu manyan flowers guda biyu, murya kasa kasa ya furta. "camera?" Wani irin bacin raine ya ziyarceshi lokaci daya tare da furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips inshi yana ayyana shikenan da aure ne ma dashi. Camarar ta riga ta gan may mata masu ita su gane masa sirrinsa, Sa'ar shi daya shi mutum ne da bai iya tsiraichi ba kowa shi kadan sane kuwa. Wani irin naushi ya kaima manyan flowers din a take suka tarwatse. ⭐ Duk wani lango da sako na bedroom din sai daya bincike ko ina. Babu wata kamara bayan wannan din dai, fasa kwanciyan yayi ya dau systerm nashi ya fara aiki cikinta, da dukkan alamu ransa a bace yake daga yanayin yadda yake sarrafa laptop din kadai zaka gane haka. Kiran sallar farko ya mike tare fadawa bathroom alwala ya dauro yana ficewa a part din kai tsaye. Babu wanda ya ganshi in banda ladanin daya kira sallar, Kai tsaye bangaren ladani ya nufa yana zama haka har mutane suka cika masallacin Aka tada sallah!. Babu wanda ya san da zuwansa haka babh wanda yayi tsammanin ganin a time din, Wannan nutsatstsiyan muryan nashi shine ya ankarar da mutanen dake cikin masallacin tare da zaburar da wasu da sanyasu faduwar gaba. Haka sautin kamilalliyar muryansa yacu gaba da tashi cikin kyakykyawar kira'arsa a cikin suratul Ma'ida. A kuma daidai lokacin me martaba ⭐ sarki Hassan Al-hassan gabban jikinsa suka fara motsawa ata sanadiyar jiwo wani babban gurbin dake cikin tsakiyar kokon Ranshi. Sanadiyar karatunsa daya karade baki daya katafanin cikin masarautar. Haka muryansa ya ringa karade ko ina da ina na cikin fadar tare da ratsa zukata, inda wannan muryan dai ke firgitar da wasu! Wasu kuwa ta saukar musu da nutsuwa tare sa sanyaya gabban jikkunansu. MOH JIDDOH kuwa wata kalan katantanwa tayi jin sautin fitar muryan da ko baka gaban me ita take da tsananin rusuna zuciyar mutum da ladabtar dashi. AL-HUSSIEN kuwa dake daya daga cikin na gaba gaban jam'i baima san sanda kafafunsa suka soma rawa ba yana neman kaiwa zaune. Amma ya dake yaki bama ko wacce alama nuna kanta a tattare dashi, Yana sanye ne cikin cikakkiyar shigarsu ta larabawa cikin wata farar kuwait jallabiya sai shiramin daya nade kansa dashi, sai wani farin glass din daya sanya. Bayan idar da sallarn nashi sosae yayi karatu tare da gabatar da adhkar, Har zuwa sanda gari ya fara haske. Xuwa lokacin manyan dogaran fada sun kewaye gaban babban masallacin musamman ma hanyar da zai fito ta wurin, Wambai, Waziri, maga tajarda, Riga daki, suna can sashen me martaba zaman isowar Garga din, Cikin wannan izzar da dan banzan takun nan nashi ya fito nan fa dogawarawan nan suka masa wani irin dafifi. Kowa nason bashi garkuwa wasu suna gaba wasu suna baya. Kai tsaye apartment din me martaba suka nufa yana a tsakiyarsu, sun sanya wasu kyawawan sandunan zinare gefe da gefen Ak din. Hasken streetlight din dake kewaye da ilahirin masarautar na sake Duk inda tawagar Ak suka gitta hadimai zubewa suke akan gwuwowunsu suna mika gaisuwa. Ko sau daya bai daga ido ya kalla kowa ba, sai hadimansa ne ke amsama duk wanda yay gaisuwarn. Tun a harabar shiga babban sashen me martaba sarki Hassan Al-hassan din ak ya dakatar da dukkanin hadiman. Sashen Sarkin⭐ shine shahi mafi kyawu da kawatuwa da duk wasu kayan kyale-ƙkyale a masarautar EMAAR's din. Gini ne da aka ginashi da zallar gilashi. Yana da hawa biyar dan haka sai da lifter kana kake isa apartment na sarki hassan din, Asalin apartment nashi kenan zama lissafa muku irin uban dukiyar da aka narka a ciki ainahin fadar me marta ban batama kai lokacine kawai. Su kansu dogayen benayen dake gine a fadar abin azo a kallo ne. Idan kahau hawan karshe kuwa na cikin ainihin fadae duk abinda ke faruwa a cikin masarauta EMAAR's din kana iya kalla daga saman fadar. Kai hatta da wajen masarautar ma kana iya hangowa. Hadiman dake tsaron sashen matsayin sojoji suka maye gurbinsu wajen take ma Ak din baya har xuwa parlourn farko. Anan din ma hadiman zubewa suka dingayi kasa kawunansu a risine domin girmamawa a gareshi har zuwa falon na biyu. Haka anan dinma wanda suke tare dashi zuwa parlou na biyu suka dakata, na falon na biyun na take masa baya har zuwa parlour na uku suma iyakarsu nan,Anan kuwa wani basamuden soja daya ne ya masa rakiyar wanda shine amintacce da yake iya haurawa har zuwa falo na hudun. Wani badakare ne kwalli daya tal a hawan karshen wanda saida amincewarsa ne kake iya ganin Sarki hassan Al-hassan kai tsaye din,Anan riga daka ha kwashi gaisuwa wurin Ak tare da bashi izinin ganin me martaba kai tsaye.

Saida na'ura tayi kururuwar isowarshi tare da tantance shi kana ya sanya kansa zuwa hasalin FADAR EMAAR's din. Wani irin numfashi ya sauke me dumi yana jin yanda namomin jikinsa ke wata iriyar tsuma, Ahankali ya lumshe kaifaffan idonsa yana ambatar sunan Allah. Kafin ya sake bude idon ahankali kai tsaye akan MOH JIDDOH dake harde bisa kilisa tana cin inibi cike da ƙkasaita irin ta masu isa ya fara sauke idonsa. Itama daga idanun kadan tayi ta dube shi a sheke tare da zubarwa tare da kara hura hancinta sama,

Wata Kujerar narkakken zinaren dake dunkule lik rug maga daka ya janwo zuwa gaban Ak. Wani irin zaune yakai zaman nan nasa mai cike da isa da tsantsar izza. Wanda hakan ke haukata wasun su domin zamane da yake fidda tsananin kwarjini da haibar da Subhanahu wata'ala ya masa. Crossing kafarsa yayi daya kan daya yana jan trow trey'n dake gaban MOH JIDDOH wanda yake shake da yayan itatuwa. Inebin dake narke cikin zuma ya dauka tare da kaiwa bakinsa yana dan cirar kadan. Wani irin motsa bakinsa yayi tare da lumshe idonsa saboda yadda tsananin zakin inibi da zumar suka tsinka yawun bakinsa. Tare da ratsa har tsakar kansa kai tsaye. Wani irin marin bazata takai ma fuskan Ak din da idonsa ke lumshe MOH JIDDOH tayi. A bazatan taji shima ya rike hannunta karafff tare da bude tsayayyun idonsa yana dan girgiza mata kansa. Irin I DON'T CARE MANNER's din nan.

Kyawawan idanunta ta juya a fuskar Al-hussien sai kuma ta janyesu zuwa ga Mahboob da mandood. Dama duka sauran mutanen dake cike da dakin. Shi kuwa Ak dake rike da hannun Moh jiddoh yi yayi tamkar besan abinda ya aikata ba, saima maida idonsa da yayi yana sake kullewa. Yanda yai tamkar besan mike faruwa a wajen ba shine ya sake hasala Moh jiddoh.. Cikin muryan daya fara manyanta amma kuma yana fita da tsananin kaushi ta furta "Me kuke bukata da bazaku wanke min fuskan wannan tantirin yaron da mari ba! Kana kumin dumu dumu da jikinsa da duka? Ko saina baku umarni ehhhhh!!?" Ta fadi tana watsama su Alhussuen din wani mugun kallo. Cike da girmamawa Al-hussien ya dan rankwafa. Tare da fadin. "An gama Ya ummienah Umarninki shine abin jiranmu kana kuma wajibane a garemu"

Kamar yanda be motsaba ba haka be bude idanuwansa. Saima karkada kafafuwansa da yake yi cikin isar da yake jin yakai koma ya zartata. Yunkurowa Al-hussien yayi da niyar kashe fuskan AK da mari. Wani irin bude idaniyarsa yayi tamkar zaki wurgi da hannun Moh yayi tare da damkar na Al-hussien din yana sauke firgitattun idonsa akan shi. Kafin ake yayi wani abu Moh ta dauke kyakykywar fuskarsa da wani lafiyayyan mari.

"Ka sani HAU'WA KULU bata yafiya haka bata daukar kuskure koda kadan ne bare kuma me girma irin naka, ka sakar min da hannun yaro daka rike shi da kazamin hannunka da bashu da tsarki!. Ka sani taba hannun mutum irinsu Al-hussien sai hannun daya cika duka sharrudan musulinci, ba kazami irin naka ba daya gama cakuduwa da dattin zina" Atare Oum, Adeenerh, jesra, al-mustapha suka wani irin kulle idonsu da karfin masifa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Oum ta furta tare da RAZEENERH da suke kira da MAH. Mahaifiya Almustapha sai kuma yarta ta fari wacce tayi batan dabi sama kasa aka nemeta aka rasa. Shi kuwa boss din wani irin tsuma jinin jikinsa ya dauka. A fusace zaid da bazai iya jurema cin mutumcin da ake ba biyuninsa bane ya mike.yana toshe kunnuwansa tare da furta "STOP" Mandood ne ya mike tsayen shima ta hanyar tarar zaid din yana jefa masa wani shegen kallo tare da fadin. "Me yasa kake da taurin kaine?, Idan ba'a kasa dakai ba baka gaggawar dauka domin gudun abin fada ko martanin da za'a iya maida maka" Wani shegen kallo ya wurgama mandood din tare da cewa. "Niba rago bane da zan zauna a gaban idona naga ana aibanta jinina na kyale haka! Taurin kaine dani! Ni mutum ne da ako da yaushe yake cin nama da nama karya kasuwan nake nabi ta kansu na mitsitstsikesu domin na gama amfana da tsokar jikinsa" Luuuuuu Ak yaja idonsa dayabi zaid dashi kamad zai kulle su gaba daya sai kuma ya budesu war akan twins dinsa gudan jininsa zaid. Wani irin fashewa da kuka Moh tayi tana mikewa tsaye tare da fadin. "Tabbas jinin Maryam masifa ce a garemu, ni dama tun farko banso hassan ya aurita ba wllh! Har iyaka na ketara masa akan auren wannan me bakin jinin, na rantse ba zata shigo cikin gidan a matsayin matar aure amma saida ta shigo tazo ta haifa mana jaraba da masifa a masarauta"

"Ashe kinga kenan baki da matsayi da iko akan dan da kike ikirarin naki ne, duk da kin yankamar iyaka amma saida ta ketara, kince ba zata shigo ta shigo! Ko wanne mutum yana da gari kana yana da iki a inda yake. Ba tare da kin tare ta daga shigowarma kuma ta shigo harta haifa miki magadan masarautar EMAAR's kina ji kina gani wannan masarautar ta zama tata. Wannan garin ya zama nata bayan wannan mene bakyason ta sake tsallaka miki, wannan masarautar tamu ce garin ma namu ne a gaban idonki zamu mulki masarautar dama kasar da kike ikirarin Oum bazara shigo ba. Saidai masu hadiyar zuciya su hadiya in yaso ta buga su mutu" Ak ya yaboma Moh maganfanun da tunda uwarta ta haifeta ba'a yaba mata koda kwatancinsu ba. "ABDOUL-MALEEK" Muryan Oum ya katse shi daga wata maganar da yake shirin sake yanko mata. Hatsaniyace sosai ta kaure a cikin dakin kowa yaki ya rusuna kowa ji yake da nasa zafin kan. Abinda ya rusunar da rigimar nasu faduwar da Oum tayi. Wannan shine dalilin lafawar komi haka Ak yama Oum dinsa daukar jarirai ya fice da abarsa zuwa clinic din masarautar, Shine da kansa ya duba Oum nashi kasancewarsa dactor, kana pilot ne idan yaso babu inda baya ketawa a kasashen duniya. Kana gashi Babban soldiers wanda matakin farko ma da Marshal ya soma.....

⭐Washe gari ⭐ A nutse yake Sakkowa daga matakalar benen zuwa entrance din da zai sada shi da bangaren oum dinsa. yana sanye cikin wasu fitinannun lallausan farin yadi. yayin da kuma ƙkafarsa ke sanye cikin wani black combat toms mai kyau irin na yayan sarakunan nan, Sai wata mini jacket din daya dora saman kayan yar filic da ita. babu abinda ke tashi ajikinsa sai wannan fitinannen kamshin turaren nan nasa me azabar tsada da bama wanda yake shakarsa cikakkiyar nutsuwa ta musamman. Tamkar wanda akema wanka da madara haka farar fatar jikinsa ke daukar idon me kallonsa. Cikin cikakkiyar takun da kallo daya zakayi masa ka gane cewar kakkarfa ne sabo da motsa jikin da yake aduk kwanan duniya ta hanyar machine gams. Blue eyes din nan rufe cikin wani luxury sun glasses wanda ya sake bayyana taswirar karan hancinsa da yake mike ziyat tamkar da biro aka zama masa shi daram. pink lips din nan nashi sai wani kalan glowing yake tsananin taushin na bayyanuwa wa me kallonsa, kallo daya zakama Ak ka gane shi din me kyau ne kana na musamman masha Allah,domin allah ya wadatashi da komi najin dadin rayuwa. cike da kwanciyar hankali da nutsuwa yake takawa irin takun dake nuna shidin kakkarfan namiji ne kana tsayayye. Marar daukan wargi da in Manners din nan. Kai tsaye babban katafaren parlourn Oum dinsa yama tsinke wanda girmansa yake dauke da wasu tsadaddun furnitures, parlour ne mara tarkace amma yana da kyau na fita daga hayyaci. Kayatattun royal cushion din dake zagaye da parlourn sunyi may kawanya, daga tsakiya kuma akwai wani shimfiɗaɗdiyar red carpet da throw pillows akai, sai wani ƙkaramin round table daga gaban wani kebantaccen rug, sai babban plat screen plasma din da ya kusa cinye bango guda na parloirn don girman shi. iskan A/cn dake kasawa kai tsaye yake fidda wani irin daddan yanayi a cikin parlourn, dubansa ya kai ga ƙkaton agogon dake manne a bango wanda yake ƙkawace da zanen pop, tare da pisc na Oum shi tare dame martaba. ⭐10:25am agogon ya buga cire pcarp din kansa yayi yana kallon ƙyakkyawar fuskan Oummey'nshi dake zaune kan caution mug ne a hannunta me dauke da zazzafan ruwan bunu marar madara. Kallo daya zaka mata kagane ita din mahaifiyarsa ce saboda kamar dake tsakaninsu, lumshe idanunsa yayi hadi da dan sauke numfashin ganin zaune cikin koshin lafiya da yayi. Cikin amon muryansa mai dadi da nutsuwa yace "Takabbalallahu minna wamin kum alaina wa'alaiki ya Oummey! ". Shafa tulin sumar kansa tayi wanda yasha gyara mai kyau da sheki yayin da yake durkushe agabanta ya dafa hannayensa duka biyu a ƙkafarta, cike da kulawa tace "Amin barkan mu da wayewar garin Alhamis lafiya habeebty"

Jesra dake tsaye hannuwanta sarke akan kirjintane ta dan turo baki gaba tare da fadin. "Aifa shikenan nikam tawa ta kare tun da nakan gaban goshin ya dawo"

Cikin yanayinsa na rashin son magana yayi dan murmushi yana faɗin "Kina kishi da hakan ne jes?" ya fadi hakan yana maida kallonsa ga mahaifiyar tasa yana faɗin "Ya Oummey nah ya saukin jikin ki?". " Alhamdulillah naji sauki tun da ka dubani HABEEBT?,kaje ga Me martaba ya kamata ka sake auna yanayinsa Garga" Kansa yayi noding yana mikewa tare sa barin shahin......

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________

*MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 47&48

# ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # Hope # courage # Survival # Humanity # Inspiration

🤍🔥✅✅✔

⭐ NIGERIA ⭐

A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take yau din kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙkaddarar jiyanka!. Rayuwa mataki biyu ce Acikin kowacce duniya duk wacce kaddararka ta zabar maka zata kaika ne zuwa makomarta, sabanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurbatacciya. A yau dai ga merrah wacce take dab da amsa sunan mrs Salma isa manu, wanda komi da komai ya gama kammala kansa daya danganci bikin aurensu wanda ya rage kwanaki biyu takkk.

Kamar kullum yanzu ma zaune take a palon Annenta tana danna wayarta wajen karfe biyar da rabi na yammacin ranan alhamis. A zahiri danna wayar take amma a badinin ta ita kanta bazatace ga abinda take aikatawa a cikin wayar ba. Abinda kawai ta sani shine tana lallatsa wayar ne. Sallamar da aka yine ya sanyata dagota da kanga. Hajiya ummace ta shigo da sallama rataye da jaka a hannunta. Mikewa tayi ta nufeta tana murmushi ta amshi jakar tana fadin "Hajiya sannu da zuwa" Zama tayi akan kujerar palon kana ta amsa da cewar "Yauwa Merrah na biyo sahun kine dama kwana biyu shiru bakya zuwa. Ni na rasa wacce iriyar amaryace wannan ace gyaran jikinka ma gudunsa kake?' Kyaje gidan ne mijin ya koroki astagfiroullah Allah na tuba. Wllh tsaya kiji wannan bikin da naje Ikaja. Bayan kai amaryar da kwana biyu mijin nan ga daho kaza a dafe rigijff tasha kayan miyarta sharr. Ai wllh nake baki labari yakai gidan su amaryar nan bayan uwarta taci taji salam babu komi tace wannnan ai kunyi mantuwa babu komi a ciki na kayan hadi. Kinsan me yace ce musu yayi yanda sukaji kazar nan haka yaji yar su, to yanzu dan Allah me amfanin hakan? Wllh babban gata nake miki yar nan" Wani murmushin da baikai zuci ba meerah ta saki tana sunkuyar da kanta kasa. Acen kasar zuciyarta tana furta (Ni wllh da yamin daidai kuwa amma fa ni bama yarda zanyi wannan me kama da birin ya taba niba, bare ya hada jiki dani nevermine wllh) Fitowar Anne shine ya katse meerah daga duniyar tunanin data fada. Kallo daya Anne ta mata ta dauke kai tana karasawa inda hajiya umma ke zaune. Gaisawa sukai nan suka fada wata maganar daban ba wacce hajiya umman keta kokarin ganin ta kawota ba. Jakar kayan Anne ta turama meerah tana fadin taje tayi amfani dasu kafin ta shigo dakin itama. Hayaniyar data kaure a cikin gidan ne ya sanya su umma fita. Wata matashiyar mata ce wacce taci wani ubansun ado jikin farin leshin daya sha doguwar riga half bubu, sai farar siririyar yarinyar dake gefenta cin mutumci take zuwaba a cikin gidan tana fadin sai an nuna mata uwar data haifi amaryar da ake shirin likama dansu, dan son zuciya da bakar zalama anga gidan arziki shine za'a likema dansu... Kallo daya Anne ta watsama matar ta dauke kanta tana komawa inda ta fito, shunenta maman affan ta mata ai kuwa ta tafi zata fusgo Anne. Wani irin juyowa Anne tayi tare da watsa mata wani mugun kallon daya sanya maman sury jan burki daga shirin fusgar da taso yima Annen. Tsananin kwarjinin da idanuwan annen suka mata ne ya sanya ta hadiye sauran maganganunta, tana kama kanta cikin muryan da baya daukar wargi ko wanne ta furta. "Idan har kun isa da danku kuje gida ki hana a daure aurensa da DIDI!, jinina yafi karfin a wulakanta shi haka jinin Ayshatul humaira ba daskararren jini bane jinin dake gudana a jikinta tafarfasa yake ya tafashensa yake. Tafi karfin ta hada zuriya da gurbat..... Maganar ce ta yanke mata sakamakon rufe bakinta da hajiya umna tayi. Ita kuwa sury tuni ta makale jikin mummynta haka nan ta tsinci kanta da shakkun matar ba karamin kwarji ta mata ba. Daya bayan daya matan gidan suka fara zamewa domin su kansu ba karamin gwarjini Annen ke musu ba barin ma idan halinta najin kai ya tashi. Su kansu yayanta wani bin sai su wuni ba tare da kalma daya ta shiga tsakaninsu ba, wannan halin nata kuma ba karamin tayarma da malam abdullahi hankali yake ba. Jan hannunta umma tayi suna komawa parlournta. Nan ta shiga bata baki amma samm taki tanka mata ita kanta tasan wannan gwamutsen hadin auren ba son shi take ba, to amma ya ta iya. Ta kasance matar da bata jayayya da hukincin ubanhiji in banda haka ko ita da tuni ta farke wannan auren da take ganinsa kamar ba tabbatacce ba har waye war garin yau din. Har yamma hajiya umma na gidan.... Bangaren meerah kuwa haka tayi wunin sukuku gashi ba damar fita bare ta dan fita ko ta samu full energy nata ya dawo. Ta hanyar shakar iskar wage, abincin da tun dazu Anne ta tura mata take ta faman jagwalgwalawa, ita bata ci ita bata dena jujjuya shiba. Har saida hajiya umma ta fasu ta furta.

"ya abincin gabanki tun dazun kinki ci sai famar jagwalgwalashi kike?. Meye haka kike yi da abincin nan meerah?" dago kanta tayi ta kalleta Itama Anne sai ta maida attention dinta kan meerah din. Wani dan murmushi ta saki irin me ciwon nan kafin a hankali tace. "Umma kinsan dazu da yamma na ci Wannan abin sam bana wani jin cin abincinne kawai na ji yanzu bana jin yunwar ma" "Toh idan baza ki ci ba ki rufe anjima kyaci" tashi tayi sai kuma jiri ya dibeta ba tare da kowa ya lura da hakan ba Kawai sai faduwarta suka ji. Da sauri Anne ta nufeta tana jijjigata, dakatawa tayi sai kuma ta juyoo da kallonta zuwa ga hajiya umma tare da furta "Bata numfashi" "Subhallah dama ba jiri bane ya dibeta?". Hajiya umma ta fadi tana yin kan meerah din " Maza kira malam ki sanar dashi Ayshatu" hajiya umma ta fadi cikin kidima domin ba karamin tashi hankalita yayi ba. Cikin kankanin lokaci saiga malam tare da Ibrahim babban dansa. Fito da ita sukai suka sanya a mota suna nufar hospital drektly.... A hankali take bude idanunta da sukaimara masifar nauyi, dan motsa idanunta tai tare da dan cije leɓe kadan. kafin ta samu nasarar bude ido da ƙkyau. "Asibiti kuma?" Ta ambata a hankali tana dan waige-waige da kallon dakin data bude ido ta ganta cikin bazata. Nan komai ya shiga dawo mata sai kawai ta koma tana jingina da jikin gadon, lokacin wajen goman dare. "Meerah ashe kin tashi ma?" Hajiya umma ta fadi tana komawa don yin magana da dactor. Tunda Anne tana gida babu jimawa hajiya umman tace taje. Ba don taso ba ta tafi tana tunanin damuwar da ake taima didinya yawa da kuma yawan tunani. Sai gasu ita da nurse ta dawo sake aunata nurse din tayi nan tace ma da umman babu wata damuwa insha allah zuwa safe ma zasu basu sallama. "Zanyi sallah ummah" Meerah ta fadi cikin muryan da yayi low sosae. Da taimakon Umma ta sakko a gadon sai yanzune ta kuma fahimtar a daki na musamman take, kuma ita kadaice a ciki hakan ya sanyata kallon umman da alamun tambaha. "Bamusan wanda ya sanar masa ba muma kawai ganinsa mukayi yazo ya sanya an sanja miki daki" dan lumshe ido tayi tana jin ma sam.. Bata son ci gaba da zaman hospital din. Sallan magrib da isha'i ta kawo tana koma ta jin gina kanta da karfen gadon. Sallamar salman din itane ta katse mata rufe idon da take niyar yi. Hannuwansa rike da manyan ledojin shopping ya shigo. Gaida umma yayi ts amsa tana tsokanarsa da angon kwana biyu. Dan murmushi yayi yana shafar sumar kansa yana jin wani irin madararn dadi na lullebeshi. Don ji yake tamkar ya jawo wannan kwanan biyun su dawo yau, kamar ya janwo nesa kusa haka yake ji da yana da damar hakan da tuni ya dawo da nesansa kusan sa. Kodan muradin wannan lafiyayyan jikin da yake ya kwadaitu sosae da sosae da tsarin halitta da kuma surar jikinta. Kallo daya ta masa ta dauke kanta shine ya gaida ta tare da mata ya jiki ciki² ta amsa. Nan ya shiga yar firarsa da umma domin gwanar tamu taki ko saurarensa. Kiran wayar sa friend's nashi suka yine akan sun sauka lafiya suna airport yazo ya dauke su, shine ya san yashi masu sallama yana cema umman abokanan sane suka zo domin tun gobe juma'a zasu fara shagwalgulan bikin. Yama so ace tun laraba suka fara amma malam da kanshi ya dakatar da hakan. Domin ya kawoma meerah katunan shagulgulan ne d nufin ta rabama friendies nata, wannan shine dalilin dakile maganar da malam abdullahi yay, ba tare daya sani ba kuwa haka salman da manyan abokanansa suka kama manya manyan hotels dake garin lagos dim suke abinda suka ga dama. Ta hilton hotel yabi ya taho da wasu domin debo manyan friends dinsa. Ajeborters na waje sa sauran garuruwa, a lokacin dayay ido biyu da dolly ba karamin baci ransa yayi ba domin idan ya tsani abu ya tsane shi kenan. Haka idan yaso tofa ya so shi kenan da dukkan zuciya da ruhinsa. Cikin kaushin murya ya kalli moussa yana fadin. "Kaine kazo da wannan abin ko?" Ya fadi yana masa nuni da dolly wani kafurin murmushi dolly ta saki tana " hey beb baka happy da zowa na ba kenan?" Tana shirin rungume shi ya ture ta a jikinsa yana fadawa motarsa yana fadin. "Le's go guys ku muje ko?" Sauran motocin suka shishshiga suna barin airport din tare da kama hanyar hilton hotel dasu..

Tun da suka shigo harabar hotel din suka soma jiyo tashin sautin Wakar da aka sanya din. Irinta shegen nan wanda suka rike a harkar tantiranci.

Tab katon harabar inda suke yake da wayayyun matasa da yan mata 'yan bana bakwai,wadanda rayuwa da kuma duniya ke musu dadi suke cashewarsu cikin kwarewa, wasu babu kayan arziki a jikinsu mafi yawan mazan kuma gajerun wanduna ne a jikinsu. Hannuwansu dauke da manyan kwalaben giya wasu cigarette's ce a hannunsu suna busa hayaki. Wasu kuwa pep na shisha ne a ganansu suna zuka su fesar da hayakin cikin wani dan iskan salo. Tun kamin motarsu ta gama parking dolly dake sanye cikin wasu shegun outfit riga da wanda na baxon ta balle murfin motar fa fito. Akan inda giya, shisha, cigarette's coc suke ta fara nufa kai tsaye. Shishar ta dauka ta mata wata kafurar zuka tana baza hayakinta daya hada hoton love. Zaune takai akan almurun kujera. Tana zare wawakeken shade din daya kusan cinye rabin fuskarta. Mafi hankalunan yayan ajebor din dake zagaye da wurin ne ya dawo kanta, Nanfa suka mata caaa aka har wasun su na kakarin kama hannuta donsu shakata tare da ita. Kai tsaye club dancing din ta shige ya soma wata kalar rawar daya sanya manyan yaran daukar ihuuuuuuu suna sowa. Nan fa kowa ga fara kokarin isa ga dolly saidai taki ba kowa damar hakan. Har suka karaci shedancinsu suka tashi wajajen karfe biyun dare.

★★KANO★★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull