Kenza eBookz

Mikiya complete Novel - Chapter 8

Mikiya complete Novel - Chapter 8

Mikiya complete Novel Chapter 8: Mikiya complete Novel Chapter 8. "Shi yasa na CE duk cikin Ku babu Wanda Zan kira da *JAN WUYA, duk kaninku "KOLAYE NE" Ya…

4,450 words

"Shi yasa na CE duk cikin Ku babu Wanda Zan kira da *JAN WUYA, duk kaninku "KOLAYE NE" Ya fada yana daga harshen Sa tare da sanya shi tsakanin seen da tongue nashi ya turo musu Yar karamar camerar. Duk cikin su babu Wanda be razana da wannan basirar tasu ak ba. Ehhhh dole suce basira mana amma sai suka waske abinsu.... Few minutes Zaune yake zama irin na harde kafar nan. Akan kujerar da Isa manu ke kanta a da a yanxu kuma ta dawo da ak din. Fuskarnan tamkar tayi aman Wuta tsabar tsananin fusata,A fusace Ajmaal yayo kan ak duk kuwa da yadda Mr President ke kokarin hana shi amma be hanu ba. "Kaida kazo da sunan kwatar yaronka to kasani kazo nan da sunan mutuwarka ne!,, A wannan rana a kuma nan wurin idan har ban dagarzaga kasusuwanka to na rantse ni ba namijine" Wani Dan iskan kallo da ak ya watsawa Ajmaal ne ya sanya jikin Isa manu ya soma karkarwa,shi da ba shi aka ma kallonba. Wani irin gyara zamansa yayi ya sakko da kafarsa daya dayar kuma ta na kan kujerar da yake kai. Ya dora hannunsa saman kafar like irin kasaitaccen basaraken nan. "Ko wane mafarauci gwarzone har sai sanda ya fuskanci ingarman zaki. Ba kamar kai da rundunar jami'anku ba!, bana da runduna bana da tsoro a jikina bare naji tsoron mutuwa. *TUN A HAIHUWATA NACI GALABA AKAN MUTUWATA_*" Ak ya furta kalaman tare da wani iriin doka hannunsa akan kujerar da yake zaune a kai. Kalaman da suka kusan zauta yar karamar kwanyar duka jama'ar dake setrest din..... A zuciye wani da suke kira da tonfal babban yaron su Isa manu yayo kan ak, da wani irin salon daukar hankali ak dake zaune ya sanya kafarsa tun kafin mutumin ya karasa ya sarke kafarsa. Ji kake rigifff mutumin ya zube kasa ba tare da ya ko motsa ba. Cikin kankanin lokaci ak ya sissince arms dake daddaure ya tafi dashi a gaban idonsu ba tare da sun Iya dakatar dashi ba haka suna ji suna gani ya sabi arms a kan shoulder nashi yabar wurin dashi.cikin wannan takun NASA me cike da bajinta,hadi da mazan taka Wanda kallo daya idan kai masa sai hantar cikin ka ta kada..... "Kai wannan yaro anyi dan tsinanne, kasa sai kace ta uwarka kazo ka zame mana fitina tare da hana mu rawar gaban hantsi" Isa manu ya fada bayan daya tabbatar ak dade da barin wurin. Ajmaal da gefen kunnansa ke digar jini ne Wanda ak ya bashi rabon shi. Cikin tsanin bacin ran ya furta. "Stoppp" Da karfin masifa "Na gaji dajin koda me irin sunan sane" Sai kuma ya dago ya kalli Mr President ya furta. "Sorry sir. Duk ba laifinka bane da alokacin da na d'ana kunamar bindigata baka tsayar dani ba ai da tuni saida wani bashi ba!, amma ka dakatar dani" "Babu dai kai ba shiba!" Tonfal ya fada Wanda babu jimawa ya farfado daga mutuwar wucin gadin da yayi. "More bit never get one choice but if we take a maximum change we get a big choice" Mr President ya fada yana gama fadar hakan ya fice a wurin...

A lokacin da akai wannan darbarwar salman yana kasar India yawan shakatawa tare da wayayyun yan matansa.

★★★ "Mommy Wllh duk inda yake a fadin duniyar nan saina dau fansar Jinin mahaifina da yayi, sai nayi sanadiyar barin numfashinsa da gangar jikinsa kamar yadda yaso raba nawa mahaifin da nashi!"

*FAROUQ AUDU BASHASHA*

kenan da ga audu bashasha shi kadai ya haifa a duniya.Shi yasa yaron ya taso cikin wani irin sangarta da tabara, Duk inda ake neman wani teteros to in akace maka Farouq fakat kenan. A yanxu haka Audu bashasha yana kasar India wurin kwararrun likitoci don kula dashi. Ashe be mutu ba da sauran ranshi lokacin da ak ya fasha kansa, Sun boye hakan ne domain gudun bacin sunan Sa, shi da kansa shine ya dauke RIYYA, ya mata wani irin mugun boye mahaifiyarsa kuma irin muta nan ne da sammmm babu ruwansu da duniya. Itace ma dalilin daya sanya ta hana. Cikin muryar da yake cike da tsantsan sarauta Hajiya Khadija suraj sunusu shureim ta dubi Dan nata Tare da furta. „Idan har Jinin dake gudana a cikin naka Jinin nawa to ban amince maka ba" Ta furta hakan tare da bar masa palon, shi kuma ya bi bayanta da kallo domin duk wani Iya shegensa da ji da samartaka da zafin kansa jinsa yake shiba komai bane a gaban hajiya Khadija. Ya ta biyu kenan ga me martaba sarki suraj sunusu shureim.

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________

*MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 27&28

# ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # BEST LOVE

🤍🔥✅

★★★★

2 months ago

Haka dai al'amurra suka ci gaba da wakana. Tuni baffa ya kashe waccen maganar haka kwanaki suka ci gaba da juyewa zuwa satikai satikai sukaci gaba da juyewa zuwa watanni. Cikin iko na Ubangiji meerah ta koma bakin aikin da ko a mafarki ba tayi tunanin komawa ba, Bisa matsawar MD da kuma wasu manyan anguwanni ta koma bakin aikin ta. Haka kuma maganar aurensu da Salman yake neman kan kama, Wannan abu shi yafi komai ɗaya hankalin meerah matuƙa saidai tana danne hakan a ranta. Kusan kullum yanzu shike zuwa har ƙofar gida ya ɗauke ta zuwa wurin aikinta saidai ta dakatar dashi first.

A tacen ɓangaren su Salman kuwa wasu irin abubuwa suke ma shirye shirye shida mahaifinsa Isa Manu.

*******

Yamma ci ne mai daɗi haka kuma yau din rana ne da ya kasance na musamman wato Jumma'a, ranan da yake ɗauke da albarka da kuma rahamar Ubangiji kala kala. Wannan dalilin yasa sassanyar iska mai cike da tsananin daɗi da kuma sanya shauƙi ke busawa, a gaba daya ko wani lungu da saƙo dake cikin gidan jaridar zamani TV Kowa ka kalla harkar gabansa yake cikin tarin nutsuwa, amma banda meerah da tayi zurfi a cikin duniyar tunanin data jima ta faɗawa.

*"MEERAH!"* *"MEERAH!!"*

Disha dake tsaye kanta ta shiga ambata tana me ƙoƙarin rataya handbag ɗin dake hannunta, Wanda kuma ahankali ta ɗan ranƙwafowa da kanta, tana me kallon Meerah.

"MEERAH wake up kodai bacci kikeyi ne?."

Disha ta faɗi tana me gyara tsayuwanta, tare kuma dasa hannu ta zunguri meerah ɗin.

Ahankali ta ɗago kanta wanda ta kifashi akan desk almost 15mn ago. Sam ba bacci takeyi ba hasalima duk abunda ƙawar nata ke faɗa tana jinta.

Numfashi ta ɗan sauke Ahankali tare da ɗago manya manyan eyes nata me kama dana mashaya masu matukar kyau, Wanda hakan ya sake bayyana tsananin kyawun dake kwance akan fuskarta, Idanunta da suka ɗanyi blue ta lumshe tare kuma da buɗe su aloƙaci guda.

Cikin unique voice ɗin ta mai daɗin amo da sanyin sauti, tamkar ana busa sarewa tace.

"What happen DISHA? ba bacci fa na keyi ba, just I'm tired." Ta ƙare maganan tana ɗan kwantar da wuyanta gefe.

"What happening kike tambaya? time ɗin tashi a aiki yayi, kalla ki gani babu kowa ya watse sai nidake kawai, oya tashi mu tafi kodai zaman wurin ne bai isheki ba?." Disha ta faɗi tana ɗan hararanta tare da yin gaba.

Fuska meerah ta ɗan kwaɓe kana cikin yanayin gajiya da kuma tsananin damuwar dake cinkushe a cikin ranta ta miƙe itama. cikin sauri ta rufa mata baya tana me ƙoƙarin rataya jakanta bisa shoulder nata.

Atare suka fito compound ɗin, tafe suke suna fira sama sama abinsu. "Disha a raina inajin ina gab da ajje wannan aikin nake ga" Meerah ta furta cikin cushewar yanayi. Dafa kafaɗarta disha tayi cikin sanyin jiki ta furta. "Haba meerah komai yayi zafi maganinsa Allah, ki barwa Allah komai Insha Allah shine maganin komai" "Hmmmmmm!" Ta sauƙe ijiyar zuciya me ɗan ƙarfi haka suka ci gaba da tafiya har suka fito gefen titin. Napep suka tara suka hau suna mai kwatancen anguwar da zai kai su. Ko a cikin napep ɗin ma wata sabuwar duniyar tunanin ta ƙara faɗawa. Na irin daskararriyar K'addarar dake kwance acikin jininta wacce ta fara motsawa kanta. Haƙiƙa akoda yaushe rayuwa tana tafiya ne tare da tarin ƙalubale.Haka kuma kowa da salon nashi Kalon ƙaddarar amma nata ƙaddarar gani take yafi na kowa, domin daga ta fita daga wannan sai kuma wannan ya kutso kai.

Kamar kuma yanda yake a bayan kowani baƙin ciki akwai farin ciki, haka kuma a bayan kowani kunci akwai sassauci. rayuwa mai juyawa ce farinciki ko akasin haka mummunan ƙaddara ko akasin haka, wayewar garin yau sun waye shine da maganar kawo kuɗin aurenta da iyayen Salman sukai har Naira miliyan ɗaya. Wanda ya tashi hankalin jama'ar gidansu, suka wuni zazzaga ruwan bala'i da masifu kala daban daban. Ita kuwa wacce ake yi ɗin dan ita sammm ba abinda ke gabanta kenan ba. Wani abu ne daban ke damun rayuwarta wanda da tayi ƙoƙarin zurfafa kanta yake neman juyewa zuwa wani ɓigiren na daban...... Cikin nisan da tayi a duniyar tunani har suka isa ƙofar gidansu bata ma san sunzo ba, Saida disha ta mata magana da ɗan ƙarfi kana tayi firgigit ta dawo hayyacinta Cikin duniyar mutane bata tunani.

*AK*

Msalin ƙarfe biyar na yamma manyan motocin Ak dake cikin garin Abuja suka ma airport ɗin tsinke. Wasu irin zafafan motocin kusan goma sha biyar irin su Range Rover, Bugatti Veyron, Toyota Highlander, Toyota Tacoma, Ferrari California,gefe ga wasu mahaukatan manyan jifa jifai har guda biyar da aka ware su baƙaƙe wulik dasu. motocine a wurin babu colourn da babu shi kansa airport ɗin kewaye yake da tsaro na musamman. Ahankali cikin takun izza dajin kai ya fara tako matakalar benen. Su kuma samudawan sa na aikin su na take mai baya, cikin sauri manyan security'n dake zagaye da airport ɗin suka shiga bashi kariya wa kallon da jama'ar airport ɗin ke binsa dashi. Don kuwa kallo ɗaya zaka masa ka kasa ɗauke idonka a kanshi. Sanye yake cikin Wani arnen cashmere valley wanda kallo ɗaya zaka ma yadin ka tabbatar da ba karamin kuɗi aka narka wurin siyen shiba... Ahankali yake taka Fararen sawayensa da tamkar wanda bai taɓa takasu ba haka suke, don tsananin taushi da kuma yadda suke sumil luwai. Wata kafurar Black blue ɗin Mota ƙirar Mercedez Benz aka buɗe masa Armstrong kuma ya faɗa cikin wata narkakkiyar bakar jeep Wrangler . Suka ɗauki hanyar wannan haɗaɗɗen Hotel ɗin na da sukayi booking tun a daren jiya. Dake babu wata tazara tsakanin support ɗin da kuma Hotel ɗin babu nisa cikin 25 minute suka isa ƙaryataccen hotel ɗin. A room me lamba 105 AK ya ɗauka su kuma duk suka rarrabu daban daban.

Kwance yake acikin bathtub dayake cike da ruwa masu tashin qamshi na musamman, Iyaka kanshi ne a waje ya lumshe idanuwan sa ya faɗa duniyar tunani me zurfi, wanda nake da tabbacin ya mantar dashi a duniyar dayake yanzu haka. ya jima sosai acikin ruwan wankan daga bisani ya wanke jikinsa ya fito towel blue ɗaure a jikinsa.ga kuma wani mini qarami a hannunsa shi kuma kalar light blue yana tsane gashin kansa dake cike sosai baqa wuluk! lotion ya shiga shafe jikinsa dashi tsadadde ya gyara tulin gashinsa da mayuka masu kyau da tsada. Kayan da aka rigada aka ciro masa ya ɗan kalla a takaice dogon wandon jeans ne blue da shirt fara qal me asalin kyau an mata zanen Lion ajiki da blue din colours, sanya kayansa yayi kafin ya fito zuwa balcony na room ɗin. Hannuwansa zube jikin wandon jeans ɗin. Wurin ba hayani sai sassanyar iskan dake kaɗawa mai cike da tarin ni'ima sakamakon hadarin da yayima sararin samaniya ƙawanya.Hakan yasa garin ya yi luf ga dukkan alamu akoda yaushe a ko wanne loƙaci ruwan sama kan iya sauƙa. Yana zaune kan Chiar silinder caution ɗin dake cikin balconyn Wata ƙatuwar Toyota land cruiser Prado ta shigo harabar wurin fara ce kal sai faman kyalli da ɗaukar ido take yi.Wurin da aka tanada dan adana motoci motar ta parker,cikin slow mamallakin motar ya yi parking. Kasancewar glass ɗin motar tinted ne yasa ba'a iya hangen mai mamallakin motar har saida ya fito.An ɗauki tsawon 10 minutes kafin matashin dake draving motar ya fito. Back sit ɗin motar ya buɗe nan kuwa sai da aka kusan 20 kafin wani siririn matashin saurayi ya fito izza. Ƙafa ɗaya ya fara zirowa ƙasa sanye da halp cover shoe white color mai adon Stone a jiki irin na sarakuna.Cikin loƙaci ƙalilan ya fito da gangar jikinsa,Dogo ne sosai amma yana da ɗan kauri jikin shi a murje yake alamu na yana cikin hutu da jin daɗi,yana da hasken fata amma ba sosai ba.Farin yadin boyal ne a jikin shi mai ɗauke da ƙananun zane,wanda ya sha ɗinki irin na samarin zamani,sai Black agogo daya ɗaure a tsintsiyar hannun shi na dama dashi,a jikin siraran fararan yatsun shi kuwa ya saka white ring mai kyau a karamar yatsa.kanshi bai saka hula ba sai baƙar sumar shi data sha gyara gwanin sha'awa kamar ɗan India. kyakkyawar face na mai ɗauke da manyan dara-daran eyes balls ɗin da suke kamar madara. A hankali ya rufe manya eyes ɗin shi yana sauke ajiyar zuciya.Tare da furzar da iskar bakin shi.Manyan wayoyin shi dake riƙe a hannu ya kalla ga dukkan alamu ƙira ne ya shigo. Ɗan siririn tsaki ya ja wanda idan ba kana gaf da shi ba ba lallai ka ji ba. A kunne ya manna woyar cikin fusata murya a daƙile ya furta. "Zanci ubanka Wllh Najeeb akan takura min da kayi!, Wllh idan ka tunzirani zan fasa maka visa'n naga uban da zakay ok" Datse woyar yayi Cike da taku irin na zaratan maza ya fara taku yana nufar cikin hotels ɗin.da sauri driver'n ya mara masa biya da system nashi da dayar woyarsa. A room na daban shima ya sauƙa tare da kayayyakinsa suka zube akan lafiyayyan gado. ZAYD SURAJ kenan ɗa ga Sarkin kano mai martaba SURAJ SUNUSU SHUREIM.

*AK*

Cikin bacci yaji ya soma jin vebration na woyarsa, da ƙyar ya iya buɗe lumsassun idonsa. Idanu ya tsurawa screen ɗin wayar dake ta faman ruri, tamkar me nazartar wani abu haka ya tsira wa woyar kaifafan idon shi. Duk da cewar yasan ZAID bazai ƙirasa haka kawai ba, lallai dole saida wani abu haka nan ya tsinci kansa da faɗuwar gaba. Hannunsa ya miƙa da niyar ɗaukar wayar saidai kafin yakai ga ɗauka ƙiran ya katse. Ɗin Jim yayi yana me tunanin bin ƙiran saidai sanin da yayi cewar mai ƙiran nasa zai sake ƙira ne yasa shi sauƙe ajiyar zuciya tare da fesar da numfashi. Anutse ya tashi zaune yana me tunani acikin zuciyarsa, haka nan Idanunsa da suka dan ɗan tara ruwa ya lumshe saboda tunowa da PAAH tare da Momma'n shi da yayi.

"ZAID EMAAR KUWAIT"

Ya furta a saman laɓɓansa woyar ya jawo tare da mannata da kunnensa. Daga cennnnn Zaid cikin yanayin sanyin jiki ya furta.

" ABDOUL-MALEEK PAPA?" Zaune ya tashi da sauri amma a zahiri ba saurin yayi ba shine a ganinsa yayi saurin. Cikin fitar sautin da yayi low sosae ya furta. "Why? Where is my PAAH"

Shiru daga cennn Zaid yayi, Ak kuma jin shirun Zaid shine ya sanya shi furta. "Ina PAAH yake you will die ko? ka buɗe baki kamin magana Zaid" Ya ƙarashe cikin sautin tsawa

"Ko ɗaya bai mutu ba anyi poisoning nashi ne agant!, wannan tafi ko wacce iriyar gubar da aka saba poisoning nashi da ita. Domin wannan da wuri zata iya zama sanadiyar rasa shi acikin loƙaci kaɗan, matuƙar akayi wasa to tabbas zamu iya rasa rayuwar PAPA gaba ɗaya"

Wani irin sakur zuciyarsa maganan da Zaid ya faɗa mishi yayi, yana jin daidai yake da bugun zuciyarsa acikin kunnuwansa, haka yake jin maganganun na yankar zuciyarsa. Saurin fusgo numfashinsa dake ƙoƙarin kwacewa zuciyarsa yayi ta hanyar furta kalman. "Innalillahi Wa Inna Ilaihirraju'un!!!" da sauri saurin dake tafiya da gudun bugun zuciyarsa ya furta.

"what? My papa his under incapable survive in the world at this condition? oh god tell me the Truth I'm very dangerous twin!"

Jin yadda lokaci daya yanayin dan uwansa twins dinsa jininsa ABDOU-LMALEEK AK KUWAIT ya sanja ne ya sanya. Ya shiga kontar masa da hankali, ganin kamar hankalinsan na kwanciya zai yi bane ya sanya ya shiga fada masa kalma daya takkk. Wadda bansan ko wacce kalma bace itane ta nutsar da AK da kuma lurar dashi......

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________

*MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 29&30

# ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # BEST LOVE

🤍🔥✅

*KUWAIT*

Zazzau ne suke a falon maza da mata kowa ran nan a haɗe wasu ido yayi ficin ficin. Mommah dake dab da ƙafafun MOH JIDDO idanunta sun kaɗa sunyi jazur tana sanye da Alkaybba hannunta rikeda tissue dakuma charbi tanaja, sai wasu daga cikin manyan fada irin su Waziri, Wambai, Makama dakuma Sarkin dawaki, chan kuma saiga wasu Manyan dattawa maza guda biyu sun shigo sun zauna suma, dan faɗuwa gaban Mommah yayi dan haduwan mutanen nan wanda bayan sarki sune masu fada aji a fadan ƙasan Kuwait kasan babban abune, ƙarasowa suka yi tsakiyan ɗakin sannan suka sami waje suka zauna

Zaid ne ya ɗago rinannun eye's nashi tare da duban MOH JIDDO cikin daƙushashshayar murya yace " JIDDO kene kika aika akirani"? Girgiza kai JIDDO tayi kafin ahankali tasa tisssue saman fuskanta tashare hawayen tasss sannan tace "Wambai ne ya aika kazo zaka ƙira musu wannan tantirin ɗan uwan naka"

dasauri yadagokai yakalleta tare da sauran jama'an ɗakin dake kallonshi yace "tooh" anatse waziri ya furta "ƴan uwanka duka sun iso na kusa dana nesa"

Sai kuma ya ɗan yi shiru a tare dukansu ƴan ɗakin suka zubama waziri ido duk kuwa da sunsan YARIMA MALEEK zai ambata amma hakan bai hana su binsa da ido ba. "YARIMA ABDOUL-MALEEK fa"? Ya faɗa wanda iyaka ambatar sunan shi da akayi Saida zuciyoyin wasu daga cikin su ya buga. Adan hankali Zaid ya sauƙe ƴar ɓoyayyen ijiyan zuciya yace "naƙi rashi ba adaddi bana samunshi" salati Al-hussein ya saki cikin babban sauti sosae ya shiga furta "Ban taɓa ganin gantalallen yaro irin ABDOUL-MALEEK ba ohh Allah Ace mahaifinka na ahalin Rai ko Rayuwa amma baka ma san a halin da yake ba" MOH JIDDO ce ta tare shi da faɗi "Dama fa ba jinin MARYAM bane yake yawo a sassan jikinsa, kaima da ɓata baki kake Wllh hussein"

cikin murya mai laushi wamzai ya furta "MOH JIDDO adai yi haƙuri muna a halin ciwo ne" ya faɗa yana rusunar da kansa ƙasss Wani mugun kallo MOH JIDDO tabi wambai dashi wanda suke ƙira da *RIGA DAKI* a yarensu na cennnnn.

Cikin tsana da jin haushi MOH JIDDO ta furta "Ni na rasa mecece matsalan ABDOUL-MALEEK da ya gwammace ya tafi yawon duniya har wata uwa Nigeria akan abbinda ba tabbacecce bane. Shi burin daya ɗauka alƙawarin cika tashin" Ijiyan zuciya Mommah ta sauƙe tana jin wani abu na yawo a dukkan sassan jikinta. "Yanzu ai idan ya riski saƙon mutuwarsa a yanar gizo ya dawo!, nasan duk inda yake aduniyar nan zaiga news na rasuwan mahaifinshi dan haka zamu ganshi idan ya riski saƙon macewar ubansa" Yana faɗin hakan ya tashi yayi gaba abinsa yawuce yafita yanajan ɗan ƙaramin tsaki aranshi bayan yakai waje. Cikeda ɓacin rai MANDOOD ya furta "MOH ve said this time without number to Mai Martaba he should call ABDOUL-MALEEK to order, duk cikin yaran me martaba babu gantalalle kaman ABDOUL-MALEEK, yaƙi zama ya koyi komi na al'addun masarautar mu, sabo da yana jin kansa shi tantiri ne"

_TUN DAGA HAIHUWA MA KUWA_ Domin Abdoul-maleek hadarine malafar duniya,funkasau babban girki, biri da gatarine shi ajalin me gonna, Jan kasa na bayan daki kowa ya ganshi ya tuna Allah. Shi kadangaren bakin tulune a barshi ya fada ruwa a taba shi kuma ya FASA TULU, Ak ginshikin dutse me kowa yayi karo dashi shika fadi, soja mazan fama namijin mazaje an buga dashi an barshi saidai su buga su barshi kuma domain shi din dashen Allah ne, murucin kan dutse be fito ba saida ya shirya_

ZAID ya furta a cikin zuciyarsa ya miƙe yana ficewa a ɗakin shima domin da biyu yaki sanar musu yayi magana da AK din.

haka suka ringa fita ɗaya bayan ɗaya, ɗakin ya rage daga Mommah sai RAZEENERH mata ta farko ga Me martaba sarki *SARKI HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT* Wasu irin kaifaffun hawayene suke saƙƙo mata, cikin ƙunar zuciya da irin raɗaɗin dake ƙona zuciyarta ta kwanto da kanta zuwa jikin Mommah MARYAM. Ta fashe da wani gurgegen kukan ɓakin ciki. "Shin Sai yaushe zamu dena zubarwa da ƙaddara hawayenmu? Sai yaushe abubuwan dake ɓoye zasu bayyana kansu? Na gaji-na gaji NA GAJI MARYAM, inajin haƙuri na na gab da ƙarewa akan abubuwan dake faruwa dani a cikin wannan azzalumar masarautar HABA!" Ta faɗa cikin sake fashewa da wani gursheshen kukun, "Haƙuri shine matakin ko wacce nasara RAZEENERH, Ko wacce Nasarar rayuwa da ɗaukaka kuma suna zuwarma baya ne da tarin ƙalubalen rayuwa salo daban daban, me yasa zamu gaza cinye ɗan takin daya saura a cikin rayuwarmu?. Xuwa yanxu AYSHATUL HUMAIRA a bayyane take garemu loƙaci kawai muke zuwa ya bayyana kansa,Ayi walƙiya Allah ya bayyana mana magautanmu na ɓoye dana fili mu gansu su fito suna hawaye anyi walƙiya!!!"

Sosae suka sha kuka me sunan kuka kafin su runguɗa zuwa ga special room donper ɗin da me martaba yake cikin haɗaɗɗen hospital ɗin masarautar. Dammmmm ɗakin yake tarin ƴan uwa na kusa dana nesa irinsu garin Makka Madina Saudi Arabia dadai sauransu aurarru da ma'aikatan da suke aiki a wojen ƙasar.

Wani gauran numfashin da sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT ya kawo ne ya sanya baki ɗaya katafanin jama'ar parloun, juyowa zuwa gareshi.

ALHAMDULILLAH wasu suka shiga furtawa wasu kuma zuciyarsu na ƙonewa ne tare da yin baƙikirin tun durun da tsabar masifar baƙin cikin da ke soya zuciyarsu ƙurmus. Ahankali ya shiga bin kowa dake parloun da ido, cike da tsananin ƙarfin hali da kuma dauriya irin ta zaratan sarakai ya saki kyakkyawan murmushinsa me kyau. Wanda exactly tsananin kamfaninsa da ABDOUL-MALEEK KUWAIT AK suka gama bayyana. "Alhamdulillah Ban mutu ba Allahu Ya tsare lafiyata a kwanana akwai ƙari don haka kowa ya kwantar da hankalinsa" sarki AL-HASSAN EMAAR ya furta Wanda wannan maganar nashi ya daki wasu ɓoyayyan rufaffun zuciyoyi daga cikin al'ummar denpor ɗin.... Haka kaifafan idonsa yaci baba da yawo har sauke kallonsa akan Ayeshan shi. Kyakykyawara mace karshe a fannin hakuri mace me kamar maza CE ita wajen danne ko wanne irin ciwon cake damun zuciyarta. Da wani sassayan kallo ya bita yanajin lallai rayuwar idan babu ita to shima babu amfanin tashi rayuwar, a jinin jikinta taji irin kallon da take binta dashi.

★★★ Abuja Nigeria

Zaune yake yayi crossing kafafunsa sanye yake cikin shigar kananan kaya na shan iska, loptop ne a gabansa kan dan table tonight din dake gabansa, yana faman sarrafata cikin kwarewa yake latsa keyboards din system din. A nutse zayd suraj shureim ya karaso har inda AK din yake zaune. Zaman shima yayi ba tare daya furta komai ba, haka suka shiga zaman kurame har na tsawon 30 minutes, A nutse Zayd dubi AK da yama nuna tamkar besan anyi ruwan zayd din bane yadan daki shoulder na AK din. Sai kuma ya dan saki wani shegen murmushi domin shima karshe ne fagen tashi izzar Wanda shima sarautar kano ta gama ratsa ilahirin Jinin dake gudana a cikin jikinsa. "Yaryadi baka yadon banza yau kuma dame kake tafe?, ka kirani ka sanya na baro garina zuwa wani garin Right?' Ka kuma shareni abunka to Dan ubanka Wllh zan komawa na domin inada abubuwan yi dana baro ba kamar kai ba" Wata katuwar harara ak ya sakarma zayd yana fadin. "Jeka mana dan uwarka ka gani idan Abbu ko ummieyn Momma basu koromin kaiba" Ya fada a daidai lokacin kuma ya kammala aikinsa na cikin laptop, tashi yayi tare da yin gaba yana fadin. "Idan kaga dama same ni a room na baka 2 mint domin INA shirye shirye bar muku kasarku ne" "Look AK karka ma soma hakan, Don munyi woya da mommah tun a daren jiya ta shaidamin cewar jikin Me mar taba da sauki sosae $0 inaga babu bukatar zuwanka!" Ko ta kanshi ak bai biba saima wucewarsa da yayi room Bayansa zayd yabi cike da shekiyanci yake tsokanarsa ai dole ya bashi girma tunda shine autan su momman ak din. Ganin nan din ma ya share shi ne ya sanya shi komawa seriously tare da furta. "Muyi abinda ya kawo mu kasan akwai Case's da yawa dana tsalallake na baro dude" Charkkk kuwa ak din ya tsaya tare da juyowa ya fuskanci zayd din. Zama sukayi a tsakiyan kayataccen palon hotel din, computer'nshi ya janyo tare dayin wosu yan danne danne said kuma ya juyo da fuskar computer system din xuwa gaban AK.

Da wani black beauty guys ya fara cin karo wanda me sanye cikin kaki na yan sanda. Tsaye yake chark a gaban Cf of the police babu alamun tsoro a tattare dashi. Gani yayi wannan ceef din ya mike a fusace yana duban wannan tsayayyen matashin, kafin kuma cikin fusata ya furta.

_Akan me zaka harbe shi?, Tambayarka nake me yasa ka harbeshi? Me yasa kai baka Iya sarrafa kankane?_ Gani yayi wannan matashin police din ya furta. _Bana Iya sarrafa kainane akan irin wadan nan tantiran yallabai!_ _Kenan saika harbe shi kuma?_ Ceef ya sake furta a tsawace. _Me yasa bazan hukunta wadan da suke barazana wa al'ummarta ba?, nayi rantsuwa da girman Allah zan kare kasata da al'ummata. Akan mene yasa bazan harbeshi bayan shidin gurbatacce a cikin al'ummar?_ Ya fada tare da sarawa a gaban Ceef din. _To hakan ba shine dalilin da yasa muke nan din ba?, muna kamasu mu gurfanar dasu a kotu domin karbar hukunci daidai da abinda suka aikata_ _Tsawon wanne lokaci ake dauka kan a kammala yallabai?_ Wannan matashin ya fada cikin sigar tambaya shima. _muna Iya kaiwa tsawon wata biyar ko kuma ma shekara_ _Kafin xuwan wannan lakacin taya kake Iya bacci?,No bana Iya baccin to yallabai_ Yayi maganar cikin tsananin fushi. _Nima wannan shine dalilin da yasan nake ta bibiyar Tanbuwal, duba wadan nan duka sun aikata manyan laifiku!, duk kuma Wanda ke a cikin wannan kundi suma a kashe su kenan?_ Ye jefawa matashin alamar tambaya. _Kashe sun shine daidai yallabai idan har muka kare ADALCI to daga nan ne shima ADALCIN saiya zama me bada KARIYA a garemu!_

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull