Kenza eBookz

Mutum da duniyarsa complete - Chapter 20

Mutum da duniyarsa complete - Chapter 20

Mutum da duniyarsa complete Chapter 20: Mutum da duniyarsa complete Chapter 20. Yau Aliyu a masallacin k'ofar gidansu yay sallar magriba saboda akwai…

3,368 words

Yau Aliyu a masallacin k'ofar gidansu yay sallar magriba saboda akwai majalisi da sukan shirya Na k'arshen kowane wata da akan gabatar bisa tsarin malam. Masallacin yacika taf da magidanta, samari, harma da tsofaffi, Ana idar da sallar isha'i Sheikh Aliyu yafara gudanar da wa'azi mai taken *DAMI MUKA SHIRYA TAFIYA LAHIRA?* , masallacin yayi tsait, daga muryar malam mustafa dake jan bak'i saikuma Sheikh Aliyu dake fassara cikin tsantsar ilimi da kuma fad'ad'a kowace aya domin a fahimta, lokaci-lokaci mutane kanyi kabbara, jikinsu dukyayi sanyi saboda tsoro, har zuwa k'arfe goma da rabi aka fara karanto tambayoyi. Kafin yabada amsar tambayar farko yacire gilas d'in idonsa yana gogewa da handky d'in hannunsa, cikin sanyin nan nasa yace, "Amin afuwa Zan amsa tambaya uku ne kacal acikin wad'annan tambayoyin, dan akwai tambayar danake da burin amsata anan wadda wani bawan ALLAH ya turomin, to Alhmdllh yace shi ma'abocin zuwa wannan masallacinne, sannan kuma wannan zaman baya wucesa aduk wata, to tambayarsa tanada muhimmancin data shafemu muduka, shiyyasa naza6i amsata anan domin mu farka daga sakacinmu, sauran tambayoyi kuma insha ALLAH zamu tsara yanda za a amsasu koda daga bayane". Take kowa ya aminta da batunsa, dan haka malam mustafa ya karanto tambayoyi uku kacal Aliyu yabada amsarsu daganan Yakoma kan Sak'on da Maimunatu ta sanarmasa d'azun da safe. Saida ya maida siririn farin gilas d'insa sannan yace, "Mai sak'on yana magana ne akan matsala dayake fuskanta gameda rayuwar aure tsakaninsa da iyalansa irinta rauni wajen biyamusu buk'ata a shimfid'a, amma dukda yasan da hakan yaje Yakuma k'ara aure batareda yatashi yafara Neman maganiba. Lallai wannan sakacine mai girma, sannan akwai cutarwa ga iyalanka, tayaya baka iya gamsar da mace d'ayaba sannan kakuma tarkato ta biyu? Sannan babu wani mataki Daka d'auka akan hakan kafin ka k'aro d'in?, tayaya muke tunanin Matsaloli bazasu k'aruba?, ayanzu dukanku nan dazance wanene *Jarumin Namiji?* saikucemin Wanda ya iya rik'e gidansa daci da sha dadai buk'atu nayau da kullum ko?". Atake suka bashi amsa da eh. Aliyu yay murmushi yana gyara zamansa, batareda ya kallesuba yace, "To lallai wannan bazamu kirashi cikakken jarumi ba gaba d'aya, sai dai dolene mu yaba masa wajen sauke nauyin dake kansa na wani 6angaren hak'k'ok'in aure. Jarumin namiji shine mai k'ok'arin tsare dukkan wani hak'i na iyalansa, ci, sha, sutura, wajen zama, ya kula da addinin iyalinsa, yakula da zamantakewarta da makwafta da zumincinta ta 6angaren danginta da danginsa, ya nuna mata soyayyar dazata saka zuciyarta kwanciya waje d'aya batareda y'an wasan kwaikwayo da jaruman littafi na birgetaba, a wajen shimfid'a yazama Oga kwata-kwata yanda za'a ringa kiransa maigida cikeda tsantsar girmamawa, ba yana magana ana kauda Kai da murgud'a bakiba". Dariya suka Sanya, yayinda shima Aliyu yake darawa da kare fuskarsa da hannu. "ALLAH kuwa karkiji wasa, duk k'ok'arin mace wajen iya girki, tsafta da kwalliya daduk wata kisisina inhar batada nagartar kar6ar mijinta a shinfid'a zakaga Mijin baya kallonta da daraja, kuma duk yawan son da yake mata saiya gudu kaga babu komai, saigaka tarasa kansa, takuma rasa ina matsalar takene?. To haka shima namiji duk k'ok'arinsa na karema mace hak'k'ok'inta inhar bashida jarumtar biya mata buk'ata to wlhy zata daina ganin darajarsa da shakkar fad'a masa duk maganar datazo bakinta, da yawan rainin da matayenmu ke mana tushensa shine ragwantakarmu a shinfid'a, kabari basir da sanyi sun gama cinyeka amma kullum idonka nakan y'ay'an mutane, da yarinya tawuce kashiga lasar la66a da had'iye yawu kana mata kallon da addini ya haramta maka, amma matarka dake gidama baka iya biya mata 6uk'ata yanda ya kamata. Akulum matayenmu sunada k'ok'arin gyaran Kansu a kanmu, dan a hasashe babu wanda yakai matanmu k'ok'arin shaye-shayen magungunan nan na k'arin Ni'ima, dukda suma matan ina k'alubalantarsu dan basabin matakan daya dace wajen shan maganin. A mashayinka namai gida daga lokacin da kukai shekaru biyu da aure da matarka yadace kafara neman gyara kanka, danfa kafara komawa cus malam. Kai kanka kazauna ka k'iyasta da watannin farko na amarcinku irin nanuk'ema amarya da kakeyimana, kai abindama yakamata namiji yayi daga shekarar dayasan zaiyi aure yadace yafara dagewa da amfani da maganin sanyi dana basir, dan sune manyan abinda kemana lahani, bakuma komai ke kawosuba sai abincin da mukeci, mutum a yini saiyaci maka abinci Kala kusan goma sha dukshi kad'ai, kuma zaka samesu duk maik'one, tayaya basir bazaiyi ram damuba?, kafara gyara kanka malam tunkan amarya tashigo daga ciki, yanda idan tashigo tajika zam, kanayin magana zatace hakane Alhaji koda bakada ko sisi kuwa". Nanma dariya mutane keyi, samari damasu kunya nata sunkuy dakai, shima kansa malam Aliyun kansa a k'asa yake baya kallon kowa, dama malam bayanan yamayi tafiya. "Ina muku wannan maganarnefa akan gaskiya y'an uwana, domin wlhy sakacin gyara kayinmu yana bada gudunmawa wajen saka matayenmu a masifu Na mad'igo da zinace-zinace ko amfani dakansu wajen samun biyan buk'ata, wata badan kud'i take aikata wad'annan fasik'ancinba, saboda kawai mijinta baya iya gamsar da itane, mace tadage tasayi kayan gyaran kanta tasha babu ko sisisnka Alhaji, kuma dan kawai ta burgeka, buk'atar mijinta ta taso Mata amma dayazo bazai iya gamsar da ita yanda ya kamataba saiyaja gefe, tayaya muke tunanin bazata nemawa kanta mafitaba?, ga masifu da kafafen social network d'innan sukazo mana dasu iri-iri, matarka taje tashiga taganoma kanta masifar dazata dameta kai baka kusa da ita, koma kana kusa bazaka iya biya Mata buk'atartaba Yaya kake ganin za'a k'are? Wlhy inda zaka zama jarumi wajen bata kulawa da kare mata duk wani hak'k'inta a shimfid'a ko soyayyar da suke gani a finafinan banzarnan bazaiyi tasiri agaresuba, dan mace kota gani saitaga ai shirmece, wadda mijinta ke Mata tawuce wannan, tayaya ta film da hikayoyin marubuta zata birgeta balle har tadinga kokwanton anya akwai irin wannan soyayyar kuwa a duniya?. To tasaba Nata Mijin daga mazurai sai matsalar Neman kud'i yasani, wanima saiyakai k'arfe sha biyu a majalissar da ba'a komai saisurutan banza da wofi da nad'oma kai zunubi, lokacin dazai shigo gidan tajima dayin barci, saidai cikin barci taji yana Neman tausheta. Mufa mazan hausawa ko d'an soyayyarnan kafin biyan buk'atama ba iyawa mukaiba, kana zaune mace bazata ra6u da jikinkaba saikunzo kwanciya, data zauna kusa dakai kace batada kunya, wanima ko a wajen kwanciyar dayasamu biyan buk'atarsa to matar tana gabashin gado shikuma yana yammaci, burinka kawai ka kashe gobarar gabanka kakoma gefe. Haba tayaya mace zata yarda akwai soyayya a duniya inba ta film da littafiba? Addininmu babu abinda bai koya manaba, babu Wanda yakai MANZON ALLAH iya soyayya ga iyalansa, miyasa bazamuyi koyi dashiba domin samun farin ciki a gidajenmu, mudaina d'aukar matanmu bayinmu komasu kula mana da gida da yara kawai, ba haihuwa da raino da bautar cikin gida bane kawai aikin mace, baka bata ci dasha da sutura kawai bane yadace dakai, ka nuna Mata soyayya da kulawar dazata ringajin itad'in macece wadda ta isa hamshak'iya, babu birgewa a garemu ace da zarar mun aure mace tayi hauhuwa d'aya shikenan saimuce soyayya ta k'are, waya gaya maka soyayya takare malam? To komin tsufanku soyayya bata tsufa, soyayyar gaskiyama ana girmane tana Kara girma, tomu matsalarmu yawancinmu shawa'a ke kaimu ga aure ba soyayyaba, shiyyasa kwanaki naja matsalolin gidajen aurenmu Na k'ara girma da bunk'asa, amma kullum idanunmu nakan matan waje, kakasa gyara wadda ka ajiye tayaya wadda take a waje bazata birgekaba?. Dan ALLAH yakamata mu gyara, akwai abubuwa da yawa dasuke gyara namiji shima, ba Mata bane kawai keda wad'annan magungunan, akwai wad'anda idan kasha kaikanka zasu motsama jarumtarka ta yadda zaka gamsar da iyalinka, amma maganar gaskiya mu maida hankalinmu wajen Neman maganin basir dana sanyi a farko, insha ALLAHU namuku alk'awarin Baku wasu sirrika a zama nagaba dazai taimakeka wajen gamsar da iyalinka, abinda muka fad'a dai-dai ALLAH kabamu lada, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka hafe mana baki d'aya...................✍🏻

*_Dadai nace bazanyi posting ba, amma ganin nagama typing da wuri nace bara nayi muku kawai_*.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [12/17/2019, 8:52 AM] 💞Noorunnisa💞: *_Typing📲_*

*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*

*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_* _(ya dace ya gyara kansa)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_[39➖40]_*

..............Zuwa yamma lik'is Zazza6i mai zafi yarufe Jiddah saboda ciwon da taji, hannun harya kumbura, Ummace talura danhaka taje inda Jiddah ke a kwance takamo hannun. Y'ar k'ara Jiddah tayi tana rik'e hannun Umma da fad'in "Wayyo Umma akwai zafi". "Yanzu nan ciwo kikaji a hannun Jiddah amma kikayi shiru da bakinki? Yanzu daban kulaba haka zakiyita zama dashi? Ga jikinkinan har zazza6i ya sauka". Hawaye kawai Jiddah keyi takasa magana, tsaki Umma tayi tana mik'ewa, yayinda can k'asan ranta ke k'ara zafafa da lamarin Abba, yau gaba d'aya a cikin 6acin ransa ta yini, kai dukama gidan harsu Balu. Waya Umma ta d'auka takira Uncle yahya, yace yaje Jigawa amma gashinan a hanyar dawowa.

Sai bayan Sallar magriba Uncle yahya yazo damai gyara, sosai Jiddah ta jigata da kukan azaba, ga lalurarta, danma yanzu ALLAH ya sauk'ak'a abun sosai bakamar daba. Ana gamawa aka bata maganin zazza6i Tasha ta kwanta sai barcin wahala.

Umma suka zauna da Uncle yahya bayan mai gyara ya tafi, bayani taimasa akan abinda Abba yazo yayi yau, sosai ran Uncle yahya ya6aci, ananma yake shaida Mata shima yaje nemansa a kasuwa akace yaje jigawa shine yayo nan gidan ya zubar musu da tujarar su. Umma tarik'e ha6a tana fad'in "Anya kuwa Alhaji yanada isashshiyar lafiya Uncle d'insu?". "Wlhy lafiyarsa lau Maman Nafisa, abinda ya shukane kawai yafara girba, dan hak'in yarannan kawai ya ishesa ishara, yanzu haka d'azun Saudah takirani take shaidamin wai yakira mijinta yabashi bashin miliyan ashirin, dan ALLAH Maman Nafisa kijifa zubarwa kai mutunci". Ran Umma a matuk'ar 6ace tace, "Takirani nima wlhy, rasama mizance Mata nayi, dan ni lamarin mahaifinsu yafara fitamin a kai gaba d'aya, jira nake kawai naga yarananan sunsami matsugunni wlhy nak'ara gaba". "Kiyi hak'uri Maman Nafisa, dan ALLAH kibar wannan tunani, ke kamar uwace agaremu, idan babuke wazamu kalla muji sanyi, dagani sai d'an uwana iyayenmu suka Haifa suka Bari, amma kece kika mayemin gurbinsa, idan kin goce ni dawa kuma Zan zauna?". "Uncle d'insu abunne da ciwo, yaufa soyay yamareni gaban Jiddah, badan ALLAH yakawo su Yaruwaiya ba yakake tunanin za'a k'are? Dan wlhy nak'udiri aniyar ramawa daya mareni". Kasama magana Uncle yahya yayi, in banda tafasa babu abinda zuciyarsa kemasa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A police station dai rufe kalifa akayi yanata kuka, kusan a tare suka Isa da Abba, yayi-yayi iya iyawa abashi belin kalifa a sasanta magana amma uban d'an ya rantse sai kalifa yayi kwanan kanta, wasa-wasa har dare Abba yanacan yana fama, sai kusan sha d'aya yabaro station d'in yadawo gida, hankali tashe Hajia Hindu ta tareshi da zancen kalifa, bayani yaymata yay shigewarsa d'aki yabarta tana kuka harda kururuwa. Suma sauran yaran duk sunyi jigum-jigum. Washe gari dai dole Abba yaje makarantar su kalifa, amma Sam principal d'in saiyak'i saurarensa, acewarsa yanzu magana tana hannun hukuma, miyasa lokacin da suka buk'aci ganinsa yak'i zuwa?. Duk yanda Abba yaso nuna musu kud'i abin ya gagara, ga hajia Hindu Nata musu kuka, dan kasa hak'uri tayi saida ta biyosu. Kwasa sukayi zuwa station d'inma, canma Sam ba'a sauraresuba, saida Abba yakashe kud'i sosai kafin aka sasanta magana akan Abba zai biya kud'in asibitin yaron daduk wasu abinda zai buk'ata harya warke, aka kuma yiwa kalifa tsakani da yaron. Sunje asibitin suka duba yaron, Ashe sosai kalifa yaji masa ciwo kuwa, sun masa sannu suka taho abinsu. Aiko wujiga-wujiga suka dawo gida, hajia Hindu ta rungume kalifa tana kuka, hakama su Hassan duk sun rungumeshi da murnar dawowarsa. Kan Abba yai zafi sosai, sannan dagashi har hajia Hindu babu Wanda yayma kalifa fad'a akan lamarin.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A washe gari Uncle yahya yaje wajen malam Abdul-ra'uff suka tattauna maganar tariyar Jiddah, sosai malam yay farin ciki da matso da maganar, dan sun yanke nanda kwanaki uku kacal. Ananma Sheikh Aliyu yazo ya samesu, shima sosai yagamsu dahakan, amma kunya ta hanashi Nuna farincikinsa a gabansu malam. Sai dai shi malam dayasan yanayin d'ansa tuni ya hango farin ciki tattare dashi.

★★★★★

A ranar da yamma kayan gadon Jiddah suka iso, kayane masu k'yau da tsari dakuma tsada gwargwadon k'arfin Uncle yahya, kowa yagani saiya yaba, saidai idan mak'iyi kuwa. Ganinfa abin da gaskene sai jikin Jiddah yakuma sanyi, ga Yaruwaiya tadage sosai take kuma gyarata da tsumata a k'amshi. Sheikh Aliyu yana kiran Jiddah su gaisa, yakuma bata hak'uri akan bazai samu sake shigowaba, dan yayi busy da yawa, ga shirin tarewarta ga walimar musabik'ar dataje Saudia wadda malam yace za'a had'a data aurensu. Ita hakanma sai yay Mata dad'i, dan dama batason yazo yaga taji ciwonan Na hannunta, sannanma dai tafison su zauna nesa-nesan, shiyyasa jitake inama su Umma zasu yarda a kuma d'aga tariyar. Daka ganta kasan tana tare da damuwa, datasamu ke6ewa ita kad'ai sai kuka, ita kanta Umma dauriya kawai takeyi, su Zarah kam duk sunyi wani sukuku dasu suma, kewar Y'ar uwarsu Na matsuk'ar damunsu.

Washe gari aunty zulai dasu Aunty Saudah, hannatu suka iso, dan haka aka rankaya gidan Aliyu yoma Jiddah Jere. Tarba ta mutunci suka samu dagasu aunty Ruk'ayya da Maimunatu, dan bazama kata6a cewa itace kishiryar Jiddanba, yanda taketa hidima dasu abun gwanin birgewa. Dukda gidan Alhaji garba yafi Na Aliyu komai hakan bai hana gidan Aliyu k'ayatar dasuba, dan ba arzik'in bane abin birgewa kawai, zaman kafiya da kwanciyar hankali shine abun buk'ata ga kowacce d'iya mace. Tsarin gidan babu ruwan kowa da kowa, dan kowacce kamar 6angarenta daban zamuce, sai dai bawani k'atun k'atunbafa, dan bawani katafaren gida baneba, yanada dai girmansa gwargwadon hali, kuma tsarin yayi, iri d'ayane da sashen Maimuna, babu wani banbanci saina kayan d'aki, komai Na Jiddah pink and White ne, iya gwargwadon iko dolene a yabama Uncle yahya, kayan gadonta d'aki biyun duk aka zuba, kicinma kam Alhamdllh, saidai mak'iyi. Dayake sunada yawa dandanan suka gama, dan zuwa magriba sun dawo gida, sunata zuzuta tsarin gidan, sun nunama Umma video recording d'in da sukayo, itama sosai ta yaba, dad'i kuma ya kamata, dan yanzune hankalinta ya kwanta da auren d'iyarta. Koda suka nunama Jiddah k'in kalla tayi, saima ta fashe musu da kuka. Aiko dariya suka sanya Mata, ganin da gaske takeyi duk sai jikinsu kuma yay saniyi suka shiga rarrashinta.

Washe garifa dangi suka Fara sauka, zuwa yamma gida yayi taf, dangin Umma danasu Abba, kamar taron farko wannan karonma sai rabuwa sukayi saboda gidan Umma yamusu kad'an. A ranar da yamma kuma aka kawo lefen Juddatulkhair daga angonta Sheikh Aliyu maina, suma ammusu tarba ta girma da mutuntawa, kuma kowa ya yaba da lefen Masha ALLAH, dan saidai mak'iyi kam, abin tamkar bana bazawara ba. Jiddah dai ko tarinta bakaji a gidan, koda su aunty siyama suka buk'aci ganinta k'in yarda tayi, dole suka hak'ura suna fad'in ai dai gobe iyanzu takusa shiga gidansu.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A yayinda ake shagalin tarewar Jiddah kuma shima Alhaji garba yanacan yana shagalin tarewa da sabuwar amaryarsa da aka d'aura aure yau hajia deluwa bata saniba, sai wajen tashin hantsi taga anzo ana kwashe kayan 6angaren Jiddah, dariya tayi sosai tana fad'in "Badole ka kwasheba, da kabarsu su shekara dan itadai tatafi kenan har Abadan". A wajen kwasar kaya masu kwasar sukaci Karo da abinda Hajia deluwa ta sakama Jiddah. Basuyi k'asa a gwiwa ba suka Kira Alhaji garba suka shaida masa.. Mamakine ya kamashi, babu jimawa yadawo gida bayan an d'aura aure, kai kawai yake iya jinjinawa saboda takaici, ko tantama bayayi wannan aikin deluwa ne, wato wannan shine yasaka Jiddah haukacewa idan tagansa, shine kuma yasatake masa wari?. Sakasu yayi suka k'ona, itakuma bai Mata maganaba dan yanzu bashida lokacinta, ta amaryarsa yakeyi wadda takasance gogaggiyar Y'ar bariki, dan hajia bariki ma ake kiranta, tafi hajia deluwa komai, idanma kud'ine itama ta Tara, tadad'e tana nunama Alhaji garba so amma yana shareta, hajia deluwa kuwa sosai ta tashi hankalinta lokacin dataji hajia Rahina bariki Na sonsa, dan shige-shigen malamai taitayi dan kar hajia rahina tashiga zuciyar Alhaji garba. To a yanzu kuma gashi tashigo batareda ta saniba, ko wane irin zama za'ayi😹 kuma🙆🏻?.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Jiddah datasha kuka zazza6i ya rufeta ta kwanta, duk hayaniyar ganin lefe da y'an biki sukeyi sama-sama takejinsu saboda barci dake fusgarta, zuwa wani lokaci barcin yay awon gaba da ita gaba d'aya. Cikin barci tafara mafarki mai ban tsoro, kafin daga bisani tasamu k'arfi akan Wanda suketa dambe a mafarkin, a fili kuwa tajik'e sharkaf da zufa, ga mazari da jikinta kemata. Fannah data shigo domain gwargwad'a Mata lefe da kayan arzik'in da ya sheikh ya zuba ta isketa a wannan hali, jijjiga Jiddah tafarayi tana kiran sunanta, ihunta shine yajawo hankalin mutane sukayo d'akin. Da k'yar aka samu Jiddah ta farka, amma saita Fara wani fisge-fisge da gurnani cikin wahaltuwa, numfashima dak'yar take fisgarsa, daga k'arshema saita sank'ame alamar ta suma. Ummace ALLAH yabama k'arfin zuciyar d'akko magungunan Jiddah da sheikh Aliyu ke bata har yanzu ta zuba turare a rushi, yayinda Maman Sadiq keta shafama Jiddah ruwan addu'oin a fuska. K'ara ta k'walla kafin tafara rawar jiki da zufar dake cigaba da kwararo Mata, bayan kamar mintuna uku saita koma tayi lakwas tamkar ba itaba, saikuma hawaye dake kwarara Mata a fuska. Daga baya kuma barci ya sake kwasheta. Uncle yahya da aka Kira a waya ya k'araso, Koda sukai masa bayani sai sukaga ya d'aga hannu sama yana fad'in "Alhamdullahi, ALLAH mungode maka dakabama yarinyarnan lafiya, ALLAH yasa iyakar wahalar kenan". Tambayarsa suka shigayi, nanfa yaymusu bayanin insha ALLAH Jiddah tasamu lafiya daga lalurarta. Kowa murna yashigayi, saidai Umma Na mamakin ya akayi haka cikin sauk'i? Kodai Uncle yahya ya d'auki wani matakine basu saniba?. Ganin babu mai bata amsa yasa ta hak'ura, tasan idan komai ya lafa zai Mata bayani. Da wannan aka cigaba da shagali.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Dukda Busy da Aliyu yayi haka yasamu ya nemi Jiddah a waya saboda duk yau basu gaisaba, amma saima yaji wayar switch up, dole ya hak'ura dan yasan gobe iwar haka insha ALLAHU tana gefensa.

Baiwar ALLAH Maimunatu, duk yanda kaso gano halin datake a ciki baka isaba, dan ta danne zuciyarta sosai, yayinda kulawa da tattalin da mijinta ke bata ya danne kaso mai yawan gaske Na damuwarta. Harkokinta taketayi, danma laulayi yana takura Mata sosai, batajin dad'in jikinta, dauriya kawai takeyi. Yauma gaba d'aya da daddare bayan yadawo nasiha yayta Mata da lallashinta cikin kalamai masu sanyi da saka zuciya nutsuwa. Hakanne yasakata itama bashi dukkan farin ciki batareda ta d'auki fushi Na tunanin gobe iyanzu yana tare da amaryarsa ba.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨.

Washe gari Jiddah ta tashi garau da ita, wannan Yakuma tabbatarma dasu Umma lallai an dace kam. Yau tunda aka tashi da gyaran jikin Jiddah aka fara, dan sunayin sallar asubahi aka Fara zuba Mata kunshi da kitson Bare-bari d'an asalai (barbarawa😹🤭⛹‍♀), tayi k'yau harta gaji. Sai dai daka ganta kasan batada sukuni, magana kad'an za'ai Mata ta6are baki tana kuka. Y'an uwama saisuka koma tsokanarta, musamman abokan wasa, saisu Aunty Sauda ne ke kareta.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Abba dai duk wannan hidimar da akeyi baya gari, dan tun Randa aka fiddo kalifa daga station suna dawowa yahad'a kaya zuwa Abuja wajen wani Alhaji Sammani Moddibo, abokinsane amma yanzu ya haye dan d'an majalisane a Adamawa, Da Abba yabuga tunaninsa yagama yaga babu wajen mafaka, danya Kira Mijin y'arsa Sauda danya ranta masa kud'i ALLAH ya tak'aita wahala Sauda ta d'aga sannan wayar na agunta, saida yagama fad'ar buk'atarsa sannan tace masa "To Abba ai nice, Ashe dama y'a mace nada amfani da Rana? Ai nazata bazakama ta6a tunamu a cikin y'ay'ankaba balle kabiyo mazajenmu da buk'ata". Batajira cewarsaba ta yanke wayar taredayin blocking d'insama gaba d'aya, shinefa takira Uncle Yahya da Umma ta sanar musu. Wannan Abu da Sauda taimasa ba k'aramin Sosa masa zuciya yayiba, dan haka yashiga tsinarta yana had'a kaya, aranar yawuce Abuja. Harkuma yau da Jiddah zata tare bai dawoba, ya iske Alhaji Sammani bayanan, amma saiya zauna jiransa saiya dawo, dan ance tafiayar kwana biyar zaiyi, to aganinsa dayayi wahala biyu bai dawoba ai gara ya zauna ya jirasa kawai, yama huta da bala'oin daya baro a cikin kano. Auren Jiddah kuwa yana komawa yabiya Alhaji garba kud'insa saiya tsinkashi, danyayi alk'awarin tunda Yaruwaiya taci zarafinsa gaban y'ay'ansa saiya huce akan Umma, sannan saiya shukama Uncle yahya rashin mutuncin da ko'a hanya bazai sake nunashi a matsayin d'an uwansaba.

🤦🏻‍♀Aɮɮa ʍɨҡaҡɛsօռ ʐaʍaռɛ աaɨsɦɨռ?.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*_11:00pm_*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull