Kenza eBookz

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 7

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 7

Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 7: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 7. Se mun hadu gobe inme duka yakaim. Masu comment na…

3,572 words

Se mun hadu gobe inme duka yakaim. Masu comment na gode Sosai Allah yamuku albarka.🥰🥰🥰

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

Page 4️⃣8️⃣

Zeenat ce ta fara farfadowa tana wani irin amai me dauke da jini da nama_nama seda ta amayar daduk wani abinda ke cikinta tsaban yanda aman yaci karfinta seda kaff kuzarinta yakare riketa sosai anty amina tayi tana kiran abu tazo ta gyara wajan daki takai zeenat ta kwanta bacci , fanan na kwance akan kujera har time din bata farfado ba kusan an hour shuru , tun suna san ran tashin fanan nan kusa har tsoro yafara kamasu jinta shuru duk wani abinda zasuyi danta tashi sunyi amma fa shuru , da karfin gaske Mr azaad ke jijjigata duk da haka bata tashi ba lamarin yabasu tsoro seyanzu suka kara danasanin barin zeenat tasha mata jini gashi yanzu taki farfadowa daukanta Mr azaad yayi yakaita bedroom dinshi yakwantar da ita akan bed sannan yarufeta da blanket.zama yayi agefenta hannunsu rike dana juna . ba abinda yake matsar dashi daga gefenta fa ce sallah gudun karta farfado ba kowa akanta har dare fanan shuru ba labari, haka ya gyara musu kwanciya suka kwanta.

Asuba ta gari.

tashi tayi ta zauna tana murza idonta kallonta tayi a dakin Mr azaad kuma babu shi aciki tuna abinda yafaru tayi danna wayarshi da ta gani a kasan pillow tayi karfe 5:40am ta gani batayi mamakin ganin haka ba tashi tayi tashiga toilet tayi wanka da alwala dressing room dinshi ta shiga bangaren jallabiya taje ta dau arche color tasaka yawa yamata ganin hijab dinta tayi akan kujera dauka tayi, tayi sallah tana zaune tana azkar ya shigo ya zauna akan kujera yazuba mata ido harta idar, juyawa tayi ta kalleshi kafin tace " Ina kwana Mr azaad" batayi tsammanin ze amsa ba taji yace " lafiya ! tashi kizo" tashi tayi taje ta tsaya a jikin kujeran da yake zaune , " malama ki zauna mana kin tsaya min akai" zama tayi dan tasan halinshi yanzu se ya fara , bayan ta zauna ne yake tambayarta " ko zan iya sanin fa'idan shan jininki da kika bar zeenat tayi?" bashi amsa tayi da " Mr azaad ka rigada kasan nidin wacece , dakuma abinda nake dauke dashi ina da ya kinin shan jinina da tayi ze iya fitar da maitar ajikinta" cike da gamsuwa da maganarta hadi da kaunarta yace " Allah yasa " ta amsa mishi da " ameen " satan kallonshi tayi suka hada ido itama ita yake kallo gyara zama yayi yace" to miye na kallon kuma " girgiza kai tayi . Kwantar da kanta tayi a kafadarshi ta lumshe ido kamar tana bacci tana shakar daddadar kamshin turarenshi , " fanannnn!" batare da ta Bude ido ko ta tashi ba tace " naam" shafa kumatunta yayi ya dan jashi kadan runtse ido tayi saboda yamata zafi ," fanannnn meyasa kike boyemin abinda ke ranki ?" cewar Mr azaad da har lokacin yana shafa mata kumatu , tashi tayi daga jikinshi ta zauna suna kallon juna tace " Mr azaad miye nake boyewa din ?" kwantar da kanshi yayi a jikin kujeran be sake ce mata komai ba ganin haka yasa fanan mikewa zata tafi bedroom dinta rike hannunta yayi yace " karki tafi please" kaman wani bako haka take kallonshi wai yau Mr azaad ne yake ce mata please anya ba mafarki takeyi ba kuwa, janyo hannunta yayi tafado jikinshi sunfi 5mint kafin ya sauke ajiyar zuciya yace " fanannnn am sorry for all mistakes nasan na miki Abubuwa da dama kiyi hakuri na miki alkawari hakan baze sake faruwa ba " sosai idonta ke fitar da ruwan hawaye tun tana hawaye harta fara shesheka azuciyarta tana godewa Allah da yasa Mr azaad ya gane abinda yake mata ba dede bane dukda bata taba rikeshi arai ba son da take mishi yasa bata ganin laifinshi . rungumota yayi ajikinshi yana rarrashinta dede kunnenta yakawo pink libs dinshi wura mata iska yayi acikin kunne da yasa taji tsigan jikinta ya tashi kafin ahankali cikin rada yace " baby be with me for the rest of my life! I love you " cak duk wata ma gudanar jinin jikinta seda yatsaya yadena aiki na wasu lokuta jin abinda ko da amafarkin wasa bata taba tsammanin ji ba hawayen farin ciki ne yafara saukowa daga idonta runtse idon tayi sosai tana rokon Allah yasa koda a mafarki nake Allah karkasa in tashi , haka ya dinga fada mata daddan kalamai dashi kanshi besan ya akayi ya iya su ba kawai abinda yasani duk abinda yafada mata daga cikin zuciyarshi yafito, rungumeshi tayi gam muryanta na shake tana kuka hade da dariya tace " I love you too Mr azaad inasanka sosai" raba jikinsu yayi ya manna mata kiss a goshi tare da fadin " Allah ya miki albarka my wifey" kallon cikin idon juna sukeyi babu ko kyaftawa hawaye me zafine ya gangaro kuncinta hannu yasa ya share matashi yana girgiza mata kai sannan yace" hawaye bashida gurbi a cikin rayuwarki har inde ina tare dake ! adah nabari kinyi amma banda yanzu domin kuwa inya sake saukowa zan hukuntashi " dariya tayi tana kwanciya ajikinshi tayi lamo .

______ bacci suka koma se 11 suka tashi komawa bedroom dinta tayi sakeyin wanka tayi ta shirya cikin atampa super Holland me purple color se touch din maroon da fari, dinkin doguwar rigace pencil gown me dogon hannu kasan hannun an mishi play wuyan rigar kuma adan bude yake batayi kwalliya sosai ba kawai powder tashafa se kwalli da libstick , dankunne da sarka tasa na gold tayi dauri me v feshe jikinta tayi da turarurruka masu dadi dakuma sanyayyar kamshi hills tasaka a kafarta maroon sak tafito a amarya tayi kyau sosai kamar wacce zataje gasar kyau gashi kayan sun matseta nafitan hankali duk wani shape dinta seda yafito fili . yau fess takejin ranta ji takeyi babu wanda yakaita farin ciki a irin wannar rana saboda wanda take matukar so shima yana santa, kallon kanta tayi a mirror ta kashe ido daya tare da fadin " excellent" knocking tayi yabata izinin shigowa, samunshi tayi yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya three quarter dark blue yasa da kuma riga armless baka waya yakeyi da yaseer dake tambayar shi jikin zeenat kamshin turarenta ne ya sanar dashi isowarta kallonta yayi da narkakkun idonshi kasa magana yayi kawai yayi hanging din kiran murmushi dauke a fuskanta, tafiya takeyi ahankali kamar wata me tausayin kasan, har izuwa lokacin be kawar da idonshi akanta ba cike da kissa ta zauna agefenshi ta shagwabe fuska tace " Mr azaad wannan kallon fah?" cize libs dinshi yayi kafin yace " to laifine dan na kalli matata?" rufe fuskanta tayi ajikinshi tana dariya dagota yayi yatsurawa libs dinta ido dayasha man baki matso da fuskanshi yayi daff danata ahankali ta lumshe manyan idanunta,hade bakinsu yayi waje daya yasakar mata hot kiss sannan yadago yana kallonta yace " baby kinyi kyau sosai" dadi ne taji yarufeta jin yabon daya mata tana kokarin yin magana sukaji anyi knocking tare da fadin " sir your food is ready" beyi magana ba sukaji alamar wanda yakawo abinci ya fita tashi sukayi sukaje falon sukayi breakfast.

Haka suka kasance cikin farin ciki a wannan rana har dare suna part dinsu suna soyewa ( ohhhhh su Mr azaad an fada tarkon love) wanka tafito tana daure da towel daya tsaya mata a cinya zama tayi agaban mirror shi , lotion dinshi me dadi tashafa tare da perfumes dinshi yana kwance akan bed ya zuba mata ido duk wani motsinta akan idonshi yana binta da mayun idonshi duk inda tayi idonsa na kanta surar jikinta yana matukar daukan hankalinshi, tashi tayi ta nufi hanyar barin bedroom din kasa_kasa yace " ina zakije " waigowa tayi tana murmushi tace " Mr azaad zansa kayane sannan in hada mana dinner" gyada Kai kawai yayi ta fita a dakin , sleeping dress tasa rigar doguwa ce har kasa white color silky gown , hula tasa akanta dan bako yaushe takeson farin gashinta awaje ba ( matan aure da yan mata kudena barin kanku abude saboda shedanu kuma haramun ne inma bazaki iya daura dankwali ba ga hula nan sekisaka akanki barin kai abude bashida kyau ko kadan wasu kam ma ahakan suke shiga bandaki batare da hula ba to ku kiyaye Allah yakyauta) kitchen tashiga tama rasa me zata musu fast food fridge tabude gashashiya ta dauka tayi musu peppe chicken se ta soya chips data gama ta jerasu akan tray da su drinks , knocking tayi " come in" kawai yace mata , ajiye tray din tayi akan center table tayi saving dinsu batare da ta kalleshi ba tace " Mr azaad food is ready" tasowa yayi yazauna, cin abincin takeyi cikin nutsuwa ji tayi kamar ana kallonta yasa tajuya suka hada ido kayittaciyar murmushi ya sakar mata mayar mishi da murmushin itama tayi sannan tace " Mr azaad meyasa bakacin abincin ?" kallon abinci yayi ya kalleta kafin yace " to ki gama ci sekiyi feeding dina" dariya yaso bata yanda yayi kamar dan karamin yaro ajiye spoon din tayi tadawo gabanshi tazauna sa hannu tayi acikin plate din kazan ta gutsura takai mishi baki,karba yayi tare da hadawa da yatsanta daya " wayyo Mr azaad zaka cinye min hannu" murmushi kawai yayi bece mata komai ba,haka tadinga bashi abaki yana hadawa da hannunta har ya koshi yasha drinks itakuma ta tattara komai takai kitchen bata dawo ba seda ta wanke komai tukun ta maidasu wajan zamansu , bedroom taje tadau dogon hijab kasancewar kayan bacci ne ajikinta tasa slippers tashiga bedroom dinshi ganinta da hijab ne yasa Shima ya mike dukda besan ina zata ba riko hannunta yayi suka bar part dinsu, part din ummi suka shiga bakowa direct bedroom din zeenat suka shiga . _____ a can kuryan gadon suka sameta ta dukunkune awaje daya ta hada kanta da guiwa waje daya tayi shuru hawa gadon fanan tayi ta dafata a firgice ta dago tana kallonta rungumeta tayi tana kuka " nagode sosai anty fanan Allah ya biyaki da gidan aljanna kimin abinda bazan taba mantawa dake ba " shafa bayanta fanan takeyi tana fada mata kalaman da suke kwantar mata da hankali raba jikinsu tayi tazauna suna kallon juna fara magana fanan tayi " zeenat ki saki jikinki kinji kidena boye kanki yanzu fadamin yaushe kika tashi ?sannan kuma kinajin akwai alamar wani abu ajikinki?" girgiza mata kai zeenat tayi tace " yanzu ina jina kamar wata yantattiyar baiwa da aka yanta,banajin komai atare dani yanzu ! dazun natashi daga bacci yanzu kusan awa 3 kenan" shafa fuskanta fanan tayi tace " in sha Allah kin rabu dasu kenan da izinin Allah" Mr azaad tunda suka shigo yazauna akan kujera yake binsu da ido bece musu komai ba se godiya yakewa Allah aransa da yasa be rabu da fanan ba itadin seyanzu yagane ita din mahadin rayuwarsa ce tundaga lokacin da tafara haduwa dashi taimakon shi da family dinshi takeyi tabbas su masu saa ne da suka samu yar baiwa atare dasu kuma me daraja wacce tasan daraja , bashi da bakin da ze mata godiya shisa a kowani awa, a ko wani minti , a kowani dakika santa kara karuwa yakeyi azuciyarshi ,san rayuwa da ita na har abada yakeyi sede kuma kash hakan ba me faruwa bane. zeenat da batasan tare suka shigo da Mr azaad ba cikin yar zolaya tace " anty fanan ina heartbeat dinki kika baroshi kikazo nan?" hannu fanan tasa tana nuna mata inda Mr azaad yake ware ido tayi tana " yaya yaushe kashigo?" yar dariya yayi dan yanda ta zare idon kamar wacce taga abin tsoro be bata amsar data tambayeshi ba yace " yanzu kam babu abinda kikeji ko?" gyada Kai tayi watsa mata harara yayi nan take ta bashi amsa da " eh ya azaad babu abinda nakeji" " good ".

Se munhadu Monday inda rai da lafiya.

Masuyin comment na gode Sosai wayanda Kuma sukeyin comment da yanzu haka kurum suka dena ko sun karanta bame cewa kala bayan Kuma da suna comment Kuma sannunku da kokari kunji nace sannunku 🤔 yanzu kunzama daya da wayanda basayi.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

Page 4️⃣9️⃣ & 5️⃣0️⃣ suna kokarin barin dakin zeenat Abba da ummi suka shigo dubata , ganin su adakin ne abba yace " Kuna nan kenan ? fatima ya kikejin ki yanzu fatan ba wata matsala ko?" amsawa fanan tayi da " eh abba bakomai" kanta a kasa zama ummi tayi akan gadon tana magana da zeenat kafin ta juyo gun fanan fuskanta da dan damuwa tace " my feena Allah ya miki albarka, tabbas ke alkhari ce acikin rayuwarmu bamuda bakin da zamu gode miki kedin ya ta garice " wasa kawai fanan takeyi da yatsunta tana sakin murmushi dan taji dadin adduah ummi, Mr azaad yana zaune yana binsu da ido seyaji sun matukar burgeshi haka zalika abba ganin irin kaunan dake tsakanin ummi da fanan duk da sudin sirkanun juna ne . ( Yanada kyau ya kasance tsakanin ki da uwar mijinki ko matar danki akwai kyakyawar mu'amula , bakomai yake kawo hakan ba fa ce kyautatawa Koda uwar mijinki bata wani sonki ke yakamata kisamo hanyar da zata fara kaunarki domin kyakyawar mu'amula da ita ze kara miki mutunci da kima a idon mijinki barinma yaga yanda kike kyautata mata ,girmamata, koda yaushe kidinga bata girmanta yanda zakiwa mijinki biyayya itama kiyi mata tunda ita ta haifeshi har ya auroki to kinga kuwa bazeji dadi yazama bakya mutunta uwarshi ba , rashin kunya banaki bane barinma da uwar miji wasu ko kadan basa ganin mutuncin surkan su a zo a ta kana nan maganganu , yanda bazakiso a rena mahaifiyarki ba karki rena mahaifiyar wasu Kuma hakan shizesa batare da bata lokaci ba ki fara fita aran mijinki da kuma family shi har azo ana maganar zaa hadashi da wata ya aura tunda ke kin renasu. Abinda zakiyi domin siye zuciyar dangin miji shine yawan kyauta inde kinada hali kidinga musu kyauta ko bama na wani abu ba wata rana de kiyi girkinki me dadi ki tura musu, sannan kowa kidinga bashi respect yanda yakamata, babu ruwanki da sa kanki a kana nan maganganunsu koda kinji kowa na tofa albarkacin bakinshi kija naki bakin kiyi shuru dan yanzu abin magana baya kadan abinda zaki tofa daban abinda zaa canza kince daban tsakaninki dasu Allah yakyauta bawai kuma hakan na nufin ba ruwanki da damuwar family bane ah ah. Se abu na gaba ziyara musamman ma mahaifiyarshi , wannan de sune kadan daga ciki. Se kuma uwar miji in danki nada mata babu ruwanki dasu babu sa ido dakuma korafe_korafe kikama girmanki yanda sirkanki bazata samu hanyar renaki ba , karda kidinga nuna mata kyara hakan zesa taja baya dake dakuma family.) Sallama suka musu suka koma part dinsu hanyar bedroom dinta tayi yariko hijab dinta har cikin bedroom dinshi dariya takeyi ganin yanda ya kwabe fuska barinta yayi yashiga toilet yayi wanka fitowa yayi yasamu bata dakin shiryawa yayi ya hau gadon ya kwanta batare da ya kashe light din ba . dauke da sallama a bakinta tashigo hannunta rike da cup din coffee yana tiriri tana sanye da hijabi dogo ajiyewa tayi tazauna agefenshi tace " Mr azaad ga coffee" bece mata komai ba yadauka yafarasha da ya gama yakoma ya kwanta lura tayi da yan maganan basa kusa cire dogon hijab din tayi wasu sexy outfit ne ajikinta wayanda da su da babu duk daya mini skirt take sanye dashi na roba daya tamketa tam se rigarshi yar karama kamar vest gashinta tayi donot dashi atsakiyar kai jikinta se tashin kamshi yakeyi , arba yayi da kyakyawan surarta yana daga kwancen be mike ba yamata alama da ta kwanta ajikinshi hakan tayi , tayi lamo ajikinshi idonsu alumshe rike kugunta yayi dakyau sannan ya sa hannu ya warware donot din datayi da gashinta dan yafison su ahaka zubowa gashin yayi yarufe musu fuska mirginawa yayi da ita takoma kasa shikuma yamata rumfa da faffadar kirjinshi kare mata kallo yayi daga sama har kasa lokaci daya yaji kasala yarufe shi murya a shake yace " baby irin wannan kwalliya haka za ki barni kuwa ?" Yar murmushi tayi daya kara mata kyau tace " Mr azaad......" Yatsanshi daya ya daura akan libs dinta hadiye abinda zata fada tayi girgiza mata kai yayi yana fadin " shiiiish ! daga rana kamar ta yau karki kara kirana da wannan sunan banaso" " tom Mr azaad mezan kira ka dashi ?" dafe goshi yayi yana " oh my God" kunshe dariyar da yake kokarin fitowa tayi dan tasan metayi , rike habarta yayi yace " nace miki banason wannan Mr azaad din " tsayawa tayi tana kyafkyafta mishi ido kamar bata gane me yake fada ba kafin tace " Mr azaad na gane me kake nufi amma ai bansan dame zan kiraka ba" tsura mata mayun idonshi yayi lumshe idonta tayi dan bazata iya kallon cikin nashi idon ba sake daga habarta yayi yace " ki kalli cikin idona fanannnn" kamar wata qadangaruwa tafara girgiza mishi kai magana yakara mata " meyasa bazaki kalla ba? in harde na isa dake ki kalli cikin idona " babu yanda ta iya haka ta dago ta kalleshi ido cikin ido , jitayi jikinta yayi sanyi sosai kallon cikin kwayar idonshi ya kashe mata jiki lumshe idanu tayi kamar wata me jin bacci tace " na kalla habiby" , manna mata kiss yayi a kumatu jin sunan data kirashi dashi, sunce igiyoyin rigar yafarayi ta baya yafara shafata shuru tayi tana jin abinda yake mata, cire mata rigar yayi ya zubawa dukiyar fulaninta ido sa hannunta tayi ta rufe ido dan kunyanshi takeji musamman yanda taga yazubawa kirjinta ido, rufe su yayi da bargo yana wasa da ita, fanan so takeyi yayi sex da ita amma taga bedama alamar hakan kasa shuru tayi kasa_kasa muryanta a narke tace " Mr azaad kaban hakkina yau ina bukatarka" dakatawa da romancing dinta da yakeyi yayi yazubawa kyakyawar fuskanta ido jin maganar da ya fito daga bakinta yamutsa fuska yayi kamar bazeyi magana ba kuma can yace " baby you're to young bazaki iya daukana ba ki bari nan gaba inkin kara girma kinji" sosai kalamansa suka batawa fanan rai jin wai she's very young, mikewa tayi ta lullube jikinta da blanket din tabar mishi dakin , bedroom dinta tashiga tasa key ta rufe toilet tashiga tayi wanka tasa wani kayan baccin ta hau gado tayi adduah bacci takwanta duk ranta a dagule . Rike kai yayi ganin babyn nashi tayi fushi ta tafi , ita bazata gane me yake guje mata ba tayi yarinya sosai tausayinta yakeyi yafiso ko da zeyi wani abu da ita seta kara girma tunani yakeyi taya ze lallasheta sannan ya fahimtar da ita, yanda yake sonta bazeyi abinda ze sa tasha bakar wahala ba, haka jiki asanyaye yatashi yayi wanka yanufi bedroom dinta knocking yayi tana jinshi taki tashi balle ta bude mai haka har ya gaji ya koma nashi bedroom din gaba daya yayi abin tausayi.

Tun datayi sallah asuba bata koma bacci ba seda ta gyara musu part dinsu ko ina yana daukan ido da kuma kamshi dawuwa yayi daga masallaci yasameta tana kunna burner tsayawa yayi akanta yayi shuru , dagowa tayi fuska ba yabo ba fallasa tace " Ina kwana Mr azaad?" be taba ganin ta canza fuska ba sede in kuka ne tayi amma ganin yanayinta nayau yasake tabbatar mishi da jiya kwana tayi da bacin rai kuma shi bawai yafadi maganar dan yabata mata rai bane, numfashi yaja sannan ya furzar yace " wifey fushi kikeyi da ni ne?" cigaba da abinda takeyi tayi batare da ta kalli inda yake ba tace " ah ah" " to in ba fushi kikeyi dani ba meyasa jiya kika tafi kika barni gashi yau mood dinki ba kamar yanda nasani ba?" cewar Mr azaad dake zama a gefenta gama kunna burner tayi bata tsaya bashi amsa ba ta wuce bedroom dinta ta kwanta dan maida baccin safe , yau de Mr azaad ji yayi kamar yasa ihu dan yarasa yanda zeyi ya shawo kan fanan ta hakura duk wani abu dakuma hakuri yayi amma daga bayama dena mishi magana tayi sede tadinga binshi da ido kamar batasan abinda yake fada ba. badan komai fanan ta mishi haka ba se dan tasan inde bayasan bacin ranta ze mata abinda take bukata domin hakan shine babban abinda takeso ta aiwatar kafin ta tafi amma shi baze gane bane hakan ba karamin taimaka musu zeyi ba .

After one month.

yau wata daya da rasuwan mansoor,haka kuma saura wata biyu da sati uku auren fawwaz da suhaima.

Mr azaad yanzu duk ya susuce kwata_kwata fanan ta dena kulashi dan bayan abinda yafaru a wannan ranar ta yafe mishi sunci gaba da mu'amularsu ranar da ta nuna tana bukatar shi nan ma yasake fada mata abinda ya fada mata kwanaki tunda ga wannan ranar ta canza mishi , haka ya koma kamar wani mara lafiya ita kanta daurewa takeyi ji tayi bazata iya cigaba da shareshi ba saboda bashi take horarwa ba kanta take horarwa.

Readers Also Read