Kenza eBookz

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 9

Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 9

Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 9: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 9. A tsaye suka samu ya usman da yarinyar akan yayantan…

3,531 words

A tsaye suka samu ya usman da yarinyar akan yayantan doctor kuma yana dubashi shima kanshi yaro ne matashi da be wuce shekara 19 ba fari kyakyawa suna kama sosai da kanwar tashi yana kwance yana baccin wahala zama sukayi akan kujerun dakin kallon yarinyar doctor yayi yace " Yan mata ki kwantar da hankalinki yayanki ze samu sauki da izinin Allah kinji" murmushin yaqe tayi shikuma ya fita , mama ce tace " zo nan yata " ita se yanzu ma ta lura dasu dan dazun da tashiga tsaban hankalinta baya jikinta bata wani lura dasu ba jiki asanyaye taje wajan mama ta tsuguna har kasa da siririyar muryanta tace " mama gani" wani irin dadi mama taji jin yarinyar ta kirata da mama lokaci daya taji hankalinta ya kwanta da yarinyar gyara murya mama tayi tace " meye sunanki ? Su waye ku?Kuma sannan ina iyayenku?" Share kwalla yarinyar tayi tace " sunana hairah ! Yayana kuma sunanshi hafiz mu yan garin gombe ne iyayenmu sun rasu wata 9 dasuka wuce, kuma tunkafin su rasu dama bamuda kowa tom dama babanmu ne yakeyin sanaar dako yake siya mana abinda muke sawa cikinmu se yazo yarasu bayan ya rasu da sati daya mamanmu ma tarasu , tundaga lokacin komai ya canza mana bama samun abinda zamuci se nayi mana bara tukun wata rana mu samu wata rana kuma mu kwana haka shine yayana yashiga kasuwa shima yafara yin dakon inya samu kudi se ya siya mana waina ko kuma rogo ko garin kwaki shine yazo yafara ciwo wani mutum dayake hayan will bairon agurinshi ya kawo shi asibiti tunda yazo sau daya be sake dawuwa ba babu kudin dazaa dubashi shisa likitocin babu wanda yakebin ta kanmu " ta gama magana tana kuka me tsuma zuciya sun matukar tausayawa rayuwarsu domin yaran sunga rayuwa ba uwa ba uba dole su wulakanta tunda babu dangin iyayen , ga ta mace kuma karamar yarinya riko hannunta mama tayi ta zaunar da ita a gefenta tana lallashinta fanan dake gefensu ta zubawa hairah ido tana kallon tsantsan kamarsu da khairaty amma tayi murna da faruwan hakan , ya usman de ya kame akan kujera se faraa yakeyi kamar wanda aka mishi kyauta da kujeran makka yanata kallon hairah ,Mr azaad shi abun ya usman ma dariya yaso bashi ganin irin murmushin dayake sakewa tsaban abinda yake nema yasamu. Baba ne yace" mamansu kuje gida mazan zasu zauna da shi ku dauketa kaima usman tashi ka bisu tunda kaji lafiyar dole ja'iri kawai " tunkafin yagama magana ya usman ya mike riko hannunta suhaima tayi duk suka fito dasu ummin sukayi gidansu fanan din a falo suka yada zango fanan kuma takai kanta dakinta tana yar dingisa kafa binta da kallo mama tayi dan tun zuwansu ta lura da tafiyarta murmushi ta sake kawai , nunawa hairah bathroom suhaima tayi ta shiga tayi wanka sosai, tafito sanye da dogon kodadden hijab dinta na roba ,masha Allah itama ba laifi dukda yanzu ta fara tasowa amma tana da sura me kyau, riga da skirt din atamfa suhaima ta bata sabo dal dan tunda ta karbosu agun dinki kala biyar taga duk sun mata kadan ta ajiyesu shine yanzu ta bawa hairah daya ta ajiye mata sauran , das kayan suka zauna mata ajiki be kamata ba tayi kyau sosai shafa mai tayi kawai ta zauna can nesa dasu duk a takure take se dar_dar take ganin haka yasa fanan ce mata " hairah ki saki jikinki damu kinji kidauke mu kamar yan uwanki na jini karki dinga dar dar daga yanzu kinzama yar gidan nan saboda haka feel free " godiya tayiwa fanan sosai harda kwalla , shigowa dakin zeenat tayi hannunta rike da plate din abinci tuwon shinkafa da miyar kubewa bushashshe yaji kifi banda hade da nama se kamshin man shanu yake, lokaci daya fanan taji yawonta ya tsinke mikawa hairah plate din zeenat tayi da ruwa , tana kokarin zama fanan tace " yau naga wariyar launin fata zee nizakiwa haka ?" Cike da mamaki suke kallonta musamman ma zeenat duk tunaninta tayi mata wani laifin ne tace " anty fanan mena miki?" Bata fuska fanan tayi tace" ni shine bazaki dibo min abincin ba ko " kallon juna suhaima da zeenat sukayi kafin suka fashe da dariya harda tafawa hada baki sukayi wajan fadin " kice mun samu karuwa " dalla musu harara fanan tayi da dara_daran idanunta tace " banason iskanci kun fara ko ?" Haka sukata tsokanata tayi banza dasu kiran layin Amira tayi ta tambayeta ko tana gida , daka tsalle amira tayi tace " besty kinzo gida kenan ?" eh kawai fanan tace mata ta kashe wayar aikuwa kafin kiftawa kawai sukaji yo sallamar amira shigowa tayi tazauna tana kallon besty nata da suka kwana biyu basu hadu ba tun rasuwan mansoor dasuka je musu taaziya " ohhh besty kina nan abun ki gaskiya bakida kirki " cewar fanan " sorry besty kinsan yanda abu suka hade min se a hankali ga school ga asibiti abin ba sauki" bude baki tayi zatayi magana wayarta yafara ringing miko mata wayar hairah tayi se anan ne amira ta ganta tace " woww suhaima aina kuka samo wannan beautyn ko de su zeenat ne suka zo da ita?" tayi maganar tana sake kallon hairah da kanta akasa ta gaisheta takoma ta zauna suhaima ce tace " bakisanta bane itama kanwar muce" kin daga kiran fanan tayi ganin bakuwar special number batasan nawaye ba , five 5 digit din last number ya kare da 99999 seda aka kira kusan sau uku kafin ta daga tasa akunne tayi shuru daddadar muryanshi me tafiya da Kuma ratsa mata jijiyoyin jikine taji ya sauka mata akunne yana " hello " nauyayyar ajiyar zuciya tasauke wanda yasa suka dago suka kalleta tace " assalamualaikum habiby " suhaima, zeenat,amira tsaban shakiyanci har suna hada baki wajen cewa " awwwwwwwwn ! Habiby" hade da shewa pillow fanan ta wurga musu hade da harara sannan tayi kwafa shagwabewa tayi tace " habiby ka gansu suna tsokanata ko ?" Jan numfashi yayi kamar wanda yaci yaji lokaci daya yaji ta tayar mishi da hankali idan tana mishi wannan shagwabar kawai daurewa yakeyi dan shi kadai yasan yanda yakeji katse kiran yayi , tabe baki tayi tace " Allah zanyi maganinku kafin in tafi " kiran hairah tayi ta zauna akusa da ita tadinga janta da labari dan tasamu tasaki jiki , Bayan 30mint har lokacin basu fito ba suna dakin suna hira gani sukayi an yaye labuyen bedroom din , Mr azaad ne tsaye ajikin kofa fuskan nan adaure tamau duk seda sukasha jinin jikinsu lokaci daya suka nutsu suka shiga taitayinsu hatta ita fanan din . " Wato matar tawace kuke tsokana ko?" Kamar zasuyi kuka suka girgiza kai alamar ah ah watsa musu harara yayi kafin yayi kwafa inda fanan take yaje yasa hannu yadauketa cak yayi hanyar fita falo mutsu_mutsu tafara ganin abinda yake shirin aikatawa tasan akwai mutane a falon yazataji in suka gansu haka ahankali tace " habiby kayi hakuri ka saukeni kasa zan iya tafiya da kaina" ko sauraranta beyi ba suka fito falo babu kowa afalon duk sun watse mama da ummi suna daki suna hira, gauron numfashi ta sauke tana godewa Allah .

Be sauketa ako ina ba se a motar yaja suka hau kan titi , cikin nutsuwa yake driving zubawa kyawawan fuskanshi ido tayi tana kallonshi cike da so da kauna, batare da ya kalleta ba yace " baby wannan kallo haka ?" tace " to ai bana gajiya da kallon kane " cize libs dinshi nakasa yayi jiyayi magana ma kadai idan tayi kara ingizashi take bece mata komai ba ya nufi migration office barinta yayi a motar yashiga ciki after some few minutes yafito hannunshi dauke da envelope daura mata yayi akan cinya ya tada motar suka dau hanya bata ko dauki envelope din ba saboda bece mata komai ba yanda yadaurashi hakan tabarshi kallonta yayi yace " open it" sa zara_zara chocolate color yatsunta tayi ta bude passport da visa ta gani nata daduk wani abu da mutum yake bukata inzashi abroad duk akwai jujjuyasu tayi a hannunta kafin ta kalleshi tace " habiby to sukuma wannan fah tafiya zamuyi ?" driving dinshi kawai yakeyi be kalli direction dinta ba ya gyada mata kai, bata sake cewa komai ba ta maidasu ta rufe , cikin makay shawarma suka shiga yayi packing motar fita yazoyi tarike hannunshi tace " habiby nide bazaka barni nidaya anan ba " matso da kanshi yayi ya manna mata kiss a libs dinta yace " bazaki iya tafiya ba kibari inje in fito" kwabe fuska tayi tana kokarin yi mishi kuka bayanson ta tayar mishi da rigima yasa yafito yazo yabude mata itama tafito duk idon jamaa yadawo kansu se kallon akeyi saboda sun burge jamaa sosai musamman ma wayanda suka ganesu , rikota sosai yayi ajikinshi yanda bazataji zafi sosai ba intana tafiya dukda tanajin zafin ba sosai ba haka ta sake daurewa tana hada tafiyanta. makay shawarma babban joint ne a gombe yana da girma dakuma kyau sosai babu abinda babu a ciki , rike hannunta yayi suka fara tafiya har ciki wajan shopping tsayawa yayi yace ta dauki abubuwan da take bukata side din su perfumes taje ta diba masu kamshi da dadi hade da lotion's se shower gel, body spray, mouthwash, sannan takoma kan kayan kwalama ta dibe chocolate sosai da ice cream security wajan ne yariko keken kayan yatura har wajan yin bills ATM ya bada suka cire kudinsu suka hada musu komai a leda karba security yayi akasa a bayan motar suka shiga suka tafi duk tunaninta daga nan gida zasuyi setaga ya sakeyin packing a yahuza suya yafita ya karbo nama da yogurt dinsu masu matukar dadi .

Agajiye de suka dawo gida fanan duk ta gaji jira kawai takeyi taganta akan gado , bude motar yayi yadauketa cakk yama daya daga cikin securities dinsu alama da ido ya kwaso kayan cikin motar yabisu dashi har part din su direta yayi akan bed dinshi ya koma falo ya karbi ledojin ya ajiye akan kujera, cire rigar jikinshi yayi wannan hadaddiyar surar nashi ya bayyana especially his 6packs and muscles amurde suke bathroom yashiga ya sakarwa kanshi shower yafito daure da karamin towel a kugunshi se dingan ruwa yakeyi tana zaune akan gadon yanda yafita yabarta haka yasameta sede ta cire hijab din jikinta ta ajiye a gefe jin yanda ya dameta wajanta yanufa yahau kan gadon ya kwantar da kanshi akan cinyarta ya lumshe ido kamar mejin bacci sa hannunta tayi ta cusa cikin gashinshi tana yamutsawa hade da shafawa burgeta gashin yayi musamman da ruwa yajika shi se yayi wara_wara gwanin burgewa, duk abinda takeyi yana jinta beyi yunkurin mikewa ba ahankali hankali reaction dinshi yafara canzawa , rike hannunta dake kanshi yayi yadawo da hannun kan faffadar kirjinshi dake dauke da kwantaccen suma baki me laushi yakwanta luf , batayi tunanin wani abu ba tafara shafa kirjin nashi musamman inda gashin yafi yawa kasa hakuri yayi yadaura hannunshi akan dukiyar fulaninta yafara yawo dasu da sauri ta cire hannunta akirjinshi tana kokarin mikewa dan bata shiryawa hakan ba a irin wannan halin da take ciki bata manta da bakar azaban datasha jiya ba qin dagata yayi yasa hannu yamaida ita ta kwanta ya mata rumfa dede kunnenta yakawo face dinshi yace " wifey where are you going to? karki tafi ina bukatarki akusa dani" sake tsorata fanan tayi jin yanda muryanshi one time ya canza ga idonshi dasuka rine suka canza kala mutsu _ mutsu tafara mishi hade da kuka runtse ido yayi dan bayason jin kukanta har cikin ranshi yakejin hakan dagata yayi yace " am sorry wifey bawai wani abu zan miki kawai bacci zamuyi " ba ta yarda da maganarshi ba ,gani takeyi kamar ze sake mata abinda yamata jiya , yasa ta maqe kafada, dafe goshi yayi ahankali yafurta " oh my goodness" tashi tayi tafara tafiya tana bin bango taje wajan kujeran tadubo ledar naman daya siya hade da yogurt dan yunwa_yunwa tafaraji dawuwa tayi inda yake tabude ledar kamshin gashashiyar naman kaza dayasha kayan hadi ne yadaki hancinta ,cike da nutsuwa tafaraci tana hadawa da yogurt din harta koshi zuba mata ruwa yayi a glass cup yayi yabata tasha tayi hamdala ta koshi qat. Mikewa tayi dan tanason tayi wanka , dakyar takai kanta bathroom dinshi tashiga tayi wanka tafito sanye da rigar towel fari kal samunshi tayi ya kishingida da pillow kanshi na kallon sama damuwa karara ya bayyana akan kyakyawan fuskanshi ganin yana kokarin sauke kanshi ne yasa ta dauke kanta daga gareshi tazauna a gaban mirror tashafa lotion dinshi da perfume ta shiga dressing room dinshi , dubawa takeyi ko zataga wani kana nan kayanshi dazata samu su mata dede dan qiwiyan komawa nata dakin takeji, idonta ne yasauka akan wata trolley me kyau sosai pink color burgeta yayi taji tanason ganin meye aciki durkusawa tayi tasa hannu ta bude akwatin kayan bacci ne kala kala aciki sunfi set 30 masu kyau da daukan hankalin duk wani da na miji daukan na farkon tayi ta bareshi a ledarshi , wata yalolon rigace me tsantsi da kuma raga_raga rigar transparent ne onion color tsayinshi iya guiwanta yatsaya hade yake da pant dinshi aciki shima onion color sunyi kyau sosai dauka tayi tasaka ajikinta babu abinda baa gani komai yana waje muraran harta pant din datasaka , rufe akwatin tayi tamaidashi inda yake tasa slippers tafito gaban mirror taje tasake feshe jikinta da different perfumes masu dadi dakuma sanyayyar kamshi ta gyara gashinta. Karfin hali tayi tasamu tahau kan gadon tana ciccije libs dinta yana nan a kishingiden taje ta kwanta akan kirjinshi da har lokacin besa kayaba dagashi se towel , tun kafin ta iso inda yake kamshin turarenshi sun sanar dashi zuwanta bude sexy eyes dinshi dasuka canza kala su da kansu suke lumshewa tsabar wutar shaawar dake damunshi yazuba mata na mujiya dagowa yayi yazauna yana bin jikinta da kallo daukewa numfashinsa yayi na wasu yan dakiku ganin dressing din datayi ta matukar tafiya da duk imaninshi kallon hips dinta dake da fadi da tudu yayi yana kallonsu duka awaje gana shanunta dasuke gaisheshi , hannu yasa yazagayo dashi a kugunta yakai kanshi kan wuyanta yana shakar kamshin jikinta dake sake birkitashi , fanan duk a tsorace take . kamar zeyi kuka yace " baby please I need you karki cemin ah ah" dukda yabata tausayi amma bazatayi gangancin barinshi ba muryanta na rawa tace " Mr azaad akwai stitches ajikina fah " tunawa yayi da anmata dinki yasa jikinshi mutuwa janta yayi ajikinshi suka kwanta yaja musu blanket yana manne da ita yanata tabe_tabe bata hanashi ba.

Su ummi basu tashi ankara da fanan bata gidan ba se bayan isha tukun nan ,anzo zasuci abinci suka ga duk sunfito mama ce ta tambayi hairah " Ina antynki " amsa mata hairah tayi da " bata nan dazun yaya yazo yadauketa " dake bayan fitar Mr azaad da fanan seta tambayesu waye shi sukace mata ai mijinta ne, jinjina rashin kunya irin na Mr azaad ummi da anty amina sukayi itakam ma anty amina duk tsoronta daya kar Mr azaad yace ze kusanci fanan da dinki ajikinta Allah_Allah takeyi sugama cin abinci su koma gida kafin me afkuwa ta afku. se wajajen 9:00 su ya Usman,ya al ameen, fawwaz, areef suka dawo gida tare da hafiz da yaji sauki sosai suna sallama hairah ta mike da gudu taje ta rungumeshi tana tsallen murna ganin yayanta jikinshi yayi sauki zama sukayi shida ita a kujera daya baba ma yana falon , kasa hafiz ya durkusa yana musu godiya sosai na taimakonshi da kanwarshi da sukayi murmushi kawai sukayi suna yabawa da hankalin yaran baba ne yace " hafiz tunda baku da kowa zaku zauna atare damu kunzama yayanmu da yardan Allah! kanwarka zata zauna a gidan nan zan maida ita makaranta! Kai kuma dazun kafin azaad yabar asibitin yamin magana kancewa tunda ni nadauki hairah shikuma yadaukeka zaka koma gidansu da zama ze mayar dakai makaranta duk sanda kakeso zakazo kaga kanwarka haka itama sanda ba makaranta zatazo ta ganka, kun zama jininmu yanzu in sha Allah bazaku sake kukan maraici ba kusaki jikinku munzama daya" tsabar farin ciki hafiz da hairah har hawaye sukeyi basuyi tunanin akwai irin wayan nan mutanen a doron duniya ba dan duk inda sukaje neman taimako sede abisu da kyara da tsangwama.

Ummi tace " bari mu gudu dare na yi hafiz mutafi ko ?" Gyada mata kai yayi ya mike shida su fawwaz rike hannun hairah yayi har waje yana ce mata " hairah kinga yanzu munsamu wayanda zasu taimakemu tsakani da Allah dukda nasan halinki bakida kiriniya da neman fada duk da haka dole insake fada miki kinji banda rashin kunya dukda shima ba halinki bane kimusu biyayya kamar appu da amma Allah yajikansu karki zama me manta halacci " ya karisa magana yana shafa kanta gyada mishi kai tayi tace " in sha Allah yaya zanyi yanda kace " ummi dake bayansu basu sani ba tajiyo duk abinda suke fada tayi murmushi tasakejin yaran sun kwanta mata arai.

Sallama suka musu suka tafi hairah se bye-bye takeyiwa yayanta hafiz , rike hannunta suhaima tayi zasu koma ciki yar gyaran murya ya usman yayi yama suhaima alama da ido tashiga ciki tagane abinda yake nufi , yasa tasaki hannun hairah tashiga ciki tabarsu a compound din gidan su biyu , kallonshi tayi da manyan idanunta tace " laaah ya usman kaine ?" Yace " eh khai.... "Sekuma yacanza tunawa da yayi ba khairaty bace yace " hairah yayanta nine zo kitayani hira " zama sukayi akan plastic chairs dasuke cikin compound din, haka yadinga janta da labari harta sake itama tadinga zuba mishi hira nan yagane itama gwanar surutuce gashi ko magana tayi se angane akwai tsantsan yarinta a tattare da ita haka yabiye mata suka dinga hira har karfe goma yace mata taje ta kwanta dare yayi gobe zasu karasa tashi tayi tashige dakinsu shima yashiga daki ranshi fess komai normal yakeji yana tafiya mishi yasan yau zeyi bacci me dadi.

Karfe 2:30 nadare fanan tafarka sakamakon Kiran sunanta da taji akeyi cikin sigan bada umarni dakuma girmamawa tashi tayi taga Mr azaad na baccinshi hankali kwance sauka tayi akan gadon tabude kofar ahankali yanda bazeji karan ba fitowa falo tayi tana sanye da kayan baccin jikinta falon ne yasauya daga falo zuwa wani irin hadaddiyar daji me dauke da shuke_shuke gwanin ban shaawa ga kamshi hade da dusan kankara sama kuma sararin samaniya ne , batayi mamakin hakan ba ji tayi an kara kiran sunan nata acan saman sararin samaniya yasa tabude hannayenta duka biyu tafiya tafarayi akan iska tana firewa sama inda sautin muryan ke fitowa seda ta kusa isowa wajan tukun kayan jikin yacanza zuwa doguwar riga fara sol komai din jikinta seda yacanza yazama hadadde hatta gashin kanta style dinshi canzawa yayi takoma sarauniya sak, isa wajan tayi taga bakowa babu alamar mutum ko tsuntsu kallon kudu da yamma tayi can ta hango jaaazana shi kadanshi akan iska yana daukar ido hular mulkin da yake ran kowa daga mutane har aljanu kowa burinshi ya mallakeshi , shine yayi wannan kira ga fanan wajanshi taje ta tsaya tanajin sanyi na ratsata , jitayi magana na fitowa daga jikin jaaazana " sarauniya fadima shin kinsan da lokacin ki yakusa karewa a duniyar bil adama? lokaci kalilan ne yarage miki da ki fara gabatar da abinda yakamata"

To semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏.

Masu comment Allah yasaka muku da aljanna ina godiya sosai matuka.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹

🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚

( J. W. A 📚📚📚)

PAGE 5️⃣3️⃣

Shuru kawai sarauniya fanan tayi tana sauraran jaaazana har ya gama fadin abinda ze fada ya narke ya shige cikin jikinta , bangarewa tayi idonta suka fifito sosai hasken su da sheki yakara fitowa kulle idonta tayi ta sake budewa ta ganta a tsakiyar falonsu ajiyar zuciya tayi tanufi bedroom din Mr azaad slowly ta bude kofar dan gudun kar ya tashi yahau tambayarta ina taje shigowa tayi tamaida kofar ta rufe , juyawa tayi zata je ta kwanta kawai taga Mr azaad a tsaye a gabanta idonshi akanta kallon tuhuma yake binta dashi kafin yace" wifey daga ina?" tace nadanje kitchen na sha ruwa ne" ta karishe maganar tana inda_inda " karya be dace dake ba domin baki iyashi ba karki fara ! sannan naga ga can bottle water akan center table ko me sanyi kikaje sha?" cewar Mr azaad da haryanzu ya tsura mata mayun idonshi da yasa takasa nutsuwa duk ta birkice se sosa wuya takeyi bazata iya sanar dashi lokacin tafiyarta ya qarato ba dan batason ya shiga wani halin damuwa, canza maganar tayi da " habiby kazo muje mu kwanta bacci nakeji" be sake dauko mata wata tambayar ba ganin bataso taki bashi amsa se kauce_kauce takeyi yasa yakoma kan bed yakwanta hawa gadon tayi itama ta shige jikinshi rungumota yayi kamar wani ze kwace mishi ita.

Washe gari 5:20am

Readers Also Read