Kenza eBookz

Noor al hayat complete by khaleesat - Chapter 12

Noor al hayat complete by khaleesat - Chapter 12

Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 12: Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 12. Mai gadin ya girgixa kai yace "Toh ku yi hakuri gobe sai ku…

3,912 words

Mai gadin ya girgixa kai yace "Toh ku yi hakuri gobe sai ku je ku dawo, amma ku tabbatar kun taho da wayar da xa ku yi communicating da ita" xai rufe gate Yakumbo tayi saurin saka kafarta daya ciki tace "Don girman Allah kayi hakuri ka bar mu mu shiga, wllh mun kashe kudin mota yayi dubu daya, kuma ni na biya, ka ji tausayina d'an nan" kamar xata rushe masa da kuka ta kai karshe, ya tsaya kallonsu da mamaki, can yace "Toh shkkn, amma har ni nasan sai kun janyo min fada wllh, amma bakomai akwai Allah, ku shigo" Yakumbo ta durkusa har kasa tana masa godiya suka shiga cikin makeken compound din gidan, uwa idonta xai fito yyi magana ta dinga bin gidan da kallo da motocin dake parking lot, Abuu ko idan da sabo ta saba shiga gidaje haka kai yara masu aiki, don haka ita ke biye da mai gadin yakumbo kuwa nata kalle kalle, bbu abinda khadijah tayi ma kallo biyu a compound din, don bbu bakonta a ciki. Karkashin wani artificial tree mai gadin ya nuna masu su jira sa, ya isa main entrance din shiga gidan, ya kusa minti biyar tsaye bakin kofar bayan ya danna bell aka bude kofar, Mai aikin gidan ce warce baxata wuce shekara ashirin da bakwai ba tana sanye da apron da hularsa alamar daga kitchen take, ganin warce ta fito yayi murmushi yace "Kyauta mun tashi lafiya?" Tace "Lafiya lau Usman, Ashe kai ne ma, ya aka yi?" Ya d'an sosa kai yace "Hajiya ce tayi bak'i ina fatan dai ta tashi bacci?" Kyauta tayi kasa da murya tace "Gata can parlor xaune ma" Muryar Hajiyar gidan suka ji tace "Waye kyauta?" Kyauta ta yi saurin barin bakin kofar tace "Hajiya, Usman mai gadi ne wai kin yi baki" Hajiyar dake gyara farcenta da nail cutter ta kalli agogo tace "Baki kuma?" Kyauta tace "Eh Hajiya" tace "Toh su shigo, amma ni bani da wasu baki da nake expecting da safen nan, da akwai ai da na gaya masa" Usman da ya ji abinda ta fada ya nufi gun da yakumbo suke yace "Allah ku daina karya bashi da amfani a rayuwa, yanxu gashi tace ita bata da wasu baki da take expecting da safen nan ku kuma har da ce min kun yi waya" yakumbo ta yi kasa da murya tace "Mu dai don Allah tunda har muka samu muka shigo gidan nan ka rufa mana asiri mu karasa idan ma ta kore mu shi kenan sai mu fita haka Allah yayi" ya nuna masu kofar shiga ya koma can bakin gate yana mamakin wasu 'yan Adam. Da yake a bude kyauta ta bar masu kofar, da sallama Yakumbo ta kutsa kai cikin parlorn tana dudduke kai ga wani daddadan kamshi dake tashi ta ko wani angle... Abuu na biye da ita a baya, Sai da duk suka shiga khadijah ta tura kofar a hankali ta rufe sannan ta bi bayansu, Hajiya Fatima matar gidan ta dinga kallonsu da mamaki har suka xauna kasan lallausan carpet din tsakar makeken parlorn, sanyin Ac yasa yakumbo ta fara rawan Dari, Hajiya tace "Sannun ku da xuwa" Yakumbo tayi saurin cewa "Yauwa ina kwana shugaba?" Ba Hajiyar kadai bace xaune parlorn ita da wata ce wanda ga dukkan alama kanwarta ce tsabar kamanninsu, matar xa kuma ta yi shekaru talatin da 'yan kai a duniya, Hajiya ta kalli kanwarta kamar yanda ita ma take kallonta, Amsa gaisuwar yakumbo Hajiyar tayi tace "Daga ina?" Yakumbo tayi gyaran murya kafin Abuu tace komai tace "Dama Hajiya da daddewa mun ji kina neman mai taimakon ki, shine ga yarinyata ganin irin haxakarta da hanxari yasa nace in rako Abuu dillaliya mu kawo maki" Hajiyar tace "Ayya ai kam ina da mai aiki bayin Allah gata can ita ta bude kofar ma...." Yakumbo ta katse ta tace "Ayya wannan d'an share share da goge goge xata ke maki Hajiya, wancan naga ai babba ce, ni ko baxa ki biya kudi mai yawa ba ki dauketa Hajiya don wllh daga waje me nisa muke ga uban kudin mota da muka kashe, ki taimaka fisabillilahi Hajiya" Abuu ta kara da cewa "Ki taimaka Hajiya wllh takanas saboda ke muka kawo yarinyar" Hajiya da tayi shiru tana kallonsu tace "Toh wacece mai aikin?" Da sauri Yakumbo ta nuna khadijah dake kallo so engrossed a katon plazma dake parlorn tana murmushi, Yakumbo ko lura da hakan ba ta yi ba, sai kallon Hajiya take ta kara jin abinda xata ce kan khadijah xuciyarta na bugawa, Hajiyar na duban khadijah tace "Ke ya sunan ki?" Inaa khadijah ana can duniyar kallo wannan karan har da dariyarta don film din ya mata dadi, yakumbo ta hadiye abu da kyar ganin irin kallon da Hajiyar ke mata, ta wani mitsileta a boye da sauri khadijah ta dawo, a fusace Abuu tace "Ba ke ake ma magana ba" khadijah ta kalli Hajiyar dake kallonta har lkcn tayi kasa da murya tace "Sorry ma'am, pardon?" Daga Hajiyar har kanwarta dake xaune kusa da ita bude ido suka yi suna kallonta sosai, Khadijah tayi kasa da manyan idanuwanta tace "I am sorry" Mikewa Yakumbo tayi jin fitsari ya taho mata, shi kenan khadijah ta cuce ta sai da ta buga masu turancin, ta nufi kofa da sauri tana cewa "Bari in d'an xaga Hajiya ku yi hakuri" Abuu ma sai kallon khadijah take baki sake jin fa kamar wani yare ta yi maimakon Hausa, Hajiya dake ta kallon khadijah tace "Alright, what's ur name!" Khadijah ta kalleta tace "My name is khadijah Muhd" Hajiyar tace "From where" khadijah tace "I am from kano, I lost my mum and dad... My step mum brought me to Kaduna 4 days ago and she left me...." Tana magana ne har hawaye ya kawo idonta, Hajiya dake kallonta keenly tace "And... Who is this woman that left to ease her self now?" Khadijah tace "My stepmum told me she is her senior sister.." Shigowar yakumbo yasa khadijah tayi shiru, Yakumbo ta shiga kalle kalle kamar munafuka ta xauna amma kuma ta kasa cewa komai tana jiran jin hukuncin Hajiya, ta ma san kawai Hajiya fasa daukar khadijah xata yi don ita tunda take bata taba jin an dauki mai aiki yar boko ba, sai ayi tunanin wani mission ya kawo ta gidan, Hajiyar na kallon Yakumbo tace "Nawa ne kudin aikin?" Xuciyar Yakumbo yyi mugun sanyi ta gyara zama tace "Wallahi ko nawa Hajiya, ko nawa Allah ya hore maki babu damuwa barin yanxu da kudi yyi wahala" Hajiya tace "Dubu uku xan bayar, yanxu kuma xan ba da na wata uku kamar yanda nake ma duk mai aiki idan na dauka" Yakumbo dake ta godiya kamar marokiya tace "Wallahi ba damuwa Allah ya bi ya maki bukatunki na alkhairi, nagode nagode nagode" Kanwar Hajiya mai sunan Khadijah dake gefenta ce tace "Why House maid again bayan kyauta Mumy? Beside I don't think this little girl will be capable, you just look at how engross she is with the TV...." Ko kadan khadijah bata ma san abinda ake cewa ba don gaskiya ne gaba daya hankalinta ta mayar kan kallo, yakumbo da babu abinda taji baya ga kyauta a xancen da Anty khadijah tayi ta marairaice tace "Kiyi hakuri baiwar Allah bbu abinda yarinyar nan ba ta iya ba wllh" Hajiya tace "Toh idan naga bbu abun kirki in sha Allah nan da kwana uku xa ku dawo ku dauki yarinyar, idan ya so sai ki mayar min da dubu shidda nah, ki rike dubu uku" Yakumbo tace "In sha Allah Hajiya, nagode nagode nagode" Hajiya ta katse ta daga godiyar da take yi tace "Toh ta wani number xa a same ki?" Yakumbo tace "ni ki ban naki idan na koma gida sai in kira ki Hajiya, na bar wayar a gida kuma ban san number ba" Hajiya ta sa kyauta ta kawo takarda da Biro tana cikin rubuta number aka bude kofar, duk suka juya kallon bakin kofar banda ita dake rubuta number, dogo ne tamkar dai khaleel din wasu can Lol... Irinsa shi ma ake kira da gentlemen, sanye yake da farar T-shirt da bakin wando, shigar ya kara haska farin fatarsa, iyakar kyau dai kam Alhmdllh Allah ya masa, tuni turarensa ya gauraye ko ina na gidan, har ya iso cikin parlorn idanuwansa na kan mahaifiyarsa dake rubuta sunanta kan number da ta rubuta a takardan hannunta, ya xauna gefenta yana murmushi ya mata side hug a hankali yace "Good morning mum" Sai a sannan ta kallesa hade da turasa tace "Morning...tashi kusa da ni sai warin asibiti kake dalla" Xaro ido yayi yana shinshina kayansa yace "Kai mum warin asibiti kuma duk kamshin nan da nake" tace "Ae kamshin daban warin asibitin daban" ya d'an yi murmushi yace "Ba dai warin asibiti ba sai dai kice kamshin magunguna mum..." Ya kalli Small mum dinsa yana shafa kai yace "Good morning small mum" tabe baki tayi tace "Allah ya kara.... ina ce nan ka tsallakeni ka tafi can gashi an gwaleka" rike kansa yyi yana d'an murmushi can ya dago a hankali yace "Mum kin ji koh" Sai a sannan ya kalli su Yakumbo, tayi saurin cewa "Ina kwana Alhaji" yace "Lafiya Alhmdllh" Hajiya da har ta bata paper din tace "Toh shkkn, yanxu saura in baku kudin ina sauraren kiran ku" kallon D'an ta dake xaune har lkcn a gefenta tayi tace "Aliyu akwai cash tare da kai yanxu?" Ya sa hannu aljihun sa, tace "10k xaka ban" dubu goman ya fiddo ya mika mata ta karba ta ba Yakumbo, Hannu bibbiyu ta karba tana jero godiya, Aliyu yyi saurin dauke kai yana kallon small mum dinsa da wani expression yace "Who are they?" Anty khadijah ta tabe baki tace "Wai house help" yace "House help kuma, did mum dismissed the one available?" Anty khadijah tace "Ina fa, duk biyun xata hada ina ga" ya yatsine fuska yace "Which means ta ba ma su Siyama daman su kara relaxing kenan" Anty khadijah ta tabe baki bata ce komai ba, yace "Which among them is the house help" Anty khadijah ta nuna masa khadijah dake rakube gu daya ana ta kallo happily, lekata ya dinga yi baki bude, can ya dago da sauri yace "Which help will this little girl render?" Anty khadijah tace "Kai ma dai ka gani" bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake vibrate a aljihu, Su Yakumbo suka tashi xa su tafi har lkcn tana ma Hajiya godiya ko bin ta kan Khadijah bata yi ba ta fita tana kara dunkule kudin hannunta Abuu na biye da ita, Hajiya ta kalli Khadijah tace "Tashi ki dau cups din nan ga kitchen can ki kai su" ko kadan khadijah bata ji mai Hajiya ke cewa ba, har sai da Anty khadijah ta mata tsawa, ta dawo daga kallon da take a firgice, Hajiya ta nuna mata cups din tace "Ga kitchen a can ki kai su" tashi khadijah tayi tana neman cups din ta gansu can kusa da Anty khadijah, tana kallon Tvn da wayo ta nufi gun cups din, xaro ido Aliyu yyi jin yanda ta take kafarsa ya fixgota a mugun fusace yace "Baki da hankali ne" Hajiya tace "Bata sani ba fa ina ji Aliyu...." Khadijah dake ta kallonsa tayi kasa da kai a hankali tace "I am sorry, I didn't notice ur leg"

_Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne kindly patronize ur writer and read happily_

Aliyu ya d'an bude ido ya kalli Mum dinsa sannan small mum da ta hade rai, mumy tace "Toh ka ji, she didn't notice" karasawa khadijah tayi ta dauke cup din ta nufi kitchen da aka nuna mata tana yi tana kallon TV har ta isa bakin kofar shiga, kin shiga tayi ta makale da bango tana kallon TV din, haka Mumy ta saki baki tana kallonta, ta kusa minti daya sai kuma ta juyo a hankali ta saci kallonsu, hada ido suka yi da Aliyu dake kallonta kamar yanda mahaifiyarsa ke kallonta ita ma, boye fuskarta tayi da hannunta da sauri tana yar dariya ta shige kitchen din, mikewa Aliyu yyi ya tabe baki yace "Lallai" sannan ya wuce sama, small mum dinsa ta mike tace "Kai fa kasan lallai, ni ban san me yasa Anty fatima take jajibe jajibe haka ba, ni abun ya isheni wllh" daga haka ta bi bayan Aliyu, Mumy dai bata ce komai ba, khadijah na ajiye cup din ta fito ta taho gun mumy ta durkusa gefenta a hankali tace "Anty naga remnant din fried potato and egg, and I am very hungry please can I take it?" Mumy ta gyada mata kai kawai tana kallonta, murmushi khadijah tayi tace "Thank you very much ma" daga haka ta mike ta wuce kitchen din cike da murna, ta dau dankalin da kwai ta xauna a nan kitchen din ta tankwashe kafarta ta fara ci tana lullumshe ido, a nutse take cin abincin kar ma ya kare ta fi minti goma a haka taji an shigo kitchen din, daga kai tayi tana kallon waye ta ga mutumin daxu ne, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya nufi gun da mugs suke a ajiye, Khadijah ta bi sa da kallo tace "Are you a medical Dr?" Juyowa yyi da sauri ya kalleta, ta wara masa manyan fararen idonta tana cin dankalin bakinta, ya daure fuska yace "Am I ur mate that u are asking me dat?" Ta girgixa kai da sauri tace "Not at all.... I just..." Sai kuma tayi shiru ta debi kwai ta kai baki, coffee ya hada ya xuba madara da sugar cube daya, tana ta kallon mug din ganin xai fita tace "Please can you give me some of ur tea" Juyowa yyi fuska daure yana kallon ta, tayi saurin sunkuyar da kanta tace "Ohk ohk sorryyy" har ya isa kofa sai kuma ya dawo ya dau wani cup ya xuba mata kusan rabi ya bude coffee powder ya debi rabin tea spoon ya kara xubawa a nata ya jujjuya sannan ya dauka ya mika mata yace "Here" wara ido tayi ta karba tana murmushi tace "That's kind of you, thank you" ko kallonta bai yi ba ya fice daga kitchen din, haka tayi ta hura shayin tana jira ya d'an huce ta sha, tana sipping din kadan ta mike a gigice tana neman kofar fita jin daci sosai, wani kofar da ta gani ta bude ta fita da gudu, bakin tap ta ga kyauta tana wanke kayan ciki, ga kifi ta gama wankesu a gefe, har da naman kaza a ajiye, khadijah ta tofar da ruwan shayin bakinta tana yatsine fuska ta nufi gun tap din tace "Dan Allah Anty xan sha ruwa kadan" matar ta kalleta fuska daure tace "Me kike yi a kitchen?" Khadijah na ci gaba da yatsine baki tace "Ina cin potatoe and egg ne" sake wukan hannunta kyauta tayi tace "Uban wa ya baki?" Khadijah ta bude hannu tace "Antyn dake parlor tace in dauka in ci, har na kusa cinyewa ma" Kyauta ta tsuke fuska tace "Mayya, wuce ki ban wuri, kuma kafin in shigo ki wanke kayan wanke wanken dake kitchen din nan, da gani a yunwace kika xo dama" Khadijah ta juya ta bar wajen ta koma kitchen, karasa cinye dankalin tayi ta ajiye plate din da cup a sink, coffeen kuma ta rufe sannan ta fito parlor, Mumy dake xaune har lkcn ta nuna mata jakar kayan ta tace "Ki dau jakar nan ga daki can ki kai ki ajiye" Mumy ta fada tana nuna mata dakin dake parlorn, khadijah ta xaro ido tace "Anty kayan fa sun yi datti sosai they are not washed, they are even smelling" Mumy tace "Me yasa baki wanke su ba toh?" Ta langwabar da kai tace "Ni ban iya ba Anty, I only use to wash plate" mumy dake ta kallon ta tace "Toh dauka ki kai su can waje ki ajiye" tace "Ohk ma" daga haka ta dau jakar ta fita da shi can waje, ta dawo, xaunawa jikin kujera kusa da Mumy tayi tana kallon wani program da Mumy ta sa, a hankali tace "Anty bakya kallon cartoon?" Kallon ta mumy tayi, tayi murmushi kafin ta canxa channel din xuwa cartoon, happily khadijah tace "Thank youuu" Mikewa mumy tayi ta wuce sama, Khadijah ta gyara xaman kallon cartoon, a haka Kyauta ta fito daga kitchen ta ganta, daure fuska tayi tace "Ke dan kaza kazan ki ba wanke wanke kwanukan dake kitchen nace kiyi ba kika taho nan kina kallo?" Khadijah ta bata fuska tace "Plss xan yi, ina son in gama wannan cartoon din ne, I have never watch it before" Kyauta ta bude baki da mamki, tana son kara tabbatar da anya ta ji xancen su yakumbo da Hajiya sosai daxu kuwa, ita dai kamar ji tayi ance aiki yarinyar nan xata yi, ko dai bata ji dai dai bane? Khadijah ta turo baki ganin Kyauta taki tafiya, ta nufi kitchen din tace "Toh naji xan wanke" daga haka ta bi gefenta ta shiga kitchen din, kyauta tayi kwafa ta fita don ba ma driver sakon da xai siyo mata na farfesun da xata yi, Khadijah na wanke cups din a kitchen cikin sink trying hard bata xubda ruwa kasan kitchen din ba a hankali take wanke wanken, Aliyu ne ya shigo rike da mug din daxu, tana ganinsa ta tsuke fuska, shi kam bai kara kallonta ba ya ajiye mug din xai fita tace "Wait" da kamar baxai tsaya ba sai kuma ya tsaya ya juyo, cup din da ya bata coffee daxu ta dauko ta cire murfin ta taho gabansata daga kai tana kallonsa tace "You didn't tell me that it was medicine u made.... I wouldn't have ask for some" kallonta ya tsaya yi, xata kama hannunsa ta sa cup din da sauri yace "Ke xan mare ki fa" turo baki tace "Toh ni nace baxan sha ba is it by force" mika masa ta kara yi, ya dauke kai yyi murmushi yana shafa beard dinsa, kallon sink yyi yace "Toh xubar" ta xaro ido tace "How? Why? For what reason? Why shud I throw it away? Ummata told me that they are consequence of throwing food away" shafa kansa yyi ya karbi cup din ya karasa sink xai xubar ta rikosa da sauri ya buge mata hannunta, ta bata fuska xata yi kuka, kusan rabi ya xubar ya nufi inda kayan shayi suke, ya kara madara ya xuba Milo da sugar cube uku ya kara ruwan xafi a ciki ya juya sannan ya mika mata, ta wara ido da sauri tace "For me?" Ya hade rai tayi saurin karbewa cike da murna tace "Thank you very much" dai dai nan kyauta ta shigo kitchen din, tayi kasa da kai tace "Sannu da xuwa yallabai, ina kwana" yace "Lafiya lau" daga haka ya fice kitchen din, khadijah ta nemi waje ta xauna ta tankwashe kafa ta fara shan shayin idonta lumshe, muryar kyauta taji tana cewa "Kee shine ya baki shayin nan?" Ta bude ido da sauri tace "Ehh" kyauta ta hade rai ta karasa ta ja kunnenta tace "Idan kina shisshige ma yan gidan nan sai na ci kaza Kazan ki shegiya kawai" khadijah ta ci gaba da shan shayin ta bata ce komai ba. Kyauta ce ta karasa wanke wanken tana gunguni khadijah sai lekota take ta cikin cup ta take shan shayin ta, Mumy ce ta shigo kitchen din tana kallon kyauta tace "Kin bada sakon da nace kyauta" cike da ladabi kyauta ta bar wanke wanken tace "Ehh Hajiya" Mumy tace "Ohk, ina yarinyar nan take" kyauta ta nuna mata khadijah, Mumy tace "Ohk, idan ta gama ki turo ta ta xo ta amshi sabulu a sama tunda akwai omo a nan ki nuna mata yanda xata wanke kayan ta ga su can a waje wai masu daud'a ne" Kyauta tace "Toh Hajiya" daga haka Mumy ta wuce, Kyauta ta balla mata khadijah harara tace "Maxa ki gama kije ki amso, ni dai bbu wanki da xan maki" khadijah ta karashe shanyewa ta nufi gun sink ta ajiye cup din xata fito kyauta ta fixgota tace "Maxa wanke ni xan wanke maki?" Turo baki khadijah tayi ta fara wankewa a hankali kyauta ta kwace cup din tace "Tafi sama ki karbo min sabulun bbu abinda kika iya wllh" Khadijah ta juya ta fita ta wuce sama, tsaye tayi corridor tana kallon doors dakunan, ko wani daki na da taxara sosai daga na kusa da shi, aka bude wani kofa sai ga Anty khadijah, tana ganin khadijah ta hade rai tace "Ke me kike yi a nan, maxa sauka ance maki masu aiki suna hayowa nan ne" a hankali khadijah tace "Am sorry, Anty ce tace in xo...." Tsawa Anty khadijah ta mata tace "Maxa sauka shegiya" Mumy ce ta bude kofa ta leko tace "Ohk ni nace ta taho ta karbi sabulu khadijah" Anty khadijah ta hade rae tace "Kai Anty ki daina haka wllh ba shi da amfani ina kika taba ganin ana haka ma dai tukun, baki ganin yanda kawayenki suke da masu aiki ne, shegun ka ja su jiki su cuce ka kawai" mumy bata ce komai ba ta shiga ciki ta fiddo wasu sabulu masu tsada ta mika ma khadijah tace "Ki kai ma kyauta" khadijah ta karba ta juya, Anty khadijah tace "Ko da wasa kika sake hayowa nan wllh sai na mareki ko da kuwa Hajiya ce ta aike ki...." Khadijah dai bata ce komai ba har ta sauka, Kyauta ta kwace sabulun suka fita, bakin tap ta xuba duk kayan a roba tana yatsine fuska ta xuba ruwa da omo tace "Maxa taho ki wanke tsummokaran ki shegiya" Khadijah ta xaro ido tace "Kai Anty ban iya wanki ba fa" dagowa kyauta tayi da sauri tace "Toh uban wa xai maki" khadijah ta bude hannu alamar bata sani ba, kyauta ta dinga masifa tana jaraba ta shiga wanke kayan khadijah na tsaye tana kallonta, tas ta wanke su gaba daya tayi ta dauraya, khadijah dake ta tsaye tace "Anty in je in dinga yin shanya?" Kyauta tace "Ja can, warce bata iya wanki bace xata iya shanya" khadijah dai bata ce komai ba, kyauta tace "Ni dai da ki tafi ki ban waje in daina ganin ki" Khadijah tace "Toh Anty" daga haka ta wuce ciki da sauri taje ta ci gaba da kallonta, xaune ta samu Anty khadijah a parlor Aliyu na xaune kusa da ita sanye da 3qtr da farin riga yana nuna mata abu a laptop, tana ganin khadijah ta yi mata alamar da ta koma inda ta fita fuskarta daure, ganin Anty khadijah tayi shiru Aliyu ya daga kai yana kallon inda take kallo, dai dai lkcn da khadijah ta juya da sauri ta koma kitchen din, Anty khadijah tayi tsaki tace "Gayyar tsiya" shi dai Aliyu bai ce komai ba yana ci gaba da danna laptop dinsa, Komawa gun kyauta Khadijah tayi, kyauta ta hade rai tace "Dawowa kika yi?" A hankali khadijah tace "Wannan Aunt din ce ta koreni" Kyauta ta tabe baki tace "Wannan aikin ai sai khadijah baxawarar gidan, warce ta fi matar gidan xakewa, ta ki xaman aure ta xo nan duk ta gallabe mu da su Usman, ai sai ki je ga dakali can ki xauna ya kika iya" tafiya khadijah tayi ta xauna tana kallon kyauta dake ta daurayan kayan ta.

Readers Also Read