Kenza eBookz

Noor al hayat complete by khaleesat - Chapter 24

Noor al hayat complete by khaleesat - Chapter 24

Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 24: Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 24. Tada motar sudais yyi bai ce komai ba suka bar layin, ban…

4,692 words

Tada motar sudais yyi bai ce komai ba suka bar layin, ban da kuka babu abinda khadijah take har da shessheka, duk a tunaninta Umma ta ki hakura ne ta kori sudais, yana driving a hankali yace "Bana son wannan kukan da kike cika min kunne da shi plss, if you are in pain it's better you pray, plss kukan ki yana damuna da yawa" a hankali khadijah ta hadiye kukan tana share hawayenta a sanyaye, bayan wani lkci sudais yayi breaking silence din cikin motar a hankali yace "Ur step mum is gone Amira" da sauri khadijah ta kallesa xuciyarta na bugawa sosai tace "To where?" Yana ci gaba da driving dinsa yace "Dama ba Nigerian bace Ita?" Khadijah na kkrin mayar da wasu sabbin hawayen da ke taruwa idonta tace "She told me she is not a Nigerian... I don't knw her country" ya lumshe ido ya bude yace "Toh ta koma kasar su in ji Co wives dinta, since the day before yesterday ta wuce" cikin rawar Khadijah tace "Me yasa?" Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, sai dai baya son gaya mata aurenta ya lalace kamar yanda su Hasana suka gaya masa, Bayan kusan minti biyar murya can kasa yace "Look, you just have to face reality Khadijah, keep all those tears and crying aside, don't cry any longer it has no use" kai kawai take gyada masa kuka na cin ta amma bata yarda ta yi ba, nan ko shi ma hankalin sa a tashe yake kamar yanda nata yake a tashe amma yayi kokarin boye hakan yana lallashinta ita, bai san yanda xai yi da ita ba, bai san inda xai kai ta ba, bai san inda xai ajiyeta ba, bai ma san ta ina xai fara ba, tunanin hakan yasa yace "Ya Allah" bai san ya fito fili ba sai da khadijah dake ta share idonta ta kallesa, ya shafa kansa yana ci gaba da driving dinsa, Nearest filling station ya shiga domin kara Fuel kafin ya dau hanyar Damaturu, tun da suka shigo station din xuciyar khadijah ke tashi jin warin fetur, ta dai rufe fuskarta da Hijab din jikinta a hankali, Sauke glass yyi yana fadi ma mata mai siyar da man na nawa xata xuba masa, tana fara xuba man khadijah ta fara kkrin bude mota ya juya yana kallonta da mamaki yace "What?" Ganin yanda ta toshe baki yyi saurin bude lock din motar ta fita, tana fita kuwa ta shiga kwarara amai nan kasan wajen, sudais ya dafe kai a hankali a ransa yace Ai shi ya shiga uku.... Ganin wata mata ta fito daga motar dake bayan nasa yasa shima ya bude motarsa a hankali ya fito, matar ta riketa tana mata sannu kamar yanda kowa na gun ke yi mata, sudais ya xagayo ya tsaya ya ma rasa abinda xai ce, mai siyar da fuel din ta tafi gun siyar da drinks a filling station din ta karbo ruwan gora daya ta dawo matar da ke rike da khadijah ta bude ta mika mata khadijah ta karba da kyar tana wanke fuskarta da ruwan, mijin matar dake rike da khadijah ya fito shi ma yana ma khadijah sannu, matar ta kalli Sudais tace "Bari ta shiga motar sai ku wuce" barin wajen sudais yyi matar ta taimaka ma khadijah ta shiga motar sannan ta rufe, mai siyar da mai ta debo kasa tana xubawa wajen aman, Cike da karfin hali sudais yace "Toh mun gode kwarai" matar tace "Ayya ba komai, Allah ya sauwake, ya kuma raba lafiya" Sudais ya juya da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ameen mun gode" daga haka ya xaga driver seat ya kara yi ma mai siyar da mai da mutanen wajen godiya ya shiga ya tada motar suka bar filling station din, Har suka hau kan titi bai ce komai ba tunanin da yake a ransa daban, can ya saci kallonta yaga idonta a lumshe ta jinginar da kai da kujera, kwantar mata da kujerar yyi ta bude ido da sauri, sai a sannan murya can kasa yace "Sorry" Bata iya ta amsa masa ba ta mayar da idanuwanta ta rufe daga nan bacci ya dauketa. Buga kujerar motar da take kai taji ana yi cikin bacci, ta bude ido a hankali Sudais dake kallonta yace "Come down" kalle kallen inda suke ta shiga yi taga kamar gidan Sudais ne, ganin har ya fita yasa ta bude motar a hankali duk jikinta ba kwari ta fito ta bi bayansa, yana tsaye parlor yana jiranta bayan ta shigo, ya nufi wani bedroom ba wanda ta fara xama ba ya bude ya juyo yana kallonta yace "Go inside xan kawo maki bedsheet yanxu ki shimfida sai ki kwanta ki huta" daga haka ya wuce ba a dau lkci ba ya dawo da bedsheet din ya bata sannan ya fita ya kulle kofar, yanda yace tayi haka tayi ta kwanta a gajiye ga baccin da ke idonta, nan da nan bacci ya sake dauketa, sai kusan azahar ta farka da kyar ta dalilin sanyin da ta dinga ji alamar xaxxabi, cike da karfin hali ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idarwa ta jinginar da kanta da gado hawaye na sakko mata, ta dau lkci me tsayi a haka aka yi knocking kofar, da sauri ta dago kanta tana goge hawayen idona, jin an kara bugawa ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, tsaye ta gansa bakin kofar rike da leda babba da karami, bai ce komai ba ya shiga dakin ta bi bayansa, sai da ya ajiye ledan hannunsa yace "Tun daxu kike kuka kenan?" Kai ta gyada masa, yace "Good, kukan me kike?" Kamar ya dada tunxurata ta kuma fashe masa da kuka sosai ta durkushe wajen har da shessheka, cikin raunin murya tace "Ni bani da kowa yanxu, I don't knw if I have any use, i...." Ta fashe da wani matsanancin kukan, ya durkusa kusa da ita shi ma a hankali yace "Noo, you have use Amira, kar ki sake cewa baki da kowa, or don't you have trust in Allah?" Ta kallesa da sauri tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace "I do" ya d'an yi murmushi yace "Then have faith in him" ledan da ya ajiye ya nuna mata yace "Ki yi wanka ki canxa kaya, take some fruits after that sai kiyi sllh ki kwanta ki huta sosai" daga haka ya mike ya fita ya kullo mata kofar, ta fi minti goma a durkushe yanda ya bar ta daga karshe ta tashi ta bude ledan taga sabulu har da toothpaste da brush, sannan ga inners da dogayen riguna uku da hijab, duk jikinta yyi sanyi, ta mike ta shiga bathroom din ta yi wanka ta fito, Apples kadai ta iya ci cikin fruits din bayan ta gama shiryawa sannan ta kwanta lkci daya kuma bacci ya sake dauketa. Buga gefen gadon taji ana yi cikin bacci ta bude ido a hankali, ganinsa gefenta ta mike xaune da sauri, yace "Ur temperature is running high, are you feeling pain anywhere?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" yace "Ba ki yi sllh ba....." Kallon agogo tayi taga karfe bakwai ya wuce, ta kallesa da sauri tace "Dare yayi?" Yace "Yea, you slept all day ai" sunkuyar da kai tayi, yace "Me kike son ci yanxu?" Shiru tayi kamar me naxari, yace "Say it" a hankali tace "Kila gyada" ya d'an bude ido yace "What? Groundnut?" Shiru tayi tana kallonsa, da wani expression a fuskarsa yace "Ina xan samo gyada da daddaren nan?" A takaice tace "A titi" kauda kansa yayi, khadijah dake ta kallonsa bayan kusan minti biyu a hankali tace "Ka barshi kawai bana jin yunwa tunda dare yyi, am not even hungry..." wani kallo yyi mata ta gefen ido ya mike ya nufi kofa kamar xai tashi sama ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka nmta wanke baki sannan ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma bayan ta idar da sllh, yanda xata koma kan gado ne ta kasa tashi duk jin jikinta take kamar ba nata ba, gaba daya bbu karfi tattare da ita, har bacci ya fara daukarta a xaunen taji an bude kofa, ta dago da sauri, karasowa yyi kusa da ita ya ajiye ledan hannunsa ya koma gefen gado ya xauna, Kallonta kawai yake yace "Ga gyadar, after I've gone round of d whole of damaturu" Khadijah ta wara ido tace "All the round of damaturu?" Bai ce komai ba ya hade girar sama da ta kasa, a hankali tace "Nagode" bude ledan tayi taga dafaffen gyada ce da Wanda aka gasa a wani ledan daban, dafaffen ta fara ci, da ta juya xata ga ita yake kallo, duk sh was uncomfortable na kasa cin gyadan, can dai ta sake kallonsa tace "Bismillah" bai ce komai ba, can ya sakko ya xauna kusa da darduman, ya dau gyada daya ya bude, haka ya dinga bude su har suka yi yawa sannan ya mika mata ta karba tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Eat" ba musu ta fara ci, ya kuma bude mata wasu masu yawa, ya mika mata, haka ya dinga mata har tace masa ta koshi, yace "Are you sure?" Tana yatsina fuska tace "Kamar amai xan yi" hade rai yyi sosai yace "Don't try dat malama, kinsan garin da naje na samo gyadar nan" khadijah ta ja baya tana nodding masa kai, can ya shafa kai a hankali murya can kasa yace "Just relax xaki daina jin aman" ta kuma gyada masa kai ta jingina da jikin gado ta lumshe ido, ji tayi aman xai taho mata, ta toshe bakinta da hannu biyu tana girgixa masa kai kamar xata yi kuka tace "Wayyo xuwa xai yiii" tashi yyi da sauri ya shiga bathroom ya debo ruwa, ya dawo ya durkusa kusa da ita ya cire Hijab din jikinta, ya watsa mata ruwan a fuska da gashinta, har ranta taji sanyin ruwan ta koma baya da sauri tana sauke ajiyar xuciya, a hankali yace "Sorry" wani ajiyar xuciya ta kara saukewa jin aman ya d'an lafa mata, ta kallesa da kyar tace "Xan kuskure baki" table water dinsa da ya shigo da ya mika mata ta tashi ta wuce bathroom da sauri, bata fito bayin ba sai da ta amayar da gaba daya gyadar da ta ci, ta fito da kyar ta xube nan tsakiyar dakin tana satan kallon sa tana mayar da numfashi, wani kallo ya dinga mata Daga inda yake xaune, bata sake kallonsa ba ta lumshe ido, lkci daya kuma bacci ya dauketa, gashin kanta taji ana gyara mata ta bude ido da sauri ta gansa durkushe gefenta yace "Ki rufe gashin ki ki hau saman gado" ba musu ta mike xaune ta hade uban gashinta waje daya ta tufke, xata mike tsaye jiri ya kwasheta ta koma da sauri ta xauna yace "Be careful" gyada masa kai tayi ta kuma tashi ta koma kan gadon ta kwanta, ac dake dakin ya rage yace "In kashe maki wutan?" Ta girgixa masa kai, yace "Sai da safe" daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin. Kafin asuba Sudais ya shigo ya fi sau biyar duba ta don da ya bude kofa xata farka, gaba daya ya kasa bacci tunanin yanda xai yi da khadijah ya damesa gashi mami Bata san ya dawo ba ma, shigowarsa na karshe ne ya rufe ta da blanket don xaxxabi ne sosai jikinta, da asuba da ya shigo tashinta tayi sllh amai tayi ba kadan ba kafin ta dauro alwala ta fito, ruwan wanka ya hada mata bayan ta idar da sllhn, da kyar ta yi wankan ta fito, ta kasa shiryawa ta kwanta nn kan gado ya lullubeta da bargo, bayan kusan minti sha biyar ya dawo gefenta yace "Daure ki tashi ki shirya mu tafi clinic" bata ce komai ba don har fuskarta ta rufe, ya cire bargon suka hada ido, sauke idonsa yyi yace "Tashi ki shirya" daga haka ya fita dakin, har ya dawo bata tashi ba, yace "Ke fa nake jira" cikin sanyin murya tace "Ni baxan iya ba" yace "Toh ni xan sa maki kayan?" Bata ce masa komai ba, yace "Look bana son in dawo in gan ki cikin bargon nn it's better ki daure ki tashi kiyi abinda xa kiyi" juyawa yyi ya fita, cike da karfin hali ta mike xaune hawaye cike idonta, kamar ynda yace mata haka ta dinga daurewa har ta sa kayan a nan inda take kan gadon, tana gama sa wa ta koma ta kwanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin, tsayawa yyi kusa da gadon yace "Toh tashi mu je" rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta mike xaune a hankali tana sauke numfashi, Wayarsa ce ta fara ring, ya daga yana kallon screen din kafin ya xauna da sauri ya daga ya kai kunne tare da sallama yace "Good morning Mami" murmushi yyi yana shafa gashin kansa a hankali yace "Ku yi hakuri Mami ban kira ba, amma in sha Allah yau xan taho, am done with what am doing" bayan wani lkci yyi mata sallama ya mayar da wayar aljihu, yana kallon khadijah yace "Tashi mu je" daga haka ya nufi kofa, a hankali ta sakko da kafafuwanta kasa tayi karfin halin mikewa, har suka isa compound din gidan bai juyo ba, sai da ya isa gun motarsa ya juyo yana kallonta, can ya bude motar ya shiga, ta karasa ta bude front seat ta xauna ta lumshe ido don ji take kamar wani aiki me wahala tayi, wani babban private asibiti suka tafi, bayan yyi parking ya juyo yana kallonta da kyau yace "Har mu bar clinic din nn bana son jin bakin ki, am nt asking for ur opinion or anything, I am doing wat I think is right, am I clear?" A hankali ta gyada masa kai, yace "Good" da yake da safe ne ba su wani dde ba suka samu ganin likita bayan ya biya kudin kati, ta xauna daya daga kujeran dake kallon likitan, ya xauna shi ma yana facing dinta, hannu ya ba likitan suka gaisa, likitan na kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "How you madam, though u look sick" khadijah tayi murmushin karfin hali, likitan yace "Allah ya sauwake, ya raba lafiya," kallon Sudais dake shafa beard dinsa yyi yace "Drugs xan rubuta maku yanxu da xata dinga sha, there is nothing more I think.... She will get better gradually" Sudais ya ce "Ba abinda ya kawo mu ba kenan Dr, though I knw it might look wrong, but... she got pregnant by mistake, it's just some weeks old, so plss I want u to get rid of it...." Tunda ya fara maganan likitan ke kallonsa da expression din mamaki, Sudais yyi kasa da murya yace "Yes plss" likitan yace "Sorry we don't do that hear sir, xaku iya tafiya wani asibitin" kallon Sudais khadijah take kamar idanuwanta xa su fito, Sudais yyi kasa da murya sosai ya marairaice yace "Yeah, I knw it's very wrong Dr... But she is my.... Wife, the last pregnancy wasn't funny, and.. She's breastfeeding an eight month old baby now" kamar ana forcing dinsa yyi magana, likitan sai kallon khadijah yake, Sudais ya ciro handkerchief ya share goshinsa don har xufa ya keto masa yace "Plss Dr, ka taimaka for d sake of d eight month child" Likitan ya girgixa kai yace "I think xai fi a daina breastfeeding babyn, she shud take care of d one she's carrying now, sai kaga Allah ya taimaka komai ya xo da sauki" Sudais yace "Nooo Dr, don Allah ka cire mata I will pay what ever amount u request for plss" likitan ya mike ya nufi show glass dake office din ya dauko wani allura da syringe, ya dawo yace "I will give her this injection sauran drugs din kuma xan rubuta maka kaje pharmacy ku siya" Sudais ya sauke ajiyar xuciya yace "Thanks very much Dr, nagode sosai" Lkci daya khadijah t fashe da kuka ta mike tace "Nooo, ni bana son a cire min don Allah ku yi hakuri" bude baki Sudais yyi yana kallonta da mamaki, ta hade hannuwanta tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, I don't want to abort d pregnancy, Allah will be angry with me plss" Likitan ya ajiye alluran ya rungume hannuwansa yana kallonta yace "Ba mijin ki bane kenan?" Hawaye na ci gaba da sakko mata ta gyada masa kai alamar eh, Sudais dake mata wani irin kallo ya mike yace "Sae ki san inda dare yyi maki kuma daga nan" daga haka ya fice daga office din kamar xae tashi sama, a hankali take kuka tana kallon likitan dake kallonta yana girgixa kai, can ta nufi kofa cikin sanyin jiki ta fita, babu motarsa a parking space, ta fita gate tana share hawayen da ya ki tsaya mata.

Har Khadijah ta isa bakin titi kuka take bata damu da mutanen dake kallonta ba, ta ma rasa inda xata bi gashi ko sisi bata da shi, all this while Sudais na cikin motarsa yyi parking motarsa ya dinga bin ta da kallo har ta d'an yi nisa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido yana kiran Allah a xuciyarsa, he is just confuse, a hankali ya ci gaba ya fara driving motar har ya iso dai dai inda take ya tsaya ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ina kika san xaki tafi yanxu?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa ta tsaya bata ce komai ba, yace "Shigo mu je" fuska daure yyi maganan, A sanyaye ta xaga ta bude motar tana kallonsa ta shiga, bai ko kalleta ba ya ja motar, har ya isa gidansa bai ce mata komai ba, ita ko tayi nisa cikin tunanin da take ya bude motar ya fita ta bi sa da ido, Juyowa yyi ganin bata fito ba Yace "Should I bring u down?" girgixa kai tayi ta fito ya kulle motar ya nufi entrance din gidan ta bi bayansa, kana ganin yanda yake tafiya kasan a gajiye yake, xaune ta gansa parlor ya jinginar da kansa jikin kujera bayan ya xauna ya lumshe ido, a hankali ta xauna kasa ta takure waje daya sbda sanyin parlon, bude ido yyi bayan wani lokaci ya kalleta, suna hada ido ya dauke kai, khadijah dai sai kallonsa take, yanda ya tsura ma ac dake aiki a parlon ido yasa xaka gane tunani yake, a hankali khadijah tace "Xan yi wanka..." sai a snn ya juya ya kalleta, a takaice yace "In kai ki bayin kenan?" Ta girgixa masa kai, yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi ta wuce dakin da ya saukar da ita, wanka tayi ta fito ta shirya ta sa Hijab, yana nan yanda ta bar sa, har ta iso kusa da shi kuma bai sani ba, duk jikinta yyi sanyi ta durkusa nan kusa da shi cikin sanyin murya tace "I knw I am a burden, u don't knw where to start from, and u don't want to send me away cos you've got a good heart... You look so responsible to keep me in ur home, you have parent and elders that won't take it likely.... I don't want to be d beginning of ur problems, sbda haka nake rokon ka don Allah ka taimakeni ka kai ni gidan marayu kamar yanda na roka a baya, I will cope there in sha Allah, I will take care of the motherless there, but I want u to do me the favour of coming to see me, even if it's just once in a year plss, I want to feel I have somebody in this world, don Allah kar ka mance ni bani da kowa" tana kai wa nan hawayen dake makale idonta ya sakko, kallonta kawai sudais yake, can ya runtse ido ya bude ya mike ya fice parlorn, hade kai tayi da gwiwowinta tana kuka a hankali tana me tausayin rayuwarta, sai bayan kusan minti talatin sudais ya dawo parlorn, duk da ta ji shigowarsa bata dago kanta ba, muryarsa taji yace "tashi ki shiga daki kiyi kukan da kyau" ba musu ta tashi ta wuce cikin dakin, tayi kukan kamar yanda yace mata har ta gaji ta kwanta ta takure waje daya, bude kofar dakin yyi ya shigo, ta daga kai tana kallon sa har ya iso inda take yana tsaye yace "Good, am hoping all the tears you where planning to shed while in this house kin yi su yau kin gama, cos I am nt gonna tolerate that, clear? Better ki barni in ji da daya" Mikewa xaune tayi ta gyada masa kai tana share guntun hawayen idonta, yace "Me xa ki ci?" Ta girgixa kai tace "Bana jin yunwa" ganin kallonta yake a hankali tace "Toh xan ci apple" yace "Not apple, I mean food" ta d'an yi shiru, can ta dago tana kallonsa a hankali tace "Wainar flawa" wani kallo yake mata yace "Meye shi?" Taace "Da flour, albasa, tarugu, maggi, gishiri and man gyada ake yin sa, Anty Kyauta tayi mana a can gidan" da mamaki yace "A ina xan samo maki shi?" Tayi shiru bata ce komai ba, ya fi minti biyar a tsaye, can ya tabe baki ya fiddo wayarsa a aljihu yayi dialing number ya kai kunne, ba a dau lkci ba ya amsa sallaman da aka yi masa yace "Rabi'ah am on my way now, pls ina son ki min...." Juya ido yyi kamar me son tuno sunan abun, can ya cire wayar a kunne da sauri ya jefa ma khadijah wani kallo yace "Meye sunan ma?" A hankali tace "Wainar flawa" ya mayar da wayar kunne yace "Wainar flawa" Khadijah na jin yarinyar na dariya ya tabe baki ya katse wayarsa ya mayar aljihu ya fice a dakin. Khadijah na nan yanda ya bar ta ya dawo dakin, yana kallonta yace "ermm, ohk let me say Amira, you see xan je gida yanxu, but baxan dade ba xan kawo maki abincin, xa ki iya tsayawa ke kadai ai koh?" Ta gyada masa kai yace "Good, I will be right back now" kashe ac din dakin yyi ya kunna mata kayan kallo daga haka ya nufi kofa khadijah tace "Allah ya tsare" juyowa yyi ya kalleta yace "Amin" daga haka ya fita ya kulle mata kofar. Kwanciya tayi duk da sonta da kallo ta rufe idonta. Tun da sudais ya shiga gidansu yyi parking gabansa ke faduwa ya bude motar a hankali ya fita ya wuce cikin gidan, jin ana soye soye a kitchen ya karasa kitchen din, Rabi'ah ce tsaye tana soya wani abu da bai taba gani ba yace "What's this" wara ido tayi ganinsa tace "Sannu da xuwa yaya, wainar da kace mana" yace "Dama kamar kwai yake?" Ta gyada masa kai tana yar dariya ya tabe baki yace "Mami fa?" Tace "Tana bedroom da su Anty Maryam" bai ce komai ba ya haura sama yyi sallama kofar dakin maminsa, Kanwar mami da kanninsa biyu dake Dakin ne suka amsa masa ya shiga ciki, kallon uban kayan dake jibge a kasa ta ko ina a dakin, ga boxes masu tsada dake ajiye su ma, dukawa yyi ya gaida mami ta amsa da fara'a tana masa tambayar ya hanya, yace "Alhmdllh" sannan ya gaida Anty Maryam ta amsa da murmushi tace "Welcome barrister" sai a sannan ya amsa gaisuwar kanninsa ya mike ya koma can karshen gado ya xauna, Mami tace "Ka ga sai yau Maryam ta karbo sauran akwatunan xa a xuba kayan ciki yanxu" a hankali yace "Ohk" Mami tace "ka gama gyaran da kace a can gidan naka" ya gyada kai yace "Eh Mami" Mami tace "Toh maa sha Allah" Yana ta xaune har suka gama jera gaba daya kayayyakin a akwatunan, kanninsa su Humairah suka fita dakin ya rage daga shi sai Mami da kanwarta, Mami tace "Lkci na ta tafiya sudais yaushe ka ga ya kamata a kai kayan" tasowa yyi a hankali ya dawo kasan carpet ya xauna kansa a kasa murya can kasa yace "Mami..." Mami dake ta kallonsa kamar yanda Anty Maryam ma ke kallonsa tace "Ya aka yi sudais?" Kasa dago kansa yyi yace "Mami ina son a dakatar da kai kayan nan yanxu ne...." Mami dake masa kallon mamaki tace "Ko saboda me Aliyu?" Ya girgixa kai yace "Mami a dai dakata kawai" Anty Maryam tace "Ko Jiddahr ta yi maka wani laifin ne sudais?" Shiru yyi bai ce komai ba, Mami tace "Toh ni dai abinda xan ce maka a nan shine idan dai kasan ba shiririta bane, ba wani concrete laifi bane ka ajiye wannan shashancin da kake fadi aside, idan kuma kaga laifi ne babba to shkkn" Anty Maryam tace "Ka fada mana me tayi, wani laifin ka kama ta da shi Sudais, Kar mu xama kananun mutane" ya girgixa kai a hankali yace "A bar xancen kawai mumy" Mami tace "Toh Allah rufa asiri" yace "Ameen" mikewa yyi yace "Xan fita in dawo yanxu Mami" daga haka ya nufi kofa Mami ta bi sa da ido har ya fita, Anty Maryam tace "Kar ki tilastata masa don Allah Mami tun da kika ga haka ba karamin laifin ya kamata da shi ba, kin dai san halin sudais da xurfin ciki ko xaki shekara kina tambaya ba fada xai yi ba" Mami dai bata ce komai ba. Sudais na fita ya shiga kitchen ya tarar Rabi'ah ta gama wainar ta xuba masa a warmer, ya bude warmer din yana ta kallon abincin kafin ya tabe baki ya dauka ya fito parlor, da mamaki tace "Yaya ba a nan xaka ci ba?" Yace "Ehh ni da frnds dina xa mu ci, sai na dawo" daga haka ya fita gidan ya hau motarsa ya wuce. Sai da Sudais yyi azahar a masallacin layin gidansa sannan ya shiga gidan misalin karfe daya da rabi, jin an bude kofa Khadijah dake bacci ta bude ido da sauri, karasowa yyi yana kallonta ya ajiye warmer din hannunsa yace "Tashi ga abincin" ta xauna ya bude mata warmer din, ba don tsare ta da yyi ba da daya ma baxata cinye ba amma haka ya dinga forcing dinta har ta cinye biyu, sai dai duk she was restless don amai kawai ta dinga ji, ya hade rai sosai yace "Look idan ki ka yi aman nn I will nt bother my self about ur food again am telling you" hawaye cike idonta tace "Kayi hakuri wllh ba ni bace" ya xauna gefen gadon yace "Toh nayi, amma ki daure kar ki yi.... Just try" ta gyada kai ta koma xata kwanta ya ce "Toh ai hakan xai sa ki yi aman" dagowa tayi da sauri ta xauna, toshe baki tayi tana girgixa kai, ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba yana kallonta, a hankali tace "Wllh amai xan yi kayi hakuri" daga haka ta mike ya fixgota har sai da ta kusa fadawa kansa, yace "Am serious baxa ki yi ba" bai rufe baki ba ta kwarara masa aman gaba daya a jikinsa da bedsheet, wani kallo ya dinga mata yana yamutse fuska, can ya runtse ido har ta gama aman, Khadijah ta kasa kallonsa sae sauke numfashi take, wani tsaki da bata taba jin irinsa ba ya ja a fusace ya mike ya shige toilet, hawaye ya dinga sakko mata a sanyaye ta hade kai da gado, bayan kusan minti goma ya fito, ita dai tana nn yanda take, taji ya dafa ta ta dago da sauri, singlet da 3qtre ne jikinsa, ya sauke idonsa yace "kije kiyi wanka na sa maki ruwa" ta girgixa masa kai tace "Baxan iya ba ynxu" yace "No ki daure" daga hka ya sa ta tashi ta wuce bayin, Tana fitowa taga har ya shimfida wani bedsheet din ya cire na da, ta kwanta tana rawan sanyi, ya shiga bayi da xanin gadon, bai fito ba sai da ya wanke da shirt dinsa ya fita dakin.

Readers Also Read