Noor al hayat complete by khaleesat - Chapter 26
Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 26: Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 26. Yau tun da Khadijah ta tashi take ta murna ta rasa dalili,…
4,655 words
Yau tun da Khadijah ta tashi take ta murna ta rasa dalili, har hirarta ya fi na ko wani rana yawa har da dariyarta wanda da wuya ka ga tayi dariya, Dattijuwar mama suwaiba da take kira da Anty har ta lura da hakan tace "Wannan murnar yayi yawa khadijah ko dai mai gidan ne xai dawo yau" Khadijah dake hada fruits salad xata sha ta daga kai tana kallon mama suwaiba tayi shiru don kuwa gaskiya ne jiya da daddare da suka yi waya da Sudais yace mata yau xai dawo, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da abinda take a hankali, mama suwaiba tace "Toh gwara a tashi a san me xa a girka masa, ki fadi duk abinda kika San yafi so sai in shirya in tafi kasuwa yanxu" Khadijah tayi shiru don har lkcn bata san komai game da Sudais ba balle ta san abinda ya fi so da wanda bai so, hakan yasa jikinta yyi sanyi sosai. A cikin watanni biyar din nan khadijah ta warware jikinta yyi kwari, babu abinda bata ci har da wanda bata ci a da can, wato wake, taliya kai har da tuwo da miyar kuka, wani kyau na musamman tayi don hatta fatar jikinta har wani glittering yake yayi taushi, yanxu kam cikinta ya fito sosai don sai ayi tunanin at anytime xata iya haihuwa don da kyar take yin komai nan ko watannin cikin bakwai, tausayi take ba mama suwaiba ganin yarinya ce sosai wa ya sani ko xata iya haihuwa da kanta ma, hakan yasa in dai ta fita cefane ko siyo wani abun bata rabo da dawowa da magunguna irin na gargajiya da tasan mai ciki na bukata, duk ranakun alhamis kuma tare da mama suwaiba suke xuwa can clinic dinsu Yusuf domin Antenatal a bisa umarnin sudais, damuwar Khadijah daya a lkcn ummarta don ko cikin dake jikinta baya damunta ta kuma rasa dalili, gaba daya tayi kokarin ganin ta mance ta taba rayuwa gidansu Aliyu, amma duk sanda cikinta yayi motsi sai ta tuna shi Aliyun, duk wannan difficulties na rayuwa da ta shiga ko sau daya bata taba jin haushin Aliyu ba kuma har ranta take jin ta yafe masa a lkcn... ko don tana tare da yarinta har sannan ne oho. Khadijah ta kasa hakuri ganin har yamma bata ga sudais ba alhalin yace mata in sha Allah yau yana Nigerian duk jikinta yayi sanyi ta tafi daki ta kwanta, Mama suwaiba kuma ta ki hakura tana ta girke girke a kitchen ita kadai. Sudais na sauka taxin da ya kawo sa har kofar gida ya shiga gidan yana rike da daya daga travelling bag dinsa guda uku da mai taxin ya dire masa a bakin gate, kai kana ganinsa kasan daga turai yake don wani fresh na musamman yyi da haske sai dai ya rame sai idanuwa da hancinsa da suka fito, sosai ya rage bak'in gashin kansa, yyi murmushi ya na amsa gaisuwar da mai gadi ke masa da fara'a yana masa sannu da dawowa sannan yace "Ka shigo min da sauran kayana bilyamin" tun a bakin kofa kanninsa suka rungumesa ko wacce na murnar dawowarsa bayan kusan watanni biyar, Mami dake parlor da Anty Maryam ma sai murmushi suke, lkci daya murmushin Sudais yyi fading ganin Jiddah da yayi xaune parlorn, ya karaso a sanyaye ya duka kasa ya gaida mami ta amsa tana murmushi tace "Sannu da xuwa Aliyu ya hanya?" Yace "Alhmdllh Mami, fatan mun same ku lafiya?" Tace "Alhmdllh" gaisawa suka yi da Anty Maryam sannan ya kalli jiddah yana kirkiran murmushi ta sunkuyar da kai tace "Sannu da xuwa ya hanya?" Yace "Alhmdllh mun same ku lafiya?" Tace "Sure" Rabi'ah da Humairah suka dau bags dinsa xa su kai daki yace "Noo don't worry sisters wancan kadai xaku dauka ku bar wa ennan, xan d'an fita yanxu" da mamaki Mami tace "Ka fita kaje ina daga dawowa, idan ma fitan xaka yi ina xaka da jaka kuma?" Ya sunkuyar da kai yace "Sakon wani abokina ne xan kai gidansu Mami" Mami tace "Ohk, to amma sai ka huta ka ci abinci koh?" D'an shiru yyi sai kuma yace "Mami baxan dade ba xan dawo yanxu" daga haka yasa kanninsa suka dau jakunkunan suka kai masa bakin motarsa sanin ko baya nan ana amfani da motar, ya mike yace "Toh sai na dawo Mami" tace "Toh don Allah kar ka jima ka dawo ka ci abinci ka huta" yace "In sha Allah" yana barin gidan bayan ya hau titi ya dau wayarsa ya shiga kiran khadijah, Khadijah dake kwance har lkcn a daki ta mike da sauri kamar jira take jin ring din wayar ta jawo ganin Sudais ne ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yyi sallama yace "Amira" turo baki tayi tace "Uhn" yace "How are you" a hankali tace "Fine baka dawo ba kuma" d'an murmushi yyi yace "I postponed the trip xuwa next month in sha Allah" wani irin faduwa gabanta yyi da har sai da ta ji a kirjinta da ya mata sauki kwana biyu sbda magungunan da Yusuf ke bata, hawaye ne ya shiga sakkowa idonta, yace "Hello are you there?" Kasa amsawa tayi ya dinga hello ta katse wayar ta hade kai da gado ta fara rera kuka, sake kiranta yyi ta ki dauka har ya katse ya kara kira, sai a snn ta dauka ta kai kunne taki cewa komai, murya can kasa yace "Amira" ta fashe masa da kuka a hankali, wara ido yyi hade da murmushi yace "Har da kuka kuma?" Ta ki cewa komai, murya can kasa yace "Cry no more, tunda kina son ganina kawai fito gate ki tsaya ni kuma xan taso daga UK yanxu, har kofar gida jirgin xai ajiye ni" mikewa tayi xaune da sauri tace "Don Allah ka bari, ka dawo pls?" yace "Da gaske fa just wait me outside xa ki ganni yanxun nan" katse wayar tayi ta tashi da sauri ta dau Hijab har Kasa ta sa sannan ta fita dakin, Ganin xata fita waje Mama suwaiba da fitowarta kitchen kenan tace "Ya iso halan" Khadijah bata iya ta ce komai ba ta kirkiri murmushi ta fita, a hankali take tafiyar har ta isa gate ta tsaya gabanta na bugawa, tsaye ta ga motarsa bakin gate din suna hada ido ya bude motar ya fito yana murmushi, tsabar farin ciki ta kasa cewa komai amma kana ganin ta kasan she is just happy, ita dai tasan yau da ace mace ce Sudais da ta tafi da gudu ta rungumesa, ya wara mata ido ganin kallon da take masa yace "Toh ko dai in koma tunda kallona xa ki tsaya yi" tahowa tayi ta tsaya gabansa ta sunkuyar da kai tana murmushi, murmushin yayi shi ma murya can kasa yace "How are you Amira" ta kasa dago kai cikin sanyin murya tace "Am fyn, sannu da dawowa" yace "Sannu, ya babies dinmu" dagowa tayi ta kallesa da sauri sai kuma ta juya masa baya, dariya yayi yana kallonta, tayi murmushi tana jan hannunta, yace "Toh mu shiga" tafiya ta fara yi ya bi bayanta bayan ya rufe motar har suka shigo parlor. Xaunawa yayi parlorn suna gaisawa da mama suwaiba dake tayi masa sannu da xuwa, khadijah ma ta xauna kasan parlorn tana kallonsa ko kiftawa bbu, mama suwaiba ta koma kitchen ya maida dubansa kan Khadijah, sauke idonta tayi kasa da sauri, yace "Are you now happy" murmushi tayi tana gyada kai a hankali shi ma yyi murmushin yana kallonta, Kirar ta Mama Suwaiba tayi ta mike ta nufi kitchen ya bi ta da ido, Mama suwaiba tace "Toh ke haka ake yi, sai ki je bayi ki hada masa ruwan wanka, idan kuma abinci xai fara ci sai ki kai masa daki" murmushi khadijah tayi bata ce komai ba, mama suwaiba tace "Toh kin yi shiru kuma" a hankali khadijah tace "Toh bari in tambayesa" daga haka ta juya ta koma parlor, Wayarsa yake dannawa ta duka gefensa ya kalleta yace "Xauna kujera mana, you are stressing ur self and the babies" sauke idonta tayi kasa tace "Dama Anty ce ta ce in tambayeka ko xaka ci abinci a kai maka daki" shiru yyi na wani lkci kafin yace "She is thinking something different, and Mamina ta min abinci a can gida but... Ohk toh kai abincin daki" Tashi Khadijah tayi ta koma kitchen ta karbi abincin da Mama suwaiba ta hada a tray ta wuce can bedroom da shi, Sudais ya mike ya bi bayanta, karban abincin yyi a hannunta ya ajiye kan rug sannan ya xauna yace "Ke kin ci abincin" tace "Na ci daxu" yace "Daxu daban, yanxu daban, so xauna mu ci" dafa gado tayi xata xauna a kasa yace "No ki xauna saman gado" xaunawa tayi gefen gado ya debi abincin a plate ya sa spoon sannan ya mika mata ta amsa a hankali tace "Nagode" ya debi kadan a wani plate din dai dai nan wayarsa yyi ring dubawa yyi da sauri ya ga Mami ce, ya d'an bude ido sannan ya daga, daga daya bangaren Mami tace "Wai daga dawowa ina ka tafi haka Aliyu? Are you even okay" a hankali yace "Gani nan tahowa Mami am sorry" katse wayarta tayi, ya ajiye wayar yana kallon abincin, samun kansa yyi da Kasa cin abincin, ya rufe yace "Amira xan je gida Mami na jirana idan kin cinye wannan sai ki kara da nawa" Bata ce komai ba sai wasa da cokalin hannunta take, ya mike yace "Kilan xan xo gobe da safe, take care of ur self" daga haka ya juya ya fita, hawaye ne ya cika idonta ta rasa dalili abincin duk ya fita ranta ta kasa ci ta ajiye tana goge hawayen dake xubo mata, Sudais na fita ya tuna bai shiga da kayan da ya taho mata da su daga UK ba, ganin xai kara bata lkci kawai yyi deciding ya bar sa a motar sai gobe idan ya xo. Ko da ya koma gida kawai yana cin abincin da Mami tayi masa ne amma gaba daya hankalinsa na kan Khadijah don bai san ko ta ci abincin da ya debar mata ko bata ci ba, Mami dake xaune ta sa shi gaba da jira har ya gama cin abincin sannan tace "Kun yi waya da jiddah xaka dawo yau ne?" Girgixa kai yyi duk da faduwar da gabansa yyi a hankali yace "Aa mun ma kwana biyu ba mu yi magana ba, fushi take ai da ni" Mami tace "Toh wasa wasa gashi har watanni kusan shidda da kace a daga biki yyi, yanxu kuma ya ake ci" kasa kallonta yayi ya fara kame kamen rufe warmers din abinci, strictly tace "Magana nake ma ka Aliyu" da kyar ya dago ya kalleta yace "Toh Mami a sa bikin nan da wata daya xuwa biyu in sha Allah" wani kallo ta watsa masa tace "Me sati biyu ko uku yayi da har sai an kai wata biyu kuma?" Ya shafa kai yace "Dai dai wannan lkcn xan koma UK kuma xan jima sosai kafin in dawo kinga kawai ana bikin a lkcn sai mu tafi tare da ita" Mami tace "Allah ya kai mu, xan ma Abbanku bayani" yace "Nagode Mami" daga haka ya mike yace mata xai kwanta ya wuce bedroom dinsa. Yana shiga dakinsa khadijah ya kira, tana dagawa yace "Kin gama cin abincin?" Turo baki tayi tace "Na koshi" yace "Baki ci ba kenan?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Me kike yanxu?" Tace "Na kwanta" yace "Tashi ki je ki dau abincin ki ci idan ba haka ba baxa ki ganni gidan nan ba for plenty days" tashi tayi xaune da sauri tace "Ni ban ce baxan ci ba" yace "Toh je ki ci" ta mike da kyar tace "Toh" yace "Idan kin gama ki kirani" gyada masa kai tayi kamar yana ganinta ya katse wayar. Sosai ta ci abincin ta hada har da wanda ya dibar ma kansa, tana gama ci ta dau wayar ta kirasa, sai da ya kusa katsewa ya daga, jin muryarsa tace "Bacci kake" a hankali yace "Yea, kin gama cin abincin?" Tace "ehh na cinye" yace "Good Mami" murmushi tayi tace "Toh kayi baccin, byee" murmushin shi ma yyi ya katse wayar. Xuwan Yusuf gidansu da daddare ne saving grace dinsa don da shi da fita kuma sai gobe, bayan Yusuf ya gaisa da Mami suka tafi dakin Sudais yana tambayar sa ko yayi ciwo a UK ne don ya rame sosai, bayan kusan minti talatin Yusuf yace xai tafi suka fito tare da sudais da yace ma Mami xai rakasa, sai da suka shiga mota Yusuf yace "Kaje ka duba mai cikin ka?" Sudais ya hade rai yace "Mai cikina kuma" dariya Yusuf yyi yace "Toh ai kusan baka da banbanci da uban yaran, kai ma uba kake a gare su kama fi sa xama masu uba kan ubansu" tsaki Sudais yyi bai ce komai ba, Yusuf yace "But don Allah Sudais da yau ko watarana xaka ga uban unborn babies din nan me xaka masa?" Sudais yyi wani murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "I won't even look at him twice yaran da xata haifa sun ishesa" Yusuf yace "What if ya xo wataran yayi claiming yaran fa?" Wani kallo Sudais yyi masa baki bude, can yyi wani dariya yace "Wllh wllh I will sue him, sai na sa yyi shekaru da dama a gidan yari" Yusuf dake driving ya wara ido yace "Tohhh, kenan yaran ka ne ba nasa ba" Yusuf na dariya ya kare maganar, Sudais yyi banxa da shi, Yusuf yace "Toh why not bayan ta haihu ka aureta kawai Sudais" juyawa Sudais yyi yana kallonsa da wani expression, can ya dake yace "Ko saboda me?" Yusuf yyi murmushi yace "Saboda ka ji dadin ci gaba da kula da ita da yaran da xata Haifa kwanan nan, kasan a yanxu kai ne ubanta kai ne uwarta, i mean kai ne gatan ta, don haka sai ka ci gaba da xama gatan nata har karshen rayuwarta, nan da shekaru biyu kai ma ta haifa maka naka yan biyun ba na wani ba"
Girgixa kai Sudais yyi bayan ya dauke idonsa daga kallon da yyi ta ma Yusuf yace "I didn't blame you Dr, why?? Because am very sure kafin ka xo gidanmu yanxu daga club din da ka saba xuwa kake, and definitely idan ka je club dole sai ka sha ruwan can na sani, soo no offense, u are drunk...." Dariya kawai Yusuf yake yace "Kai kuma tun bayan haduwarka da marainiyar nan ka daina xuwa can koh? Thank God we where both drunkards before" Sudais da yyi mugun hade rai yace "Drop me here my frnd" Yusuf yyi parking yace "Ji dan iska kamar wani driver din sa wai drop me here my frnd" Bude motar Sudais yyi ya fice ya juya yana masa wani kallo, da yatsarsa yyi masa xagin turawa yayi wucewarsa, dariya kawai Yusuf yake ya ja motarsa ya wuce gida, Da kafa Sudais ya karasa gidansa, Mama suwaiba kadai ce parlor tana cin abinci TV a kunne, tana ganinsa ta mike da sauri tana masa sannu da xuwa yace "A'a yi xaman ki mama" Mama suwaiba ta koma ta xauna tace "Toh nagode" yana son tambayarta khadijah amma yyi shiru, can ya mike ya wuce bedroom, kwance ya ganta tayi bacci tana rufe da bargo, ya karasa kusa da gadon yana kallonta, dukawa yyi dai dai fuskarta murya can kasa yace "So early?" Ko motsi bata yi ba alamar ta jima da yin baccin, a hankali yyi murmushi ya kai hannu dogon hancinta ko mai ya tuna yyi saurin withdrawing din hannunsa ya mike ya kashe mata wuta ya fita daga dakin, Sallama yyi ma Mama suwaiba ya nufi kofa ta bi sa da kallon mamaki, yau ma da ya dawo baxai kwana gidansa tare da matarsa ba, wannan wani irin aure ne a gantale, har ya rufe kofa kallonsa take baki sake. Washegari lahadu Khadijah na xaune parlor da tuwo da miyar kuka da mama suwaiba tayi mata, da cokali take cin tuwon mama suwaiba kuma na kitchen tana wanke wanke, bude kofa aka yi ta daga kai da sauri sudais ya shigo parlorn rike da babban jaka, ajiye jakar yyi yana wara ido yace "Kaiiii yanxu xa ki iya cinye wannan tuwon Amira?" Rufe fuskarta tayi da kujera da sauri tace "A'a fa xan rage in ci anjima" dariya yyi ya juya ya fita ya shigo da daya jakar ya ajiye sannan ya xauna kan lallausan carpet da take xaune yace "Ci da yawa abin ki kin ji, sai ki haifo mana yara masu karfi" bata dago kanta ba har lkcn yyi murmushi ya bude zip din jakar ya fara fiddo kayan ciki, sai bayan da ya Ciro kayan jakunkunan gaba daya sannan yace "Here... you like them?" sai a sannan khadijah ta dago a hankali tana kallon kayan, kayan babies ne masu tsada ko wanne set biyu, shiru ta yi tana kallon kayan, ya ware nata dogayen riguna masu kyau gudu hudu yace "Wannan kuma naki" sauke idonta da ya kawo ruwa tayi a hankali, ya hade rai yace "Baki so ne xa ki min kuka" bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta hade kanta da kujera, yyi shiru yana kallonta, can ya fara mayar da kayan gaba daya jaka yana gamawa ya kai jakunkunan daki sannan ya nufi kofa ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce. Har bayan kwana biyu Sudais bai je gidan ba duk da he is just trying not to go amma hankalinsa gaba daya na can, sosai hankalin khadijah ya tashi don tasan kilan fushi yake ne ya sa, tana son kiransa amma ta kasa, ganin baxata iya jurewa ba kuma ta kira sa, a lokacin yana gida bedroom din Mami suna hira da Anty Maryam, ganin kiran yyi ta kallon screen din kafin yyi silencing wayar ya mike yace "Mami bari in tafi in shirya xan fita yanxu" daga haka ya bar dakin bayan yayi ma Anty Maryam ma sallama, Mami ta tabe baki tace "Kwata kwata Aliyu ba shi da gaskiya yanxu, I really don't knw what he is up to, tun ma kafin ya bar kasar months back na lura da haka kuma gashi ya dawo ya ci gaba da behavior din, there is something big he is hiding kuma shi ya hanasa auren ma, dubi fa yanda ya axalxalemu a kan jiddah duk ya daga mana hankali shi aure amma lkci daya kinga kuma abinda yyi, ni na haifesa ba shi ya haifeni ba don hka I will fish out what he is up to soon" ita dai Anty Maryam bata ce komai ba sai kallon yayarta take. Sudais na barin gidan ya tafi can gidansa, Khadijah na kitchen tare da Mama suwaiba suka ji an shigo parlorn, fitowa tayi tana ganinsa ta turo baki, ya karaso parlorn ya xauna yana idonsa a kanta, ta sunkuyar da kai ta isa kusa da shi ta xauna a kasa, yace "How are you?" Kin cewa komai tayi, ya d'an yi murmushi ya dau wayarsa yana danna, a hankali tace "Ina yini" ya kalleta yace "Ban yini ba" kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me nayi maka ba" yace "Na kawo maki abu kince baki so mana" xaro ido tayi tana kallonsa tace "Ni??" Yace "Ehh" murmushi tayi tace "I don't knw how to thank you that day, that was why...." Hawaye cike idonta ta kare maganar, Kallonta kawai yake bai ce komai ba. Haka nan rayuwa ya ci gaba da kasancewa bayan dawowar sudais Nigeria, duk safiya, rana har da daddare xai xo ganin khadijah, kayan ciye ciye yake xuwa mata shi idan xai xo da daddare wani lkcn shi ma ya ci abinda xai ci a gidan, ita dai Mama suwaiba na son sanin me ya janyo bai kwana gidan amma bata san wa xa ta tambaya ba tunda ba wani hira can suke yi da Khadijah ba, toh ko don tana da ciki ne yake haka, tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan har hakan yasa ta d'an fara jin haushin sudais din, rana daddaya ne xai shigo gidan ba tare da kayan baby ba, xuwa yanxu irin siyayyar kayan baby da yyi mata sai ayi xaton yara goma xata haifa, komai ya gani ya Burgesa sai ya daukar mata. A haka har watan haihuwar Khadijah ya tsaya, mama suwaiba bata yi kasa a gwiwa ba wajen bata taimako irin na gargajiya don tausayi take bata, kusan duk yamma sudais sai ya lallaba Yusuf sun je gidan kawai don ya dubata, har ransa yake fargabar kar abu ya sameta, wani sanyi tayi gaba daya a kwanakin ko da yaushe a kwance xaka ganta, idan ya tambayeta ko akwai inda ke mata ciwo sai tace babu ko ina. Ranan Sunday da sassafe ya shirya ya fito parlor yana kallon Mami dake dinning yace "Mami xan fita in dawo" tace "Ranan lahadin ma?" Murmushi yayi yace "Mami it's urgent ne, kuma akan..." Katse sa tayi tace "Aliyu" ya dago da sauri, bata fuska yayi yace "Mami wllh duk kika ce min Aliyu sai gabana ya fadi, cos u always call that name when serious" ta masa wani kallo tace "Toh da meye sunan naka?" Yar dariya yyi yace "Sudais mana" tace "Ni na sa maka sudais?" Dariya yyi sosai yace "Ni na sa ma kaina Mami Aliyun sunan tsoffi ne I...." Ta katse sa tace "What ever.... kaje duk inda xaka ka dawo ka sameni in sha Allah gobe xa a kai kayan can da kasa nayi jere da su a daki" yace "Allah ya kai mu Mami" daga haka ya fice daga parlorn, gidansa ya nufa direct. Mama suwaiba na kitchen tana aiki, bai jira sun gaisa ba ya wuce daki, xaune ya ga khadijah ta takure waje daya, Ya durkusa kusa da ita da sauri yace "Are you okay Amira?" Ta girgixa masa kai da kyar, da damuwa yace "What's wrong? Kina jin ciwo ne jikin ki?" Karfin halin nuna masa bayanta tayi, yace "Yana maki ciwo?" hawayen da ya gani idonta ya rikitar da shi lkci daya ya dagota yace "Let get to the hospital....." Kwace kanta tayi ta koma ta durkushe a wajen tana rintsa ido tace "Ya daina" Allah ma yasan daurewa kawai take, ga ciwon kamar ana kara mata take ji, bata san lkcn da ta sakar masa kuka ba a hankali tace "Wayyo ka taimakeni plss" bai sake saurararta ba suka fita dakin, Mama suwaiba bata ma san sun bar gidan ba tana kitchen, har suka isa asibiti Khadijah bata sani ba duk ta rikice, wani asibiti me tsada ya kai ta banda Wanda Yusuf ke aiki, bbu bata lkci nurses suka amsheta da wani likita, yanda Sudais ya daga hankali sai ka rantse ance masa mutuwa xata yi, khadijah bata yi fatan kara experiencing kwatankwacin irin wahalar da ta sha na labour ba har ta bar duniya, tun da suka je take wahala amma shiru, Sudais ya kira Yusuf ya sanar da shi suna asibiti, Yusuf yace "Me yasa baka kawo ta asibitin mu ba" Sudais yace "Just" Yusuf yace "Toh wani asibitin ku ke?" Sudais ya gaya masa, tabe baki Yusuf yyi yace "Kudi ya ma yawa ne, any way idan ta haihu ka kirani" Sudais ya katse wayar ya jinginar da kansa da kujera yana mai yi ma khadijah addu'a a xuciyarsa, bayan awanni biyu ya sake kiran Yusuf, Yusuf yace "Ya? is she delivered" a hankali Sudais yace "Har yanxu" Yusuf yace "Toh fah, ko dai cs xa ayi mata, dama am thinking it will be difficult ta haihu da kanta, any way bari in taho yanxu" bayan wani lkci Yusuf ya xo, dariya Yusuf ya shiga yi ganin yanayin sudais yace "Kaiiii... To ai ko jiddah ke labour sai haka bawan Allah" Shi dai Sudais bai tanka sa ba, yawanci likitocin asibitin duk Yusuf ya san su, don haka har labour room yaje gun khadijah, ya ji tausayinta ba kadan ba ganin irin dauriyarta, baxa ka taba cewa haihuwar fari xata yi ba tsabar karfin halinta, bayan wani lkci Yusuf ya bar asibitin bayan ya kwantar ma da Sudais hankali yace labour kawai take babu wani matsala, wasa wasa dai shiru ake ji wanda hakan yasa likitocin suka kira Sudais office nan suka nuna masa it's better ayi mata Cs kada yaran da ita kanta su samu matsala, kusan ba da son ransa yyi signing takardar da aka basa ba, bayan wasu yan mintuna aka fitar da Khadijah labour room xuwa Theatre, anan kuma aka yi nasarar ciro mata boys dinta, sai dai sun jigata kamar yanda ita ma ta jigata. Khadijah ta bude ido a hankali ta ganta kwance wani ward, Mama suwaiba dake gefenta ta sakar mata murmushi tace "Sannu Amira, Allah ya baki lafiya" tashi xaune take son yi taji kamar an danneta ta kasa tashin, Mama suwaiba ta mayar da ita ta kwantar tace "Aa kinga ba ki da lafiya ki yi kwanciyar ki kawai kinji" sai a snn taji wani axaba tun daga cikinta har xuwa kafafuwanta, wasu hawaye suka shiga sakko mata cikin rawar murya tace "xafi nake ji" fita Mama suwaiba tayi sai ga ta ta dawo da likita, likitan ya duddubata ya mata Allah ya sauwake sannan ya fita, Nurse ce ta shigo ta mata allura ta fita, bayan fitar ta sai ga Sudais ya shigo khadijah ta bude ido tana kallonsa, ya karaso gefenta cikin sanyin murya yace "Amira...." Bata iya ta amsa sa ba, a hankali ya sa hannunsa cikin nata cikin sanyin murya yace "Be strong Amira, you will get better in sha Allah.." Hawaye ya sakko idonta sai dai bata ce komai ba, ya sakko da fuskarsa dai dai nata yana murmushi a hankali yace "Baki tambayi yaran ki ba ko bakya son su?" Ta gyada masa kai, shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace "Toh sai ki bani su" Murya can kasa hawaye na xuba idonta tace "Na baka" ya fadada murmushin fuskarsa yace "Sure?" Throughout ranan Sudais was by her side tare da Mama suwaiba, Yusuf ma ya xo yyi mata barka ya wuce, ba a nuna mata yaran ba kuma bata tambaya ba har ta sa a rai kila ma mutuwa suka yi wanda tunanin hakan yasa mata nutsuwa sosai don har ga Allah bata ma son ganinsu, haka kawai taji bata san su, Sudais dake lura da cewa she was so depressed ya dinga kokarin ganin ya sa ta walwala sai dai ta kirkiri murmushin karfin hali, sallah kadai ke sa shi ya bar gefenta, tun karfe shidda mama suwaiba ta koma gida dauko kaya, duk kiran da aka dinga ma sudais a waya kin dagawa yyi daga karshe ma ya sa wayar a silent, A daren ranan bayan sudais yaje sallar magrib da ya tashi dawowa ya shigo rike da daya daga yaran wata nurse na biye da shi da dayan, tun da suka shigo khadijah ke kallonsu, yana murmushi ya ajiye babyn a gefenta, sosai gabanta ya fadi ta dinga yi ma jaririn wani kallo ganin kamar Aliyu yyi kaki, babu abinda new born din ya mance na ubansa tun daga haske, hanci, kai har bakinsa... Nurse din ta ajiye mata daya carbon copy din yaron dake gefenta kusa da d'an uwansa tana murmushi tace "Congrat mum twins, Allah ya raya su" daga haka ta fita, a hankali Sudais yace "Ain't they cute? I mean the innocent new souls" khadijah bata san lkcn da ta fashe da kukan takaici ba cikin rawar murya tace "Don Allah ka tafi da su, wllh bana son su, ni dai bana son su ka maida masu su" kuka take sosai kamar xata shide, ganin haka Sudais ya mike ya dau yaran gaba daya ya fita da su dakin.