Noor al hayat complete by khaleesat - Chapter 43
Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 43: Noor al hayat complete by khaleesat Chapter 43. Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta…
3,442 words
Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta inda xata fito amma bata fito ba, karasawa yayi kan kujera a hankali ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe manyan idanuwansa, bayan wani lkci sai ga ta ta fito daga daki da hijab a jikinta, mikewa yyi yana kallonta amma bai ce komai ba, Babu yabo babu fallasa tace "How may I help you?" Yana shafa lallausan gashin kansa a hankali ce "Where is.... the food?" Tace "Wani abincin? I didn't cook with you ai" ya d'an kalleta na few seconds sai kuma ya nufi kitchen cikin takunsa na kasaita ta bi sa da ido, rike da warmer din Irish din ya dawo yana dubanta yace "This" daga haka ya bude kofa ya fita ta bi sa da harara ta ja tsaki. Khadijah na ji suka fita gidan da Shureim wajen karfe goma, kafin sha daya ta gama duk abinda xata yi a gidan ta kwanta duk da ta so tafiya makaranta amma ta bari gobe kawai, ganin bacci ya ki xuwa mata ta dauko kayan karatun ta ta shiga yi, tana ta xaune har azahar yayi, ta mike daga karshe ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta kwanta, lkci daya bacci ya dauketa. A hankali khadijah ta bude idonta bayan wasu awanni ta mike xaune cikin sanyin jiki tana tunanin mafarkin da tayi, bell taji an danna wanda hakan sai da ya d'an tsorata ta, bayan wasu yan dakiku ta mike tsaye da kyar har lkcn mafarkin ya kasa fita a xuciyarta, jin an kara danna bell din ta sa hijab ta fita kamar mai counting steps dinta, tana isa gun kofar ta bude a hankali, Vanessa da Angela sai Maryam ta gani bakin kofar, sosai gaban Khadija ya fadi ganin Maryam bakin kofar, da farko kallonta ta dinga yi, sai kuma ta kirkiri murmushi tana masu sannu da xuwa ta basu hanya suka shigo parlorn, mamaki ta dinga yi a ranta, me ya kawo Maryam gidanta, after all she isn't her course mate nor her frnd, bayan sun gaisa suka mata gaisuwar Sudais, khadijah ta mike ta wuce kitchen don kawo masu ruwa da cakes din da ta siyo daxu da safe da ta fita, Maryam na kallonta tace "Mumy tace da daya twin din kika taho koh?" Ba tare da Khadija ta kalleta ba tace "Ehh tare muka xo" Maryam tace "Yana Ina?" Khadija tace "Ya fita ne" Maryam bata sake cewa komai ba, Khadija suka dinga hira da su Vanessa, sai dai hirar duk ta makaranta ce bayan kusan minti talatin suka ce mata xa su koma, har waje ta rakasu inda xa su samu cab, wani cab ne yyi parking dai dai su, aka bude cab din khaleel ya fito tare da Shureim da wani leda hannunsa, kallonsa kawai Maryam take, ya wara ido ganinta yace "Isn't this Maryam?" Yar dariya tayi tace "A nan anguwar kake dama Dr khaleel?" Yace "Sure, me kika xo yi nan?" Ta nuna masa Khadija tace "My frnd, mun xo mata gaisuwa ne yaron ta ya rasu" ya kalli khadijah yace "Ohh that's nyc, a schl kika santa kenan" Maryam tace "Eh a schl na santa" yace "Good" Maryam ta karasa gun Shureim tana kallonsa a hankali tace "Hello boy" gaisheta yayi, ta amsa tana murmushi jin muryarsa kamar na Aliyu, Su Vanessa ma suka taho gunsa duk ya gaishe su da turanci, ita dai Khadijah na tsaye, Khaleel na kallon Maryam yace "Alryt bari in shiga ciki Maryam, sai anjima" tace "Yauwa Dr, ya mutuniyar fa?" Har ya fara tafiya ya tsaya yace "Wai jawahir?" Tace "Ehh" yace "Haba ai ke ya kamata in tambaya, kun fi kusa" Maryam tace "Au haka ma xaka ce" Yace "Yes, nasan yau ma baxa ku rasa waya ba ni kam bata kira ni ba" Maryam tace "Lallai ma, ita ce ma xata kira ka kenan, soon ma xa su xo hutu nan da yayarta ar" Khaleel ya d'an kalleta yace "Really?" Girgixa kai Maryam tayi tace "Dad dina naji ya fadi haka nima" Ya dauke kai ya nufi cikin gida yana rike da Shureim yace "Allah ya kawo su lafiya" Taxin da Khaleel ya sauka suka hau Khadija ta daga masu hannu tace "We'll meet in school tomorrow, thank ya all" daga haka ta wuce ciki. Khadija na kitchen tana girkin lunch khaleel ya taho ya tsaya gun window yana kallonta yace "Ya kike?" Dauke idonta tayi daga kallonsa tace "Lafiya lau" Shureim dake kusa da shi a tsaye yace "Anty I am missing you" Khaleel yace "Bude masa ya shiga" kallon Shureim tayi sannan ta ajiye wukar hannunta ta isa gun kofar ta bude, Khaleel ya shigar da Shureim ciki sannan ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, ya jawo kofar ya rufe gam, ya jinginar da ita jiki yana mata wani kallo murya can kasa yace "Ni kike daga ma hanci" A tsorace tace "Kaga bana son haka ka bari, ka kyaleni plss" Duk ta kasa kallon idanuwansa da ya tsare ta da shi ga kamshin sa da ya cikata, A hankali yace "Fushin me kike yi da ni?" cikin rawar murya tace "Toh Fushin me xan yi da kai Dr, don Allah ka sakeni" d'aga kanta yayi tayi saurin runtse idanuwanta xuciyarta na bugawa, ya dinga kallon lips dinta, a hankali ya saketa yace "Where did you know Maryam from?" Ta shiga kokarin bude kofarta da sauri, ya rike handle din kofar yace "Au Ina maki magana xaki wuce?" Ta juyo kamar xata yi kuka tace "Ni ban santa ba sosai fah, kawai ina ganinta ne a schl kawar course mates dina ce" yace "Ohk, don't frnd her for some reasons kin ji?" kallonsa tayi da sauri, lkci daya tayi saurin kauda kanta xuciyarta na bugawa, his eyes are always not encouraging, d'an murmushi yayi a hankali yace "Ki gaya min meye da idona Khadijah?" Ta hade rai tace "I don't like them" wani murmushin yyi kamar me rada yace "Xan koya maki son su" murda kofar yayi ya bude ta juya da sauri ta shige kitchen din ta rufe kofar da makulli fuskarta daure. Shureim na cin abincin da ta xuba masa bayan magrib yace "Anty uncle yace gobe xan fara xuwa schl, we even went to the schl, uniform din na gidansa, in je in karbo?" Khadija dake ta kallonsa tace "I didn't send you" yace "Ohk" sannan ya ci gaba da cin abincinsa. Washegari da asuba khaleel ya miko mata uniforms din Shureim ta kitchen, rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta karba tana kallonsa a hankali tace "Mun gode" ko kallonta bai yi ba ya wuce. Karfe takwas saura khaleel yayi dropping Shureim a makarantar da yayi enrolling dinsa, Khadija dake xaune bayan motar ta bi Shureim dake daga mata hannu da kallo har aka wuce da shi cikin makarantar, khaleel yayi parking in da ya saba ajiye ta a schl ya juya yana kallonta, ta bude motar a hankali ta fito,, bata ce komai ba ta kulle motar ya ja motarsa ya bar wajen, a sanyaye ta karasa department dinsu don saura few minutes a shiga lectures. Karfe sha biyu saura Khadija ta fito daga lectures, cafeteria ta tafi ita kadai ganin Maryam na tare da su Vanessa, tana xaune ita kadai a cafterian da lemonade a gabanta idonta a kan wayarta tana dannawa, kujerar dake kallon nata taga an ja ta daga kai da sauri, sosai gabanta yayi mugun faduwa bayan sun hada ido, tayi saurin dauke idonta, xaunawa yayi yana kallonta a hankali yace "Hi Iman" kasa cewa komai tayi ta kuma kasa dago kanta, bayan few seconds ta dago da kyar tana dubansa tace "Hello" Murmushi yayi yace "Ya boko?" Kasa amsawa tayi lkci daya little Sudais dinta ya fado mata, taji xuciyarta ya mata rauni, ganin tayi shiru ya fiddo wayarsa ya fara dannawa, a hankali tace "Ya su mumy" yace "Na baro su lafiya, how is Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Har kinyi enrolling dinsa a nan?" Tace "Ehh" shiru ya d'an yi, kafin a hankali yace "How much did you spend Iman?" Ta kallesa lkci daya ta hade rai tace "What about it?" ya girgixa kai da sauri yace "Ohk, I am sorry I asked" bata ce komai ba, ya mike yana kallonta yace "Alryt, I will be on my way now Iman, my regards to Shureim" da ido ta bi sa, har ya tafi ya dawo da sauri ya sa hannu a aljihunsa yace "I think I've got something here" Chocolate guda daya ya fiddo ya duka yana kallonta ya mika mata yace "Ki ba Shureim plss" a hankali ta sauke idonta daga kallonsa ta karbi chocolate din tace "Ohk" yace "Thanks" daga haka ya mike ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya bace mata, kallon chocolate din hannunta tayi ta bude jakarta ta saka a ciki, tayi tagumi tana tunanin me yasa in dai ta ga Aliyu sai little Sudais dinta ya fado mata, or is it because of the resemblance, jin wayarta na ring ta sauke kai a hankali tana kallon mai kiran nata.
Sorry for the short chappy kilan in kara post around one na dare😦
A hankali khadijah tayi picking wayar ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Ya kike Amira?" Khadija tace "Alhmdllh ya aiki?" Yace "Lafiya lau, account number ki xa ki turo min yanxu" shiru ta yi na wani lkci kafin tace "Barrister.... Shureim fa yana da kayan sanyi, wllh you shouldn't bother...." Katse ta yayi yace "I am not asking for you opinion Khadijah" a hankali tace "Toh shkkn, ya Amira fah?" Sudais yace "Tana gun ummanta" bai karasa maganar ba ya ga jiddah tsaye kusa da dinning din da yake xaune tana kallonsa, ya dauke kansa yace "I will call you later Amira" katse wayar yayi ya ajiye, jiddah tayi dariya tana tafe hannu tana masa wani kallo tace "Cin amanar har cikin gidana Aliyu?" Sudais bai kalleta ba balle ya tanka ta, lkci daya idanuwanta suka kankance tace "Toh ko ma wace yar iskar ka samu wlh wlh sai tayi da ta sanin sanin ka a rayuwar ta, sai na nuna mata tayi kadan tayi kishi da ni, ba ma xai yiwu bane, mu xuba da ita sai dai idan ba mijina take cusa ma kanta ba" mikewa yayi yana kallonta yace "Wannan da kike gani wllh ta fi ki k'ima a idanuwana Jiddah, kuma kina nan xaki ga ta shigo gidan nan ta koya maki yanda ake kula da miji" bai sake sauraranta ba ya bar parlorn, jiddah ta kasa tsaye gu daya, ta ja kujera ta xauna da kyar xuciyarta na tafarfasa, lkci daya tayi wani murmushi tace "Babu boka babu malam, amma kai xaka bata shawarar ta rabu da kai, mu dai je xuwa, da kuluwa take xancen" Har khadijah ta iso gun motar khaleel idonta na kansa, shi kuma yana jingine jikin motar yana danna waya, bai san ta iso ba kawai kamshin ta ya ji, ya daga kai yana kallonta, a hankali tace "Good evening" ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ya lectures?" Tace "Alhmdllh, karfe nawa su Shureim ke tashi?" Ya buda ido yace "Ke fa yarinyar nan baki da kara" turo baki tayi tace "Toh me nayi, am just asking" yyi murmushi yace "Daga nan xa mu dauko sa, yanxu suke tashi su ma" ta karasa ta bude front seat ta shiga, shi ma ya shiga motar ya tada suka bar wajen, har suka iso makarantar shureim khaleel bai ce komai ba ita ma haka, ya bude motar ya fita, ba a dau lkci ba suka dawo tare da Shureim, xagayowa Shureim yayi ya bude inda khadijah take xaune ya rungumeta yace "Anty good afternoon" ta shigo da shi cikin motar ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa da murmushi tace "How you sweetheart?" Yace "Fyn Anty, I love the schl, I wish Sudais will come here also, am really missing him" Khadija bata ce komai ba, inda sabo ta saba, don bbu ranar da xai wuce Shureim baxai mata xancen Dan uwansa ba, he is always wishing Sudais is with him, lkci daya chocolate da Aliyu ya bata ya fado mata, ta bude jakarta a hankali ta fiddo chocolate din ta mika masa, karba yyi cike da jin dadi yace "Waow, Anty ke kika siya min?" Girgixa masa kai tayi tace "No" ya wara ido ya juya yana kallon Khaleel dake driving yace "Uncle kai ka siya min?" Khaleel ya kallesa yyi murmushi yace "No bani bane" Shureim ya mayar da dubansa kan Khadija yace "Toh Anty waye ya siya min" Khadijah tace "Idan baxa ka ci ba bani in cinye" Shureim ya bude chocolates din yace "Noo Anty ina so, ai irin wanda kind uncle din nan yake ba mu a gidansu maman nan ne, he told me his name is Dr Aliyu, Anty ina son a kai ni gidansu a Nigeria" Ita dai khadijah kallon yaron kawai take, ya gutsura ma khaleel ya mika masa yace "Uncle taste it" khaleel yyi murmushi yana girgixa kai yace "Noo thanks son, cinye abun, ko Anty kar ka ba" dariya yaron yayi bai ce komai ba, can ya kalli Khadija, alama yayi mata da ta bude bakinta, tayi murmushi ta bude masa bakin ya sa mata chocolate din a hankali yana satan kallon Khaleel. Suna isa gida bayan khaleel yyi parking khadijah ta bude motar ta fito tare da Shureim tana kallonsa murya can kasa tace "Thank you" fitowa yayi yana mimicking din muryarta yace "Thank you" daga haka ya rufe motarsa, hararansa ta fara yi sai kuma tayi murmushi ta wuce apartment dinta rike da hannun Shureim, ya jingina da mota ya rungume hannayensa ya bi su da kallo. Tun da Khadijah ta fito daga lectures yau take xaune cafteria ta rasa dalili, har lkcn lectures din karfe biyu yyi tana xaune gun bata tashi ba, Maryam ce ta shigo cafterian tare da wata kana ganinta kasa yar Nigeria ce, Maryam na ganin Khadijah tayi murmushi tace "Khadijah kina nan ashe, ya lectures?" Khadija tace "Alhmdllh ya naki?" Maryam tace "Alhmdllh" Maryam ta kalli yarinyar dake gefenta tace "Deejah meet ur namesake Khadija, tana studying pharmacy ne a nan, she is also a Nigerian from kaduna" Warce Maryam ta Kira da Deejah tayi murmushi tace "Its nyc meeting you namesake" Khadija tayi murmushi sosai tace "Nyc meeting you too" gun Khadija suka xauna su biyun, Maryam tace "Sun xo hutu ne nan da kanwarta shine na shigo da ita taga Cambridge" Deejah na kallon Maryam tace "Khadijah tana min kama da Safeenah, ko ke baki gani ba" Maryam ta kalli Khadijah da kyau, sai kuma tayi dariya tace "Suna dai yanayi ba kama ba, and the nose..." Deejah tace "Exactly, dama Ammi xata ganta cewa xata yi Safeenah ce" ita dai Khadijah bata ce komai ba banda murmushin da take yi, haka kawai taji tana son Deejah.... drinks da snack Maryam ta sa a kawo masu su uku, Maryam na shan drink din gabanta tace "Deejah wai me yasa jawahir ta ki biyo mu?" Khadijah ta daga kai tana kallonsu, Deejah ta tabe baki tace "Kilan kar su hadu da Dr Ayman" Maryam tace "Tab, Ayman sau biyu yake shigowa makarantar nan a sati, Mondays and Thursdays, I think ranakun yake nasa karatun" Maryam ta kalli Khadijah tace "Kingakiwa neighbor dinsa ce Khadijah fa" Deejah ta kalli Khadijah da sauri tace "Haba dai" Maryam tayi dariya tace "Wlh, ranan da naje gidanta tare da frnds dinmu na gan sa, yace min nan yake" Deejah tace "Wani anguwa kenan?" Maryam ta fada mata anguwar tana cin snack din hannunta, Deejah tace "Ayya, daxu dai naji da suka yi waya jawahir ta bashi address yace xai je anjima da yamma" Maryam tace "Gidan mu?" Deejah tace "Sure" Maryam tace "Ohk ai gwara dai ya je" Khadijah ta mike tana murmushi tace "Maryam xan shiga lectures yanxu" Maryam tace "Haba to baki dau snack din ba ai da drink" Khadija ta kirkiri murmushi ta dauka tace "Toh nagode" daga haka ta bar cafteria din bayan tayi ma Deejah ma sallama, Deejah ta bi ga da ido, kafin ta kalli Maryam tace "Maryam joke apart wllh kamar Safeenah, idan kin lura har da Maimoon ma suna yanayi, Maryam tace "A coincident" wani gun Khadija ta tafi ta xauna don sun cika mata kunne da surutu ne gaskiyar magana. Tana ta xaune nan har khaleel ya kirata bayan kusan awa daya, tana ta kallon Kiran kafin ta daga yace "Are you done with lectures Khadijah?" Girgixa kai tayi tace "No, idan na gama xan taho gida, kawai ka tafi" yace "Karfe nawa xa ku gama?" Turo baki tayi da kamar baxa tace komai ba sai kuma tace "Anjima" yace "Toh Ina jiran ki" daga haka ya katse wayar. Karfe hudu saura Khadijah ta isa gun da Khaleel ke jiran ta, fuskarta daure ta bude motar a hankali ta shiga, yana kallonta yace "Ya lectures?" Kamar ana tilastata tace "Fyn" sai bayan da suka bar cikin makarantar yace "Wa ya bata maki rai?" Shiru tayi bata ce komai ba, bai sake cewa komai ba har ya isa schl din Shureim ya fita ya daukosa ya dawo sannan suka dau hanyar gida, a waje yyi parking yana kallon Khadijah da ta bude motar ta fita, Shureim ma ya fito, yace "Am going somewhere now, sai na dawo" Khadija ta d'an buda ido tana kallonsa tace "Gun jawahir din ne somewhere??" Kallonta ya dinga yi da mamaki, ta tabe baki tace "Wai somewhere...." daga haka ta kama hannun Shureim suka wuce ciki, shafa kansa yayi ya tada motar yayi reverse ya bar wajen. Da daddare Khadijah na parlor aka danna bell, ta mike ta isa gun kofar tace "who is there" yace "Somebody" bude kofar tayi tana kallonsa ya mika mata ledan hannunsa yace "Ki ba Shureim?" Bata karbi ledan ba tace "Yayi Bacci" yace "Toh ki ajiye masa" Bata yarda ta kallesa ba ta amshi ledan daga haka ta rufe kofarta. Washegari da sassafe Khadija ta fito apartment dinta tare da Shureim da tayi ma Shirin makaranta, ganin waje xa su fita Shureim yace "Anty baxa mu jira uncle ba yau" hararansa tayi bata ce komai ba har suka fita ta tsayar masu da cab, sai da ta fara dropping dinsa schl sannan ta wuce nata makarantar. Tare da su Vanessa suka fito daga lectures misalin karfe sha biyu, tun daga nesa ta hangosa da wani bature suna tahowa, har ya iso inda suke xaune bai gansu ba yana magana da baturen Khadijah ta dinga kallonsa har suka wuce, still ta bi sa da ido, muryar Vanessa ne ya dawo da ita tana cewa su je su ci abinci, mikewa tayi a hankali suka bar wajen xuwa cafterian da suka saba xuwa, xaune ta ga Aliyu da Baturen a ciki, suna shigowa kuma ya ganta, ta dauke idonta daga kallonsa bayan sun hada ido, waje daya suka xauna tare da su Vanessa, Vanessa tayi masu ordering abinda xa su ci, drink kawai Khadija ta sa aka kawo mata, duk suka gama cin abincin Vanessa ta biya bill sannan suka mike, Khadijah dai na xaune bata tashi ba, Vanessa tace "Ain't you attending the next lecture?" Khadijah tace "I will be going home soon" Tana kallon su Vanessa suka wuce, dai dai lkcn da Baturen dake tare da Aliyu ya mike shi ma ya fita, tasowa Aliyu yyi ya dawo inda take ya ja kujera ya xauna yana kallonta yace "Good afternoon" ba tare da ta kallesa ba tace "Same...." Ya shafa kansa yace "Ya Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Ohk kin gama lectures yau ne?" Girgixa kai tayi tace "Aa xan wuce gida ne" yace "Ohk, yanxu?" Sai a sannan ta kallesa tace "Soon" yace "Alryt if you are ready mu je sai in yi dropping din ki" tace "I prefer cab" yace "Ohk then," wayarsa ya mika mata yace "Sa min digit din ki anjima da yamma xan kawo maki sakon Shureim or I give Dr.. Ayman, Maryam tace min same house ku ke da shi, and I saw him a gidanmu jiya" Khadijah bata ce komai ba da farko, can dai tace "Sakon me?" Yace "Shine xan bada a kai maki ai" Ta Girgixa kai ta karbi wayarsa ta na sa number ta tace "You call me instead" daga haka ta mayar masa da wayarsa, ita ta fara mikewa kafin shi, ya bi bayanta suka fita cafterian, sai da suka isa gun motarsa ya kalleta yace "Let me drop you Iman"