Reader mode
Kwai acikin kaya book 1 Chapter 10
4,043 words
Na buɗe idanuna da ƙyar bayan fitar numfashi na daya fara nisa daga gangar jikina, akan Uwargida dake gabana tsirara na saukesu, nai saurin maidawa na rufe jikina na wani azabar rawa, jin motsin zata sake dawowa kaina ya sani tashi cikin azama ina matse jikina da kare ƙirjina da ta yaga rigar ya fita fili. Cikin muryarta mai razanarwa tace, "Wacece ke? Waya turoki cikinmu?". "Wlhy babu wanda ya turoni gareku sai ƙaddadarar rayuwa, dan ALLAH kirufamin asiri ki barni na tafi, wlhy bana buƙatar aikata wannan abun a rayuwata, na miki alƙawarin har duniya ta tashi babu maijin sirrinku a bakina hajiya". Wata dariya ta saki tana matsowa jikina, murya ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa take min magana, "Ƴammata waya gaya miki muna tsoron sirrinmu ya fitane? Hakan ba matsalarmu bane, kisa a ranki kamar yadda ƙaddara ta kawoki cikinmu itace zata wajabta miki zama damu, kina da sura mai ƙyau da zaki mori lokacinki, matana biyar dana aura, nakumayi alƙawarin daga su bazan sake auren kowaba, sai dai ɗanɗano, amma ganinki yasa naji alƙawarina bazaiyi tasiriba, dan tun jiya dana ganki kika kwantamin a rai, da tsantsar kwaɗayinki na kwana a daren jiya, ki kwantar da hankalinki zan jiyar dake daɗi, tare da mallaka miki dukiya mai tsoka da saikin wucema tsaranki. Sonki da nake na gaskiya zai hanani yimiki fyaɗe, duk da kuwa kin ɓatamin rai da maganganun da kike faɗama yarana, da watace bakeba yau ta aikata hakan wlhy saina kasheta, amma ke bazanyi hakanba, bakuma zanyi mu'amula dake ta ƙarfiba, zan biki a hankali harki saki jikinki dani kema ki soni, dan haka daga yanzu kin dawo zama sashena". Rumtse idanuna nayi da ƙarfi hawaye masu zafi dana tara a cikinsu suna rige-rigen fitowa, ta janye jikinta daga gareni tana sauka, riga mai igiya naga ta ɗauka ta sakama jikinta, ta buɗe ɗakin ta fita tana faɗin, "Ki buɗe drawer ɗinnan duk nau'in kayan da kike buƙata zaki samu a ciki, karna dawo na sameki kina wannan kukan, dan na tsani kuka, sunana Uwargidan farin ciki, burina kullum na saka duk wanda ya raɓeni farin ciki kawai". Harta gama ɓaɓatun ta ta fice ban kalletaba, na kwashi kusan mintuna goma ina kukan nawa tare da sambatun yanda kullum duniyata ke garawa da sabon salo mai saka ruɗani, maimakon haske kullum duhu nake sake gani, maimakon fahimta kullum toshewar basira nake sake gamo dashi, maimakon canji kullum tsanani nake sake gamo dashi, maimakon cigaba kullum ci bayane yake zoma rayuwata, shin haka rayuwata zata ƙare kenan?. Na sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, jinake tamkar nama kashe kaina kozan huta ne.
Ban sake ganinta ba, dan bata sake shigowa ɗakinba, ni kaɗai na wuni a cikinsa, nayi yunƙurin fita amma naji an kulleni ta baya, sai wajen ƙarfe biyu wani saurayi ya kawo min abinci, ni bamma taɓa ganinsa a gidanba, baimin magana ba ban masaba, ya ajiye ya juya ya fita abinsa, inaji ya sake kulleni ta bayan. Ko kallon inda abincin yake banyiba, danni yanzu komai na gidan ƙyankyaminsa nakeyi wlhy, tunda nasan kuɗin siyen komai ta hanyar wannan ƙazantar suka sameta. Gadonma tuni na sakko na dawo ƙasa na zauna, amma sanyin tayis dake shigata yasa na kasa jurewa na miƙe na koma saman gadon na zauna. Yunwa da ƙishirwa duk sun gallaba mini, rabona da abinci tun jiya da safe da su ƴar daɓas suka takurani naci indomie ɗinsu. Babu abinda ke tadani zaune sai salloli, har zuwa dare kuma ban sake jin motsin kowa ba a gidan, sai bayan isha'i saurayin ya kuma kawo min abincin dare, ya ɗauki kwanikan rana zai fita dasu sai yajisu da nauyi alamar banci abincinba. Ya ɗan kalleni da mamaki, kamar zaiyi magana sai kuma naga ya share, ya ɗiba kwanikan ya fita abunsa.. Na darenma da ya kawo ƙin ci nayi, haka na kwanta abina da yunwa, dan harna fara sallar dare rashin ƙarfin jiki ya sani komawa na kwanta, dan nakasa tsaiwar, na komayi a zaune shina saina fara ganin jiri, dole dai na haƙura gaba ɗaya na zube a tsakar ɗakin barci yay awan gaba dani badan na shirya ba.
Da asuba dana farka da ƙyar na iya gabatar da sallar asubahi, ina zaune ina addu'a Uwargida ta shigo. Batace dani komaiba ta wuce ciki, a gabana babu kunya ta cire kayanta ta ɗaura tawul ta nufi ban ɗaki. Bani da damar fita a ɗakin tunda a kulle yake, hakan yasa na maida kallona ta inda bazan gantaba koda ta fito. Ta jima a cikin bayin kafin ta fito, "Babyna kin tashi lafiya" ta faɗa cikin salon yaudara. Ba ƙaramin ɗacine ya mamaye zuciyata ba, hakan yasa nai banza da ita ban amsaba. A mamakina sai naji tayi murmushi mai sauti, tace, "Karki bar wata ƙofa da zatasaka raina fara zafi a kanki kinji, ina sonkine shiyyasa kike samun sauƙi da ga wajena". Daga wannan maganar bata sake tankaminba, tai shirinta cikin shiga ta alfarma tanata zabga kamshi, sai kace ba itace shugabar sheɗanun nanba. Gaban kwanikan abincin jiya taje ta buɗa, ganin banciba ne ya sata faɗin, "Kai-kai wai bayan ƙuntata kanki harma horon yunwa kikema Kanki? Rufamin asiri kar wannan ƙyaƙyƙyawan jikin dana ɗorama buri ya lalace matata". Babu shiri na juya na kalleta da tsagwaron mamaki akan fuskata, wannan matar lallai zuciyarta ta rigada ta gama bushewa, idanuna da sukai nauyi kawai naɗan lumshe na maida kaina na jingina da gadon. Ƙamshin turarenta da ya yawaita a hancina da motsinta ya sani tabbatar da tana a kusa dani, hakan yasa naƙi buɗe ido, ta kama hannuna tana murzawa cikin wani salo na shaiɗanci. "Haba gimbiyar mata, kiyi haƙuri haka nan, dan bazaki taɓa kuɓuta daga gareniba, na rufe dukkan ƙofofin da hakan zata iya faruwa ma, ki cire komai a ranki ki bada kai bori ya hau kinji, idanma tsoron shiga wuta kikeyi ai kafin tsufa yazo mana zamu bari ko". A hankali na buɗe idanuna saboda jin furucinta na ƙarshe, ba tare da na shiryaba na sakar mata murmushi ina kaɗa kaina a hankali, banso mata magana ba tsawon zaman da zanyi da ita, amma a wannan gaɓar sai na kasa jurewa hakan, "Hajiya waya faɗa miki anama ALLAH wayone? Wakuma ya baki albishir saikin tsufa zaki mutu?". Hannuna ta saki da sauri tana ƴar dariya ta mike, "Humm Ustazu sauri nake, ajiye waɗannan tambayoyin naki kinji, ki daure kici abinci zanje anguwa na dawo, dan gobe ne za'a mana baiko ni da ke, sai kuma a tsaida ranar da za'a ɗaura mana aure". Da kallo kawai na iya binta harta fice, inaji ta sake kulleni. Sam na nema hawaye na rasa a idanuna, kuma ko kukan zuci ma na kasa yi, ina nan zaune niba mai tunaniba ba kuma gunkiba har hasken rana ya buɗe sosai, saurayin dake kawomin abinci ya shigo ɗauke da ture a hannunsa, yanzunma baimin magana ba ya ajiye tiren ya ɗauki abincin daren jiya ya fice abinsa. Nima kala bance masaba, dan maganar da Uwargida ta ambatamin akan baikon nan ta toshe dukkan tunanina, ni Bilkisu mace ƴar uwata take dangatani da aurenta?. "Hummm" na faɗa a fili ina maida kaina na kwantar a jikin gadon, yanda cikina ke murɗawar yunwa ya sani jin ya kamata naci abincin koda kaɗanne. Tiren da saurayin ya ajiye na jawo gabana, na buɗe kular farko farfesune na naman kai, sai ɗayar kuma soyayyar doya da ƙwai, sai ruwan shayi a ƙaramin filas, an zuba kayan shayin cikin kofi da aka ɗoro a tiren. Takarda mai rubutu da aka shinfiɗa akan tire ɗince taja hankalina. Na ja kular da aka ɗora ta lulluɓe kusan rabinta gefe.
*ALLAH YASA KIN IYA KARATU?* *_Kar kiyi abinda wani zai fahimta akan takardarnan, dan ɗakinnan akwai cctv a ciki_*
Abinda na fara cin karo da shi kenan a rubuce, hakanne ya sakani nutsuwa, naci gaba da ƙoƙarin haɗa shayi a kofin ina bin sauran rubutun ƙasan ina karantawa.
*_Na miki alƙawarin zan taimakeki, saboda baki dace da zama a wannan gidanba, Uwargida mahaifiya tace, inason ki saki jikinki da ita, duk abincin dana kawo miki kicisa dan wlhy bazan cutar da keba, insha ALLAHU gobe idan munkai da rai zan kuɓutar dake a wajen bikin baikon sheɗancin data ambata miki, dan inhar zaki cigaba da ƙuntata kanki bazata bari ki fito a ɗakin nanba, in kuma har kina a ciki bazaki samu damar barin gidan nanba, sakin jikin da zakiyi kamar kin amincewa buƙatartane kawai zai taimaka mana._*
Bansan wani nannauyan numfashi ya suɓuce mani ba, na share hawayen da suka kwaranyomin, cikin sauri na zuba abinci naci kamar yanda ya shawarceni, nakuma tashi na shiga wanka, dirowan tata na buɗe na ɗauki doguwar riga baƙa na saka. Ina nan zaune kusan sha biyu da rabi saurayin yazo ɗauke da wani abincin, nayi mamaki, dan ba'a irin wannan lokacin yake zuwa ba, sai dai zuciyata ta bani yanason fitar da rubutun da yayo minne, tattare kwanikan safen yayi, cikin wani dabara yaymin magana da idanu dake tabbatar min da abinda ya rubuto. Yanzunma daya fita dai sake rufeni yayi, banci abincinba har saida nai sallar zuhur. Zuwa yanzu naɗanji ƙarfin jikina, na gama babu jimawa Uwargida ta shigo, sosai mamaki na karanto a fuskarta gani na ba'a yanda ta barni ba. Ta dire jakar hannunta tana faɗin, "Babie kece kuwa?". Cikin danne ɗacin da nakeji na kalleta da murmushi a fuskata, "Nice hajiya, bayan fitarki nayi nazari akan maganarki, sai naga ma to idan na matsawa kaina barinku ina zanje?, na amince da bukatarki kawai". Shiru Uwargida tayi kamar bata amince da magana ta ba, sai naga ta nufi wata ƙofa, ashe nan ma ɗakine, kusan mintunanta goma da shiga ta fito, babu tsammani naji ta rungumeni tana murna sosai.
★★★★★
Tun daga haka sai Uwargida taita nan nan dani kamar zata maidani ciki, tanayin wanka taja hannuna muka fito falon, falon nan ya haɗu, haɗuwar da idan na zauna misaltashi ma ɓata lokacine. Zuwa dare na sake gaskata maganar saurayin, dan kuwa ta gama amincewa dani, harda zaunawa tana ƙara bani sirrikan arziki dake cikin harkar tasu, ni dai jinta kawai nake ina sake neman tsarin ALLAH da sharrinta a zuciyata..............✍🏻
https://youtu.be/5xN4SGMIzME
Garzaya ka saurari littafin *SAUYIN ƘADDARA*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*_ALƘALAMI TV_* ta shigo gari, tasha mai ɗunbin abubuwan ilmi, akwai littatafai na soyhayya da zasu dinga zuwa muku bisa tsaftataccen karatu, sai kuma gudunmawar hanyoyin da amarya da uwar gida zasu gyara jikinsu hankali kwance daga cikin gida basai wata taci ko sisinki ba.
Shin duk wannan gara ɓasar ka yarda ayita babu kai?🙆🏻🤔.
Maza garzaya ALƘALAMI TV dake dandalin manhajar youtobe kajiyo abubuwan bukatarka a sauƙaƙe.
Na zaune baiga gariba masoyanmu🤤🤤😋⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀
A danna mana subscribing domin tabbatar da ƙaunarmu😍😍❤❤🥰🥰😘😻😻👌🏻
*_ZAFAFA BIYAR_*🔥🔥🔥 *(SABON TAKU)*
*_NESA TAZO KUSA_*
*_KEWA TA QARE_*
*'YAN BIYAR DINKU NE SUKA SAKE DAWOWA DA KANSU BA AIKE BA*
*_Abishir a gareku makaranta litattafan hausa,ga 'yan biyar dinku sai sake tasowa da k'arfinsu d'auke da wasu ZAFAFAN LABARAn nasu har guda biyar rigis kamar wancan karon_*
*_idan kin taba kasancewa cikin tafiyar zafafa wancan karon basai an gaya miki ba,kinsan yadda tafiyar ta kasance_*
*Zakin Nadiya*
*Khaliphan Aysha*
*Amaan* *Ummukulsoom*
*Arkel / Maryam*
*Shamsu / Aliya*
*wannan karon kuma da wanne salo suka zo muku?,lallai akwai zazzafan kafce fiye dana baya cikin labaran da wadan nan zafafan marubuta zasu zo muku dasu,sunayen littafan nasu sune*
*Mamuhgee* ❤️ _QAUNARMU_
*miss xoxo* ♾️ _IGIYAR ZATO_
*Hafsat rano* 🖤 _DAURIN GORO_
*Billyn abdul* 🏃🏾♀️ _GUDU DA WAIWAIYE_
*huguma* 🤞🏾 _ALKAWARIN ALLAH_
*Ga mai buqatar kasancewa cikin tafiyar tamu,zai biya naira 500 ga dukka litattafan biyar,mai buqatar biyu zai biya 300,mai buqatar uku zai biya 400,mai buqatar hudu zai biya 450*
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
*Munyi kun gani,hausawa sukance wai sai an gwada akan san na qwarai,idan bakisan dad'in tafiyar ba tambayi wadanda aka tab'a damawa dasu*🤞🏾🤞🏾🤞🏾🤞🏾
*_Mallaki naki kici gashin kanki,da'a baki labari gwara ki bayar_* 🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*
*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_
*______________________________________* *_BOOK ONE_* _Shafi na goma sha biyar_ *______________________________________*
...........Washe gari ma dai naga gata wajen Uwargida, yanda na saki jikina da ita sai itama ta sake yarda dani ɗari bisa ɗari, dan har barina tai naje wajensu ƴar daɓas. Yanda suketa sinne kai basason mu haɗa ido sai suka bani mamaki, amma sai ban nunaba, dan na lura kunyata sukeji. Nima dai a kunyacen nake dasu, amma sai na dake tamkar baniba, nanko ƙasan zuciyata a matuƙar tsorace nake da kowa na gidan, nakan danne zuciyata bana kukan zahiri sai na zuci, tunanin iyayena dasu Firdausi yana sake gallabar zuciyata. Tun a yammacin ranar naga anata shigowa da drinks da wasu kayayyaki a kwalaye, tsoro ya sake kamani, danfa tabbas da gaske wannan sheɗaniyar takeyi, cigaba nai da neman tsarin ALLAH da sharrin kowannensu a zuciyata.
★★★★★★
Washe gari aka tashi da shirin baiko kamar yanda Uwargida ta faɗa, tun da rana manyan hajiyoyi suka fara isowa gidan, abin idan ka gani zat tashin hankali, sam banyi tunanin wannan ƙazantar tayi girma da yaɗuwar haka a cikin al'ummar musulmai jinin hausa fulani ba, wanda ma baka taɓa zato ko tsammani ba saika ganshi a wajen. Yara ƙanana ƴammata duk an tsundumasu wannan ƙazamar harka, mafi yawansu kuma saboda abin duniyane, gashi idan kana sauraren hirarrakinsu zaka fahimci sanadin waya suka haɗe da hajiyoyin a yanar gizo, bansan hawaye sun fara wanken fuskaba, sai da naji ɗigarsu akan hannuna, nai saurin gogewa ina haɗiyar rai. Kowa ya ganni sai ya yabama ƙoƙarin Hajiya, suna kurantata wai ta more, dan inada karuwan jiki, dukda ba wata ƙyaƙyƙyawa bace a fuska kuwa. Wasu mata kuwa su biyu sai hararata suke, ni ban saniba ashe wai matan hajiyarne, waisu nan kishina sukeyi. Kai jama'a, ALLAH kai mana tsari da asararriyar rayuwa dai.
Anmin wankin kai saikace wata amaryar data samu miji, sannan aka kawo mai kwalliyar da zatamin, bansan yanda zan musalta muku ɗunbin tashin hankalin da nake cikiba a wannan lokaci har aka gama kwalliyar. Duk wannan shiri da akeyi bikin zai gudana ne bayan sallar isha'i, amma abinda zai baka tsoro babu wanda naga yayi salla a cikinsu koma ambatarta a bakunansu. An kawomin wata riga mai ƙyau da zan saka, harda takalma da sarƙa da nake zaton ta gwal ce, dan ƙyawunta a ido kawai ya isa ka shaida hakan. Dakatar dasu nayi akan inason sai nayi sallar isha'i, da mamaki kuwa sai naga abun ya basu dariya, ni dai ban kulasu ba naje nai sallata, bayan na idarne na duba takardar da saurayinnan ya bani ɗazun da rana a ɓoye, bayanin danaga yayi a ciki ne ya sakani miƙewa da sauri, kaya na buɗe drawer ɗin Uwargida na ɗauka, na saka tare da gyara jikina tamkar ba niba, a yanda na fito inba sani kaimin na tsiyaba bazaka taɓa gane niceba, balle dama tunda akaimin kwalliyar babu wanda ya ganni a cikinsu har Uwargida. Cikin taimakon ALLAH na fito falon cikinsu ina taku da yauƙi, na saki jikina tamkar nima irinsu ce, duk da na fahimci wasu suna min kallon rashin sani, amma harkar ta wayewace sai kowa ya amsheni ba tare da bincikeba. Uwargida ta miƙe akan zataje ta fito dani, hakan yasa wasu manyan mata suka bita ɗakin, suna shiga watar gidan na ɗaukewa baki ɗaya. Jikina har rawa yake na ajiye takalma da jakka tare da sarƙar danasa ta gwal ta uwar gida na fito da lalube, dan dama a hanyar ƙofar fita na zauna kamar yanda saurayin ya shawarceni. Ina fitowa kuwa ana kama hannuna, cikin raɗa yace, "Karki damu nine". Bansan inda muke jefa ƙafa ba, kasancewar gidan babban gidane, maido wutar da akayine ya saka gabana faɗuwa, ni dashi duk mukaja birki ba tare da mun shirya ma hakanba. Surutai muka fara jiyowa wanda da alama ni suke nema, wasu na faɗin ta gudu, wasu na cewa ai da alama wata baƙuwace data shigo ta saceta kota kuɓutar da ita, dama su basu yarda da baƙuwar fuskarba. Cikin hanzari yaja hannuna muka faɗa ɗakin mai gadi dake a bakin gate, hawaye kawai nake jikina na rawa. Duk bidirin nemana da sukeyi muna jiyosu, wata naji tana tambayar Uwargida ko ina Sani?. Uwargida tace tun da rana ta turashi can wani ƙauye danya bar gidan ma tace ya kwana acan da safe ya dawo. Kallonsa nayi, dan da alama na lura shi ake nufi, kenan wasu sun fara zargin akwai saka hannunsa. Tun suna ɗaukar neman nawa wasa har abun ya fara caja musu kai, dan haka suka rabu, akabar ƙalilan a cikin gidan, ɗaukar kowa na fice, saboda sun iske gate buɗe. Saurayin ya ɗan leƙa ta Window, sai da ya tabbatar babu kowa kusa yay min nuni muje, hijjab ya bani na saka, ta bayan ɗakin mai gadin muka iske tsani, duk da tsahon katangar nan haka na hau tsanin nan ga tsoro na cina ga hawaye, da taimakonsa muka dira can baya, dayake ta canma ya saka tsani, kuma akwai abokinsa dake tsaye yana jiranmu. Duk naji ciwo a jikina, amma sam tashin hankalin da nake ciki baisa na damu da ciwukanba. Babu ɓata lokaci muka bar wajen, muna matsawa muka jiyo hayaniyar su Uwargida suna faɗin "tanan ta biyo" kugafa harda tsani, aiko tabbas akwai waɗanda suka taimaka mata ta gudu kenan. Buɗar bakin wata sai naji tace "kodai su ƴar daɓas ne". Bamu jiyo amsar da Uwargida ta bata ba mai adaidaitar da suka sakani ciki yaja yay gaba. Na damƙe jakkar da saurayin ya bani a jikina sosai ina cigaba da yin hawaye, yanzu kuma ko ina zan dosa kenan?. Wata zuciya ce tace, "Bilkisu duk kibar wannan guje-gujen, kibi shawarar zaɓi biyu, kodai ki miƙa kanki ga ƴan sanda, kokuma ki nema gidan ƴan uwan mahaifinki ko mahaifiya kije ga wani, idan sun riƙeki shikenan, idan sun nuna bazasu iyaba sai kisan mafita". Wannan shawara itace tai tasiri a raina, koda mai napep ya tambayeni batare da na shiryaba na faɗa masa anguwar da zai kaini. Ganinai ya tsaya da napep ɗin yana kallona, "Hajiya kinsan kuwa mi kike faɗane? Anguwar nan gaskiya tana da nisa, nikuma wanda ya bani ke ya cemin tashar mota zan kaiki". Hawayen fuskata na share, murya na rawa nace ka taimakeni bawan ALLAH, kaga ni mace ce, tashar mota kuwa wajene mai haɗari musamman da daddare, amma anguwar da zaka kaini yanzu akwai wanda na sani, wajenta zanje kafin safiya idan ALLAH ya kaimu". "Gaskiya Hajiya bazan ɓoye mikiba, a darennan bazan iya zuwa har canba, yanzu idan mun tafi sai mukai goma na dare bamu isaba, to yaushene na ajiyeki harna juyo nikuma na dawo gida. Ki dai faɗi wani wajen bayan wannan ɗin". "Shikenan na gode" nai maganar cikin jan majina ina sharce hawaye, zuwa can wani tunanin ya sake faɗomin, bara naje gidan Inna zainaba, ko arziƙin kwana ɗaya tamin, da safe saina doshi gidan baba manu ɗin da nai niyyar zuwa, duk da dai bana zaton samun alfarma daga ko ɗayansu, amma zan gwada, karya zam na yanke hukunci akan gaibu. Sake faɗa masa anguwar da zamuje nayi, dan haka ya tada napep muka cigaba da tafiya, sai yake cemin to ai shima cannema anguwarsu. Wani daɗine ya kamani, dan dama dai bawani iya gane gidan inna zainaba ɗin zanyiba sai na haɗa da tambaya. Shiru mukai na wasu mintuna, lokacu-lokaci ina cigaba da sharar hawayena. Muryarsa na tsinkayo yana cewa, "Baiwar ALLAH kibar kukannan, ita rayuwa duk jarabawace, haƙuri kawai kesa a cimma buri, da alama dai wanda ya sakaki a keken nan mijinkine ko?". Shiru na masa ban tankaba, jin haka shima sai ya tsuke bakinsa, mun ɗan ƙara tafiya na sake jiyoshi yana faɗin, "Dai-dai ina zan ajiyeki baiwar ALLAH?". Muryata a dasashe saboda kukan dana sha nace, "Kace nan anguwar kake ai kaima? Dan ALLAH ko kasan gidan dogo kafinta?". Da sauri ya juyo ya kalleni, bakinsa har harɗewa yake wajen faɗin, "Can gidan zakije?". "Eh" na faɗa cikin mamakin razanar danaga yayi. Yace, "Kai, to ai babanane dogo kafintan hajiya? Dan ALLAH kozan iya sanin ke wacece?". "Gidankune? To ko dai Yaya Shu'aibu ne?". "Ikon ALLAH, tabbas kuwa kin canka dai-dai, Shu'aibu ne kuwa, wacece ke dan ALLAH? daga ina kuma?". Murmushin yaƙe mai haɗe da takaici nayi, ganin yanda taɓarbarewar zuminci tasa ko juna bamu saniba dukda kusanci mai ƙarfi da muke dashi, shi kansa sunansa kawai nakeji a bakin Innata, amma ban taɓa ganinsa ba a ido, "Da wahala ka sanni, sai dai bansan ko kasan Asiya gurguwa data rasu kusan shekara ɗaya kenan?". "Tabbas na santa, dan gwaggona ce ma ai, tunda ƙanuwar innatace". Murmushi nayi mai ciwo, na maida kallona ga wata tukubar mai nama da muka tsaya dai-dai satinsa, mazane cike da wajen saboda mai shayi dake gefe, daga can kuma gabansu kaɗan mai doya da ƙwai, zaman masu wannan sana'a ne ya maida wajen dandali, harda masu suyar awara, gaddamar siyasa kawai kake jiyowa a wajen kamar zasu fara danbe, cikin share hawaye nace, "To ita mahaifiyata ce, ni kaɗaice kuma ƴarta tilo data bari a duniya". Jinai kawai yanata jero salati da sallalami, na maida hankalina sosai a garesa, cike da tsagwaron mamaki yace, "Yanzu nan dama Gwaggo Asiya nada ƴa amma ban saniba? Har tambaya nayi wlhy a randa mukaje zana idarta sai akace ai bata haihuba, to kodai dama baƙya tare da ita?". "Muna tare" kawai na iya cemasa saboda abinda ya tokaremin maƙoshi. Saurin tada Napep ɗin yayi yana faɗin, "Kinga yi haƙuri na tsareki da tambayoyi a titi, muje gida duk a yisu............
________________________ JAZUGA ________________________
Alhaji, ina baka shawara muyi amfani da maganat likitannan, gara ka ɗauke yaronnan ya koma yin jiyya wani waje, mukuma saimu fito mu sanarma duniya ya rasu, a ajiye wata gawar a maimakonsa kamar yanda mukai na yarinyarnan. Wlhy wannan sabon d.p.o ɗin baida mutunci, sannan baya amsar cin hanci, kaga dai yau kwanansa uku kawai da kawowa ko? To wlhy harya lalata wasu ɓoyayun cases guda huɗu da wancan d.p.o ɗin yaci ƙuɗi a kansu, to kaga kafin yazo kan bayanan case ɗin yaronka gara dai musan mai yuwuwa. Saboda tsaf zai gano gaskiya ta tashi mana mu duka wlhy". Wani irin nishin damuwa Alhaji lado yaja, yace, "Zanbi shawararku, amma lallai naso ace burina ya cika an kama yarinyarnan, dan shine kawai zai kawo ƙarshen wannan case ɗin". "Indai dan kamatane karka damu, zamu cigaba da ƙokari har sai mun ganta, kuma bazamu bartaba, tunda kaga yanzu kowa zai ɗauka yaronka ya mutune ai". "To shikenan yallaɓai, nagode sosai da ƙoƙarinka, zan shirya mota a darennan abar asibitin da Jazuli, da safe kuma saiku bamu sabuwar gawar a maimakonsa". "Hakan yayi Alhaji, na barka lafiya".
Bayan tafiyar ɗan sanda Alhaji Lado yata kai kawo akan zancen, tsarin likitan shima ya masa, amma fa yana burin a kama yarinyar kodan ya wulaƙantata, ya ɗaukama yaronsa fansa.
Nace, "Humm".
Duk yanda suka shirya haka aka tsara, washe gari saiga gawa a zuwan ta jazuga, mutane da yawa sunyi farin ciki, dan koba komai saji sakat, waɗanda sukaima wannan muwa kuma mutanene ƙalilan, suma na jikinsa, mutanen gari dai ko a fuska basa nuna jin kunyarsu akan gakan. Haka akayi zana idar gawa aka kaita makwancinta, yayinda acan bayan fage Jazuga ke cigaba da jiyya.
★★★★
Haka abubuwa sukaita shuɗawa, jikin jazuga na samun sauki, sai dai da alama dukan da Bilkisu tai masa ya taɓa masa ƙwalwar kai, dan idan abun ya motsa haka zaita dukan kansa yana wata irin ƙara har sai an bashi maganin barci, idan kuma ya farka sai ka ganshi normal sai kuma ya sake motsa masa. Sunje asibiti akan matsalar, suma dai magani suka bashi, tare da tabbacin inhar yabi soka komai zai dai-daita. Dalilin sun sanarma duniya Jazuga ya mutu dole ya haɗa kayansa da yaransa suka bar garin akan sai komai ya lafa zai dawo. Wannan abu ya sake masa ciwo, tare da dasa tsanar Bilkisu mai tsanani fiye da farko ma a zuciyarsa, yakuma saka a ransa duk randa suka haɗu kasheta kawai zaiyi kowa ya huta.
😱🙆🏻♀️.
_________________________ JAWAAD _________________________