Kenza Novels

Kwai acikin kaya book 1

Chapter 15

All chapters

Reader mode

Kwai acikin kaya book 1 Chapter 15

4,290 words

Har Jawaad ya baro office ya dawo gida ransa babu daɗi sam, ya kumazo ya iske Shahudah bata dawo ba, tsaki kawai yaja yay shigewarsa ɗakinsa, wanka kawai yay ya kwanta dukda masifar yunwar dake cinsa, amma gajiyar dake tare dashi har bishi-bishi yake ganin gari. Yana kwanciya kuwa barci mai ɗan karen nauyi yay awon gaba dashi, bai sake sanin wane hali ake cikiba sai gabda sallar magriba. A rikice ya tashi saboda salloli da suka wucesa, yay azamar yin ramuwarsu yana jero istigifari ga UBANGIJI. Bayan ya idar yay shirinsa tsaf ya fice zuwa gidan kakansa daya haifi Mamansa, mijin kakarsa mama maryam kenan. Ya iskesa yana da baƙi, dan haka bayan ya gaishe da baƙin yay wucewarsa cikin falon tsohon, kuloli yaci karo dasu, dan haka ya zauna yana buɗewa, yasan dai bai wuce tuwo ba, kuma daga gidan Ummansa ne ake kawoma baba, dan tunda mama maryam ta rasu bai sake aureba, shi kaɗai yake zaune a bunsa a gidan saisu idan sunzo. Tuwonsa ya zuba yaci ya ƙoshi yanamai jin nishaɗi, yaushe rabonsa da abinci mai nagarta irin haka? Yanama zaton tun masar da umman ta aika masace. "Kai ja'iri, tuwon nawa kake cinyewa?". Baba dake shigowa ya faɗa yana harar Jawaad da wasa. Dariya Jawaad ɗin yayi idonsa akan kakansa da tsufa ya kama sosai, "Haba mai ran ƙarfe kaimafa tuwon na gidan Umma nane, tunda kaƙi fita a gwaurantaka kayo mana amarya". Dariya sosai tsohon yayi, yasa sandarsa ya daki kafaɗar Jawaad da saida ya sosa wajen saboda zafi. "Dan gidanku, ni da kai munada banbanci ne? Kaima da kake da matar baka da banbanci da tuzurun da baima taɓa aureba". Murmushi Jawaad yay yana ɗan taɓe bakinsa, saboda tsoho dai ya taɓo masa inda ke masa ƙaiƙayi, aiko bai bada amsaba ya miƙe yaje ya wanko hannunsa sannan ya dawo ya zauna. Baba dake binsa da kallo yace, "Daga ina kake a darennan?". Jawaad ya zauna kusa da baba yana jingina kansa da kafaɗarsa yace, "Daga gida". Shafa kansa baba yayi yana maijin tausayinsa, yace, "Yau an tuna da tsoho kenan?". "Nikam dama kana raina, wani aikine kawai ya dabaibayeni sai yau na sauke nauyinsa". Murmushi baba yayi, "Naga komai ai a tv Jawaad, shiyyasa a kullum bana haufi a gareka, sai yanzu ne nake sake gaskta maganar mahaifinka da tun bakasan kanka ba yake dangantaka da aikin ƴan sanda, ashe shiya san miya hango mana" Murmushi kawai Jawaad yay yana haɗiye abu mai ɗaci a maƙoshinsa, daga nan ya cigaba da sauraren yabo da kakansa keta jerawa akan ƙyawawan halayyar mahaifinsa, a haka barci ya sake sacesa. Baba yakai dubansa ga fuskar Jawaad, ganin yay barci sai yay murmushi yana kai hannunsa ya shafa kumatun Jawaad ɗin. Ido Jawaad ya buɗe a hankali ya kallesa, baba yace, "Tashi kaje ɗaki ka kwanta". Bai musaba ya miƙe ya shige bedroom ɗin baba, lafiyayyen ɗaki dayasha gyara tamkar bana tsohon da rayuwa taima nisa ba, lallausan gadon baba Jawaad ya haye, yaja bargo ya rufe jikinsa yana lumshe idanunsa, kafin kace mi nan nauyan barcin ya sake ɗaukesa kamar wasa.

Yau dai kam Jawaad anan ya kwana tare da kakansa, sai da yay sallar asuba ya karya da breakfast ɗin da Faisal ya kawo daga gidan Umma sannan yayma baba sallama ya tafi gida akan yana nan dawowa anjima zasuyi wata magana da baba. Baba yace "to ALLAH ya kaimu saika dawo, ALLAH ya tsareka akoda yaushe". "Amin" Jawaad ya amsa yana fita.

_________________________ BAYAN SATI BIYU _________________________

Har wannan lokacin Aunty Shahudah da dai na gida, bata komaba kuma mijinta bai zoba, sannan jack na nan bai tafiba sai kace gidan tsohonsa. Nikam tun ranar da mukaci abinci tare ban sake zama inda yakeba, saboda har ɗaki ta biyoni ta ƙaremin zagi da cin zarafi akan ko Dad ne ya kuma buƙatar na zauna dasu cib abinci nasan yanda zan zame, idan ba hakaba wlhy saita ci mutuncina. Haƙuri kawai na bata nikam, dan yanzu ni bana ɗaukarta sahun masu isashen tunani. Tamin wannan abun ma da kwana uku Dad yace na shirya zuwa makarantar da zanje na zana jarabawata, ranar dai kamar anmin gafara naji, har kukan daɗi nayi kuwa. Kwana biyu na cika na tattara komai na sayayyar da Dad ya yo mani domin tafiya, dan makarantar boarding school ce, sai dai yanda naji su Aunty Aamila na faɗin wai ban dace da makarantar ba nasan babbar makarantace. Ranar dazan wuce na lura kowama murna yake da tafiyata, dan Salman harda faɗin, "ALLAH raka taki gona, koba komai sa huta da kallon baƙar fuskata abin amai". Dariya mummy da aunty Aamila suka sanya, dan mu kaɗaine a wajen, Shahudah da jack suna can baya suna hira.

Har bakin mota Amina da kuku sukai min rakkiya, sai da sukaga na shiga mota mun fice a gidan sannan. Na share ƙwallar data zubomin ina murmushin kewa da farin ciki.

😅👏🏼ALLAH ya bada nasa takwara, sai dai fa ni ƴar team Shahudah ce😆😜, bara na fece kafin naci mazga⛹‍♀.

_________________________

Tunda Jack ya bata shawarar zubar da cikinnan burinta ya dawo sabi fil, dan ya tabbatar mata Jawaad burga kawai yake mata babu wani sakinta da zaiyi tunda yana masifar sonta. Ta shafa cikinta da ayanzu haka yake mata ciwo, tabbas tana wahala akan wannan cikin da bata shiryama zuwansa ba, gashi harya fara sakata ƙiba, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, duka shekarunta nawa da za'ace ta ɗauki ciki? Kamar yanda Jack ya faɗa, ita kanta tasan dan tayi gaggawar yin aurene kawai, bakomai ya jawo hakanba kuma sai ƙaunar Jawaad data tunzurata, da shawarar Mummynta, anya kuwa bazata zubarba kawai ta huta? Iyakaci dai ayi badakalar da za'ai na ɗan lokaci ta wuce, daga baya komai zai lafa a wuce wajen. Zama tai a bakin gado ta dafe kanta tare da cije bakinta saboda murɗawar da cikinta ke mata, kusan min tuna uku tana a haka kafin ta samu ya lafa mata, sai wani zazzaɓi da takeji wanda ya zame mata jiki a yanzu kullum yamma saita yisa. Wayarta ta ɗauka ta kira Aamila, babu jimawa sai gata ta shigo ɗakin. "Sisi lafiya kike kirana?". Miƙewa Shahudah tayi idonta akan Aamila, "Aamila na yarda da shawararku zan zubar da cikinnan kawai". Zaro ido Aamila tayi tana ɗan ja baya, "Wai da gaske dan ALLAH?". "Na taɓa miki maganar hakan?". "A'a, ai abunne da mamaki, keda kike mugun tsoron Brother Jawaad karya rabu dake, amma yanzu lokaci ɗaya kizo da batun amincewa". Tsaki Shahudah taɗanyi, "Karki damu, ni nasan barazanace kawai, son da bb kemin bazai taɓa yarda ya rabu daniba wlhy, kawai yanamin burgane dan karna zubar, idan kuma yay haƙuri nan gaba ai zan haihun, amma gaskiya ba yanzu ba". "Kinyi ƙyan kai gaskiya, yanzu ke mikike buƙata?". "Shawarar da nake buƙata kenan daga gareki, ɗazun jack yace yasan maganin da zaimin aiki ba tare da nasha wahala ba, inaga kije kufita tare kozaku samu a wani pharmacy ɗin, sai dai dan ALLAH karki bar Mummy ta sani". "Karki damu, insha ALLAHU babu wanda zaiji".

Koda Aamila ta fice sai Shahudah ta koma ta zauna, wayarta ta ɗauka ta dannama Jawaad kira, sai dai harta katse bai ɗagaba. Text massege ta tura masa kamar yanda suka shirya da jack, kodaga baya cikin ya zube wai bazai zargeta akan itace ta zubarba. Mummy batasan mi suke shiryawa ba, a gabanta Aamila da jack suka fita a gidan. Sun bazama neman maganai cikin manyan pharmacy's ɗin garin, amma samunsa ya gagara, saboda ba kowane ke saidawa ba, dabara ce ta faɗoma Aamila a rai ta kira number Munira cikin yaran gidan su Jawaad, dan ta taɓa bata labarin wata ƙawarta da ta raka zubar da ciki. Sun sanar mata abinda suke buƙata sai dai basu faɗa mata gaskiyar wanda zaiyi amfani da shiba, itace ta kira likitan daya bama ƙawarta wancan maganin ta haɗasu dasu Aamila, shi kuma yay musu kwatancen inda zasu sameshi. A asibitinsa da ya kasance privet suka samesa, babu ko ɗar suka biya kuɗin daya yanka musu ya basu allurar da za'ai amfani da ita, a cewarsa itace tafi aiki shap-shap kuma bata cutarwa. Sai da jack ya duba sukkan bayanan allurar ya kuma tabbatar da maganar Doctor sannan ya suka amsa suka nufi gida.

Jack bashi da shamaki da shiga ɗakin Shahudah a duk sanda yaso, dan haka koda suka dawo a gaban idon Mummy ya shiga, Aamila kuma ta zauna a falon dansu ɓadda hankalin Mummy wai. Ƙudundune ya iske Shahudah zazzaɓi ya rufeta, ya yaye bargon data rufa yana taɓa gefen wuyanta, buɗe idanunta tayi, ganin jack ne yasata miƙewa da ƙyar tana kallonsa, "Kun samo?" tambayar data fara jefa masa kenan cikin harshen turanci. Kansa ya ɗaga mata, ya ciro allurar daga aljihunsa yana nuna mata. Amsa tayi ta jujjuya allurar a hannunta, sai kuma ta kallesa da tambayarsa wai miyasa basu sayo maganinba? Yafasan batason allura. Bayanin duk yanda sukai ya bata, ya kuma tabbatar mata wannan allurar tafi maganin inganci, hakan ya saka ta aminta da batunsa. Hannu ta bashi yay mata allurar tana matse baki, can ƙasan zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai biyo baya daga Jawaad.............✍🏻

*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_

*_____________________________________* *_BOOK ONE_* _Shafi na ashirin da uku_ *_____________________________________*

..........Tunda aka buɗe mana katafaren gate ɗin makarantar muka shigo nake baje idanu da hanci ina kallon wannan tsararren gini da tamkar ba makaranta ba. Yanzu nan ni Bilkisu ɗiyar malam Ado makahoce cikin wannan makarantar? Abu kamar mafarki kamar kuma almara. Niko tayaya zan manta da Dad a rayuwata. Ƙwallar data cikamin ido na share ina fitowa daga cikin motar, ɗalibai duk suna cikin aji, hakan yasa security kawai kake iya gani na shawagi sai malamai. Mun samu tarba ta musamman ga wani malamin da nakeda tabbacin yazo garemune bisa umarnin Dad, na gaishesa cikin girmamawar da naga nuna jin daɗinsa saman fusakarsa. Bisa jagorancinsa muka isa har Office ɗin shugabar makarantar, bayan an bani wani form na cike aka haɗani da malamai uku sukaimini interview, duk da karatun bai kasance ɗayaba sun yabama ƙoƙarina. Na sauke nannauyan numfashi da naji cewar komai yayi, duk da dai ba ɗari bisa ɗari na ƙoƙartaba amma sun amsheni, to dayake kuma abun ya haɗa da harkar kuɗi sai babu wata matsala aka kammala komai tsaf. Malamin nan dai yana tare dani muka fito, sallama mukai da driver ya tafi domin shi ya gama aikinsa, sai kuma naji hawaye sun cikamin ido, a gaban idona ya wuce. Malamin ya kalleni yana murmushi, "Ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai-dai kinji, alkairin Alhaji a gareni bazaisa na zuba ido kiƙi nasara ba, sai dai idan ALLAH ya ƙaddaro hakan, akwai yarinyata anan makarantar insha ALLAHU zan haɗaki da ita, zata taimaka miki sosai kafin ku fara zana jarabawar, tunda akwai tazarar kusan 5weeks yanzu haka insha ALLAHU". Cikin girmamawa nace, "Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi, ya kuma bada ladan zuminci". "Amin" ya faɗa yana maijin daɗin addu'ar yarinyar da yaba tarbiyyarta, dan kuwa yakuma tabbatarwa ba'a gidan Alhaji ta tashiba, saboda sanin da yayma yaransa da sam tarbiyya bata gama wadatar da suba. Security ɗin dake kusa ya kira, shine ya kwasar min kayana muka nufi inda yace min Hostel ɗinmu kenan, dan lokacin an tashi Ɗalibai duk sun shige ciki. Mun iske hostel ɗin shiru babu wata hayaniya a cikinsa, sannan ɗalibanma ɗai-ɗai muke gani suna shawagi, kowa kuma harkar gabansa yake babu ruwan wani da wani, a ƙofar wani ɗaki mukaja birki, security ɗin ya ƙwankwasa ƙofar, babu bata lokaci aka buɗe. Budurwa da bazata gaza sa'a taba ce ta fito, sai dai shigarta zai tabbatar maka da wahala ta kasance musulma. Ganin malamin dake tare danine yasakata juyawa da gudu ciki tana dariya, ko minti biyu bata rufaba sai gata sun fito itada wata mai tsananin kama da malamin. "Daddy baƙuwar harta iso?" ta faɗa cikin zumuɗi tana ɗan tsalle a gabansa. Murmushi yayi mata, ya jinjina kansa tare da faɗin "Eh Ummie na ta iso, gata nan ma sunanta Bilkisu Adam". Juyowa tai gareni cikin ɗoki tace, "Barka da zuwa Bily cikin makarantarmu". Haɗiye hawayen farin cikin da suka cikamin ido nayi ina amsa mata, banyi zaton zanje waje a karbeni lokaci gudaba kamar yanda Ummie tai mini yau, gata dai da gani itama ƴar gatace amma sam babu fuskar wulaƙanci a tare da ita. Ta kama hannuna cikin nata tana sauraren bayanin da daddynta ke mata a kaina cikin nuna zaƙuwa da ɗoki, ya maida dubansa gareni yana faɗin, "Bilkisu wannan itace ɗiyata kamar yanda na sanar miki, karkiji komai ki saki jikinki da ita, insha ALLAHU zakiji daɗin zama da ita kamar yanda nima nake ƙyautata mata zato a kanki, komai na tsarin makarantar zata fahimtar dake, karkuma ki cutama kanki, duk abinda ya shige miki duhu ki tambayeta kinji". Kaina na ɗaga masa ina risinawar girmamawa a garesa, nace, "Insha ALLAHU Daddy, ngd sosai da karamcinka a gareni". "Karki damu Bilkisu, Alhaji Aliyu ya wuce hakan ma a gareni, ALLAH ya bada nasara ni bara na wuce". Sallama yay mana Ummie nata masa shagwaɓa ya wuce ya barmu. Itako ta rungumeni tana sake min barka da zuwa, ta shiga ƙwalama wasu kira da nake ƙyautata zaton ƙawayentane, dan kuwa daga cikin ɗakin suka fito harda wadda ta leƙo ɗazun, su uku ne, kuma duk bazasu wuce sa'anni naba. Biyu a ciki sun amsheni hannu biyu, ɗaya kam dai sai yamutse fuska takeyi, ban damuba dan na saba ganin irinta tun shaiɗan na yawo da ɗan kanfai cikin duniya. Sune suka kwasar min kaya har cikin ɗakin dake da gado biyar kacal a cikinsa, sannan komai tsaf tamkar ba makaranta ba. Zaunar dani Ummie tayi a gado na ƙarshen ɗakin tana faɗin, "Wannan shine gadonki, akwai mai shi da, amma ALLAH ya mata rasuwa hutun da mukaje ɗinnan, yaya tace, tanada ciwon sikila ne. Nace, "ALLAH sarki, ALLAH ya gafarta mata, kukuma ya baku haƙurin rashinta". "Amin" Ummi ta faɗa tana sharar hawaye. Tace, "Sunana Sumayya Sadik, amma anfi sanina da Ummie saboda sunan Momy na aka saka min". Murmushi nayi mata, nace, "Nice name, nima zance Ummie ɗin tunda sunan Momynmu ne". Ƴar dariya tayi tajin daɗi, ta nuna sauran su ukun, "Waɗanan ƙawayenmu ne, mu biyarne a guruf ɗinmu kafin rasuwar ƴar uwata, mu ƙawayen junane, ajinmu ɗaya, abu ɗaya muke karanta, kuma burinmu ɗaya. Wannan sunanta Nazifa Sulaiman, wannan kuma Rebecca Emanuel, sai Zuhrah Abbas". "Masha ALLAH, sunayenku masu daɗi dukan ku". Duk Dariya sukai am ma banda Nazifa da tun farko ta Nuna bata ra'ayina, yanzunma dai tana kwance a gadonta sai latse-latsen wayama take. Nima na faɗa musu sunana Bilkisu Adam. Rebecca tai saurin faɗin, "Bilkisu muna fata zaki cike mana gurbin guruf ɗinmu da muka rasa a yanzun". Murmushi nai bance komaiba, dan bazance zanyi saurin aminta da suba tunda banga halayyarsu ba........ Zuhrah ta katse tunanina da faɗin, "Please Bily karkice a'a, muna buƙatarki a cikinmu dan mudai kin mana". Nanma murmushi nayi dai, a raina ina mamakin ni da kullum su aunty Shahudah ke kushe munina da ƙyamata ce kuma har suke iƙirarin na musu su kuma?. Magiya suka shiga min da roƙon karnace a'a, dan haka kawai sainace musu su bari zanyi tunani to. Murna sukaitayi wadda ni taita bani mamaki, sai dai ina jiyo tsakin da Nazifa tayi kaɗan. Ban damuba, dan amsar da ƴan uwanta kawai sukaimin ta wadatar dani, da taimakonsu na kintsa kayana tsaf, daga nan muka zauna sunamin lissafin abinda makarantar ta ƙunsa. Zakuyi mamaki idan nace muku harna kwanta barcin dare ban tuno ko ɗaya daga cikin su aunty Aamila ba bayan Dad kawai da tunda muka iso nake jerama addu'a a zuciyata.

_________________________

Kamar yanda dokar allurar take sai bayan minti arba'in zata fara aiki, dan haka Jack ya fita yabar Shahudah a ɗakin ita kaɗai, kwanciya tai luf a gadon, sai kuma lokacinne wani mashahurin tsoro da fargaba suke shigarta, babu abinda ke mata kaikawo cikin rai sai Jawaad. Tabbas ita kanta tasan ta taro match na haƙiƙa a filin da bata da ƙarfin buga ƙwallon, fatanta dai ALLAH yasa tsarin da sukai ya tafi dai-dai, shine kawai zai zama mafita a gareta daga buyagin Jawaad mai zuciyar masifa idan aka ƙuresa. Da wannan tunanin wani barci mai daɗi ya kwasheta.

★★★★★★

Haka kawai gaban Jawaad yaketa faɗuwa, kuma sai Shahudah kezo masa cikin rai baisan dalilin hakanba, zaune suke a Office ɗinsa shi dasu Aliyu suna tsara yanda zasu fuskanci case ɗin da aka basu dangane da ƴan fashin nan a safiyar yau. Tsayawa yay daga rubutun da yake a blackboard ya matse maker ɗin hannunsa yana dafe ƙirjinsa. Zuba masa idanu su Hafeez sukai, Jabeer yace, "Boss lafiya kuwa?". Numfashi ya sauke a hankali yana musu murmushin yaƙe, yaɗan girgiza kansa sai kuma ya cigaba da abinda yakeyi. Badan sun yardaba suka barshi, shikuma zuciyarsa na cigaba da tsitstsinkewa. Lallai yanaji a ransa wani abu zai faru dashi kuwa, to amma minene? Wannan amsarce baida ita, dan haka ya share abun yana cigaba da karanto addu'a cikin ransa da maida hankali gasu Aliyun.......

★★★★★★

Wani azababben ciwon marane ya farkar da Shahudah daga daddaɗan barcin daya ɗauketa, ba tare data shiryaba ta fasa ƙarar data jawo hankalin su Mummy dake falo, a matuƙar rikice suka shigo ɗakin har suna ƴar rige-rige kuwa. Dukansu kanta sukai suna tambayar lafiya kuwa? Cikin kuka take nuna musu cikinta, a razane Mummy tabi santaleliyar farar ƙafar Shahudah da jini kebi da kallo, har taune harshe take wajen ambaton "Jiniii!!?". Cikin ruɗewa Aamila itama ta maimaita "Jini kuma Mummy?". Shi dai jack baice komaiba, saboda da hausa su Mummy sukai magana baiji mi sukace ba, sai ƙoƙarin ɗaura kan Shahudah ma yake bisa cinyarsa yana jero mata sorry. Gaba ɗaya Mummy ta rikice, jikinta sai rawa yake tana jerama Shahudah tambaya akan miya sameta? Miya kawo zubar wannan jinin kuma?. Bata samu amsa ko guda ba, dan haka ta fice kamar zararriya, Dad ta kira a waya tana sanar masa yazo gida babu lafiya. Dama yana hanya, dan haka yace mata ga shinan zuwa a rikice.

Ba Mummy ba, hatta su Aamila da sukasan tushen komai sun rikice, dan jini bana wasaba ya ɓallema Shahudah, ta jiƙe inda take kwance sharkaf cikin mintunan da basu wuce goma ba, jikinta kam harya fara saki saboda mahaukacin jinin da take ɓararwa. A wannan halin Salman da Dad sukazo suka samesu, suma rikicewar sukai, wasu suce a kira Doctor wasu suce a tafi asibiti, daga ƙarshe dai sukabi shawarar Salman da yace akira Doctor kawai, dan kafin su isa asibiti Shahudah zata iya rasa rantama gaba ɗaya. Kowa ya gamsu da hakan, dan haka aka dannama family Doctor ɗinsu kiran gaggawa. Doctor ya iso akan lokaci, dan haka ya kora kowa a ɗakin ya shiga ƙoƙarin ganin ya shawo kan matsalar sai dai hakan ya faskara cikin sauƙi, dan kuwa tuni Shahudah da dai ta sanƙame masa alamar suma. Dole Doctor ya nema taimakon wani abokin aikinsa, babu ɓata lokaci shima ya iso tare da ƙaro musu ƙarin kayan aiki. Su Dad duk sun rasa ina zasu saka kansu, Mummy kam kuka take rurus wanda ya kasance da biyu, damuwar halin da ɗiyarta ta tsinci kanta da ɓoyayyen burinsu akan cikin da suka ƙwallafa rai. Salman zai kira Jawaad Dad ya hanashi, acewarsa kar a tada masa da hankaki su jira suga abinda zai biyo baya tukinna. Dole Salman ya haƙura ya ajiye wayar suka cigaba da zagayen falo, inda lokaci-lokaci Dad kan jeho musu tambaya akan miya kawo sanadin matsalar?. Amsa ɗaya Mummy ke badawa "Ita bata saniba, wai Shahudah tana ɗakine tun ɗazun tana barci". Sam Dad bai gamsu da wannan maganarba, amma sai baija zancenba saboda a yanzu damuwarsu a ceto ran Shahudah tukunna.

★★★★★★

Koda su Rose suka fita suka bar Jawaad shi kaɗai a office ɗin sai zuciyarsa ta kuma ƙuntata da zungurinsa da tunanin Shahudah, abin ya ɗaure masa kai sosai, dan kuwa a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya saboda takaicinta da yakeji ko kawota a ransa bayayi ma sam. Yanzunma dai ƙoƙarin sake ingijeta yay a zuciyarsa ya shiga wani aikin, yanayi yana jan tsaki a duk sanda ta sake faɗo masa cikin rai. A haka dai har ya samu nasarar janyeta cikin rai baki ɗaya ya cigaba da harkokinsa kawai.

★★★★★★★

Likitocin nan sunsha wahala kafin su sami nasarar shawo kan jinin dake kwarara a jikin Shahudah, daga nan suka koma ƙoƙarin ganin numfashinta ya dawo, bayan ɗaukar kusan awa biyar a kanta suka samu komai ya dai-daita, sai dai sun zangaɗa mata allurar barci tare da ƙarin ruwa. Suka fito kowa na yarce gumi, tare da sanarma su Dad jini da Shahudah take buƙata saboda nata data kwararar. A nannefa aka shiga kallon kallo, dan kuwa kaf gidan jinin kowa baima Shahudah sai na Jawaad, ta taɓa samun wata matsala lokacin tana secondary, har takai ana bukatar ƙara mata jini, a time ɗin an gwada na kowa a gidan bai mataba sai Jawaad, lokacin shikuma sunje can tare da kawu Nasiru ne. Dad yace, "To amma Doctor kafin muje ga wannan yaya maganar cikin jikinta ne?". "Alhaji ai muma ajiye batun ciki gefe, yanzu dai jinin muke buƙata da gaggawa domin tana matuƙar bukatarsa gaskiya, daga baya mayi maganar cikin". Ajiyar zuciya Dad yayi, ya ciro wayarsa a aljihu yay kiran Jawaad, kusan kira uku bai amsaba, hakanne ya saka Dad tunanin lallai Jawaad yana kan aiki, dan baya taɓa masa kira biyu a ce bai ɗaukaba inhar yana kusa. Yana cikin yin zancen zucine sai ga kiran Jay ɗin ya shigo, jikin Dad har rawa yake ya ɗaga. Haƙuri Jawaad ya bashi akan yay masa afuwa suna yin sallar la'asar ne. Ajiyar zuciya Dad ya sauke, danshi ruɗewar da suka tsinci kansu a ciki bata bari sunji kiran sallarba ma. "Babu komai My Son, wlhy wata matsalace ta taso shine nace ALLAH yasa bakan aiki kakeba zan katseka". Gaban Jawaad ya faɗi, dan muryar Dad kawai ta mugun tsorashi, yay saurin faɗin, "Babu damuwa Dad, kana buƙatar ganinane?". "Sosaima kuwa my son". "Insha ALLAHU ka bani nanda mintuna talatin zan iso". "ALLAH ya kawoka lafiya". Dad ya faɗa yana sauke wayar a kunnensa.

Jawaad ya rasa mizaiyi hasashe a wannan wayar da sukai da Dad, jacket ɗinsa sky blue daya ɗoro saman baƙaƙen kayan jikinsa ya ɗauka jikin hanga ya fice cikin matuƙar hanzarinsa. Gimba na hangosa ya taso da hanzari yazo ya buɗe masa mota ya shiga, ba tare da ya tambayi ina suka dosaba ya tada motar suka fito. Saida suka hau kan titi Gimba yace, "Boss ina zamuje". "Zangina road" kawai ya iya furata masa yaja bakinsa ya tsuƙe. Gimba daya fahimci ina suka dosa ya ɗauki hanyar da zata sadasu da gidan su Shahudah. Tunda aka buɗe gate ɗin gidan gaban Aamila da tasan dokar ya shiga faɗuwa, jitake kamar Jawaad zai gane komai da ya faru a kan fuskarta. Jawaad ya shigo cikin bajintarsa da jin shiɗinfa ya isa, fuskarsa sam babu walwa. Yanda yaga duk sun nutsu waje guda sun zuba tagumine ya sakashi tsaresu da mayun idanunsa, Ya sauke akan Jack dake zaune kusa da Salman, aransa ya furta "Jack again?". Janyewa yay ya maida ga Dad daya miƙe tsaye yana faɗin, "Yauwa My son ka iso?". Kai kawai Jawaad ya iya jinjina masa yana haɗiye wani yawu mai kauri saboda ganin Jack. Mummy ma ta miƙe ta nufoshi kamar yanda Dad yayi. Kusan a tare suke ƙoƙarin masa bayani, dan haka ya zuba musu idanu ko ƙyaftawa bayayi. Tunda suka ambaci jini da Shahudah ta zubar yaji tamkar an buga masa guduma a kansa, ya wani lumshe idanunsa da suka fara canja launi yana fidda numfashi da sauri-sauri......... Maganar Dad dake cewa, "My Son yanzu haka sunce tana buƙatar jini da gaggawa, inba hakaba zamu iya rasata" ta katse tunaninsa. Buɗe idanunsa yayi yana buso numfashinsa, ba tare daya cema su Dad ɗin komaiba ya juya ya kalli likitocin dake tsaye tsuru-tsuru suna kallonsa. Takawa ya farayi a hankali cikin nuna halin ko in kula zuwa garesu, ya zauna cikin kujerar dake wajen yana harɗe ƙafafu tare da miƙa musu hannunsa kawai, saboda t-sheat ce jikinsa baƙa wadda ta fidda dukkan ainahin surarsa, sai jacket dake samanta itama tsawon hannun iyakarsa gwiwar hannunsa. Yanda Doctor yaga Jawaad ɗin duk sai ya dabarbarce, a harzuƙe Jawaad ya kallesa, cikin daka tsawa yace, "Jinin zaka ɗiba kokuwa kallona zaka tsayayi malam?!". "A'a yallaɓai, ALLAH ya huci zuciyarka" Doctor ya faɗa jiki na ɓari.