Reader mode
Kwai acikin kaya book 1 Chapter 25
4,106 words
Abubuwan da Jay yakeyi ba ƙaramin ɓata ran Uncle's nashi sukeba, amma duk sai suka danne zukatansu da addu'ar ALLAH yasa karya watsa musu ƙasa a idanunsu yadai zaɓi matar aure kamar yanda manufar taron take. Dukanin tunaninsu bai gama tsayawaba sai da Jawaad ya miƙe bayan mintuna biyar da ajiye cokalinsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yay musu sallama tare da miƙa kalamun godiya na wannan tarba daya samu daga garesu, yay addu'ar sake samun haɗin kai na wannan family mai ɗorewa, tare da jaddada musu abinda sukai masa yau din ya ƙayatar dashi kuma ya bashi farin cikin da bazai mantaba har sai ya rubutashi ya ajiye. Kowa fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallon Jawaad ɗin, kowa yaji daɗin kalamansa kuwa, dan basuyi zaton jin hakan daga gareba. Shikuma yay wani munafikin murmushin da ya kusa zautar da dukkan ƴanmatan wajen, shikuma shi kaɗai yasan ma'anar kayansa, kafin ya nema alfarmar tafiya domin ya huta saboda ciwo da kansa ke ɗan masa kaɗan-kaɗan na alamar gajiyar tafiya. Basu da yanda suka iya dashi, amma dai Uncle Nasir ya dakatar dashi har ya miƙe yay ɗan guntun bayani na sake masa sannu da zuwa, tare da roƙon Jawaad ɗin ya sake jikinsa tare da yafema duk wanda yake ganin ya masa ba dai-dai ba akan abinda ya faru wancan karo har yayma gidan yaji na kusan shekara. Nanma dai godiyar Jawaad ya sakeyi sannan ya tabbatar musu shi komai ya wuce a ransa tuni, suma yana fatan hakan daga garesu, daga ƙarshe yay musu sallama ya koma sashensa. Murmushi kawai Umma tai tana girgiza kai da bin Jawaad ɗin da kallo harya ɓacema ganinsu. Barinsa wajen ya saka taron ya fara watsewa a hankali, mafi yawansu zukatansu babu daɗi a ciki, musamman ma ƴan matan da suka ƙwallafa rai a kansa babu gaira babu sabar. Shi dai baimasan sunaiba, dan yana barin gurin ƙwafa yay yana maijin takaicin rainin da ake neman jawo masa wajen yaran gidan, zama yay a falon yana jiran shigowarsu Umma domin su gaisa kafin ya kwanta. Zaman nasa kuwa baifi da mintuna goma ba sai ga Umma dasu batool sun shigo. Dariya Batool ta fara masa tana tafa hannaye. Harara yaketa zabga dan yasan tsokanarsa zatayi, mata amma baice komaiba, dan itace kawai ke iya taɓasa kasancewar sa'anni suke dashi ta kwana lafiya, wani lokacinma har yakan biye mata, batool bata taɓa aureba, munadai tayata fatan samun miji na gari. Ɗauke idonsa yay akan Batool ɗin data zauna a kujerar gefensa tana faɗin, "Kaga mai ƴammata buhu-buhu na Shahudah bada kanka a sare kazo gida kace ya faɗi". "Umma ALLAH kicema yarinyarnan ta kama kanta kota fita falonnan da ƙafa guda". Jay yay maganar cikin matuƙar ɓata fuska. Murmushi Ummah dake zama tayi, yayinda Batool ta bushe da dariya, hakama su Nabeelah duk sai gyale sukasa suna kare fuska dan karya gani. "Manta da ita kaji My son, yau ba ranar ɓata fuska bace ba, ina fatan dai ka dawo cikin ƙoshin lafiya?". Numfashi yaɗan sauke mai haɗe da ajiyar zuciya yana faɗin, "Alhmdllh Ummana, sai dai kewarku kawai, yaya jikin Baba?". "A jikinsa Alhmdllh, ai yama samu sauƙi dama murace ta canjawar wannan yanayin, sai kuma jikin tsufa da aketa rarrakawa". Jawaad yace, "ALLAH sarki baba, ALLAH ya ƙara tsahon rai". Da amin suka amsa su duka. Su Nabeelah suka sake gaidashi cikin girmamawa, yayinda shima yake amsawa da ƴar kulawa. Batool kam cayay bazai amsa mata gaisuwaba. Tace, "Karka amsa mana Jay, duk dai wani ɗacin ranka kayisa ka gama Aurene sai anyi makashi, danni harma na zaɓa maka waɗanda suka dace dakai a ƴammatan nan da aketa faman maka talla kana wani fuskewa, auren gata zamuyi maka, ƴammata uku zuƙa-zuƙa sai Shahudah uwar gida ran gida". Remote dake center table ya ɗauka ya jefeta dashi, ta tashi ta fice daga falon tana dariya, shi kuma ya kuma haɗe fuska yana ƙwafa. Su Nabeelah ma dai ficewa sukai dansu bashi waje ya tattauna da Umma. Dariya Umma ma taɗanyi kaɗan tana faɗin, "Da gaskefa Fatima keyi, waɗanan yaran daka gani dansu aka shirya maka wannan tarbar, ni kuma naga bakama nuna wata alamar zaka zaɓa ɗinba". Cikin takaici Jay yace, "Na sani Ummah, amma dan ALLAH karku biyema shirmensu, zan kuma taka musu birkine dan wannan neman jawomin rainine wajen yara kawai, bansan minene matsalarsu da aurena ba ko rashin yinsa? Nace musu ina buƙatar aurene ko yaya? Za'a wani ringa cusamin yara ƙanan kamar wani ɗan iska......" Cikin tare masa numfashi Umma tace, "Dole zaka buƙaci aure Jawaad, dan koba komai ka rigada ka ɗanɗani zama da mace, kuma koba hakaba ma cikar mutuncinka shine auren, babu wanda zaka sanarma kai kamiline ya yarda bayan mu da mukasan kai wanene, ka daure koda ba'a cikin yaran nasuba ka sami matar aure, idan kuma matarka kakeson maidawa ka maidota dan maybe ta canja zuwa yanzu, tunda na fahimci son da kake matane ya hanaka sake kallon wata mace da sigar auren, baba kansa yana damuwa sosai da rashin sake aurenka, shekarafa huɗu kenan da wasu watanni da rabuwarka da matarka, da aurenma kayi ƙila da yanzu ƴan jikokinmu na kai kawo a falonnan, sannan akwai wasu takardun dukiyarka masu matuƙar muhimmanci dake da alamar tambaya, dan sune silar komai da lokacine kawai zai buɗe kowanne sirrin da mu da kai zamu fahimta baki ɗaya...." Shiru Jawaad yay yana nazari dason ƙarin bayani akan maganarta ta ƙarshe, sai dai bata bashi wata damar masa tambaya akan hakanba, shiyyasa yay shiru yana kallonta, sai kuma ya sauke numfashi yana faɗin, "Shikenan Ummah, kuyi haƙuri indai aurene zanyi da izinin ALLAH, duk da har yanzu babu wata mace a raina, kuma ba hasashenku bane ya hanani aure na cewar son Hudah ne har yanzu, sai dai kodan farin cikinku zanyi insha ALLAH, amma ku kwantar da hankalinku ku bani lokaci, dan banason a sake komawa ƴar gidan jiya kamar aurena na baya". Umma tace, "To ALLAH ya tabbatar mana da alkairi. ya kuma kawo mana ta gari wadda zata zo mana da alkairai". Bai iya ce mata komaiba, dan gaba ɗaya sun dagula masa lissafi, basu san yanda yakejin haushin mata bane a ransa da sunbar ambatar aurenan da suka damu ransu akan sai ya ƙara..............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/T8bCANmJA5E
*_MANHA HAUSA NOVELS_*
https://youtu.be/xUINNiDdeH0
*_AL-ƘALAMI TV_*
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=102039014953186&id=100054412625125
*_Facebook_* _Bilyn Abdull_ 😉
*_Typing📲_*
*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_
*__________________________________* *_BOOK ONE_* _Shafi na talatin da bakwai_ *__________________________________*
............Bayan shigewar Qaseem da Bily babu daɗewa Mummy na zaune tana saƙawa da kwancewa ta yanda zasu ɓulloma zaman Shahudah da Jawaad kira ya shigowa wayarta. Ɗauka tayi babu ɓata lokaci, dan kuwa kirane mai matuƙar muhimmanci. Sama-sama sukai gaisuwa mai kiran ta fara zayyane mata abinda ya faru a family house ɗin su Jay a yau, wato dai walimar cin abincin da aka shirya masa mai taken yaɗa manufar tallar matan aure. Ran Mummy ya ɓaci ƙololuwa, dan a ganinta wannan tsagwaron munafurci ne kawai ƴan uwan nata suka shirya, taya zasu nema aikata haka?, bayan sunsan akwai soyayya mai ƙarfi tsakanin Shahudah da Jawaad ɗin, saɓanine kawai da sharrin shaiɗan ya gitta har wancan matsalar ta faru, maimakon su nema hanyar da za'a sulhunta shine zasu haɗa wannan annamimancin? To lallai lokaci yayi da za'ai uwar watsi kuwa ashe, yanzu ace har mahaifiyarsu ta gaza kiranta ta sanar mata balle ƴan uwanta su Uncle Uwaisu, dan bata saka Maimuna ƙanwarta a wannan sabgar, tunda tuni ta nuna musu bata tare dasu ita dama. A wannan dare gaba ɗaya barci gagarar idanun Mummy yayi, gashi Dad baya gari, tayi kiran wayarsa yafi sau goma taƙi shiga, ta kuma kira Mama Atika ba'a ɗaukaba, ta kira Shahudah shima bai shigaba. Gaba ɗaya sai kanta ya ƙara ɗaukar zafi, sai sauke ajiyar zuciya takeyi a jere a jere.
Gari na wayewa duk da uban barcin dake cin idanunta haka tai shiri tunda farar safiya ta fice a gidan, ko jiran driver bata tsaya yiba, dan aganinta kafin yazo an gama ɓata mata lokacinta.
Tun shigowarta falon mama Atika dake zaune tana lazimi ke kallonta, Mummy sai sake cika take tana batsewa, ganinfa mahaifiyartasu ba ida addu'ar nan tata zataiba ya sata faɗin, "Wai nikam mama wannan addu'ar bata ƙarewa ne?, nifa a ƙage nazo". Mama Atika batace mata komaiba, hakama bata tsaya da addu'arta ba sai da takai aya, ta shafa tana faɗin, "Ke dai Wlhy Ai'sha sam baki da ɗabi'ar ƙwarai, ba ƙaramin lalacewa rayuwarki taiba a garincan na marasa sallah, mike faruwa na ganki da wannan uwar safiyar?". Cikin sake ɓata fuska Mummy tace, "Ba dole ake ganina da farar safiya ba, yanzu mama dan ALLAH munafurcin da ake shirin ƙullawa ya ƙyautu kenan a gidannan?, kowa yasan alaƙar dake tsakanin Shahudah da yaron nan na wajen Abdul-aziz, amma shine za'a shirya wani annamimanci ta bayan fage ba tare da nasaniba ma........" Saurin katseta mama Atika tai da faɗin, "Ke da ALLAH rufama mutane baki, waye zai sake haɗa sabgarsa da wannan shashashar ƴar taku mai kama da wadda aka yaye jiya, idan barci kike to kidawo hankalinki Ai'sha, badan wawiyar yarinyarnanba da yanzu mun gama mallakar fiyema da abinda muke buƙata, amma tazo ta ɓata mana komai saboda ita shashashar yarinyace taɓararriya, ki duba yanzu wulakancin data jawo mana ne ya saka dukkan manufofin mutan gidannan ya gama bayyana, yanzu kowama yima ƴarsa farautar yaron nan yake, dan dama can shakkatane ya sakasu haɗiye ƙwaɗayinsu a fili, dukda wasunsu na taƙamar komai yana hannunsu ne ai, maimakon kuma a shekaru huɗun nan ku nema hanyar gyara komai tunkan abunma yay nisa ta bashi haƙuri amma sai kuka ɗauketa kuka sake turawa cikin yahudawa, kekuma kika ɗauki fushi damu, yanzu har nai ciwona na gama a gidannan Ai'sha baki leƙoniba, saboda ke mai ƴa ko? To mune muka saketa? Kokuwa mune muka sakashi sakinta? Muda ta ɓatama komai mune ya dace muyi fushi ba keba? ai ko......." "Nidai mama naji, ya isa dan ALLAH, sai faɗa kike ko haɗiyar yawu baƙyayi, naji anyi kuskure, amma kuma ai bai ƙyautu a wancan karon kowa yaƙi fahimtar ƙaddarace sanadin komai ba, ALLAH ya rubuta cikinnan bazaizo duniyaba, daga baya kuma dai ai komai ya dawo ya daidaita, amma sai babu wanda ya kirani a cikinku, ta yaya bazan ɗauki fushiba to?". "Kedai kika sani, ai kuma fushin naki bai miki amfaniba, tunda gashi kin dawo da ƙafarki ko?, kuma a lokacin da kuka makara keda ƴar taki, dan kuwa a yanzu filin dagar ya zama na mafarauta da yawa". "Mama ki daina faɗin mun makara, babu wata makara tunda kowa yasan Jawaad nason Shahudah, kuna insha ALLAHU a cikin watannan zata dawo ƙasarnan". Baki mama Atika ta taɓe da yamusashshiyar fatarta ta tsufa, tace, "Kudai kuka jiyo, danni tawa tai ƙyau, dama kune masu amfana baniba, a shekaruna ni yanzu amfanin mi abinda akemawa ɗin zaimin?, komai da kukaga inayi danku nake yinsa". Shiru itadai Mummy tayi bata tankaba, tana nan zaune har su Uncle Uwaisu suka shigo gaishe da mama Atika, annanfa suma Mummy ta balbalesu da masifa, ta inda take shiga ba tanan take fitaba. Wasa-wasa rigima ta kaure a tsakaninsu, dan kuwa yanzu suma ba ɗaga mata ƙafa zasuyiba duk da tana babbar yarsu a ɗakin, duk yanda mama Atika taso suyi shiru sunƙi, har sai da ta saka musu kuka sannan suka dawo hankalinsu sukai shiru.
__________________________________
To nidai sam bansan bikin da akeba a gidan, naji dai Aunty Aamilah na magana akan Aunty Shahudah zata dawo, banji an faɗi rana ba, bakuma a faɗaminba, nima sai banbi takaiba, dan bakowace sabgar gidan nake shigaba musamman ma yanzu danasan ciwon kaina.
Tsawon kwanakin da suka biyo baya a satin ban sake jin komai na faɗuwar gaba ba, hakama wanda muka taro a ranar nan ban sake ganin koda ɗaya a cikinsuba. Duk da abubuwa masu yawa game dashi sunƙi barin raina, duk kuma ƙoƙarin turesun da nakeyi hakan baisa na damu kaina da rashin ganin nasa ba, na cigaba da harkokin gabana har a yau da mukai safiyar fita aiki kasancewarta Monday tushen aiki. Kamar kullum nayi tsaf dani, tamkar ka saceni ka gudu, musamman ma data kasance a yau sanye nake da baƙaƙen suit na mata wando da riga, na kawo farin baby hijjab na saka tamkar yanda na saba a kowace rana, kayan sun zaunamin sosai a jiki tamkar dan jikin aka haliccesu, na saka siririn farin eyeglasess ɗina sannan na fito ɗauke da takalmana a hannu. Babu kowa a falon, na ajiye takalman na nufi kicin, kuku harya kammala haɗa mana breakfast ni da Yah Qaseem, tea na shiga haɗawa muna gaisawa dashi, ban fitaba na zauna a ɗaya daga kujerun huɗun dake a kicin din, tebir a tsakkiyarsu, ina fara shan shayin Yah Qaseem na shigowa shi da Salman. Nayi mamakin ganin Yah Salman da wannan farar safiyar, shi da kullum sai anyi fama dashi ma yake tashi da safen yay shirin zuwa aiki, da yake a kamfanin Dad yake aikin sai yakai goma bai fitaba ma. Hannu Yah Qaseem ya miƙomin alamar mu gaisa, amma sai na girgiza masa kai ina murmushi da faɗin, "Yaya ina kwana". Hararata yayi sannan ya zauna, Yah Salman da shima ke zama ya taɓe baki. Shima gaishesa nayi ya amsa a ɗage kamar yanda ya saba. Ban sake bi takansuba naci gaba da shan tea ɗina nidai, suma kowanne ƙoƙarin karyawan yakeyi. Ban wani ci abincin kirkiba na tashi na koma falo na barsu a kicin ɗin, ina ɗaura takalmina sai ga Yah Qaseem ɗin ya fito yana faɗin, "Tashi muwuce mun makara". Miƙewa nayi muka fice.
★★★★★
Yayin da muka isa office ina fitowa daga mota da shi na fara tozali. Hakanne ya saka gabana faɗuwa, ganin bamu yake kalloba na ɗauke kaina daga garesa, sai ta gefen ido nake satar kallonsa, sanye yake da jeans ruwan toka da farar shirt mai gajeren hannu, idanunsa sakaye cikin glasess da yay masa matuƙar ƙyawu. Dole inda suke tsaye shi da wani a jikin wata mota itace hanyar da zanbi ta kaini inda zanje, sai kawai na canja hanya saboda yanda nakejin gabana na cigaba da tsananta faɗuwa. Nidai nasan ba tsoro bane ba, sai dai yanamin kwarjini da zan iya rantsewa wani ɗa namiji bai taɓamin irinsa ba, bansan miyasa hakanba? Bankuma san minene dalilin hakanba?. Hanya na canja, sai dai inajin tamkar ana bina da kallo, juyowa nayi kaɗan dan inga ko zanga mai kallon nawa, sai dai banga kowaba. Na cigaba da tafiya ina karanto addu'ar duk da tazomin kan harshe. Ikon ALLAH tunda nayi nesa da wajen dana gansa sai na koma normal, harna ƙarasa wajen da nake ƙyautata zaton ganin Ummie.
Ɓangaren Jawaad kam da a yau suka dawo aiki shi da tawagarsa, ya iske ayyuka da dama, musamman waɗanda suke da matuƙar haɗarin da ake buƙatar mutum mai ƙwazo da jajircewa irinsu, wasu ayyukan kuma an badasu ga wasu jami'an ne amma sunata musu tafiyar hawainiya basu ƙarasaba babuma wani bayani mai gamsarwa, hakan yasa yau aka miƙasu gaban su Jawaad ɗin. Kansa yaɗauki zafi da ganin ayyukan dake jibge a gabansu, duk da kuwa a yanzu sun sake samo dabaru na musamman shida abokan aikinsa da suka samu zuwa wannan horo na musamman a ƙasar amuruka, ya kuma dawo ne da karsashin aikin canja wani abu a ƙasarsa dan bai isa canja komaiba shi yasan wannan, irinsu masu son jajircewa ƙalilanne, tayaya kuwa suka isa canja komai? Sai dai suyi nasu ƙoƙari su koma gefe, UBANGIJI shike da sauran hanyoyin maganin sauran tunkafin nasu, rahamarsace ta saka zukatansu suma jin son gyaran. Baƙon da yayi wani abokinsa da sukai secondary tare lauya, yazone bincike akan wani case shine ya rakoshi suka tsaya a jikin motarsa suna magana. Sarai Jawaad yaga lokacin da Qaseem da Bily suka fito a motar Qaseem ɗin, amma sai ya ɗauke kansa cikin basarwa, duk da a ƙasan zuciyarsa yana tunanin minene alaƙar Qaseem da wannan yarinyar? Saboda a koda yaushe yake ganinsu tare da juna. Sai kuma akai rashin Sa'a shima abokin nasa idonsa suka hango su Bilkisun. Yace, "Woow, Jay kaga wata ƙyaƙyƙyawar halitta mai tsada da daraja kuwa?". Jawaad da ras ya fahimci inda abokinsa ya dosa tsabar rainin wayo sai yay tamkar bai fahimtaba............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/T8bCANmJA5E
*_MANHA HAUSA NOVELS_*
https://youtu.be/xUINNiDdeH0
*_AL-ƘALAMI TV_*
*_Typing📲_*
*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_
*__________________________________* *_BOOK ONE_* _Shafi na talatin da takwas_ *__________________________________*
..............Bayan wucewar abokinsa office ɗin Sir Ahmad ya wuce domin amsa kiransa, yana ƙoƙarin shiga yaci karo da Qaseem shima ya fito. Ƙoƙarin ɗauke kai Qaseem keyi, shima Jawaad ɗin har yayi niyyar hakan, sai kuma yaga rashin ƙyautuwar abun, Murmushi ya saki har kumatunsa na loɓawa, ya miƙama Qaseem hannu yana faɗin, "Assalamu alaika". Ƙin miƙo nasa Qaseem yayi, sai dai ya amsa masa sallamar. Jawaad ya kamo hannun Qaseem cikin nasa tare da faɗin, "Haba ɗan uwana, miyay zafi shiba wutaba? Ina fatan na sameku lfy? Ya jama'ar gidan?". Ran Qaseem ya sosu da wannan rainin hankali na Jawaad, danshi matsayin rainin hankali kawai ya kalli abun, dan haka ya kasa daurewa yace, "Da wannna salon kuma ka dawo?". Jawaad ya murmusa yana sakin hannunsa, cikin gyara tsaiwarsa yana shafa gemu da tura hannunsa ɗaya a aljihu yace, "Minene abin salo anan Qaseem? Kaifa ɗan uwanane jinina, sannan ga alaƙar musulinci a tsakanina dakai, kuma kai yarenane, ogana a wajen aiki, shekara biyu rabon da ka ganni na ganka, da akwai ƙaddarar mutuwa tsakaninmu maybe wani zai samu saƙon mutuwar wanine a tsakaninmu, nidai tsakanina da ALLAH na gaisheka, ya rage naka ka ɗauka hakan kaima ko saɓaninsa, na barka lafiya".. Sagade Qaseem yay yanabin Jawaad da kallo harya shige office ɗin Sir Ahmad, yayi kamar ya bisa cikin office ɗin sai kuma ya fasa, ya nufi office ɗinsa yana juya kalamun Jawaad cikin ransa. Jawaad kam koda ya shiga, bayan yayi gaisuwar girmamawa ga sir Ahmad sai ya nuna masa wajen zama. Hannu Sir Ahmad ya bashi cikin musabaha suka sake gaisawa, dukda dai Jawaad na nuna jin kunyar haka ɗin. "Jay kasan miyasa na kiraka kuwa?". "A'a Sir". 'Jawaad ya faɗa cikin kaɗa kai'. Zama sosai Sir Ahmad ya gyara, ya fara magana idanunsa akan Jawaad ɗin. "Wato zakayi mamaki idan nace maka baƙin abubuwa da yawa sun sake shigoma hukumarnan, masu ban tsoro da mamaki. Akwai cases da yawa dakai kanka ka fara ka tafi kabari to ina mai tabbatar maka da yawansu ba'a ƙarasa suba har zuwa yau da nake maka maganar nan, waɗanda kuma aka ƙarasa ɗin sun canzu ga bisa salon daka barsu gaba ɗaya ma. Gashi wasu cases ɗin sun sake ƙaruwa da yawa, akwai jami'inmu mai matuƙar ƙwazo kamar kai ɗinnan, bayan tafiyarku nagartarsa ta sake fitowa, amma kamar yanda na sanar maka ranar ya fita wani aiki sai dai gawarsa aka kawo mana, kasan wani abun mamaki?". Jawaad da idonsa ya kaɗa yay jazur ya girgiza kansa. Murmushi Sir Ahmad yayi na takaici yana cigaba da faɗin, "Abun mamakin da har yanzu yake cizon zuciyata shine bullets guda uku da aka harbi Abdallah dashi a ƙarjinsa da cikinsa dukansu bullets ne na jami'an tsaro, abi mafi al'ajab Bullets ɗin suna cikin bullets guda dubu sittin da shida da aka kawo ƙasarnan shekaru tara da suka wuce, waɗanda a zahirance bayanai sun nuna bullets ɗin sun ƙare gaba ɗaya bayan shekara ɗaya da wata bakwai da kawosu, bullets ne masu matuƙar haɗari, dan inhar akai harbi mutum dasu acikin seconds ashirin dukkanin illahirin jinin mutum ke tsinkewa, idan ba'ai gaggawar kaisa asibiti ba ya samu taimakon gaggawa zai iya rasa ransa a ƙanƙanin lokaci, sannan ba a kowacce bindiga yake aikiba. To abin tambaya anan, yaya akai bullets ɗin da suka ƙare shekara huɗu baya kuma suka kashe mana jami'inmu? Daga ina suka fito? Wasune aka sake shigowa dasu? Koko dai sune ɗin?". Gaba ɗaya jijiyoyin Kan Jawaad sun mimmiƙe ruɗu-ruɗu, maƙoshinsa sai kaikawo yake a wuyansa saboda tsabar haɗiyar busashshen yawu mai ƙona zuciya. Ya matse idanunsa tare da rumtse hannu, muryarsa a matuƙar kausashe yace, "Sir akan wane case wannan abun ya faru?". Sir Ahmad yay murmusa idonsa akan Jawaad, mazantakar Jay akan aiki da kishin ƙasarsa yasa ako wane lokaci yafi sha'awar ganinsa akan aiki na musamman, yaɗan ɗage kafaɗa yana buga tebir kaɗan da komawa cikin kujera ya kwanta, har lokacin idonsa akan Jawaad, "Jay ƴan bindiga daɗi ne kawai, amma ga dukkan bayanan komai anan". 'Ya ƙare maganar da tura masa wani file gabansa'. Ɗauka Jay yayi ba tare daya buɗeba, babu abinda zuciyarsa keyi sai tafarfasa kawai, shiru Office ɗin yayi na wasu mintoci, kafin Sir Ahmad ya katse shirun da faɗin, "A yanzu kana buƙatar runduna ta musamman Jay, fiye dasu Jabeer kawai, munada sabbin ma'aikata masu jini a jika da karsashin aiki a ransu saboda yanzune jinin jikinsu ke zagayawa cikin kowacce jijiya dalilin ƙuruciya da zafin rai mai tare da ɗokin aikin, sannan a cikinsu akwai kwararrun maharban da suka samu horo na musamman a ɓangaren harbi, wanda an daɗe ba'a yaye sabbin horaswa da wannan ƙwazonba a hukumarnan tamu, shawara kawai na baka ba umarniba, dan zuciyata ta yarda da kai, yarda irin wadda ko ɗan dana haifa ban yimawaba duk da kasan cewarsa jami'in tsaro shima, ALLAH yayi jagora haziƙi kuma jarumin yarona abin alfaharin ƙasarsa da ƴan ƙasa". Zazzafan numfashi Jawaad ya sauke yana miƙewa idonsa a matuƙar jazur tamkar ya haɗiyi wuta, yay salute din sir Ahmad sannan ya fice tamkar wanda zaije filin daga. Koda ya isa office ma gaba ɗaya zuciyarsa a dagule take, yama rasa wane kalar tunani ya dace ace yayi, dan lamarin ƙasarsa a kullum sake bashi tsoro take, tsoro irin mai firgitarwa da ban ta'ajibi, komai anayinsane saboda kuɗi, kuɗi! Dai kuɗi! Dai, sai yaushene mutane zasu ajiye son zuciya da burin mallakar kuɗaɗe su amshi gaskiya? Da wannan rayuwarne kuma kullum muke fatan ganin kayinmu cikin aljanna, a haka mukeso ALLAH yay mana rahama, a haka mukeso MANZON ALLAH yayi alfahari damu?, Ya rumtse idanunsa sosai yana cigaba da haɗiyar ɓacin ran daya tokare maƙoshinsa. Bai sake fitaba, bai kuma sake barin wani ya gansaba koda a cikin su Aliyu ne, dan kulle kansa yay a Office ɗin yanata saƙawa da kwancewa. Har sai da lokacin salla yayine sannan ya fito domin gabatarwa.
★★★★★★
Bayan sallar la'asar ya bama Rose damar tattara masa ƙananun jami'ansu sabbin ɗaukar wannan karon. Duk da tayi mamakin hakan sai bata tambayesa ba, dan bataga alamun wasa tattare da shi ba, a yandama taga fuskarsa a matuƙar murtuke sai abun ya bata tsoro, dan irin wannan fushin nasa mafi yawan lokuta sukan gansane idan aiki ya ɗauki zafi.
Bamusan miya faruba mudai an taramu waje guda, inda aka nema mu rabu rukuni-rukuni akan abinda mukafi samun ƙwarewa dashi a wajen horaswa. Ina cikin jami'ai masu ƙwazo da suka samu ƙwarewa wajen harbi, dan haka banyi ƙasa a gwiwa ba wajen shiga cikinsu. Sai da duk muka gama rarrabuwa sannan wanda ya saka a taramun ya fito.
Yanda sautin takun takalman ke fidda ƙara haka nake jin sautin bugun zuciyata na fidda ƙarar bugu, zuwa yanzunkam na ɗan fara jin tsoro, ba komai ya kawo tsoron nawa ba kuwa sai fahimtar da nai kasantuwar wannan mutumin a kusa dani ke kawo min wannan yanayin da bansan dalilinsa ba. "Miyasa sai a kansa kawai?" naima kaina tambayar da bani da amsarta..... Na tafi tunani sam bansan bikin da ake ba, sai da naji ƙarar sautin bugawar ƙafarsune nai firgigit, dai-dai zasu ajiye hannayensu da sukai Salutes nashi. Hakan ya sakani saurin kallon inda yake nima ina ƙoƙarin kai hannuna saman goshina. Karaf na tsinci idanunsa a kaina yana watsamin wani kallo mai kama da gargaɗi. Ƙasa na maida kaina, muka ajiye hannayenmu tare da ƴan uwana. Tsayuwarsa ya gyara har yanzu dukkan hannayensa na cikin aljihun jeans ɗinsa ruwan toka, ƙamshin turarensa na cigaba da addabama ƙofofin hancinanmu, ya ɗan furzar da huci kaɗan yana cigaba da tsatstsaremu da idanunsa masu ban tsoro, gasu yau sunyi jazur alamun yana tattare da ɓacin rai. Ganin yanda yake mana kallon ɗaɗɗayan ne yasani fahimtar nazartarmu yake ɗaya bayan ɗaya, babu zato muka tsinkayo muryarsa mai tarin nutsuwa wadda yau shine karo na farko da zan jita, sai dai kuma bamu yay ma maganarba, hakan yasa bamuji miya faɗa ɗinba duka bayan kalmomin farko na ambatar suna Rose da yayi. Rose dake gefensa ta kallemu tana matsowa kusa damu sosai da mana bayani akan abinda yace. A cikin kowane rukuni yana buƙatar mutum biyu, dan haka zai gwada ƙwazon kowa. Mun amsa da girmamawa, kafin kowane rukunu a haɗasu da waɗanda zasuyi nusu gwajin.