Kenza eBookz

Raina kama 1 and 2 & 3 all in 1 1 to 1 - Chapter 29

Raina kama 1 and 2 & 3 all in 1 1 to 1 - Chapter 29

Raina kama 1 and 2 & 3 all in 1 1 to 1 Chapter 29: Raina kama 1 and 2 & 3 all in 1 1 to 1 Chapter 29. Tunda suka katse wayar saiyayta sauke ajiyar zuciya,…

4,180 words

Tunda suka katse wayar saiyayta sauke ajiyar zuciya, koba komai ya sami nutsuwa akan wayar dasukai da papi. tashi yay ya k'arasa shafa man, sannan yasaka kayan da bazasu takurashi ba. Falonsa ya fito, abinda ake nunawa a tv ya d'auki hankalinsa sosai, ana cigiyar d'iyar Minister Ce, wai an nemeta an rasa tun a daren jiya. Akan la66ansa ya furta “Nuren!” Sai kuma yayi murmushi kawai ya kwanta saman doguwar kujera. A haka Sauban ya shigo ya sameshi da sallama, sai bayi buyu dake binsa a baya d'auke da ledoji. Galadima ya bud'e idanunsa yana kallonsu amma bai tashiba, bayan bayin sun ajiye suka zube sunama Galadima barka da hutawa, murmushi kawai ya musu ya d'aga musu hannu. Sauban yabasu izinin tafiya. Zama Sauban yayi a kujerar dake kallon Galadima, “kai yau ina cikin nishad'i wlhy yaa Sam...” Kallonsa Galadima yayi yana d'an murmushi, amma baice komaiba. Sauban yace “yaa Sam... Aunty gimbiya fa?”.. Galadima yace “barci takeyi”. “tofa Unborn babynmu yazo da sabon salo kenan”. Hararsa Galadima yayi, ya mik'e yana dariya ya shige bedroom. Galadima ya girgiza kai kawai yana tashi zaune. ledojin ya duba dan ganin mi suka sayo?. Abinda yasan zata iya ci ya d'auka ya fita. Saida ya d'anyi jimm a k'ofar d'akin sannan ya shiga da sallama, har yanzu tana a kwance tana kuka, lips d'insa ya d'an cija sannan ya ajiye abin hannunsa saman table d'in dake gaban gadon, idanu ya tsura ma bayanta nawasu 'yan seconds, ko alk'yabbar bata cireba, zama yayi a bakin gadon kusada ita, amma ya juya mata baya. Tun daga shigowarsa har zamansa tana jinsa, amma ko motsi batayiba, kusan mintuna 3 suna zaune a haka, ganin batada niyyar tashi ko kulashi ya sakashi juyawa yana kallonta, gyaran murya yayi sannan yace, “tashi kici abinci”. Shiru tayi ta shareshi, ko motsima bata yiba. Tsawa ya daka mata, babu shiri ta tashi zaune, jikinta sai rawa yakeyi, tunba yanzuba munaya akwai tsoron tsawa, bata barin saita kwana amma batason amata tsawa. Shi kansa yayi mamakin tsoratar tata, ya watsa mata harara yana kwafa, sai kuma yaja tsaki, alk'yabbar yacire mata, sai hawaye take zirarwa, bai kuma cemata uffanba ya bud'e abincin ya ajiye a gabanta, kafeta kawai yayi da idanu, hakan saiya tasirantar da tsoronsa a zuciyarta, dan haka tafara cin abincin, tanayi dai hawaye na zurara, cikin nata bamai tsurfa baneba, komai ci take hankali kwance, sai dai laulayi na ciwo. Dolenta ta saki jiki taci abincin, danya kafeta da idanu ga fuska cid'in-cid'in, duk jarumtarka dolene kaji shakkarsa. Kallo d'aga tamasa ta janye idonta, shi kuma ya harareta yana fad'in “kin k'oshi ne?”. Kanta ta jinjina masa tana matso kwalla. baice komaiba ya sauke sauran abincin k'asa, sannan yace “sauka kije kiyi wanka”. Baki ta bud'e zatayi magana ya dalla mata harara. sauka tayi tana k'unk'uni akan la66a. yana kallon motsin la66an nata, sai dai bayajin mi take fad'a.

Yau kam Alhmdllh taji dad'in jikinta, ko k'arin ruwan da aka saka matane yasakata jin kwarin oho, ruwa mai d'an d'umi ta tara tayi wankan, tanayi tana hawaye, itafa ko mi zaiyi ba masifaba bazata bar cikinnan ba, babu yanda za'ayi ta reni ciki ta haifeshi sannan yazo daga baya ya saketa, bazata d'auki wannan rainin hankalinba, su maza a kullum d'aukar mace suke mai k'arancin tunani, kowane yayin rashin mutuncinsu suka kwaso saiya k'are akan mata, wlhy akan cikinnan tata d'aga masa hankali kenan harsai ya amince an zubar dashi sannan, kuma ana zubarwa zata k'ara gaba, mahaifinsa kam kobasa tare insha ALLAH zata cigaba da masa addu'oi ana aika masa.

Jin shiru tak'i fitowa ya sakashi mik'ewa, bai wani kwankwasa ba ya bud'e k'ofar bathroom d'in kawai, danshi zatonsa ba wankan takeba ta tsaya kukane. A birkice munaya ta kalli k'ofar, ganin Galadima tsaye yana kallonta ta fasa k'ara, yay hanzarin ida shiga bayin ya rufe bakinta da tafin hannunsa dankar ta tara masa jama'a. Juyawa tayi ta ruk'unk'umesa, tare da saka hannayenta ta zagaye bayansa ta manne k'irjinta da nasa, ita duk bata son yaga jikinta ne😂😝. Shima fuskantar hakan da yayi ya sakashi sakin murmushi, saiya saka hannunsa biyu ya zagaye bayanta ya manneta sosai a jikin nasa. Shiru sukayi nawasu seconds, tana sauke ajiyar zuciya shima yana saukewa, saboda yanason ganin yanda zatayi saiya fara k'ok'arin janye jikinsa itama zai janye ta. K'ank'ameshi tayi ta fashe da kuka, jiyay tamkar ya kwashe da dariya, amma saiya daure, cikin dakiya yace, “malama sakeni mana? konaci bashinki ne wai?”. Cikin dasashshiyar muryarta datasha kuka tace, “to kabani zanina da hijjab na saka”. “to kin k'udunduneni ta ina zan iya baki wani zani? sakeni saina baki”. Kafad'a ta nok'e alamar tak'i. Murmushi Galadima yayi, ya shafa bayanta cikin murya k'asa-k'asa yace, “idan an hanani ganin can ai gashi ina kallon nan”. Da sauri tayi wata wulk'itawa ta koma bayansa ta 6uya. Kansa ya dafe yana fad'in “yau Sameer kaga ta kanka, ranar farin cikinka sai saka maka ciwon kai da zafin kai akeyi, wai ke yalla6iya mikike 6oyemin daban saniba ne?”. Baki ta murgud'a masa tana fari da idanu, dayake ba ganinta yakeba baisan hidimar datakeyi ba. K'ok'arin juyo da ita ya farayi amma tabi ta kanannad'e shi, rasa yanda zai mata yayi. yakula yarinyarnan 'Yar daruce kawai. zaninta ya jawo ya mik'a mata, saida ta tabbatar ta d'aura sannan ta sakeshi, yana juyowa ta juya masa baya ita kuma. Baice komaiba ya ta6e baki ya fice daga bathroom d'in. Harar bayansa tayi ta na fad'in “ALLAH ya isana”.

Nace Humm.😏

Fita yay daga d'akin gaba d'aya, tunda dai yasamu taci abincin, harya kai k'ofarsa ya tuna batasha maganinta ba, dawowa yayi da baya. Ita kuma motsin fitarsa dataji yabata kwarin guywar fitowa. Shigowarsa tasata kwakumar hijjab ta saka, bakinsa ya ta6e ya wuce wajen handbag d'inta batare daya kalleta ba. Magungunan ya fido, ya zauna bakin gadon, “kizo kisha magani”. ya fad'a cikin k'asaitarsa. 6ata fuska tayi, tace “babu amfanin tattalin abinda za'a zubar ai”. Lips d'insa ya cije, sai kuma ya ajiye drugs d'in yana kallonta, mik'ewa yayi ya taka inda take, a bayanta ya tsaya, fisgota yayi ta fad'o saman k'irjinsa, saida ta rumtse ido dan zafin dataji, ya matso da fuskarsa daf da tata, a wani yanayin data kasa fassarawa yace “adadin nawa kike buk'atar na biyaki danki barsa?”. Rik'esa nayi da k'yau gudun karna fad'i, na janye idona dake cike da kwalla daga cikin nasa, “Bana buk'atar ko sisinka yalla6ai, cikinne kawai bana buk'ata, kuma bazan raineshi ba balle nakai ga haifeshi”. Wani murmushi mugunta yayi, sanan ya sakeni tamkar zai hankad'ani, mikuma ya tuna oho masa, saiya kuma damk'e hannuna, muryarsa a kausashe yace “wlhy idan kinga baki haifi cikin nanba to sai dai idan wanine a cikinmu numfashinsa yabar gangar jikinsa, sai kuma idan ubangiji ya kaddara Shiba mai Shak'ar iskar duniya bane, dan bani da hakk'in kowa, ubangiji kuma bazai barki ki shiga nawa ba”. yana gama fad'ar haka ya saki hannuna yafice daga d'akin baki d'aya.

Yariga yasan zai fuskanci abindama yafi haka daga munaya, shiyyasa bai zafafama zuciyarsa akan wannan rikicin nata ba, shi babbanma burinsa yanzu Abbanta yabar k'asar nan, danya samu damar gudanar da aikinsa yanda ya kama ta. Da wannan tunanin ya dawo d'akinsa, ya iske Sauban kwance wai zaiyi barci, hararsa yayi yana fad'in “ kama tashi, time d'in zuhur yayi.

Yana fita na raka bayansa da harara ina murgid'a baki, “oho dai, koma mizaka fad'a ka fad'a, nima ai bani tare da hak'k'in kowan, ALLAH kuma bazai baka damar danne nawaba, sokake nazama shashar mace ko? munyi auren contract batare da sanin iyayena ko naka ba, kazo kamin ciki na haifa maka ka sakeni na koma gidanmu, katashi da riba biyu kenan, nikuma babu ko d'aya sai bak'incikin danakema iyayena tanadi da kaina, Galadima ko a matanma ai _AKWAI BANBANCI?_ wlhy.

gaskiyane Munaya, rik'e darajarki shine 'yancinki😄👍🏻.

*******

Bayan sun fito massalaci sukejin labarin wai an rasa inda Muftahu yake, a safiyar yau aka samu motarsa a bud'e, sai kuma agogonsa da takalminsa d'aya a k'asa alamar da k'arfin tsiya aka saceshi. Hakan yasaka aka kama dogaran dake tsaron k'ofa ta uku, dan anga alamun tanan aka fita dashi. Dukda Galadima najin haushinsa saida hankalinsa ya tashi, dan haka suna shigowa ya d'au waya ya kira Nuren. Nuren na d'aga wayar Galadima yace, “Nuren Muftahu, kaine ko?”. “Muftahu kuma? nine naimi?”. “A daren jiya an rasa Wanda ya bar masarauta dashi”. “humm brother, dukda muna ganin Muftahu cikin masu mana zagon k'asa banta6a tunanin saina d'aukeshi zan gane hakaba, wlhy bani bane”. “ya salam”. ‘galadima ya fad'a cikin dafe kai da cije lips, wayar ya yanke ya Shiga safa da marwa, yarasa wazai hararo. Yana cikin wannan halin saiga harun shima a rikice, kowa yasan su ukunnan abokan junane, kuma akwai shak'uwa tsakaninsu, matawalle ne dama bai cika shiga cikinsu ba, saboda mama Fulani Na hanashi tun yana yaro, a cewarta shine d'an Sarki mai mulki, kuma shine mai jiran gado, darajarsa datasu Galadima ba dai-dai takeba, wannan hud'ubar ce tamasa tasiri sosai, amma yanason 'yan uwansa har zuciyarsa. “galadima shin kaji kuwa mike faruwa a masarautarnan?”. Cikin damuwa Galadima yace, “Harun su waye da wannan aikin?”. “kowa abinda yake tambaya kenan Sameer, Muftahu bashida wani abokin fad'a”. Hankalin Galadima kuma tashi yayi, shi duk damuwarsa karda a cutar da Muftahu ta dalilinsa, tunda ya kula duk wani makusancinsu shine abin harin mak'iyansa. shifa baima yarda ba Nuren bane da wannan aikin, dan yasan halinsa sarai, dolene kuwa yafita wajensa yanzunnan. Harun yace bara yaje, suna son akai report gidan radio da television. Jin jina kai Galadima kawai yayi, shima ya shige ciki danya shirya.

Tun safe an sanarda jami'an tsaro 6atan Muftahu n, kuma suna a kan aikinsu.

★★★

Yunwar da yakeji tasashi bayan yayi shiri ya samu fresh milk yasha kawai, sannan yafito, d'akin Munaya ya lek'a, saiya isketa baje a gado tana shak'ar barci, baiyi yunk'urin tashinta ba yafito. Har dogaransa sun taso yace suyi zamansu su huta, zai fita shida Sauban, cikin damuwa sarkin mota yace, “kayi hak'uri ranka ya dad'e, koda nine kawai mu fita, Mai martaba ya sanar yau a fada kar'a sake barin wani d'an gidannan yafita wani waje shi kad'ai”. Kallonsa Galadima yayi, kamar zaiyi magana saikuma yafasa ya bud'e mortar da kansa ya shiga, batare da ya jira an bud'e masa ba. Da hannu sarkin mota yayma sauran dogaran nuni da su biyosu a baya idan sun tafi.

A wani waje suka had'u da Nuren, Nuren ya fito daga motarsa yadawo inda Galadima yake, sai sarkin mota yafita yabasu waje kawai. Galadima yace “please idan kaine ka sakeshi”. Da mamaki Nuren yace, “wai Muftahu n dai? am telling you banida alak'a da d'aukarsa. yarinyar Minister ce kawai a hannuna”. “innalillahi, wlhy Nuren inajin tsoro, karsuje su cutar dashi”. “Sameer! nifa ina zargin kawai ya had'a baki da wasune suka kamashi dan yayi wasa da hankalinmu”. Idanu Galadima ya tsurama Nuren tamkar yana hango gaskiyar maganarsa, ya saki wani guntun murmushi, sannan ya gyara zamansa yana fad'in “well, koma minene dai zai fito ai”.

Nuren yace “ni kaga dama kabar zancen wani Muftahu n banza can, way note mu wuce gidan sirikanka kozamu samu wasu evidence daga canma akan Accident d'innan”. Agogon hannunsa ya kalla, sannan ya kalli Nuren d'in alamar suje.

Anan Nuren yabar motarsa suka tafi ata Galadima, saida suka fara tafiya Galadima ya lura da mototin dogaransa a bayansu. d'an murmushi yayi yana kallon Sarkin mota, yace “sarkin mota an karya min doka kenan?”. Sarkin mota daya fahimci Galadima yagane dogarai Na binsu sai yayi 'yar dariya, yace “ka gafarceni ranka ya dad'e, bazai yuwu mu barka ka fita kai kad'aiba ai, dan fitarka babu kowa tafi ta kowa had'ari a masarautarnan, mai martaba ma nasan saboda kaine ya saka dokar ai”. Galadima baice komaiba sai murmushi dayayi, Nuren ma murmushin yayi, sannan yace “amma kamar bayan motar dogaranka akwai wata bak'ar mota Na bin tasu?”. Galadima ya juya shima, tabbas anabin motar dogaran a baya, “sarkin mota su wucemu, karsu tsaya”. “To ranka ya dad'e”. Bayan sarkin mota ya sanar musu suka wuce su Galadima, motarma ta wuce, da kallo Nuren da Galadima suka bita, Nuren yay hanzarin d'aukar motar hoto a wayarsa. “humm da alama suna zaton kana d'aya daga cikin motocin canne”. Murmushi Galadima yayi, a k'asaitarsa yace, “kokuma suna son wasa da hankalinmu ba”. Da mamaki Nuren yace “kamar ya?”. Murmusawa Galadima ya kuma yi, ya kwantar da kansa jikin seat yana lumshe idanu, “Nuriddeen! Sameer ya wuce tunanin dukkan mai tunani, kai tsaye ba'a gane manufar zuciya, kwanji ko dama basu ke nuna k'arfin ikon mai ikoba, nazarin komai daki-daki da iya sarrafa duniya a yanda tazo shike nuna k'arfin gwarzan taka, mazantaka ba'a shaidata a fuskar namiji, duk lokacinda kai gamo da nama, kud'i, mata bisa hanya, karkayi rawarkan d'auka ko murnar ALLAH ne ya baka, zata iya yuwuwa tarko aka d'ana maka, shi k'yawu had'arine, 6oyeshi kuma nagartace, maiyi baya fad'an zaiyi, sai dai aga aikinsa a k'asa, tasowar iskar hadari bashi ke nufin ruwan zai zuba ba, watak'il sunan wannan iskar gyara kayanka. Dalili da dalilai basa ta6a saka zuciyar Wanda yake nema ta raunana, time d'in da zan nunama mak'iyan mahaifina d'an zaki ya girma yayi, sun durk'usar da shi a k'asa batareda tunaninsu yabasu ya haifi Raina kama ba, Su cigaba da raina aikin Muhammad Sameer daga k'arshe kuma saisuga gayya, tafiyar hawainiya bashike nufin gazawar kuzarinta bane, lokuta da dama hanzari kan katse igiyar cikar buri, a sannu kowa zai fahimci wanene *_RAINA KAMA....._*👎🏻

Ba Nuren ba hatta da sarkin mota maganganun Galadima ya shigeshi, tabbas mutane dayawa sunama Galadima kallon mutum mai yawan sakaci da rashin ho66asa, koshi yana d'aya daga ciki, amma wannan zantukan nasa sai suka sakasu a rud'ani, kenan akwai abinda sud'in basu saniba........... Dole tunaninsu ya katse saboda isowarsu gidansu Munaya.

Fita sarkin mota yayi yanema musu iso, babu dad'ewa saiga baba k'arami ya fito, sarkin mota ya bud'ema Galadima, yayinda Nuren ya bud'e da kansa, zuciyarsa sai jujjuya hannunka mai sandar Galadima yakeyi. Dukda baba k'arami yayi mamakin zuwan Galadima haka ya danne, yaymusu k'ar6a ta girma, sannan suka shiga cikin gidan. Gidan tsitt tamkar babu mutane, saikace ba gidannan bane mai kama Dana 'yan dambe😂, (yo kowa Na tsoron a korashi gidansu🤣😝). A falon daddy aka musu masauki, dan danan aka cika musu gaba da kayayyaki, baba k'arami ya fita domin basu damar cin wani Abu. Babu abinda suka ta6a, dukda kuma Galadima ma yunwa yakeji, a haka daddy da baba k'arami suka dawo. Daddy yace “anya kuwa wannan d'an namu yana d'aukar gidannan matsayin nasu?”. Murmushi Galadima da Nuren sukayi, Galadima yace “sosaima daddy”. Baba k'arami yace “ta INA zamu amince da haka kuwa, bayan inada tabbacin ko ruwan gidannan Baka ta6a sha ba”. Kunya Ce ta kama Galadima, sai kuma yaga bai k'yautaba, ya rissinar da kai yana fad'in “amin afuwa zan gyara”. Mik'ewa baba k'arami da daddy suka kumayi, “to mun bada dama ta biyu”. cewar Dady yana dariya. Bayan fitarsu Nuren ya bud'e kulolin shima yana dariyar, danbun shinkafane daya samu nutsuwa ta musamman, sai k'amshi mai dad'i yakeyi, daga Galadima har nuren saida kwad'ayin cin abincin yazo musu. Kallon Galadima Nuren yayi yana d'aga gira, Galadima yay murmusa tareda fad'in “kadaiji kunya”. “kaima jinta zakayi yanzu, dan nasan ci zakayi”.

Yau dai kam Galadima yaci abincin gidansu Munaya, kuma gashi girkin innarsu, babu kunya sukaita zuba Santi shida Nuren sunama juna dariya, Galadima harda su6utar baki yana fad'in “amma my mata muguwace, bata ta6amin irin wannan ba”.🙀 Mi Nuren zaiyi inba dariya ba🤣, su Galadima anji dad'i har kwalwar kai Baki ya bud'e😂😝.

Saida suka mammala tsaf sannan su baba k'arami suka dawo, sunji dad'i dasuka iske sunci. Daga nan sukayi gaisuwa, su baba k'arami suka d'ora da godiyar d'awainiyar Abba da Galadima ya d'auke musu. Murmushi kawai Galadima yayi. Nuren ya gyara zama, a ladabce yamusu bayanin son fidda Abba da Galadima kesonyi, dan likitoci sunce ana buk'atar kulawa saboda karayar hak'ark'arinsa data k'ugu, “to yanzu haka dai angama setting d'in komai gameda tafiyarsa, har asibitin daza'a kaisa, visa d'insa da komai, sai dai anason tafiya da mutum biyu a cikinsu, mi kuka gani akan Wanda za'aje da shid'in?”. Daddy da baba k'arami suka kalli juna, summa rasa wane irin farin ciki zasu nuna dan Galadima yasan sunji dad'i? sunta jero masa k'yawawan addu'oi, kafin daddy yace “ai kawai sai atafi da jafaru da Ai'sha, dan bai kamata mutafi mu duka ba gida babu kowa, dukda akwai su Anas, gakuma su Hameed zasuke zagayowa, amma hakan yafi dai. Duk sun gamsu da hakan, dan haka suka buk'aci passport d'in baba k'arami da inna, ita inna babu, sai sunje an mata, amma baba k'arami an samu. Sun bari akan zuwa anjima za'azo akai inna tayo. Daga nan Galadima ya buk'aci number da aka kira aka sanar musu da accident d'in Abba. Daddy yace Ai'sha aka kira, saidai akawo wayar tata. Kiranta yay yace tabama cikin su Aryaan ya kawo wayarta. Babu dad'ewa saiga Aryaan d'in da ita, yanda yaron ya gaishesu saida abin ya birge Galadima, ya yarda yaran gidan akwai tarbiyya babu laifi kam. Galadima yace, “amma Dady ko numbers nawa Abba ke amfani dasu?”. baba k'arami ya bashi amsa da cewar “uku ne”. Nuren yace “kozamu samesu dukansu?”. Dukda baba k'arami da daddy sunshiga mamaki, dansu zukatansu basu kawo musu akwai wani Abu a k'asa ba, sun d'auka kawai Abba yayi Accident ne dai. Baba k'arami yabasu Numbers d'in duka. Bawani bincike Galadima yayi a wayar innarsu Munaya ba, wani Abu kawai ya saka (Wanda Nima ban saniba😱) yabama Dady wayar yana fad'in “zata bar wayar anan dan a can bazatayi aikiba, kuma gashi muna buk'atar wayar, dan haka daddy saika rik'e a hannunka tunda kai kana gida”. Dady ya amsa da to, duk su Galadima sun kuma sakasu a duhu. Sallama sukai musu suna fito domin tafiya. Harsun Shiga mota saiga Aiyaan da gud'u d'auke da wata Leda. Sarkin mota ya tareshi yana fad'in yaro miya farune?”. “Auntynmu za'a kaimawa inji innarmu”. Galadima yayma sarkin mota nuni da yabar Aiyaan d'in ya k'araso. Bud'e murfin Galadima yayi, Aiyaan ya k'arso, Galadima ya kamo hannun Aiyaan yana murmushi, “my friend ya akayi?”. 'Uncle innarmu ce tace akaima Auntynmu dan ALLAH”. murmushi Galadima yakumayi, sannan ya kar6i ledan yana fad'in “ita kad'ai banda ni?”. Aiyaan yad'an zaro ido waje, sai kuma yace “to bara naje Na fad'am innarmu kaima ta baka naka”. Da sauri Galadima ya kamo hannunsa dan yana neman tsillawa da gudune, “kaga dakata, idan naje saimu raba wannan da ita, yanzu dai ka fad'ama innarmu ta shiryaka gobe zan aiko a d'aukeka kazo ka zauna damu tunda kuna hutu ”. Cikin murna Aiyaan yace, “wajen auntymu?”. Galadima ya jinjina masa kai. “to amma kuma Aryaan fa?”. Cikin mamaki Galadima yace, “wanene Aryaan d'in?”. “lah baka San mu 2wins bane ba?”. “da gaske?”. “ALLAH kuwa”. “to shikenan, kacema innarmu ta shiryaku Ku duka biyun zakujema Aunty hutu”. Cikeda murna Aiyaan ya shek'a da gudu gida danya kai labari. Galadima yay murmushi yana rufe k'ofar motar, Nuren ma murmushi yakeyi, a fili yace, “yara sunyi wlhy”. Galadima ya kalleshi, cikin d'age gira sama yace, “kayi aure”. Sosai Nuren yay dariya.

****** A inda suka d'auki Nuren anan suka ajiyeshi, su kuma suka koma masarauta, sun iske tuni dogaran sun dawo abinsu. d'akinsa ya Shiga, ya iske Sauban nata barcinsa. Bai tadashiba, yadawo falo ya zauna.

_____________________________

Da daddare Galadima Na falonsa zaune yana aiki a system akayi knocking d'in k'ofa, izinin shigowa ya bada, sarkin mota ya shigo hannunsa d'auke da leda. Galadima dake aikinsa bai d'agoba, a haka ya amsa gaisuwar sarkin mota. Sarkin mota yace “ranka ya dad'e kayi mantuwane a mota ”. d'agowa Galadima yayi ya kallesa, ganin ledar da Aiyaan ya kawo yatuna masa sak'on munaya, nuni yama sarkin mota daya ajiye. Sarkin mota ya ajiye yana masa saida safe. Nanma bai tankaba, kansa kawai ya jinjina masa. Bayan fitar sarkin mota ya mik'e d'auke da laptop d'insa da ledar, dama tunda ya shigo baima lek'a ta ba, dan Sauban yace yakai mata abinci, kuma tun d'azu suna tare suna hira. Hakan yasa yagane shine ta raina kenan. wannan haushin ya hanashi Neman inda take.

A bakin gado ya isketa zaune tagama waya da Munubiya, k'in d'agowa tayi ta kallesa, tadai amsa masa sallama. Shima bai kula taba ya zauna bakin gadon d'an nesa da ita. Shiru kowa yayi suka share juna, haushi ya turnuk'e Galadima, lokaci yayi dazai daina d'agama yarinyar nan k'afa, yakamata su goga raini shi da ita. ta gefen ido ya saci kallonta, sai wani cika da batsewa takeyi, ya cije lips nashi. “k baki iya gaisuwa bane?”. Saida takuma tura bakin sannan tace “ina yini” tana mik'ewa da nufin bar masa d'akin, tana k'unk'uni Bai amsata, sai mik'ewa da yayi shima, matsawa tashiga yi baya yana binta, fuskarsa a matuk'ar d'aure, da jikin bango ta manne, shikuma ya mata runfa, hannunsa d'aya a dogare da bangon yayinda yasaka d'aya ya rik'o hannunta ya matsa da k'arfi, zatai magana ya jawota tafad'o jikinsa, ya manne bakinsa kan nata, duk yanda taso kwatar kanta hakan ya gagara, dan ya kama hannuwanta biyu ya murd'esu ta baya yanda ta kasa koda motsi. A haka ya wulk'itata takoma saman gadon, shima yabi bayanta. Ya d'ora hannunsa kan bakinta dan karta ishesa da tsiwa, idonsa ya saka cikin nata ya hanata kata6us, cikin tsare gida yace “dolene yau Na kora miki warning na musamman danki ringa banbance inda zakiyi tsiwa”. Bai bata damar dazata fad'i nata ba yashiga aikata yanda yakeso da ita🤥🙆🏻.................✍🏼

Kutttt Galadima auren Contract nefa😱😂, ba ruwana kaida masoyan Munaya aradu🤣⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀🤧.

i miss you wujiga-wujiga my sweet fans😂😜😜😜🥳.

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 *_Typing📲_*

*_Haske writer's asso...._*💡

*_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻

~Book 2~ 👉🏻9⃣

.................Salon nasa yasani bashi ragama, dan Galadima yazo min da sabon salo mai tafiya da gudun jini dana zuciya. Duk da kasancewata farin shiga, hakan bai hanani gane Galadima Na daban bane, kamar yanda kuka sanshi mutum mai izza da k'asaita, hakan bai canja ba ta wannan fanin, komansa a nurse da izzar k'asaita yake gudanar dashi. ban tashi farga nayi kuskure ba saida labari yafara nisan zango, anzo wajenda tsorosa yafara tasiri a gareni, Sai dai kuma nayi sakacin da Galadima yazama kurman dutsen dabaya ji baya gani. Sai lokacin hawaye suka fara ambaliya ga fuskata, hannayena na k'ok'arin d'agawa domin rok'o, sai dai ya hanani wannan damar gaba d'aya..........

🤥🙆🏻kai babu ruwana, iya nan nagani nima🤫 aradu aunty Magajiya da aunty Ni'ima zasuci k'aniyata ne idan na k'arasa fad'a😱🤭⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀.

Tabbas na gurzu, dan yau na banbance tsakanin aya da tsakkuwa, banbancin baya cikin hayyacinsa da yau d'inma kad'anne, dukda babu yanda za'ayi daren farko yayi dai-dai da kowacce rana ta bayansa. Duk ajiyar zuciyar danake saukewa yana jina, amma yay luf a gefena, hakan ne Yakuma tunzurani, a zalinceka akasa lallashinka saboda jin kai, wlhy kasaitar bawannan tayi masa yawa, duk randa yazama sarki kam fadawa sunga takansu, dan magana dai idan sarki na uku a fada toshi bazaiyi ko guda d'aya ba😏. Galadima daduk yake sauraren kukan nata da ajiyar zuciya ya juyo kad'an yana fuskantarta, hannu yasaka ya tallafo fuskarta ta matso dai-dai da tasa, jinai kawai ana huramin iska saman ido, tsaf na fahimmci iskar bakinsa yake huramin, amma saina dake nak'i bud'e idona. Muryarsa can k'asan mak'oshi ya furta “my friend are you okay?”. Banza na masa, nakuma k'i bud'e odon, lallai mutuminnan yacika d'an latsin rainin wayo number 1, yanzunan Galadima har yanada bakin yimin wannan banzar tambayar?, idona a rufe har yanzu na bud'e baki cikin salon tsiwa zan maka masa bak'ar magana, amma saiya d'ora yatsansa saman bakina yana fad'in “shiiii!🤫” da bakinsa, shirun kuwa nayi kamar an rufemin bakin Dan Nina Na tuna illar yin tsiwar.(😝😂) Ya matso dani jikinsa ya rungume, hannunsa na buga gadon bayana k'ad'an-k'ad'an, ya d'ora bakinsa saitin kunnena, “yanzu kin gane banbancin Sameer da Munaya right?, idan kuma har yanzu baki fahimta ba to bakinki ya cigaba d'amin tsiwa OK?, nikuma bazan gaji da punishment nashi ba sala-sala yalla6iya💋”. ‘ya k'are maganar da sumbatar cikin kunnena’. Babu shiri na k'ank'amesa dan har cikin kwalwar kaina naji sumbar nan. Kad'an ya buga bayana sannan ya janyeni daga jikinsa ya sauka daga saman gadon. “hasbinallahu wani'imal wakil” na iya maimaitawa kawai, na k'ank'ame pillows d'in gabana ina rintse idanu da cije lips (copy copy😝).

Kusan mintuna 15 duk nazata yama fitane, sai kawai jinai an d'aukeni. a razane na bud'e idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, da matuk'ar Sauri na maida nawa na lumshe. Wani muskilin murmushi Galadima yayi yana cije lips. Ba shiri na bud'e ido, saboda jina cikin ruwan zafi, yunk'urawa nayi zan mik'e cikin 6ata fuska ya maidani ya zaunar yana fad'in “za6i ya rage naki, zama kiyi da kanki, kokuma ni nayi miki..” Banma bari yakai k'arsheba na koma na zauna ina kare k'urjina. Kafad'a ya d'age sama yana ta6e baki da fad'in “hummm”. Fita yay daga bathroom d'in ya rufe mata K'ofar.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull