Kenza eBookz

Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 23

Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 23

Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 23: Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 23. Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda…

4,431 words

Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda shigowar innaro, innaro bata kulaba, dan haka ta zauna a kujerar falon idonta akan Zarah, ganin yanda duk jikinta shatin duka, “kekauwa zara'u miya sameki haka? Ga ciki?”. Harara mamansu yaa hameed taketa zubama Zarah, amma ina bata kulaba, ta share kwallar fuskarta tana fad'in “innaro wai kud'i ya ajiye a gidan jiya, shinefa yaduba yau bai ganiba, ina kitchen yashigo yana tambayata wai kona canja musu wajene? shine nace bammasan yashigo da kud'i gidan ba bare harna canja musu waje, ko rufe baki bai bari nayiba ya fallamin mari, nikuma naji zafi namasa ALLAH ya Isa, shinefa kawai yacire belt d'in jikinsa yahau buguna, wlhy da k'yar nagudo na fito, nasan idan nashiga gidan Siyama zai iya bina har can, tunda gidan d'an uwansane, dak'yar nasamu napep a anguwar nataho gida”. Innaro tarik'e ha6a tana fad'in “oh ni marwanatu jikar Falalu, yanzu shi Sa'eedunne yamiki haka da hankalinsa? toke kin tabbata baki d'aukar masa kud'iba?”. “wlhy innaro ban d'auka ba, kinji na rantse miki, shi dama halinsane haka?, indai ransa ya6aci ko kika masa kuskure sai dai kawai kiji mari, wlhy zuwana gidannan tun bankai satiba yake marina idan namasa Abu, yaune harda duka, gashi ko kad'an bashida hak'uri, Abu kad'an yagani saiyayi tsogumi, idan kuma kin masa na kirki bazai yaba mikiba, dawuya kimabasa Abu sau 10 bai kushe 8 a cikiba, 2 kuma bawai zai nuna yaji dad'i baneba😢”. “kai amma wannan yaro anyi wulak'antaccen yaro, yoshi dama dukan mata yake akasa nabashi jikata? Bari su Auwalun suzo, koti zansa su kaishi, sai an kwatar miki hak'inki,”. “nidai babu wani court k innaro, kawai akirasa amasa bayani a sasantamu nakoma d'akina, inason mijina wlhy”. “enyeee! A lallai zara'u kinkai kuwa, nikike fad'ama kina son mijinki? to dan ubanki auwalu saiku tashi ki koma yanzu, idan yagadama anjima akiramu jana'izar gawarki”. fuuu tafito tana sababi, kayaya tunta da maimaita maganar da Zarah tafad'a mata yasaka 'yan gidanmu fahimta komai, wasu dad'i har tsakar kansu, (yo dama gidanmu kowa bawani son d'an uwansa yakeba, salon munafurcine kawai da bariki na tsoffin mata).

'Daki Momy Hadiza tashige takira Siyama danjin k'arin bayani, anan Siyaman ke sanar mata wai dama ba wannan ne karon farko da Sa'eed d'in yay Complain Zarah na d'auka masa kud'i ba”. Momy Hadiza ta rabga salati tana fad'in “k 'yarnan da gaske?”. “wlhy kuwa Momy, yanzu haka ma gashi anan gidanmu suna maganar da Sulaiman”. “to ALLAH ya k'yauta, ni dama auren ya mutu ki zauna daga ke saike, danni bama na k'aunar wannan had'in gambizar family d'in, komai yaro yamaka ido nakai”. “yo nifa Momy wlhy yanzu haka bama magana da Zarah, daga ranar mun had'u da ita a gidan sunan Hanan k'anwarsu, toni shine ya kaini da kansa, itakuma Ashe bashi yakawitaba, shine ta tambayeni miyasa ban biya mata mun taho tareba? Nace mata ai shine yakawoni, itama nazata Sa'eed d'inne zai kawota, shinefa taketa faman fushi da gaba dani”. “eye, kice tafara miki hassada kawai saboda taga mijinki tafi kulawa dake? to wlhy bance ki d'aga mata k'afaba, karma kituna da ubanki da ubanta ciki d'aya suka fito”. “insha ALLAHU Momy bazan raga mataba”. “yauwa 'yar albarka. Yanzu yamaganar kud'in damukayi ranar? kinsan fa bikin nata tahowa?”. “zan aiko miki Momy, wai Momy da gaske Munaya bata Nigeria? ”. Tsaki Momy Hadiza taja, cikin bak'in ciki tace “haka dai iyayenta sukace, mudai bamuda tabbas tunda ba'a gabanmu jirgin yatashiba, anzo dai mana sallamar munafunci itada wannan miskilallen mijin nata”. “aikam Momy indai da sunzo d'in to da gaskefa sun tafin, dan Sulaiman yacemin yaga Galadima a airport shekaranjiya da sister d'inan watawa, shikuma yaje raka babansune zaiyi tafiya”. “suyita tafiyar mana, kema dan sakaraice ai, yo mi mijin nata yafi naki? Amma kod'an Honeymoon d'in nan da ake zuwa ke kin kasa sakashi ya kaiki”. “lallai momyn nan, shikenan tunda laifina kike gani, nidai zan kiraki anjima, yanzu jirana suke nakai musu abinci”. ‘bata jira cewarta ba ta yanke wayar’. Takaici yakuma kama Momy Hadiza, saitaja tsaki, amma saboda munafurci saita nufi d'akin mamansu yaa Hameed jiyo abinda ya maido Zarah gida. (Fuska biyu😆👿).

*******************

Hotunan na ajiye nafara bud'e wayar, woow irinfa wayarsa ce komai da komai, saidai tawa pink ce, gakuma extra condom na wayar har kala uku, kai gsky wayar tayi babu k'arya, layin dana gani a ciki na d'auka na saka sannan na jona charge saboda d'oki, sauran ledojin nahau bud'ewa, duk kayan sawane k'ananu marasa nauyi, kuma bamasu fidda tairaiciba, zan iya sakasu gaban kowa, a raina nace Ashe Galadima yanada kirki haka?, saida nagama had'a kayan waje d'aya sannan na haye gadonsa da yaune karon farko zan haushi, nawani 6ararraje ina kallon hotunan, wasu hotunan abin dariya wlhy, dan wasu yana yarone k'arami, wani a makaranta, wani awajen wasan yara, wani a masarautarsu, wani tareda mom, wani da aunty mimi da sauban, duk inda suke da Abie saida nayi kuka, dan abie duk yana kwancene, k'alilanne yakeda lafiya sannan. wasu kam ya zube wayoyi yanata had'e-had'en abubuwa na wasan yara😄. Kallon hotunan ne suka d'aukemin hankali har wani lokaci dasu Sauban suka dawo, bamma san sun dawoba saida Samha tahawo saman. Zama tayi tanamin bayanin wasu mutanen jikin hotunan muna dariya, bamu sakkoba saida Sauban ya hawo yakiramu.

******

Sai bayan isha'i suka dawo shida aunty mimi. Ina d'aki zaune har sannan ina kallon pictures d'in ya shigo, d'ago kaina nayi na kalleshi tareda amsa masa sallamar. Namasa sannu da zuwa. Ciki-ciki ya amsa yana zubewa bakin gadon, d'an kwanciya yayi kusan minti 10 kafin yamik'e yashiga bathroom, kusan 1hour sannan yafito maybe su yalla6ai an sauke nauyine (🚽🤭).

Yau saida na jirasa harya idar da shafa'i da wutirinsa, dan magana nakeson muyi, ganin ya idar ya zauna latsa wayane nace “dan ALLAH yalla6ai in tambayeka?”. Batareda ya d'agoba yace “uhmm”. Zamana na gyara cikin nutsuwa nace, “shin tunda Abie yafara jiyya anta6a masa maganin gargajiya ko amaida hankali ga addu'oi haka?”. Yanzun kam d'ago ido yayi ya kalleni, dama tunda nafara maganar ya dakata daga latsa wayar. “lips d'insa yad'an cije, kamar zaiyi magana saikuma yay shiru. Nace “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawaba”. Nanma shiru yamin, saida yaja wasu mintuna kafin ya ajiye wayar yagyara zamansa, cikin alamun bak'in ciki yace, “duk an gwada masa, saidai gaskiya bakamar yanda aka maida hankali gana asibitinba, saboda anriga da an sanar mana Allurar gubace aka masa, amma muna k'ok'arin sakashi a sallalolinmu na farilla dana nafila. Kullum addu'oinmu akansa yake”. Ajiyar zuciya na sauke, nace “ALLAH yabashi lafiya, yakawo mana iyaka, yakuma bashi ikon cinye jarabawar nan”. “amin yafad'a a la66ansa”.

Dagani harshi babu Wanda yasake magana har muka kwanta, saidai yauma banyi isashen barciba, inata cud'awa da kwancewa, har gabannin asubahi kafin barcin ya saceni..................✍🏼

_To Alhmddlh my sweet fans, zamu dakata anan kenan, saikuma ALLAH yakaimu bayan salla darai da lafiya, zanbar wannan a matsayin *RAINA KAMA..... PART ONE* yanda zamu tafi a tsare kawai, basai mundawo ba kuma mushiga tunanin inama aka tsaya? Ina kuma za'a tashi, a *RAINA KAMA PART TWO* zamuga yanda Munaya zata taimaki Galadima kamar yanda Momma ta buk'ata, shin zai bata had'in kaima Kuwa? domin kunji Momma dai tace bashida yarda? ya matsayin auren Zarah? Muftahu yaya zata kasance idan Galadima ya cafkoshi? shin Munaya tanada wani fikra ne game da ciwon Abie?. wannan amsoshin duk suna cikin *RAINA KAMA PART TWO* da zaizo bayan sallah insha ALLAHU my guys, one Luv😍😍😍😘😘😘🥰👌🏻_

_tabbas banida bakin godiya a gareku, saboda addu'oi da mahaifina ke samu agareku, Comments naku suna matuk'ar sakani a farinciki sosai, ngd ALLAH yabar zuminci, duk inda masoyin wannan buk yake yasaka aransa yana can k'ark'ashin zuciyar Bilyn Abdull.🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘👌🏻🤝🏻._

_ga azumi zamu shiga, 'yan uwana dan ALLAH mu maida hankalinmu ga ibada, sadaka da k'autatama marasa k'arfi, marayu,, k'autata mu'amullarmu da jama'a dayin amfani da abinda malamai zasu fad'akar damu, karya zam kullum muna wahalar zuwa tafseer amma bamu d'aukar komai, da bayan salla yawuce munkuma koma kan munanan ayukanmu, karmu manta irin wannan watan saikuma mai rabon gani, sau 1 tak yake zuwa mana akowacce shekara, wani yawuce agaresa kenan har Abadan, zata iya yuwuwa nice ma😭, zata iya yuwa kece 'Yar uwa👉🏻😭, zata iya yuwa kaine d'an uwa👉🏻😭. dan ALLAH mu gyara please & please, muyi amfani da damarmu kafin ta kufce mana, (kullu nafsin za'ikatul maut, kowane rai saiya d'and'ani mutuwa, ubangiji bai turo maka date d'in da rundunar mala'iku zasuzo d'aukar rayin nakaba,😭 mutuwa bata kwankwasa k'ofa, batada wata alamar yanda zatazo ta riskeka, kana tafiya ne, ko kana barci, ko kana salla, ko zaune, ko kana hira, ko kana aikata wani sa6o, ko kana wani abin alkairi😭, ya ALLAH ka d'auki ruhinmu muna masu imani agareka da tsoranka, ALLAH ka gafarta mana, kamana maganin abinda muka Sani da wandama bamu saniba._ _ina rok'on dukkan Wanda na 6atamawa a yayin wannan rubutun ko kafin shima dan ALLAH Ya gafarceni, nidai na yafema kowa._😢👏🏻

*_duk masoyina na gaskiya Dan ALLAH inason yasakani a ddu'arsa ta cikin azuminnan koda sau d'ayane, idan munada Rabon haihuwa adunaya nida mijina ALLAH ka azurtamu da samu masu albarka cikin sauk'i da rahamar ubangijin talikai, idan ba alkairi bace agaremu ALLAH kasamana hak'uri da juriyar azuciyata😭👏🏻, ALLAH kayaye mana dukkan damuwarmu baki d'aya._*😭👏🏻 Dan ALLAH ko sau 1 yane kar'a manta dani🙏🏻😊

Amin afuwa zan rage groups saboda yawan groups d'in suna cimin data wlhy, idan nayi sub na wata d'aya ko sati bata yimin take k'arewa🙏🏻. Ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, ALLAH yasa munada rabon sake had'uwa a bayan salla, ALLAH ka kar6i ibadunmu baki d'aya. yabamu juriya da hak'urin ibadar dake tunkaromu nanda kwana 1👌🏻.

Happy Ramadan Advance😊🥰🥰🥰🥰😍😍😍👍🏻

Binyn Ku Ce dai👌🏻

Writer✍🏼 *Abdul-maleek bobo!!* *Auren k'addara ko biyayya!?* *Ban saketa ba!!* *Ciki da gaskiya...!!* *Karayar arzeek'i!!* *k'anwar uwace ko kishiyar uwa!?* *Kukan krciya...!!* *Ni da Aminiyata!!* *Nawaff!!* *Rashin Sani!!* *Raina kama.....!!* *Sabon Al-amaree!!* *Sanadin bikin salla!!* *Siyasa ko k'abilanci!?*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 *_Typing📲_*

*_Haske writer's asso...._*💡

*_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻

____________________________

*_Dolene page d'in farko yazama sadaukarwa agareki MAMAN JUNIOR😭, ALLAH ya gafarta miki, ya raya abinda kika bari, ALLAH ya k'addara bazakiga k'arshen wannan littafiba. (Masoyan Raina kama kusaka wannan baiwa a addu'arku, ta rasu cikin azumi, kusanma k'arshe, member ce a group d'in raina kama, ALLAY ya yafe mata🙏🏻😭._*

_INA fata kunyi salla lafiya gaba d'ayanku, ALLAH ya kar6i ibadunmu. Ya yafe mana, yasa kar6a66iyar ibada mukayi🙏🏻😭._ Sai dai banci naman salla ba sosai, gashi banida d'inkin dallah🤦🏻‍♀🤥.

______________________________

~Book 2~ 👉🏻1⃣

.............Tunda mukayi maganar nan dashi banyi k'asa a gyuwa ba wajen dagewa da addu'oi wa mahaifinsa, ina buk'atar ruwan zam-zam, dan haka yau nashirya fad'a masa ya nemomin. tunda safe ya fice, dan haka bamuga juna ba. Yauma dai haka Na tashi banida wata isashshiyar lafiya, Na tak'ark'ara nayi gyaran d'akin har zuwa falo, sannan Na had'a ruwa mai zafi nayi wanka dashi. Ina cikin shiri najiyo sallamar Samha a k'ofar falon, rigar dana fara sakawa Na k'arasa, sannan nace ta shigo. “humm Aunty gimbiya kina kallon kanki a mirror kuwa?”. Cikeda mamaki Na kalleta sannan Na kalli jikina, nace, “kamarya?”. Zama tayi a sofa tana 'yar dariya, sannan tace, “wlhy kinyi k'iba, sati uku kacal da zuwanmu India kin koma wata madam”. Nad'an fiddo idanu waje, sannan Na harareta, “lallai Samha nagode da zagi to”. “tab wlhy babu wani zagi gaskiya Na fad'a, halan Uncle Sam bai ta6a fad'a mi ki ba........” Ta k'arasa Maganarta da d'ai-d'ai saboda shigowarasa d'akin da sallama ciki-ciki. Suna had'a idanu ya watsa mata harara, hakan ya tabbatar mana da yaji maganar tata, da sauri tamik'e ta fita, Nikuma najawo gyalena na yafa sannan Na kallesa. Saman sofar ya zauna ya dafe kai, kallo d'aya zaka masa ka karanci damuwar dake shimfid'e bisa fuskarsa. “yalla6ai lafiya kuwa?”. ‘nafad'a cikin tausayawa’. Shiru bai amsaniba, banyi zuciyaba nataka a hankali zuwa gabansa, durk'usawa nayi a gaban nasa, a d'arare nasa hannu Na najanye nasa dayay tagumi dashi. Ya d'ago idanunsa da sukai jaa yana kallona. kasa jurar kallon cikin idonsa nayi, Na janye nawa gefe, cikin dakiyar zuciya nakuma fad'in “bakada lafiya yalla6ai?”. Yanda nayi maganar a marairaice saiyaji yakamata ya fad'amin, kodan nuna damuwar danayi akansa...... Ganin yamin shiru nikuma saina yink'ura natashi ina fad'in “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawab......” Bankai k'arshen maganarba naji tattausan tafin hannunsa cikin nawa. Rintse idanuna nayi, saboda wani yarrr da tsigar jikina tayi, shima agaresa saiya lumshe idanu kawai. najuyo danufin zare hannun kawai ya fisgoni na fad'a saman kujerar, rabin jikinna duk yana a jikinsa, yayinda sauran rabin nake a kan kujera. Bansan nawani lumshe idanuba saboda daddad'an k'amshin turarensa d'aya ratsa hancina zuwa magudanar jinina. shikuma ya sauk'e 6oyayyiyar ajiyar zuciya. Ya karkato da fuskarsa inda tawa take a gefen kafad'arsa har inajin saukar numfashinsa saman face d'ina, mayun idanun nan nasa suka kuma shiga cikin nawa, na janye da sauri, sannan nafara k'ok'arin cire kannawa daga kafad'arsa. Hannunsa na dama da nake jiki ya sak'alo ta bayana, ya maida kai na ya kwantar a kafad'ar tasa, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa tilas yace, “jikin Abie ne ya motsa, Ashe tun jiya basuyi barciba gaba d'aya, da safennan Akash yakirani yake sanarmin, nakasa kallon halin da mahaifina yake ciki Munaaya! Abie na yana cikin mawuyacin hali..” ‘yak'are maganar cikin zirarowar kwallar data cika masa idanu tunda yafara maganar’. Wani matsanancin tausayinsa ne ya ratsani, duk jarumtar Galadima kaga yana kuka ai kasan lamari ya 6aci gaskiya, nima hawayen suka fara gudun fanfalak'e a kumatuna, tashi nayi zaune sosai, cikin wata jarumtar da bansan inada itaba nasaka hannu Na kamo hannunsa cikin nawa. Sai kawai naga ya zame sosai ya kwantar da Kansa bisa cinyata, tareda hard'e hannayensa a k'irji. duk da kujerar tama tsawonsa kad'an, dan ma Love's chair ce. Kansa nafara shafawa a hankali, hawaye na zirara daga idona har yanzun. Shikam idanunsa a lumshe suke. Cikin tausasa harshe da tsantsar Nuna kulawa da tausayawa nace, “Yalla6ai kayi hak'uri, Abie d'inmu yana buk'ar addu'armu ne fiye da kukanmu, sannan itace jarabawarsa, wad'anda suka aikata masa hakan summa kansune, domin ALLAH bazai barsuba. idan ka amince akwai wasu addu'oi Dana Sani, Nina kakanmu ne yabama innarmu kafin yarasu, shine ta koya mana, mizai hana ka samo mana zam-zam muma mu farayima Abie su, Ubangiji gafurun rahimunne, babu abinda ya gagaresa, kuma shine yace mu rok'esa zai amsa mana”. Tunda nafara maganar bai bud'e idonsa ba, nikuma ban fasa shafa masa kaiba. Saida nakai k'arshen zancen sannan ya bud'e lumsassun idanunsa dasuka koma launin jaa a kaina. yamotsa baki kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru. Nima shirun nayi ban sake yink'urin yin magana ba, nadai cigaba da shafa kan nasa a hankali. ba akai 3minutes ba barci ya d'aukesa, sai numfashinsa danaji yakoma sauka a hankali. Ajiyar zuciya na sauke kawai, na tsurama fuskarsa ido, yaune ranar farko dana ta6a nutsuwa namasa kallon tsaff, sosai yake kamanni da dukkan iyayensa, Abie da Momma, amma yafi tsananin kama da Momma gsky, duniyar tunani nafad'a batare dana fargaba, tausayin Galadima da families nashi yana cukurkud'ar ruhina, insha ALLAH nayi alk'awarin bada gudun mawa a duniyarsu har zuwa lokacin da aurenmu zai k'are. kaina na jingina da jikin kujera, nima sai barcin ya kwasheni, dama bajin dad'in jikina nakeyiba.

********

Bayan anma Abie allurar datake temaka masa yin barci mai nauyi idan jikinsa yamotsa irin haka su Momma suka sami nutsuwa, dan yayi barci. Sai alokacin hankalin Momma yadawo kan Neman Galadima, tabbas taga yafita hankali a tashe lokacin da Abie ke fidda numfashi a wahale, amma hankalinta bai koma kan Galadiman ba. Aunty Mimi ta kalla tace, “Mimi ina d'an uwanki?”. Itama aunty Mimi sai yanzu hankalinta yadawo ta farga babu Galadima d'in, hankalinta a tashe tace, “Momma inagafa ya fita, bara na duba”. Bata jira cewar Momma ba tafito daga d'akin da sauri. ganin babu Galadima a wajen hankalinta yak'ara tashi, fitowa tayi harabar asibitin tana tambayar securitys d'in wajen. d'aya ya sanar mata ya fita a rikice gaskiya, dan suma sun nemi su taimaka masa amma baima tanka musuba. Innalillahi tashiga ambata. Bata koma wajen Momma ba tashiga mota tanufo gidan. Ta iske Samha a falo kwance, ko sauraren sannun datake mata batayiba tace, “k ina Uncle d'inku?”. Samha tace, “yana sama Mummy”. Da sassarfa ta haye step's d'in, itadai Samha da mamaki taringa binta da kallo. Ko knocking bata tsaya musuba ta turo k'ofar ta shigo. Ajiyar zuciya ta sauke dan ganin Galadima kwance, kansa bisa cinyar Munaya, hannunta d'aya na bisa Kansa, yayinda shikuma yarik'o d'ayan hannun munaya ya had'e da nasa ya d'ora kan kirjinsa, suduka barci ya kwashesu a haka. cikin sand'a ta juya ta fita taja musu k'ofar tana share hawaye dayima ALLAH godiya d'aya bama d'an uwanta mace tagari wadda take kulawa dashi. inda dane kafin yayi aure shima sai ciwonsa yatashi saboda damuwar dazai saka Kansa akan motsawar jikin Abie, amma gashi yanzun yasamu mai kwantar masa da hankali, suma kuma nasu ya kwanta suji da Abie kawai. Momma ta kira ta fad'amawa dan hankalinta itama ya kwanta. Momma harda hawayen farinciki, tana godema ALLAH. Aunty Mimi bata zaunaba suka koma asibitin itada Samha da tace zata bita, itama sai yanzu takejin jikin Abie ya motsa.

*************

A k'alla munyi barcin 47minute's, Galadima ne yafara farkawa, ya bud'e idanunsa a hankali, hannuna dake rik'e a nasa yafara kallo, kafin yad'ago ido zuwa kaina, yamin kallo kusan na 2minutes sannan yad'an motsa da nufin gyara kwanciya, saina bud'e idona, ido muka had'a, kowa yay saurin janyewa cikin basarwa, hannuna dake kansa na cire, sannan nazame Wanda yarik'e d'in, dan wata matsananciyar kunya ce kuma takamani. Shima sai ya tashi zaune sosai, a hankali yacemin “thanks”. Daba kusa dashi nakeba ma bazanjiba. Bance komaiba, shima bai sake cewa komaiba yamik'e tsaye. takalmansa kawai yacire ya d'auki jallabiya a wardrobe d'insa yashige bayi. A hankali na sauke ajiyar zuciya, tareda janye idona daga k'ofar bayin, komai banceba nakuma zamewa saman kujerar na kwanta.

Ya d'auki adadin wasu mintuna masu tsawo kafin yafito sanye da jallabiya ruwan toka, da alama wanka yayi, kallona yayi batareda yayi magana ba ya nunamin agogon dake ajiye a drowan gefen gadon alamar time d'in salla yayi. Kaina kawai na girgiza na mik'e, zuciya ta na mamakin hali irinna Galadima. Shikam turare kawai ya d'auka ya fesa yafice salla.

★★★ ((★))(())((★)) ★★★

A gidanmu kam hankalin mamansu yaa hameed da Zarah a tashe yake, dan babu Sa'eed babu labarinsa, kira Zarah tamasa yafi 50 amma yak'i d'agawa, ta tura massages babu reply, bata aikin komai sai kuka, ga ciki. Abbanmu kuma jin sanadin sawowar tata gida yace bazai kira Alhaji halliru ba har sai Zarah tafad'i ainahin gaskiya, danshi bai yarda ba itace ta d'auki kud'inba.. Innarmu dai dasuke zagi suna kallonta mak'iyarsu batakai komaiba itace tashiga lalla6a Abba damasa magiya. Itama da farko buris yay da ita, saida yaga tanace sannan yace, “wai kekam Ai'sha miyasa kika damu kankine? kinbi kin damu da lamarin wad'anda basu damu dakeba, na tabbatar da Munaya ko Munubiya ke cikin wannan halin su murna zasuyi a gidannan”. Murmushi innarmu tayi, cikin kwantar da murya tace, “Alhaji ai daga Zarah harsu munubiya duk d'ayane a wajena, domin kaine mahaifin Zarah, dukkan abinda kuma yakasance naka ina kaunarsa fiye da zatonka, a duba lamarin yarinyar kodan abinda ke gabanta, ba'a son mace mai ciki da shiga tashin hankali, muyima tufk'ar hanci tun munada sauran dama, basai Abu yayi tsamariba kuma muce zamu nemo mafita, hannunka baya ru6ewa ka yanke kayar alhaji, dan ALLAH kayi hak'uri kaji”. Jawota yayi jikinsa ya rungume yanamai saka mata albarka da aminta da buk'atarta na kiran senator halluru da safe insha ALLAH. Innarmu tamasa godiya itama.

**********

“Babyna wai mike faruwane haka?”. Da gyar Munubiya ta d'ago ido daga kwancen datake a kujera ta kalli yaa Marwan dake mata tambayar. Ta shagwa6e fuska tace, “wlhy Yaya jikinne babu dad'i, kamar jiya sai kwankwatsa kasusuwane keyi”. Zama yay kusada ita, yad'ago kanta ya jinginata a jikinsa yana ta6a wuyanta, “please ki yarda muje asibiti adubaki mana?”. “a'a dan ALLAH Yaya, wlhy banason zuwa, kabari muga kwana biyu idan bai dainaba saimuje d'in”. “Amma kuma k'ya zauna da ciwo, ki daure dai, kinga ko abinci kin kasa mana fa”. “babu damuwa Yaya, yanzu zan tashi na d'ora, dan zazza6inma ya sauka ALLAH”. “Ana dai so aima Yaya wayo kawai”. Murmushi tayi tana tashi daga jikinsa,, takama hannunsa ta sumbata sannan tatashi tafice daga falon. Binta kawai yay da kallo yana murmushi, yana k'aunar matarsa kuma 'Yar uwarsa, gaba d'aya Munubiya ta canjashi, dukda bawai miskilancinsa yabariba, itace kawai yanzu baya iyama miskilancin nasa, komai a d'auren da fuskarsa take da zarar ya tunkaro gida zakiga yafara sakin murmushi, balle yay tozali da fuskar tauraruwar nan tashi mai haske da kawalwalniya a zuciyarsa. Mik'ewa yayi yabi bayanta zuwa kitchen d'in danya taimaka mata da aikin, dan yau d'in weekend ne baije aikiba. dan yayi resume tun last week.

((★))*((★))*((★))*((★))

Tunda na idar da sallar nazame a wajen na kwanta, bawai barcin nakeba, jikinane kawai da baya min dad'i, jinake kamar ana kwankwatsamin kashin jiki, sallamarsa tasakani d'ago ido na kallesa, sannan na amsa ciki-ciki nima. Frigate ya bud'e ya d'auki ruwa yakoma saman sofar ya zauna, murfin kawai ya 6alle ya hau kwankwad'a, saida ya shanyeshi tas sannan ya ajiye goran yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. nikam na k'ura masa idanu nakasa janyewa. saida yad'ago muka had'a idanu sannan nayi saurin yin k'asa da nawa. Shi bai janyeba yana kallona yace, “tashi muje hospital d'in, daga nan saimu samo zam-zam d'in”. Tunkan yakai k'arshen maganarma na mik'e tsaye, hijjab kawai nasaka nad'an gyara fuskata, shikuma ya d'auki kaya yashiga bayi ya canjo sannan muka fice. Jin gidan shiru yasashi d'aukar waya yakira sashen bayin gidan, babu dad'ewa saiga d'aya acikinsu tazo. Zubewa tayi tana gaishemu, ya d'aga mata hannu yayinda nikuma na amsa. yace, “ina Samha?”. “Ranka ya dad'e sunfita suda mummy”. Yasan aunty Mimi take nufi, dan haka bai sake cewa uffan ba yafice abinsa. sai nice nace tatashi taje, sannan nabiyoshi abaya. Sai da yasakama k'ofar security sannan muka nufi wajen motarsa, bayin dake zaune a harabar gidan maza sukazo da sauri suna gaishemu, hannu kawai suma ya d'aga musu muka shiga motar, suka bud'e mana gate d'in muka fice. Tunda muka fita babu Wanda yay magana tsakanin ni da shi, yana aikin tuk'insa da sauraren redio daya kunna a motar, nikam ina lafe a kujera ciwo ya isheni, dan bana fahimtar yaren dasukeyi a redio d'in, tunda ba English baneba gaskiya.

Mun Isa wani babban shagon Islamic camix, komai zaka iya samunsa daya shafi maganin muslinci. Abinda ya kaimu muka shigayi, yad'ebo zam-zam dayawa, sannan ya kalleni yana fad'in “saikuma mi?”? Shiru nayi ina nazari. Dame yakamata muk'ara?, zuwa can nad'an hau duddubawa ina karanta sunayen magungunan ajikin kwalin, duk maganin danaga zai iya shafar jinnu ko sihiri, saida na d'akkoshi, (a tunanina idan mun dawo gidan zan d'auki hotunansu na turama Munubiya ta bincikamin yanda yadace ayi amfani dasu. Duk abinda nake yana a tsaye yana kallona, saida na kammala sannan nasanar masa na gama. Mun k'arasa wajen biyan kud'i, bayan yabiya yaran shagon d'aya ya d'aukar mana zuwa mota.

Daga nan asibitin muka nufa, mun tarar har lokacin Abie yana barci, sai gaisawa nukayi da momma da aunty Mimi, duk sunji dad'in yanda sukaga Galadima cikin nutsuwarsa. Zama yay kusada Abie yana mai tsurama masa idanu da masa addu'oi samun lafiya a zuciya, da kuma kudirar binne Wanda ya cutar masa da mahaifi da ransa idan ya kamashi a hannu. Momma tayi farinciki da yanayin Galadima d'in cikin k'oshin lafiyarsa, dan da a dane da yanzu shima yana gadon asibitin, amma Alhmdllh yanzu gashi normal. Mukam ni da Samha muna gefe zaune muma, ba hira mukeba, kowa yayi shirune yana tunanin duniya. Sauban ma yana dawowa daga school shida Khaleel nan suka taho. Bamu bar asibitinba sai dare, harda Momma muka wuce, dan yau suna buk'atar Abie ya kwana tare da ma'aikatansu.

Koda muka shigo Galadima sama ya wuce abinsa, ganin haka Momma tace natashi na naje nima na kwanta na huta hakanan. A kunyace na mik'e domin cika umarninta. Na iske yana cire kaya, dan haka nakoma da baya zuwa falo, saida na kintaci yagama sannan na shigo, na iskeshi yashiga wanka, nima natu6e nawa na d'aura zani nasaka hijjab tareda d'aukar kayan barcina ina jiran fitowarsa. Bai dad'eba sosai kuwa yafito, sanye yake da bathtub fara tas, ban yarda na kalleshi ba natashi nashige nima. Mai makon yayi shirin barci saiya kwanta a bakin gadon a haka, k'afafunsa na k'asa, ya tsurama rufin d'akin idanu alamar yatafi duniyar tunani. Nikam ruwa mai zafi na had'a nashiga koda zanji dad'in jikina, na dad'e acikin ruwan kwance, jinakema kamar karna fito. shikansa yafara tunanin lafiya kuwa?, lokaci-lokaci yakan kalli k'ofar bayin, Amma babuni babu dalilina. Yana shirin zuwa yamin knocking sai gani nafito kuma, janye idonsa yayi daga saitin k'ofar cikeda basarwa. Ni bammasan yanayiba, dama nayi shirin barcina tun aciki, saina d'auki zani na d'ora a saman kayan nasaka hijjab nayi sallar shafa'i da wutiri, bayan na idar nad'akko roban zam-zam d'in d'aya na zauna nafara karatu Qur'an acikin ruwan zam-zam d'in. a hankali nake karatun cikin nutsuwa, dukda barcin dakecin idona. Har cikin 6argonsa da jini yakejin sautin karatuna, ya lumshe idanu yanamaijin kamar mu kwana a haka inayi. mik'ewa yayi shima yayo alwala yazo yay shafa'i da witiri yay joining d'ina muka cigaba da karatun a tare. Bamu kwanta ba saida mukayi sallar asubahi. (da yake sai zuwa 1 zasu bari ashiga wajen Abie, yau kuma babu aiki).

____((()))((*((()))*))((()))____

Yauma dai haka innarmu tadagema abbanmu saida yakira Senator Halluru agabanta, dan Zarah tana kwance babuma lafiya, ga mamansu Yaa Hameed ita kanta kallo d'aya xaka mata kagane abirkice take. Innarmu duksai suka bata tausayi, matan gidanmu kuwa abin magana yasamu, sai gulma da dariyar gatsatsa, ita kanta Momy Hadiza ta hannun damar mamansu yaa Hameed d'in dad'i takeji, tanadai nuna damuwarta agaban mamansu Yaa hameed d'inne. Bayan Abba sun gaisa da Senator halluri sukad'anyi barkwancinsu na abokai sannan yasakko xancen Zarah. Hankalin Senator halluru yatashi, danshi koda wasana baisan Zarah bata nanba, yadai lura kullum Sa'eed saiyaje gida yaci abinci, shi duk zatonsa Zaran bata iya girkine saboda ciki. Hak'uri yashiga bama Abbanmu yace wlhy shi baima saniba, amma insha ALLAH zai bincika, zuwa dare sa'eed d'in zaizo ya d'auki matarsa. Dahaka sukai sallana da Abba kowa nakuma bama d'an uwansa hak'uri akan lamarin. Innarmu bata buk'atar jin k'arin bayani dantaji komai, takumaji dad'i sosai.

()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull