Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 26
Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 26: Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 26. Ran mama Fulani a 6ace yake kallon manyan jikokin nata maza guda uku tayi,…
4,419 words
Ran mama Fulani a 6ace yake kallon manyan jikokin nata maza guda uku tayi, cikin isarta da k'asaitarta tafara kiran sunayensu, “Talba! Wanbai! Matawalle!, kunsan dalilina Na taraku anan kuwa?”. A tare suka girgiza mata kai kawai. Takuma gyara zamanta cikin tsantsar mulki da izza, tace, “nakula mahaifinku har zuwa yanzu baison ciwonku ba, shi dole yanaso ace masa adalin Sarki, shiyyasa kullum yake fifita d'an wani bisa Ku da ALLAH ya bashi, Matawalle shekarunka dana Galadima kusan d'ayane, amma mahaifinku nagani Galadima yay aure bai ta6a nuna damuwarsa akan kai kayiba balle sauran 'yan uwanka, to yanzu matar Galadima cikine da ita, kuma tabbas ta haifi namiji kuda sarautar gagara badau saidai kallo”. A razane Talba da wambai suka zaro idanu waje a zabure, matawalle kuwa murmushi kawai yayi yana girgiza kai da mamakin wannan kakar tasu mai shegen son kanta. Wambai yace, “haba Granny miyasa kike fad'ar wannan maganar, yakamata bakinki ya fad'i alkairi mana, shi dan uban cikin basai mun bari an haifesa ba, koshi uban cikin dayake tak'ama yana jiran gado bai isa yayi mulkiba balle cikin da babu tabbas d'in haifosa, ni wlhy kinma 6atamin rai”. Talba yaja tsuka shima yana harare-harare, “Granny ya akayi kikasan tanama da cikin to? wannan sarkin girman kai d'inne zai iyama mace ciki?”. Harara mama Fulani ta zubama Talba, “to uban matanbaya, azatonka zai zuba mata idone yana kallonta kamar hoto ko television a gida? ince kwana nan 4 kenan dabaro inda suke”. Wambai yace “amma shine bakiyi maganarba sai yau Granny?”. “to ubana koyamin yanda zanyi”. “ALLAH yabaki hak'uri”. ‘cewar wambai yana k'unk'uni k'asa-k'asa’. Matawalle dabaice uffanba tunda aka fara maganar yay guntun murmushi, muryarsa a tausashe yace, “Ranki ya dad'e ni banga amfanin wannan maganarba, ALLAH shine ya azurta Galadima da samun ciki a jikin matarsa, wannan kuma abun farin cikinmu ne amatsayinmu Na 'yan uwansa, shi dai mulki Na ALLAH ne, shike badawa ga Wanda yaso akuma lokacin da yaso, bamuda tabbacin tsawancin ran ganin gobenmu ma balle maganar gadar sarautar cikinma daba'a San miza a haifaba, please musama zukatanmu sallama kodan mutuwa, nifa banga wani dalili dazamu ke saka kammu a wahala akan mulkin da ubangijine kawai madawwami a mulkinsa, nikam kunga tafiyata, ki gafarceni inada uzuri”. Tunda matawalle yafara maganar Mama Fulani da Talba da wambai ido suka zuba masa, harya fice ba'a samu mai iya tanka masaba. haka yake shi, babu ruwansa da bak'in mugun abun masarautar, da zuciya d'aya yakeson d'an uwansa, shi bama wani zaman k'asar ma yakeba sosai. Wani wawan tsaki Talba yaja, yabi bayan Matawalle da harara yana fad'in “lusari kawai, inkai bakason sarautar mu ai munaso, shifa wannan ko sarautar ya gada wlhy lusarin Sarki mai lasisi za'ayi anan, duk wannan wahalar akansa akeyinta danya zama magajin Abba amma shashashan nan baya gani”. “mtsoww!! bar banza d'an uwa, idan zai bamu matsala kai basai ka zama magajin Abban ba, nifa harma tunani nake, anya matawalle jinin gidannan ne?..........” “kai ya isa haka, banason rashin tauna magana, Ku k'yalesa zaima dawo hanyane, miye mafita yanzun?”. “mafita d'ayace Granny a 6arar da shegen cikin kawai, kuma ma ai Galadiman yazo jiya”. Da sauri mama Fulani ta tashi zaune daga kishin gid'ar datayi, “wambai kana nufin Sameer na a masarautar nan?”. “kwarai ma kuwa, da safe nagansa zaishiga mota a k'ofar sashensa, yanata faman d'aurema mutane wannan shegiyar fuskar tashi da yakejin tafi ta kowa k'yawun gani”. Wani k'asaitaccen murmushi mama Fulani tayi tana fad'in “lallai yaronnan ya isa, kuje kawai, bayan nagama tsara komai zan nemeku”. atare suka mik'e suna fad'in “ahuta lafiya ranki ya dad'e sarauniyar gagara badau”. Murmushi tama jikokin nata tana gyad'a musu kai.
____((____(((★)))____))____
Galadima da Nuren sun shiga ainahin matsakaicin gidan Nuren dake a gidan gonarsa Na kiwo, sosai ya tsara cikin gidan, dan ananne yake holewa da 'yammatansa a watannin baya, sai dai yanzu kam alhmdllh yabari gaskiya, dan sai lokaci-lokaci yake d'an ta6awa, fatansa ma yabari gaba d'aya, dama ta silar abokai ya koya🤦🏻♀. Galadima ya zauna saman kujerar guda d'aya yana sauke numfashi, har yanzu zuciyarsa tak'i nutsuwa waje d'aya, halin da yaga Abban Munaya ya dank'are masa zuciya. Cikin ma'aikatan wajen yay sallama daga waje, Nuren yabashi izinin shigowa, kayan marmarine yahad'o ya kawo musu bayan ya tsaftacesu, a saman center table d'in ya ajiye, sannan yakona yaciro musu ruwa a freight d'in dake falon da cups Na glass. Bayan fitarsa Galadima ya kalli Nuren d'in, “Brother wai miyasa ka kawoni nan ne?”. “cinikin kanka nayi”. ‘cewar Nuren yana harar Galadima’. “Wani k'asaitaccen murmushi Galadima ya saki, yakai hannu yana shafa sajensa zuwa gemu, cikin d'age kafad'a da la6e baki yace “baka kai girman saida kainaba yaro”. “uyim! Haka kace ko?”. ‘cewar Nuren yana kallon galadima’. “kaima kasan hakanne ai”. Mik'ewa Nuren yayi yashiga wani d'aki yana dariya, mintuna 4kacal saigashi tare da wani dattijo. Galadima da yake kishingid'e yad'ago ido yana kallon Nuren da dattijon, amma baice komaiba yacigaba da latsa wayarsa hankali kwance. Dattijo direban Alhaji balala ya zube k'asa yana kwasar gaisuwa ga Galadima. Galadima shi mutumne mai mutunta Wanda ya girmesa, dan haka Yakuma d'ago kai yana kallon dattijon, fuskarsa ba'a d'aureba ba'a sakeba, cikin muryarnan tasa ta isar masu mulki da k'asaita yace “no baba zauna da k'yau, kabar durk'usamin banaso”. Dattijo yace, “ai girmanka ne ranka ya dad'e”. Murmushi kawai Galadima yayi, ya ajiye wayar hannunsa yatashi zaune sosai, ruwa ya d'auka ya zuba a cup sannan ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallon dattijo. “bawan ALLAH minene sunanka?”. Jikin dattijo Na rawa yace “Barau ranka ya dad'e”. “humyim baba barau, koka sanni?”. “sosaima ranka ya dad'e, wanene zaice bai sankaba a wannan nahiyar”. Galadima ya wani lumshe idanu yana cije lips nashi, ya bud'e idanun akan Mal barau da duk yake a tsure, sosai kwarjinin Galadima da cikar haibarsa suka rikita dukkan tunaninsa da kwarin guywarsa. Galadima ya katse masa tunani da fad'in, “Baba barau nasan akwai tambayoyi taf bakinka a gareni, saidai bazan baka amsar ko guda d'ayaba, zan baka dama da sharad'i, Na farko shine kanada damar fad'amin gaskiyar abinda kasani idan Na tambayeka, nikuma nabarka ka tafi salin alin, Na biyu inada sharad'in ka d'aukarmin alk'awarin komai zai fito abakinka ya zamto gaskiyar abinda Na tambayeka, idan kamin k'arya koka yaudareni kuma.... Humm”. ‘yak'are maganar da cije lips nashi batare da ya k'arasaba’. Hakan yasaka jinin Malam barau rawa, yana karkarwa yace, “insha ALLAHU ranka ya dad'e zaka sameni yanda duk kake buk'ata”. Nuren yace, “good daka fahimci hakan”.
Galadima bai sake cewa komaiba yacigaba da latsa wayarsa.
Nuren ya kalli Malam barau yace, “malam barau kasan wanene tsohon Sarki?”. “eh kwarai ranka ya dad'e Na sanshi, shine yake jinya a India yanzu haka aiko”. “shin minene alak'ar uban gidanka da tsohon Sarki?”. A rikice Malam barau yace “ranka ya dad'e miyasa zakamin wannan tambayar? Ku gafarceni, kuyi wata amma ba wannanan ba dan ALLAH”. Galadima ya d'ago idanu ya zubama Malam barau su, jiyay zuciyarsa tana Neman fara hasala, har zaiyi maganar sai kuma miya tuna yay shiru ya had'iyeta, maida kansa yayi yacigaba da latsa wayarsa. Nuren ya bud'e k'aramar drowa dake jikin center table d'in falon, saiga bindiga 'Yar k'arama ta bayyana, Malam barau ya waro idanu waje yana kallon yanda Nuren ke d'ura Bullets a cikin bindigar. Galadima duk yana kallon Nuren ta gefen ido amma baice masa uffanba, saida Nuren ya gama sannan ya tashi ya koma kujerar kusada Malam barau, cikin d'aure face yace, “nasan dai tsoron mutuwa ko rasa aiki zai hanaka bamu amsar tambayarmu, to tabbas in baka fad'anba zan fasa kwalwar kanka da wannan gun d'in, kuma ko k'arar fitar bullet d'inta baza'ajiba ballema asan an kasheka, akuma cikin falonnan zan binne gawarka wlhy!!”. Jikin Malam barau Na 6ari yarik'e wandonsa, dan har fitsari yafara fito masa kad'an, yace, “ranka ya dad'e mi kuke son sanine?”.
Galadima dake latsa wayarsa hankali kwance, batareda ya d'agoba yace, 20 ga watan Yuli miya faru a masarautar gagara badau”. “ranka ya dad'e wlhy bansan komaiba, amma tabbas ogana yafito ransa a 6ace daga wajen meeting d'in dasukayi da Sarki shida abokansa. daga hakan bansan komaiba wlhy kaji Na rantse maka”. Idanu Galadima ya d'ago ya zubama Malam barau, yace, “malam Saminu kafadda!. koba shine ainahin sunanka ba? Na sanar da kai karkamin k'arya, dan tunkan nakawoka nan nasan komai daya shafeka, amma a tashin farko kamin k'aryar sunanka Malam barau, humm abin dariya, inason mutum mai gardama dason ku6tar da kai. Malam Saminu shiga tarkon Muhammad Sameer ba abune mai sauk'iba, ina aiki da kwakwalwa, kamar yanda gangar jiki take aiki da zuciya, karka yarda a maganarka ta gaba k'arya ta shigo, idan hakan ta kasance saina binneka da ranka, wannan tabbatacciyar maganar Muhammad Sameer Saifuddeen ce”. ‘ya k'are maganar da mik'ewa tsaye yana had'a yatsunsa biyu ya buga a saitin fuskar Malam Saminu, suka bada sautin d'as! d'ass!, sannan ya ra6a ta gefensa yafice’.
Nuren ya girgiza kansa, “dattijo kayi kuskure kwarai da gaske, Galadima ya wuce dukkan tunaninka, tashi mu koma inda ka fito, a yanzu kam bazai ta6a saurarenka ba sai kuma wani karon”. Hawaye Malam Saminu yafarayi yana bama Nuren hak'uri, “yalla6ai dan girman ALLAH ka kirashi, wlhy zan fad'a yanzu, wlhy nagaji da zaman kurkukunnan, nasan hankalin iyalaina da mai gidana a tashe take, ka taimakeni”. K'ala Nuren baice masaba, ya dannashi a d'akin ya maida ya kulle sannan yabi bayan Galadima.
★):(★):(★):(★)(★):(★):(★):(★):(★
Tunda suka tafi babu Wanda yay maganar, saida suka shigo cikin gari sosai. Nuren yace, “dattijonnan nakula zaiyi taurin kai gaskiya”. Murmushi Galadima yayi yana kuma lafewa cikin seat, idonsa a lumshe batareda ya bud'eba yace, “mu wuce asibiti”. Amsawa da to kawai Nuren yayi.
Sun isa asibiti suka iske duk 'yan gidanmu suna nan, saisu Munubiya da Dady yace su tafi gidajensu hakanan, tundama ba bari ake aga Abban ba basuga amfanin zaman nasuba, gashi mafi yawansu duk da tsohon ciki, sai kuma Munubiya da Fauziyya da Haleematu dake fama da laulayi. Haka ba dan sun soba kowacce takama hanyar gidanta, wadda mijinta kuma yace ta jirasa ta zauna jiransa. Suma su innarmu Yaa Anas ya kwashesu ya maida gida.
Lokacin da su Galadima suka shigo asibitin mafi yawansu duk sun wuce, sai mazan kawaine a asibitin. Dan haka Galadima yasamu gaisawa da Munubiya dake jiran yaa marwan yazo d'aukarta. Munubiya ta tambayi 'Yar uwarta fa?, gaban Galadima yafad'i, danshi yama manta su Munaya suna hanya, guntun murmushi yayma Munubiya yace insha ALLAH suna hanya itama, maybe su iso cikin darene kokuma da asuba”. “ALLAH ya kawosu lafiya”. ‘cewar Munubiya tana sharar hawaye’.
Tabama Galadima tausayi sosai, haka ya k'arasa wajen doctor domin kumajin ko ansamu wani cigaba a jikin abban.. Doctor yamasa bayanin duk an gyara karayar jikin Abba, hakama sauran ciwukan suna samun kulawa, kuma bugun zuciyarsa ta daidaita bakamar jiya zuwa safiyar yauba. Galadima ya jinjina kai, tareda sake jaddadama doctor gargad'in kulawa da Abba d'in sosai. Yad'an jima a asibitin sannan su sarkin mota sukazo d'aukarsa, Nuren kuma daga nan hotel d'in daya sauka yanufa. ya sauka hotel ne saboda basa buk'atar wani a masarautar su Galadima yasan da Nuren d'in.
___________________________
Wajen misalin 2:30 na dare su Munaya suka sauka, Sauban yayta wayge-wayge ko an zo d'aukarsu, amma baiga alamun wani mai alak'a da masarautaba, ya kalli Munaya yana dariyar tsokana, “Aunty gimbiya Honey d'inki ya manta damu, bai aiko d'aukarmu ba, kuma inatsoron mu shiga motar haya azo a kwamushemu, kinsan yanzun kasuwancin kidnapping shine keda tsada a 9ja”. Duk da Munaya tana tare da damuwa hakan bai hanata yin dariyaba, tace, “kai yaa Sauban bakada dama, ina zamu samu waya mu kirashi to?”. Kafin Sauban yabata amsa sukaji magana a bayansu. “to maganannu, saikuzo mu wuce, wannan surutun nakuma bayasa ayi kidnapping d'in naku ba”. Gaba d'ayansu juyowa sukai suna kallonsa, Galadima ne sanye cikin wando fari 3quarter da riga t-shirt pink mai gajeren hannu. harya kwanta suka fad'o masa a rai, babu shiri yazari mukullan mota yafito, bai tada kowaba a dogaransa saboda kasada irin tasa ya fito zuwa airport, isowarsa baifi da 17minutes ba jirginsu Munaya ya sauka, tunda suka fara fitowa daga jirgin idonsu a kansa, har tsayuwarsu da waige-waigen dasukeyi na son ganin Wanda yazo d'aukarsu yana kallonsu. shagala yay da kallon Munaya, wadda sai a yanzune yaga k'ibar da Samha ke fad'in tayi, ta murje tayi 6ul-6ul da ita, har wani haske yaga ta k'ara masa, saboda hasken daya haske ko'ina a cikin airport d'in. yadad'e tsaye a bayansu, duk gulmarsa da Sauban yayi akan kunnensa ne.
Sauban ya k'araso da sauri ya rungume d'an uwansa, dukda jiyane kawai suka rabu saiyaji yayi kewarsa. Galadima yad'an daki bayansa yana fad'in “k'aton banza, ka girma bakasan ka girma ba”. d'agowa Sauban yayi daga jikin Galadima yana dariya, yayinda Munaya da Galadima suka had'a idanu, gira d'aya ya d'aga mata, itakuma tayi guntun murmushi tana kauda idonta gefe. (A ranta tace d'an duniya). Juyawa yayi batare da yak'ara magana ba, Munaya da Sauban sukabi bayansa, Sauban ya shiga baya, badan Munaya tasoba tashiga gaba kusada Galadima da zaiyi driving nasu, wannan ne karon farko da zataga tuk'insa a k'asarsa. Saida yatada motar suka fita daga airport d'in sannan a hankali kamar bataso tace, “yalla6ai mun sameku lafiya?”. Juyowa yayi kad'an ya kalleta ya maida kansa ga titi, saida yaja numfashi sannan yace, “kunzo lafiya my Friend?”. Kallonsa kawai tayi kad'an ta girgiza kai, a zuciyarta tace su Friend anji jiki, zanbika a hakan kodan samun yanda nakeso a kanka, danna cika alk'awarin danama mahaifiyarka insha ALLAH. jin batace komaiba yakuma fad'in “ko gajiyar tafiyarce?”. “kusan haka yalla6ai”. Yace, “to sannu yalla6iya”. Ba Munaya ba har Sauban saida yayi dariya da wannan suna, daganan motar ta d'auki shiru, har suka Isa masarautar.
Muftahu dake binsu abaya ya sauke ajiyar zuciya, sannan shima ya shigo masarautar, tunda Galadima ya fito daga sashensa akan idonsane, Dan haka yay saurin bin bayansa da mota shima Dan yaga inda zaije. (Humm Muftahu😏).
Sosai Munaya kejin barci da farinciki, yau gata tadawo k'asarta ta haihuwa, sun shiga sashen komai need tagansa, sai k'amshi dake tashi kamar kullum. d'akinta ta shige, Sauban da Galadima suka nufi nasa. Sauban ya zube a kujera yana kiran “wash!”. Galadima ya d'an hararesa, “amma idan yawonkane aibaka gajiya”. “yaya wlhy bazaka ganeba, nidai kawai bani wajen kwana na kwanta wlhy”. “Saidai ka kwana anan falo kuwa, kafin da safe a gyara sashenku ka koma can”. 6ata fuska Sauban yayi, “haba Yaya da gatana na kwana saman kujera, kadai katafi d'akin Aunty gimbiya ka kwana gaskiya kabani gadonka”. Galadima zaiyi magana Sauban yatashi da gudu ya shige bedroom d'insa ya saka key. Da sauri Galadima yace, “zan 6ata maka rai fa Sauban”. Ina, baima sauraresa ba, dafe kai Galadima yayi kawai, wlhy baisan lokacin da Sauban yafara rainashiba, kodan yaga tsawonsu kusan d'aya yanzu?. babu yanda ya iya dole yafita zuwa d'akin Munaya🤫.................✍🏼
Ho Sauban aikinka yay k'yau🤣, su Galadima dole a tafi😝, ba ruwana karya jini🤭⛹🏻♀
Readers kuma kuyi dariya a hankali fa🤫😝.
Barkanku da juma'a🙋🏻.
Musha weekend lafiya sisters😁🙋🏻⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_* AWESOME WRITER'S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA! 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 (bansan ita bace) 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
Wannan page din nakune INA TARE DA ITA fans club gsky naji dadi sosai da comments dinku na jiya dan yafi na kowa😻😻
NOT EDITED
🅿69&70
Kafin tayi mgn taga get man yabudewa yah Suleiman get ya cinno hancin motarsa ....wani irin bugawa kirjinta yyi sbd tunawa datayi da warning d'in da yah Suleiman yyi mata game da maganar Abbas din agabanshi... Shikuwa Abbas kallon ta yake yanata zuba surutunsa har yalura tana duniyar tunani"fuskarsa ya matsa gab da tata yahura mata iskar bakinsa....adede nan Yah Suleiman dakeyin parking idanunsa suka hasko masa baby da wani gab da juna dan saiyaga kamar kissing d'in ta zaiyi.. Wani mugun burki yaja,yana huci yafito azafafe ko murfin motar be rufeba yanufi gunsu. Wani irin zafi da k'una yakeji azuciyar sa afili yace gsky yarinyar nan ta rainani ,amma zanyi maganinta dg shi har ita,yafad'a idanunsa sunyi jajir zuciyarsa nace masa ko shine ABBAS?" Azafafe yakoma mota yaciro bindigarsa yanufo gunsu...
Baby kuwa tunda ta ga yadoso gurunsu atsorace ta kalli Abbas daketa tambayar ta tunanin me take haka?" Murya na rawa sbd tsoro tace pls yah Abbas kabar gidan nan yanxun ga yah Suleiman nan kuma wlh zai iya maka illa dan zafin zuciya ne da shi" D'agowa Abbas yyi yahango jarimi ,sadauki ingarman namiji cikin kakinsa na sodoji. yanufosu sai kuma yaga yajuya gun motarsa. Da sauri yace wanene shi ?"meye matsayinsa agunki? da kika tsorata dan yaganmu tare da ke matsayina na Wanda zaki aura.....maganar ta mak'alemasa ganin yah Suleiman din yasake nufosu da bindiga ahannunsa. Salati baby tayi sai hawaye shar afuskarta ta San lallai yau me kwatar Abbas gunsa sai ALLAH .
Shikuwa yah Suleiman wani mugun kallo yake jifarsu da shi yana ganin duk Dan sbd Abbas din ko waye take zubda hawayenta sbd shi bata sonsa aidama be manceba tace bata sonsa Abbas take so. Kamar yadda shima baya sonta IFTI ce aransa...tuni yasake zuciya bbu annuri a fuskarsa ya ida isa gunsu.. Abbas kuwa daurewa kawai yake amma hankalinsa inyyi dubu tashe yake sbd yalura bbu sassauci afuskar yah Suleiman din ."
Cikin tsawa had'e da karaji yace kai dan k'auye !dak'iki me yashigo dakai gidan mutane?"bbu izininsu.....da sauri baby ta katsesa da pls yaya kayi hkuri wlh na laifinsa bane laifinane amma yah Abbas be.....wani gigitaccen mari yawanko mata "saida taga stars namata shawagi tuni tadafe gurin tasaki k'ara.. Abbas yyi karfin halin cewa gsky wannan ba adalci bne dazaka kamata kadaketa sbd..wata wawar fincika yah Suleiman yyi masa had'e da makasa jikin bango atake bakinsa yafashe. Cikin isa yah Suleiman yace yes na mareta sbd na isa ne kuma kaima yanxun zan Nuna maka isata ta hanyar yimaka hukunci da laifinka duk da nasan.bakasan wanene niba! Tuni yasaita bindigarsa zai harbi Abbas ....da sauri baby dke tsaye dafe da kunci tana kuka tamatsa gaban Abbas cikin dakiya tace ah ah ni zaka kashe bashiba ,ta fad'a had'e da tare Abbas d'in kafin yah Suleiman yyi wani abu yaji Abba abdullahi na masa tsawa had'e da cewa kada kasake kayi Harbin nan....tuni yah Suleiman yyi wurgi da bindigar ya finciko baby da hannu daya ,hannudaya yakaiwa abbas wani wawan punch a fuska tuni hancinsa yafashe yyinda Abba ya iso afusace ya wanke yah Suleiman da mari had'e da cewa me yamaka ?"
Beyi mgn ba idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa duk sun mik'e rad'o rad'o, yanajin zafin hanasa da Abba yyi yama Abbas hukunci......sai botsare botsare take tanaso yacikata ta taimakawa Abbas ganin halin dayake kuma sbd ita"amma yarik'e ta gam.
"Abba ne daya lura yah Suleiman bazaiyi bayaniba sbd dokin zuciyar dayahau " yasa Yakama Abbas suka nufi get . https://2gnblog.blogspot.com/ Shikuwa gogan ganin abinda baby keyi yasake bata masa rai azafafe yadauketa da bindigarsa yyi part d'in sa da ita tanata ihu da kiran sunan Abbas din.
Abba kuwa suna fita saiga motar yah Yusuf tuni yatsayar dashi suka shige hade da nufar asibiti.
Bayan duk anbasa treatment d'in da yadace aka samasa drip had'e da yimasa allurar bacci sannan Abba yakira abbu yace su had'u a asibitin.
Shikuwa yah Yusuf yanufo gd yana tambayar kansa wanene wancan saurayin ?"kuma waye yajimasa ciwo haka acikin gidan?"
"Xuciyarsa tace yah Suleiman ne"
Shiru yyi had'e da yin parking yafito yanufi part d'in su...zubaida dke kallonsa ta window tana Dakon zuwansa tun dazun ,jitake kamar ta bisa saidai zuciyarta nace mata hmmm kije kici dukaba....
**********
Abbu kuwa byn yaje asibitin nan Abba yyimasa bayanin iya abinda yasani game da abbas,ajiyar zuciya yyi yace hmmmm wannan Yaro ALLAH yarabasa da Wannan zafin zuciya tasa! Yanxun dabakazoba fazai iya kissan kai "oh ALLAH yakyauta ,amma yanxun mujira asallamesa muwuce gd naga Suleiman din yyimun bayani meye hujjarsa na zubarwa da wannan Yaro jini.
Abbu yyi ajiyar zuciya afili yace gsky yaya Wannan karon zan yadda kwallon mangwaro na huta da kuda..
Abbu da mamaki yace mekake nufi?"
Abba yyi masa bayanin abinda yafaru da mm zulai dg karshe yace datadawo takardar sakinta zanbata nagaji wlh bazan iyaba ,mace daya nasan samun hawan jini da bacin ciwon zuciyar data samun...
Cikin rarrashi da ban baki abbu yace ah ah bazaa yi hakaba kodan sbd y'ayanta,kak'ara hkuri dan ALLAH kaje kabiyasu ayo Belin nata....katsesa yyi da cewa ah ah wlh kokai ban amince ka biyaba gwara abarta can kotasaduda da duniya....
Kiran sallar laasarne yasa suka fita masallacin , kafin sudawo ya farka ancire masa drip,bbu laifi jikin yyi masa sauki saidai yasha alwashin bazai koma gidan su baby ba yanxun zai koma kauye ko da dare ne ya isa"sbd yatsorata da sojan nan dan yatabbar mutumin bashida imani,inbachin yanada sauran shan ruwa da sai dai wani bashiba ,saidai yasha alwashin daya sauka gd zaije gun mlm yyimasa bayani ,wanene sojan nan?"meye matsayinsa agun nah nah? """""
Saurin tashi yyi ganin bbu kowa a room d'in dan beso ma su had'e da Abba daya taimakesa yakasa asibitin, yyi saurin ficewa yyi tasha yahau motar garinsu...
Su abbu nadawowa suka sami room d'in wayam,bbu Abbas bbu alamarsa ,nan suka tambaya a reception akace ai ya fita ,abbu yacewa Abba to shikenan ALLAH shi kyauta muje yanxun gd ni naga Suleiman din dolensa yyimun bayani da haka suka nufi gd...
-----------------------------------
Bangaren mm zulai kuwa tun amota take hawaye tana gayawa Laure saita d'au fansar abinda Tamara,dariya Laure tayi tace hmmm wlh zakijawa kanki natona abinda kika binne....cikin ko inkula mm zulai ta ce eh ai harda ke ,baki daya zaki tonama asirin .....police guda yace malamai kuyimana shiru,tsit sukayi harsuka iso aka saka mm zulai cell,aciki tasami wasu mata 8itace ta Tara ta tsorata ain in dan bata taba zuwa police station ba sai yau jiki bbu kwari ta zauna aka rufesu ciki. Sai kallon su take tana Dade hanci sbd wari da zauri da gurin keyi,tuni tafara jin tukar amai sbd ko break batayiba aka taho da ita. Kakarin amai ta fara ...cikin matan dake cell din wata tantiriya y'ar tasha ta watsawa mama zulai mugun kallo had'e da cewa ke karamar y'ar iska! Zakixo Okinawa mutane iyayi d hura hanci ke mai tsabta harda yunkurin amai ko?in har da gske ke me tsabtar zuciya ce bazakiyi laifi akaiki police station....afusace mama zulai tace ke matsiyaciya karamar y'ar bariki me ruwanki dani dazakizo kinamun halin dabbanci...
Azafafe tayi gun mm zulai had'e da mata wawar fincika tacigaba da jibga ,tun mm zulai na iya ramawa harta tagayyara sbd batayi break ba,tuni matar ta kumbura mata fuska ,sukuwa sauran dama tsoron matar suke basuce komai ba harta gaji ta kyale mm zulai din ta yi kwance yashe kamar kayan wanki.
Zuwa 12:00 har jikinta yyi zafida zazzabi da ciwon kai, mace daya ce mai dan tausayi tasanar da Wanda yakekae musu abinci ,yaje yakarbo magani yakawo ,byn taci abincin da ko almajiri bazata iya bashiba tasha maganin ,tana tuna yayanta da gd tana hawaye...
Yah Suleiman kuwa..
Share..
📚📚mmn fareesa ce✍✍ *_Typing📲_*
*_Haske writer's asso...._*💡
*_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻
~Book 2~ 👉🏻6⃣ https://2gnblog.blogspot.com/
............Har ya fita ya dawo, laptop da wasu takardu ya d'auka a falonsa ya fita, zai zauna a falonta saikuma wata dabara ta fad'o masa, bedroom d'inta ya nufa yana wani ciccijewa (kaida zaka karoro, miye na fuska to yalla6ai?🤔😂). Munaya Na tsaye tana ninke hijjab d'in data rama sallolin dasuka risketa a hanya sai kawai shigowarsa tagani da sallama ciki-ciki. k'ok'arin warware hijjabin tafarayi tana masifa ita kad'ai a zuciya, haka kawai aita shigoma mutum d'aki babu izini, wannan wane irin rayuwane. https://2gnblog.blogspot.com/ Shikam Galadima kallo d'aya yamata ya d'auke kansa, Dan daga ita sai zani d'aurin k'irji. Laptop d'in hannunsa da takardu ya ajiye a bakin gadon, sannan shima ya zauna, batare da ya kuma kalllon Munaya ba yace, “kinajin yunwa ne?”. Ba yunwar takeji ba, amma dan Neman magana kawai tace “eh”. Kallonta ya sakeyi, bata yarda sun had'a idoba, yace “Saidai kisha fresh milk kuwa, dan bani da abinci”. Manyan idanunta ta waro masa waje, kamar wadda akace tasha wuta, cikin dafe k'irji tace “yalla6ai fresh milk?”. Da mamaki ya kalleta, danshi bai fahimci ma'anar razanar tataba, yace, “uhmmm”.... “Na yafe wlhy”. Tafad'a da saurinta. “To mine nawani birkicewa haka? fresh milk d'in wani abune dashi?”. “Humm”. Munaya tafad'a tana ta6e baki, tace “yalla6ai nikam idan kaga nasha fresh milk d'in data fito daga d'akinka saidai idan bana a hayyacina”. Da tsantsar mamakin furucinta yake kallonta, da yake basuda nisa saiya mik'a hannu ya rik'o nata, zatayi magana ya fizgota ta zauna kusadashi, kad'an ya rage ta hau masa laptop, amma yay saurin janyewa da d'ayan hannunsa. “wash hannuna”. Munaya tafad'a tana matse baki. Banza yamata, yakuma matsa hannun da mugunta. tasaki k'aramar k'ara tana fad'awa gefen kafad'arsa. Ya d'an kalleta ya janye yana ta6e baki “ban fahimci zancenki daga nesa ba, maimaitamin”.. Cikin tunzuro masa baki tace, “yoni babu abinda nake nufi fa, nidai bazan sha fresh milk d'in data fito daga d'akinka ba wlhy. haka kawai aje asakama mutum abinda zai halakashi”. ‘k'asa-k'asa ta k'arasa maganar, amma yajita sarai’. Shifa saima yanzu yagane inda zancenta ya nufa, wani miskilin murmushi yasaki yana danne dariyarsa datake shirin kufcewa, amma dukda haka saida taji sautin fitar murmushin nasa. Munaya dake satar kallonsa idonta harya cika da kwalla, a zuciyarta tace mugu d'an masa, dole fa kamin dariya. Saida yayi dariyarsa a zuciya ya gama ya kalleta, itakuma saiwani mar-mar takeyi da idanu wai zatayi kuka. Murmushi ya kumayi, sannan yace, “wannan bakin dakike tunzuromin ko, hummm.....”. ‘yak'are maganar da cije lips nashi’. Yunk'urawa tayi zata mik'e, tace, “yalla6ai ni wlhy barci nakeji fa”. Dawo da ita yayi ta fad'o jikinsa shima yana fad'in “nikuma gadinki zanyi ko? yalla6iya!”. Tace “wayyo innarmu kice ya fitarmin a d'aki please”. “ko waya zan baki ki kiratane”. ‘yay maganar cikin d'age gira d'aya’. Munaya tai saurin janye idanunta daga Kansa ga k'amshin turarensa ya gallabeta, barci takeji, amma takula mugunnan soyake ya hanata ma. Kamar zatayi kuka tace, “yalla6ai wai mikazo nemane please? Wlhy barci na keson yi?”. Shiru yamata, saida ya mula dan kansa sannan yace “jikina fa”. ‘yay maganar yana kallon k'ugunta’. Da sauri Munaya ta sauka daga jikinsa tana k'unk'uni da tura baki. Medical glasses d'insa ya d'auka ya saka, tareda cigaba da aikinsa a laptop, a zuciyarsa yana fad'in yarinyarnan akwai ruwan tsiwa, amma duk randa Na kama bakin tsiwarcan sai yamin bayani dalla-dalla kuwa.