Raina kama book 1, 2, & 3 - Chapter 48
Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 48: Raina kama book 1, 2, & 3 Chapter 48. Bayan tafiyar Shazali ya kallesu yana sauke ajiyar zuciya da gyara zamansa, ya…
4,136 words
Bayan tafiyar Shazali ya kallesu yana sauke ajiyar zuciya da gyara zamansa, ya d'auki kwalin hollandia yazuba a cup, Muftahu da Nuren dai na kallonsa, saida yafara sha da kallon agogon hannunsa sannan yace, “Zanje India gobe idan ALLAH ya kaimu, akwai ayyukan dazan tattara na kwanaki uku, sannan na d'auki Hutu a wajen aiki, dukda muna shirye-shiryen fidda kaya na shekara mai zuwa, a Daren yau Harun zaisan matsayinsa, Dan tuni nagama da matsalarsa dama, wannan ranar nake jira, so Nuren ka bincikamin inda matarnan take zaune a yanzu, Dan ina dawowa zan shiga aikine sosai, matsalar Harun da ita da Sarauniya kowanne akwai manufa, su nasu wasan yarane a wajena. Erfan shine yajema Munaya a matsayin Fu'aad, yanzu na fahimci sune suka saka aka buga waccan jaridar, amma da saka hannun wasu a gefe........” Muftahu yay saurin cewa “yi hak'uri ranka ya dad'e zan katseka, sai yanzu wani Abu yazomin a rai, wato ranar salla a filin idi, kasan Erfaan yana tare damu, anya kuwa ba a wannan time d'in ya ganku kaida gimbiya ba, lokacin da kukayi karo, wata k'il shikuma yayi tunanin alak'a Ce a tsakaninku?”. Murmushi Galadima yayi yana lumshe ido, “ni kaina ina tunanin haka, saidai akwai wani Abu bayan wanna, dan haka sarakuna uku sun shigo cikin aikina”. Da mamaki Muftahu da Nuren sukace sarakuna kuma?. K'ala baice da suba ya mik'e tsaye, ya kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan ya kallesu, “gobe da safe Alhaji Shehu Darma zaije taron k'arama juna sani a jihar Katsina, lallai bana buk'atar yama k'arasa”. Kusan a tare sukace Alhaji Shehu Darma kuma?. Ficewarsa yayi batareda yabasu amsaba balle su sami k'arin bayani. baki bud'e Nuren da Muftahu suka kalli juna, Muftahu yace, “shikuma miye nasa to?”. Cikin jimami Nuren yace, “nima abinda nake son Sani kenan, mutumin da tunda mijin aunty Mimi ya rasu yake fad'i tashi a kanta da yaranta, danma tak'i amincewa ne da aurenta zaiyi, anya kuwa shi yake nufi kodai wanine mai irin sunansa?”. Jiki a sanyaye Muftahu ya yarfar da hannu alamar bai saniba shima. danshi lamarin Galadima yafara bashi tsoro, mutum kamar wani tsohon aljani.
Shikam koda yabar wajensu wani office yace Sarkin mota ya kaisa, yakai tsawon lokacin a wajen tareda wani mutum dabazai gaza shekaru 56 ba a duniya, bansan mi suka tattauna ba, dan ba'a bani damar jinba. A wajen yay sallar azhur har la'asar sannan yayo masa rakkiya wajen Motocinsa, saida yaga fitarsu sannan yakoma Office d'in.
Daga nan masarauta suka nufa, dan Galadima a matuk'ar gajiye yake, Ya iske sashensa fes an gyara, ko ina yana tashin k'amshi tamkar yadda yake buk'ata, kayansa yacire ya watso ruwa, bai nemi kowa baya ya zauna a falo yana aiki a System, dukda yaga abincin da aka ajiye masa baiko bud'eba balle tunanin cinsa, Yakuma san Aunty Mimi ce zata saka a kawo. Yana tsaka da aikin Sauban ya shigo, bai kallesaba koda ya gaidashi, yadai Amsa. Sauban yace, “yaa Sam tafiyar safe zamuyine goben?”.. Ido Galadima yad'an d'ago ya kallesa, ya maida kansa ga laptop d'in yana fad'in, “Kwana 3 zamuyi ni da kai mu dawo, komanka na gameda bautar k'asa yagama kammaluwa”. Kamar Sauban zai sanya kuka yace, “Amma Yaa Sam su Momma sai abarsu babu kowa?”. “kafin ka girma dawa suke zaune?, Sauban ka kiyayeni, karka bari na fusata akanka, tashi bani waje”. Sauban ya mik'e zuciyarsa na zafi, harzai fita Galadima yace, “zonan”. Dawowa yay yana mirgina kai, batareda Galadima ya kallesa ba yace, kar6a wannan, kaje ka sakashi jikin rigar Abdurrahman ko Amaturrahman ka d'auki Wanda ka samawa d'in kaje sashen Ummu Amaan (gimbiya Zulfa) dashi”. Sauban baice komaiba ya kar6a abinda yabashi mai kama da ma6alli ya fita, ya iske Munaya na barci, yaran kuma na tare da Khaleel dake ta fama jagwalgwalasu, Abdurrahman ya d'auka ya sakamawa ya nad'eshi a showal ya fita......
Nikam wannan gangancin na Galadima ya isheni😨🙆🏽.
Bansake jin miya faruba dan banbi Sauban ba nikam, ina tsoron ganin abinda zai hanani barci😌.
__________________________
Misalin 8:30 na dare Galadima ke shiri bayan ya dawo daga sallar isha'i, yagama tsaf cikin k'ananun kaya da jacket d'insa wadda takai masa har gwiwa, ya saka safa har a hannunsa, cikin takunnan nasa na gwarzantaka ya fito, sashen Munaya ya nufa, sukaci karo a k'ofar d'aki zata fito a rikice, sauri tareta yayi ta fad'o jikinsa saboda kad'an yarage ta fad'i, k'amshin turarensa ya sakata shaida shine, ta share hawayenta tana kallonsa a rikice, shima kallonta yakeyi, Muryarta na rawa saboda kuka tace, “yalla6ai Abdurrahman sai kuka yakeyi, jikinsa ya d'auki zafi”. Baice komaiba ya kama hannunta suka koma cikin d'akin, laraba da aunty Mimi na zaune, aunty Mimi tana zarema Abdurrahman kayan jikinsa za'a watsa masa ruwan d'umi kozaiyi shiru. Zama yayi ya kar6e sa daga hannun Aunty mimi, ya fiddo wani kwali k'arami daga aljihun jacket d'insa ya bud'e, k'aramar kwalbar dake cikeda magani ya fiddo, ya d'iba maganin cikin tsinken da ake bama yara magani ya zubama yaran a bak'i, dak'yar ya shanyeshi. Sudai sunyi jugum-jugum suna kallonsa. Yunk'urin amai da yaron keyi yasaka Galadima d'agashi daga jikinsa dan kar yay masa, baimayi amanba, hakanne yasaka Galadima sauke ajiyar zuciya ya mannashi da k'irjinsa yana hura cikin kunnen yaron a hankali. Tun yana kukan kad'an-kad'an ya koma ajiyar zuciya, sai gashi yayi barci. Kwantar dashi yayi kusada y'an uwansa ya lullu6esa. Ya kalli aunty Mimi yana mik'ewa, “insha ALLAH zai sauka zaza6in”.. Yanda Aunty Mimi kebinsa da kallon tuhuma saiya janye idonsa yakama hanyar fita, da sauri tamik'e tabi bayansa a fusace. Dan Sauban ya sanar mata Galadima ya sashi kai yaron sashen mai martaba d'azun. “Dakata Sameer”. Cak ya tsaya yanajan hular rigar bisa kansa, amma bai juyoba. “Sameer wai mike damun kankane haka? da zaka ringa wasa da rayuwar yaranka da kanka?”. Lips d'insa ya ciza, ya juyo yana kallonta, amma ita bata ganin idanunsa saboda hular ta rufe, murmushin takaici yayi, yace, “Ni ba wasa da rayuwarsu nakeba aunty Mimi, komai kikaga nayi nasan abinda nakeyi, zuwa nangaba kad'an kuma zaku fahimci komai”. “ALLAH yasa to, amma ni yanzu na zone muyi maganar komawar Munaya gida kafin mu wuce goben, tunda jirgin rana zamubi”. Agogon hannunsa ya kalla, yace, “yanzu kam inada uzirin fita?”. “fita? Inakuma zakaje a wannan daren?”. Batareda ya tanka mataba yajuya yakama hanyar fita, saida yaje bakin k'ofa sannan yace, “Farauta”. yay ficewarsa.
Kasa motsi aunty Mimi tayi a wajen, sai maimaita Sunan Galadima kawai takeyi akan la66anta.
******
Tacan baya yabi shikam, hanyar akwai k'arancin mutane sosai, yana zuwa ta wani waje yagamu da wani Wanda ke sanye da irin kayan hadiman masarautar, rissinawa yay yabashi keys d'in mota. ya kar6a batareda sunma juna maganaba ya wuce. Can sashen su Harun naga ya nufa, dukda tazarar dake tsakaninsu baiji tafiyarba, motar dake fake a wajen ya bud'e ya shiga ya zauna, zamansa da mintuna uku Harun yafito ad'an hanzarce, motar yabud'e seat d'in baya ya shiga ya zauna, cikin bada Umarni yace, lawandi muje, kasan d'an bala'innan yanada securitys dake kaimasa rahoto”. Murmuahin gefen baki Galadima yayi yatada motar yafice daga masarautar................✍🏻
“Hummmm! Reader's harna sauke numfashi, babbar magana, yau dai ga Galadima ga Harun, sauran abinda zai faru kuma sai a buk 3 na raina kama”. Miya faru da Abdurrahman lokacin da Sauban ya kaisa sashen gimbiya zulfah ne🤔? Yaya batun kama SD?, wad'anne sarakuna ne Galadima yake zargi? Kodai dama can Galadima yasan wanene Harun yabashi damane kawai?🤔, Yaya batun warkewar Abie da Auren Contract tsakanin Galadima da Munaya?, mi suke shiryawa itada Momma da suka damu da zuwanta wankan gida? Ko Galadima zai amince?”.
Yaya batun gano asalin innarsu Munaya? Da ita Munayar ta d'auki alwashi?.
Tofa wannan amsar dai duk zatazo a littafi na 3 kuma na k'arshe da izinin ubangiji, dukkan wasu tambayoyinku amsarku na cikinsa, zan had'a muku da albishirin zan dingayi a weekend rana 1, kodai asabar ko lahadi, kowacce rana nasamu dama aciki, dan buk 3 inason kammalashi ne a gaggauce saboda uzirin danake dashi insha ALLAH.
Ngd sosai da had'in kan da kuke bani, muje zuwa my guys⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀🥰🥰🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍😍😍❤❤❤.
Barkanku da juma'a🙋🏻.
Musha weekend lafiya⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼 *_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* __________________________
*_Kai jama'a yau dai kun Sani typing dole saboda munafurcin y'an bani Na iya, wannan karon kuma kurasa k'ullin da zakuyi sai akan Uwa da 'Diya?, nikam yau koda mamana (mamu gee) kwaikwayar RAINA KAMA tayi to wlhy birgeni zatayi, ai baiwace ma wani yayi Abu kabishi daki-daki kana kwaikwayo. Irin wannan shirmen naku baya cikin kan Bily, ba mamu gee ba koda watace aka jingina da hakan bazanji komaiba wlhy, sannanma nifa abinda yabani mamaki a writeup d'in da mamana tayi bata ambaci sunan RAINA KAMA ba aciki ko wani littafi daban, to tayaya y'an bani Na iya da tsugunne-tsugunne su anasu writeup d'in suka saka sunan RAINA KAMA? (Wlhy halin wasu daga cikin writers namu ko kad'an bashida k'yau, neman sunane kokuwa son asanine niban saniba🤦🏻♀)._* _Reader's kuma da naku, sometimes bakunanku basuda linzami, irin wannan abubuwan kune ke fara tsirarsu saisuzo kuma su buwayeku, Ku ke karanta RAINA KAMA DA TARAYYA Ku kusan banbancin abinda ke cikin kowanne, amma dayake Ku irin wannan dama shine farin cikinku saikuyita k'irk'irar abinda dolene daga k'arshe saiya zama rikici, to nikam zan sanar muku, awanan karon sai had'in naku baiyiba, Dan MAMU GEE DA BILYN ABDUL duk Abu d'ayane, daga tarayya har Raina kama buks d'inmu ne, mu muke rubuta abunmu, babu wata munafukar writer ko reader da mukayi shawara da ita kafin mu d'aura alk'alaminmu a takarda, masu had'a husuma kuma sai kusha fetur Ku had'iyi ashana kuyi bombing d'in kanku, ina dai shikenan ko?🙅🏻_. *Daga k'arshe inamai muku nasiha da kuji tsoron ALLAH, wlhy bashin naira 10 kacal yana hana bawa kwanciyar kabari, karo tsakanin rago da rago kawai akwai hisabi tsakaninsu, aranar kiyama bayan an tsaya hisabi duk Wanda kasani koya sanka saika Ganshi kakuma ganeshi, bawai kaitsaye za tantanceka akaika wuta ko aljanna ba, wlhy sai an tsidaka, ancire hak'in mutane a kanka, ka zagi wane babu hak'k'insa, ka harari wane, kama wane zind'e, ka cinye kud'in wane, ka had'a fad'a tsakanin wane, ka 6ata sunan wane, ka cuci makwafcin, ka...ka...ka...da yawan gaske, duk wani cin amana ko zalunci dakama wani inhar bai yafe makaba a wannan ranar sai an cire masa hak'insa a cikin ayyukanka, (Dan sune kad'ai guzirinka) komai tarin aikin alkairin daka tara inhar kanada irin wad'annan bashishshikan d'aya bayan d'aya sai an zaresu daga gareka, koda dabba da kafiri ka zalunta kuwa, idan dama bakada komai, sai ayita kwashe nasu zunubai ana lafta maka, sai angama tas, kabiya an biyaka saikuma a gwada ayyukanka a kan mizani, miyarage kuma? Saika koma gefe jiran sakamako. Wlhy y'an uwa babu babban tashin hankali irin kar6ar sakamako, a wannan lokacin uba baya gane d'ansa, y'a bata gane uwarta, miji baya gane matarsa saboda tsantsar tashin hankalin da ake ciki, da wane hannu xaka amsa, ina ne zaizama mazauni Na dindindin, duk baka saniba, haba y'ar uwata, kinada wannan babban aiki a gabanki amma kika shagala wajen had'a husuma irin ta social media wadda bansanki ba, baki sanniba, maybe ma har Abadan bazamu ta6a sanin junanmu ba, muji tsoron ALLAH wlhy, yakamata irin wannan abubuwan su tsaya hakanan, daga ni har mamana badan Neman suna mukeba, domin Isar da sak'o mukeyi a cikin tarayya da raina kama, burinmu kuma ko mutum d'aya ya amfanu da manufarmu ya wadatar, bawai tarin masu karantawa ba, ni miyasa babu Wanda yata6a tarata yacemin tarayya copy d'in raina kama ne? to Ku kama kanku please, kodan tsoron ALLAH.*
_My Sweet mah-mah mamu gee wannan page d'in sadaukarwane a gareki, kiyi yadda kikeso dashi nabaki, ALLAH yabarmu tare, I love you irin trillions d'innan, kisamun albarka nakuma zama gagara badau😁😘._
Bilyn Abdull & Mamu gee RAINA KAMA ne mu, sannan munyi TARAYYA NE akan Isar da sak'o mai muhimmanci, mabiyanmu Na gaskiya a KAFTA kawai⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀😂👍🏻.
HARUN da GALADIMA kuma Ku KAFTA naku wasan🤣🤣🤣🤸🏻♀🤸🏻♀✍🏻😜. __________________________
~Book 3~ 👉🏻1⃣➖2⃣
...............Saida suka fara tafiya sai Harun yafara jin tamkar k'amshin turaren Galadima yakeji, mamaki ya kamasa, ya kalli gaban motar yana fad'in “lawwali nikam kaji minakeji kuwa? k'amshin Sameer fa”. Murmushi Galadima yayi, baice komaiba sai “Uhmm”. Hakan yakuma d'aure kan Harun, kamar zai sake magana saiya fasa, ya d'auki wayarsa domin son kira yaji ina Galadima, yasan Abu dolene ke fiddashi da daddare daga masarauta, amma sai kira ya shigo a wayarsa, k'aramin tsaki yayi Dan ba'a ko'ina yake d'aga wayaba, ya yarda da lawwali drivern babansa waziri amma bakomai yake barin ya saniba, ganinfa an damesa da kiran saiya d'aga. Da sauri ya janye wayar a kunnensa yana lek'o kansa gaban motar danya tabbatar. shin ina tunaninsa ya tafi dahar ya iya gaza banbance lawwali da Sameer?. yace “Sameer!”. Galadima dake tuk'insa hankali kwance yana kuma sauraren wayar Harun ta abinda yasa akunne, saboda ya saita duk wayar dazata shiga ta Fita a war Harun saiya shigo wayarsa shima kota fita yace, “Uhmyim”. A tsorace Harun yakoma baya ya bigi seat da k'arfi, babu abinda zuciyarsa keyi sai dukan 100-100, wayarsa ya jawo jiki Na rawa yafara k'ok'arin kiran wani. Galadima yay murmushi, cike da izzar k'asaita yace, “bar wahal da kanka my dear friend, duk wata waya dazaka kira a yanzu wayata zata shiga”. Harun yay jifa da wayarsa a kujera jiki yana rawa, batare da wani tunaniba ya mik'e kawai ya shak'e Galadima, da hannu d'aya Galadima yake driving, hannu d'aya kuma yana k'ok'arin kare kansa daga shak'ar da Harun ya masa. Da k'yar yasamu ya gangara gefen titi, yasaka hannunsa d'aya ya bigi gefen cikin Harun daya samu damar shak'esa da k'yau, Dan numfashin sa harya fara fita afisge. Dukan cikinsa da Galadima yayi yasakashi sakinsa da sauri, Galadima ya juya yakuma naushin bakin Harun saiga jini, dama bai gama dawowa hayyacinsa ba daga dukan cikinsa da yayi. Harun ya fad'a saman kujera yana rik'e ciki da shafar hancinsa dayaji yana yoyo, kallon hannunsa yayi saiyaga jini, ya zaro ido cikin matuk'ar mamakin shi Sameer ya fasama baki, yo ko danbe zasuyi ai babu abin zai d'auka a jikinsa, (Dan shima Harun d'infa ba bayaba). Galadima daketa huci ya dafe sitiyari da kife kansa ya kuma tada motar a harzuk'e ya fara tafiya cikin tsananin gudu. Cikin hakki da fidda numfashi a wahalce Harun yace “Sameer n..n..ni ka daka? harda fidda jini?”. Banza Galadima yamasa yacigaba da tuk'insa, Harun ya kuma yunk'urawa zai tashi amma saiya kasa, saboda ba k'aramin duka Galadima ya masa a gefen cikiba, wajen ya k'ulle, dole ya koma ya kwanta yana cije baki da matse ido, hannunsa rik'e da wajen har yanzu.
Suna isa inda ya nufa yay horn, saiga Nuren da kansa yazo ya bud'e masa k'ofa, a fusace ya shiga gidan, shi Nuren ma har yana tsorata. Yana tsaida motar ko kashewa baiyiba yabud'e ya fito a harzuk'e, inda Harun yake ya bud'e ya jawoshi, yakuma kai masa naushi, shima ya kai masa dukda azabarda cikinsa ke masa. Nuren da Muftahu sun iso wajen a hanzarce, Dan ganin danbe Na Neman hark'ewa tsakanin aminai guda biyu, Nuren yaja Harun, shikuma Muftahu Galadima. “Waishin mikukeyi ne haka brother? Da girmanku da ajinku kuke danbe? danbe fa? Wannan wane irin kuma abin kunyane? Lallai da y'an jarida zasu samu labari gobe dasunci kasuwa sosai.....” Hankad'a Muftahu Galadima yayi baya, yay taga-taga zai fad'i, bai kuma kallon ko wanne a cikinsuba ya nuna Harun da d'an yatsa, “Mara kwakwalwa kawai, kafin ni ka kasheni ninan zan kasheka daga kai har munafikin ubanka, dak'ik'i kawai”. yana gama fad'ar haka yabar wajen zuwa cikin gida, taku yake kamar wani bajimi ya fito za6en sarauniyar k'yau. Daga Nuren har Muftahu da kallon mamaki suka bisa, shi kansa Harun maganar Galadima tasakashi girgiza, kardai guy d'innan yana sane da wanene ni tun tuni amma ya k'yaleni? da k'arfi ya fisge shima daga jikin Nuren yana kaima Muftahu duka, “Munafiki dakai zan fara”. Saurin kare kansa Muftahu yayi, Nuren yakuma yunk'urin rik'e Harun, danshifa abin yafara d'aure kansa, kowa yasan Harun aminin Galadima ne Na kusa, yau kuma miya had'osu haka? harda zancen kisa? Galadima yanada matuk'ar zuciya, idan ransa ya 6aci babu ubanda ke gane kansa.... Fad'a dai Neman komawa yay ga Muftahu, saida su Ameer sukazo suka rirrik'e Harun, cak suka d'aukesa yana fisge-fisge da fad'ama Muftahu magana suka shiga dashi ciki. Nuren ya kalli Muftahu dake murmushi yana gyaran kwalar rigarsa. “Amma mike faruwa kuma haka? Yau Sameer ne ke fad'a da Harun?”. Muftahu ya dafa kafad'ar Nuren, “'Dan uwa akwai abinda baka Sani bane, amma Na tabbatar yanzu zama sanshi”. Yana gama fad'ar haka yayi gaba abinsa, shima da kallon Nuren ya bisa, kenan shima yasan dalilin fad'an nasu ashe? jiki a sanyaye ya nufi wajen motar ya kashe sannan ya nufi gidan shima, a yanzu kam lamarin wanan case yafara rud'ar dashi, dan yanda Sameer keta abubuwa a tsakaninnan basuyi kama da nasa zarginba shi. Galadima Na kwance cikin kujera doguwa, tunda ya shigo anan yazufe, duk yanda zuciyarsa taso 6aci sai kalaman Munaya su danne su (mata kunga amfanin hikimar zance ga mazajenmu ko), zantuttukanta suka shiga dawo masa a rai daki-daki, tabbas a yanzu ba fushinsa bane abin buk'ata, jarumtar hak'uri ce, kamar yanda ta fad'a idan kwallo ta 6ata ba daina wasa akeyiba, wata kwallon ake d'auka ayi da ita, cikin lumshe ido ya ciji lips nashi yana wani miskilin murmushi. Daga Muftahu har Nuren dai ido suka zuba masa, ga Harun da aka saka a wani d'aki aka kulle sai bugun k'ofa yake yana fad'ar magana masu zafi akan Galadima. Mik'ewa Galadima yayi yana gyara rigarsa, ya kalli su Muftahu yana cire safar hannunsa, “bara naje gida”. Abinda kawai ya fad'a kenan yay ficewarsa. Tamkar sokaye haka suka bishi da kallo, yana fitowa ya iske sarkin mota a waje yana jiransa (Ashe dama ya biyo bayansu) da hanzari ya bud'e masa motar ya shiga, Galadima ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a cikin kujera. Har suka Isa masarauta babu Wanda ya iya tankawa. Sarkin mota nayin parking baima jira an bud'e masaba ya bud'e da kansa ya fice, hadimai masu tsaron sashen Na masa barka da zuwa amma ko kallo basu isheshiba. Kai tsaye sashen Munaya ya nufa, babuko sallama balle Neman iso ya danna kai cikin d'akin. Laraba da samba da yara duk sunyi barci, Munaya kam takasa hakan, sai safa da marwa takeyi tun d'azun, taje d'akin Galadima yafi sau 7 amma bai dawoba, hankalinta a tashe yake da tunanin ina yaje a darennan? shida idon mak'iya kullum a kansa yake, dama kad'an suke nema ta cuta masa?..... Cak tunaninta ya tsaya lokacin da taji anyi sama da ita, zata fasa ihu yace, “yima mutane shiru”. A hankali yayi maganar, Dan haka ta had'iye ihunta cikin sauri da mamakin abinda yayi, yana fitowa falonta ya ajiyeta yaja hannunta zuwa sashensa. Babu abinda zuciyarta takeyi sai dukan 50-50, miye yashiga kansa haka wai?. Basu tsaya a falo ba sai bedroom d'insa, dama tun a hanya ya fara cire jacket d'insa, suna shigowa yana ida cirewar, yay wurgi da ita a tsakar d'akin yakuma d'aukar Munaya suka fad'a saman gado. Tsoronsa yakuma shigarta lokacin dataji ya sakata jikinsa ya matseta, kaikace zai maidata a cikine. Cikin matse baki da sakin k'aramar k'ara tace, “wai minene haka yalla6ai?”. “shiiii!!”. Yafad'a yana d'ora yatsansa d'aya akan bakinta, batada za6in daya wuce tayi shirun, sai zuciyarsa dake wani irin bugu da k'arfi, hannunta ta saka a saitin zuciyar tana karanto addu'a. Duk abinda takeyi yana jinta, hawaye masu zafi suna kwarara masa a ido, saidai tacan gefene shiyyasa Munaya bata saniba, tsawon lokaci muna a haka, har zuciyarsa tafara dai-daita bugawa, takoma normal, sai ajiyar zuciya da k'ok'arin dai-daitar numfashi kawai yakeyi, a haka barci ya kwasheshi, saida nabari barcin yayi nisa sannan nazare jikinna cikin dabara da k'yar nabarshi, Dan Dana motsa saiya k'ara k'ank'ameni, da k'yar dai Na kwaci kaina Na maye masa gurbina da filo, cikeda tausayawa nake kallonsa ina hawaye, a haka Na cire masa takalman k'afarsa, naja bargo Na lullu6a masa, addu'ar barci nayi Na tofa masa, gudun karna ta6ashi ya farka na tofa d'in, Na kashe wutar d'akin nabar da barci kawai na fice ina share sauran kwalla. 'Dakin da Sauban yake kwance na kwankwasa, yataso cikin mayen barci ya bud'e, ganina yasashi watstsakewa babu shiri, “Aunty gimbiya lafiya kuwa?”. “lafiya lau Yaa Sauban, cazan dama kaje d'akin Abban su Amaturrahman ka kwanta tare dashi, naga kamar bayajin dad'i, ba'asan mi dare zaiyiba”. Kansa ya jinjina yace, “to aunty”. https://2gnblog.blogspot.com/
Tunda na koma d'aki sai damuwa ta katantaneni, na dad'e ban barciba, daga k'arshema saida na saka karatun Qur'an da k'ara kad'an sannan barci ya saceni batare da na shiryaba.
https://2gnblog.blogspot.com/ *_Washe gari_*
Tunda asuba kasa hak'uri nayi na nufi d'akinsa. Mamaki da kunya suka kamani, Dan ganinsa ragal ya fito wanka, gashi d'aure yake da towel, Sauban yafita saishi kad'ai. Da sauri na juya da nufin komawa amma sai naji an rik'o hannuna, kasa juyawa nayi, yamatso dani ya saka a jikinsa, laimar ruwan da k'amshin sabulun sai suka sakani lumshe ido, ya d'ora hannunsa d'aya bisa cikina ya rik'e hannuna da d'aya, kansa a dokin wuyana yace, “Thanks matar Contract”. Kamar bazanyi magana ba sai dai nayi, Dan karna barta ta kasheni, nace, “Tausayinsu Abie ya sakani, kaji mijin Contract”. Murmushi yayi mai sauti yana shinshinar dokin wuyana, hannu na saka na ture kansa ina fad'in “ka dinga kula fa”. Ya kuma maida hancinsa a wajen, cikin tura hannunsa a rigata yace, “Nida sadakina gwaggo tsiwa”. Ban tanka masaba na fisge jikina, shima saiya barni yana wani bina da ido cikin k'ank'ancesu da miskilin murmushi. Saida naje bakin k'ofa na tsinkayi muryarsa yana fad'in “Kinzo kawai kin karyamin alwala”. Babu shiri na juya Na kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayi maganarba, yama juya ya nufi hanyar bathroom. Kwafa nayi na ida ficewa.
Bayan Galadima yakuma d'auro alwala ya fito saiya iske tea a mug da da cake a k'aramin bowl, ya d'anyi luuu da ido tamkar zai lumshe saikuma ya bud'e yana murmushi da shafar kansa. jallabiya ya saka yay salla a d'aki, bayan ya idar yazauna yasha tea d'in, dama jiya baici komaiba ya fita, yunwa yakeji, koda ya kammala saiya fice abinsa. Sashen mai martaba ya nufa hadimai nata zubewa suna kwasar gaisuwa, sukan samu amsa iya kan la66a da d'aga hannu, da haka harya Isa. Saida jakadiya tamasa iso sannan ya shiga, a k'aramin falon mai martaba dayake hutawa idan baya buk'atar ganin kowa har matarsa ya iskeshi, yayi mamaki kwarai, dan inhar mai martaba ya shiga falonnan kofa mama Fulani sai dai tayi hak'uri da ganinsa. Yana kishingid'e saman tattausar darduma da aka k'awata da kilisa ta asalin sarakuna masuji da tsantsar mulki, ga tumtum da sauran kayan k'awa, an saka na'urar dake d'umama d'aki kad'an saboda yanayin sanyin safiya musamman na wannan lokacin da bazara take kunno kai. Da hannu mai martaba yayma Galadima nuni da kusa dashi, Galadima yaje ya zauna yana tankwashe kafafu, cikin girmamawa ya risinar da kai yana fad'in “barka da asuba Abba”. Mai martaba ya jinjina kai yana lumshe ido da amsa cikin fad'in, “barka dai yarona, ina d'iya ta da abokaina da amarya?”. Murmushi Galadima yayi, kansa a k'asa yace, “duk suna lafiya Abba”. “Masha ALLAH, yaya jikin naka to?”. “Na warke ai Ranka ya dad'e”. “To Alhmdllh, haka akeso ai, Yaya maganar tafiyar ita mai d'akin naka? duk da dai abin yazo da tsoratarwa yakamata a ayi yanda kowa yakeyi Sameer, ALLAH shine mai tsarewa, kuma zai tsaresu, domin ransu a hannunsa yake, idan an hanata zuwa an tauye hak'inta, zakuma ta iya ganin hakan kamar ita danba wata baceba, nagama shirya komai yau za'amata rakkiya kamar yadda akema kowacce mace dake aure a masarautarnan”. Cikin had'iye yawu da wani Abu daya tokare mak'oahinsa yace, “to Abba, ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, nima zuwa yamma zan koma India, akwai abubuwan da zanyi na kwanaki biyu zuwa uku zan dawo”. Mai martaba yay murmushinsu irin na manya, cikin jinjina kai ya ajiye k'aramin mug d'in hannunsa mai k'yau yana fad'in “ALLAH ya taimaka, Maybe kana dawowa nima zanje insha ALLAH”. Galadima yace, “ALLAH ya kaimu”. Daga nan sund'an cigaba da ta6a hira, a haka jakadiya ta shigo nemawa matawalle iso, yabada izinin a shigo dashi. bayan shigowarsa da yin gaisuwa sai suka d'ora hirar su uku gwanin sha'awa da birgewa. da Wanbai yazo gaida Sarki jakadiya ta sanar masa ai Galadima da matawalle suna ciki, shi komawa yay wai yafasa gaisuwar, jakadiya ta ta6e baki tana 6azgar goro da fad'in “kaikuma kasani gwandararren banza, kai koma y'ar k'autarnan ta jinin girma ba iyawa kaiba, dakasha kanu da sirrika a wajena wlhy”. duk a hankali take maganar yanda kowa bazai jitaba🤣.