Kenza eBookz

Raina kama book 1 complete - Chapter 1

Raina kama book 1 complete - Chapter 1

Raina kama book 1 complete Chapter 1: Raina kama book 1 complete Chapter 1. [4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*

4,425 words

[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*

*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*

*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._*

👉🏻1�?

*Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe, daga matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga tsatso d'aya muka fitoba. Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad'in “kai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za'ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?�?. gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje nace, “ashema mu akanmu fitinar take yau?�?. yink'urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad'a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk'oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce. “wlhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar iskar mata zama agidannan dan kutu..... Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta. Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu. Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta sukaji. Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da mamarsu sukayo kaina danufin duka.... Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k'afafu danufin barin wajen. A tsawace yace, “kar wadda tabar wajen!!�?. Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi bane d'azun ya cakud'e da hayaniya tamkar ana biki ko suna. Jarabar gidanmu ba bak'on Abu bane a anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu take (yo ajininmu mana zance) tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan kokuma mu 'ya'yan gidan. Babu mai d'agama wani k'afa koda na second d'ayane kuwa, yanzun zakaji gidan shiru, anjima k'ad'an kaji an doka gangar shaid'an, musamman ma fad'an yara dayafi komai saurin had'a fad'an matan gidan da a kulum, a rana sai ayi fad'a biyar akan yara kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda k'ok'arin K'aucewa irin wannan fitintunun dasuka zama tamkar shan ruwa acikin gidanmu. Baba k'arami yafara fad'a tamkar zai ari baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa yayi tsit yana saurarensa, (saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan yajuya yafita yana fad'in nida Safara'u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.

Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana had'a Karin kumallon safe, kuma kalma d'aya bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.

A falon baba jafaru yanemi jin ba'asin tushen fitinar, cikin d'aga muryar da hargowa maman Safara'u tafara fad'in “Alhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama sauran matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye ubana ehe, kum....... Hannu yay saurin d'aga mata, “kinga Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba, sonake naji minene ya kawo hayaniyar?�?. Cikin jin haushin an tareta tace, “Alhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen Safara'u yake zuwa a unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake ALLAH yatashi tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d'an Aiken ya kwatsa maganar a tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d'in Safara'u baneba, goshin magriba saiga Safara'u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya da k'yar tacemin cikinsu 'yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu suna hira da dariya, kuma hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta na sake aiken Rahma taganomin da idonta, harma taji Sadeeq d'in nafad'in ai koma miza'ayi bazai auri Safara'u ba, cikin wad'an nan munafukan yaran daba ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d'inne maganar a raina har safiyar yau d'inan, amma wlhy Alhaji da k'yar na iya barci nida Safara'u jiya.

“hummm�? kawai nafad'a ina dafe kaina, saboda jin Yanda aka canja maganar.

Babak'arami ya kalleni yace, “Munubiya ce ko Munaya?�? (dan basa ganemu saboda tsananin kamata da hassana ta). Zuciyata cikeda bak'in ciki nace, “Baba Munaya ce�?. “yauwa Munaya, ina 'yar uwarki?�?. “Tana ciki baba�?. Baba ya kalli Safara'u daketa matse kwallan munafurci tun d'azun yace, “k! Safara'u tashi kiramin Munubiya �?. Batareda ta amsaba tatashi tafita, mintuna kad'an saigata sun dawo tareda Munubiya datasha kuka idanu sukayi luhu-luhu. tsaki naja a raina ina hararta ta gefen ido, rashin jarumtar ta na bani haushi, ta cika hak'uri da sanyin hali tamkar innarmu....... Maganar baba ce tadawo dani daga tunanin dana tafi. nad'ago ina kallonsa saboda kiran sunana dayayi, muryar a dake na amsa da “na'am baba�?. kallonsa ya maida kan Safara'u yana fad'in “wacece acikinsu kika gani tareda Saddik'un?�?. Binmu da kallo Safara'u tayi, cikin matse kwalla tace, “baba niba ganesu nakeba, sai sun banbanta min Kansu sannan�?. Baice komaiba dan shima yasan da hakan, (ta hallaya ne kawai kowa ke banbantamu agidan, hatta da innarmu kuwa). Baba yabimu da kallo alamar son sanin wacece acikinmu. Da sauri Munubiya tace, “baba nice�?. Nima na kar6e da fad'in “baba k'arya takeyi nice jiya Sadeeq ya aiko kira, kuma babu wata alak'a dake tsakaninmu, hasalima ya kirani ne akan Safara'un, sune dai suka maida zancen haka�?. Daga Safara'u har mamanta harara suka ballamin, babu ragi nima na rama kuwa. Baba ne yakatsemu da fad'in “miya faru to Munaya?�?. Janye idona nayi daga Kansu na maida gareshi, kaina ak'asa Nace, “baba ya kirani ne yana tambayata minene abinda Safara'u tafiso a rayuwarta, dan yanason yabata gift na birthday d'inta, kuma soyake yayi mata bazata. shinefa nake lissafa masa muna dariya saboda ina cewa ya had'o mata da gyad'a soyayya dan ita mayyarta ce, a dai-dai lokacinne kuma na hangota zata shigo gida, nifa dama tsokana namata gwalon, Ashe ita ta d'aukeshi wani Abu. Kuma wlhy Rahma k'arya takeyi, lokacin data fito tareda yaa Hameed ta ganni yana bani kayansa nakai masa ciki shi zai shiga masallaci salla. Wannan shinefa abinda yafaru, shine suke cewa nakwace mata Sadeeq, har ana cin zarafin innarmu da farar safiyar nan�?.

Ajiyar zuciya innarmu ta sauke a hankali, taji dad'i daba abinda suke zargin baneba. Wata uwar harara baba jafaru ya watsama maman Safara'u, “kai Suwaiba kedai ALLAH ya gyaraki, dan ALLAH kuringa bincike akan Abu idan yara sun fad'a muku, tokinji dai abinda yafaru, kekuma Safara'u dayake bakida tarbiyya har bakinki yana iyama Ai'sha rashin kunya ko, ki tabbatar saina saka Abdulhameed yacimin ubanku keda Rahama yau a gidannan. Ai'sha kiyi hak'uri dan ALLAH �?. Innarmu ta yink'ura zata mik'e tana fad'in babu komai babansu, ALLAH ya kauda fitinar gaba�?. “Amin�? muka fad'a muma muna mik'ewa mukabi innarmu a baya.

Koda muka fito, sai matan gidan suka zubo mana ido suna kallo tamkar yau suka fara ganinmu, a raina nace munafukai, haka zaku k'are.

Ran innarmu ya6aci matuk'a a wannan karon, amma kasancewarta mutum mai hak'uri da shanye damuwa sai bata nunaba. Nida Munubiya kam kasa shanye 6acin ranmu mukayi, munsan koma wace irin wulak'antawa za ai mana agidan *KAKARMU* ce taja mana, itace tabada kowacce iriyar k'ofar tozartamu, idan kaga abubuwan da ake mana saika d'auka ba jinin gidan baneba, tunda muka taso a haka muka tsinci kanmu, hakama mahaifiyarmu a wannan halin muka risketa tana fuskantar k'ask'anci da wulak'anci daga Kakarmu da matan Abban mu, harma da matan k'annensa, bamuda 'yanci irin na 'ya'ya, mahaifiyarmu batada kima irinta matar gida (Uwargida), hakan yasamo asaline dalilin................✍�?

👎🏻

Tofa masu karatu dalilin mi? Dani daku duk muna buk'atar jin wannan dalili a bakin MUNAYA!, saiku kasance dani danjin Yanda wannan labari mai d'unbin harmutsi da tsalle-tsalle zai kaya, miye manufarsa? ina kuma ya dosa?.

Amsa d'aya zan iya baku.👇🏻

*_LABARIN MAI TSAWONE_*

saikun kasance dani a hankali zancigaba da warware muku lauje cikin nad'i. ALLAH yasa zaku bani had'in kai, tabbatarwata shine yanda zaku kar6i wannan labarin.

Dan haka kumuje zuwa🥺✍🏼✍🏼

Zamu cigaba Monday insha ALLAH, wannan d'and'anone.

Sannan wannan karon zandinga typing ne Monday to Friday kawai insha ALLAH, kunga banda weekend kenan😊.

One luv🥰

*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu😭👏🏻._* [4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*

*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*

*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

👉🏻3�?

.........Fad'a sosai innarmu tamin akan Marin Safara'u danayi, sannan ta d'ora da nasiha kamar yanda tasaba, wani kam yashiga kunnena, wani kuwa tabaya yabi, dan harga ALLAH Na daina zama kowa yana taka mana mahaifiya a gidan. Innarmu tace, “ku shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Ku tafi gidan mamanku Rabi'a Ku k'arasa hutunku, banason zamanku a gidan nan tunda fitina yake kawowa�?. A sanyaye Munubiya ta amsa da “to innarmu�?. Amma ni saina tunzuro baki gaba ina k'unk'uni, dan banason tafiya ko ina, canma saboda d'an mama Rabi'a d'inne Marwan, ko kad'an bama shiri dashi, saboda masifarsa. “kai innarmu, yanzu dan ALLAH saboda wasu can bazamu mik'e kafa yanda mukeso ba agidanmu, duka fa hutun sati biyu ne kacal, amma saimunje wani waje?, ni wlhy inkika barni babu mai k'ara mana koda kallon banza a gidannan, harma innaro bazan bartaba.........�? Maficin danaga innarmu tajawo yasani tashi da sauri nabar gurin, Na tabbata shirin bugamin takeyi. Munubiya ta saka dariya tana kallona, “ke ga rashin arzik'i ga tsoron tsiya, dukan maficin kikema wannan gudun?�?. Harara Na balla mata, “yo k'ya fad'i haka mana tunda ba jikinki baneba, tsoro kam kinsan waye matsoraci acikinmu ai�?. Munubiya ta ta6e baki “naji dai, koma mizaki ce kije kiyita cewa, inama kayana dakika saka jiya? na wanke, dan dasu zanje�?. Wayar innarmu Na d'auka ina dannawa, batareda na bata amsaba Na nuna mata laundry basket d'inmu. Innarmu tace, “to Aljanar waya ajiyemin kafin ki k'ararmin kud'in ciki, ina taki?�?. “kai innarmu, please mana, zan kira Ayusher nefa nasanar mata muna zuwa gobe, ALLAH wayata babu ko nera aciki Munu ta cinye min jiya�?. “kiji tsoron ALLAH munaya, Nina cinye mini kud'in waya? bake kika kira Balkisu ba da kanki?�?. “to dana kirata sai nace kuyita surutu har kud'ina ya k'are�? innarmu Na shirin yin magana muka jiyo kururuwar kukan Safara'u da Rahama. dariya Na k'yalk'yale da ita, ina fad'in “o, ALLAH ga yaa hameed can yana gwajin kwanji a jikin gayu�?. Harara innarmu ta ballamin, saikuma tamik'e tana shirin fita, nasan kar6arsu zataje, nai saurin fad'in “kai innarmu, kid'an barsu su lallasu mana�?. Dakk'uwa ta watsomin tareda fad'in “K'aniyarki Munaya�?. Dagani har Munubiya dariya muka sanya harda tafawa kuwa.

Ba'a rufa mintuna 3 da fitar innarmu ba muka fara jiyo hargowar Maman safara'u (dama ita bata magana a hankali) Yaa hameed takema masifa akan dukansu safara'u dayakeyi, maman su yaa hameed babu hak'uri, itama tafito suka fara cacar baki, yaa hameed kam ficewarsa yayi bayan innarmu ta kwaci su Rahama a hannunsa da k'yar. kafin kace mi gidan yakuma kaurewa. Munubiya tace, “kai jama'a ko breakfast ba'ayi agidanba har antafi wrestling zagaye na biyu�?. Na fad'a saman gado ina Dariya, danni mamaki 'yan gidanmu nakeyi da bala'insu. wayar Innarmu tayi ringing, da Sauri Na duba sainaga Abbanmu ne, cikeda d'oki Na amsa tareda masa sallama sannan Na gaidashi. Yace, “Munubiya ina maman takune?�?. “Abba ba munu bace, nicefa�?. “to to munaya ce? hayaniyar mi nakeji haka agidanne Munaya?�?. K'yafta min ido da zungurina Munubiya tashiga yi wai karna fad'a masa (dayake a Hans free nasaka wayar, tana jin komai) amma saina harareta da murgud'a baki nace, “Abba Mama Ce da maman safara'u suke fad'a�?. Tsaki yaja da fad'in “ALLAH ya shiryesu to, ina maman taku ne?�?. “Amin Abba, Innarmu tana can wajen rabon fad'an ai�?. “shike Nan, idan tashigo kice takirani muyi magana�?. “to Abba bye�?. Yace, “ok dear bye�?. Sannan ya yanke wayar. Ina yanke wayar Munubiya ta kaimin bugu, Na kauce ina dariya “yo da bakina a hanani fad'ar gaskiya�?. “ba hanaki akayiba, amma kinsan idan Allura ta tono garma mune tushen fad'an ai, kinkuma san halin Abba da d'aukar zafi kamar baba k'arami�?. “tab, ta k'are musu dai suda suka takalo wlhy, jarababbu dangin masifa�?. “kina ciki kenan tunda kema dangin kine ai�?. Dariya muka Sanya nida munubiya.

*washe gari*

Tafiyar mu gidan mama Rabi bai yuwuba, saboda dawowar Abbanmu, da innarmu ta sanar masa a waya zamuje can muk'arasa Hutu sai yace a'a muyi hak'uri mu zauna, Dan akwai bak'in da zaiyi a k'arshen sati (weekend), kuma yanason dukkan yaran mukasance muna nan. Innarmu tace shikenan. Wannan dalilinne ya hanamu tafiya Hutu, dama ni ba so nakeba, Munubiya ce keta zakwad'in tafiyar.

Yau ta kasance alhamis, tunda safe muka tashi da himmar wanki nida Munubiya, ina sharar sashenmu Munubiya na fidda kayan wankin, yayinda Aryan da Aiyan keta tara mana ruwa daga fanfo zuwa banbu. Ina gama sharar na wanke hannuna na k'arasa bakin fanfo inda Munubiya ke k'ok'arin jik'a kayan. zama nayi bisa d'an dakali da akayi wajen saboda irin hakan, wanki ko wanke-wanke da sauransu, waya nake latsawa ina nemo mana wak'a, dan muji dad'in wankin, maganar aunty khaleesa kawai mukji a kanmu tana fad'in, “k! Munaya tashi kije ki gyaramin d'akinmu, akwai wani zanina nan ki d'akkosa ku wankemin�?. Banza namata ban d'agoba, sai Munubiya ce tace, “to aunty khaleesa�?. Shirun danayi ina kuma tamke fuska yasata gane nice munaya, Dan haka ta kalli Munubiya dahar tatafi, “k Munubiya!... dawo, bakece zakiyiba, k! Dan uwarku Munaya tashi kije kimin�?. Da sauri Munubiya tace, "Aunty khaleesa ai nice munaya, waccan Munubiya ce�?. Hararta tayi, “mai dani 'yar iska to, ko kina tunanin ban ganeku nima d'in?�?. Banyi niyyar d'agowa ba, amma jin abinda tafad'a yasani sakin guntun murmushi, nasan k'arya takeyi tace tana ganemu kai tsaye, yanzu ma dan kawai na nunu halin nawane shiyyasa tagane nice, kawai tafad'ane dai, mai da kaina nayi nacigaba da abinda nakeyi....... Wata ashar ta lailayo ta makamin, tareda zaburowa tamkar zata dakeni, dai dai nan sallamar innaro ta karad'e tsakar gidan. mu duka kallonta mukayi, nikam kallo d'aya namata na d'auke kaina, (dan nikam natsani kakarnan tamu) Munubiya da aunty khaleesa suka gaidata, nikam a d'age nace “ina kwana�?. “kin yima uwarki Ai'sha dan Ubanki�?, cewar innaro ta na nunani da d'anyatsanta manuniya👉🏻, tacigaba da fad'in “ni zakima gaisuwa a haka? kamar wata sa'ar uwarki?, aiko Aisha da ubanki basu isa sumin gaisuwa hakaba balle ke haihuwar yanzun�?. Baki na la6e, ba tareda na kalleta ba natashi nahau wankin, Munubiya kuma tawuce danta gyarama su aunty khaleesa d'akinsu. abinda nayi na nuna halin ko in kula saiya kuma tunzura innaro, ta fara hayagaga da matse kwalla wai naci zarafinta. Wannan yasaka matan gidanmu da yara fara fitowa d'ai-d'ai suna kallonmu (dan al'adar gidanmu ce hakan, da anji kaya-kaya kowa zaiyo waje yaganema idonsa abinda ke faruwa). Dady ya k'araso da sauri yana fad'in “Inna miya farune haka da kuka? Keda waye?�?. “wannan shed'aniyar yarinyar mana�? tayi maganar tana nunani “waini yarinyar nan zataima d'ibar albarka saboda uwarsu kullum tana aibantani a gurinsu, shiyyasa duk sun rainani....�? Baki bud'e nake kallon innaro da sherinta. wlhy wannan tsohuwar bazataga Annabi ba........ Maganar Dady ta dawo dani daga mamakin innaro. Yace, “Munaya ce ko Munubiya? miya farune keda inna?�?. Dady yanada sauk'i, ba kamar Abbanmu da baba k'arami ba sun fishi zafi. Nace, “dady Munaya ce. wlhy babu abinda namata, kawaifa daga shigowarta duk muka gaidata, shine kawai ta hau zagina wai ban gaidata da k'yauba.......�? “amma ai gaisuwar rashin tarbiya kikai mata�?. ‘cewar Aunty khaleesa�?. Dady zaiyi magana Aunty Ramlah tace, “wlhy Dady ba haka bane, duk abinda yafaru akan idona yafaru, dan nafito zan d'iba ruwa a fanfo�?. Dakuwa Innaro ta mata, “kinci uwarki hadiza, kema ashe munafukace ban saniba, to ko hadizar ta haifama Ai'sha ne ke?�?. Fakar idon Dady aunty Ramlah tayi ta dallama innaro harara, sannan tace, “yo daga fad'ar gaskiya, nidai wlhy Dady abinda nagani nakuma ji kenan�?. Girgiza kai Dady yayi, sannan yace, “kiyi hak'uri Inna, Munaya tayi kuskure amma bazata sakeba. Munaya zoki bata hak'uri�?. Ban musaba nazo har gabanta nace tayi hak'uri, bata amsamin ba, saima hararata datayi kawai. nima saina bar wajen nakoma kan wankina. Dady Yakama hannun innaro suka shiga falonsa, matan gidanmu duk suka bar wajen, basuso wasan yak'are a nanba, sunso ace cin mutuncin innaro yasauka har kan innarmu. Innarmu dake tsaye daga k'ofar falonta tanajiyo abinda ke faruwa dukda katanga ta shiga tsakiya, ta girgiza kai kawai tana komawa ciki da fad'in ALLAH ya k'yauta.

Ina wanki ina zubda hawaye, sosai raina ya sosu yau akan abinda Innaro tamin, dukda bawai yaune karon farko da hakan ya faruba, sai dai na yau yamin zafi ainun, har inaji natsani zaman gidanmu, a fili na furta ALLAH kabamu miji muyi aurenmu mubar gidannan�?. Munubiya dabansan tazo wajenba naji ta amsa da Amin sweetheart, wlhy koni yanzu addu'ar danake mana kenan, sai dai banason mutafi mubar innarmu a wannan halin dasu Aryaan�?. “hakane Munu..., karki damu, insha ALLAH munayin aure d'auke innarmu zamuyi ko Abbah ya yarda kobai yardaba wlhy!!�?. ‘ta k'arashe maganar a harzuk'e�?. Murmushi Munubiya tayi, dan tasan ran 'yar uwar tata yakai k'ololuwar 6aci. Har muka gama wankin innaro na gidan bata tafiba, bamusan uwarmi takeyiba. dayake girkin gwaggon Haleema nema ranar. ina tsaye a bayan flowers d'in d'akinmu ina goge glass d'in windows naga Abdul yafito d'aukeda tire an jera sabbin kuloli akai, nasan Abbanmu baya gari, dan haka nace, “Abdul wazaka kaima abinci haka?�?. Yace, “Aunty zan kaima innaro tana falon dady�?. Kai na jinjina masa kawai nace jeka, cigaba nayi da aikina ina fad'in “shidai munafurci ai dodone, maishi yakeci�?. Koda na koma ciki sai nake bama Munubiya labari, innarmu dake bayanmu bamu saniba tace, “to ina ruwankine wai Munaya?, nifa banason gutsiri tsoma wlhy, wai sai yaushene zaku daina jamin fitina a gidanan ne?�?. A sanyaye mukace kiyi hak'uri innarmu�?. Batace komaiba tashige d'akinta, muduka da kallon tausayi muka bita, dukda tasan ita ake tauyema hak'i amma bata ta6a nuna itace mara laifi, kullum ta amince itace a k'asan kamar yanda kowa ke kallonta agidan.

★★★★�?

Washe gari Abbah yadawo da yamma, duk munyi murnar ganinsa, shima kuma hakan take a garesa. Sai da daddare suka tara iyayenmu mata meeting shida Dady da baba k'arami. Abbanmu yay gyaran murya sannan yace, “dama wani abune yasaka muka taraku, maganace akan yaranmu mata, Ramlah da khaleesa da Rahaima da Hauwa'u kowa yasan sun fida mazajen aure harma an tsaida bikinsu nanda bayan salla�?. Duk suka amsa da eh. “yauwa to Alhmdllh, yanzu munada sauran yara 'yan mata agidanan ak'alla su 8, kuma duk kusan Kansu d'ayane, dukda su Ramlah sun girmemusu, to wani uzirine yataso na tilas zamu had'awa auren wasunsu danasu khaleesa. shin ko akwai wad'anda a cikinsu sukeda tsayayye? domin a fiddasu?�?. Da sauri maman safara'u tace, “Safara'u nadashi, dan harma yanason turo iyayensa, amma nace ta dakatar dashi sai angama na yayyensu�?. “to Alhmdllhi, sai kuma wa?�?. Umma Ruk'ayya ma tace, “Fiddausi tanada tsayayye itama�?. “masha ALLAH, to bayansu fa?�?. “mamansu yaa hameed tace, “ai inaga sukenan kam Abban Hameed�?. “yanzu su 6 kenan suka rage? to dama Alhaji halliru d'an majalissar datta6ai, nasan duk kunsan abokinane shak'ik'i? to shine yanemi alfarmar nemama 'ya'yansa maza biyu auren biyu daga cikin 'ya'yana, d'aya d'ansane na cikinsa, d'aya kuma d'an yayarsane tarasu tabari yacigaba da rik'onsa. to harga ALLAH nasan yaransa sunada tarbiyya dan haka na amince, amma dukda haka saida nasake dogon bincike akan yaran saboda yaron yanzu ka haifeshine baka haifi halinsa ba, to Alhmdllh suma basuda wata matsala, dan haka mun yanke magana dashi akan suzo saisu za6a acikinsu, wannan shine dalilin dayasa muka taraku kenan�?.

Hummm yaufa anzo da Sabon al'amari a gidan namu, nanafa iyayenmu mata suka hau tsugunne-tsugunne, kowa burinta ace d'iyarta aka za6a, harma da iyayensu safara'u dakeda mijin a hannu, ganin sunji gidan maik'one kowacce tafara k'ok'arin gani da fatan 'yarta ta kasance acikin gidan, aiko sai shirye-shirye kowa keyi a asirce, aka fara gyara 'ya'ya. Mudai a 6angarenmu babu abinda innarmu kemana, hasalima inda taji maganar anan ta barta, komu bata sanarma ba, sai abakin Fauziyya mukejin komai. Yanda ake shirye-shiryen bak'i takowanne 6angare saika d'auka 'ya'ya. Shugaban k'asane zasuzo, ni abinma mamaki yabani dan kowanne d'aki da nasu shirin, dayake kowane d'aki akwai budurwa d'aya, mu 8ne, su shida kowanne d'aki 1 kenan, saimu mu biyu a d'akinmu, 'ya'yan abbanmu mu 4 kenan, na baba k'arami 2 na Dady 2, gashi biyu za'a za6a acikinmu amma saika d'auka mu duka za'a za6a saboda shirye-shiryen da iyayenmu keyi.

Ranar Asabar (Saturday) kenan takama zasuzo, dan haka muduka 'yan Matan 8 baba k'arami yace muhad'u muyi girkin tarbarsu. Ni Munaya, Munubiya, Safara'u, Fauziyya, Haleematu, Fiddausi, Zarah, Siyama. A kitchen d'in 6angarenmu muke girkin, dukda dai iyayenmu sun d'an saka mana hannu wajen tsara kalolin abincin daya dace a tanada. Ni abunma haushi yabani, yanda naga 'yan uwana NATA rawar kai, sai wani k'alk'ale-k'alk'ale akema abinci da drinks na gargajiya damuka had'a. A raina nace Kodai sune iyayen cin tsiya, ai bazasuci ko quarter d'in abincinnan ba, wannanma ai almabazzaranci ne wlhy, mutun biyu kawai amma anmusu abinci wajen kala 6, banda kuma kayan ciye-ciye irinsu snakes da nau'in nama da aka sarrafa zuwa daban-daban. haka dai muka gama aka kai falon baba k'arami aka shirya, sannan kowa takoma 6angarensu danta kimtsa........✍�?

Anan ne za'ayi kece rainin👌🏻😄🏃🏻‍♀

Guys kumuje zuwa😉👎🏻

One luv🥰🥰

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*👏🏻😭 [4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*

*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*

*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

_Ban yarda wani yaymin amfani da labarin nanba tako wace irin hanya, idan hakan tafaru ban yafeba gsky, ALLAH yabani ikon fad'ar abinda zai amfanar dani da Ku, ya tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar damu baki d'aya._

*_ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai dasuka kwanta dama, kabama marasa lafiyarmu lafiya👏🏻._*

👉🏻2�?

...........Zan iya ce muku fitinar gidanmu ta farone daga tushe, dan kuwa ginannen abune tun zamanin k'uruciyar iyayenmu...

Malam Faruku shine kakanmu, matarsa d'aya Marwa'natu (Innaro), 'ya'ya hud'u suka Haifa a duniya, maza uku mace 1. Auwal, Hameesu, Saffiya, Jafaru. ALLAH yayi Innaro mace mai mugun son abin duniya, arayuwarta tanason ace komai daga gareta aka fara ganinsa, kokuma wajen 'ya'yanta, sun tsayama 'ya'yansu duk sunyi karatun addini dana boko, sai dai Safiya iyakarta primary aka mata aure. Sukuma mazan duk sunkai matakin babar makaranta (jami'a). wannan yasaka Innaro d'aukar burin duniya ta d'ora akan 'ya'yan, harma matan dazasu aura. Auwal shine yafara kammala karatunsa, dan haka Malam faruku mahaifinsu yace ya fiddo matar Aure. Bai wani tsaya Jan rai ba ya gabatar da Ai'sha amatsayin wadda yakeso. Kai tsaye innaro tace sam bata aminceba, d'anta bazai auri d'iyar buzayeba kuma 'Yar iska, Auwal yayi lallashin yayi rok'on akan fahimtar da ita sonda sukema juna shi da Ai'sha, amma Sam tak'i saurarensa balle ta fahimcesa. Da farko Malam faruku yasaka musu ido, azatonsa innaro zata sakko cikin sauk'i, amma ganin yanda ta kafe akan bakanta saiya sanya baki da tambayarta dalilin k'in amincewar. Kai tsaye tace batason su Ai'shar ne, Dan ba'asan asalin suba, sannan kuma 'Yar iskace, shima kuma yasani ai. cikin hikima Malam yaso fahimtar da ita halin k'addara kowa da irin tasa, itama Aishar bayin kanta bane ba, amma tak'i saurarensa shima. ganin abin zai tasamma rashin mutumci yace to aure tsakanin Auwalu da Ai'sha kamar anyi an gama. A wannan lokacin ba k'aramin birkicewa innaro tayi musuba, amma Malam faruku yace tayi tagama, dan hujjarta batada muhimmancin dazai haramta auren Auwal da Ai'sha. babu 6ata lokaci kuma aka fara shirin bikin.

*Wacece Ai'sha?* Ai'sha d'iyace gawasu buzaye 'yan k'asar Niger wad'anda k'addarar rayuwa ta jawosu zuwa k'asar Nigeria, su biyu kacal iyayensu suka Haifa, Aisha itace babba, sai k'anwarta Rabi'atu, wurjanjan suka shigo k'asar Nigeria, sun fara rayuwane awata tashar mota, inda anan tsautsayi ya fad'ama Ai'sha wani mara imani yamata fyad'e anan cikin tasha da daddare, randa abin yafaru Malam faruku yaje tashar zai bada sak'o akaima wani d'an uwansa dake garin Maiduguri, ya taras anata cecekuce atashar, yayinda Ai'sha da iyayenta ke rungume da d'iyarsu sunata kuka da kururuwa. Malam faruku yatambayi abinda ke faruwa daga wajen mutanen dasuka zagayesu suna kallo, babu 6ata lokaci matashin saurayi yafad'a masa komai. Hankalin Malam faruku yayi matuk'ar tashi, danshi mutumne mai kishin al'umma, anan ya d'auki Ai'sha da iyayenta suka nufi asibiti, saboda jinin daketa zuba daga jikinta (Dan bazata wuce 15 ba sannan), duk wata kulawar da yakamata anbama Ai'sha a asibitin, har tsawon kwanaki hud'u tasamu lafiya sarai, kamarma komai bai faruba, sai dai tabo Na zuciya da aka bar mata itada iyayenta. tun suna zaman asibiti Malam faruku ya fiskanci iyayen Aisha basuda wajen zama, dan haka yak'udiri niyyar taimakonsu. Akwai wani d'aki k'arami ciki da falo dake gidansa, saiya zagaye musu shi da Katanga yamasa gyara. Tunda aka fara aikin innaro ta tada hankalinta, duk zatonta aure zai k'ara, ganin tana neman tara masa k'asa ya zaunar da ita yamata bayani dallah-dallah, maimakon ta kwantar da hankalinta tunda ba kishiyar bace saima takuma tadashi, tace bazata zauna da iyayen Aisha ba. Malam faruku yace bata isaba, Dan gidansane babu mai hanashi ajiye Wanda yakeso akuma lokacin dayaso. Dole badan innaro tasoba su maman Aisha suka zauna agidan, sai dai ko kad'an basajin dad'in zama da ita, kullum gori da cin mutunci take musu, su Aisha kam basuda sakat awajenta, saita koma sakasu aiki tamkar boyi-boyinta. Malam faruku ne ya koyama mahaifin su Aisha sana'a, har shima yasamu rufin asirin rik'e iyalensa dai-dai gwargwado, amma ko kama k'afar Malam faruku baiyiba, lokuta da fama ma shine ke taimakonsa dawasu abubuwan Na rayuwa, musamman d'inkin sitturar su Aisha da wasu matsaloli Na yau da kullum dasukan taso. tun zuwansu gidan Auwal yafara k'aunar Aisha, duk da mahaifinsu ya Sanar musu da komai akan k'addarar da ta fad'ama Aishan kuwa, shekararsu biyu suna soyayya, tun Aisha Na d'ari-d'ari dashi saboda tsoron abinda aka aikata mata har tazo tasaki jikinta dashi, sai dai babu Wanda yasan suna soyayyar sai Rabi'a k'anwarta.

Ana haka kuma Auwal yazo da zancen Aisha zai aura.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull