Kenza eBookz

Raina kama book 1 complete - Chapter 14

Raina kama book 1 complete - Chapter 14

Raina kama book 1 complete Chapter 14: Raina kama book 1 complete Chapter 14. A gidanmu ma dai bak'i kowa yakama gabansa, an barsu daga su sai su, da…

4,497 words

A gidanmu ma dai bak'i kowa yakama gabansa, an barsu daga su sai su, da daddare Abba yace ashirya da safe kowacce abita da akwatunanta, shi baiga dalilin ajiya ba. Duk sun amsa da to, amma kowacce burinta ace da ita aka kai nawa, Dan sunason suyo kallon kwaf, basu gamsu da labarin da 'yan kai amarya suka fad'aba akan gidana Dana munubiya, su a tunaninsu ma an aurenine domin a maisheni baiwa, yaushe nakai matsayin da har d'an Sarki guda mai sarautar Galadima zai gani yace yanaso, bayan lungu da sak'on hotunan mun gama zagaye duniya ni da shi. K'ilama da gaske yagama lalatani d'in. Haka dai sukaita gutsiri tsomarsu da kushe irinta masu hassada, duk da wasu abubuwan suna dawo kunnen innarmu batako damuba, ita dai babu abinda zatace ma ALLAH sai godiya, tunda 'ya'yanta kowanne yasamu matsugunni, yanzu saita maida hankalinta ga ibadar ALLAH da tarbiyar yaranta biyu maza dasuka rage, sune basu gajiba indai tozarcine.

������

Zuwa la'asar mama Fulani tafara k'ananun magana akan rashin nuna shaidar Munaya takawo budurcinta, dakuma rashin fitowarsu gaida mutane. ALLAH Sarki Aunty Mimi sai abin ya dameta ganin yanda aketa k'ananun magana a masarautar, hakkane yasata nufar sashen Galadima, babu zancen jiran a mata iso, sarkin k'ofa yabata hanyar tashiga. Tun'a falon farko daya raba sashina da nasa tace bayinta su jirata. Babu kowa a falonsa, Dan haka ta zauna tad'au waya ta kirasa, dan batasan halin dayake acikiba, baikuma kamata tashiga kai tsayeba, balle yanzu yanada mata. Fitowarsa kenan daga wanka saboda tashin dayayi a makare baisamu sallar la'asar ba, sai anan d'aki yayita sannan yashiga wanka. Wayar ya kalla yayinda yake goge ruwan fuskarsa, ganin aunty Mimi yasashi picking call d'in, saiya saka a Hans free yana cigaba da hidimarsa. ��my aunty kin 6uya fa��. ��na 6uya ko ka 6uya my k'ani, gani zaune ai a falonka��. ��kai haba dai? to bani kamar 5minutes na shirya nafito��. ��ok babu damuwa��.

Bai wani dad'eba yafito sanye cikin farin boyal mai shara-shara, yayi k'au sosai, sai zabga k'amshin turarensa yakeyi na koyaushe. daga shi har Aunty Mimi suka sakarma juna murmushi, ya zauna kujerar dake kallonta yana fad'in ��sweet aunty na ni kad'ai��. ��anya kuwa yanzu bamu raba da Munaya ba my k'ani?��. Murmushi yayi wadda har hak'waransa na bayyana, ya d'ora k'afafunsa d'aya kan d'aya yana gyara zama, ��in haka kikeso my Aunty saiku raba ai��. dariya tayi tace, ��nama bar mata. wai kasan mike faruwa a gidannan kuwa?��. ��A'a saikin fad'a��. ��tun kafin tafiyar su mom aka fara k'ananun magana a masarautar nan, wai anzo kar6ar yankin mutuntaka ka hana��. ��mtsoww!�� yaja tsaki yana jingina da kujerar da lumshe idanunsa, ��Aunty Mimi dan ALLAH karki biyema wannan jahilcin kema�� yabud'e idonsa akanta, ransa a d'an 6ace yacigaba da fad'in ��kawai da Wanda yakai sanin sirrinka da Wanda ma baikaiba wai duk sai sun sani?, a wace ayar alkur'ani ko hadisi akace dan ka tare da matarka a daren farko sai duniya ta sani?. ita mai aiko a d'auki k'yallen ince agaban kowa na gidannan lokacin da abunnan yafaru take fad'in bakinta bazai iya maimaita k'azantar danayiba?, to kuma tunda tariga da tasan nayi k'azantar abaya miye na aiko da wani k'yallen banza da wofi? wlhy fa suka kaini k'arshe zan shuka rashin mutunci kinji na rantse��. Shiru Aunty Mimi tayi tana kallonsa, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, dan Galadima yanada hak'uri sosai, gudun kar matsala ta biyo saboda ciwonsa saita kwantar da murya, ��haba my k'ani kwantar da hankalinka mana, ai abun bana 6acin rai baneba kaji, haba my habibi��. ��Aunty Mimi nagaji ne wlhy, rashin mutuncin masarautar nan yafara isata, nifa komai zan iya kawoshi karshe a wannan karon��. Tasowa tayi ta zauna kujerar gefensa, ta kama hannunsa ��please cool down mana my man, kaci gaba da hak'uri tamkar yanda kakeyi abaya, ALLAH yana tare da masu hak'uri, Momma bazataji dad'in wani Abu yabiyo bayaba, hakama Abie duk da yana a kwance zuciyarsa zatayi kunci, kansu ai sukema wa, yanzu ina k'yallen? ��. Iska ya furzar daga bakinsa, sannan ya nuna mata bedroom d'insa da hannu. Tashi tayi tashiga, a saman sofa taga k'yallen dan haka ta d'akko ta fito. zama takuma yi a kusa da shi, ��my K'ani ina zamu samu syringe?��. Idonsa yabud'e ya kalleta, ��syringe kuma? mizakiyi dashi?��. ��Sameer duk abinda zamuyi mu kare mutuncin mahaifanmu da lafiyarka muyishi mu zauna lafiya. yanzu dai kasa wani ya kawo mana��. Baice komaiba yajawo wayarsa yakira Muftahu, buk'atarsa ya fad'a masa sannan ya yanke wayar batareda yajira cewar Muftahun ba. Wata hirar Aunty Mimi ta d'akko masa, tun yana basar da ita, har ya fara tanka ta, daga nan suka cigaba da hira. Knocking d'in k'ofar akayi, Galadima yace, ��waye��. Sarkin k'ofa yace, ��ranka ya dad'e yalla6ai Muftahu ne yazo yace amasa iso��. ��kace ya shigo��.

Da sallama Muftahu ya shigo, ya rissina ya gaida Aunty Mimi sannan yabama Galadima hannu suka gaisa cikin musabaha. Ledar hannunsa ya mik'ama Galadima, ��no kabama aunty mimi��. Aunty Mimi ta kar6a ta fiddo da Syringe ta 6are daga ledar, had'awa tayi tare da Allurar sannan ta janyo charger ta d'aure tsintsiyar hannunta, Galadima da Muftahu dai kallonta sukeyi, allurar zata tsira Galadima ya rik'e ��mizakiyi hakane Aunty Mimi?��. ��Sameer! wannan itace kawai mafita, kabari kawai na d'iba a saka musu, da safe saika basu��. lips d'insa ya cije da k'arfi, yashiga kwance charger data d'aure hannunta, ��ki barsa zan saka musu nawa, yanzu ma koda an saka zai bushene, dan yayi wuri ai��. ��karfa kazo ka shukani��. ��karki damu zanyi, kema kin sani ai, tunda na amsa to zanyin��. Mik'ewa tayi tana fad'in ��shikenan to, bara na duba k'anwata itama��. Kansa kawai ya jinjina mata, yayinda muftahu yamata sallama ta fice.

��wai mike faruwa? ranka ya dad'e��. Tsaki Galadima yaja, yay shiru kusan minti 2, har Muftahu ya yanke tsammani da samun amsa. labarin komai yabashi. Shima Muftahu tsuka yaja, ��wai dan ALLAH yaushe za'a daina jahillar al'adarnan a masarautar nan? abinda ba addini ya wajabtaba sun kama sun rik'e, kuma duk matsalar tsohuwar nan ce wlhy, masarautu nawa ne suka daina wannan abun, amma mu takafa ta tsare, ALLAH lokacin da akayi na Uncle Hayatudden, kunya abinnan yabani saboda shi kawai nata6a gani, sashe-sashefa haka akaita nuniyar abinnan a masarautar nan wlhy��. Wani mugun tsuka Galadima yaja saboda haushi da abin yakuma bashi, fitarma da yay niya saiyaji yafasa.

����

Ni bansan mike faruwa ba ma, ina d'aki kwance duk kewa da kad'aici sun gallabeni, ga wayata babu caji saboda na manto cajan a gida. Nayi zurfi a tunani naji ana sallama. firgigit nayi sannan na amsa, hijjab d'ina najawo na saka, ina k'ok'arin tashi tashigo. da Sauri na mik'e ina mata sannu da zuwa, dan nariga da na shaidata itace aunty Mimi. rissinawa nayi na gaidata, ta amsa cikeda fara'a sannan ta zauna. mik'ewa nayi na nufi freight domin bata ruwan amma saita dakatar dani ta hanyar kamo hannuna. ��no k'anwata barshi kinji, yi zaman ki, ya zaman kad'aici da bak'unta?��. Kaina a k'asa nayi murmushi kawai, sannan nace ��Alhmdllh aunty��. ��masha ALLAHU k'anwata, babu dai wata matsala ko?��. Kai na na d'aga mata alamar babu, daga nan mukayi shiru saboda rashin sabo. Zuwa can nace, ��ina Samha?, tun d'azu tace zata dawo amma har yanzu?��. Murmushi tayi, tace, ��sun fitane itada Sauban tun d'azun, amma nasan suna hanyar dawowa kam��. ��Ayya ALLAH ya dawo dasu lafiya��. Ta amsa da amin tana mik'ewa. har falona namata rakiya, inajin dad'in yanda take nuna tana sona.

*******

A can kuwa bayan Muftahu yafito daga wajen Galadima sai yayi murmushi, tabbas yasamu hanyar dazata zame masa tsanin *CIKAR BURINSA*, da wannan kawai zai iya cin galaba akan Galadima. Da wannan tunanin ya hau mota yabar masarautar gaba d'aya.

Mikake k'ullawa ne Muftahu??

�������

Bayan sallar isha'i ina zaune ina karatun Alkur'ani Galadima ya shigo, ban daina ba saida na kai aya sannan, na d'ago domin gaidashi sainaga idonsa a kai na. Janyewa nayi nace ��barka da dare��. Bai amsaba cewa kawai yayi ��tashi ki shirya zamuje gaisuwa cikin gida��. Nima sai ban amsa shiba namik'e kawai na maida Alkur'anin inda na gansa. tashi yayi yafita danya bani damar shiryawa. banja wani lokacin mai tsayiba nafito cikin Alk'yabba, tsaye na iskeshi a falona, batareda yace uffanba yafara k'ok'arin fita, nima sai nabi bayansa batareda na tanka d'inba.................??

?mun tafi sashen mama Fulani, maison jin yanda zata kaya saiya biyoni. ???��???��???��

Barka da juma'a???

*_YA ALLAHA KA GAFARTAMA IYAYENMU_*??? [4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*

*_HASKE WRITERS ASSO...?_* _(Home of expert and perfect writer's)_

*_?RAINA KAMA......!!?_* _{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce??_*

??2?5?

..........Bugu biyu ta d'auka, jinayi tamkar anmin bishara da aljanna dan dad'i, lokacin danaji muryar innarmu tayi sallama cikin sanyinta sai kawai na Sanya mata kuka. Ita kuma daga can batasan wayeba, a sanyaye tace ��baiwar ALLAH ko bawan ALLAH lafiya kuwa?��. Murmushi nayi, gakuma hawaye na kwaranya, nace ��innarmu nice fa��. Cikeda d'okantuwa tace, ��Munaya kece? ya kuke?��. Murmushi nayi mai sauti, nace ��innarmu ina yini? inasu Aryaan? Wlhy ina missing d'inku innarmu, ALLAH kamar na dawo gida��. na k'are maganar da sakin kuka. Kallon juna sukayi da Abbanmu, da yake girkin tane tana d'akinsa, sukama juna murmushi, Abba yace, ��haba dai munaya ta jaruma ce da kuka haka? Ina aka ta6a kai mutum gidan miji yayi sha'awar dawowa gida inbada yawoba?��. ��wayyo Abbanmu I miss u so much kaima wlhy��. Dariya suka sanyamin shida innarmu, Abba yace, ��yo ga sakaran yarinya, miyeto na kukan hakan? Yaya mijin naki da jama'ar gidan?��. ��komai lafiya lau Abba, sai kewarku, musamman ma Munubiya, ALLAH ina kewarta Abba, dan ALLAH kace ya kaini na ganta��. Yanzu kam dai su Abba sosai sukemin dariya, saikuma suka shiga tsokanata, tun ina kukan harna ware nima ina dariya, munyi hira sosai, kafin Abba yace ��saida safe hakanan, karda ki k'are masa kud'in, ki gaidashi��. Cikeda farinciki namusu sallama, da cewa zankirama gobe. Na yanke wayar ina murmushi, Munubiya na kira itama, cikin sa'a tashiga kuwa. tana kwance jikin yaa Marwan yana d'an rage zafisa?, wayar tafara ring, shine yamik'o mata, ta amsa tana kallon number, irin Special number d'in Nance, wadda zaka ganta a tsare. (?bara na Baku, amma banda matan aure 07000000000?)???��???��.

Saida ta kalli yaa marwan ya d'aga mata kai alamar tayi picking sannan ta d'aga. Muryar Munaya dataji yasata mik'ewa zaune zumbur cikeda d'oki. Kowa yay kewar d'an uwansa, dan haka ko gaisuwa bamu tsaya yiba muka shiga fad'ama juna yanda mukai missing. muka 6alle hira kamar zamu ga juna tacikin wayar.. Mun d'au tsawon lokaci munayi kafin yaa Marwan yasamu dole yin sallama, wayar ya kar6a ya jawo matarsa ya rungume, zatayi magana ya d'ora yatsansa a bakinta alamar tayi shiru tareda yanke wayar ko sallamar arzik'i bamuyiba. Inajin sukur-sukur d'insu ta wayar, dan haka na tuntsure da dariya ina fad'in oni su yaa marwan Ashe dai ashe?....??. Number Fauziyya na gwada itama akashe, nace lallai amarci yayi dad'i kenan?, itama Ayusher na kira number busy, 'Yar tara, nasan tanacan itada khamees ana soyewa. Feena ma wayarta Switch up, nad'anyi tsok'i na ajiye wayar Na tashi domin yin shirin barci, dan yau ina cikin farin ciki, tunda naji muryar families d'ina.

Tun bayan fitar Munaya kam Galadima yafara jin canji a jikinsa, a hankali yakejin wani feelings na bijiro masa, kamar wasa abufa yafara tsamari, tun yana basarwa har mamaki yafara kamashi, shin wai mike faruwa ne dashi haka? bazaice baya sha'awa ba, yanayi sosai, dan wani time d'inma saiyasha tablets, ko allurar kwantar da sha'awan, amma baita6a jin irin na yauba, k'arfin sha'awarsa yasashi katange kansa daga dukkan abinda zai iya zurmasa ga halaka har yazama hanyar tsanin aikata zina. duk da jiya yad'ansha wahala saboda abinda yafaru tsakaninsa da yarinyar can duk da shi yayine badan yaji wani abuba, amma Abu yaso zamar masa Matsala a yinin gaba d'aya, sai dai tunda yaje yay allura sai nutsuwa tazo masa. Dauriyarsa ce take Neman zuwa k'arshe, sai kawai jikinsa yafara rawa, da bin bango yashiga bedroom d'insa, drowan gefen gadomsa yabud'e yad'iba drugs kusan uku ya watsa a baki, ruwa ya d'auka frigate ya korasu suka wuce. Humm abanza wai man kare, maimakon yaji sauk'i saima abin ya k'aru. yadawo falo saman doguwar kujera Yakuma kwanciya bayan ya kashe AC n gaba d'aya, Dan k'ara dulmiyar dashi yakeyi.

Nima d'in agareni kusan hakane, kad'an-kad'an nafara jin tsigar jikina Na tashi. Kamar wasa ina wanka sai Abu yafara shan kaina, abinda bansan ma'anarsa ba yafara bin jinin jikina da 6argo, na lumshe idona ina hango abunda yafaru tsakani na d'azun da Galadima, duk dani wahala ma nasha, wani feelings na tashin hankali yafara bijiromin, idanuna harsun sauya kamanni, da k'yar nayi wanka nafito, ko towel d'in ban cireba na saka hijjab Na d'au wayarsa Na fita, koda nayi sallama a k'ofar falonsa banji ya amsa ba, nayi har sau uku shiru kakeji, shikam yana kwance yana jina, amma bakinsa yakasa koda motsawa barema ya amsa min, saima muryata dake sakashin jin wani zirrr, duk sanda nayi sallamar sautin muryata na motsawa da tsigar jikinsa ne, gaba d'aya gashin jikinsa ya tashi. Jin shirun yayi yawa natura k'ofar kawai Na Shiga abuna, azatona ko barci ya d'aukesa kokuma bai jiniba. Ganinsa kwance saman doguwar kujera yasa gabana d'an fad'i, gawani iri dana kuma ji jikina yayi, dagashi sai boxer da vest, hannunsa d'aya dafe da mararsa, d'ayan kuma dafe da kansa, kauda kaina nayi daga kallonsa saboda tsorata da ganinsa a ainahinsa, gaskiya ba k'aramin namiji bane guy d'innan, duk kunya ta isheni, ban ta6a ganin namiji ba a haka, yo samarin gidanmu basa zama haka. duk tunanina barci yakeyi, na ajiye wayar saman cikinsa a hankali, kamar yanda naga d'ayar a ajiye, caraf ya rik'e hannuna da hannunsa daya dafe kansa, tsoro yakamani lokacin daya bud'e idonsa yana kallona, jazur idon yake abin tsoro. Muryarsa a matuk'ar sanyin daban ta6a Sanin yana da shiba yace ��mi zakiyi?��. idanu na nad'an waro waje cikin tsarguwa nace, ��mi zanyi kuma? wayarkace fa na ajiye maka��. ajiyar zuciya yad'an sauke, ya zuba min idanu batareda yasakimin hannunba. Gaba d'aya jikina yakuma rikicemin, jima nake tamkar Na fad'a kansa saboda abinda nakeji, ganin karna aikata abinda zanzo ina nadama saina zare hannuna dad'an k'arfi, jikinshi babu kuzarin kirki, danhaka yasaki hannun kawai, nikuma na juya nafice daga d'akin da saurina. Lips d'insa ya cije da matuk'ar k'arfi kamar zai huda, Yakuma dafe mararsa datayi tamkar zata fashe masa, kai bazai iya daurewaba, domin zai iya mutuwa wlhy, ganin yarinyarnan kuma Yakuma birkita tunaninsa. idonsa yarigada yarufe, ya manta matsayin Auren Nasu, duk da gargad'in da wani sashen zuciyarsa yake masa akan alk'awarin daya d'auka, burinsa kawai ya sauke wannan nauyin kozai samu nutsuwa, da k'yar yamik'e ya fice zuwa d'akina.

Nikam INA zuwa na zube saman gado bayan Na zare hijjab d'in, dagani sai towel, marata data d'aure tamkar zata fashe na rik'e da hannu biyu Ina hawaye, wai wannan wace iriyar masiface ne?, nashiga uku ni Munaya, mike shirin faruwa dani ne?.. ��innalillahi�� kawai nake iya karantawa saboda tashin hankali, jikina harwani rawa yakeyi, ko kad'an bansan Galadima ya shigo d'akinba, dan nafad'a wata duniya ta daban, babu zato kawai naji mutum yafad'o jikina yana sauke numfashi wani na k'orar wani, wata wawiyar runguma yamin tareda matseni ajikinsa gam, kai kace cikinsa zai maidani. Humm maimakon na turesa sai nima nakuma k'ank'amesa, banyi k'asa a guywaba wajen maida masa murtani abinda yakemin.. Daga ni harshi kowa yafita hankalinsa, dan idonmu yarufe bamusan mi Muke aikatawa bama. Hankalina bai nemi dawowa ba saida naji Galadima na neman kasheni, duk da inajin lokacin dayake jero addu'a amma ban dawo dai-daiba, nayi nisan da banajin kira kam, saida mai gayya mai aiki ke shirin faruwane na farga. Ina yayi Nisan da bazaiji kiranaba balle kuka da magiyata akan karya cutar dani, yatuna alk'awarin daya d'auka please, baimasan inayiba, duka, cizo, yakushi, babu kalar da ban masa ba, amma bawan ALLAH nan saida yamin biji-biji, dukkan fushinsa na shekarun baya saida ya fanshe a wannan daren. Nayi kuka harma ba'a jin sautin fitarsa, a jama'ar gidanmu kuwa ai mutum d'ai-d'aine ban kiraba, duk tsanar innaro danayi ranar saida nakirata ta taimakeni (?Munaya anga idi?).

����*��*��*����

A can kuwa muftahu Na fita sukaci karo da Harun, kallon-kallo akama juna, cikeda tsantsar mamaki Harun yace, ��wai Muftahu mikake shiryawa ne?��. Kallon rainin hankali muftahun yamasa, yagyara tsayuwarsa yana wani murmushin da bakowa zai iya fassara Shiba, ��ban fahimci tambayar takaba, amma mikake nufi?��. Harun ya d'an hararesa, ��Muftahu karka rainamin wayo, tabbas nasan ni da kai duk abokan Galadima ne, bayan zumunta dake a tsakaninmu, amma shige masan dakake fiye da kowa a wannan tsakanin yana bani mamaki��. Muftahu ya ta6e baki yana wani basarwa, kafin ya kalli Harun a wani yanayi, ��Harun kana sakamin idone kenan a al'amurana? humm bazance ka bariba to, kacigaba, ni da kai d'an halak ka fasa, idan kaga dama ka kunna wutar jefani bayan kaga abinda zanyin, wannan ba damuwata baceba, inar Na cimma burina right?��. yana gama fad'ar haka yabar wajen kawai. Yayinda Harun yabishi da kallo kawai tamkar wani soko, a zuciyarsa yana tunanin mi Muftahu ke shiryawa ne akan Galadima? tun kwanaki yakeson fargar da Galadima illar kusanta Muftahu a jikinsa, amma abin kamar wani tsafi, da Zarar sun ke6ance da Galadima to saikaga Muftahu a wajen, saikace mai gani har hanji, kenan yakamata yasake shiri akan Muftahu?. Da wannan tunanin shima yashige mota yabar gidan, saikuma Galadima ya fad'o ransa, waya ya d'auka ya kirashi, amma saiyaji Number busy, hakanne yad'an sakashi nutsuwa, a tunaninsa ko Galadima yana wayane dasu Momma. (A time d'in Munaya Na waya da phone d'in Galadima).

����*��*���*��*����

Yanda ta tashi a firgice haka shima ya tashi, jikinsa ya jawota ya rungume saboda waige-waige da takeyi tana kwala kiran sunan MUNAYA!. jinta a jikinsa saita d'an sami nutsuwa, cikin kuka tace, ��yaa marwan mike faruwa da 'yar uwata ne?, nayi mafarkinta cikin mawuyacin hali tana kuka da kiran sunana Nazo Na ceceta��. ��sorry baby, ki kwantar da hankalinki mafarki ai ba gaskiya baneba, maybe shaid'anune kawai suka taswuranta hakan a gareki, amma ba d'anzun kuka gama wayaba? kofa awa 5 ma ba'ayiba da gama wayar taku?��. ��hakane yaa marwan, amma acikin awa 3 wani Abu bazai iya faruwa ba? ka kiramin ita please naji?��. ��no kiyi hak'uri, dare yayi gaskiya, babu yanda za'ayi mu kirata a wannan time d'in, k'arfe 1 fa ta wuce, 2 ma saura, karkuma ki manta tanada miji itama yanzu. Muyi addu'a ALLAH yasa alkairine, da safe saiki kirata ko?��. Cikin share kwalla ta d'aga masa kanta, a hankali ya kwantar da ita a jikinsa bayan shima ya kwanta, yad'an furzo huci kafin yakai hannu yana shafa kanta tareda sumbatar goshinta yacigaba da bubbuga bayanta a hankali, kowa yana yin adu'a, ahaka barci ya kwashesu, duk da sun dad'e basu koma ba, musamman ma Munubiya da mafarkin yak'i barin ranta, Dan takasa yadda Munaya Na cikin k'oshin lafiya gaskiya, ka wai dai dan batada yanda zatayine ta hak'ura.

*****����*����****

Hawaye kawai nake iya zirarwa, amma kwakwkwaran numfashi bana iyawa saboda jigata, zan iya danganta abinda Galadima yayimin da fyad'e, dan baya cikin hayyacinsa ko kad'an, kamar yanda nima nawa ya gushe daga farko nabashi gudunmawa. (Nasan duk mai hankali ya k'iyasta a yanda Galadima ya zomin zai tabbatar dolene na jigata d'in?). Tunda yasamu nutsuwa yana gefena a kwance kawai, a hankali memory d'in brain nasa ke tariyo masa abinda ya aikata tamkar a mafarki, ya bud'e idonsa da hanzari akaina, domin kuma gaskata abinda yafarun, shin da gaskene ya aikata? ��innalilahi�� yashiga maimaitawa dan ganina kwance a gefensa ina hawaye, daganin yanda nake a kwancen ina fidda numfashi d'ai-d'ai kasan nagama jigata, yabi d'akin da kallo cikin tsantsar takaici, yaushema shikam yazo d'akinnan? ��Hasbinallahu wa ni'imal wakil. mike faruwa danine ni Sameer? wace k'addarace kuma ta kutsoma rayuwata? yanzu nan ni Muhammad Sameer ne da wannan d'anyan aikin? miya samu tunanina haka?.......�� Tunaninsa ya tsaya cak lokacin daya jiyo dasashshiyar muryata ina kiran innarmu da Munubiya, muryata a raunane, runtse idanunsa yayi tareda mik'ewa zaune da k'yar, dan jikinsa gaba d'aya yayi week, ga wani masifaffen ciwo da kansa keyi. da k'yar ya iya kuma bud'e idanunsa a kaina, babu shiri yakuma runtsewa saboda tsorata da ganin yanda yamin, hawaye kawai yaji suna neman zubowa a face nashi saboda shi mutum ne mai tausayi, bayason yaga ancutar dawani bare kuma shi da Kansa ya aikata, jarumtar had'iyesu yayi tareda kuma bud'ewa, yazubama fuskata ido batareda ya iya cemin uffanba, yama rasa ta inane zai fara shikam, mizai fad'amin kuma a yanzu Na yarda dashi? mizai cemin shikuwa?. Innarmu dana sake ambata murya a sark'e yasakashi saurin kallona, baisan yarik'o hannuna ba ya rumtse anasa, la66ansa sai motsawa suke amma yagaza yin magana, shi yanzu ma baisan wane irin taimako zai baniba, bai ta6a irin hirarnan dawani abokiba balle yace yasan ya zaiyi, bai ta6a aikata zinaba, zai iya rantsuwa da Ubangijin daya haliccesa bai ta6a ta6a jikin wadda ba muharramarsa ba, sai ita Munayar daya d'auketa randa yasa a sato masa ita. Kuma ko muharramar tasa bazai wuce yarik'e hannun taba shima ba kowaba wlhy, inhar kacire Samha Momma Aunty Mimi ko Mom, sukad'aine mata Muharramsa da zaice yanada shak'uwa ta musamman dasu, amma shi ko yaran masarautar nan bama kowacce zai iya ambatarta da sunanta dai-daiba..... Rashin ya cika da tashin hankali, kukan danakeyine yasakashi waigen phone nashi, baiga komaiba, tunawa yayi ba d'akinsa baneba nan, ya saki hannuna ya sakko agadon bayan ya suturta jikinsa, jikinsa gaba d'aya ya mutu, ahaka da sand'a yakai falonsa, wayarsa dake a saman kujera ya d'auka, to inama zai dosa shikam? wazai kira akan wannan abin kunyar daya aikata? tunanin bincike a network ne ya fad'o masa a rai, maybe yasamu bakin zaren, Google yashiga yay d'an rubutu yahau Searching, amamakinsa kam saigashi sun bashi, saiya kuma wata tambayar, nanma yasamu amsa dai-dai, ��Alhmdllh�� yafad'a yana mik'ewa rik'e da wayar. Inda yabarni ya iskeni, Toilet yawuce kai tsaye, yayinda nabishi da kallon tsana, nikad'ai nasan minakeji akansa, ayanda nakeji ko wuk'a aka bani zan iya fidda masa hanji waje, tabbas yanzu nakuma yarda banida wayo, yanda tun farko Na yarda da maganar wai auren yarjejeniya mukayi da Wanda yafi k'arfin ajina da matsayina, inma banda wauta irin tawa tayaya mutum kamar Galadima zai nemi kulla aure dani?, Na manta namiji zai iya komai domin cikar burinsa, k'ilama *AUREN 'DAN'DANE* yayi dani, ai sainaji wani kuka ya tokaremin mak'oshi, har ina neman shid'ewa. Kamar yanda yaga sunsa ya had'a ruwa mai zafi-zafi, sannan yafito, ficewa yakumayi, babu dad'ewa sosai yadawo yakuma shigewa toilet d'in, ni dai idonama Na rufe gaba d'aya, dan bana k'aunar ganinsa. Jinai kawai an kama hannuna ana k'ok'arin tadani zaune, wata azaba naji har cikin kwalwar kaina, saina fashe dawani marayan kuka Wanda yasakashi saurin sakina nakoma Na kwanta. Runtse idonsa yayi saboda jin addu'ar danake jero masa ta neman sakayya ga ALLAH tsakanina dashi, wani bai ta6a masa makaman ciyar addu'ar nanba, amma gashi matarsa ta sunnah tana masa, duk da yasan hak'in sane ya k'ar6a agareta hakan bai hanashi jin bak'in cikiba, dan aganinsa inada hujjar masa addu'ar da tafi wannan muni, tunda Bahaka mukayi dashiba. Cikin tsantsar damuwa ya d'aukeni zuwa bayin, yayinda nikuma nake kuka ina fad'in ya saukeni, duk da a hankali nake maganar yana jina.

Ba k'aramin daga mukayi dashiba wajen taimakona, harda cizonsa nayi a damtsen hannunasa, aiko yacizu wlhy, dan hakwarana saida suka huda lallausar fatarsa, (to dama ba wahala tasaniba fatar) amma a mamakina sainaga ko gezau baiyiba, kuma Na tabbata yaji zafin cizonnan, saidai bansan dalilinsa Na daurewaba, da k'yar ya samu nayi wankan tsarki kuwa, dan saida yakusa makeni ma dan haushi sannan nayi, harya dawo dani d'akin ban daina jera masa ALLAH ya isaba a fili da kiransa mugu azzalumi. Duk da kalamaina suna sukar zuciyarsa haka yadake yanuna tamkarma baya jina. Bashida maganin dasuka rubuta akan matsalata, sai dai yanada Wanda zai iya taimaka min kafin zuwa Safiya ya nemo wancan. Haka yakawo min maganin da tea wai nasha, harara kawai Na zuba masa Na maida kaina Na kwanta batareda nako motsaba balle yayi zaton zan tashi. Shima baice komaiba yakamani ya tayar, hannunsa da k'irjinsa nashiga bugu, ina kuma kaimasa cizo, amma k'arfin ba d'ayaba, bai barniba saida ya tadani, sannan ya wani ci uban Magani fusakarsa amatuk'ar murtuke, yace ��kinsan ALLAH koki kar6a kokuma....humm��. Yanda yay maganar kuma sai tsoro ya kamani, Na watsa masa harara kafin nabud'e bakin, da kansa yabani shayin, sannan yabani magani. mugun Ashe harda Na barci, cikin mintuna k'alilan barci yay awon gaba dani. Sai lokacin ya samu damar sauke ajiyar zuciyarsa tareda dafe kansa dake tsananin sara masa. Duk yanda yaso yayi tunanin ya akayi hakan tafaru yakasa, saboda matsanancin ciwon da kansa kemasa, dole yamik'e zuwa d'akinsa, shima ruwan mai zafi yay wanka dashi sannan ya tsarkake jikinsa ya fito, Magani yasha ya haye gado ya kwanta shima, yasan bazan farkaba a nan kusa. Maganin barcin da shima yashane yasaka barci suresa shima.

������(())������

Tun daga shigar Muftahu wajen Galadima har zuwa sanda ya zuba Abu cikin milk d'in Galadima lokacin daya Shiga bedroom d'insa d'aukar Abu suna kallo, har ya girgiza ya ajiye kwalin da sauri inda ya d'auka, fitowar Galadima zamansa da files d'in daya bama Muftahu Na masu buk'atar taimako a asibiti da aka kawo masa zai biya, har shigowar Munaya falon Galadima da fitar Muftahu, zamanta da kar6ar wayarsa zuwa fitarta itama, yanda Galadima yafara fita hayyacinsa har dawowar Munaya sashen takawo masa wayarsa, fitarta dakuma bin bayanta dayayi, hankalinsu ne yad'an tashi ganin yadad'e bai dawoba, gakuma a yanayin daya fita. Hakanne yasaka aka turo wasu mata biyu da kayan fruits wai sukawoma Galadima domin suyi CID d'in yana ina?. Sai dai sarkin k'ofa kuma yace saiya musu iso, kamar yasani saiya rufe k'ofar ta ciki sannan yanufi sashen Galadima d'in, yayi sallama tafi sau 15 amma babu amsa, ya tabbata da yana kusa daya amsa, komawa yayi yace musu ai yamayi barci, su koma dashi kawai, babu magiyar dabasu masaba yak'i bud'e musu, dan yarigada yasan komai Na kitumurmurar gidan, sannan yasan Galadima bayacin abincin kowa a masarautar, ko ankawo su yake bamawa, idan kaga yaci abincin dawani yadafa a masarautar to tabbas aunty Mimi tana k'asar, sunzo tare kotazo ta iskeshi. dan haka yahanasu shiga, harma yad'an tsargu da tunanin kawai wani Abu a k'asa ganin sun jajurce dason shigar. Ransu a 6ace sukabar wajen, inda aka aikisu suka koma, sun Isar da abinda yafaru. Hakan kuma yakuma tada hankalin masu Aiken nasu, domin an ruguza musu plan d'insu kenan...........??

?hummmm.????��???��???��

_ko Yaya za'a kwashe tsakanin Galadima da Munaya da safe kuma??, Munaya team amin afuwa???ku kora da wanan??????????._ ??

*_Masu karatu nasan kowa yamatsu yasan tarihin masarautar su Galadima, insha ALLAH zakuji, inason muzo ga6ar daya kamata kuji d'inne insha ALLAH, saura k'iris???._*

Barkanmu da dawowa???.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*?[4/30, 7:46 PM] Sis Naja Atuh: *_Typing?_*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull