Raina kama book 1 complete - Chapter 6
Raina kama book 1 complete Chapter 6: Raina kama book 1 complete Chapter 6. A plaza ma tunda yashigo kowa ya fahimci yanda cikin 6acin rai, Dan ko kallon…
4,381 words
A plaza ma tunda yashigo kowa ya fahimci yanda cikin 6acin rai, Dan ko kallon masu gaisheshi bayayi, mutane masu siyayya sai kallonshi sukeyi, dama wasu gulmace takawosu dansu k'ara ganema idonsu akan labarin da ayau yazaga ko'ina da ina. kai tsaye wani Office yashiga. Cikin hanzari Wanda yake a office d'in yamik'e domin kwasar gaisuwa, sai dai yanayin ogan NASA yayi masifar rikitashi. Bai saurari gaisuwarba yace, “inason ganin abinda yafayu a CCTV tundaga safiyay jiya hay daye�?. Jiki Na rawa guy d'in yace “angama ranka ya dad'e�?. Kujera ya jawoma Galadima ya zauna, sannan yagyra zaman computers d'in wajen sosai, tariyo wa yafarayi cikin nutsuwa, saida yadawo Sunday morning 6pm sannan ya saki, tundaga bud'e plaza har zuwa masu share-share da goge-goge dasukayi aikinsu, har lokacin da masu sayayya suka fara Shiga da fita a plaza d'in, har an wuce yace “dawo baya kad'an�?. A slowly yadawo bayan kad'an, har zuwa kan wasu samari biyu d'aya sanye da jallabiya d'ayan wandon Jeans da farar t-shirt. “kayo zooming d'in yayannan dake tsaye sunan waige-waige�?. Zooming d'insu yayi, sannan yasanya play yanna tafiya a slow. Samarin sunata 'yan kalle-kallene, saikuma zuwa can d'aya yasaka waya a kunne yana magana da kallon cctv camera d'in dake hasko tsakkiyar plaza d'in Inda motoci ke Parking, saikuma ya janye idonsa ya maida kan motocin dakeJere a wajen. da ganin Kasan yana maganane, Dan d'ayan dasuke tare yanata gyad'a Kansa alamar gamsuwa da abinda d'an uwansa yake fad'a. Galadima Na zaune shiru, idonsa nakan computers d'in yana nazarin gayun har aka wuce Kansu, baice uffanba yacigaba da kallon shigi da ficin jama har zuwa 8:11pm, daga nan Computer tayi d'iff. Da Sauri Galadima ya kalli sarayin “mi yake fayuwane?�?. “Ranka ya dad'e wlhy nima ban saniba, amma bara Na duba�?. Danne danne saurayin yafara da 'yan dube-dube, babu wata matsala daga nan. Kallon Galadima yayi yace “ranka ya dad'e babu wata Matsala daga nan, sai dai Idan daga cameras d'inne�?. A tsawace yace “bangane mikake nufi daga cameyas d'inne ba!? Kenan hay shigowata jiya babu kenan!? kuma kana zaune a office amma bakayi complain ba tun ajiyan? mika aikata!!? mi suka baka ne domin tozarta ni!!? nace nawa suka baka Saleem!!!!?�?. Kusan duk Wanda ke cikin plaza d'inan a yau yaji wannan hargagin Na Galadima. Jikin matashin saurayin ne yafara rawa, ya zube a k'asa gaban Galadima saboda tsabar tsoratar dayayi da yanayinsa, tunda yake aiki a k'ark'ashinsa baita6a ganinsa cikin wannan yanayin irin Na yau d'inna ba, duk da labarin abinda yafaru yazo kunanensu, sunkuma ganin a jarida da social media baiyi zaton lamarin zaiyi zafi hakaba. “wlhy yalla6ai babu Wanda yakeda abinda zai sayeni na cutar dakai, Kaine ka ceci rayuwata daga garari, ka tallafi maraicina a lokacin da nake Neman lalacewa saboda rashin matallafi, kazama gatana nida mahaifiyata da k'annena, mizaisa nabiyema rud'in wasu akan 6ata maka suna....�? “ya Isa haka!!�?. ‘galadima yafad'a cikin tsawa�?. Gaba d'aya Galadima ya birkice musu a plaza, yasa securitys d'in wajen da dogaransa sun kori dukkan masu sayya dake ciki, ya tartare ma'aikatan wajen a d'aya, ya tabbatar musu da in har munafukan cikinsu da aka had'a baki dasu basu fidda kansuba gaba d'aya sai sunyi dana sanin saninsa. Kaf d'insu sun rud'e, sai rantse-rantse da k'ok'arin kare Kansu sukeyi, amma yak'i saurarensu, ganin zasu kuma dagula masa lissafi saiya basu suspension kawai aka rufe plaza d'in baki d'aya. Motocinsa Na k'ok'arin barin wajen motar Muftahu tashigo. Muftahu ya faka motarsa waje d'aya suka fito shida Harun, (shima Harun abokin Galadima ne makusanci, Dan zan iya cewama yafi sanin sirrin Galadima fiye da kowa a abokansa gaba d'aya, shi d'an waziri ne). Tunkan su k'araso Galadima ya sauke glass d'in motar da kansa. kallo d'aya sukai masa duk suka tsorata, Dan basu ta6a ganinsa a irin wannan 6acin ranba, baice uffanba, sai nuni daya musu akan su shigo motar. Basu musaba suka bud'e suka shiga, Muftahu a gaba, Harun yashiga baya kusada Galadima. Bayan gaisuwa dasukayi garesa babu Wanda Yakuma cewa komai, Dan ko gaisuwar bai amsa musuba, hannu kawai ya d'aga musu. Sun hau titi sarkin mota yace “Ranka ya dad'e ina muka dosa?�?. ‘cikin girmamawa da taka tsantsan yay maganar�?. Murya a shak'e yace “gidan Jayiday�?. Sarkin mota bai fahimtaba, amma yana tsoron tanbaya, murya k'asa-k'asa ya tambayi Muftahu �?. Murmushi kawai Muftahu yayi yana girgiza kai, shiya shiga yima sarkin mota kwatance har suka Isa.....
�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?
Muna tsaka da barci saboda allurar da doctor yamana Innaro tafad'o d'akin, babu ko tausayi tashiga tashinmu cikin d'ad'd'aka mana duka a baya da cinyoyinmu. Dagani har Munubiya a firgice muka tashi zaune. “kutashi munafukai, Ashe abin ba a iya runguma da kama hannu ya tsayaba harda ciki kuka kwaso mana?, tsinannun gayyar tsiya, wlhy dagaku har uwarku yau saikin bar gidanan, a yau d'inan idan ubanku bai saki uwarkuba kun tattara kun tafi saina tsine masa albarka, yazo yaza6a ko Ku ko ni yau agidanan. sai kuma tafashe dakuka, takama bakin zaninta datayo lullu6i tana sharar hawaye, “kai ni dai Malam ya cutar dani akan had'a wannan aure da d'iyar marasa asali, ai gashinan ta Haifa mana bala'i da masifa, shikuma yatafi yabarni da kunyata, Malam kacuceni katafi kabar mana baya da k'ura. Wlhy yau sai A'isha tabar gidanan itada gayyar tsiyar 'ya'yanta, natsaneku daduk wandama zai soki A'isha, natsaneku wlhy, takuma fashewa da kuka. Tuni matan gidanmu kowa yafito, wasu harsun shigo falonmu, wasu kuma Na daga k'ofar d'aki, harda tsirarin 'yan biki da sukak'i tafiya domin tsayawa kallon kwaf. Cikin matan gidanmu ne wata taje tasanarma innaro wai bamuda lafiya munata amai duk abinda mukaci, anakiran likita ya dubamu yace duk munada ciki wata uku-uku.
Ni da Munubiya mun had'e kai muna kuka mai tsuma rai saboda tozarcin da innaro kemana muda mahaifiyarmu agaban bainar jama'a. Dady da Abba k'aramine suka shigo sunama innaro magana akan bafa haka zancen yakeba, babu Wanda yace munada ciki. Hayayyak'o musu tayi tana zaginsu, wai k'aryane suna kare Innarmu ne, aida likitan bai fad'aba baza'aje a sanar mata ba. Cikin 6acin rai baba k'arami yace, “inna waye yaje yafad'a miki wannan maganar to?�?. “cikin matan gidanan mana, kuma daga bakin wadda nasan bazataimin k'aryaba�?. Ran Dady ma a wannan karon ya 6aci, afusace yace, “inna wacece acikinsu? Wace 'Yar isakar matace�?. Nanafa matan gidanan mu suka shiga raba idanu akan juna. Innaro tace “karka kuma zaginta, idaba ayiba bazatace anyinba, kuma koma wacece bazan fad'aba, idan kuma ni kake zagi sainaji?�?. “ALLAH ya huci zuciyarki inna, ni yaza'ayi Na zageki�?. “kai dai kasani sakarai�?.
Duk abinda ke faruwa Abbanmu da Innarmu Na saurare daga d'akinsa amma acikinsu babu Wanda yayi yunk'urin fitowa. Kayanmu innaro tafara kwasa tana watsowa waje, wai saimun bar gidan.
“Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, wannan wane irin tashin hankaline?�?. ‘innarmu tafad'a cikin matsanancin kuka�?. Rungumeta Abbanmu yayi shima yana k'ok'arin maida kwallar data cika masa idanu.
Ganin abin yana Neman wuce gona da iri baba k'arami yafita da hanzari, wani tsoho dake can k'asan layinmu yaje ya d'akko, tsohon abokin Malam faruku ne na k'ut da k'ut, shika d'aine zai iya takama Innaro burki kuma.
Aiko hakance ta kasance, tunda yashigo yay magana Innaro ta dakata da abinda takeyi tana huci da fidda numfashi. Tsoho Malam Labaran yace, “haba innar jafaru, da hankalinki da girmanki kike aikata wannan abin Na yara a gaban sirikanki da 'ya'yanki da jikokinki? Shin babu mai fad'a miki kijine wai kekam?�?. Cikin sassauta murya tace, “malam mai kanwa nasan bakasan ainahin abinda yafaru bane kaima, amma wlhy da dakanka zakace Auwalu yasaki marar asalinnan sukama gabansu itada 'ya'yanta am.....�? Hannu ya d'aga mata, yagyara tsayuwarsa jikin sandarsa dake taimaka masa tafiya, naji komai innar jafaru, amma wannan hanyar da kuka biyo ba wai itace mai 6illewa ba, bincike yakamata ayi domin asan gaskiyar lamarin. dan haka zoki wuce gida, zuwa gobe zamu tattauna akan lamarin sannan kowa ya nutsu, mukuma jira abinda zai fito daga can gidan Sarkin�?. Badan innaro tasoba tafice, hakama matan gidanan mu basuso wasan yak'are iya nanba, sunso a yau Innarmu tabar gidan da saki, sannan mukuma mahaifinmu ya koremu. Kowa taja k'afa takoma d'akinta cikeda takaici da addu'ar ALLAH yasa daga gidan sarkin suma su d'auki mummunan mataki akanmu.....
Maman fauziyya Ce kawai ta nuna damuwarta akan lamarin
�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?
Su Galadima ma sun isa gidan jaridar *Manuniya* tun sanarwar isowarsa ta kad'a hantar cikin ma'aikatan wajen, musamman wad'anda basuda laifi akan lamarin, tirsasu akayi. Shi kansa manaja d'in wajen a kid'ime yake, dukya rikice yarasa matsugunni har Galadima da gayyarsa suka iso office d'in bisa jagorancin sakatare d'insa. K'asa yazube kawai yana kwasar gaisuwa wajen Galadima, ko kallo bai ishi Galadima ba, cikin daka tsawa yafara magana...........✍�?
Tofa masu karatu, ko manajan jaridar MANUNIYA zai amsa laifinsa? Kokuwa zai fad'i wad'anda suka sanyashine inba laifinsa bane shima? to koma dai shima da had'in bakinsa?. Wane mataki masarautar su Galadima kuke ganin zata d'auka akansa? Shin ina ma maganganun Momma suka dosa ne? Miya faru da mahaifin Galadima har suka koma k'asar India da zama?.😕
Kumuje zuwa my guys danjin yanda zata kaya. da amsoshin d'unbin tambayoyinkun nan.⛹🏻♀⛹🏻♀🤾🏻♀
_Naga mutane basa fahimtar yaren yarima😂, yarima later R ne baidashi, bawai tsamin bakine dashiba fa, kun gane, naga wasu kamar suna zaton tsamin bakine dashi🤣._
_Ngd da comments d'inku, kuna sakani farin ciki sosai, kuyi hak'uri da rashin amsawa ta, kunada d'unbin yawane wallahi😊🥰🥰🥰🥰. I love you wujiga-wijiga all😁✋�?._
*_Ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*😭👏🏻[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_* _(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
__________________________
*_Naga idi🙆🏻, Galadima fa ba tsamin baki bane dashi, Ku fahimta😂, bashida (R) ne, amma gashinan nayi gyara, ina fatan yanzu zakuna fahimtarsa🤣._*
_______________________________
👉🏻1�?1�?
.........Ba manager kawaiba, hatta da sauran jama'ar dake gidan jaridar saida suka tsorata da tsawar Galadima, su Muftahu ma tsorone ya kamasu, sunsan irin wannan matsanancin fushin gareshi babbar matsala ce ga lafiyarsa. Aikam sai gashi ya dafe kansa, saboda yay wani mugun sara masa, da sauri Harun yajawo kujera ya kamashi ya zaunar, har yanzu dafe yake da kan nasa. Muftahu ya furzar da hucin, matsalar da suke gudun ta d'akko hanyar faruwa kenan. kallon manaja dake durk'ushe har yanzun yayi, yace “tashi ka zauna�?. Mik'ewa manaja yayi jiki Na rawa yakoma saman kujera, Muftahu da Harun ma suka zazzauna. Cikin tsare gida Harun yace, “manager ka nutsu, kabamu had'inkai wajan fad'ar gaskiya, inba hakaba wlhy zakayi nadama ne, ba kaiba hatta da ahalinka saisunyi nadamar kasancewarka acikinsu�?. Manaja yashare guntun kwallar dasuka taru masa a idanu, a nutse yafara fad'in “ai tunkan jaridar jiya tafita nake acikin nadama, nayi dana Sanin kasancewata ma'aikacin jaridar da aka ci zarafin d'an Wanda yay tushen kasan cewata a wannan matsayin danake, da ace remote d'in rayuwata a hannuna yake, dana tariyo bayana jiya bata shigo rayuwata ba, amma Na.....�? Muftahu ya katseshi cikin d'aga masa hannu “kaga manager, ba rayuwarka mukazo saniba, munason ka fad'a mana waye yasaka wannan aikin? nawa suka biyaka kamusu shi?�?. “wlhy tallahi yalla6ai basu biyani komaiba, kaga wacan jakar sune suka ajiye min ita, amma ko bud'eta banyiba. kuma babu wani ma'aikaci daya buga labarinan agidan jaridar nan da hannunsa. sune da Kansu adaren jiya sukayi komai, bayan sun had'emu waje guda da bindugu, kuma sunzo nannane dukansu fuska arufe, wlhy ko fuskar mutum d'aya bamu ganiba, yanzu haka sun kwashe muhimman documents dake ma'aikatar nan sun tafi dasu. kuma sunsan da zuwan yalla6ai gurinnan yau, Dan komai sunyishine a tsare kamar yanda mukaji suna hira a tsakaninsu�? manaja ya fashe da kuka, sannan yacigaba da fad'in “saboda sunsan zakuzo nan yau, sunje gidana tun adaren jiya, sun kwashemin iyali da mahaifiyata, yanzu haka suna wajensu, sun tabbatar min inhar wani magana yafito abakina abakin ran matata da yarana hud'u da mahaifiyata sai k'anwata. wlhy ina cikin masifa, yau anan Na kwana, nakasa fita waje saboda banason jin 6atancin da jama'a suka gani a wannan safiyar akan yalla6ai. Wlhy Na rantse muku bansan komaiba�?. Tunda manaja yafara magana kowa yay tsit, Galadima bai d'agoba saida yaji manaja ya ambaci iyalansa Na wajen wad'anda suka aikata aika-aikar. Idonsa yakad'a yayi jazur, sosai manaja ya tsorata da idanun Galadima, haryana tunani a zuciyarsa anya Galadima shi kad'aine, bashida aljanu kuwa?. Komai Galadima bai ceba, ya tashi dafe dakai yafice daga office d'in, ma'aikatan wajen sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, amma kallon kowa baiyiba yafice. Dogaransa suna ganinsa suka mik'e da Sauri, Mota suka bud'e masa yashiga, suma su Muftahu suka fito da hanzari.
�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?
Tun daga fitar innaro sai gidan yay tsit, kowa ya kama gabansa zuwa d'akinsa, a can suka cigaba da gulmace-gulmacensu suda bak'insu.
Niko da Munubiya muka shiga raira sabon kuka, munubiya ta kamo hannuna ta rik'e anata. “Munaya dan girman ALLAH kibarni Na kar6i hukuncin laifina, nice Na aikata bakeba, miyasa zaki cema iyayenmu kece? kibari nafad'a musu gaskiya please �?. “A'a Munubiya, wannan laifin nawane, karki manta ta sanadina abinnan yafaru, da ace Fu'aad bai kaimu plaza d'innanba da hakan bata faruba wlhy, munubiya farincikina fansane agareki, har abada bazan iya juriyar ganinki cikin k'unciba, Dan Girman ALLAH koda da wasa kar wani agidannan yaji banice Na aikata abunnanba koda kuwa innarmu Ce, namiki alk'awarin zan jure duk wata fitina dazata taso, zankira Fu'aad yafito muyi aure, duk da naso ace rana d'aya aurenmu zai kasance, amma haka ALLAH ya k'addara mana�?. rungume juna mukayi muka kuma fashewa da kuka, cikin shashshekar kuka Munubiya ke fad'in “mi mukaima Wanda ya k'ulla mana wannan sharrin? mi muka tare masa agidan duniyarnan Munaya?�?. “ban saniba Munubiya, bansan waneneba? Amma nafi zargin gidan wannan jaridar, aganinsu sun sami babban labari, bara su buga suyi suna, Sun zaluncemu Munubiya, sun yad'a labarin abinda ba haka faruwarsa ta kasanceba, Galadima ko ta6aki baiyiba amma suka saka har yana kissing d'inki, wane irin zaluncine wannan? wlhy nima bai ta6a niba da mukayi karo a filin idi, amma ki duba hannunsa rik'e da nawa ajaridar, Munubiya banga laifin iyayenmu ba, kowanne mahaifa bazasu so ganin wannan mummunan abinba, kuma ko zamu kwana rantsuwa bakowa zai amince damu ba, INA tausayama innarmu, ada Yaya muka k'are ma a gidannan bare yanzu?, munubiya innarmu innarmu, banason innarmu tashiga mummunan hali akanmu, yazamuyi innarmu ta fahimcemu, koda ace kowa bai yarda damu ba inason innarmu fahimcemu munubiya.....�?
“Na fahimceku 'ya'yana, tabbas nashiga tashin hankali da ganin hotonku a jarida, kuma a yanayin da kowace uwa ba zataso ganin 'ya'yanta a wanna halinba, kuma ace bazata shiga fiyeda yanayin Dana fad'aba, sai dai ni ba abinda naganine yasakani cikin rud'ani irin haka ba harna yanke jiki na fad'i, cin zarafin innaro ne. 'ya'yana nasan bazaku aikata koda makamancin hakanba, dan naji ajikina sharri akai muku.....�? Da gudu suka sakko a gadon sukazo suka fad'a jikin innarsu suka cigaba da raira kuka harda ita kanta innar, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru. Duk suka nutsu suka mata bayanin komai, har Munaya ta d'akko wayar da Galadima ya barta da ita a filin idi ta nuna musu. Nanna INA ta kuma fahimtar akwai 6oyayyen al'amarin abinda basu saniba akan lamarin, kuma tafi zargin k'ullin Anma Galadima ne kawai, 'ya'yanta k'addara Ce ta sakasu cikin sark'ak'iyar, itadai Addu'arta ALLAH ya fiddashi da 'ya'yanta baki d'aya, saitaji yabata matuk'ar tausayima. Suna cikin haka saiga mama Rabi'a dasu Ayusher, nanma aka kuma zaman warware zance, mama Rabi'a da inna suka kuma fahimtar komai yanda yake. Nasiha suka Shiga yima 'ya'yan Nasu mai ratsa jiki, sannan suka nuna musu illar biyema samari batareda wani dogon tunaniba, duk sai jikin su Munaya yayi sanyi, sun fahimci bin Fu'aad dasukayi plaza shine yazama babban kuskurensu. Sun nemi gafarar iyayen nasu akan hakan dasuka aikata, daganan suka Shiga tattauna maganar Auren munaya da Abba yakafe akan nanda sati biyu. Sun Yanke shawara akan akira Fu'aad, inhar da gaske yakeyi to saiya fito kawai. Akan wannan shawarrar suka zauna gaba d'aya.
★★.★★.★★.★★.★★
Har suka Isa cikin masarautar Galadima baiko motsaba, yana tangad'i da layi yashige 6angarensa, daga Muftahu har Harun babu Wanda yayi yunk'urin binsa. Tunda yaje yazube saman 3seater bai sake sanin inda kansa yakeba saboda matsanancin ciwon kai dake damunsa, da k'yar ya iya gabatar da sallar magrib da isha'i a lokaci d'aya, a saman abin sallar ya kwanta rigingine dafe da goshi, yana kwance shiba mai barciba shiba ido biyuba.
8:30pm dukkan mai ruwa da tsaki a meeting d'in ya hallara, hatta da sarki gaba d'aya, sai dai kuma babu Galadima babu dalilinsa har mama Fulani tafito. (Babbar magana 😨) na fad'a a raina, saboda ganin tsantsar mulki da isa ajikin hamshak'iyar tsohuwa dazata iya kaiwa shekaru 77 a duniya, sai dai tsantsar hutu da gayu ya 6oye ziryan d'in tsufan nata, gata da k'aramin jiki kuma, daka ganta haka bafulatanar asali. Tunda ta fito kowa a falon yamik'e tsaye saboda girmamawa a gareta, amma banda sarki, ya risinar da kansane kawai alamun girmamawa ga mahaifiyar tasa. Saman kujera 2seater ta zauna cikeda izzar mulki, (saikace itace sarkin🤦🏻♀) sai da ta gamaima kowa dake falon kallon tsaf sannan takuma kamewa, cikeda k'asaita tace, “Shi yana ina? Ko raini. Hankalin nasane ya hanashi zuwa?�?. Kowa dake wajen yasan galadima take nufi, babu wanda ya iya cewa komai sai wani matashin saurayi dazasu iya zama sa'annin juna da galadima, ya gyara zamansa yana wani 6ata rai shima, “Granny kinsan halinsa aii, ba ganin kowa da gashi yakeba a masarautar nan mtsoww�?. Mama Fulani ta turo hanci ga bada, cikeda fushi ta bada umarnin a kira mata jakadiya. babu dad'ewa saiga jakadiya tashigo, k'asa ta zube tamkar zatayi mata sujuda tafara fad'in “ALLAH yaja zamaninki ranki ya dad'e, kinga taki kinga tawasu, fatanmu kiga tawasun wasuma, Sarautar gagara badau a hannunki take, domin kaida kaya ai duk mallakar wuyane, duk mai shirin ganin barcinki ya tabbata shima bazaiyi nasaba, kece k'i gudu samaza gudu, jaruma mai dad'and'en tarihi, kin ajiye tarihin da babu wanda yake dashi a masarautar nan, koda kuwa mai martaba gagara badaune, ALLAH ya tsare gabanki ya tsare bayanki, mace mai kamar maza, mazanma a tafin k'afafunki suke ya uwar gijiyata�?. Sosai kirarin jakadiya yayima mama Fulani dad'i, takuma kishingid'a a kujerar, cikeda izza tace, “inason ganin Galadima yanzunan�?. Angama damusa k'i sabo, cika umarninki wajabtaccene a gareni 'Yar sarki, matar sairi kuma mamar sarki, wata ran kakar sarki, ki huta lafiya babbar giwa�?. Fita jakadiya tayi. Ta isa 6angaren galadima, inda sarkin k'ofa yashiga domin yimata iso, halin daya isake shugaban nasa ya razanashi, amma haka yadake ya isar da sak'on jakadiya. Da k'yar galadima yay masa nuni akan yabarta tashigo. Babu dad'ewa saiga jakadiya, ta rusina cikin girmamawa ta gaisheshi, bata damu da rashin amsawar tashiba ta isar da sak'on mama Fulani. hannu kawai ya iya d'aga mata.
Kusan mintuna 7 da fitar jakadiya yamik'e dafe da kansa dayakejin tamkar zai fad'o k'asa, jiyay falon na juya masa, ya dafe bango da gyar kusan 2munute sannan yad'an lafa, haka yafito yana d'an tangad'i, wajen mota yanufa, dan bazai iya zuwa sashen mama Fulani da k'afaba, saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu. Da sauri sarkin mota yataso ya bud'e masa, shima shiga yayi mazaunin driver, sauran dogaranma suka shishshiga mota. Da k'yar galadima yafurta “sashen mama Fulani zamuje, sauran su zauna�?. cikin girmamawa sarkin mota ya amsa, sannan ya sanarma sauran dogaran.
dukkan jama'ar dake falon idanu suka zuboma Galadima daya shigo dafe da kansa, baima kowa magana ba yasamu can gefe ya zauna, har yanzu hanunsa na saman kansa, muryarsa a shak'e yace, “barkanku da dare�?. Hakan yayi masifar k'ona ran mama Fulani, saboda ma ya rainata tare zai gaidata da kowa? kuma bazaizo gaban taba ma yabata girmanta?. A falonma wasu sun amsa wasu basu amsa mishiba, shi baima San sunayiba, ta kansa kawai yakeyi. Cikeda izza mama Fulani tace, “to isashe, gaisuwar ma saina rok'a ko yaya�?. Dukda halin dayake ciki bai hanashi sakin guntun murmushiba, ya janye hannunsa daga goshinsa, idanunsa dasuke matuk'ar jajur yad'ago ya kalleta, ba mama Fulani niba kowama a falon ya firgita daganin idanunsa, hakan ya tabbatar musu da bashida lfy kenan. Ahankali Yakuma furta “bagykanki da hutawa�?. “ALLAH yarabamu da bak'in hali�? . ‘mama Fulani tafad'a batareda ta amsa gaisuwar ba�?. Baice uffanba ya maida kansa ya duk'ar, tareda kuma tallafe goshin yana ta6e baki. Idanun Ummu Hasheem yacika da kwalla saboda tausayin Galadima, ko kad'an batasan bashida lafiya ba, dukda d'azun ta aika bayinta su duba matashi suka tarar yafita.
Mama Fulani kam baki ta k'ya6e tareda kuma hard'ewa a kujera, takai dubanta ga wani dake gefenta, Matawalle! ahad'amin video call da Zeenah yanzunan�?. “angama ranki ya dad'e�? Dan danan yahad'a video call bayan yakira wata number, wata kamilalliyar matace ta bayyana ajikin System d'in, tana sanye cikin shigar kamala, kallo d'aya namata Na hango kamannin Galadima tartare da ita, dukda kamar tafisa haske, hakkane ya tabbatar min da Momma ce. Cikin girmamawa ta gaida mama Fulani, ita kuma ta amsa cikeda k'asaita sannan tafara magana kamar haka. “nasan kowa yasan miya taramu anan wajen?, bana buk'atar maimaita wannan shed'ancin a harshena, wanda kuma ya aikata yasan kansa, Dan haka hukunci biyune, yanada za6i aciki. Na farko tozarcin da yayama masarautarnan da zubar mana mutunci mun haramta masa auren kowacce yarinya data fito daga kowacce masarauta, na biyu ya gaggauta fidda matar aure acikin shekararnan kafin yaje yayma wata ciki a waje akawo mana d'an tsakar gida a masarauta, kokuma mu muza6a masa acikin bayin gidannan, hukunci na farko babu sasauci acikinsa kuma babu canji, Na biyu yanada za6i nemowa komu nema masa. Wannan shine tabbataccen hukuncin kotun fulani. Idan akwai mai abun fad'a sainaji?�?. Kowa ya girgiza kai alamun a'a, wasu hukuncin bai musu dad'iba, wasuko yamusu fiye da zaton mai karatu.
A hankali Galadima ya yunk'ura yatashi batareda yacema kowa uffanba yanufi hanyar fita. “to fand'ararre, daka tafi ba'a gama magana ba ai uwarka zataji, mara mutunci mai bak'in hali�?. Juyowa Galadima yayi ya kalli mama Fulani, wani k'asaitaccen murmushi ya sakar mata sannan yay salute nata yafice abinsa�?. Mafi yawansu saida suka zaro idanun mamakinsa, dama Kowa yasan galadima baya tsoron mama Fulani a masarautar, duk masifarta saima yagadama yake amsata, gaisheta kam saiya zo k'asar yatafi ma bata ganshiba. Iya kacinta tayi masifarta da sababi ta hak'ura, babu yanda ta iya dashi. Murmushi kawai shima sarki yayi baice komaiba. Mama Fulani kam kasa koda motsi tayi a kujerar saboda abin kunyar da galadima yayi mata gaban kowa, ta tsani shed'anin yaronnan mai ido a tsaitsaye dabaya shakkar kowa. Kwafa tayi sannan tatashi tabar falon tana tafiya cikeda mulki da izza. Gaba d'aya suke fad'in ALLAH ya huci zuciyar sarauniyar sarakuna. Duk abinda ke faruwa Momma naji kuma tana gani, amma dayake Galadima yana bayan laptop d'in bataga miyayiba, hasalima bataji ko sau d'aya yayi magana ba, hakanne ya tada hankalinta, mama Fulani Na barin wajen ta katse call d'in, waya ta d'auka takira number Galadima, amma harta tainke bai d'agaba. Kira Na biyu ta sakeyi, hakan yay dai-dai da shigowar Galadima falon dafe da kansa. Da k'yar ya iya d'aga wayar, muryarsa a shak'e yace, “Momma zan kigyaki anjima�? bai jira cewarta ba ya yanke wayar. Hankalin Momma yakuma tashi, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, da sauri ta danna kiran Harun, yana d'agawa ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace, “Harun maza jeka duba min Moh'd yanzunan�?. Yanda yaji Momma Na magana shima kansa saiya kid'ime.....
�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?.�?
Ayusher tafita tasiyo min credit domin kiran Fu'aad. Jikina a sanyaye nagama loda katin, tunani nakeyi shin Fu'aad zai kar6eni bayan yaji abinda yafaru a jiya zuwa yau? tunda komai akan idonsa yafaru. Na dad'e ina juya wayar a hannu kafin Nayi dialing d'in Number d'insa d'in, harta tsinke bai d'agaba, ban damuba Na sake kiransa da tunanin ko baya kusa da wayarne. Bugun farko kuwa ya d'aga wayar...........✍�?
Humm masu karatu, mi kuke tunanin zai faru tsakanin Munaya da Fu'aad a waya, zai kar6eta kokuwa sa6anin haka?. Yaya zata kasance ga Galadima kuma?.
Wannan amsar tana a page 12 da zaizo muku ranar Monday😃👌🏻.
Barkanku da juma'a.
Musha weekend lafiya🤝🏻🥰🥰.
Team *_INNARO & MAMA FULANI_*🥴🥴⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*😭👏🏻 [4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_* _(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_* _{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉1�?2�?
.......Murya a sanyaye Munaya tace, “Assalamu alaika�?. “wa'alaikissalam�?. ‘wata murya ta amsa sa6anin Fu'aad�?. “Uhhm 'yar uwa please, ko ina mai wayar dan ALLAH?�?. “Mai wayar kuma? ai nice mai wayar�?. Wani iri munaya taji a zuciyarta, suka kalli juna itada Munubiya dan a Hans free tasaka wayar. alama munubiya tamata akan tayi magana. kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, “ayya 'yar uwa sorry dan ALLAH, wlhy wanine yabani number d'innan mai suna Fu'aad�?. “Fu'aad!�?. ‘yarinyar ta maimaita daga can�?, saikuma tace “to gaskiya 'yar uwa yabaki wrong Number, ni sunana Afnan, ina Katsina state ne�?. Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Munaya, “shikenan ngd sis..., kiyi hak'uri�?. “no babu damuwa�?. Bayan Munaya ta katse wayar ta dafe kai tana hawaye, daga Ayusher har Munubiya basa Neman k'arin bayani, tunda sunji komai, Munubiya ta share hawayenta tana murmushin takaici, “kibarshi karki sake kiranshi, nasan shine yabama yarinyar nan wayar akan tace wrong number ne, ya ALLAH ka kawo mana sauk'i a wannan lamari dai�?. Tsaki Ayusher taja, ta kamo hannun Munaya “sweet sis..., please wannan karya zama abinda zai ta6a zuciyarki, ki d'auki hakan matsayin ba komaiba, kuma hakan da Fu'aad yayi yasani kuma tabbatar da zargin danake a kansa, ku duba yanda yazage saimunje birnin gayu plaza aranar�?. Gaba d'ayansu zuba mata ido sukayi cikin wani yanayi. Feena dake kwance tatashi zaune, “humm aini wlhy tunda zancen jaridar nan yafito zargina yana kan Fu'aad ne, Na barine akirashi dama danna sake tabbatarwa�?. Munubiya tace, “sisters nifa duk Na kasan fahimtar zancennan naku fa, zargi babu k'yau ai, miye ribarsa idan ya aikata hakan? dukama yaushe muka San juna dazai yi hakan a garemu? yarasa kuma dawa zai mana hakan sai galadima?�?. Zama Ayusher ta gyara, tafara musu bayani dalla-dalla. “tad'ora da fad'in kinsani ko saboda galadiman yayi?�?. “to amma Dan zaima Galadima mu miye Na had'awa damu kuma?�?. “wannan amasar tana wajen Fu'aad sister �?. Hankalin Munaya yatashi ainun, itafa ko kad'an bata ta6a kawo Fu'aad acikin wad'anda take zargiba, amma maganar Ayusher tasata dogon nazari yanzu, duk da dai bawai tama yarda baneba kwata-kwata..
★★★★★★★★★★