Raina kama book 2 - Chapter 3
Raina kama book 2 Chapter 3: Raina kama book 2 Chapter 3. Tun bayan tafiyar Galadima saina zama wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai,…
4,342 words
Tun bayan tafiyar Galadima saina zama wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai, gaba d'aya yinin sai nayishi wani babu dad'i, ga gabana yanata yawan fad'uwa, jinake kamar wani al'amari yana shirin faruwa da rayuwata. Sauban ma sarkin tsokana kasa shiru yayi saida yay magana. Bayan ya dawo school sai muka tafi asibiti, tunda Na gaida Abie da Momma da Aunty Mimi saina koma gefe nayi shiru abina, ciwon jikine kawai ke nuk'urk'usata, dan ga6o6ina masifar ciwo sukemin, narasa wannan dalili? zazza6inma banaji yanzun, ga yawan fad'uwar gaban dana yini inayi, sai kasa kunne nake naji ko Galadima zai kira wani a 'yan uwansa yace ya sauka lafiya, dan zuciyata tafi karkata da fargaba a kansa. Shirun da Sauban yaga nayi shine ya kalleni yana dariya k'asa-k'asa. “Aunty gimbiyarmu har kin fara kewar Hubbin naki halan?”. Idanu nad'an waro ina kallonsa, ganin su Momma Na dariya saina 6oye face d'ina cikin veil d'ina ina fad'in “kai yaa Sauban ALLAH a'a”. Dariya suka kuma sanyamin, Abie nata murmushi shidai, Momma tace, “A'a Mrs Galadima kifad'a gaskiya dai?”. Kunya takuma lullu6eni, saina k'udundune kaina gaba d'ayama a gyalen saboda. ina k'aunar wannan family sosai a raina, saboda nima suna nunamin tsantsar k'auna, ko yau nabar cikinsu auren contract d'inmu yak'are bazan manta da alkairinsuba a gareni. Haka nagama shirin barci Na kwanta a gadonsa ina shak'ar k'amshin turarensa danakejin dad'insa fiye da da. nadad'e ina juye-juye banyi barciba saboda damuwace cinkushe da raina, ga zazza6i mai zafi ya rufeni, bansan ina Galadima yajeba balle nayi tunanin samun number na kirashi, Na gwada number shi ta nan India tak'i wucewa, dama a wayar Samha Na d'auki number bama ta saniba, yau babu mai kulawa dani, sainaji wata kewar innarmu da Munubiyata sun dawomin sabo fil a zuciya. Sai da dare yakusa rabawa kafin barci mai nauyi ya d'aukeni.
_____ .★. _____ .★. _____
Har yamma ba'abari kowa yaga Abba ba, 'yan gidanmu sunci kuka harsun gode ALLAH, Su Munubiya da dukkan yaran gidanmu Na ma'auri tuni labari ya iso musu, kuma duk sun tattara a asibitin suma. Doctor d'in dayake kan Abbanmu ne yafito yana basu hak'uri akan suje gida hakanan, dan gaskiya baza'a bari suga Abba ba a yau. Sabon kukane yatashi, musamman ga innaro, idan ka kalleta dolene tabaka tausayi wlhy, yau babu jarabarnan da rashin mutunci, kuka take da fad'in Auwalu karya tafi ya barta.......... Sambatunta yakuma raunana zukatan mutane da yawa a wajen. Munubiya tayi yunk'urin kirana amma network yahana, da Yaa marwan yakula da hakan kuma ya hanata, yace karta sake ta sanarmin yanzu. Wannan dalilin yahana a sanar min d'in. Kowa zuciya babu dad'i suka tattara suka tattafi gida, dady da baba k'arami, yaa hameed yaa shafi'u da ya Naseer aka bari a asibitin zasu kwana. Ranar duk Wanda yasan gidanmu yasan babu lafiya, Dan gidan yayi tsitt, kowa tashi ta isheshi a zuciya, barcima k'alilanne daga cikinsu suka yisa.
___________________________
Sosai hadimansa sukayi farincikin ganinsa, kamar yanda shima yay farin cikin ganin Nasu, sud'in mutanene masu muhimmanci a rayuwarsa, sunzama wasu 6angare na duniyarsa. Kwance yake a bayan motar idonsa a lumshe, ya saki guntun murmushi saboda tinano yanda zata k'are masa a wajen Momma, koda wasa bai sanar mata Nigeria zai zoba, yayi hakane kuma dan kartayi yunk'urin dakatar dashi ma. jin alamar motar ta tsaya ya bud'e lumsassun idanunsa tareda furzo k'aramar iska, duk da isowar dare yayi hakan baisa sauran hadimansa sun kwanta ba, ya iskesu zazzune a k'ofar sashensa suna jiran isowarsa. Dogarin daya bud'e masa k'ofar yafara k'ok'arin d'aukar briefcase d'insa domin shigar masa. Shima ziro k'afarsa d'aya yayi ta inda aka bud'e masan, ya zuk'i iskar masarautarsa tareda fesota tabaki yana lumshe idanunsa, ko ina kwanyar yake da hasken lantarki tamkar rana, duk lokacin daya zo cikin masarautarsa, mahaifarsa, yakan tsinci kansa cikin tunano abubuwa masu d'aci da rad'ad'i a zuciyarsa, yakanji inama ace shid'in ba kowa baneba, inama ace shid'in talakane fitik mai tarin kwanciyar hankali, da za'ace yaza6i rayuwar dazaiyi, da zai za6ama kansa zama talakane, dan babu Wanda yakai talaka kwanciyar hankali inhar yanada k'yak'yk'yawar zuciya da wadatar zuci, amma babu komai a cikin dukiya da mulki sai damuwa darashin kwanciyar hankali, kai kenan kullum cikin rashin nutsuwa, idan kayi wasama ibadar da ubangiji ya halicceka dominta bazakayiba, ya had'iye wani Abu mai d'acin gaske a mak'oshinsa. sannan yashiga k'ak'aro murmushin dole ga sauran hadimansa dake gida basuje tarbarsaba. daka kallesu kasan suna cikin tsantsar farincikin ganinsa, dan sunyi kewarsa, shima hakance agaresa. bayan sun gama gaggaisawa ya tambayesu lafiyarsu sannan yashige ciki. Ko ina k'al yake tamkar yanda yake buk'atar ganinsa, (hadimansa nada k'ok'arin tsaftace sashensa koda baya k'asar). Zama yay bisa kujera yana fad'in “ya ALLAH! Alhmdllh”. Dogarin daya shigo masa da jakka yakuma masa sannu da zuwa sannan yafice. Yakai mintuna 5 a wajen zaune, sai k'ullawa da kwancewa kawai yakeyi, ga gajiyar zaman jirgi na nuk'urk'usarsa data rashin isashen barci dabasa samu shida Munaya. da k'yar dai yamik'e zuwa bedroom d'in, komai need sai k'amshin mayen turarensa da air fresheners mai sanyin dad'i ke tashi, ya ajiye jikkarsa a kan gadon sannan yafara zame kayansa danya samu ya watsa ruwa.
Ya d'an jima a bayin sannan ya fito d'aure da towel, yana tsane fuskarsa zuwa kai dawani. wardrobe yabud'e ya d'akko boxes kawai yasaka, sannan ya saka jallabiya, sallolin da suka riskesa a hanya ya rama, yana idarwa yacire jallabiyar, matsawa yay jikin mirror ya fesa turare kad'an ya hau gadonsa da yay missing. harya kwanta yatashi zaune, briefcase d'in dayazo da ita ya bud'e, ya Ciro wayoyinsa tareda layinkansa na Nigeria duk ya saka, sannan ya ijiye wayoyin, insha ALLAH zuwa lokacin da zai tashi yana fata komai ya dai-daita. Addu'ar barci yayi ya gyara kwanciya, amma sai barci yace bai gadaba, tunanin ahalinsa daya baro wata k'asa ya dabaibaye zuciyarsa, wata kewarsu ke tsikarar zuciyarsa, yanzu yasan Abie yayi barci, hakama Momma watak'il ta kwanta, dan macece mai yawan k'iyamull laili, duk da a asibiti takan kwana hakan baya hanata kusanta kanta ga mahaliccinta, Aunty Mimi da Samha ma yasan sunyu barci, Sauban ne dai dakamar wahala ace ya kwanta, ya juya kwanciyar sa yana murmushi, zuciyarsa tace “to matar contract fa?”. ya d'age kafad'a da ta6e bakinsa kad'an, saikuma yasaki k'aramar dariya, daren jiyane kawai ya fad'o masa a rai, yau kuma koyaya ta yini ta kwana? (danba time d'inmu d'aya da India ba), a fili yace, “ALLAH yasa yau dai babu zazza6in, my Friend kin cika taurin kai, dakin yarda nakaiki asibiti zanfi samun nutsuwa, oh god🤦🏼♂”. ‘ya k'are maganar da dafe kai’. Shima yajima baiyi barciba, sai can dare yaja da nisa sannan ya saceshi.
Da asubahi da k'yar ya iya tashi, alwala yay yafita massalaci, bayan an idar da salla yafito suka had'u da Sarki da jama'a keta zubewa suna kwasar gaisuwa. Sarki yayi mamakin ganinsa, dan har saida fuskarsa ta nuna hakan, murmushi kawai Galadima yayi yana rissinar da kansa k'asa. Sarki baice masa komaiba yanufi sashensa, sai Galadima yabi bayansa, dogarai kuma suka take musu baya, bayan sun gaida Galadima d'in.
A hamshak'in falon mai martaba na farko suka yada zango, Sarki na zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu, Galadima na k'asa kusada k'afafunsa. Kukun Sarki ne suka shigo shida jakadiyya bayan sunyi sallama.. K'aramin tire suka ajiye dake d'auke da butar shayi, sai mug da wani k'aramin bowl mai k'yau anzuba sukari, sai jug k'arami shima an zuba tataccen lemon tsami, saikuma Zuma shima a k'aramin bowl. Kuku da jakadiyya suka zube gaban mai martaba suna kwasar gaisuwa, sannan suka gaida Galadima shima da masa barka da zuwa. Cikeda kulawa ya masa musu, har kuku ya durk'usa zai had'ama mai martaba shayin Galadima ya dakatar dashi, tareda masa nuni dayaje abinsa. Kuku ya rissinar da kai alamar girmamawa sannan suka fice shida jakadiyya suka basu waje. Galadima ya had'ama Mai martaba shayi da ruwan lemon tsami kamar yanda yasan yana sha a kowacce Safiya, (ada mahaifinsa yasani da wannan al'adar, dan awajensa Sarki jalaludden ya koya). cikeda girmamawa ya mik'ama mai martaba mug d'in, kar6a yayi yana masa murmushi, sannan yace “kaifa?”. Girgiza kai Galadima yayi, yace “a'a Abba, wannan sai ku”. Mai martaba yay murmushinsu na manya sannan yace “Saukar yaushe Sameer?”. Galadima yad'an shafa wuyansa, cikin tsantseni yace, “da daddare Abbah, wani business ne ya kawoni, inaga insha ALLAH zamu bud'e company anan Nigeria saboda muma matasanmu su Mora daga guminmu”. Murmushi mai martaba yayi, ya kur6i shayinsa sannan yace “tunani mai k'yau yarona, ALLAH yasaka hannu a lamarin. ya jikin d'an uwana dasu auntyna Zeenah?”. “jikin Abie Alhmdllh Abba, dan bayan tahowarku sauk'i yakuma samuwa gaskiya, Momma kam suma lafiyarsu lau”. “to Masha ALLAH, tareda iyalin naka kazo kenan?”. “a'a Abba, ni kad'ai nazo, saina kammala abinda nazoyi itama idan zan dawo zamu dawo tare”. “to ALLAH ya tabbatar”. “Amin Abba, bara naje nad'an kimtsa mu gaisa da jama'a, dan zan d'an fita”. “ok, ALLAH yayi Albarka”. “amin Abba, a huta lafiya”. Hannu kawai mai martaba ya d'aga masa, Galadima kuma yafita.
Babu inda ya Shiga, ya koma sashensa domin yayi shiri. saida ya had'a coffee da kansa kamar yanda ya saba idan yazo k'asar, ya zauna yasha danba abincin kowa yakeci a masarautarba, ko Ummu hasheem bayacin abincinta kota kawo, duk da kuma kulawa datake nuna masa fiye da kowa a gidan, gimbiya zulfah uwargidan sarkima tanada k'ok'arin aika masa abincin inhar yazo, amma ko kallon kulolin ma bayayi, saidai bayinsa su cinye.
Yafito wanka yana tsane jikinsa wayarsa tayi k'ara alamar shigowar sak'o, wayar ya d'auka danya duba ko company ne, dan yana fatan ace komai ya daidaita ne, yanason kiran su Momma yaji Yaya jikin mahaifinsa. Ganin number ce sai abin yabashi mamaki, bud'e sak'on yayi kawai azatonsa ko Nuren ne.
_Gargad'i!! tabbas sirikinka ya tsira a wanan karon, amma ka tabbatar masa next time bazamu barsaba, saimun raba ruhinsa da gangar jikinsa!!!!.................._✍🏼
*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_* [7:28PM, 6/13/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: *_Typing📲_*
*_Haske writer's asso...._*💡
*_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻
~Book 2~ 👉🏻4⃣
.............Cikeda tsantsar mamaki Galadima ya jujjuya wayar a hannunsa, kai kace itace zata fassara masa ma'anar sak'on, kuma komawa yay yana karanta sak'on a karo na biyu, a fili yace, *“SURIKI! SURIKI!.* to nikam wanenen sirikina?”. A take zuciyarsa tabashi amsa da *Baban matarka ta contract*. wata fad'uwar gabace ta samesa lokaci guda, wadda ALLAH ya tak'aita bata buga da bugun zuciyarsa ba, cikin tsitstsinkewar tunani dana zuciya yashiga bitar message d'in kamar mai haddar karatu, idan ya fahimci sak'onan dai akwai mummunan al'amari daya faru akan mahaifin munaya kenan? “ya salam”. ‘ya furta a fili, cikin dafe kansa yakuma fad'in “to adalilin mi wani abu zai samesa kuma yazam kamar yashafeni?”. gabansa yakuma fad'uwa, mutuwar Alhaji Abdussalam Abba mahaifinsu Samha ta dawo masa a rai, (mijin aunty Mimi). dafe kansa dake shirin sara masa yayi, to mizai kawo Abban munaya cikin case d'insa kuma? Sam bazai yuwuba ma, koma dai by mistake wani yaturo masa sak'on ne?. “mtoww! K'ilama hakane”. ‘yay maganar a fili yanajan guntun tsaki, tareda jefa wayar kan gado yacigaba da shirinsa. Shiri yake amma yakasa fidda abin a ransa, koyayi k'ok'arin ture tunanin gefe sai yakasa, dukda zuciyarsa tak'i yarda ta gaskata sak'on nasane. shiri ya kammala cikin Ash color d'in shadda gizna dakakkiya, tamasa k'yau ainun, komai nasa saiya saka Ash, Takalminsa helf cover, agogo da hula duk ash, ya kwashi phones nashi a hannu, ya fesa turare da gyara zaman hularsa sannan ya ciro wayarsa d'aya a aljihu, dan yakasa daurewa, number yaa marwan ya lalubo ya kirasa.
A time d'in yaa marwan nata lallashin Munubiya tasha shayi sutafi asibitin amma tak'i, ta gardame akan ta k'oshi itadai su tafi kawai, mama Rabi'a dasu Ayusher sunyi lallashi amma tak'i yin shiru tasha, sai kuka take, hakan yasaka feena zuwa d'akin yaa marwan takirasa, shine yaketa lalla6ata amma tak'i kar6a, sai kawai ya had'e fuska ya koma mata ainahin marwan da bai d'aukar raini, cikin daka tsawa da hargagi yamik'a mata shayin, jiki na rawa takar6a tafara sha, tayi nisa dashan tafara amai kuma, mama Rabi'a tarik'eta, sukuma suka shiga mata sannu, yaa marwan na dafe da kansa cikin damuwa kiran Galadima ya shigo masa, kamar bazai d'aukaba saikuma yaciro wayar a aljihu ya diba. Mamakine ya kamashi dayaga sunan Galadima ta Nigeria, (ko sunzo k'asarne?), da hanzari ya d'auka tana gab da katsewa. Yanda Galadima yaji muryar yaa marwan yayinda yake amsa masa sallama sai hankalinsa ya tashi, ko gaisuwar kirki basuyiba Galadima ya hau masa tambaya akan Abba. Yaa marwan yace “gaskiyane ranka ya dad'e, jiya misalin 12pm Abba yayi accident, sunyi taho mu gama da wata thriller, yanzu hakama yana general hospital”. Zufar dake tsatstsafowa a fuskarsa yasa handkerchief ya share, muryarsa na rawa yace, “Marwan da gaske?”. Kula yaa marwan yayi Galadima kamar ba a hayyacinsa yakeba, shima muryarsa na rawa yace, “da gaskene ranka ya dad'e”.
“hasbinallahu wani'imal'wakil” Galadima yafara maimaitawa akan la66ansa, ya sauke wayar a hankali zuciyarsa na wani irin suya, yama rasa wane kalar tunani yakamata ace yayi? Yaya zai fassara wannan lamarin? Kenan akwai wani Abu dabai saniba, kodai Abban munaya yanada wata masaniya akan lamarinsa, kokuma bai saniba yafad'a tarko, tabbas yakamata ma akan kansa yay wannan tunanin kodan abinda yayta faruwa tsakaninsa da Munaya, cikin k'araji yace “MUFTAHU!! kasan komai, dolenema kasan komai muftahu!!!, tabbas duk da kasancewarka d'an uwana, jinina, saina binneka da ranka a tsakkiyar masarautarnan inhar mahaifin matata ya rasa ransa wlhy, wannan ALWASHI NANE!!. ya k'are maganar yana buga table glass dake gabansa da masifar k'arfi, aiko ya tarwatse a wajen, kwalba ta yanka masa hannu. baibi takan ciwon dayaji ba yamik'e a harzuk'e ya d'auki wayar ya fice.
A yanda yafito sai hankali hadimansa ya tashi, ga hannunsa yana d'igar da mini kad'an-kad'an, kuma suna gaisheshi yak'i amsama kowa gaisuwarsa, ko hannun daya saba d'aga musu inbaya buk'atar maganar yau basu samuba, da kansa yabud'e motar yashiga, hakan yasaka sarkin Mora Shiga da hanzari shima shida sauran dogaran dakan bisa in zai fita. Ko takan zuwa fada yay gaisuwa baibiba, suna fita daga masarautar kiran Nuren yashigo wayarsa. Yana d'agawa yace, “kajiramu a plaza”. ‘abinda yace kenan kawai ya Yanke wayar'. Nuren yabi wayar da kallo, inhar kunnensa yajiye masa dai-dai to ran Galadima a matsanancin 6ace yake, to mi aka masa? kokuma shida mutuniyar tasane mama Fulani? Nuren ya girgiza kai kawai yana murmushi, mama Fulani da Galadima sai addu'a kawai, dan tamkar suna ganin hanjin junane. Tafiyar mintuna 30 takawosu plaza, amma basu shigoba, dan haka Nuren yana hangosu yataso yafito. Matashin Saurayine shima, mai kama da Galadima sosai, dan wandama bai saniba saiya d'auka tagwayene, abubuwa kad'anne suka banbantasu, dan a shekaruma zasu iya zuwa d'aya, shima Nuren dagani yana cikin Hutu sosai, gashi d'an gaye ajin farko cikin nutsatstsun matasa masu ji da kai. Da sauri dogari d'aya yafito ya rissina yana gaisheshi, hannu ya d'aga masa cikin sarauta (hakan ya tabbatar min shima jinin sarautar ne) dogarin yabud'e masa inda Galadima yake ya shiga. Kallo d'aya yayma Galadima ya tabbatar akwai Matsala, hannu yabashi sukayi musabaha, cikin tsantsar kulawa yace, “brother mike faruwa ne?”. Galadima ya kalli Nuren da idanunsa da suka koma jajaye, cikin matsanancin d'acin zuciya yace, “bansan alak'ar data sashi cikin tawa ba”. Nuren yace, “waye?”. Kauda idonsa Galadima yayi daga kallon Nuren, ya maida ga window yana kallon mutane daketa harkokinsu, wani murmushin takaici yayi, sanan yafurta *“SIRIKI!”* Nuren yazaro idanunsa waje, a zabure yace, “yanzu haka yana ina?”. “general hospital ”. Nuren yay hanzarin fad'ama sarkin mota “muje general hospital na garinnan”. “to ranka ya dad'e”. ‘sarkin mota yafad'a a ladabce.
Hannun Galadima dake d'igar jini har yanzu Nuren ya kamo, ya kalli Galadima da alamar tambayar miya damesa? amma shi galadiman sai yamak'i kallonsa, Nuren ya girgiza kai kawai Dan yasan hakan dayayi bazai fad'aba ne, handkerchief d'insa ya Ciro ya d'aure hannun Na Galadima Dan jinin a samu ya tsaya daga zubar, dukya d'an 6ata seat d'in mortar kad'an, da yake a nan ya ajiye hannun daga gefe. ran Nuren a 6ace yace “brother dolene muyi bincike akan Surukinka, dan duk ta yanda zamu fassara a yanzu, zukatanmu bazasu d'aukaba. zamu iya zargin akwaima hannunsa a ciki, zamu iya zargin sunnemi wani Abu daga garesa yak'i basu had'in kai, zamu iya zargin abubuwa da dama”. Iska Galadima ya furzar daga bakinsa, yasaka hannu ya tura hularsa baya, kansa ya jingina da kujerar tareda lumshe idanu. zuciyarsa tana tunani yaushene zai kawo k'arshen mak'iyan mahaifinsa? Sai yaushene za'ayi walk'iya yagansu? yana buk'atar sanin dalilinsu Na za6ar maida masa mahaifi haka, miyayi musu?. Wannan tambayoyin yakema kansa kullu yaumin ta kowacce rana. Hannunsa Nuren yakamo yad'an matsa, Galadima yabud'e idonsa dasuka fara komawa kalar jaa. “brother a wannan karon bana buk'atar 6acin ranka, dan duk sanda ranka ya6aci baka iya Controlling d'in fushinka, fushinka Na saka aikinmu tafiyar wahainiya, lokaci yayi dazaka saba da irin wad'annan abubuwan fa, karinga saka nutsuwa a zuciyarka aduk lokacin da irin haka tafaru, kamarfa yanda takawa (papi) yake fad'a mana ne a kullum, sufa sunayin wad'annan abubuwanne dan kawai su fusata ka, a haukansu zasu iya samun nasara a kankan saboda ciwon da ALLAH ya jarabceka dashi, waynote kaikuma ka karya wannan kwarin guywar tasu OK?”. Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, shima ya dafa hannun Nuren d'in yana lumshe idanu, a hankali yace “Okey it's better”. Daga nan motar ta d'auki shiru, ahaka suka isa asibitin.
Zuwa lokacin jama'ar gidanmu sun kuma cika asibitin, harsu Munubiya duk sunzo suma. Tunda motocin Galadima uku suka shigo asibitin kallo ya koma Kansu, kowa son ganin mai fitowa yakeyi. Dogaraine suka fara fitowa, kafin abud'ema su Galadima. 'Yan gidanmu sun fahimci daga masarautane, amma babu Wanda yay tunanin ganin Galadima d'in. Tunda yafito kwarjininsa da cikar haibarsa ta kasancewarsa jinin sarauta ta cika idanun jama'ar wajen, dogarensa sun tsare ko ina babu mai damar ra6arsa, Nuren na gefen hannun damarsa. Wayyo, nanfa ido yaymasa caa, baya son kallo ko kad'an, amma yaya zaiyi, tunda jama'a sunga abin kallon.🤦🏻♀ Tunkan ya k'araso su yaa Hameed suka mik'e suka nufoshi. Munubiya kam bayansa kawai take lek'awa, azatonta harda 'Yar uwarta. amma ganin babu alamar mace ma acikinsu sai jikinta yay sanyi. Hannu Galadima ya d'agama dogaransa alamar su dakata, baya suka ja, yayinda shikuma yamik'ama yaa Shafi'u daya fara k'arasowa hannu, sun gaisa da yayuna cikin girmama juna, kafin sumasa jagora zuwa ciki inda Abba yake. Dayake su Munubiya suna daga gefene, shiyyasa basu gaisa da Galadima ba, sai k'amshin turarensa daya cika hancinansu. Dukda halin da ake ciki, saida 'yan gidanmu sukaji Hassada, kowa jitake inama mijin 'yartane🤕🥴.
Humm doctor daya hana kowa ganin Abba saigashi jikinsa Na rawa ya tarbi Galadima, daddy da baba k'arami sunje gida suyo wanka, bayan dawowar su yaa Naseer sai sukuma suka tafi. Doctor yama Galadima jagora har d'akin da Abba yake kwance. “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un” kawa Galadima ke iya fad'a a la66ansa, maganar gaskiya jikin Abba babu k'yawun gani, yaa Shafi'u ma mai ragguwar zuciya kasa daurewa yayi yafice da sauri yana hawaye, yaa Hameed kam runshe ido yayi zuciyarsa Na suya kamar zata fad'o k'asa. Galadima ya dafe bango tareda rik'e kansa dayaji ya sara masa, halin da Abba yake ciki exactly dana Alhaji Abdus'salam Abba. Da sauri Nuren yaruk'o hannunsa, a hankali yake fad'in “Control yourself please”. Doctor yajawo kujera biyu yabama Galadima da Nuren dansu zauna. Ina kasa zaman sukayi, dole suka fito. Galadima yabuk'aci ganin doctor d'in.
'Yan gidanmu kuwa fitowar yaa Shafi'u yana share hawaye yasaka zukatansu kuma tashi, caa sukayo kansa da tambayar lafiya. Kasa magana yayi, ahaka su Dady suka samesu, sukansu jiki a sanyaye suka k'araso wajen, kardai ace d'an uwansu yatafi ya barsune. muryoyinsu har rawa sukeyi wajen tambayar lafiya?. Sai alokacin yaa shafi'u yasamu bakin maganar cemusu bafa rasuwa yayiba, jikinnasane sai babu dad'in kallo. Baba k'arami yace, “sun bari kun gansane?”. “Eh baba, Galadima ne mijin Munaya yazo”. Dady da baba k'arami ciki suka shiga, sukabar 'yan gidanmu dake kuka abin gwanin tausayi.
Doctor bai 6oyema Galadima komaiba, yafad'a masa gaskiya jikin Abban yayi tsanani, dan yaji raunuka Na tashin hankali, ga karaya a jikinsa takai hud'u. Galadima ya cije lips d'insa, kafin yace, “ina police d'in dasuka kawoshi nan?”. “ai wlhy yalla6ai basu kwana ba, tun jiya around 11pm suka tafi abinsu, kuma har yau basu dawoba”. Amatuk'ar fusace Galadima yace “Why!!?”. Doctor yagama rikicewa, jiki Na rawa yace “ban saniba wlhy ranka ya dad'e”. Harara Galadima ya watsa masa, yace “saboda kaima bakasan aikinka ba? wai......”. Nuren yay sarin fad'i “Cool down Sameer!”. “haba Nuren, kajifa wani zancen banza, saboda jami'an tsaron k'asarnan basu san aikinsuba, su kawo mutum cikin irin wannan mawuyacin halin amma bazasu dakata suji wani issues akansaba su tafi, bazama su iya zama zuwa washe gariba ko za'a iya buk'atarsu”. “sorry ranka ya dad'e”. ‘cewar doctor a tsorace’. Dady da baba k'arami dake tsaye abakin k'ofa tun d'azun suka k'arasa shigowa, sune suka kwantarma Galadima hankali da nuna masa yayi hak'uri. A girmame ya risina ya gaidasu da tambayar mai jiki. Suka amsa masa da Alhmdllh.
Cikin mintuna 30 Galadima yasa aka canjama Abba d'aki Na musamman, sannan aka kawo police 5 suka zagaye d'akin. Hakan yama familyna dad'i sosai, dansu baba k'arami tun a daren jiya sukaga wasu sunata zagaye-zagaye a k'ofar d'akin da Abban ke kwance, ba k'aramin tsoro abin yabasuba, amma basuda mai taimakonsu, sai addu'a dasukai tayi da Neman tsarin ALLAH akan mutanen. Amma gashi yanzu ALLAH ya kawo musu Galadima. Galadima yasaka doctor yayi shirye-shirye daduk tattara bayanan Abba.
Da k'yar Nuren ya lalla6a Galadima ya amince aka masa treatment d'in hannunsa shima, sai da Dady yasa baki ma, amma da ya dage akan abarsa shifa baya masa ciwo, saigashi hardasu d'inki akayi masa a wajen. Daga nan suka fito daga office d'in doctor d'in, sunason zuwa inda Accident d'in yafarune. Harsun kusa fita Galadima yatuna, ya buk'aci abashi wayar Abba idan babu damuwa. Baba k'arami yace, “ai bama azo da wayarsa asibitin ba gaskiya, maybe ma tana can inda abun yafarune”. Galadima ya jinjina kai kawai suka tafi. Su innarmu sunji dad'in abinda Galadima yayi, innaro sai kwararo masa addu'oi takeyi tana kuka.
____(((★)))____
Zuwa yanzu hankalina yakai k'ololuwar tashi, saboda mafarkin Abba na danayi da daddare, abin mamaki a barcin safema dana koma hakance ta faru, nakuma mafarkin Abba yana cikin mawuyacin hali, a firgice na farka jikina sharkaf da zufa, wayata na lalubo nashiga neman wayar Abbana, amma Switch up, nakira Innarmu network yahanata wucewa, hakama Munubiya, hankalina fa ya tashi, haka naitabin Number's d'in 'yan gidanmu ina kira. Amma daga Wanda zaik'i amsamin sai wadda zan kira switch up, saikuma marasa tafiya. kuka nazauna rerawa babu mai lallashina. A wannan halin Samha tashigo ta sameni, itama hankalinta tashi yayi, takira Momma a waya ta sanar mata gani inata kuka. Babu shiri Momma tabaro jakadiya da aunty Mimi a hospital tanufo gida, dan itama a cikin damuwa take, na rashinjin Galadima. dan bai sanar da ita ina zaijeba, itakuma bata kawo yana Nigeria bane, tunda bai ta6a tafiya bai sanar mataba, tazata tafiyar kota shafi company d'insu ne. Ta iso ta iske Samha nata lallashina, jikinta a sanyaye tazo bakin gadon ta zauna, hannuna ta kamo ta jawoni jikinta, batayi maganaba tashiga shafa kaina da bubbuga bayana, munkai kusan 10minutes a haka, harna bar kukan sai ajiyar zuciya kawai. A tausashe tace, “kiyi hak'uri kinji Munaya, ni kaina hankalina a tashe yake da rashin kiran, dan baita6a hakaba”. (ALLAH Sarki momma ita ta zata saboda rashin kiran Galadima ne, shima rashin jinsa na damuna kam, amma yanzu na Abba ya danne komai). Samha tace, “Momma amma an gwada Number sa ta Nigeria?”. “Samha banyi tunanin can yajeba, amma bara na gwada na gani”. Wayarta ta d'auka ta kira number Galadima ta Nigeria, a mamakinta kuwa saita shiga, cikeda al'ajabi taciro wayar a kunnenta takuma kallon number d'in, tabbas itace dai da gaske. Harta katse bai d'aukaba, takuma kira a karo na biyu.
Lokacin Galadima suna mota zasuje inda Accident d'in Abba yafaru. ganin momma saida gabansa ya fad'i, harta tsinke yakasa d'auka, sai da aka kuma kira Nuren ya d'aga yasaka masa a kunne. muryarsa a sanyaye yay sallama, daga can Momma tace, “lallai Muh'd, yanzu nan dan zakaje Nigeria shine ka 6oyemin? kabi ka tada mana hankali muda matarka, maimakon ma ka sauka kakiramu hankalinmu ya kwanta”. Runtse idanunsa yayi, muryarsa a sark'e yace, “ki gafarceni Momma, wlhy banason ki hanani zuwanne, nazo kuma na iske wani tashin hankali, shiyyasa ban kirakuba”. Mik'ewa Momma tayi tafice daga d'akin, ni da Samha muka bita da kallo, tace “innalillahi.. miya farune Muh'd? ”. Zuciyarsa na suya ya zayyane mata komai daya faru, dukta rikice, “kodai wani yafad'ama Munaya Muh'd?”. “banajin hakan gaskiya Momma, dan mutanen gidansu basuda Nutsuwar ma sanar da ita, amma miya faru?”. “hankalinta gaskiya a tashe yake, dan ina asibiti Samha takirani tana sanarmin Munaya nata kuka, babu shiri nabaro asibitin nazo gida, da k'yar na lallasheta, ni na zatama ko rashin kiran dabaka yi baneba”. “to maybe rashin kiran nawane gaskiya. Amma batasan komaiba, Momma kuma banason tasani harsai yafara samun sauk'i kin...........” Da sauri Momma ta katseshi “bazai yuwuba Muh'd, dolene anema mata ticket ta taho ko itada Sauban ne, mahaifi yawuce gaban wasa, ko kai baka sanar da itaba dolene wani a cikin 'yan uwanta ya sanar mata, bakuma zata ta6a samun kwanciyar hankaliba, mukuma saita mana wani kallo daban na 6oye matan da mukayi”. “to shikenan Momma, Sauban yaje ya bincika ko'akwai jirgin dazaizo Nigeria, saiya nema musu tickets, yanzu muna kan hanyar zuwa inda Accident d'in yafaru, idan na koma gida zan kiraki”. “to shikenan saina jika”.
Momma ta kwantarmin da hankali sosai, sannan takoma asibiti da alk'awarin indai gida nakeso zatasa Sauban ya nema min ticket natafi, amma bata fito ta nunamin ainahin abinda ya faru zanje gidanba. Dukda inason tafiya gida sainaji kamar akwai abinda ake 6oyemin, saboda wannan tafiya ta gaggawa, sai dai ban tambaya ba nabarma zuciyata kawai. Sauban kuma yashiga mana shirin tafiya.
______________________________