Kenza eBookz

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 4

Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 4

Rawanin zalinci 1 complete Chapter 4: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 4. Kamar dai yadda kuka sani ne, daji ne mai matuƙar girman gaske wanda kallon…

3,307 words

Kamar dai yadda kuka sani ne, daji ne mai matuƙar girman gaske wanda kallon iyakarsa ma ba abu bane mai yiwu wa sam sam, sannan akwai haɗari sosai a cikinsa, sai dai haɗarin ta wasu ɓangarori daga cikin dajin ne yake, ba dukka ko'ina bane, muggan namun dawan ba'a ko'ina suke zama ba, suna da ɓangarorin da suke zama a cikin dajin, already kunsa kowani dabba da irin wajen da yake yin rayuwa, ko a daji ba'a ko'ina suke zama ba, sai wajen da ya yi dai'dai da rayuwarsu.

Saman wani katafaren tsauni, a hankali wani hayaki yake tashi daga wajen, da alama akwai mutane a wajen, saboda su dai namun dawa basu shiri da wuta bare hayaki, sam basu so, basu zama ma a wajen da aka kunna wuta, sai dai idan ɗauresu a wajen aka yi babu yadda zasu yi, amma basu son wuta ko ya take.

Sannu a hankali wannan yanaki yake fitowa, kuma bashi da yawa, sannan hayaki ne mai haske ba irin bakin hayakin nan ba, wannan tsauni yana nesa daga in da maman waɗan nan ƴan biyun take, sai dai idan ka tsaya a samanta ka yi magana da karfi, to duk wanda yake kewayen wannan yanki zai jika, saboda dajin tana amsakuwa.

Dai'dai tsakiyar saman wannan tsauni ta gabas ta sakiya, wani jibgegen dutse ne a wajen, yana da girma da kuma faɗi, sannan yana nan tamkar kogo, dan yana da zurfi da faɗi cikinsa, daga ta cikinsa wannan hayaki yake fitowa, kofar shiga cikinsa kuwa, ɗan ƙaramin ne wanda babban abu ba zai iya shiga ba, idan ɗan Adam ya cika ƙiba sosai, to ba zai iya wucewa ta kofar ba, dan bata da girma, sannan akwai wata ƙaramar dutse mai kauri da ake rufe ɗan bakin kogon da shi, alama dai ya nuna wannan ƙaramin dutsen shi ne kofar kogon.

Tamkar gida haka cikin wannan kogon yake, an yi ciki da parlour da wani ɗaki na daban, duk kuma jinin anyisu ne da taɓo, ma'ana an gine cikin kogon, kasancewar yana da girma sosai cikin kogon, sai ya bada abin da ake so, ginin nasu kuma ya fita sosai, duk da cewa da taɓo suka yi shi, ga kuma itatuwan bambu da suka yi amfani da su wajen kawata kujerun zama na saka, tamkar gado haka suka yi kujerun zamar, ma'ana babu Head na kujerun, iya wajen zama ne kawai, haka zalika beds dake a cikin bedrooms guda biyun, dukka da itacen bambu da kuma ganyen ciyawa mai kyau aka yi su, shi ainahin gadon anyi shi da itacen, katifa kuma da ciyawan harawa, sai dai ya saƙu da kyau da kyau ba karya, ya yi matuƙar kyau kuma, an shinfiɗe bed's ɗin da bedsheet na sakar audiga ta hannu, kunsan sakar hannu da masifar kyau, ga shi bedsheet ɗin an yi mai two color, sai abin ya kawata idanuwar mai kallo sosai, ga ɗaukar hankali, wasu kyawawan smalls pillows ne jere a saman beds ɗin dukka ɗakuna biyun, suma pillows ɗin suna sanye ne a cikin rigarsu irin kalar bedsheet ɗin, sun kara kawata beds ɗin sosai.

Komai da yake a cikin wannan kogo da itacen bambu da kuma taɓo aka kyara su, tukunyaye da kaskon wuta duk na taɓo ne, da alama makyarin waɗan nan abubuwa mutun ne mai kaifin basira da ƙwaƙwalwa sosai, dan harda kwanon cin abinci da aka yi da itace, ga su cups, tamkar kowani gida dai, haka suke, harda yi wa kwanikan nasu design kala kala da wani jar kala, sun kuma yi bala'in kyau ba kaɗan ba.

Ƙasar wannan kogon kuwa ya kasance itacen bambu ne suka yi shi kamar tiles, ya kawata wajen sosai, abin da zai kara burgeku da wannan gida nasu shi ne, yadda ya kasance kowane kofar ɗaki da labulen da aka saka da audiga, very talented people's ne suke zaune a wannan waje, dan komai dake wajen basira ce ziryan ta yi aiki a kansa ba kaɗan ba, da akwai ramuka da suka ɗan huhhuda, saboda samun haske da kuma iska a cikin ƙogan, ramukan suna da yawa, amma basu da girma, kanana aka hudasu, kuma haske da iska suna shiga sosai, dan kunsan shi iska baya rena hanyar wucewa, abin kara ɗaukar hankali ma cikin wannan gida shi ne, harda dining table suke da shi a parlourn nasu, dining ɗin shi ma da itacen bambu suka yi shi, ya saku sosai, ya yi matuƙar kawata wajen sosai da sosai.

Ko'ina tsab yake tamkar babu kowa da yake amfani da wajen, sai kamshin kayan itatuwa da yake tashi a wajen.

Kwance a saman ƴar kyakkyawar bed nasa KAMRAN yake, a nasa bedroom ɗin kenan, hannunsa na rike da wani littafi mai matuƙar kyau yana karantawa, da alama littafin tarihi ne, sam ba kayan ɗazun bane a jikinsa, ya canza izuwa wasu masu kyau, suma dukka na tsakar audigan ne, still da akwai hular sanyi a kansa, kyakyawar fuskar nan tasa sai glowing take yi, tamkar ya shafa baby oil, sai ya kara wani irin kyau abinsa.

A zahiri idan ka kalle shi karatun littafin yake yi, amma kuma baɗininsa ba ita yake yi ba, ya rike littafin ne kawai, hankalinsa yana can wani wajen.

"Kamran the food is ready, am waiting for you". Wannan zazzaƙar murya ta ɗazun da ta kira shi ne time da yake wajen maman ƴan biyu, ita ce ta sake yin wannan magana a yanzu.

"Mamma am okey, I can't eat anything today". Ya faɗa yana ɗaure fuska, tamkar Mamman tasa tana a gabansa.

A hanzarce aka yaye labulen dake kofar bedroom ɗin nasa aka shigo. Kyakkyawar mace ce kyakkyawar gaske, doguwa sosai, gata ƴar caras cas, fara kal da ita kamar madara, launin fatarta ya banbanta da tasa sosai, saboda ta fishi haske nesa ba kusa ba, ga hanci har baka, da gani ba tambaya kasan mahaifiyarsa ce, saboda tsananin kamanceceniya da take a saman fuskokinsu, itama idanuwanta dara dara farare kal da su, sai dai ita kwayar idanuwanta ba baki irin nasa bane ba, ya ɗan yi brown mai haske, sai ya yi kamar foreign tiger eyes, tana da tsananin kyau da abin da ake cewa farin jini, da ganinta ba tambaya kasan jarumace sosai, dan kuwa waɗan nan idanuwan nata babu alamar tsoro ko miskala zarratin a tattare da ita, macece mai kamar maza, jarumar gaske, da alama a wajenta ya gaji jarumta.

Ita ma tana sanye da doguwar riga ta saka launin white color mai matuƙar kyau.

"Kamran what are you saying? You can't eat anything today? why?".

Ta faɗa a ruɗe, tana magana dimple nata suna lotsawa, ga dimple ɗin nata gwanin ban sha'awa, dan bai yi irin zurfin nan sosai ba, ɗan daidai mai ɗaukar hankali. Tana da sayayyar murya irin tasa, da ga ji maganarta kasan a wajenta ya gado cool voice.

"Mamma yes i can't eat anything today until you tell me the reason why you don't like people? Why you don't want me to go out? Everyday you're try to hidden our life, ni gaskiya am tied, kuma ni ina son in taimaki mutane, meyasa ke baki so? Haka last time wancan mutumin da Tiger can ta cinye, kika ki yarda mu taimaka mashi, muna ji muna gani wannan bakar damusa ta hallaka shi har lahira, why?".

Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana mai rufe littafin da yake a hannunsa, ya ajiye a saman waɗan nan kananan pillows ɗin.

Ƙarisowa cikin ɗakin ta yi, jiki a sanyaye ta zauna a saman bed ɗin, hannu ta kai ta fara shafa lallausan kumatunsa da yake kamar ta jarirai saboda laushi.

A nutse ta fara magana. "Kamran you know that i can't do something to hot you or na takurawa rayuwarka ko? Duk abin da zan yi i can do it because of your happiness ne my son, mutane ba abin yarda bane, don't trust anyone in your life, just trust yourself only".

"Amma kuma Mamma wasu mutanen ai ba mugaye bane ba, wannan mata da na gaya maki fa wlh she's...........".

Katse mashi maganar tasa ta yi ta hanyar ɗaga mashi hannu.

"Kamran! Kowani mutun da kake gani a rayuwar nan to wlh ba abin yarda bane, suffar tausayi ita ce suffa mafi haɗari a duniya, wanda kuma ni ba zan taɓa yarda da ita ba, duk wanda zai zo mun da fuskar tausayi dan na tausaya mashi, ba zan taɓa yarda da hakan ba".

"Mamma koda kuwa da gaske yake yi yana da bukatar taimakon ki?".

Ɗaure fuska sosai ta yi kafin ta ce. "Yes Kamran, ina son ka sani shi fa mugu bashi da kama, mugu yana yin galaba a kan mutun ne ta hanyar suffar tausayi, tabbas akwai masu bukatar a tausaya masu ɗin, amma kuma wake ɗaya yake ɓata gari, tabbas na tsani na ga mutun ya zo mun da suffar ban tausayi, dan haka na yanke hukunci, mu ba zamu taɓa taimakon kowa ba a rayuwarmu, mu kaɗai zamu zauna, ko da kuwa me zai faru!!".

Ta kai karshen maganar tare da miƙewa da nufin ta fice daga cikin ɗakin, da alama ranta ya ɓaci sosai, dan kuwa gabaɗaya yanayin face nata ya sauya.

Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa. "Mamma but why? Ki gaya mun dalilinki na ji, if the reason is so......".

Katse shi ta yi ta hanyar cewa. "Kamran ni ce nan na haifeka ba kai ka haifeni ba, babu wani dalili, bani da wata dalilin da zan ce maka ga shi da yasa bana son kowa ya raɓemu, kada ka sake jefo mun wata tambayar kuma!!".

Tana kai karshen maganar ta fice daga cikin ɗakin da sauri.

Idan ransa ya yi dubu, to ya ɓaci, meyasa Mammansa take yin hakan ne? Furzar da iska mai zafi daga bakinsa ya yi yana wani huci.

Wani irin dunƙule hannunsa ya yi tare da kaiwa jikin bangon kogon dutsen wani irin naushi. Nan take hannun nasa ta fashe sosai, saboda dutsen yana da masifar karfi.

Sake kaiwa dutsen naushi a karo na biyu ya yi, kuma dukka da wannan hannu da ta fashe a karon farko, ga jini har ya fara malala, jajir jinin nasa, tamkar ba jikinsa bane ba, tamkar baya jin zafi haka ya sake kaiwa dutsen naushi a karo na uku, yana yi yana huci kamar wani kububuwa.

Da gudu Mamma ta dawo cikin ɗakin, a ruɗe take faɗin. "Kamran ka fara halin nan naka ko? Ka bari mana".

Sake dunƙule hannun nasa ya yi a karo na ukun zai kai naushi wa bangon.

A dubu ɗari ta rike hannun nasa tana faɗin. "Ya isa haka mana".

Ƙoƙarin kwace hannun nasa ya fara yi, sai dai ina ya kasa kwacewa. Da hannu ɗaya ta rike shi, amma ya kasa kwacewa, dan Mamma fa jarumar macece ba raguwa ba, akwaita da karfi sosai.

Ganin ba zai iya kwace hannun nasa bane yasa ya yi ƙoƙarin miƙewa ya fice mata daga cikin ɗakin.

Riƙo shi ta yi da kyau tana faɗin. "Haba my son, what's all this meaning for?". Ta yi maganar cikin sanyin murya.

Sai huci yake yi yaki ya yi magana, ga hannunsa dake ta famar malalar da jini, yatsarsa ta tsakiyar nan ma kamar ta karye ne ko dai ta samu targaɗe, domin kuwa gata ta kumbura suntum.

Rungumarsa Mamman ta yi tana ɗan bubbuga bayansa alamar rarrashi, kamar zata yi kuka take faɗin.

"Kamran wai sai yaushe zaka dai'na wannan halin naka ne? Meyasa kake son ganina a cikin ɓacin rai ne? Meyasa kake damuwa da al'umma? Meyasa kullum akan jama'a muke samun saɓani da kai? Baka taɓa ɓata mun ba, baka taɓa kin bin maganata ba, baka yi mun musu, baka ce mun a'a, komai nace to kawai kake cewa, but why a wannan karon ma a kan jama'a ba zaka ce mun to ba? Why?".

Har wa lokacin bai iya ce mata ko uppan ba, bayan wannan huci da yake yi babu wani abin kuma da yake fitowa daga garesa, ya dai kwantar da kansa shiru a saman shoulder ɗinta, ya lumshe idanuwansa kamar mai jin barci, zuciyarsa ce take tafasa mashi tamkar an ɗaura dalma a wuta, hakan ce ma ta hana shi iya buɗe baki ya yi magana, wannan abin yana mugun damunsa, yana kuma taɓa mashi zuciya, meyasa Mammarsa bata son ya yi taimako? Ga shi dai tana da kyakkyawar zuciya a gare shi, amma kuma ko mutuwa a gabanta wani bare yake yi ba zata taimaka mashi ba, kuma ba zata taɓa bari shi ya taimaka mashi ba, to meyasa? Ga shi shi kuma Allah ya yi shi mutun ne mai bala'in son taimako, baya burin yaga wani bawa a cikin damuwa bai taimaka mashi ba, amma Mamma sam bata son hakan, ko zai yi taimako sai dai y yi a ɓoye kada ta sani, idan ta sani sai sun samu saɓani sosai.

Nasan zaku so jin wanenen KAMRAN, to ku kasa kunne kuji ɗan kaɗan daga cikin labarin wanene shi.

Su dai mazauna wannan dajin ne na tsawon shekaru, kusan ma za'a ce a nan aka haifi Kamran ɗin, su biyu kawai suke yin rayuwarsu, daga shi sai Mamma, suna rayuwa ne cike da so da kaunar juna, Mamma tana bala'in kaunar ɗan nata, Mamma mace ce jaruma mai tafasasshiyar jini, bata da tsoro ko kaɗan, a shekarun baya lokacin da Kamran yake ƙarami har faɗa da damusa ta taɓa yi, Allah ya bata nasara kuma ta kashe damusar, sam bata san menene tsoro ba, bugu da kari mace ce mai magana guda ɗaya, tana da tsayawa a kan maganarta kuma, duk wuya duk daɗi baya sa Mamma ta juya baya a kan abin da ta yi niyya, abin ban mamaki tare da ban sha'awa a rayuwar tasu kuma shi ne, Mamma mace ce mai bala'in ilimi ga tarin baiwa da Allah ya yi mata, duk wasu abubuwan da yake a cikin gidan ita ta kera kayanta, a matakin karatu ko mai degree ba zai nuna mata komai ba, tana karanta da Kamran sosai, a yanzu yana matakin Ss 2 a makarantar tata da dake karantar da shi, yana da ilimi na wuce misali, ga baiwa da ya gada daga wajen Mammar tasa, sai dai kuma yafi Mamma zuciya, duk da take mace jaruma mai zuciya, to wlh ya ninkata, dan idan ransa ya ɓaci kamar yadda kuka ga ya yi yanzu, ya rinƙa buga hannunsa da jikin dutse har ya ji ciwo, to haka yake yi idan ransa ya ɓaci. Dole ce tasa yake yin hakan, domin ba yadda zai yi da Mamma, mahaifiyarsa ce, ko murya bai isa ya ɗaga mata ba, so dole idan ransa ya ɓaci ya nemi mafita, kada ya je ya haɗiyi zuciya ya mutu a banza, ga shi shi mutun ne da bai iya danne zuciyarsa ba, hakan tasa yake yin irin wannan abin na buga hannunsa da dutse ya jiwa kansa ciwo dan ya samu zuciyarsa ta yi sanyi.

(Ba wani a kusa bare ya sauke ɓacin ran a kansa😅 Mamma dai ita kaɗai ce😅 dole nan gani nan bari😅 ba yadda zai yi da ita)

A kowace safiya Mamma da Kamran suna gabatar da training na motsa jiki, a tare suke yin komai, ita ce malamarsa mai koya mashi faɗa, duk wasu dabarun yaki da salon faɗa ta koya mashi, ga shi daman kakkarfar mutun ne shi, sabon jini mai tafasa, hakan yasa Mamma take matuƙar Alfahari da shi.

Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin Mamma da kuma Kamran. Nasan kuna da tambayoyi da dama a kansu, ni kai'na ina da waɗan nan tambayoyin, dan dole ne rayuwarsu akwai tambayoyi! Amma koma me, lokaci ne zai nuna mana!.

Ta jima a rungume da shi tana jiran zuciyar tasa ta ɗan yi sanyi. Ba ita ta sake shi ba har sai da ta ji ya dai'na wannan hucin, sannan ta sake shi tare da miƙewa ta nufi waje.

Jingina bayansa da jikin ƙogon dutsen ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali.

Jim kaɗan Mamma ta dawo hannunta a ɗauke da wani kwando irin na itacen ayaba da ake sakawar nan, kwando ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƙasashen Arewacin duniya sun fi yawan amfani da ita wajen zuba kayan miya ko kuma fruits.

A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da riƙo hannun nasa. Wani farin audiga mai ɗan girma ta fitar daga cikin kwandon, fari tas da shi. Jinin hannun nasa ta fara goge mashi tana yi mashi sannu.

Lumshe idanuwansa ya yi kamar bai ji me ta ce ba.

Bayan ta goge jinin ne ta ɗauko wani purple abu a cikin wani ɗan ƙaramin mazubi wanda ta kyara kayanta da itace, ta yi kamar kwanon sha da marfin, gwanin birgewa, da alama Mamma likita ce.

Wani audiga ta gutsuro tare da ɗan dangwalo wannan purple abin, sannan ta fara goga mashi a wajajen da hannun nasa ta farfashe. Sai sannu take ce mashi, saboda tasan abin akwai bala'in zafi sosai, amma shi kuwa yadda yake zaune tun farko, ko motsawa bai yi ba, kuma bai nuna wata alama da zata nuna cewa ya ji zafin abin ba, ya dai ɗaure fuska tamau kamar hadari.

Bayan ta gama saka mashi wannan abin ne ta mayar da abin cikin kwandon, sannan ta ɗauko wani ɗan ƙaramin audiga tare da wani ganye da ta kwaɓa da wani magani, shima yana cikin wani ɗan mazubi ne wadda ta kyara kayanta.

A gefe guda kusa da ita ta ajiyesu kafin ta riko yatsar nasa da ta kunburar. Duba yatsar ta fara yi dan ta gani karayace ko gocewar ƙashi.

Ta ɗan ɗauki lokaci da a kallah zai kai 5 mins tana ɗan jujjuya yatsar kafin ta saki hannun nasa, sannan ta miƙe ta nufi waje.

Duk abin da take yi mashi yana ji har cikin ransa, amma saboda dakiya da jarumta sam bai nuna alamar kamar yasan tana taɓa shi bama.

Hannunta ɗauke da wani kyakkyawan mazubin ruwa da ta kyara da itace ta dawo cikin ɗakin. Ruwa mai zafi ta ɗebo a cikin wannan mazubin, sai tashin tiririn hayaki ruwan yake yi.

A kusa da shi ta zo ta ajiye ruwan kafin ta wuce wajen ajiye kayansa. Wani ɗan karamin towel na sakar zare ta ɗauko, fari kal towel ɗin.

A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da sake riƙo hannun nasa, sai kara kumbura hannun nasa yake yi sosai da sosai, ba karya ya bugu kam.

Ɗan dai'dai tsakiyar yatsar ta riƙo ta fara ɗan jujjuyata daga kasa kafin ta ja da karfi.

Har lokacin bai nuna wani alama ta yana jin abin da take yi ba, saboda tsabar jarumta da juriya, ya dake tamkar bai san ta rike hannun ba.

Bayan ta ja sai ta ɗauki wannan ɗan ƙaramin towel ɗin ta saka shi a cikin ruwan zafi, sai da ya ɗauki zafi sosai, ta sa hannu babu ko tsoro ta ciro towel ɗin, da zafinsa yana tiririn hayaki ta matse ruwan jikin, ko kaɗan ita ma babu alamar tsoro ko jin wani yanayi mara kyau a tattare da ita.

A saman hannun nasa ta kai towel ɗin ta fara ɗabba mashi wajen. Haka ta cigaba da yi har sai da wannan ruwan zafin ya yi sanyi.

Abinku da fararen fata jikin madara, nan take daga ita mai rike towel ɗin da hannunta har shi da ake ɗabbawa hannu dukkansu hannayensu ya yi jajir tamkar ya tara jini ne a wajen, sai dai duk da haka babu alamar kamar sun ji zafi ko wani raɗaɗi a saman face nasu.

Wani irin mai mai sanyaya ciwo ta shafa mashi. Har cikin ransa ya ji sanyi sosai, bandeji ta ɗauko ta ɗaure mashi hannun nasa.

Har lokacin kuma bai buɗe idanuwansa ba, yana dai ji ta gama mashi komai tsab, sannan ta miƙe tare da ɗaukar kayayyakin da ta shigo dasu dukka ta fitar da su.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull