Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 50
Rawanin zalinci 1 complete Chapter 50: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 50. Har uncle ɗin ya so ya zanesu ma kuma sai ya hakura ya kyalesu, daga nan sai…
3,339 words
Har uncle ɗin ya so ya zanesu ma kuma sai ya hakura ya kyalesu, daga nan sai ya raba masu wajen zama a class ɗin, dan idan suna a tare wlh ko malami yana class suka so yin magana sai sun yi, basu jin magana ne na wuce misali, ga shariya da mannin hauka game da izza. To su wannan raba masu wajen zama da ya yi ne ya baƙanta masu rai, ba zasu iya rabuwa da juna ba ko dede da minti ɗaya, hakan yasa suka shammaci bawan Allah suka sanya mashi diaza a cikin ruwan shansa, yana sha ya haukace a school ɗin, 24 hours yana aiki kamar computer, ko barci bai iya yi ba, bawan Allah ya wahala a lokacin, abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya idan kuka kalli yadda yake tiƙar aikin. Diaza wata shegiyar kwaya ce mai haukatar da mutun, yasa ka yi ta aiki kamar jaki babu gajiya. Ko a ina suke samo abubuwan kulla muguntar tasu? Ƴan yara da su, abin da mamaki, dole akwai mai basu wasu abubuwa, dan dai su idan ba shopping ba basu zuwa ko'ina bayan school, ko gidan uncles nasu kaisu ake yi a kuma dawo dasu, basu driving da kansu ma bare ace sun ɗauki mota sun fita sun je sun sayi wani abin, idan zasu fita sai da driver and bodyguards masu rai da lafiya da zasu yi tsaron lafiyarsu, su kaisu su kuma dawo da su gida lafiya, to a ina suke samo kwayoyi masu haɗari haka? Akwai matsala kam babba ma kuwa..........🤔
Za dai mu gani, lokacin zai nuna mana komai, amma dai twins Obaid and Omaid kamar ba ƴaƴan Momma ba wlh, basu ji sam.
Yah Jawad ya zo wucewa ta saitin bedroom ɗin nasu zai je wajen Akka ya jiyo sautin dariya kamar wasu zararru. Ƴar mamaki ce ta kama shi, dan shi dai yasan twin's basa dariya, kuma basu da yawan magana, bai san a waje ne suke haka kamar malaman islamiya ba, idan suna ɗaki su biyu kamar ƴaƴan shaiɗan haka suke, su yi ta tuna muguntar da suka yi a baya wa mutane suna ɓaɓɓaka dariya kamar waɗan da aljanu suka shafa.
Room ɗin nasu ya nufo, handle ɗin door ɗin ya rike tare da murɗawa a hankali ya sanyo kai. Suna jin an buɗe kofar suka wani irin nutsu sit. Wani irin kallo ya wurga masu.
Nan take suka sha jinin jikinsu, tsuru tsuru suka yi da idanu. "Me yake damunku haka?". Shi ne tambayar da ya jefa masu yana ɗaure fuska.
Omaid ne ya ce. "Nothing Yah Jawad, kawai we're watching some comedys in my phone ne yake bamu dariya".
"Shi ne kuke dariya haka like you're out of your sense?".
Obaid ne ya ce. "Sorry Yah Jawad ba zamu sake ba".
Juyawa ya yi ba tare da ya sake yi masu magana ba ya fice daga ɗakin. Kallon juna suka yi tare da sake kwashewa da dariya ƙasa ƙasa suna toshe baki kada sauti ya fita Yah Jawad ya dawo ya karairayasu.
Shi kuwa Yah Jawad yana fita part ɗin Akka ya nufa. Gimbiya Chuchu ta tsantsara kwalliyarta cikin wani abaya pink color mai shegen kyau, ta yi kyau sosai, arab hair ɗin nan nata ta ɗaure shi part biyu, Kuyanga mama Haulat ta kitse mata jelar gashin nata gwanin birgewa, sai sheki yake yi ita kuma tana ta tashin kamshin daddaɗar perfume mai sanyaya zuciyar mai shaƙa wadda Momma ta basu ita da auta Zunaira.
Sam ta manta da yarjejeniyar da suka yi da Yah Jawad, ta tsaya sai ɗaukar kanta hoto da videos take yi a wayarta abinta, dan ba karya ta yi kyau over......... Dama ai mai hali baya fasawa, da wuya ta dai'na ɗaukar hoton nan lokaci guda haka, abin da ta saba yabi jininta ai ko zata dai'na ba lokaci guda haka ba, sai a hankali.
Yana shigowa ɗakin ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana binta da kallo tare da jingina jikinsa da jikin door ɗin shigowa room ɗin, tunani yake yi yadda zai yi da yarinyar nan a duniya..............
Nima tunani nake yi lokacin da zan dasa aya ya yi, sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu da rai da lafiya, zamu ji ya Yah Jawad zai yi da Gimbiya Chuchu? Wani hukunci zai yanke mata?....🤔
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 7/8/2024.....✍️📚🌹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________30🔥
Yana shigowa ɗakin ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana binta da kallo tare da jingina jikinsa da jikin door ɗin shigowa room ɗin, tunani yake yi yadda zai yi da yarinyar nan a duniya.
Sam bata ji motsinsa ba, videonta kawai take ɗauka, ta turo bakin nan ta sake ɗaga jera ɗaya, sai style kala kala take yi. Kamar a mafarki ta gansa ta cikin camerar wayar tata. Ai a dubu ɗari ta juyo har wayar tata sai da ya faɗi ƙasa.
Tana juyowa suka haɗa idanu, ko kyafta idanu daga kallonta bai yi ba. Tana juyowa sai da ya ji gabansa ya faɗi, saboda kyan da ta yi, kun santa da shegen iya make up, dama kuma ga kyau kamar su suka yi wa kansu.
Ƙasa da kai ta yi kamar wata mumina sahabiya. Tun bai yi mata magana ba ta fara ƴan kame kame tana in'ina ta ce. "Am.... Im so sorry Yah Jawad...... Na mance na ce ba zan sake bane". Tana magana kirjinta na dukan uku uku.
Kamar mutun mutumi ne a wajen ba shi ba, ko motsawa bai yi ba bare tasa ran zai amsa mata, in fact ko kallonsa daga kanta bai kawar ba, ya tsareta da ido kamar wadda aka yi wa guduma a tsakar kai ya yi tsumar tsaye.
Duk baiwar Allah ta tsargu, tana son ta ɗago kai ta saci kallonsa, amma tana tsoron su haɗa idanun, ga shi ta ji ya yi shiru bai yi magana ba, tana son ta ga action da ya ɗauka, shin yana harararta ne ko kuma dai yaya? Face ɗinsa a ɗaure take ne ko kuma dai a ɗan sake? Duk tana son sani, amma ba halin ta ɗago kai, saboda tsoronsa. Sai addu'a take yi Allah ya kawo Akka, idan Akka ta shigo shikenan ta tsira. Har kerma ƴan hannayenta suka fara yi, ba abin da take tunawa irin punishment na ranar, narai narai ta yi da idanun tana shirin fara yin kuka kawai.
Almost 10 mins yana tsaye a haka, sai da ya ga hawaye ya fara bin kyakkyawar kumatunta yana ɓata mata make up nata ne, a nan ne ya ɗan sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa ya sake buɗesu. A hankali ya fara takowa izuwa cikin ɗakin.
Datse idanunta gam ta yi tana jiran kawai ta ji saukar mari. Gabanta ya ƙariso yadda ta tsaya kamar wadda aka sassaka.
Ɗan sunkuyawa ya yi ya ɗauko wayarta da ta yasar a kasar, pause ɗin video da take ɗauka ya yi, sannan ya yi saving video, yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi mata magana ta raɓa gefensa da gudu da nufin ta yi waje.
Cikin sauri ya riƙo hannunta tare da ɗaure fuska sosai. "Where are you going?". Ya faɗa cikin sanyin murya.
Bai san cewa uncle Abbas ta gani a bayansa yasa zata gudu ta je wajensa ba, yanzu ya shigo room ɗin, sallama ya zo yi da Akka zai wuce, shi ne da ta ga ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu zata gudu ta je wajensa, hankalinta ya ɗan kwanta uncle nata ya zo shikenan ta tsira, shi kuwa Yah Jawad bai san da uncle Abbas ɗin ya shigo ba.
Janyota ya yi ta dawo ta gabansa, kara ɗaure fuska sosai ya yi irin ba wasan nan. Gabaɗaya hankalinta na'a kan uncle Abbas ɗin, shi ma ya harɗe hannu a saman kirjinsa yana kallonsu. Ganin hankalinta na'a kansa yasa ya yi mata alama da ta yi shiru bari ya ga gudun ruwan Jawad ɗin.
Ganin uncle Abbas ɗin ya yi mata alamar ta nutsu ne yasa ta nutsu tare da yin ƙasa da kanta.
"Am i not talking to you?". Yah Jawad ya yi maganar yana sakin hannun nata da ya riƙe.
"Am so sorry babu in da zanje". Ta bashi amsa tana ɗan satar kallon uncle Abbas.
"Wai Jannat anya babu wata matsala a tattare da ke kuwa? Ban hanaki ɗaukar hoto ba?".
"Mantawa na yi, amma ka yi hakuri ba zan sake ba".
Nisawa ya ɗan yi kamar wani wadda ya yi wani aikin ya gaji. "Yanzu wani hukunci kike son na yi maki?".
Sai a lokacin ta ɗan ɗago da kanta, a hankali ta kai kallonta izuwa saman face ɗinsa, while shi ma face ɗin tata yake kallo, hakan yasa suka kalli juna a cikin idanu. "Dan Allah Yah Jawad kada ka yi mun komai, Allah ba zan sake ba, na tuba, wlh bana son kneel down ɗin nan, please Yah Jawad, gwara mun ka kwace wayata na har abada akan ka ka bani punishment ka ji?". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar, a shagwaɓe kuma ta yi maganar, ga ragowar guntun hawayen ɗazun a saman fuskarta.
Lumshe idanunsa ya yi, har cikin ransa ya ji voice ɗin nan nata. "Last time bana ce ki sameni a part ɗina ba? Meyasa baki zo ba? Kin rai'na ni ko?".
A hanzarce ta girgiza mashi kai alamar a'a tana mai cigaba da maimaita mashi kalmar sorryn nan dai da ta saba faɗa kullum.
"Ina Akka?". A hanzarce ta amsa mashi da. "Bata nan ta fita, ina ga ko tana wajen daddy ko kuma wajensu mummy".
"Meyasa kika ce mata ni na hanaki zuwa Dubai?".
Zaro idanu waje ta yi, ita kwata kwata ma ta mance da cewa ta kai karansa wajen Akka ɗin, wannan shi ne laifi a kan laifi, dan kuwa Akka ta je har part ɗinsa wai sai ya gaya mata dalilin da yasa ya hana Chuchu zuwa Dubai?. Da kyar ya shawo kanta ta rabu da shi, wannan dalilin yasa ya biyo Chuchun, yasan confirm zai sameta a nan ɗin, shi ne ya zo.
"Ba zaki bani amsa ba kenan ko? Wai ni Jannat yaushe na zama abokin wasanki ne?".
Cigaba da girgiza mashi kai ta yi, nan take idanunta suka sake ciko da kwallah, kan kace me sun fara bin kumatunta.
"Another case kenan, bana hanaki kuka ba?".
Da sauri ta sanya hannu ta fara goge hawayen nata.
"Okey jeki part ɗina ki yi kneel down ina zuwa".
Okey ta amsa mashi da shi tare da raɓawa jefensa ta wucewa da sauri. Tana wucewa ya juyo da kallonsa a kanta domin ya kara tsareta da idanu. Mugun jin daɗin kallonta yake yi ɗan rainin wayo, amma tsabar walaƙanci da mugunta sai ya rinƙa baƙanta mata rai, ya yi ta takura mata yana sakata kuka.
Yana juyowa suka yi ido huɗu da uncle Abbas da ya saki baki yana ganin ikon Allah, shi dai yasan babu wanda ya taɓa yi wa su Jawad ɗin makamancin haka, amma su sun zo suna cin zalin kannesu.
Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon daddyn nasa, yana son ya san yaushe uncle Abbas ɗin ya shigo room ɗin, adduarsa ɗaya Allah yasa bai ji abin da ya ce da Chuchu ba, dan yasan halin uncle Abbas sarai, idan kana son kaga ɓacin ransa to ka taɓa mashi ƴan matan nan nasa, sam baya son yaga an taɓasu, ƴan lelene, shagwaɓasu yake yi over, shiyasa suma suke matuƙar kaunarsa sosai, ba dan ba dan bama sai mu ce sun fi kaunarsa sama da daddynsu King Zuhair.
"Welcome daddy yaushe ka shigo?". Ya faɗa yana satar kallon Chuchu da ta fita a yanzu, yana magana yana fargabar kada ace daddyn nasa ya ji maganganunsu da ita.
Shiru uncle Abbas ɗin ya yi har sai da Chuchu ta yi nisa da room ɗin, sannan ya ce. "Tun lokacin da kake sanya mun ƴata kuka na shigo".
Ɗan shafa arab hairnsa ya yi tare da ɗan sunkuyar da kai ƙasa. "Kai daddy ni yaushe na sakata kuka? Kawai sune sun cika yin kuka banza banza, kuma duk kai ka shagwaɓasu ai, ni iya faɗa kawai nake yi mata".
"Jawad wlh ina jiye maka tsoron kar ka tabka kuskure". Uncle Abbas ya faɗa tare da ƙarisowa cikin room ɗin. A saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare da ɓalle botir na suit ɗin jikinsa.
"Daddy kuskuren me kuma?". Ya faɗa da iya gaskiyarsa, dan shi bai san wani kuskure daddyn nasa yake hango mashi ba.
"Zaka ce mun baka san abin da nake jiye maka tsoro bane?". Ya yi maganar yana wurga mashi wani irin kallo da waɗan nan idanun nasa irin na Akka.
"Kai daddy wannan kallon fa?". Ya kai karshen maganar tare da dawowa kusa da daddyn nasa ya zauna a saman sofar.
"Ai dole na kalleka da kyau tukun nan, na tabbatar lafiya kake da zaka ce mun baka san tsoron da nake jiye maka ba".
Ɗaura wayar Chuchu a saman hannun sofar ya yi tare da cewa. "Daddy da gaske ban san wani irin kuskure kake ji mun tsoron na tabka ba".
"Jawad kenan, to ina jiye maka tsoron ranar da zaka bayyanawa Jannat gaskiya ita kuma ta ce bata so bazata yarda ba saboda kana mata mutunta, a ranar ne zaka gane ka yi kuskure".
Ɗan zaro idanu ya yi, ƴar mamaki ce ta bayyana a saman face ɗinsa. "Daddy wace gaskiya kuma zan bayyanawa Jannat har da zata ce bata so?".
Hararar wasa uncle Abbas ɗin ya wurga mashi kafin ya ce. "Yanzu zaka ce mun ba son Jannat kake yi bane?".
"So kuma daddy? Ni ɗin?". Ya faɗa cike da mamaki sosai.
"A'a ba kai ba ni, wai Jawad lafiyarka ma kuwa?".
Shiru ya ɗan yi yana tunani, sake furta cewa son Jannat ni kuma, ya yi tare da nuna kansa, mamaki abin ya bashi ne.
"Baka yardanwa kanka kana sonta ba ko? To bari na baka wani Assignment ka je ka aiwatar da shi yanzu, idan ka kammala sai ka kirani a waya ka sanar da ni amsa".
Dawo da kallonsa a kan daddyn nasa da kyau ya yi kafin ya ce. "Okey daddy ina jinka wani Assignment?".
Kallon shi da kyau uncle Abbas ɗin ya yi kafin ya ce. "Ba ka ce ta je ta yi kneel down a part ɗinka yanzu ba?"
Gyaɗa mashi kai ya yi almar e ya ce.
"Okey in ka je part ɗin naka yanzu ka barta ta yi one hour tana kneel down, kuma kada ka hanata yin kuka, ka barta ta yi kukanta, sannan idan ta cika one hour ɗin ka ce ta tafi room ɗinta da kafafunta, idan ta kasa ka ce dole ta tafi, ko kukan jini zata yi kada ka kulata ta taka da kafafunta dole, idan ka iya aikata hakan ka kirani ka gaya mun.....". Ya kai karshen maganar yana kallon ɗan nasa har cikin ido, dan shi dai yasan tun Chuchu bata kai haka ba yasan da cewa Jawad ɗin yana sonta, shi ne dai bai gane hakan ba, amma yanzu zai gane ne dolensa, uncle Abbas yasan ko dede da minti ɗaya Jawad ba zai iya jure kukanta ba, amma dai koma me yanzu zai gane ai.
"Daddy wai yau da kanka kake cewa na bawa ƴan gatanka punishment? Kuma kace ko ta yi kuka na barta ta yi ta yi? Anya daddy kai ne kuwa?".
Ɗan murmushi ya yi tare da faɗin. "Ni ɗin ne dai, Abbas ɗin da kasani ne, ni nace ka je ka yi ai, kawai ka je ka aikata, idan ka iya sai ka kirani ka sanar da ni, dan ni daga nan wucewa zan yi......".
Girgiza kai ya fara yi yana faɗin. "No daddy banda kuka kam, ni bana son ganin kukanta, amma zan iya sanyata kneel down sosai, har ma fin one hour, amma ba zan iya jure ganin kukan nata ba".
Harararsa uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Okey tom shikenan na janye wannan Assignment ɗin bari na baka wani, idan ka koma part ɗin naka yanzu, ka kalleta ido cikin ido na a kallah one mint, duk tunanin da ya zo zuciyarka a wannan lokacin ka kirani ka gaya mun, dan shi ne gaskiyar abin da yake a tsakaninku".
"Daddyyyyyy kai ni wlh wahalar dani kawai kake son yi, Jannat is my sister that's all, bayan haka ni babu wani abin, to daddy Jannat ma nawa take? Yaushe ta girma ma? Me zan yi da ita? Ai ta yi mun ƙanƙanta, ni bani ma da lokacin mata a yanzu". Ya kai karshen maganar yana turɓune fuska, shi sam bai ma san cewa ya saki layi a maganar tasa ba, ko da yake shi dama bai kai Jaish kunya ba.
"Babu abin da zaka yi da ita, kuma bata girma ba amma a haka kullum kake tsare mun ita da ido, idan kana kallonta ma har mantawa kake da in da kake, jiya ma fa a parlourn Yah Zuhair ina ganinka sai kalle mun ita kake yi kamar ka samu Tv, gaskiya zan gayawa yaya ma duk ku bar family part ɗin nan ku koma gidajenku, saboda kun sakawa ƴaƴana ido, ku barmun su su sakata su wala".
Da yake gidajen nasu dukka a cikin kingdom ɗin yake, sai dai yana da ɗan nisa da family part gaskiya.
"Kai daddy wai ni yaushe na kalleta ne? Kai da uncle Taheer da dad kun saka mun ido fa, shi ma dad daren jiya har da ce mun wai yanzu aure zai yi mun ni da Jaish ya huta, to mu laifin me muka yi yanzu fisabilillahi da kuke neman ɗaura mana wahala?.". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗauki wayar Chuchu ɗin da ya ajiye, sannan ya nufi waje. "Allah ya kiyaye hanya daddy".
"Zaka ga mun saka maka idanu ne, sai na yi mata miji cikin ɗaya daga cikin ƴaƴan abokaina ba tare da saninka ba za'a ɗaura auren, a nan ne zaka san mun saka maka ido, ka jira ka gani".
Shiru ya yi, dan har ya ji ransa ya ɗan ɓaci da last zancen daddyn nasa, da sauri ya wuce ya fita dan kada ma daddyn ya ƙara yi mashi magana mara daɗi irin haka.
Da kallo uncle Abbas ya bishi, sai da ya fice ne ya ce yaro yaro ne, zaka yi bayani ne, ai ita so ba'ayi mata wargi.
Part ɗinsa kai tsaye ya nufa, sai saƙa kalaman daddyn nasa yake yi a cikin ransa. Ƙasa ƙasa ya yi sallama kamar mai ciwon baki. Babu kowa a parlourn nasa, sai tashin kamashi da ko'ina yake yi, kai tsaye cikin room ɗinsa ya nufa.
A nan ya isko Gimbiya Chuchu ta yi kneel down sai aikin sharar kwallah take yi, har idanunta sun yi jajir saboda kuka.
A kusa da ita saman katafaren bed ɗinsa ya zo ya zauna tare da ajiye wayoyinsa haɗe da nata a gefensa. Zancen daddy nasa ne kawai yake yi mashi yawo a cikin kansa. Ji kawai ya yi zuciyarsa ta aminta da ya yi abin da daddyn nasa ya faɗa.
Slowly ya kai hannunsa ya ɗago haɓarta daga yadda ta sunkuyar da kai ƙasa tana ruwan hawaye. Datse idanunta gam ta yi saboda tsoron su haɗa idanu da shi.
Sai da ya ji tsikar jikinsa ya wani irin tashi na ganin face nata kawai da ya yi, a haka ma ba cikin kwayar idanun nata ya gani ba, ga shi face ɗin nata ma ya yi jaga jaga da hawaye, duk ya ɓata mata kwalliyarta.
In a low voice sosai ya furta. "Open your eyes".