Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 57
Rawanin zalinci 1 complete Chapter 57: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 57. Knocking suka yi masu Sadiq a kofar ɗakin, ba'afi second ashirin ba sai ga…
3,325 words
Knocking suka yi masu Sadiq a kofar ɗakin, ba'afi second ashirin ba sai ga Sadiq ɗin nan ya buɗe kofar ya fito. Shirye yake cikin dakakkiyar shaddar mai shegiyar kyau, da alama yau ma yana da class.
Har suna haɗa baki wajen cewa Uncle Sadiq ina kwana. Murmushi ya yi yana kallon Zainab sarkin tsiwa kafin ya amsa masu gaisuwar, yarinyar nan Zainab ba dai iyayi ba, haka take zama ta karewa maman Haidar da kakansu zagi fes kamar an aikota, bata da sauki, Khadija kam daga e sai a'a, sai kuma gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa.
"Dama na shirya ku nake jira, ina da class karfe 7:30 dai'dai mu je ko?". Sadiq ya faɗa yana kai hannunsa ya ɗan bugi bakin Zee da take aikin turo shi kamar wadda aka zaga.
"Kai kawu Sadiq menayi maka to?". Ta faɗa tana ɗaure fuska.
Khadijah ce ta amsa mata da. "Kwaɗayin duka yake ji yasa ya dake ki, ko dai bai kai bane?".
Wani irin harara ta bi Khadija da shi. Shi dai Sadiq wucewa ya yi izuwa wajen mashin ɗin baban nasu, da yake key na a hannunsa, fito da mashin ɗin ya yi kamar yadda suka saba, ba ɓata lokaci ya ce su yi sauri su hau su tafi lokaci yana ƙurewa. Da sauri suka hau Zainab sai raki take yi. Da haka suka bar gida, shi kuwa Haidar yana can yana barcin asara, wani lokaci ma sai 10 yake tashi ya tafi kasuwa ko kuma wajen mamarsa or kakarsa, kullum aiki ɗaya, ya kusa yin aurema bai canza hali ba, ko waye zai ciyar mashi da matar idan ya yi auren? Shi da kasuwar ma sai yaga dama yake zuwa. Akwai matsala sosai, akwai case ba kaɗan ba.
Misalin karfe 9 dai'dai sai ga Aunty Hauwa ta nufo gidan kamar yadda ta faɗawa maman Zainab zata zo jiya. A lokacin baban Zainab bai fita ba, yana ciki, da alama yau ba zai je kasuwa da wuri ba, ita ma maman Zainab tana cikin ɗakinta ta yi zaman ƴan bori a saman tsakiyar gado, ta haɗa hannayenta ta buga uwar tagumi kamar wadda aka aikowa da wahayin yinsa, ta luluƙa duniyar tunanin ya zata yi da rayuwarta, har yanzu ta kasa iya gane cewa damar da Allah ya bata a baya ne take wasa da shi son ranta, tana yi kuma ba tare da godiya ga Allah ba, to yanzu damar tana neman kubce mata, ta kasa iya gane hakan ma bare ta yi ƙoƙarin dawo da damar izuwa gareta..... Tirƙashi, akwai matsala fa my people's, mu je dai zuwa.
A parlourn Aunty Hauwa ta zauna, ta tsantsara kwalliyarta cikin wata shegiyar lace mai kyan gaske, da alama ma case ɗin maman Zainab ɗin bai wani dameta ba, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya a kanta irin yau ba mutuncin nan, sai wani kwaɓe fuska take yi kamar wadda taga kashi.
Fitowa maman Zainab ta yi daga room ɗinta cike da damuwar halin da take a ciki, tsawon shekarun nan da suka yi aure baban Zainab bai taɓa yi mata makamancin haka ba, har ya share tun jiya bai yi mata magana ba har yau, abin dole ya jefata cikin damuwa sosai, a maimakon ta kira mahaifiyarta ta sanar da ita abin da yake faruwa, sai ta sake kirawo Aunty Hauwa kuma.
"Hauwa ki zo mu shiga cikin bedroom, baban Zainab yana nan fa". Maman Zainab ta faɗa murya ƙasa ƙasa.
Okey Aunty Hauwa ta amsa tare da ɗaukar wata ƴar figaggiyar jakarta irin na dillalai, ga gyalenta dama a kafaɗa ta yafo shi kamar ba matar aure ba, burinta kawai su shiga ciki ta tambayi maman Zainab ɗin baban Zainab ya sha maganin? A ƙage take da ta ji ya sha ɗin ko bai sha ba?. A haka ta miƙe da nufin su shiga cikin bedroom ɗin dan rashin hankali irin na maman Zainab da kuma damuwa da ya rufe mata idanu.
Tana miƙewa tsaye sai ga baban Zainab ya fito cikin shirinsa na shadda mai shegen kyau launin sky blue, ɗinkin manyan kaya ne, so ya ɗaura babbar rigar ma a sama, a takaice dai makurar shigar mutunci ya yi, da alama yau ma ba zai ci abincin maman Zainab ba, kamar dai daren jiya, dan dai ga shi ya kammala shirin fita abinsa.
"Sannu da fitowa, ina kwana?". Aunty Hauwa ta faɗa cikin sanyin murya.
Turus ya ja birki ya tsaya tare da juyo da kallonsa a kanta, wani irin faɗuwar gaba ya ji a lokacin da ya sauke idanunsa a kanta. Da ni da ku duka mun san cewa baban Zainab in ya shigo ya sami maman Zainab da bakuwa wlh ko kallon in da suke baya yi, baƙin suna gaishesa ma baya tsayawa, wani lokaci kafin ya amsa masu gaisuwar nasu ma ya kai bakin kofar ɗakinsa, amma yau sai ya tsaya tare da juyowa yana kallon Aunty Hauwa.
Maman Zainab ta ɗan yi mamaki, amma sai ta ce kila zai tambayi Aunty Hauwa ɗin ina ta je jiya ne, dan haka sai bata wani damu ba.
"Sannunki da zuwa Hauwa ya gida ya yara?". Ya faɗa yana bata full attention ɗinsa.
Murmushi ta sakar mashi kafin ta amsa mashi da komai lafiya lou.
Shiru ya ɗan tsaya tare da zuba mata idanu yana ta kallonta. Maman Zainab kuwa sai ta taɓe baki tana ganin abin kamar a Tv a gabanta, ita kuma Aunty Hauwa sai wani irin murmushi take yi mashi.
"Yanzu zaki tafi ne na kai ki gida?". Baban Zainab ya tambaya.
Wani irin zaro idanu maman Zainab ta yi, abin da bata taɓa ji ba, ba kuma ta taɓa gani a tattare da shi ba, kai ina bata yarda ba, a mafarki ta ɗauki abin, dan haka sai ta kai hannunta saman face ɗinta ta ɗan mari kumatunta wai idan mafarki take yi ma ta farka.
Amma ina sai ma ji da ta yi Aunty Hauwa tana cewa. "E zamu iya tafiya a tare duk da ba yanzu naso tafiya ba, amma tun da zaka mayar dani ai komawa ta kamani".
"To muje ko?". Ya faɗa yana mai cigaba da kallon face ɗinta sosai, sai wani uban murmushi take yi.
Maman Zainab bata ankara ba tana can tana tunanin mafarki take yi ne ko ba mafarki ba kawai sai ganin Aunty Hauwa ta yi sun jera da baban Zainab sun nufi wajen parlourn.
Ai bata san lokacin da ta bi bayansu ba, a harabar gidan ta ce. "Hauwa menene haka kuma?".
Dakatawa daga tafiyar da suke yi Aunty Hauwa ta yi tare da juyowa ga maman Zainab ɗin, ɗaure fuska ta yi sosai kafin ta ce. "Wacece kuma Hauwa? Ni kike kira ko dai wata?". Tashin hankali da ba'a sanya mashi date kenan!!.
Wani irin zaro idanu waje maman Zainab ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa, cikin tashin hankali ta ce. "Hauwa ban gane me kike faɗa ba? Ban gane me kike nufi ba? Ko dai kunnuwana sun dai'na ji ne? Ko dai har yanzu a cikin mafarki nake ne?".
Kallon baban Zainab Aunty Hauwar ta yi tare da cewa. "Abu Zee mu je ko? Bani da lokacin A'isha ni kam".
Da okey kawai ya amsa mata ba tare da ya kalli in da maman Zainab ɗin take tsaye ba, kamar bai taɓa saninta ba a duniya.... Tashin sense kenan yau ake yinta a wannan gidan.
Gaba Aunty Hauwa ta yi tana wani rangwaɗa tare da kara gaya mashi su je ita fa bata da lokacin maman Zainab a yanzu. Rufa mata baya ya yi da nufin su tafi ɗin.
Ai tsabar kishi da bakin ciki yasa Maman Zainab bata san lokacin da ta yi kukan kura ta damko wuyar Aunty Hauwar ba, idanunta sun rufe, wani irin bakin cikin take ji kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, wani irin cin amana ne wannan mai azaban raɗaɗin zafi haka?.
Cikin sauri baban Zainab ya fara ƙoƙarin kwatar Aunty Hauwar daga shaƙar da maman Zainab ta yi mata, da alama mafa baban Zainab ya manta wacece maman Zainab. Tirƙashi.
Maman Zainab kuwa ta shaƙeta da iya karfinta na karshe tana faɗin wlh sai ta kasheta, azzaluma maciyi amana, su taso a tare su yi karatu a tare, komai a tare suke yi ne zata nemi ta ci amanarta haka? To wlh ba zata barta ba, kasheta zata yi sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta................
Tashin hankali, akwai babbar cakwakiya na kin ƙarawa a wannan gidan, kenan Aunty Hauwa amanar maman Zainab ta ci? Ta kaita wajen malami da sunan samun mafita kenan kanta ta shiryawa hanya mai kyau ba maman Zainab ɗin ba?🤔 Ita kuma maman Zainab cikin rashin sani ta bashi maganin kaunar Aunty Hauwar da hannunta ya sha?🤔 Ga shi har da ƴaƴanta su Khadijah ta bawa suka sha dan rashin hankali da rashin tunani? To kenan ya makomarsu take su kuma? Suma zasu bi ayarin Aunty Hauwa kamar babansu kenan? Bala'in nan, wannan shi ne bala'i, akwai yaki gagarumi a cikin wannan gida, ya makomar maman Zainab? Farkoma ya makomar auren Aunty Hauwar? Da ni da ku dai duk mun san tana da aure? Alamu kuma sun nuna baban Zainab dai ya kamu da sonta, kuma ga dukkan alamu ita ma hakan take so, to ya kenan batun nata mijin?🤔 Ina su maman Haidar? Zasu yarda da hakan kuwa? Kada ku manta sun yi mashi mata fa a cikin family, lallai akwai rikici da rikita rikita, yau akan Aunty Hauwa baban Zainab ya mari Maman Zainab, tab duniya kenan, amana ta yi ƙaranci, ni dai PRINCESS TEEMA na haɗa kayana sai mun haɗe daku gobe dan jin yadda wannan bala'in yakin da ta tinkaromu zata kaya!! RAWANIN ZALINCI ya fara ɗaukar tafasa ma ba zafi ba, Zalunci ta ko'ina😥💔
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/8/2024.....✍️📚🌹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________34🔥
Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta damko wuyar Aunty Hauwar, idanunta sun rufe, ita dai ta kashe Aunty Hauwa kawai hankalinta ya kwanta.
A karo na biyu baban Zainab ya kara mata wani zazzafar mari, sai dai a wannan karon ko da ya mareta bata saki Hauwar ba, sai ma kara ƙanƙame wuyarta da ta yi, yadda ta ji zafin wannan mari haka ta kara shaƙe mata wuya gam.
Kafin baban Zainab ya samu ya kwaceta daga hannunta har Hauwa ta sume, saboda azaba, tasha shaƙar manya, ga shi cikin fushi aka yi mata shaƙar.
Fara ƙoƙarin dukan maman Zainab ɗin ya yi, amma ina, ai bata tsaya ya daketa ba, sai ma kwasawa da ta yi a guje ta nufi cikin kitchen, muciyar tuƙa tuwonta ya je ta ɗauko, hauka hauka ta nunawa baban Zainab a in da ta fara ƙoƙarin dukan Hauwa dake sume yashe a ƙasa da wannan muciya, ta sumar da ita ɗin ma ba zata kyaleta ba.
Da baban Zainab da ya ga haka sai shi ma ya sanya mata karfi da nufi ya yi mata duka ya kuma karewa Hauwa dake sume faɗar. Amma ina maman Zainab taki yarda ta bari ya sake ɗaura hannunsa a jikinta, sai zulle mashi take yi, shi kuma yaki barinta ko sau ɗaya ne ta kwalawa Hauwa wannan muciya da ta ɗauko.
Daga karshe dai ya yi nasarar kwace muciyar tare da kamata ya turata cikin ɗaki, ya kuma rufo kofar ta waje ya barota a ciki. Kamar zararriya haka ta rinƙa dukan kofar nan da iya karfinta na karshe, tamkar zata ɓalle kofar, hakan yasa Haidar ya farka daga barcin asararsa da yake yi.
Shi kuwa baban Zee bai ma sake bi ta kanta ba, ruwa kawai ya ɗebo a kitchen ya zo ya yayyafawa Hauwa ta farfaɗo. A haukace ta farfaɗo tana ambatar ta shiga uku yau zata mutu.
Hakuri ya fara bata kamar wani ɗanta, harda tsugunnawa a gabanta ya fara rarrashinta. Ji maman Zainab take yi zuciyarta zai iya fasa kirjinta ya fito waje, hakan yasa ta fara neman abin da zata karya wannan kofar da shi ta fito waje, yau ji take yi idan bata kashe Hauwa ba ba ita ba zaman lafiya, kada ku manta dama baban Zainab ya ce tana da balai'n kishi na wuce tunani, bare kuma ace irin wannan cin amana mai bala'in zafin da Hauwa ta yi mata ai dole ne ta haukace masu, kawarta ce fa da suka taso tun yarinta, duk da tun suna yara halinsu ya sha banban, amma hakan bai sa sun rabu ba, kawance ta ɗaure har girma izuwa aure, ace rana tsaka ta yi mata irin wannan ɗanyen aiki ɗanyen cin amana, ai dole zuciya ta sosu over.
Fatana a nan dai shi Allah yasa mata kun ɗauki darasi! Duk abin da yake faruwa da maman Zainab ita ta jawa kanta, kama daga abin da su maman Haidar suke yi mata har wadda Hauwa ta yi mata a yau, duk ita ce da laifi, ta ya za'ayi ki rinƙa sakin baki kina gayawa wata cewa mijinki yana kula dake hundred over hundred? Kuma sai ma ki rasa wadda zaki rinƙa gayawa hakan sai wadda ita mijin nata baya yi mata hakan, a haka kike tunanin zaki samu zaman lafiya? Ke kina tunanin cewa ai kawarki ce, kun taso tare ba zata ci amanarki ba, to ai ga shi nan kun gani ido da ido, ita tana can tana fama sai ta sha rana ta yi kasuwanci tukun nan ta iya biyawa kanta dukkannin buƙatun da take so, ke kuma kina daga kwance ake yi maki komai, sannan kizo kina bata labarin irin daɗin da kike ji ki ce ba zata yi tunanin ita ma bari ta yi join ɗinki kuci daɗin a tare ba? Waye baya son daɗi? Waye yake son wahala? Kin yi kuskure babba idan ma haka kike tunani, wata ma domin hasada da bakin cikin bata samun abin da kike samu ko ba zata auri mijin naki ta shigo kuci daɗin a tare ba zata yi duk yadda zata yi ta rabaki da mijin, idan kuma hakan bai samu ba to zata yi duk yadda zata yi ta ga ya dai'na kyautata maki kin koma wahala kamar ita.
Ai a zamanin yanzun nan duk yadda kuke tare da mutun da ya tambayeki ya mijinki? Alhdulillah kawai zaki ce mashi, daga wannan Alhdulillah ɗin kada ki kara kada ki rage, bakinki kanin kafarki, idan kuma kin ki ji to fa ba kyaki gani ba.
Idan muka koma muka yi duba da abin da yake a tsakaninta da su maman Haidar nan ma ita ta jawa kanta, domin kuwa ita ce nan tun farko ta sakewa Haidar ya san komai ɗinta da har yake kwasan sirrin gidan yana kaiwa kakarsa da kuma mahaifiyar tasa. Kunga ita ma maman Haidar ɗin ba samun jin daɗin nan wajen mijinta take yi ba, baban Zainab ɗin ne ma mai ciyar da ita, saboda mutuwar zuciya irin na mijinta, ai dole ita ma zata ji haushin bata samun abin da maman Zainab take samu, dole ta yi mata hasada da bakin ciki, shiyasa take zuga kakan su Khadijah dan kawai ta takurawa maman Zainab ɗin kuma ta ƙuntata mata. Yaushe zaki bari har familynsa su san irin kyautatawar da yake yi maki? Ai a irin haka ne ma wata daga cikin family zata maƙale ta ce idan ba shi ba ba zata yi aure ba, haka kina ji kina gani za'a sanya ya aurota kamar dai yadda kuka ga aya a kan maman Zainab. Ai ko mijinki ya ɗauko kaninsa ya kawo maki ki rike, sai ki san ta yadda zaki zauna da shi baki cuce shi ba kuma baki bari ya cuceki ba, kada ki yarda ki bari yasan cewa ga abin da yayansa yake yi maki, ki koyawa mijinki ko abu zai baki to ya baki tun daga cikin bedroom ba sai anzo parlourn bama bare har a kai ga tsakar gida. Fatana dai my people's kun ɗauki darasi na farko a kan maman Zainab?.
Sosai baban Zainab ya rarrashi Hauwa, sai kukan makirci da kisisina take yi, ita kuma maman Zainab tana can tana ƙoƙarin haɗiyar zuciya kofa yaki buɗewa. Tana ji tana gani baban Zainab dai ya saka Hauwa a gaba suka bar gidan, sai lallaɓata yake yi. Dama kun san shi ya iya sosai..........😅
Suna fita gidan Haidar kuma ya fito daga cikin nasu ɗakin, dukar kofar parlourn da maman Zee ke yi ne yasa ya farka, sai dai bai yi nasarar ganin menene ya faru ba, baban Zee ya ja Hauwa sun yi gaba. Ko da ya fito waje bai ga kowa a harabar gidan ba, ita ma Maman Zee a lokacin ta dai'na buga kofar parlourn ta kwasa a guje ta nufi cikin bedroom ɗinta, dan taga tafiyarsu ta window, sun riga sun fita, ko ta buga kofar ba amfani, dan haka sai ta kwasa da gudu ta yi cikin room ɗinta.
Jikinta har wani irin kerma yake yi saboda bakin ciki, wani irin zufar wahala yana tsastsafo mata a gabaɗaya face ɗinta, kuka take yi hawaye bibbiyu, idanunta sun yi jajir kamar wata ƴar shaye shaye. A gigice ta ɗauko wayarta, har wani yana yana take gani a cikin idanunta, bata ganin screen ɗin wayar da kyau saboda kuka.
Number mahaifiyarta ta fara kira a haukace, sai yanzu ta tuna da cewa ta kira mahaifiyar tata, da can duk bata tuna ba, sai da abu ya kwaɓe mata.
Bugu biyu mamar tata ta ɗauka. Cikin kuka ta fara faɗin. "Nashiga uku mama, na mutu na lalace Hauwa ta cuceni".
A gigice ƴar tsohuwa ta ce. "A'isha lafiyarki kuwa? Babu sallama sai ihu haka? Menene yake faruwa? Me Hauwa ɗin ta yi maki?". Da gaji maganar tsohuwar nan kasa ta firgice, baiwar Allah maman Zee ta ɗaga mata hankali babu shiri.
"Mama Hauwa ta cuceni, ta kaini wajen boka, da kai'na kuma tasa na bawa baban Zainab maganin da zai sota, da kuɗina kuma muka karɓo maganin, yanzu shikenan sonta yake, ga shi can ya ɗauketa sun tafi, na shiga ukuna, mama ki taimakeni kada na mutu". Yadda take maganar zaka fahimci cewa tabbas ba'a cikin hayyacinta take ba, bata ma san me bakinta yake faɗa ba, kawai sambatun surutai barkate take yi.
Ƙara rikicewa ƴar tsohuwar nan ta yi, sai cewa take yi. "A'isha ki nutsuwa ki yi mun magana a nutse ta yadda zan fahimta, yanzu ni bana iya gane komai da kike faɗe". Ita ma tana magana tana haɗe words, saboda a rikice take, kun san irin wannan call ɗin ma sai mai dakiyar zuciya yake iya jurewa baya suma, amma a kiraka irin haka ana kuka ga shi ba gari ɗaya kuke ba, baka san halin da ake ciki ba kuma baka san kan zance ba, in fact bata ma taɓa kiranka ta ce maka tana cikin wata damuwa ba, rana tsaka kawai ayi maka irin wannan kira ai dole bawa ya rikice, idan akwai abin da ya fi rikicewa ma yi zai yi.
Sai sambatu maman Zee take yi ta kasa iya nutsuwa, a haka dai ta kwashe duk abin da ya faru tun daga farko kan auren Khadija da Haidar har izuwa yau ta gayawa mamar tata, tana yi tana kuka hawaye bibbiyu.