Rawanin zalinci 1 complete - Chapter 90
Rawanin zalinci 1 complete Chapter 90: Rawanin zalinci 1 complete Chapter 90. Tashin hankali kenan, ɗan tsokaci a tsakanin Mamma da Kamran kenan, menene…
386 words
Tashin hankali kenan, ɗan tsokaci a tsakanin Mamma da Kamran kenan, menene dalilin Mamma na hana shi sanin tarihin babansa bayan ya buƙaci sani? Waye shi? Ina mahaifin nasa yake? Meyasa take cewa zai mutu idan ya sake yin magana a kan babansa? Meyasa?!!.
SWEETIE.🔥
"Ɗago idanunki da kyau ki kalleni, sannan kuma ki yi mun shiru, a nan ba'a son hayaniya, kada ki bari a jiyo ki".
Shiru dole ta yi ba dan ta so ba, sai dan tsoron irin muryar da ta ji anyi mata magana da shi, tabbas wannan murya da ta ji ba muryar wasa bace, kuma da alama babu imani a tattare da mai wannan murya ko ɗigo.
"Ina Spender yake? Shi kawai muke da buƙatar ki bamu, kina bamu zamu sakeki, mu bamu da bukatarki a nan wajen!". Wannan murya ce ta sake katseta da faɗin hakan.
Su waye su? Meyasa suka ɗauketa? Menene Spender? Ina kuma yake? Me zasu yi da shi?.
Murya a dashe saboda kukan da ta rinƙa sha tun safe, murya ya dashe, da kyar ta iya furta. "Menene Spender?".
A fusace Delisha ta ɗaga wannan katakon hannu nata zata zabga mata mari, dan a ganinta Sweetien ta raina masu wayo ne, ta isa tace bata san Spender ba? Ba zai yiwu ba dole ta basu yau, abin da suke haukace suke nema, nemansa suke yi kamar hauka, kuma sun san yana wajenta, sama da shekaru biyar suna nemanta, da kyar suka ganota, sun sha bakar wahala a nemanta, amma ta nuna masu bata ma san shi ba? Tama isa?!!.
Tana ƙoƙarin sauke mata wannan katakon hannun nata a saman lallausan kumatunta kwatsam ta ji hannun nata ya sage a saman iska bai ƙarisa kai saman kumatun Sweetien ba.
Yar karar azaba ta saki kafin ta furta.............
Kai kai kai taɓa ka lashen ya isa haka my people's, sai dai mun haɗu a step two kawai, akwai cakwakiya over. Hanzarta ki biya kuɗin karatu dan ki morewa ganin wannan cakwakiyar!.🤸💃💃
Ƴan Niger kuma ban barku a baya ba, ku mun magana ta wannan numberta ɗin dan na gaya maku ta yadda zaku yi naku payment ɗin. 08161390581
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍