Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 26
Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 26: Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 26. "Dalla kada ka bada maza. Kawai ka sabunta mata…
4,436 words
"Dalla kada ka bada maza. Kawai ka sabunta mata karatu yau yau ɗinnan. Su fa mata kana rarrashinsu ka gama dasu."
Taj ya gyaɗa kai "Allah bari in samu a kai min rigimammiyar nan gida. Zan yiwa su Mama famfo akanka sosai. Dr. Mubina will be Mrs Happiness."
Kamal murmushin yaƙe kawai ya yi. Taj ya yi wanka ya saka shirt da wando abinsa ya zo zai fita.
"Wani sabon salon wulaƙanci ne wannan ko me? Ina kayan da Abba ya karɓo daga wajen tela?"
"Direba fa zan yi. Amma ta ce ba zan shiga ba. Kuma kawai sai na saka sababbin kayana su yamutse?"
"Kaina ciwo yake Happy. Bani da ƙarfin yi maka surutu. Kayi abin da ya dace ka fita."
Kamar ya yi musu sai dai yaga babu alamun wasa tattare da Kamal ɗin. Dama kuma tsokana ce tasa shi saka waɗancan. Ya canja da wasu sababbi cikin na bikin. Sai gashi yayi kyau sosai. Ya tambaye Kamal ko zai sha magani ya ce a'a. Gajiya ce.
Taj na fita ya kira Mubina ya faɗa mata jikinsa fa babu daɗi. Tana hanyar zuwa wurin kamun ita da ƙanwarta don har gida Yaya Kubra ta aika mata katunan bikin duka. Dole ta juya ta koma asibiti. A hanya ta sauke ƙanwar ta ta tace mata patient gareta.
Ruwa ta saka masa da wasu magunguna masu ƙarfi har ya dawo daidai.
"Ban faɗawa Dr. Kubra ba saboda bana son raba mata hankali. Ciwon nan mun barshi tsakaninmu zuwa lokacin da za a gama bikin ɗan uwanka kamar yadda ka buƙata. Idan bata faɗa ba ni zan je har wajen Alhajinku wallahi."
Ranta a ɓace yake. Kamal ya yi mata murmushi. "Wannan faɗan duk don na hanaki zuwa cin shinkafar biki ne ko?"
Harara ya samu "Wasa ma ka mayar da abin?"
"Sorry Doc." Ya ɗauko wayarsa dake gefen gadon "zo mu yi hoto."
Yadda ya yi maganar ya taɓa mata zuciya. Tayi murmushi duk da tana ƙoƙarin nuna masa fushinta. Ya gyara zama ta koma gefensa ta zauna tayi musu selfie. Tana tashi ya ɗauketa wasu. Bai taɓa ganinta da kwalliya irin ta yau ba. Kasa haƙuri ya yi ya ce da ita,
"A misali da zan warke za ki iya aurena Mubina?"
Abin control ɗin gudun ruwan da take ƙara masa take dubawa da ya yi tambayar. Yasa ta kusa ture ƙarfen gabaɗaya saboda yadda zancen ya taɓa ta. Allah Yasa bayanta yake kallo da yaga halin da ya jefa zuciyarta. Tattaro nutsuwa tayi
"A'a."
"Ni? Ni?" Ya nuna kansa kamar yato ya sanyata dariya "nayi tsammanin za ki bani amsar da zan ji daɗi."
"Baka cancanci hakan ba Kamal. You are very stubborn. Rantsuwar dake kare alaƙar likita da patient ce kawai ta hanani yi maka handsfree."
"Na nawa kuma? Ba kin faɗawa Yaya Kubra ba?"
"Da kai da ita akwai wanda zai rantse cewa na faɗa? Magani ta gani ta zo tayi tambaya."
Kallonta kawai yake yi yana jin inama ƙalau yake. Da ita ma tana wajen Kamu ana kama masa ita.
"To da ace ni ɗin patient ne mai bada haɗin kai irin yadda kike so, za ki iya aurena idan na warke?"
Sai da ta kalli idanunsa sannan ta bashi amsa "Da gudu" sai kuma ta soma hawaye "please let us help you Kamal. Akwai dama indai mu ka sami donor. Kada ka ɗora min zawarci tun kafin nayi aure don Allah."
Tana gama faɗin haka ta fice saboda kukan da take shirin yi a gabansa. Shi ma hawaye ya goge bayan ta fita. Yana tsoron sanya rai da rayuwa bayan samun lafiyarsa ba abu bane mai sauƙi. Shi yasa yake ta kaucewa sanar da mutane. Amma zai bi shawararta. Idan an gama bikin Taj da kamar sati ɗaya da kan shi zai faɗawa iyayensa.
*
Mota Sajida da Fadila su ka rako Hamdi bayan an rufa mata wani net ja wanda dama an faɗa musu da shi za ta fara shiga. Sai an yi kamun za a cire mata. Haka aka rufe motar gabanta yana matsanancin faɗuwa.
A hankali yake tuƙi cikin nutsuwa. Ƙamshin da take yi ya kwance duk wani notin arziƙi na kansa. Yana son yi mata maganar abin da ya faru amma yana jin nauyin hakan. Kamal ya ce ya bata haƙuri. Amma idan kuma ya bata ta sake yi masa maganar da wancan yanayin zai dawo fa?
Tsoron da yake ji bai kai nata ba. In ka cire gaisuwar da tayi masa a gaban su Sajida bata sake ko da ɗaga kanta ba. Kwata kwata bata yarda da bakinta ba. Yanzu dai lafiya ƙalau su ke tafiya. Idan kuma tayi magana irin kalaman nan dake fita da kansu su ka bar harshenta fa?
Kowa kama bakinsa ya yi. Da Salwa za ta ga yadda aikinta ya yi tasiri a wajen nan da ta daka tsallen ƴan bori ta dire don murna.
Shirun damunsa ya yi ya kunna musu rediyo. Tashar farko da ya samu ya bari. Aka yi dace ko rashinsa domin kuwa a daidai lokacin mai tallan maganin gargajiya ce take ta kwararo bayanin maganin basir.
(Wato shi fa basir idan yaci jikin magidanci sai kaga ko kukan jarirai an daina yi a gidansa. Cikinsa kullum a ƙulle tamau kamar yarinya tana koyon ɗaurin zani. Da shi da matarsa babu maraba. A jaraba maganin nan domin kawo ƙarshensa. Akwai mai tsiro, da mai jini.)
Cikin kujera Hamdi ta shige saboda tsabar kunya. Mai magani ta cigaba da ɓaro zance mai nauyi. Aka barta da satar kallon Taj. Ɗan duniya da ya fahimci kunya take ji sai ya ƙara volume. Can sai cewa yayi
"Nagode Allah ni dai ƙalau nake. Masu fama kuma Allah Ya yaye musu."
Shiru tayi tana ƙifta idanu. Gara yayi mata waƙoƙinsa akan wannan magana.
Kallonta ya yi ya saki murmushi. Wani irin jindaɗi da nutsuwa yake ji a ransa. "Ko kina da shi in saya miki..."
"Innalillahi..." ta kalle shi babu shiri ta yaye lulluɓin.
Numfashi ya ja da ƙarfi da su ka haɗa ido. Tayi masa kyau ba kaɗan ba.
"Ni lafiyata ƙalau wallahi."
A daidai lokacin mai maganin ta zaɓi ɗora zancenta da dawowa kan mata.
(Na dawo gareku matan gida. Ina da magunguna sahihai waɗanda mu ka gada tun kakanni. Maganin sanyi da magungunan mata masu gigita maigida.)
Hannu ta kai za ta kashe rediyon ya damƙe shi yana murzawa a hankali.
"Don Allah ka canja."
"Shhh...an zo wajen naku. Bari mu ji."
"A ji me?" Ta tambaye shi looking horrified.
(Mace sai ta bari sanyi ya gama cinye mata jiki. Sai miji ya mayar da ita bora sannan za ta fara neman magani. Ina mai fama da ƙaiƙayin...)
Hamdi ta dube shi kamar tayi kuka. "Allah idan baka kashe ba zan iya yin kuka."
"Allah Ya baki haƙuri. Daga taimako?"
"Ba na so." Ta turo baki.
Soyayyarta da ta kwanta wucin gadi ta dawo masa sabuwa fil. Ba ƙaramin kewar wannan Hamdin yayi ba. Yana son faɗa mata amma sun riga sun iso gidan Alh. Lurwanu. Inda zai ajiyeta Amma ta faɗa masa bayan ya shiga ciki da motar. Yana hango masu rakata wurin zamanta su Zee da su Firdaus.
"Wanne zan saya miki? Kin dai ji ance mace bora take zama idan bata sha ba."
Tsuke bakinta tayi. Sai da ya buɗe lock za ta fita ta yi magana a hankali yadda babu mai ji cikin ƴan rakiyarta.
"Nafi ƙarfin zama borar gida."
"Za ki maimaita wannan maganar nan da saturday."
"Allah Ya kaimu" ta faɗi sannan ta ƙifta masa ido don tsokana.
A tunaninta za ta samu guduwa ne a lokacin. Sai gashi su Firdaus sun dage sai sun yi musu hoto kafin a shiga da ita ciki. Fitowa yayi daga motar ya tsaya a gefenta.
"Kai Uncle Taj. Irin wannan hoton tun zamanin su Mama. Ku ɗan ƙara matsowa mana."
Hamdi bata ankara ba taji ya janyota kusa dashi. Hannunsa ɗaya a tsakiyar bayanta. Jin kamar za ta faɗi sai ta ɗora nata hannuwan a kafaɗunsa.
"In miki waƙa?" Ya ce a saitin kunnenta. Hakan ya bada style na hoton masoyan da su ka yi nisa da ƙaunar juna.
Ta san tsokanarta yake yi shi yasa tayi dariya. A haka aka ɗauki hoton. Ya yi kyau sosai.
Bayan an gama taro mai ban sha'awa da Firdaus ta koma gida ta dinga ɗora hotunan kamu a status. Kuma wannan hoto shi ne na farkon da Salwa ta fara cin karo dashi. Zuciyarta a take ta ɗauki zafi. Ta juya ta kalli Mami dake kwance tana bacci ga yawu yana dalala ta gefen bakinta. Dole taje Kano ko ta wane hali. Wayarta ta ɗauko ta kira Ahmad ta faɗa masa hatsarin da Mami tayi da roƙonsa akan ya dawo dasu Aminu Kano Teaching Hospital saboda a nan Bauchi babanta yaƙi sakin kuɗi a dubata yadda ya dace (a ƙaryarta). Duk da baban nata ya gargaɗesu da ƴan uwanta da su yi shiru har sai ta farfaɗo saboda bai san me zai cewa Ahmad ɗin ba. Yana kunyar yaron kuma yana tsoron sake ɓatawa Alh. Hayatu rai.
"Me ya sa zai ce kada a faɗa min? Kwananku nawa a asibitin? Shi ne kullum idan na kira ki ke min ƙaryar ƙauye ta tafi" Ahmad ya ce cikin tashin hankali.
"Sharri aka yi mata wai tayi masa asiri."
"Zan kira shi mu yi magana. Ku shirya, idan na zo gobe in sha Allah sai mu taho tare." RAYUWA DA GIƁI 27
Batul Mamman💖
_For Maryam Yusra because you deserve it! Allah Ya baki lafiya._
(Don Allah duk waɗanda su ka biya kuɗin talla na cikin labari kada su ƙosa. Saboda kun fi son wanda zai fito cikin labarin dole sai an zo gaɓar da zai dace. Ina fatan jinkirin ba zai sa muku damuwa ba. Har kullum ina godiya. SonSo)
***
A mafarki ko ido biyu, Alhaji bai taɓa tunanin zuwan wannan rana ba sai da ta zo ɗin. Yau dai zahiri ba zance ba shi ne yake zaune a cikin falonsa babu kowa sai masu gadi da direbansa dake bakin gate su na hira da daddare. Gabaɗaya gidan ana idar da sallar magariba su ka daɗe. Duk an tafi wajen dinner ɗin Taj da Hamdi. Hatta masu aikin gidan babu wanda aka bari. Kasa zaman falon nasa ya yi ya shiga ɓangaren matan gidan. Nan kam sai da zuciyarsa ta motsa da tausayin kansa. Shiru ne mai ratsa ɓargo. Sai kayayyyakin ƴaƴansa da jikoki da ba a gama tattarewa ba. Wasu ma a ƙasa su ka bar nasu.
"Ganɗoki" ya yi murmushi yana mai duƙawa ya ɗauke kwalbar turaren da aka bari a ƙasa.
Samun kansa ya yi da tsince duk wani abu dake ƙasa wanda bai kamata ba. Yana yi ransa na tunatar dashi cewa duka mutanen da su ka shirya a wajen nan da ɗakunan matansa fa nasa ne. Zuri'arsa ce. Shi kaɗai a shekarunsa sittin da takwas ya tara jikoki sama da arba'in. Ga ƴaƴa ga tarin dukiyar da ko yau ya ajiye kasuwanci ba za su buƙaci komai ba a shekara goma masu zuwa.
Ya auro mata masu mabambantan tushe amma waɗanda su ka yi tarayya wajen taya shi gina gida irin wannan. Tabbas shi ma ya sani cewa arziƙinsa ba a naira da kwabo yake ba. Iyalinsa sune arziƙinsa. Banda dai abubuwan yau da gobe da ba a rasawa amma ya tabbatar cikin ƴaƴansa babu fasiƙi. Allah Ya yi masa gamdakatar Ya shirya masa zuri'a. Kuma komai ya ce ya zauna daram kenan a gidan. Duka ya ɗauka ƙarfin ikonsa da tsare gida ne wanda cikakken namiji kaɗai ke iyawa.
Sai gashi an wayi gari sun haɗa kai suna neman juya masa baya. Jiya sun tafi wajen kamu ƙwai da kwarkwata. Bayan saboda girman gidansa ƴaƴan dangi ma suna cin arziƙin ayi bikinsu a nan. Shi su ka tafi gidan Alh. Lurwanu don su nunawa duniya gazawarsa. Yau kuma Hajiya ta ce masa event centre za su je kuma sai an gansu. Abin tambaya a wajensa yanzu shi ne wai me yasa su duka su ke ganin aibun hukuncinnda ya yankewa Taj? Anya sun san yadda illar dake tattare da daudanci? Habibunsa fa daga son girki ya fara kamar wasa. Idan a baya Taj bai yi ɗabi'un mata ba yanzu zai iya. Surukuta ta shiga tsakaninsu da ɗan daudu kuma ga aiki suna yi tare. Ya numfasa a yayinda ya zauna ya kula cewa gyara sosai ya yiwa falon. Dole ne ya raba Taj da Hamdi. Barazanar da ya yi a Bauchi bata nufin ya karɓi wannan aure. Salwa ce ba zai taɓa bari ta kusanci danginsa ba. Duk lalacewar ɗan daudu yafi mushriki a wurinsa.
***
Ƙememe Yaya taƙi shiryawa,wai ba za ta je wajen bikin ba. Duk ga ƴan uwa za su wakilceta. Za ta zauna a gida da Innarta Luba da ta zo jiya. Aka kaɗa aka raya taƙi chanja shawara. Gashi ƴan matan nata duka ukun basa nan. Yanayin gidansu bai basu damar yin ƙawaye ba. Shi yasa duk wani abu da za ayi da ƙawa tare su ke yi.
Tun azahar Safwan ya kwashesu zuwa event centre ɗin inda a saman wurin ne za a rangaɗa musu kwalliya. Kowacce mijinta ne ya biya mata. Ita Hamdi lalle aka fara yi mata. Ɗaya daga cikin yayyen Taj tana da saloon da wurin lallen amare da na matan ƙwalisa. Wadda tafi iyawa ta tura ta yiwa Hamdi baƙi da ja. Tun kafin a gama ake santin kyawun da yayi. Ana gamawa aka koma kwalliya bayan tayi sallar la'asar. An fito da ita fita ta girma. Sai wanda ya sani ne kawai zai iya gane ita ɗin Hamdiyya ce ɗiyar Habibu Simagade. A haka kuwa za ka yi zaton ƴar wani ƙusa ce. Ana kammala kwalliyar tayi sallar magariba sannan ta saka kaya.
Anti Labiba ce ta kira Sajida ta faɗa mata rigimar da ake yi da Yaya akan ta shirya. Sajida tana ji ta san babu wani kunya ko kawaici da yasa mahaifiyar tasu son zaman gida. A nata tunanin rashin zuwan zai taimaka ya ɗago darajar ƴaƴanta a idon mutane. Bata son yin abin da zai janyo mata ido harma ayi ta ambaton ita ce maman amarya, daga nan wanda bai sani ba a bashi labarin cewa babansu ma tsohon ɗan daudu ne.
"Don Allah ba ta wayar Anti."
Harara kala kala Yaya ta gama yiwa Anti Labiba kafin ta karɓa.
"Yaya me yasa ba za ki je ba?"
Caraf a kunnen Hamdi. Ta karɓi wayar ana yi mata ɗauri da wani yadi haɗe da net mai santsi.
"Yaya ba za ki ba?"
Shiru tayi saboda taji yadda muryar Hamdin ta canja.
"Yaya?"
"Ina jin ki. Ga iyayenku nan. Kowa zai je. Me zan je yi ni kuma?"
Zee da Sajida kusa da Hamdi su ka dawo su ka kara kunnuwansu. Kowacce tana iya gane zancen na Yaya akwai damuwa a ciki. Hamdi sai cewa tayi,
"Wallahi Yaya idan baki je ba nima daga nan gida zan taho." Su Zee jinjina mata su ka yi da thumbs up da ta faɗi haka.
"Ke ba na son rashin kunya."
"Allah Yaya. Zan zauna a saman nan har sai kin zo."
Sajida ta miƙawa wayarta ta koma aka cigaba da ɗauri. Sai dai ana yi ƙwalla na sauko mata. Mai kwalliya tabi ta tada hankali. Idan kwalliyar ta caɓe ko amarya bata sauka da wuri ba za a sami matsala.
"Za fa ta zo tunda taji kin yi rantsuwar nan." Cewar Sajida.
"Ke ma ai bata je naki ba." Zee ta tunatar da ita.
Ita dai me kwalliya haƙuri ta soma bawa Hamdi ganin wankin hula yana neman kai su dare. Sai da ya rage pins kawai za a saka a jikin mayafi da head ɗin sannan kukan nata ya ƙaru. Daga can ƙasan zuciyarta take yinsa. Ta ƙara jinjinawa uwa a duk inda take. Babu yadda za ayi ace Yaya bata son ganin ƴaƴanta a wajen bikinsu suna walwala kamar kowacce uwa. Amma kawai don kada a aibata mata su saboda yanayin tafiyarta shi ne ta zaɓi zaman gida.
Da bikin Sajida duk sun ɗauka kawaicin uwa ne. Musamman da basu ga mahaifiyar Safwan a wajen event ɗin nasu ba (baban Safwan ya hanata zuwa). Yanzu kuwa jiya komai da iyayen Taj aka yi. Yau ma su ne ƙirjin biki. Sai ace babu mahaifiyarta? Saboda miskiniya ce.
"Ya Hamdi meye haka ne? Ji idonki har ya soma caɓewa fa." Cewar Zee ta ƙara miƙawa mai kwalliyar tissue domin a gyara idon.
Sajida wayarta ta shiga dannawa tana cewa "bar ni da ita."
Sai ji su ka yi tana gaishe da Taj. Ta kuma faɗa masa kukan da Hamdi take yi da dalilinsa.
"Saka mata wayar a kunne."
Da canjin numfashin da yaji ya gane ta saka mata ɗin. Da rarrashi ya yi mata magana.
"Zan kawo miki Yaya in sha Allahu. Ki daina kuka idan ba haka ba kuma yau sai mun yi kuch kuch hota hai a gaban mutane. Mu yi ta rangwaɗa kai kamar ƙadangaru."
Dariya ce ta kama Hamdi. Sajida, Zee da maikwalliya su ka saki baki suna kallon ikon Allah.
"Waƙar bata da hayaniya sai na taya ka."
"Haka ki ka ce?" Ya tambayeta yana murmushi "Wayarki na kusa?"
"Eh"
"To ki dubo waƙar I am a disco dancer a youtube. Ni kuma idan baki daina wannan kukan shagwaɓar ba in baki mamaki a gaban mutane. Ita zan yi. Kin kuma san zan iya. 80s aka yi ta ba ta zamaninku bace."
"To Baba Happy. Na ma share hawayen" ta goge idonta da kanta don barazanar Taj ba abin da za ta share bane.
"Wannan ladabin ba na gaske bane. Sai na tambayi Sajida naji ko kin ƙara yin kuka."
"Allah na daina."
"Hamdiyya" ya kirata a tausashe.
Kasa buɗe baki ta amsa tayi saboda kiran nasa na daban ne. "Uhmm"
"I'll see you later."
"Bye" ta miƙawa Sajida wayar.
"Iiiiiikon Allah" Sajida ta faɗi baki buɗe "me zan gani ni Sajida ƴar Habibu? Hamdi? Dama rashin jin muryar mijinki ne yasa ki kuka? Shi ne ki ka ɗorawa baiwar Allah Yaya. Ai kuwa bari nace mata tayi zamanta."
Da sauri Hamdi ta miƙe tana kici kicin karɓe wayar "ɗaukota fa zai je ya yi. Shi yasa ki ka ga nayi dariya."
Zee tayi dariya "anya kuwa? Naji fa kina zancen wata waƙa wai bata da hayaniya."
"Ke, kira Ya Baballe ku gaisa kema ki ji daɗi."
"Baballen lafiya? Sunansa Sadiq" ta faɗa tana kallon yayyen nata.
A tare su ka bushe da dariya sannan Hamdi ta koma ta zauna aka gyare fuskarta kamar bata yi kuka ba. Ana gamawa ta koma gefe ta buɗe youtube. Hannunta yana ƙaiƙayin ganin waƙar da Taj yake cewa zai yi. Da ta kunna ɗaya tayi kama da ta 80s ɗin daga ɗaukan ma. Ɗayar kuwa ɗaukan zamani ne. Bata ma ɓata lokacin kallon ta zamanin ba wadda ta kasance remake ɗin tsohuwar. Danna tsohuwar tayi inda kunya ta kusa sumar da ita da rawar da Mithun yake yi. Saboda raye raye nan taƙi jinin waƙe-waƙe. Idan Taj ya yi wannan girgizar da karya jikin tabbas a wurin dinar za ta tafi ta barshi.
Su Zee dai kallonta kawai suke yi. Tana duban waya da ido ɗaya tana kawar da kai.
"Ta fa ci kai wannan." Sajida ta faɗi su ka yi dariya ko kula su bata yi ba duk da taji.
*
Da Taj ya gama wayar, ji ya yi an ture shi. Sai lokacin ya ankara ashe a jikin Kamal ya jingina da shauƙi na ɗibarsa. Ya rasa me yasa shi da Hamdi basa iya yiwa juna baƙunta. Kamar ba jiya jiyan nan da sauran ƴar rigimarsu ba. Yau kam komai ya wuce!
Ɗaure fuska Kamal ya yi "Na ma rasa abin da zan ce maka Happy? Wato haka ake soyayyar ni ka barni ina fama da instagram da daddare?"
Taj ya kama dariya "ba dai ka tsaya wasa ba? So kake sai Dr. Mubina ta kawo maka katin aurenta ka zo ka ce min zuciyarka za ta fashe ko?"
"Allah ma Ya kiyaye. In sha Allah ba zan ga aurenta ba." Cewar Kamal yana mantawa da wa yake magana.
Wata irin juyowa Taj ya yi yana kallonsa "saboda kai za ka aureta ko kuwa ƙasar za ka bari idan ta tashi auren wani a dalilin nauyin bakinka?"
Wayancewa Kamal ya yi "likitoci na auren ƴan kasuwa ne? Idan rabon wani ce sai in tafi China odar kaya kafin a gama bikin."
Tsaki Taj ya yi "ta nan kuma ka ɓullo? Hmmm, kai ka san yanayin aurena da matsalar Alhaji ne su ka shige min gaba. Ba don haka ba da yanzu kai ma kana kwanciya kamar gasara a ruwa idan kuna waya."
"Wannan karin magana ne ko me?" Kamal yana dariya ya tambaye shi.
"A bakin Ƴar Ficikar nan naji."
Dariya su ka yi sannan Kamal ya ce zai fita waje ya tada mota kafin Taj ya fito sai su ɗauko Yaya. Ɓata lokacinsu faɗan iyaye zai jawo musu.
Yana fita Taj ya bishi da ido. Jikinsa yana bashi tabbas akwai abin da ɗan uwan nasa yake ɓoyewa. Kwana biyu ma tunda ya dawo ya gan shi a rame. Yanzu ne ma ya ɗan ciko. Zuciyarsa ta bashi ko ma mene ne ya shafi Dr. Mubina. Kuma yafi tunanin ƙila soyayyar Happiness ce bata karɓa ba. Da an gama bikin nan zai je ya sameta har asibiti ko ya nemi gidansu. Indai ba wani aka bawa ita ba zai nuna mata cewa rashin karɓar Kamal asararta ce. Happiness is a rare gem. Ko shi da ya same shi a matsayin ɗan uwa ba ƙaramin dace ya yi ba.
Ƙarasa shirinsa ya yi su ka fice daga gidan. A daidai bakin layin su ka ga motar Ahmad wanda dawowarsa kenan daga Bauchi. Horn su ka yiwa juna. Basu kula da Salwa a gaban motar da kuma Mami dake kwance a baya ba.
Kiran wayarsa Kamal ya yi yana sanar dashi kayansa wanda duka ƴan mazan gidan zasu saka banda ango suna ɗakinsa. Sun bawa Anti Zahra ta ajiye masa kafin ta tafi.
"Zan ɗan makara amma. A gajiye nake."
"Wai ina ka je ne? Ance tun safe ka fita."
Ahmad ya kalli bayan motarsa ya sauke numfashi.
"Sai mun haɗu dai."
Da taimakon Salwa su ka shigar da Mami cikin gidan. Gabaɗaya ta rikirkice saboda ƙamshin turaren Taj da hancinta yake iya bambancewa duk inda ta ji shi. Ɗakin da take zama Ahmad ya ce su shiga da Mami.
"Bari nayi wanka naje wajen dinner ɗinnan. Ba zan jima ba in sha Allah. Gobe da safe sai mu tafi asibitin."
Da azama ta miƙe ita ma bayan ta kwantar da Mami "Nima bari na shirya kafin ka fito."
Haɗe fuska Ahmad ya yi "Salwa."
"Na'am." Sai kuma tayi murmushi "wallahi sauri zan yi Yaya."
"Ba ki da hankali ashe." Ya nuna kansa yana juya ɗan manunin yatsansa cikin ɓacin rai "wa za ki barwa Mamin da kike zancen zuwa dinner?"
Murmushi tayi "lahh, Ya Ahmad ai kai ma ka san ba zan tafi haka kawai ba. Tun a hanya nayi magana da Anti Zabba'u (ƙanwar Mami). Tana hanya ma don na faɗa mata mun shigo gari."
"Yaushe ku ka yi maganar ban sani ba?" Ahmad ya tuhume ta.
"Tun jiya ne bayan mun yi waya da kai."
Zama ya yi a gefen gadon yana matse gaban goshinsa kafin ya ɗaga kai ya kalleta da takaici.
"Dama shirinki kenan shi yasa ki ka yi min ƙaryar Alhajinku ba ya kula da lafiyarta?"
"Wallahi Yaya..."
A harzuƙe ya tashi kamar zai kifa mata mari "Shut up Salwa. You are very stupid."
"Don na ce zan je bikin ƙaninka kake zagina Ya Ahmad?"
"Ba za ki ba! Ko ƙalau Mami take babu inda zaki. Haba! Yarinya kin bi kin haukace kuma kina neman haukata kowa. Taj baya son ki, kuma ko yana so ina cikin masu hana shi aurenki saboda baki san bambancin so da obcession ba."
Kuka ta fashe masa dashi. Tana jin saukar maganganunsa tamkar sukar mashi. Sai ta mallaki Taj a matsayin miji kuma akan idonsa ta ƙudurta a ranta.
Mami tana daga kwance tana ɗaga lafiyayyen hannunta akan su yi shiru. Kallonta Ahmad ya yi ya fice kawai domin dai ba a canjawa tuwo suna. Alh. Mukhtar ya faɗa masa komai da yaje ɗaukarta. Ya kuma sanar dashi cewa ya saketa sannan idan sun tafi to ta tafi kenan daga rayuwarsa. Har abada baya son sake ganinta. Ƙannen Salwa mazan suna wajensa. Ita kuma ya ce idan sun gama zaman asibiti ya dawo masa da ita domin aurar da ita zai yi. Sun gama magana da wanda zai aureta ma.
Wannan ne dalilin da yasa ya taho da ita. Ba wai ƙaryar da tayi masa ba. Don tabbas komai na buƙata Ahmad yaje ya samu suna dashi. Kawai mijin nata ne dai ya fita harkarta.
"Zan jira Anti Zabba'u ta iso kafin na tafi." Ta ce da Mami.
"Uhmm uhmm Salwa" Mami ta ce da ƙyar.
"Mami zani fa. Na san da lafiyarki ƙalau za ki bani goyon baya."
Banɗaki ta shiga ta sillo wanka. Ta fito tana cikin shiri Anti Zabba'u tayi mata waya cewa tana bakin gate. Garin saurin ta buɗe mata abu ya faɗo daga jikinta bata sani ba. Yunƙurawa Mami tayi ta leƙa abin. Sai da jikinta ya kama rawa. Sabuwar laya ce don zaren fari ne tas irin wadda take taunawa idan za ta yiwa Alh. Mukhtar magana. Zarginta akan Salwa ya tabbata. A asibiti Salwan tayi zaton bacci take ta ɗauki wayarta ta kwafi lamba. Kuma taji buƙatar da ta faɗa...tana son mallake wani. Sai yanzu ta gane malamin tsibbunta ne Salwan ta ɗauki lambarsa. Kenan duk abin da take yi ƴar na lura? Bata son inda tabi har rayuwa tayi mata wannan atishawar ƴan tsakin ita ma Salwa ta bi. Da ƙalau take duk inda ake takawa zata je domin farincikin ƴarta, amma bata so ƴaƴan su yi wannan rayuwar.
Bakin Salwa kasa rufuwa ya yi da ta buɗe ƙaramar ƙofar gate su Anti Zabba'u su ka shigo. Don ma babu motar Ahmad ta san ya tafi. Gayya guda har su shida. Ita da ƴan matan ƴaƴanta guda uku. Sai babbar bazawara da goyo. Kowacce ta bawa shabiyar baya. Ita ma Anti Zabba'un ta gaji da aure aure ta haƙura. Dama kuma ta jima tana roƙon Mami ta tilasta Ahmad auren guda cikin ƴaƴan nata amma taƙi yarda saboda kar ta san kar ne. Sai gashi Salwa ta faɗa mata halin da Mamin take ciki. Da murna ta kwaso jiki. Ko Ahmad yana so ko baya so sai ya auri ɗaya kuma ya saki wannan mai dara daran idanuwan.