Rayuwa da gibi complete na batul mamman - Chapter 40
Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 40: Rayuwa da gibi complete na batul mamman Chapter 40. Tattaunawa su ka cigaba da yi cikin lumana da…
4,460 words
Tattaunawa su ka cigaba da yi cikin lumana da girmamawa na ɗan lokaci. Hamdi ta ji duk ta takura. Zantukan nasu sun shafe su amma bai kamata ta tsaya musu a wajen ba. Tunanin dabarar ficewa ta fara yi sai ga kiran Bishir ta wayar Hajiya. Ya faɗa mata yana ƙasa tare da Mubina. Wai tana son tafiya Madina ne yau shi ne ta zo tayi musu sallama.
"Amma don ragon azanci ta kasa faɗa mana mu taho tare?"
Dariya taji ya soma yi yayi magana da zolaya "Hajiyarmu ta gargajiya kenan. Yanzu duk ɓarin hawayen da ta gama yi a asibitin nan baki gane komai ba?"
"Me aka yi?" Kafin ya bata amsa ta soma murmushi "kai Bishir ka tabbata?"
"Kin gano kenan" ya kama dariya sosai. Mubina dake gefensa ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin ɓoye murmushin dake neman kufce mata. Ta ji abin da yake cewa ta kuma gane me hakan yake nufi.
Hajiya cewa tayi su hawo da sauri sannan ta zaga bayan Mama ta faɗa mata yadda su ka yi da Bishir. Baki ya kasa rufuwa da Mama ta fesawa kowa zancen. Yaya ma daga kwance ta taya su murna. Sannan ko kusa bata yi mamaki ba. A ganinta dama soyayya ce kaɗai za ta sanya Mubina biyo bayan patient har wata ƙasar.
Alhaji da Abba Habibu ma sun nuna farinciki ƙwarai. Hamdi sai ta sake amfani da wannan damar za ta sulale ta gudu kafin su farga. Kamar haɗin baki ta na buɗewa Taj ya turo Kamal akan wheelchair.
Hirar iyayen a take ta yanke sai tambayar me yake faruwa.
"Wajen Yaya na zo." Kamal ya ba su amsa da kansa.
Murmushi Yaya ta yi masa da su ka haɗa ido "ai bai kamata ka fito a wannan yanayin ba. Taj da ba ka kawo shi ba."
"Nayi ƙoƙarin hana shi Yaya amma wallahi ya ƙi. Dole na kira wani Nurse shi ne ya ɗora shi a nan" ya nuna wheelchair ɗin.
A daidai lokacin kuma Bishir da Mubina su ka shigo ɗakin. Hankalin Kamal ya yi gaba bai kula da su ba da farko. Ya ce Taj ya matsar da shi daf da gadon Yaya. Ya tura shi kuwa jikin gadon sosai. Kamal ya miƙa hannunsa na dama dake ɗauke da canula saboda ƙarin ruwa da ake yi masa ya riƙe nata hannun sannan ya kalli Abba Habibu.
"Abba na riga na zama ɗan Yaya shi ya sa ban nemi izinin taɓa hannunta ba."
Abba Habibu ya gyaɗa kai yana murmushin nan nasa. Ragowar kuwa duka aka yi shiru ana sauraron Kamal.
"Duk wahalar dake tattare da ɗaukar ciki da haihuwa a wurin mata a ƙarshe tana da riba Yaya. Za a kalli mace a kira ta UWA ko da ɗan ba a gabanta yake rayuwa ba. Su kan su mata abinda ya sa su ke jurar wannan wahalar komai tsananinta bai wuce domin samun wannan matsayin ba. Mace za ta zama mai cikakken iko akan wani bawan Allah da yake rayuwa da jinin jikinta." Ya ja numfashi "Allah Yana biyan wahalhalun da ta sha akan ƴaƴanta da mafi ƙololuwar daraja. Ya bata martabar da babu mai kamo ta a wajen wannan bawa har ƙarshen rayuwarsu su biyun." Ya yi murmushi idanunsa fal hawaye. Ko da ya ɗaga kai ya kalli Yaya sai hawayen ya zubo. Nata ma ya zubo...idan ka cire Alhaji, Abba Habibu, Ahmad da Taj, duka waɗanda su ke ɗakin sai da su ka zubar da ƙwalla.
"Yaya wace daraja ki ke tunanin Allah Ya tanadarwa matar da ta bawa ɗan da bata da alaƙa da shi ta jini wani ɓangare na jikinta don ya rayu? Bayan kin san cewa wahala, azabar ciwo da fargabar me zai je ya dawo a dalilin sadaukar da ƙodarki ba zai mayar dani ɗan ki ba. Taki juriyar naƙasu ce a jikinki da lafiyarki. Babu wata riba ta kurkusa ko ta nesa don ban ga abin da za a biya ki da zai maye gurbin ɓangaren jikin ki da ki ka bani ba Yaya."
"Kamal ka yi shiru don Allah. Jikin ka babu ƙwari." Yaya ta faɗi cikin kuka.
"Yadda ɗa baya yin godiya ga iyayensa akan haihuwarsa da su ka yi, haka ni ma ba zan yi miki godiya akan kyautar da ki ka yi min ba. Alfarma kawai na zo sake roƙa domin Allah."
"Ina jin ka Kamal. Don Allah ka daina kukan nan."
"Yaya idan kina lissafin ƴaƴanki ki dinga farawa daga Kamaluddeen Hayatu don Allah." Kuka sosai yake yi a wannan gaɓar. "Idan kina da sirri irin na uwa da ɗa don Allah ki yi dani." Yaya ta gyaɗa kai. "Damuwa ko wacce iri ce irin ta uwa da ɗa kada ki tsallake ni." Nan ma ta sake nuna amincewarta. "Buƙata ko wacce iri ce ta uwa da ɗa ki fara faɗa min tunda kin ga Halifa ƙarami ne. Su Hamdi kuma mata ne ma su rauni."
"To Kamal" Yaya ta amsa cikin kuka.
"Idan su Sajida sun yi miki laifi don Allah kada ki ɓoye min. Ki rufa musu asiri a wajen Abba amma ki sanar dani. Zan yi mu su faɗa tamkar cikin mu ɗaya."
"Na sani Kamal, ko babu wannan abu ai kai me tsaya mu su ne."
Kamal ya girgiza kai "a da sai dai nayi kara, yanzu kuwa duk abin da ya shafe ki Yaya ya zama dolena." Ku san sai a lokacin ya lura da tsayuwar Mubina a ɗakin. Sai ya yafito ta da hannu. Ta so cogewa amma Mama da kanta ta kaita kusa da Kamal ɗin.
"Kin amince da zaɓina Yaya? Idan na auri Mubina ƴar mu ta farko in sha Allahu sunan ku ɗaya. Sunan ta..." ya kalli Hamdi yana jiran ta ba shi amsa.
"Khadija."
"In sha Allahu sunanta Khadija."
Yaya ta rasa abin cewa. Tana gudun zaƙalƙalewa a gaban iyayensa. Gashi kuma ya tsare ta da idanu yana kallonta with so much adoration.
Alhaji ne ya yi stepping in da ya ga ta kasa magana.
"Ba ki ce komai ba game da zaɓin ɗan naki Yaya?"
Yaya ta ɗaga kai a rikice ta kalli Abba Habibu tana neman agajin sa. Ita fa komai bambarakwai take jin sa tun shigowar Alhaji ɗakin nata. Ba ta son yin abin da zai sake janyo wa mijinta abin magana.
Cikin nutsuwa Hajiya ta matso ta kama ɗayan hannun Yaya a yayinda ɗayan har lokacin ya na cikin na Kamal.
"Ko ba ki karɓi tayin da Kamal ya yi miki bane na zama uwa a gare shi?" Ta haɗa hannuwanta biyu tana magiya "Don Allah ka da ki kasa yi masa wannan alfarmar. Kamar yadda ya faɗa babu zancen biya ta kowacce fuska tsakanin mu. Hakan raini ne ma akan girman abin da ki ka yi mana. Ƙara shi cikin zuri'arki ne kaɗai abin da za mu iya duk da cewa mu ne dai da sake samun riba."
"Don Allah ku daina magana irin haka. Domin Allah nayi." Ta zame hannunta dake cikin na Kamal ta nuna ƙirjinta "Karamcin Ubangina a gare ni mai girma ne. Shi Ya nufe ni da zuwa a lokacin da Kamal yake tsananin buƙatar hakan ba tare da sani ko shirin wanin mu ba. Kuma Ya azurta ni da dakewar zuciya na cika umarnin ƙaddara. Ni da har yau nake tsoron allura sai gashi na kawo kaina inda za a yanka min ciki. Na fi ku riba wallahi. Allah Ya bani ikon ceton rai sannan Ya ƙara faɗaɗa ƴaƴana." Ta sanya hannu ta shafa kumatun Kamal. Shi kuwa ya ɗora hannunsa akan nata ya lumshe idanunsa cikin farinciki.
Maimakon kuka kuma sai farinciki ya mamaye ɗakin. Mubina ta kasa daurewa ta bawa Yaya haƙuri domin tana ganin cewa ita ce ta jawo mata zuwa nan ɗin.
"Kada ki sake magana irin wannan Dokta. Mu duka mu na yin komai ne cikin tsarin Ubangijinmu. Ba ki yi min laifi ba amaryar ɗana."
Kunya ta kama Mubina. Ta koma kusa da Hamdi ta sunkuyar da kanta.
Da jindaɗi Alhaji ya ce "Tunda abin ya zo da haka ku ba ni dama na yi mu ku karambani akan Baban Khadija da Maman Khadija mana."
"Innalillahi..." Mubina ta faɗi a kiɗime da jin furucin Alhaji tana mai ƙanƙame hannun Hamdi. Ita ma dai babu halin zolaya kunyar ce ta kama ta.
"Abban Kamal ka yi shiru."
"To Alhaji mun ba ka dama." Abba Habibu shi ma dai yana cikin jin nauyin wannan sabon lamari.
Shi kuwa Alhaji dama da gayya ya yi. Yana so ne ya canja takun mu'amala a tsakanin su tun wuri saboda a sake sabon lale tun kafin su koma gida. Waya ya ɗaga a gaban su ya kira kawun Dr. Mubina, yayan mahaifinta. Ita kanta ba ta san inda ya samo numbar ba tunda bai tambayeta ba. Maganar su ta ƙarshe ita da shi sosai dai tun kwanciyar Kamal a asibiti ne inda su ka fara haɗuwa har ya ce ya san Marigayi mahaifinta.
Ya fara da gabatar da kansa wanda da alamu hakan bai yi wa kawun nata wahalar ganewa ba. Daga nan ga mamakin dukkanin su ya ɗauko maganar su da Kamal. Ya soma yi masa bayanin rashin lafiyar sa sai kawun ya ce ya gane shi. Bai dai san cewa ɗan Alhajin ne patient ɗin da ta dinga roƙonsa har ya barta tahowa duba shi da yin Umra ba.
"Tunda dai har an dace ya sami ƙodar, ina ganin kawai ta zauna ta ƙarasa ladanta. Ina fata ka fahimce ni."
A take Alhaji ya danna speaker yana murmushi sosai. Komai ya zo masa da sauƙi fiye da yadda ya yi tsammani. "Ƙwarai kuwa. Na saka ka a speaker a gaban iyalina, Kamal da ita Mubina. Zan so ka maimaita abin da ka ce domin nima dalilin kiran kenan. Ina son a san da zaman mu zuwa lokacin da Allah zai sa ya sami lafiya ya dawo gida."
Kawu ya maimaita "Ka fi ƙarfin haka Alh. Hayatu. Me yiwu wa ba za ka iya tunawa ba amma ni abin yana raina sosai. Mun taɓa zuwa wajen ka nema wa yaran wasu ƙauyuka kuɗin jarabawar SSCE har su ɗari da sittin da bakwai. Bayan ka biya ka ɗauki ukun farko ka biya musu kuɗin jami'a in full sannan ka sa mu ka yi alƙawarin ba za su taɓa sanin kai ne ba. Shi ya sa wasu lokutan taimako yake zuwa ga bayin Allah ta inda ba sa zato. Sadaka babban jari ce."
Alhaji ya yi ɗan murmushi kawai. Ɗan Adam ba ma'asomi ba. Kullum mu na cikin iyo tsakanin dai-dai da kura-kurai. Yawan tuba, ƙoƙarin fifita aikata ayyukan alkhairi da uwa uwa kyautatawa Allah SWT zato shi ne babbar maslahar rayuwa. Zai iya cewa a tsukin lokacin nan ya ƙara fahimtar rayuwa ta fuskoki mabambanta. Da fari ya yi karo da tsohon kuskurensa sannan yanzu ya gamu da tsohon alkhairi. FABI AYYI AALA'I RABBIKUMA TUKAZZIBAN
Kawu kuma ya ɗora maganar sa. "Mubina ki zauna ki ƙarasa ladan ki har a sallame shi ."
Mamaki tayi sosai "Kawu aikina fa? Kuma ..." ta saci kallon su Ahmad "ba ya buƙatar zama na."
"Ai kuwa ki shirya domin kowa zai tafi ya bar ki da shi. Haɗa ni da Alh. Hayatun."
Jikin Mubina ya yi sanyi ƙalau har ta kasa motsin kirki. Zuciyarta kawai ke harbawa da daidai da fitar kalmomin godiya daga bakin Alhaji domin ya cire wayar daga handsfree. Bayan ɗan lokaci ya miƙa mata wayar.
"Je ki waje ki amsa"
Da sauri ta fita har lokacin tana riƙe da hannun Hamdi. Ita kuma ganin haka sai ta nemi zare hannunta. Mubina ta dube ta da raunin murya. "Raka ni don Allah."
*
Shiru Mubina tayi tana sauraron Kawunta.
"Alh. Hayatu ya ce zai sake kira na anjima kaɗan mu ƙarƙare magana. Idan komai ya tafi daidai in sha Allahu yau zan sauke amanar ɗan uwana, zan aurar dake ga mutumin da na tabbatar ki na so sannan ga dangin da nake fatan ba za su taɓa wulaƙanta ki ba."
"Amma Kawu..."
"Na san ban shiga haƙƙin ki ba da na yanke wannan shawarar. Soyayya ta Fisabilillahi ce kaɗai ta saka ki kusan zaucewa akan yaron nan kafin ki tafi. Yanayin ki ya bani tsoro shi ya sa ban hana ki tafiya ba da ki ka buƙaci zuwa Umra ke kaɗai saɓanin yadda mu ka yi shirin tafiyar gida cikin ƴan uwa."
Kuka ta fashe da shi.
"Ki bar kuka Mubina. Ina son amincewar ki ne domin yanzu zan tafi wajen Umman ki. Ki amince?"
Da ka ta fara amsawa sai ta tuna ba ya ganin ta shi ne ta ce "Uhm" a hankali.
"Allah Ya yi miki albarka."
Rungume Hamdi tayi bayan ta gama wayar. Hamdi ta dinga bubbuga mata baya saboda kuka ne take yi sosai. Bata taɓa zato ko da wasa akwai ranar da burinta zai cika akan Kamal ba. Ta fi karkata da tunanin cewa zuwa yanzu ya ma bar duniyar.
"Ki daina kukan nan haka Matar Yaya. Ni ce ke sujjada zan yi domin wannan babbar falala ce daga Allah SWT." Hamdi ta rarrasheta.
"Nagode Hamdi. Abin ne duk wani iri. Kin ga ana shirin aurar dani babu kowa nawa."
"Gani." Ta sakar mata murmushi "Don Allah ko da wasa kada ki taɓa yi min kallon matar ƙanin miji. Ƴan gidansu sun yi min tarbar ƴa kuma ƴar uwa ba suruka ba. Ina ganin rashin adalci ne zai sa mu kuma mu ɗauki kan mu da wani matsayi daban da na ƴan uwan taka."
* A cikin ɗakin kuma bayan fitar su Mubina, Kamal ya ce Taj ya mayar da shi ɗaki. A hankali ya juya wheelchair ɗin yana mai kulawa da dukkan motsin da zai iya janyo wa Kamal jin zafi.
Sallama Kamal ya yi wa kowa. Da ya zo kan Alhaji sai cewa ya yi da Taj ya tsaya.
"Na ji kana ta magana a hankali ga Alhajin ka tambaye shi da kan ka?"
Taj ya yi turus domin gabaɗaya bai gane me Kamal yake nufi ba. Ya kuma san cewa tunda ya yi haka to akwai abin da yake ransa. Lokacin wana shi ya samu. Sai ya rama ɓoye-ɓoyen da aka yi masa.
"Me ka ke son tambaya?" Alhaji ya zuba mu su ido don ya gano wayon Kamal.
"A bar maganar Alhaji. Zan dawo idan na kai shi ɗaki." Taj ya ɗan tura Kamal sai yaji kujerar ta turje. Kamal ya saki burkin tayar don kada su tafi. Ya yi kalar tausayi.
"Ai gara ka tambaya yanzu saboda ni bana so ka tafi ka barni ni kaɗai."
Abba Habibu murmushi ya yi. It is obvious Kamal a matse yake da son jin manufar maganganun Alhaji a waya. Ahmad kam dariya yake yi sosai.
Alhaji ya yi ƴar dariya shi ma "Kamal ina jin ka. Me Taj ya ke son sani?"
"Cewa ya yi wai ya ji kamar ana maganar aure na."
Taj bai san lokacin da ya ce "Ni? Kamal yaushe?" Don bai yi tunanin tambayar da Kamal ɗin zai yi kenan ba.
Inna ta shigar wa Kamal "Ai tunda ya ce ka yi kawai ka yarda cewa ka yi ɗin don a zauna lafiya."
Da gangan Taj ya ce "Shikenan to." Ya kalli Alhaji "na ji kamar ka na maganar aure na."
Ya yi nasarar tunzura Kamal kuwa don bai san lokacin da ya gyara masa ba. "Aurenka kuma? Yaushe ka yi aure da har ka ke tunanin ƙari?"
"Ƙarin aure kuma Allah na tuba ai ba abu bane mai wahala."
"To wai nufin ka Hamdi za ka yi wa kishiya? Happy akan su fa ni babu ruwana da dangantaka. Hamdi comes first yanzu. Da kai da mazajen su Sajida duk ɗaya ne a wajena. Kai suruki ne, ni kuwa ɗa ne ko Yaya?" Shi ma ya rama zolayar da Taj ya yi masa.
Sai ga Taj da riƙe haɓa. Aiki ya biyo ta kan ma su gida. "Lallai ma! Happiness kada mu ɓata daga farfaɗowarka fa. Har za ka faɗa min kusanci da Yaya?"
"Wannan ko shakka babu." Kamal ya ce kai tsaye "kai ƴa kawai ta baka. Ni kuwa ƙoda ta bani. Akwai jinin jikinta a tare da ni. Tsakanin mu ma babu haɗi.
Mayar da rigimar tasu aka yi abin dariya a ɗakin. Taj ya nemi taimakon Abba Habibu da Yaya ta gyaɗa kai tana supporting ɗin Kamal.
"Abba ka na jin sa fa."
"Ƙyale su Taj kai fa ɗan maigida ne. Shi kuwa Kamal agolan gida ne, ka san su akwai rawar kai. Gida na hannunka. Duk yadda ka dama dole a sha ko ba a so."
Dariya aka sake yi inda Kamal da Yaya su ka ce basu yarda da wannan muƙami da Abba Habibu ya bawa Taj ba. A wannan halin Hamdi da Mubina su ka dawo. Taj ya ja Kamal su ka koma nasa ɗakin. Ahmad kuma ya mayar da Mubina da Hamdi hotel. Yayinda Alh. Hayatu ya cigaba da nasa shirin daga nan. Ƴan uwansa maza ya kira ya sanar da su shawarar da ya yanke. Su ka yi na'am da farinciki. Yaya Babba ya shiga gaba su ka haɗu da ƴan uwan Hajiya, wani abokin Alh. Hayatu da ƴan uwa shaƙiƙan sauran matan mutum ɗaiɗai sai gidan Kawun Mubina. Shi ma kafin zuwan nasu ya riga ya faɗawa duk wanda ya kamata. Ana idar da sallar la'asar wanda ya yi daidai da magrib a birnin Jeddah aka ɗaura auren a masallacin unguwa.
Asibitin gabaɗaya ya kaure da murna. Ma'aikatansu waɗanda su ka san Kamal da Yaya su ma duka sun taya su murna sosai. RAYUWA DA GIƁI 40 ƘARSHE
Batul Mamman💖
Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN
A can hotel Mubina ba ƙaramar takura ta shiga ba. Aure dai an ɗaura amma kamar yadda ta ce babu kowa nata sai dangin miji. Duk sai ta koma abar tausayi. Yaya Kubra ta lura da haka sai su ka yi magana da Yaya Hajiyayye, aka kama mata ɗaki daban domin kwana biyun da su ka yi ɗakunan da su ka kama na group ne masu gado hurhuɗu.
"Hamdiyya ki koma wajenta ki tayata zama. Idan kuna buƙatar wani abu ki mana magana. Na san ba za ta sake da mu ba yanzu kuma sai a hankali."
Hamdi tayi murmushi harda rufe fuska da tafukan hannu "nima dama kunyar taku nake ji har yanzu."
Yaya Kubra ta harareta da wasa "Ehhh lallai, wallahi ki ka sake cewa kina jin kunyarmu sai na yi mi ki handsfree a gaban Alhaji."
"Tsegumta min mana likita. Me ki ka gani? Tajo ya yi ajiya ko? Oh ni uwar babana. Aure ko wata biyu ba a yi ba. Dama na san za a rina. Taj ko kaɗan bai yi kama da salihai ba.
Hararar da take yiwa Hamdi komawa tayi kan Yaya Hajiyayye. "Ke fa daɗina da ke sakin zance wallahi. Don Allah kina yi kina tauna magana kafin ki furzar. Me ya kawo batun salihanci tsakanin mata da miji banda abin ki?"
"Raini ya jima da shiga tsakaninmu dama Kubra. Gara ki kwaye min baya a gaban...." ta waiga babu Hamdi babu dalilinta. Can ta hangota ta kusa ƙure korido tana ta zuba sauri kamar ta kifa. Ita da Kubra su ka haɗa ido su ka kwashe da dariya. Faɗan da ba su ƙarasa ba kenan.
*
Ƙarfe tara da rabi Umma ta shiga ɗakin su Mubina. Hamdi kaɗai ta samu ta kashingiɗe akan abin sallah. Umman na shiga ta tashi zaune.
Umma tayi murmushi "ƙanwar Ango ina amaryar yayanki?"
"Tana banɗaki" ta amsa mata ita ma tana murmushin.
"Ai gara tayi wank..."
Caraf Mubina ta katse Umma daga cikin toilet ɗin da rawar murya. Tsoro muraran ya bayyana a tare da ita.
"Ba wanka nake yi ba. Alwala zan yi na fito."
"Ai ba laifi ki ka yi ba Mubina. Ki yi wankan ki shirya a nutse Alhaji ya ce ni da Hajiyayye mu raka ki asibitin."
"Na'am? Asibiti kuma" Ta buɗe ƙofar ta fito a firgice. Idanunta zuru-zuru sai ɓare-ɓare take yi. Mubina akwai ruɗewa sai a lokacin hakan ya bayyana.
Hamdi ta kalli Mubina sai taji wani tausayinta ya tsirga mata. Shi fa aure kwarjini gare shi na daban. Gashi dai da ƙafarta ta taho ƙasar amma yau ɗaya duk ta sauya saboda alhini.
Umma zama tayi akan gado ta yafito Mubina da hannu. "Mene ne amfanin aure idan mace bata kasance tare da mijinta ba Mubina? Asibitin da kansu su ka ce sun yarje miki zama tare da shi tunda ke likita ce sannan sabon aure."
"Umma ni dai don Allah" sai kawai ta fashe da kuka.
Umma ta tashi tsam ta rungume ta.
"Kamal ɗin ne ba kya so?"
Mubina ta girgiza kai.
"Aure a irin wannan yanayin ko? Ba haka aka saba ba na sani, amma faruwarsa a hakan ya sa naku ya zama special."
Ba kunya Mubina ta ɓare baki "ni dai Mamana, Umma don Allah wajen Mamana zan tafi."
Ɗago kanta Umma tayi ta ce "Tamɓali! Mubina? Shekararki nawa ne?"
Mubina ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana kuka tana murmushi lokaci guda.
"Na fahimce ki" Umma ta sake yin murmushi "ƙarasa abin da ki ke yi ki kwanta"
Ta juya za ta fita Mubina ta kira ta kai a ƙasa saboda nauyinta da take ji.
"Umma ba za ku yi fushi ba?"
"Haba dai. Mubina ba na jin Kamal zai taɓa samun soyayya irin wadda ki ke yi masa. Kin haɗu da shi a halin ciwo kin so shi. Sannan a lokacin da dukkan wata ƙofa ta ƙulle sai Allah Ya yi amfani da ƙudurinki na biyo shi domin..." muryarta ta karye "ku yi sallama sai Ya kawo mafita. Hamdiyya kina ganin akwai..." ta juya ko sama ko ƙasa babu Hamdi sai kawai ta kama dariya "wannan ƙanwar taki ta san yakamata sosai Mubina. A duk lokacin da take jin ana buƙatar keɓewa cikin magana sai ki ga ta bar wajen da dabara."
"Nima na kula Umma."
"Idan ku ka rayu tamkar ƴan uwa tare da sauran yaran namu da matar Ahmad haƙiƙa kun gama yi mana komai."
"In sha Allahu."
"To amarya sai da safe."
Umma ta fita fuskarta babu komai sai annashuwa. Mubina kuwa wata ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi ta faɗa kan gado. Yanzu da Umma ba mai fahimta bace kawai sai a wuce da ita asibiti tinƙis-tinƙis. Gobe kuma a dinga zuwa dubiya ana ganinta a ɗakin Kamal. Ai da kunya!
'Kamal' ta maimaita sunan a zuciyarta. Yanzu fa wai ya zama mijinta. Wani juyi tayi na farinciki tana ƙara yiwa Allah godiya.
*
Hamdi na fita ɗakinsu da Taj ta wuce da niyyar ta ɗauko kayan baccinta ta dawo wajen Mubina. She was just smiling idan ta tuna yadda ta baro Mubinan. Tana ji a jikinta Umma ba za ta matsanta mata ba. Nata key ɗin ta saka ta buɗe ɗakin. Tana shiga taji anyi sama da ita. Ta buɗe baki za ta yi ihu Taj ya sauketa ya jingina bayanta da ƙofar ɗakin. Ya tare mata hanyar wucewa.
"Kina yi su Alhaji za su zo kinga sai mu taru mu yi musu bayanin me ya firgita mu."
Ta harare shi "abin da ya firgita ni dai."
"Da na sani ma a toilet na ɓuya sai kin fi tsorata."
Hango irin tsoron da za ta ji tayi ta yi murmushi "da kuwa mai raba ka da yayana sai Allah."
"Kinga ki kiyaye ni da zancen yayanki ɗan kalen dangi. Yana can gadon asibiti me zai iya? Taj will do what Taj wants." Ya ƙare magana girarsa ɗaya a sama.
Kai ta girgiza "Gobe idan mun je ka maimaita abin da ka ce yanzu in koma gefe in sha kallo."
"You are looking for my trouble fa, and I will give it to you har sai kin ce ya isa."
Dariya ya bata ta kama ƙugu da hannu guda. "Bring it on."
Janyota ya yi su ka nufi 3 sitter ɗin ɗakin su ka zauna. Ta ɗora kanta a ƙirjinsa shi kuma ya sake rungumeta.
"Ƴar caras matar Tajuddeen." Ya kira ta affectionately.
"Uhmmm." Ta amsa muryarta can ƙasa-ƙasa.
Kasancewarsu tare ya saukar mata da nutsuwa fiye da kullum a yau. Jikin Yaya yana ta ƙara kyau. Sai yanzu ta sami damar appreciating zuwa ƙasa mai tsarki a dalilinsa.
"Yau ban ce miki ina son ki ba Hamdi na. I love you."
"Ni ɗin kake so ko ƴar caras?" Ta tambaye shi bayan ta zauna su na fuskantar juna.
"Why do you ask?"
Baki ta tura kafin ta ce "Tun ina yarinya ake cewa jiki zan yi idan nayi aure. Wai ƙirar mu ɗaya da ƴaƴan Anti Zinatu."
"Ƙira kuma sai ka ce wata mota?"
"To dai ance zan yi ƙiba. Kai kuma har wani ƴar caras kake cewa. Kada na fashe nan gaba na daina burge ka."
Damuwa sosai yake iya gani tare da ita. Ya yi dariya ya kuma zolayarta. "Ki fashe kamar wata kwalba?"
"Happy manaaaa" ta buga ƙafa a ƙasa.
He hugged her tightly sannan ya yi magana a hankali.
"Ko me za a ce mi ki, ko me ki ka zama a gaba Hamdiyya ki sani cewa Taj is your home. You can be anything as long as Hamdin Abba Habibu ce ina son abata. Hamdi ƴar tsinke" ya fara ƙirge da yatsansa "Hamdi ƴar doguwa, Hamdi ƴar gajera, Hamdi ƴar lukuta, Hamdi mai tumbi, Hamdi shafi mulera..."
Yana kaiwa nan wata wawuyar cakuma yaji ta kai masa tana rigima ya kwashe da dariya.
"Wai ina faɗa ne don ki san cewa ke nake so ba jikinki ba."
Daga nan ya lallaɓa abarsa su ka kwanta. Sai shabiyu saura Hamdi ta farka firgigit kamar an tsunkule ta.
"Mubina tana jira na mu kwana tare. Ya Subhanallah." Ta tashi tana neman hijabi.
Sai da ta saka tukunna Taj ya ce "to amara ƙirjin biki dawo ki kwanta. Amarya tana wajen Angonta."
"Anya kuwa? Ban ga alamun za ta tafi ba." Ta faɗa masa iya abin da ta gani da Umma taje ɗakin.
Taj ya soma dariyar mugunta. Hamdi tun tana mamaki har ta koma kusa da shi tana jiran ya faɗa mata me ya kawo dariyar.
"Kaza gashin Najeriya" ya ce da ƙyar dariya na cin sa.
"Ban gane ba fa."
"Yayanki..." dariyar harda ƙwalla.
Hamdi ta kama baki "yau ina ganin ikon Allah."
Da ƙyar ya saisaita kansa "ana cewa an ɗaura auren nan yayanki ɗan kalen dangi ya sa ni fita neman kaza. Wai bai dace amarya ta zo babu wani abu da zai tuna mata al'adar gida ba." Yana kallonta ya cigaba da cewa "kin dai sanni da faɗin gaskiya ko Hamdi na...to haka na aje kunya a gefe na nuna masa rashin fa'idar nemo kazar nan saboda kada amarya ta fassara shi yana kwance magashiyan." Ya sake yin dariya.
"Ba ka da kirki fa" ita ma ta soma dariya don ta hango inda zancen zai dire.