Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 10
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 10: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 10. Taj da Anisa su ka saka dariya. Ita tana cewa "yeeyyyy, Hajjo ta tuno…
3,332 words
Taj da Anisa su ka saka dariya. Ita tana cewa "yeeyyyy, Hajjo ta tuno zama cikin turawa."
"Zan zagi babanki wallahi. Zo ki fice."
Kafaɗa Anisa ta noƙe ai kuwa Hajjo ta bita da daƙuwa hannu bibbiyu. "Na iyayenki su uku."
Alamun rashin jindaɗi Anisa ta nuna wanda Taj ya lura. Da ka ya yi mata ishara ta fita daga ɗakin.
"Hajjo sai ki yi ta zagar mana iyaye saboda Allah? Kinga bata jidaɗi ba daga ɗan yin wasa da kakarta."
Lura tayi shima kamar bai jidaɗin ba sai kuma ta saki fuska. Ita a dole Taj ne kaɗai jikanta namiji na wajen babban ɗanta. Tunda ya koma hannun Amma bata taɓa canja masa ba. Saboda tun asali dama kakarsa wadda ta haifi Alhaji da ita ƙawaye ne da su ka yi ƴan matanci tare.
Ita ta fara zayyano masa ƙorafinta akan zaman Amma ita kaɗai a gida ga mijinta a wata uwa duniyar.
"Saura bai fi sati uku ba na koma in sha Allahu. Kuma zan zauna har tayi ritayar. Ai na san zamana ne sharaɗin da yasa ki ka yarda ta cigaba da aikin."
Hajjo ta ƙara sakin fuskarta saboda Taj akwai iya tsara zance.
"Ka san ita mace bata tsufa da buƙatar kulawa. Yau ko ƙwan fitila ne ya mutu wata idan babu namiji a gidan sai dai ta zauna a duhu."
Haƙuri ya sake bata da yaga ya samo kanta kuma ya yi mata bayanin gininsa da ya yi nisa.
"Shi uban taurin kan har yanzu baku daidaita bane?"
Dariya Taj ya yi. Kamar ba ita ta nuna ta daina ƴan mintuna ƙadan baya ba.
"An dawo kansa kuma?"
Ko a jikinta ta ce "Ai Hayatun ne akwai wuyar sha'ani sai ka rantse ni na haife shi. Don ita babar tasu haka take ba cas ba as."
"Ahhhh. Ni fa Hajjo zan tashi wallahi. Harda kakata kuma."
Yadda ya ɓata fuska sai da tayi dariya. Daga nan aka kashe maganar dawowar Amma. Sai kuma ta sako zancen da yake cin ranta. Dama can ba dawowar Amman bace a gabanta. Tafi kowa sanin halinta tunda a gabansu ta tashi. Ita ce ma ta haɗa auren nata da ɗanta. Da gangan ta tayar mata da hankali yanzu kawai don Taj ɗin yazo. Don tayi imanin indai yaji ba zai ƙasa a gwiwa ba zai zo neman sulhu.
"Tajo."
Babu yadda ya iya. Dole yake amsa sunan nan da baya son a faɗi indai daga bakinta ne.
"Nace wai me zai hana ka nemi ƙanwarka Anisa ku daidaita? Karatunta sai gudu yake har an shiga aji huɗu a jami'ar nan."
Gabansa yaji ya faɗi. Duk kirkin Hajjo kowa ya san rigimammiya ce ta buga misali. Yanzun nan sai ta yiwa mutum dabaibayin da zai sarƙe wuyansa bai sani ba.
Ƙofa ya kalla tana gama maganar "Hajjo daina faɗa kada ta zata gaske ne ta soma jin haushina don na tabbatar ba za ta rasa masoyi ba."
Shan kunu tayi harda yi masa daƙuwa. "Ƙaniyarka Tajo."
Ya sunkuyar da kai yana sauraron sababinta.
"Da akwai wanin ai ka san ni ba mai yiwa jikoki shisshigi bace. Sannan na tabbata da daga cikin Jamila ta fito ba ma za ka ce komai ba."
Hankalinsa tashi ya yi ya miƙe tsaye yana ɗan tausar kafaɗarta. "Allah Ya huci zuciyarki. Ba haka nake nufi ba."
"Za ka yi mata maganar ko na kirata yanzu?"
Gani ya yi za ta rushe masa ginin da bai fara saka tubali ba akan yarinyar nan Hamdiyya. Shi yasa da saurinsa ya ce ta bari shi zai yi.
"Alƙawari fa za ka yi min."
"In sha Allahu zan yi mata magana."
Tana jin haka ta washe baki hankali kwance. A ranar da washegari da zai taho bata sake tada wata rigimar ba. Daddy kawai ta kira ta ce masa tayi mai wuyar. Ya fara shiri don ba za ta zuba ido ya bar ƴan mata a gabansa babu aure ba. Da yaji waye zaɓin da ta yiwa Anisa sai taga ya fita farinciki. Kuma da murnarsa ya kira Amma ya faɗa mata. Sai ta nuna masa ta fishi jindaɗi domin ita ba butulu bace. Duk wata gudunmawa da ta dace financially da morally ya bata wajen kulawa da cikar burin Taj.
***
Rayuwa ta fara tsanani ga iyalin Abba. Da yake mutum ne mai sakarwa iyali aji daɗi da abin da Allah Ya hore masa, yanzu da ajiyar ta soma ƙasa sai suke ƙuntata. Yawancin samunsa in ka cire buƙatun gida to anyi amfani dasu wajen tarin kayan ɗaki da yake yiwa ƴan matansa. Komai na mutum uku yake saya. Yaya bata san yiwa ƴaƴa komai ba ta wannan fannin don bata sana'ar komai. Tun da ƙuruciya babu irin nacin da bata yi ba amma sam yaƙi yarda tayi saboda a cewarsa ta gama aikinta da ta aure shi. Nan kuwa yana tausayin lafiyarta ne. A ganinsa rashin imani ne zai sa ya sanya rai da ta dinga neman kuɗi a yanayin da take ciki. Gashi dama bai tsira daga dariya da surutun mutane ba. Idan ya bari tana shiga jama'a da sunan sana'a babu mamaki a karyar mata zuciya da zancen lalurarta. Shi yasa ya yiwa tufkar hanci da wurwuri.
Sauƙinsu ɗaya yanzu a gidan shi ne kitson da Sajida take yi. Hamdi kuma satinta biyu da dawowa gida Anti Labiban Abuja da ta zo Kano ta roƙi alfarmar tafiya da ita idan za ta koma. Kowa ya san miskilancin Hamdi idan ta so. Suna ta zaton za ta ƙi. Sai gashi da kanta ta amince za ta bita. Weekend na zagayowa kuwa su ka tafi.
*
Abin haushi da takaici da Taj ya tambayi Firdaus game da yarinyar da ta kasance overall a makarantarsu wai bata san komai a kanta ba.
"Ba ƙawarki bace?"
"Hamdiyya ai bata da ƙawa ko ɗaya. Sai da case ɗin babanta ya tashi ne ma ta ɗan sake da mutane."
Interest ya nuna na son jin me ya faru da baban nata. Firdaus kuwa ta zage ta kora masa jawabi tiryan tiryan. Har hukuncin da makaranta ta ɗauka akan ƙawayen Ummi tunda ita an cireta.
Tana gama jawabin ta tashi tayi gaba abinta. Ta bar shi da shiga ruɗani da mamaki. Ba kuma komai bane ya sanya haka illa tuna sunan mahaifin Hamdi da kuma sana'arsa da Firdaus ta faɗa.
Tunani barkatai ya shiga yi game da yadda aka haihu a ragaya. Indai shi ne Habibun da Alhaji yake ƙyamar ya yi koyi da halayyarsa to yaya aka yi ya yi aure? Me ya faru da rayuwarsa? Kuma wace irin rayuwa yake yi yanzu?
Tabbas zai so sani. Shi Tajuddin zai so ƙwarai ya shiga cikin rayuwarsa ba don ƴarsa kaɗai da ta tarwatsa masa zuciya ba. Wasu burika ne suka mamaye zuciyarsa wanda zai so ya cimma in har shi ne wanda Alhaji ya sani ɗin.
Kwana biyar kacal su ka ɗauka shi da Kamal wurin neman Habibu Simagade na Soron ɗinki. Sai gashi an kai su har ƙofar gidansa. Mutumin da ya rako su magidanci ne amma har su ka isa hirarsa akansa bata wuce alkhairinsa da kyakkyawar tarbiyar ahalinsa ba.
"Ai wato banda ance kowa da ƙaddararsa da in kaga wani aka ce maka zai sami sauyin rayuwa sai ka ƙaryata."
"Me yasa ka ce haka?" Kamal da Taj bai ɓoyewa komai ba illa son Hamdi ya tambayi mutumin.
Shi kuwa ya daina tafiya tare da binsu da kallon rashin yarda. Sannan ya nuna Taj.
"Ka ce min kai sana'ar girki kake yi. Ɗan uwanka kuma kasuwanci."
"Haka ne."
Da faɗa-faɗa ya cigaba da magana "zamanin yanzu ai babu yarda a tsakanin mutane. Da naji aikin naka na zata taimakon Habibu ka zo yi. Shi yasa ma zan kai ku gidan."
Taj ya yi murmushi "sana'ar girki yake kenan?"
"Watannin baya ba. Kafin ƴan hassada su sako shi a gaba su ka ƙwace wurin da yake haya. Banda haka ko garau garau Habibu ya dafa maka wallahi sai ka ji bambanci."
Duk surutun mutumin nan bai ƙara yarda ya đara daga inda yake tsaye ba yana jiran su faɗa masa gaskiya ko su waye su sai ga Abba ya fito. Daga yanayin tafiyarsa da kamanni da ya gani da Hamdi Taj ya gane shi. Kafin ya iso wurin da su ke ya tsaya ya fi sau huɗu yana gaisawa da mutane. Wannan abu ya sake burge Taj sosai har bai san lokacin da haƙoransa su ka bayyana da farincikin da ya shiga ba. RAYUWA DA GIƁI 11
Batul Mamman💖
Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya ɗagawa Taj da Kamal hannu yana ɗan ranƙwafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani.
"Ƴan samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora." Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce "na barku lafiya."
"Dakata Mal. Habibu. Waɗannan fa kai su ke nema."
Tsayuwa ya yi ya sake kallonsu sai dai bai tuna taɓa haɗuwa dasu ba.
"To Allah dai Yasa lafiya" ya ce muryarsa na raguwa saboda rashin sanin ko ba da alkhairi su ka zo ba.
Kamal ne ya amsa masa "lafiya ƙalau." Sannan ya gabatar da kansa da Taj.
Jin cewa Taj chef ne kuma a yanzu haka ginin restaurant yake sai Abba ya sami kansa da daina saurin zuwa uzurin da ya fito dashi. Zancen bai wuce fita nema ba dama.
"Dama nayi tunanin maganar ba za ta wuce ta ɗaukarka aiki ba. Shi yasa na rako su. Bari na wuce."
Abba ya yi masa godiya sosai sannan ya nunawa su Taj gidansa. "Ko mu ƙarasa daga soro mu zauna?"
A duk lokacin da ya yi magana sai Kamal yaji zuciyarsa ta karye. Allah Ya sani a yau ya daina ganin baƙin Alhajinsu. Tabbas da wannan rayuwar Taj ya faɗawa da shi ma sai ya yi kuka ba iyayensu ba. Ta yaya zuciya za ta jidaɗin ganin namijin da ya cika a halitta yana irin wannan muryar? Don ma bai san lanƙwasar jikin da sauƙi yanzu ba.
Gidan su ka bi shi. Daga soron ya ɗaga murya yana ta kiran sunan Zee amma sai da ya yi kamar sau biyar su ka ga ƴar budurwa ta fito a guje. Don shi Kamal ji ya yi kamar ya taya shi kiran saboda muryar ba ta tashi yadda ya dace.
"Abba yi haƙuri ban ji ba ne."
Mutanen da ta gani tare dashi ne yasa ta saurin komawa da baya don bata fito da lulluɓi ba. Ta bayan ƙofa ta gaishe su. Su duka biyun yadda tayi ɗin ya burge su sosai.
"Tabarma za ki kawo da ruwa."
Bata jima ba ta dawo da hijabi a jikinta ta shimfiɗa tabarmar. Abba ya sake gaisawa dasu sannan ya buƙaci jin neman da su ke yi masa.
"Kamar yadda ɗan uwana ya faɗa maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana'arka."
"Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya."
Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce "hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?"
"Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?" Kamal ya yi saurin katse shi.
"Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?" Abba ya tambaya da sakin fuska.
"Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faɗa maka. Ina so nayi recruiting ma'aikata da wuri kafin na gama ginin."
Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman abin da zai ƙara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki?
Abba ya ƙare musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo ɗaya ba don yaga irin kallon da Kamal yake yiwa Taj.
"Samari nagode amma ina mai baku haƙuri. Ina da mata da ƴaƴa huɗu. Zama haka a yanzu ma yana damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma'aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara."
Kuɗi Taj ya ciro daga aljihunsa da sauri. "Zan fara baka albashi tun yanzu kafin mu fara aikin."
"Happy!"
Taj ya yi biris da Kamal. Shi kuwa bai barshi ba ya dubi Abba da kyau.
"Kayi haƙuri don Allah. Bari mu tafi."
Taj ya ɓata fuska "Da gaske nake ina son aiki da shi Happiness."
Abba sai ya nuna kamar bai ji haushi ba. Yana ƴar dariya ya yi musu godiya kawai ya tashi. Kamal kuma haƙuri ya yi ta bashi sannan ya janye Taj su ka tafi. A mota kuwa kafin su isa gidan Ahmad anyi faɗa kaca-kaca.
"So kake Alhaji ya mutu da baƙincikin ka ko me? Kai yanzu rayuwarka tana yi maka daɗi?"
"Kai baka ji komai ba da aka ce bashi da aiki yanzu?"
"Sai ka taimaka masa da kuɗi." Kamal ya ce har zuciyarsa.
"Are you serious? Yanzu da aiki da kuɗi wanne ya fi?"
Da wannan cacar bakin su ka koma gidan. Don takaici Kamal ko shiga bai yi ba. A waje ya sauke shi ya tafi.
"Masifaffe." Taj ya furta yana harar motar.
*
Ikon Allah Zahra ta gani yau tun dawowar Salwa gida. Kwananta shida a Bauchi da aka yi musu gajeren hutum mid-semester. Abin da aka bayar da kwana goma har weekend ya kama shabiyu, a daddafe tayi shida ta dawo. Ƙarya ma ta yiwa mamansu wai field work za su je. Da yake Agricultural Extention take karantawa. Nan kuwa kewar Taj ce ta isheta har tana neman zautar da tunaninta. Abin baƙinciki kuma shi ne tunda ta tafi ko sau ɗaya bai kirata ba. Ita ce ma da ta gaji tayi masa waya harda ɗan ƙorafi.
"Idan mutum yaje gida baya son damu Salwa. Tunda ba daɗewa za ki yi ba gara duka time ɗin ki ya zama na family."
Ji tayi kamar ya faɗa mata magana. Ta daure ta ce "Ba ka cikin family ɗina kenan?"
"In ji wa? Idan kin dawo zan baki wayata ki gani a yanzu zan chanja yadda nayi saving sunanki."
Zuciyarta ta harba da wani irin farinciki ta ce "me za ka saka?"
"Ƙanwata Salwa. Yadda nake saving sunan ƴan gidanmu. Manyan kuma ina saka musu Yayata" Kuma bai barta ta gama jin haushin hakan ba kamar shi ys kira ya ce "bari na barki ki huta haka. Sai da safe."
Azahar a Kano tayi mata. Tana zuwa gidan ko hutawa bata yi ba ta karɓi girkin dare. Zahra tana ta faɗa mata ta jira ayi la'asar amma ta ce gara tayi da wuri tunda tuwo ne. Daga nan ta haɗa juice ɗin abarba, mangwaro da ɗanyar citta saboda ta kula Taj yafi son fresh fruit juice. Da su ta taho tun daga Bauchi.
Bayan tayi sallar la'asar ta shiga ɗakin Taj. Yana ƙullewa idan zai fita amma baya taɓa zare key ɗin. A cewarsa tunda masu gidan suna da kaya a ciki me yiwuwa za su buƙaci shiga idan baya nan.
"Salwa me ki ke nema a nan?" Zahra ta taho da sauri da taji alamun buɗe ƙofar.
Tsintsiya ta sameta tana gyarawa ɗauri. Tana ganinta tayi murmushi. "Anti Zahra gyara ɗakin zan yi."
Curiosity yasa Zahra ta ɗan leƙa. Baya buƙatar wani gyara na a zo a gani.
"Yana gyarawa. Ki fito don yayanki sai da ya yi min warning akan bari ke ko mai aiki ku shiga ɗakinsa."
"Yau ɗaya dai Anti. Ai gara ayi masa gyara sosai. Tunda baya gida zan yi sauri."
Tafiyarta tayi ta soma da wankin toilet. A sink inda ya tara boxers da singlets da socks ta haɗa komai ta wanke. Sai ta bar masa a bucket yadda zai shanya idan ya dawo. Wankin ma ana yi ana rurrufe ido saboda kunyar da ta dinga ji. Ɗaki ya fito fes dashi don har bedsheet sai da ta canja masa. Bayan ta gama komai ta rura gawayi akan gas cooker ta wuce da robar turaren wutan da ta siya online. Tun Zahra na bin ta da ido har tsananin mamaki yasa ta koma cewa 'uhmmm'. Yau ko ɗakin miji ne aka yiwa haka ai dole ya yabawa matar balle wanda a iya saninta babu soyayya a tsakaninsu.
Ahmad ne ya fara dawowa gidan. Lokacin tuni Salwa ta gama har tayi wanka. Doguwar rigar atampa ta saka da ƙaramin mayafi ta zauna a falo tana ta ƙamshi. Wannan karambani duk aminiyarta ce ta kitsa mata. A cewarta da kyautatawa ake sayen soyayyar namiji. Jindaɗin yadda take kula da shi zai kwaɗaita masa mallakarta a matsayin matar aure.
Wuraren ƙarfe biyar da rabi Taj ɗin ya shigo da sauran fushin faɗansu da Kamal. Sama sama ya gaisa da Ahmad. Ya ɗauki baby Aisha bayan gaisawa da Zahra. Salwa kuwa sai da tayi masa magana ya kula da ita.
Ya dakata da tafiya "Har hutun ya ƙare? Ko dai kin dawo birnin da yafi ƙauyenku?" Ya ce da ita da zolaya.
Murmushi kawai tayi. Ahmad ya girgiza kai. Dama tunda ta dawo da wurwuri ya san ba zai wuce saboda taji cewa Taj ya kusa komawa bane.
Da Aisha ya shige ɗaki a kafaɗarsa ya kwantar da ita a kan gado. Ya yi mamakin yadda ya sami ɗakin. Waye ya gyara? Komai an killace shi gwanin sha'awa. Ya shiga toilet nan ma ƙamshi kawai yake tashi. Da sauri ya duba sink da ya tuna ya bar kaya da zai wanke sai yaga babu. Nan fa yaji wani abu ya taɓa masa rai. Yana duba bokiti kuwa sai gasu a wanke an matse. Ya fiddo gajeren wandonsa ɗaya ya tabbatar dai a wanke yake. Bai san lokacin da ya sake shi a bokitin ba. Ya ɗauki Aisha ya koma falo fuska babu annuri.
"Anti Zahra waye ya gyara min ɗaki ne?"
Ahmad ya yi saurin kallon Zahra ita kuma ta nuna Salwa dake faman doka murmushi tana sunkuyar da kai. Sauƙin hali irin na Taj bai hana shi nuna ɓacin rai ba kuwa.
"Ke ki ka wanke min underwear?"
Idanun Zahra waje su ka yo. Ahmad kuwa bai san lokacin da ya ce "underwear kuma?"
Da me tambayar da kuma yanayin maganar Ahmad sai Salwa taji tsoro.
Taj ya murtuke fuska. "You shouldn't have. Next time please kada ki taɓa min." Ya duƙa ya miƙawa Zahra ɗiyarta sannan ya dubi Ahmad "Yaya zan ɗan kwanta kafin magrib. Da headache na dawo."
Shigewa ya yi ya barsu. Da Zahra taga irin kallon da Ahmad yake yiwa Salwa sai ta tashi tsam ta shige ɗaki.
Ai kuwa kamar jira yake ya soma faɗa. "Wannan wane irin rashin daraja kai ne haka Salwa? Are you crazy or what?"
Kai ta sunkuyar tana kuka. Ba kuma na faɗan yayanta ba. Fushin Taj da tsoron kada gwanintar ta tayi sanadin nesanta ta dashi kawai take gudu.
"Ba tun yau na kula kina son Taj ba..." sai a lokacin ta kalle shi hankalinta na tashi. Ya taɓe baki "wanda bai damu da lamarinki bane kawai ba zai gane ba."
"Yaya..."
Tausayi ta bashi don ta soma kukan gaske. Amma hakan ba zai hana shi faɗa mata gaskiya ba.
"Kin san komai dake faruwa a gidanmu da dalilin zamansa a gidan nan. He is trying his best ya daidaita da Alhaji. Kina tunanin soyayyar Taj dake, ƴar matar da ya saka zai faranta masa rai?"
A tsorace ta kalle shi "Yaya ni meye laifina?"
"Salwa kin fini sanin rigimar Mama tunda a gabanta ki ka tashi. Ke shaida ce irin yadda ta fitini Abbanku. Abubuwan da take yi bana jin akwai wanda Alhaji bai sani ba. Tun da in naso zuwa wajenta hutu baya son bari saboda yana gudun kada na koyo abin da zai haɗa rigima a gidanmu."
Hawaye ta goge da mayafinta. Da muryar da kuka ya gama dusashewa ta ce "To ni yaya zan yi? Ba ni na ɗorawa kaina ba"