Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 21

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 21

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 21: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 21. "Ita kuwa take da aibu tunda kai ne ubanta." Ya haɗe rai "Habibu, na…

3,366 words

"Ita kuwa take da aibu tunda kai ne ubanta." Ya haɗe rai "Habibu, na baka wata uku ka kashe auren nan. Cire zuri'arka daga jikina shi ne kaɗai abin da zai sa na dawo da Taj gidana. In har da gaske ka damu da shi ba za ka bari rayuwarsa ta ƙare a bin gidan ƴan uwa idan yana son ganawa da mahaifiyarsa ba."

Duk dauriya sai da yaji ƙwalla na neman zubo masa. "Me yasa ka yarda aka yi auren?"

"Saboda banga alamun idan naƙi zai haƙura ba. Ka riga kayi tasirin da maganarka tafi tawa a wajensa. Zai iya yin komai domin fitar da kai kunya a yadda ya zo min."

Gumi sosai Abba ya dinga yi. Allah Ya sani yafi jin Yaya akan Hamdi. Wannan tsananin farincikin da ta shiga idan ya koma baƙinciki kamar ba za ta iya ɗauka ba. Mutane da yawa za su yi musu dariya. Wadda za ta fi yi mata ciwo kuwa ta ƴan uwanta da su ka haɗa uba ce da ta mahaifin nata da har yanzu yake aibata halittarta da aurenta da đan daudu.

Ya sake kallon Alhaji sai dai babu wata fuska ta yin magana. Magana ɗaya Alhajin ya ƙara yi masa kafin ya koma ciki.

"Ina fata za ka nuna dattako ka riƙe maganar nan tsakaninmu. Dabarar kashe auren tana hannunka. Ni dai kawai nan da wata uku magana ta ƙare."

"In sha Allahu."

Jikinsa rawa ya dinga yi shi yasa ya kasa komawa motar har sai da Taj ya fito. Kafin ya ƙaraso Abba ya yi composing kansa.

"Yau dai na shanyaka da yawa. Muje kada dare ya ƙara yi."

Kasa haƙuri yayi ya tambaye shi "Babu matsala ko Abba? Me ya ce maka?"

"Ban sanka da haka ba Taj. Tattaunawa ce dai ta yaushe gamo da kuma rashin jindaɗinsa da bamu tuntuɓe shi da maganar auren ba sai a makare."

Kallon rashin yarda Taj ya yi masa. Sai dai Abban ya toshe duk wata ƙofar da zai fahimci matsalar. Sun kama hanya za su koma motar Taj yaji Kamal na kiransa. Da ya juya sai yaga Inna tare da Kamal ɗin.

Fuskarsa ta haskaka da wani irin annuri. Ya ce da Abba "Innata ce."

Kamal juyawa ya yi bai biyota ba. Ta ƙarasa kusa da gate ɗin. Idanunta cike da ƙwalla. Taj kuwa tuni ya yi laushi don ya kwana biyu sai dai su gaisa a waya.

"Baki kwanta ba?"

"Ina fa. Ina ta fakon shigowar Alhaji ne idan kun gama." Sai kuma tayi murmushi "ango ka sha ƙamshi."

Dariya ya yi ya rungumo kafaɗarta. Ba shiri ta ruɗe tana fama ture shi gami da waigawa don kada a gansu.

"Ga Abba...surukinki."

Abinka da sabo. Ƙasa ya yi zai gaisheta.

"Subhanallahi. Haba don Allah. Tashi mu gaisa. Ai mun zama đaya kuma."

Duk da bata so amma a mutumce su ka gaishe da juna. Yana ta bata girma.

"Da farko zan fara da baka haƙuri don nayi imanin ko me Alhaji ya faɗa maka ba mai daɗi bane. Sannan don Allah kada ka wahalar da kanka wajen yiwa ƴata komai. Tunda ka iya bawa yaron nan ƴarka in sha Allahu ba zan bari ta kuka da komai ba. Nagode da karamcinka a garemu."

"Ikon Allah. Hajiya ai nine da godiya da Taj bai ƙyamaci zuri'ata ba."

"Wanda ya baka ƴa ai ya gama maka komai." Ta faɗi tana murmushi "idan babu damuwa ina son ya kawo mana ita cikin sati mai zuwa. Zan karɓi numbar mamanta mu yi magana kafin na zo. Ka san Alhajin naku sai da lallaɓawa."

Murmushi ya yi shi ma "kada ki damu. Hamdi ƴarki ce kuma ikonki. Ina ƙara godiya."

Taj ma godiyar ya yi mata. Abba ya dubi uwa da ɗan su ka bashi tausayi. Me yafi wannan ciwo ace uwa tana son ganin ɗanta amma sai dai ta saci hanya ta fito kamar mai laifi? Dole zai san yadda ya yi da Yaya da Hamdi a raba auren cikin lumana.

***

Har ƙofar gida Taj ya kai Abba. Su ka yi sallama ta girmamawa. Taj yana ta sake tambayarsa ko babu matsala game da ziyarar da su ka kaiwa Alhaji. Shi kuma ya tabbatar masa babu komai.

"Gobe in sha Allahu zan tafi Abuja. Idan komai ya tafi yadda nake so ba zan wuce kwana biyu ba in sha Allahu."

"Kada ka damu. Happy Taj zai tafi kamar kana nan da yardar Allah."

"Ba manufata ba kenan" Taj ya faɗi yana sosa ƙeya "dama akan ..."

Gira Abba ya ɗage gira "matarka ko? In turo ta ku yi sallama ne?"

Da sauri Taj ya koma mota yana ta dariya shi ma Abban ita yake yi. Da gangan dama ya yi tsokanar don kawai ya kawar da damuwar da yake gani a tattare da shi tun a gidansu.

Hamdi na jin shigowar Abba ta leƙo yi masa sannu da zuwa. Ya kalleta ya kalli Yaya da ita ma fitowar tayi da sauri.

"Suruka da matar Taj jiran me kuke yi min ne?"

"Jin inda magana ta kwana mana." Cewar Yaya.

Ita kuwa Hamdi wayancewa tayi ta gudu. Ɗakinsu ta koma amma akwai mutane. Sai ta zaga bayan gidan amma bata yi nisa ba. Ta zauna akan wani bulo ko tsoro bata ji ta kira Taj.

Murmushi ya yi da call ɗin nata ya shigo. Ko tada motar bai yi ba don ya tsaya duba wani saƙo a waya. Ya bari sai da ta gama ringing sannan ya kirata.

"Za mu iya magana yanzu?" Ta furta a hankali bayan ta kuma gaishe shi.

"Yes."

Raba kanta tayi da dogon tunani ta faɗi abin da ya kamata duk da ba shi bane ranta yake so.

"Dama cewa nayi tunda Ya Sajida tayi aure namu ba dole bane ko? Kada ka takura kanka saboda gidanmu."

Kamar bai fahimceta ba ya ce "Ban gane ba. Wani abin ne ya faru?"

"Uhmmmm. Dama wai ko za ka sakeni" tayi saurin ƙarawa da "tunda ba sona kake ba. In aka ce dole ka zauna dani za a shiga haƙƙinka. Kaga kuma hakan bai dace ba. Ace mun takura maka ta wannan hanyar bayan duk irin taimakon da kake yi mana."

Wannan yarinya da abin dariya take ya ayyana a zuci. Ji yadda take zuba zance kamar wadda ake karantowa.

Ita kuma kasa jurewa shirun nasa tayi ta ce "Baka ce komai ba."

"To me zan ce? Naga kin gama yanke hukunci ke kaɗai."

Haƙuri tayi saurin bashi. Sam bata so ta ɓata masa rai kada ya yi amfani da hakan a kanta.

"Wai dama tunda ba so ka ke ba..."

"Ni yaushe mu ka yi maganar nan dake har nace bana so?"

Gabanta ne ya faɗi. Kada fa yaƙi amincewa.

"Rannan ɗin nannnn. Ka tuna? Da nayi maka rashin kunya ka ce ai ba sona kake baaa." Ta marairaice masa.

"Anya kuwa nine? Ban tuna ba Hamdi." Ya danne dariyar da yake son yi.

"Allah kuwa ba ƙarya nake ba."

Muryarta yaji ta fara rawa. "Yanzu dai so kike a raba auren?"

"Eh."

"Amma bai yi wuri ba? Kada sunanki ya ɓaci a gari."

"Kaga bamu zauna tare ba. Ko mun rabu babu mai cewa don nayi wani abu ne. Za ma a fahimta sosai."

"Tun yaushe ki ka fara wannan tunanin?"

Hamdi ta fara murnar jin muryarsa a sake. "Tun yamma. Wallahi har ciwon kai da zazzaɓi sai da su ka kamani saboda neman mafita...au...saboda nema maka mafita. Bana son mutum ya takura saboda ni."

'Zan yi maganinki' Lokaci ya duba a wayarsa. Tara da arba'in da biyu. "Yaya jikin naki? In ba a rufe muku gida ba ki ɗan fito mana."

Sai kuma taji faɗuwar gaba "takardar za ka bani?"

"Ina jiranki" kawai ya ce.

Da sanɗa ta fito tayi sa'a ƙofar soronsu mai ƙara idan an turata a buɗe take har yanzu. Ƙofar gidan ta buɗe tana sako ƙafa su ka kusa karo da Taj. Baya tayi za ta faɗi ya yi saurin riƙo kafaɗunta. Ita da shi duka wani sabon al'amari ya baƙuncesu lokaci guda. Sai da ta daidaita tsayuwarta ya ce,

"Sannu."

Ta amsa da ka. Yawun bakinta ne a bushe. Tana tare da fargabar ko har ta saku. Bata yi aune ba taji hannun Taj a goshinta.

"Mene ne?"

"Zazzaɓin nake son ji. Da alama akwai saura. Zo mu je asibiti."

"Na'am?" Ta waro masa idanunta.

Wayarsa ya ɗago "bari na kira Abba na faɗa masa za mu fita."

"Dani ɗin?" Ta ce a gigice. Idanunta sun soma raina fata.

"Idan dare ya ƙara yi kafin mu dawo sai su rufe gidan kawai. Sai mu wuce gida mu kwana."

Hanjin cikinta ya wani cure waje guda don tsoro "Wai da ni?"

"Kada ki damu. Zai fahimta. Mata ta ce so babu wani abu" ya bata amsa kai tsaye.

"Don Allah kayi haƙuri."

"Ban yi wasa da ciwon wanda bashi da kusanci dani ba ballantana kuma naki."

"Na warke tun da rana."

Taj ya ƙanƙance ido "ki ka ce kuma da yamma."

Da sauri ta ce "Eh, da yamman nake nufi. Kafin rana tayi sanyi."

"Hamdiyya kenan. In tambayeki mana."

"Ina ji."

"Kina so na?"

Tsareta yayi da kallo. Ta sunkuyar da kai.

"Kada ki cuci kanki. Da amsarki zan yi amfani."

"Ba za ka ji haushi ba?"

Taj ya yi murmushi "ko kusa."

"Zan fi so mu rabu."

"Ban yi miki ba kenan?"

Yau acting kamar daraktan kannywood ya bata training, ta marairaice masa.

"A'a, ba haka nake nufi ba. Naga kamar bamu dace ba. Ka fi ƙarfin ƴar talakawa iri na."

"Zan sanar da Abba duk yadda mu ka yi...."

"Wane Abban? Nawa?" Ta ɗaga murya fiye da yadda ta soma magana saboda tsoro.

"Kinsan ina girmama shi sosai. Ba zan yi komai ba tare da shawartarsa ba."

Ganin zai ɓallo mata ruwa ba shiri ta ce "to a bar zancen nan don Allah."

"Kin fasa karɓar takardar?"

Ta sha kunu "na fasa."

"Za mu je asibitin?" Ya kanne mata ido.

Murguɗa masa baki tayi "na ma zama abar tsokana ko?"

Ya rasa me yasa komai tayi yake burge shi. Wannan tsiwar ma da ba don dare ba da zai yi ta zurma ta ne tana yi masa.

"Gobe zan yi tafiya. Ki min addu'a don Allah."

"Allah Ya tsare hanya" ta furta kamar an matse bakin.

"Baki roƙa min samun nasarar abin da zai kai ni ba."

"Me zai kai ka?"

"Maganar aurena da wata ƙanwata. Tunda ke ba sona kike ba gara na kawo wadda za ta so ni, nima na so ta."

Yana kallon yadda fuskarta ta haɗe kamar hadari. Ya gimtse harda yi mata sai da safe ya wuce. A mota ta sami damar yin murmushi mai haɗe da dariya. Ya gama ganota. Tana so tana kaiwa kasuwa. Birkita mata lissafi kawai zai yi ta haƙura don kanta ta karɓi zuciyar da ya jima da miƙa mata.

A nata ɓangaren tana shiga gida ta sauke ajiyar zuciya. Wato da ya miƙo takardar da take barazanar nema anya za ta iya karɓa kuwa? Ita kaɗai ta dinga saƙe saƙe. Sai kuma ta kama murmushi da ta tuna maganganunsu. Ko ba a faɗa ba ta san tsokana ce da shi. A ƙarshe dai ta gaji da kokawa da zuciyarta ta amince za ta bashi dama. She will give this pure feeling she has for him a chance.

Ƙofar ɗakinsu ta kama za ta buɗe taji kira daga Abba. Soro ya ja hannunta su ka koma don a nan ne kawai ya san babu kunnen da zai ji su. Ya gama ninke Yaya ya nuna mata babu matsala don ta kwantar da hankalinta. Tsoron da yaji yanzu shi ne na ganin dawowar Hamdi daga wajen Taj. Idan ya bari alaƙarsu tayi nisa ƴarsa zai bari da jidali. Ya rasa abin yi sama da faɗa mata halin da ake ciki. Cikin hikima ya bata labarin Taj tun daga farko har zuwa aurensu. Taji wani irin tausayinsa da kwaɗayin ya daidaita da babansa. Hankalinta bai ƙarasa tashi ba sai da Abba ya faɗa mata tsakaninsa da Alh. Hayatu da yadda aka yi aurensu. Da kuma sharaɗin da ya gindaya masa.

"Ko mahaifiyarku ban sanarwa gaskiya ba. Shi kuma Taj nayi imanin ba zai taɓa sakinki ba idan yaji daga ina umarnin ya fito. Zaɓi ɗaya ya rage min..."

Kuka take a lokacin ta ce "mene ne Abba? Me za mu yi?"

"Ki nuna masa na kya sonsa. Na tabbatar idan yayi tunanin da gaske kike zai sauwaƙe miki. Ni kuma zan baki goyon baya. In ta kama sai ya fita daga rayuwarmu bakiɗaya ya sami salama."

"Abba kada ka saka kanka a ciki. Yanzu banda ƴan uwansa kana cikin waɗanda yake yiwa kallon uba. Ya ma faɗa min. Idan ka juya masa baya it will break his heart."

"Ki yafe min Hamdiyya. Koma mene ne ni na cuceku. Rayuwa tana gaba amma kullum ana yanke muku hukunci da abin da na shuka a baya."

Zuciyarta rauni tayi mara misaltuwa. Bayan shuɗewar lokaci tana gudun mahaifinta yau da kanta ta rungume shi tana kuka. Shi kaɗai yake ta haɗiyar abubuwa domin farincikinsu amma kullum ƙorafi take yi.

"Abba ka yafe min nima. Ba zan ƙara faɗin aibun sana'arka ba. Kuma in sha Allahu babu mai jin zancen nan. Zan yi ƙoƙari in ga ya haƙura da auren da kansa."

"Allah Ya yi miki albarka. Allah Ya bamu ikon sakawa Taj da abin da yafi buƙata a rayuwarsa wato albarkar duka iyayensa."

Amin ɗin a zuci ta iya faɗinta. Ta shige ɗaki ta kwanta tana zubar da hawayen damuwar da tafi ƙarfin shekarunta RAYUWA DA GIƁI 19

Batul Mamman💖

***

Bayan sallar asuba Taj ya kira Kamal domin su yi sallama. Jiya basu sami haɗuwa a gida ba. Ya yi ta waya shiru Kamal ɗin bai ɗauka ba. Wanka ya yi ya gama shiri da sauri ya sake duba wayar. Abin mamaki Kamal bai bi kiran nasa ba. Da wahala hakan ke faruwa. Jikinsa sai ya bashi ko ba ƙalau ba. Abba ƙaninsa ya kira ko tunawa da lokaci bai yi ba.

"Happiness ya fito sallar asuba kuwa?"

Abba ya ɗan wartsake idanu "ya fito amma yau ya riga kowa baro masallacin. Saƙo ne?"

"Ɗan leƙa min shi please."

Abba baya son fita don bacci ne sosai a idonsa ya ce "Ya Taj ya dai kamata ku rage wayar asubar nan. Kai kayi aure, idan shi ma ya yi wallahi za ku dinga samun matsala da matanku."

"Za ka tashi ko kuwa?" Taj ya ɗan ɗaga murya da ƙoƙarinsa na ɓoye yadda ya damu.

Yana jin ƙunƙunin Abba har ya isa ƙofar ɗakin Kamal. Sallama ya haɗa da ƙwanƙwasawa.

Da ƙyar Kamal ya iya buɗe jajayen idanunsa da su ka kumbura kamar wanda ya kwana yana kuka. Jikinsa gabaɗaya ciwo yake yi. Kansa kamar ana sara guduma saboda azabar ciwo.

"Waye?" Muryarsa ta fito a dusashe.

"Ya Taj ke nemanka." Abba ya faɗa yana saita bakinsa da ƙofar yadda za a ji da kyau "na sanar dashi. Can I go back to bed now?"

"Thanks" Taj ya ce da kulawa.

Wayar Kamal ya sake nema. Yadda yaji muryarsa ya tayar masa da hankali. Amma Kamal ɗin ya tabbatar masa da mura ce ta kama shi da zazzaɓi.

"Allah Ya ƙara sauƙi. Ko na bar tafiyar yau muje asibiti?" Hamdi ce ta faɗo masa ya yi murmushi.

"Ka tafi kafin Amma ta sauka a garin nan duk mu shiga tara."

"Don Allah ka je asibiti dai. Bana so ana raina mura da zazzaɓi. Ciwukan gaske ne."

"To doctor." Kamal ya zolaye shi.

Suna gama wayar ya ɗauki ƴar jakarsa ta goyo (backpack) wadda ya sanya duka abubuwan buƙatarsa a ciki. Ƙananan kaya ya saka ya koma matashi sosai. Haramar tafiya ya yi sai ya tuna yadda Kamal ya damu kada Ahmad yaji babu daɗi akan halin da Salwa ke ciki. Lokaci ya duba akwai đan saura. Ya fito falo ya kira wayar Ahmad ɗin.

"Yaya na shirya zan tafi."

Ahmad ya miƙe da sauri. Dama bai koma bacci ba tun sallar asuba.

"Bari na zo na kai ka airport."

"Ka barshi. Zan sami adaidaita sahu."

Fitowa Ahmad ɗin ya yi. Su ka gaisa sannan ya miƙa masa key ɗin motar Kamal.

"Incase ban sami dawowa akan lokaci ba, ina sa rai jibi motata za ta iso. In bawa mutumin numbarka sai ya kawota nan ya ajiye?"

"Da ina zai kai?" Cewar Ahmad yana zura muƙullin a aljihun wando.

Zama Taj ya yi ya buƙaci yin magana da shi na mintuna kaɗan.

"Yaya akan Salwa ne."

Ahmad ya ɗan ɓata rai "ka cire lamarin yarinyar nan daga gabanka ka fuskanci matsalolinka."

"A'a Yaya. Idan da kara nima ƙanwata ce. Ba kuma zan so ta shiga irin wannan yanayin akan wani ba."

"Shin ka taɓa yi mata magana ko nuna mata alamun soyayya ne?"

Ya kaɗa kai da sauri "a'a."

"To ka gani. Rigima ce kawai irin ta ta. Tun abin nata bai yi nisa ba na bata shawara taƙi ji. Ya take so ayi mata? Ana forcing soyayya ne?"

Taj dai duk nauyin yayan nasa yake ji. Sai yanzu ya gane manufar Kamal.

"Duk da haka ni dai ka rarrasheta. Allah Ya bata wanda ya fini. Mafi alkhairi."

"Kada ka damu. Dama a gidansu babanta ya yi mata miji. Amma kaga don fitina taƙi komawa gida. Wai tana jiran service kuma."

Dariya su ka yi su biyun. Ahmad ya kwantar masa da hankali. Da ace soyayya su ke yi yanzu ya gujeta shi ne zai zama rashin kyautawa. Amma tunda hakan bata taɓa faruwa ba babu mai ɗora masa laifi. Ahmad ya sako jallabiya ya kai shi airport tunda jirgin sassafe zai bi.

*

Yadda Amma taga rana jiya haka taga dare. Wajajen ƙarfe biyar ta sami labarin auren Taj daga wajen matar ɗaya daga cikin ƴan uwanta. Ba don shekaru ba da tabbas ƙaryata ta za ta yi. Ta dai daure su ka gama wayar. Yaya Babba ta fara kira ya ce mata haka ne. Ji tayi tamkar an kwaɗa mata guduma. Taj ya yi aure bata sani ba. Kuma har dare bai kira ba. Haka ta ƙarasa wunin ranar cike da fargabar kada mutan gidan su ji.

Da taga Allah Ya taimaketa har bayan Isha babu wanda ya ce komai shi ne Daddy na gama cin abinci ta ce masa tana son zuwa Kano gobe.

Kamar Anti jira take ta shigo falon a lokacin "Hummm, Maman Ihsan kenan. Kin gaji da ɓoye ɓoyen?"

Gabanta faɗuwa ya yi amma ta dake. "Ɓoyo kuma? Wani abin ne ya faru?"

"Kada ki raina min hankali mana. Za ki ce ba da saninki Taj ya yi aure bane? Ko kin zata bamu sani ba?"

Anti ta faɗi da matuƙar ɓacin rai. Taci burin suruka da shi saboda ya haɗa dukkan abin so. Kyau, kuɗi, suna da kuma kyawawan ɗabi'u. Idan Anisa ta sami miji irinsa ta wuce raini a wurin kowa. A dangi ma sai an dinga bata girma na musamman.

"Yadda ki ka ji maganar nan nima haka na ji ta. Kuma dalilinta nake son zuwa Kanon ma kenan. Babu wanda ya neme ni. Sai aure kawai naji."

"Ai in duk jikina kunne ne ni ba zan yarda ba. Yaudara ce dai an yiwa ƴata."

Ran Amma ya soma ɓaci ta ce "Ita Anisan ce ta ce ya yaudare ta?"

Hankali kwance Daddy ya gama cin abincinsa sannan ya tsawatar musu.

"Idan kuma ban isa daku ba sai ku fita ku ƙarasa."

Amma kwantar da murya tayi ta bashi haƙuri sannan tayi masa bayanin rashin sanin auren.

"Idan haka ne kuwa kema bai mutuntaki ba. Kuma ya nuna bai san alkhairi ba."

Wani irin kallo Amma ta yiwa Anti. Bata son cigaba da rigima a daren nan amma take taken Antin so ta a cigaba da maganar har Hajja ta ji.

Daddy sallamarsu ya yi akan su bar zancen zuwa washegari. Anti na fita ta koma ɗakinta inda ta sami Anisa a zaune da waya a hannu. Zuciya ta raya mata Taj take kira ƙila yaƙi ɗauka. Ai kuwa ta tashi ta nufi ɗakin Hajja tana kuka ta karanta mata ƙarya da gaskiya. Wani abin idan ta faɗa sai Anisa ta riƙe baki don mamakin yadda uwa take yanko ƙarya bisa son zuciya.

"Damuwata yanzu yadda ta saka shi a ranta."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull