Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 34
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 34: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 34. Haƙuri ya bawa ƴar tasa. Ya rasa matakin ɗauka na gaba. Ita ta bashi…
3,355 words
Haƙuri ya bawa ƴar tasa. Ya rasa matakin ɗauka na gaba. Ita ta bashi shawarar su ƙona komai. Ya ce kada ta taɓa. Da tsintsiya da abin kwasar shara ya tattara komai ya tara a tsakar gida. Ya kawo fetur ya zuba sannan ya kira Mami ya ce su dawo.
"Har maganin ya fita?"
"An fasa, sai gobe."
Masifa ta yi masa na katse mata baccin yamma sannan su ka taho gida. Ana buɗe musu gate ta hango shi daga shi sai ƴar shara a jikinsa ya sanya wasu tarkace a gaba. Su ka fito daga mota ta taho inda yake. Jikinta ne ya saki lokaci guda da ta gane mene ne a gabansa.
"Alllll....hhhhajjii? Mmmmene nee wannnnan?"
Haɗe rai ya yi sosai ya tura mata ashana da ƙafarsa.
"Ɗauki ki cinna musu wuta."
Jikinta rawa ya kama yi sosai. Tana ta gumi ta rasa abin yi.
"Ɗauki mana!" Ya daka mata tsawa.
Ta kasa motsi sai ƙullewar ciki. Salwa da taga halin da babarta ta shiga ita ma tsorata tayi. Tunda bata san kayan mene ne ba durƙusawa tayi ta ɗauki ashanar.
"Baba ni bari na ƙona."
Kafin Mami ta iya tare ta har ta ƙyasta ashana. Tana cillawa kuwa kayan nan su ka yi wata mahaukaciyar ƙara tamkar tashin gurneti. Mami tayi zaman daɓaro a ƙasa tana ihu.
"Kin kashe ni. Salwa kin kashe gidan nan."
Da faɗa Alh. Mukhtar ya ce "ta dai kashe ki ke kaɗai banda gidana."
"Mami kayan meye?" Salwa ta tambayeta ganin kuka take haiƙan. Bata sami amsa ba sai daga bakin babanta.
"Nagodewa Allah da Ya turo Alh. Hayatu gareni ya farkar dani mugun baccin da nake yi. Sai yau na gane ashe zaman waɗannan abubuwan muke yi ba aure ba."
Mami kuka kawai take yi da gurnani. Hankalinta ya kai ƙarshen tashi. Idan ya saketa bata da tudun dafawa. A zaune ta ja jiki zuwa inda yake za ta kama ƙafarsa ya janye da sauri.
"Ka rufa min asiri."
"Ki rufawa kan ki dai" ya dubesu ita da Salwa dake tayata kuka "yauwa, Alh. Hayatu ya ce in faɗa miki ki warware abin da ki ka yiwa ɗansa har su ke rigima da matarsa. Idan ba haka ba kuma ki jira martani daga gare shi." Ya wuce ciki.
Mami ta zauna tana tumami da kuka kafin ta tashi ta bishi ciki da sauri.
"Wane ɗan? Taj? Wallahi ban yi masa komai ba."
"Ki daina saurin kama sunan Allah tunda baki san shi ba. Da idona naga laya da sunansa."
Mami ta kwantar da murya "Ayyaaa Alhaji, bamu yi amfani da ita ba. Dama na ajiye ne sai sun yi aure da Salwa. Ai ban baki ba ko...."
Ta juya babu Salwa babu dalilinta.
"Salwa? Alhaji ina Salwa?" Tayi maganar kamar wata zararriya. Tsoro take ji kada ƙona kayan nan ya janyowa ƴarta wani abu. Don dai tabbas malaminta ya sha yi mata kashedi akan kada ma wani ya gani balle a taɓa.
Ɗakunan gidan ta duba bata ganta ba. Tayi wajen gate tana faman kiranta ko kallon titi bata yi. Bata yi aune ba mota ta ɗebe ta tayi sama ta dawo. Maigadin Alh. Mukhtar da ya biyota yana son faɗa mata Salwan ta fita ne ya koma ya sanar dashi abin da ya faru. Ya fito su ka wuce asibiti tare da mai motar da ya bugeta.
Salwa kuwa tunda taji saƙon babanta hankalinta ya tashi. Indai Alhajinsu Taj ne ya yi waccan maganar kenan asirin ya kama su. Matsalar kawai tunda ake zargin Mami a hankali zsi gano ita ce. In haka ta faru kuma zai hana Taj aurenta idan su ka fara soyayya. Tasha ta wuce tunda da atm a jikinta ta ciri kuɗi sai Kano. Wurin Ummi za ta je ta taimaka mata da wanda za a rufe bakin Alhaji.
Motarsu ko fita gari bata yi ba Alh. Mukhtar ya kirata ya faɗa mata abin da ya sami Mami. Don baƙinciki sai da tayi kuka. Haka ta sauka daga motar ta tafi asibiti.
***
Mai shawara aka ce aikinsa ba ya ɓaci. Duka abubuwan da Inna ta sa Taj yi ya rungumesu hannu bibbiyu. Ƙuncin zuciyarsa ya ragu sosai. Duk da ya kan ji haushin Hamdi yana taso masa lokaci zuwa lokaci tunda fitar asiri sai a hankali, amma a zuciyarsa ya sani cewa ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba kamar yadda ya dinga ji a kwanakin baya. Banda yawan addu'a, Inna ta sa yanzu ya ware plate goma na abinci kullum sai sun bayar sadaka. Ba wai ragowar na mutane ba. Mai kyau da an gama dafawa ake packaging. Ranar farko ma na mutum ɗari biyu su ka yi aka kai asibitin gwamnati. Kusan zai rantse ma daga ranar ya fara jin canji sosai. Ciyar da mabuƙata ba ƙaramin abu bane.
Duka wani jere da gyaran gidan amarya an gama shi a farkon sati. Duk wanda ya shiga kamar kada ya fito. Hatta kayan da za su saka Kamal ya kai wa Hamdi nata ana jibi fara biki. Bayan ta shiga gida ta gwaggwada ta dawo ta same shi. Ta faɗa masa babu wanda yake buƙatar gyara. Sai kuma tayi godiya sosai.
"Yanzu yaya kike ji game da ɗan uwana?"
Kai ta sunkuyar tana murmushi. Da ya sake yin tambayar ta ce "Alhamdulillah."
"Kina ganin faɗa ya ƙare? Za ku iya zama babu tashin hankali?"
"Ban sani ba ko daga wurin shi." Ita ce amsar da ta bayar da ƙaramar murya.
"Nayi magana da shi. Ke nake tambaya kuma."
Kunya ce ta isheta ya ce gara ma ta daina domin tunda ta shigo danginsu ta sani cewa bayan shi yanzu ta sami ƙarin ƴan uwa. Kuma kowa zai tsaya mata idan Taj ya yi nufin cutar da ita.
"Zan iya in sha Allah."
"Alhamdulillah. Kamar yadda na faɗa masa ku bi komai a sannu. Kada ku ce dole a yau ko gobe ku ke son ganin alaƙarku ta dawo kamar da. Wannan zai janyo muku too much expectation, wanda kuma rashin samunsa zai sa ku zama disappointed."
"In sha Allah zan kiyaye."
"Hamdiyya"
Mrs Happy ya saba kiranta. Shi yasa Hamdiyyar ya faɗar mata da gaba.
"Na'am Ya Kamal."
"Don Allah ki riƙe min Taj amana. Abubuwa da yawa sun same shi. Yana buƙatar inda zai sami kwanciyar hankali."
Ɗan murmuhi tayi "ai kana nan Ya Kamal sai mu dinga shawara. Ka fini sanin abin da ya dace da shi."
Murmushin da Kamal ya mayar mata mai matuƙar rauni ne. Da ace idanunsa ma take kallo za ta ga sun kaɗa.
"Yanzu ke ce mafi kusa dashi."
"Ba zan shiga tsakaninku ba in sha Allah" ta faɗi da sauri.
"Rayuwa da yau da gobe za su iya shiga. Ni dai na baki amanar Happy. Please Hamdiyya, give him the happiness he deserves."
Har ya tafi tana juyayin maganganunsa masu kama da sallama. Anya lafiya kuwa?
***
Idan ka ji yara na waƙar gobe Juma'a, kuturu dariya yake ko zai sami ɗan kwabo to lallai ranar ta kama Alhamis. Ta wannan satin ita ce ranar Kamun amarya Hamdi wadda iyayen ango Taj su ka yi rawar gani wurin tsara taro na burgewa. Biki ne na ƴan kasuwa kuma ƴan boko. In baka yi bani wuri. Sun tsara abinsu na yau ma mata kawai. Mazan gidansu ko mutum ɗaya ba a yarje masa zuwa ba. Daga DJ ɗinsu kuwa har mai hoto da MC duka mata ne. Daga cikin wani katari da Alh. Hayatu ya sake yi a rayuwa harda dacewa da kyakkyawar tarbiyar ƴaƴansa akan sunnar Fiyayyen halitta SAW. Ba dai a rasa nono a ruga, wani dole sai ya bauɗe. To amma dai majority a gidan sun ginu da wannan tarbiyar ta iyayensu mata. Wannan yana daga cikin dalilan da su ka sa Alhaji ya kan kasa yiwa wanda ya kuskure uzuri. Shi fa kusan komai Allah Ya bashi. Bai san wani nau'i bane na gwajin rayuwa. Idan ya ƙanƙantar da kai ya yarda rahama ce daga cikin taskar Ubangijinsa sai Allah Ya ƙara masa da lada mai gwaɓi. Idan kuwa girman kai da jin cewa isarsa da iyawarsa ne su ka bashi kamar yadda ya tsinci kansa yanzu, to dama Allah barin mutum yake da iyawar tasa.
Ƙarfe ɗayan rana mai kwalliya ta zo ta fara rangaɗawa Hamdi bayan tayi sallar azahar. Jiki ya sha gyara na gaske saboda haka in ka ganta sai ka ƙara kallo. Ga ƙamshi wanda da kanta ta ce a bar turara mata jiki haka nan saboda kada ta fara ɗaukar zunubi a cikin mutane.
Tana idar da sallar la'asar ta saka kaya aka ɗaura mata ashoke. Da ta fito daga ɗaki Yaya tashi tayi ta bar wajen. Bata son kowa yaga ƙwallar da ta cika mata idanu. Yau ita ce Allah Ya nufi ƴarta da auren gata irin wannan. Da bikin Sajida abin bai yi armashi sosai ba saboda tangal tangal da auren ya soma yi tun kafin a ɗaura shi.
Leshi ne haɗaɗɗe mai laushi aka yi mata ɗinkin gargajiya wato buba da zani. Ado da kyan leshin kaɗai sun wadata ba sai an ɓata ɗinkin da tarkace ba. Ruwan toka ne da adon ja kaɗan a jikin zare sai navy blue ɗin fulawoyi. Ta riƙo jar ƙaramar jaka ta amare tana kuma sanye da jan takalmi mai tsini da maɗauri. Ashokenta na ka da na kafaɗa navy blue da silver. Sai wata danƙareriyar sarƙa mai duwatsu navy blue su ma da ja. Make up ɗinta na hankali bata koma aljana a kwaba ba.
A tsakar gidan aka tsaya ana ta ɗauke ɗauken hotuna da ƴan uwa. Bata sani ba ashe Taj ya kirata ya kai sau shida. Amma ce ta turo shi ɗauko musu amarya. Fitowar tasa ma sai da tayi da gaske. Anti Zahra tun safe ta bar gidan. Su na can gidan Alh. Lurwanu yayan Inna don a nan za ayi Kamun. Saboda ƙurewar lokaci basu iya samun event centre ba.
A waya ta faɗa masa cewa ana la'asar yaje ya ɗauko Hamdi. Hankalinsa a take ya tashi. Wato ƴan kwanakin nan da ya soma dawowa daidai babu abin da yake gudu kamar haɗuwa da amaryar tasa. Da wane baki zai bata haƙuri akan marin da ya yi mata? Inna bata ce masa komai akan asiri ba tunda Yaya Malam ya gargaɗeta da zargi. Gani yake girmansa ya gama zubewa a idanunta. Namiji mai dukan mata bashi da wata daraja a idonsa.
"Bari na faɗawa Happiness ya shirya mu tafi da wuri."
"Kai Happino. Nace happino" Amma tayi magana a fusace "ɗauko matar auren naka ma sai da shi? Ince ko daren farkon ma tare za ku."
Da mamaki ya ce "Amma me ya yi zafi? Kamal nake nufi fa."
"Shi ɗin fa! Ku yanzu sam baku iya lissafi da zurfin tunani. Dama me yasa ake haɗa angwaye da ƴan rakiya? Ai saboda gudun fitinar zamani ne. Ku kuwa tunda an riga an ɗaura aure me za ka yi da ɗan rakiya?"
Dariya sosai ta bashi ya ce "to Allah Ya baki haƙuri. In kina so ma sai na ɗaukota na kai muku ita har kujerar da za ta zauna."
"Ɗan banza mai bakin tsiya. In baka yi wasa ba wallahi har wurin zaman sai in ce ka kawota mu ga ƙarshen rashin kunya."
"Cewa dai za ayi tarbiyarki ce." Ya ce da tsokana.
Ita ma da ta san hali bata san me ya sa ta biye masa ba. Rabuwa tayi da shi bayan ta tuna masa ƙarfe biyar daidai su ke son farawa.
Da ya faɗawa Kamal yadda su ka yi a wayar dariya su ka dinga yi son ransu. Kamal na cewa Happy ya girma shi kuma yana baya so.
"Ni wallahi kunyar haɗuwarmu ma nake ji."
"Hamdi fa bata da matsala. Kawai ka bata haƙuri a wuce wajen."
"Kaga last faɗanmu kuwa da na kai mata kati? Tana faɗa ina yi kamar wasu kaji. I am seriously ashamed og myself." Ya rufe fuska da tafukan hannayensa.
"Dalla kada ka bada maza. Kawai ka sabunta mata karatu yau yau ɗinnan. Su fa mata kana rarrashinsu ka gama dasu."
Taj ya gyaɗa kai "Allah bari in samu a kai min rigimammiyar nan gida. Zan yiwa su Mama famfo akanka sosai. Dr. Mubina will be Mrs Happiness."
Kamal murmushin yaƙe kawai ya yi. Taj ya yi wanka ya saka shirt da wando abinsa ya zo zai fita.
"Wani sabon salon wulaƙanci ne wannan ko me? Ina kayan da Abba ya karɓo daga wajen tela?"
"Direba fa zan yi. Amma ta ce ba zan shiga ba. Kuma kawai sai na saka sababbin kayana su yamutse?"
"Kaina ciwo yake Happy. Bani da ƙarfin yi maka surutu. Kayi abin da ya dace ka fita."
Kamar ya yi musu sai dai yaga babu alamun wasa tattare da Kamal ɗin. Dama kuma tsokana ce tasa shi saka waɗancan. Ya canja da wasu sababbi cikin na bikin. Sai gashi yayi kyau sosai. Ya tambaye Kamal ko zai sha magani ya ce a'a. Gajiya ce.
Taj na fita ya kira Mubina ya faɗa mata jikinsa fa babu daɗi. Tana hanyar zuwa wurin kamun ita da ƙanwarta don har gida Yaya Kubra ta aika mata katunan bikin duka. Dole ta juya ta koma asibiti. A hanya ta sauke ƙanwar ta ta tace mata patient gareta.
Ruwa ta saka masa da wasu magunguna masu ƙarfi har ya dawo daidai.
"Ban faɗawa Dr. Kubra ba saboda bana son raba mata hankali. Ciwon nan mun barshi tsakaninmu zuwa lokacin da za a gama bikin ɗan uwanka kamar yadda ka buƙata. Idan bata faɗa ba ni zan je har wajen Alhajinku wallahi."
Ranta a ɓace yake. Kamal ya yi mata murmushi. "Wannan faɗan duk don na hanaki zuwa cin shinkafar biki ne ko?"
Harara ya samu "Wasa ma ka mayar da abin?"
"Sorry Doc." Ya ɗauko wayarsa dake gefen gadon "zo mu yi hoto."
Yadda ya yi maganar ya taɓa mata zuciya. Tayi murmushi duk da tana ƙoƙarin nuna masa fushinta. Ya gyara zama ta koma gefensa ta zauna tayi musu selfie. Tana tashi ya ɗauketa wasu. Bai taɓa ganinta da kwalliya irin ta yau ba. Kasa haƙuri ya yi ya ce da ita,
"A misali da zan warke za ki iya aurena Mubina?"
Abin control ɗin gudun ruwan da take ƙara masa take dubawa da ya yi tambayar. Yasa ta kusa ture ƙarfen gabaɗaya saboda yadda zancen ya taɓa ta. Allah Yasa bayanta yake kallo da yaga halin da ya jefa zuciyarta. Tattaro nutsuwa tayi
"A'a."
"Ni? Ni?" Ya nuna kansa kamar yato ya sanyata dariya "nayi tsammanin za ki bani amsar da zan ji daɗi."
"Baka cancanci hakan ba Kamal. You are very stubborn. Rantsuwar dake kare alaƙar likita da patient ce kawai ta hanani yi maka handsfree."
"Na nawa kuma? Ba kin faɗawa Yaya Kubra ba?"
"Da kai da ita akwai wanda zai rantse cewa na faɗa? Magani ta gani ta zo tayi tambaya."
Kallonta kawai yake yi yana jin inama ƙalau yake. Da ita ma tana wajen Kamu ana kama masa ita.
"To da ace ni ɗin patient ne mai bada haɗin kai irin yadda kike so, za ki iya aurena idan na warke?"
Sai da ta kalli idanunsa sannan ta bashi amsa "Da gudu" sai kuma ta soma hawaye "please let us help you Kamal. Akwai dama indai mu ka sami donor. Kada ka ɗora min zawarci tun kafin nayi aure don Allah."
Tana gama faɗin haka ta fice saboda kukan da take shirin yi a gabansa. Shi ma hawaye ya goge bayan ta fita. Yana tsoron sanya rai da rayuwa bayan samun lafiyarsa ba abu bane mai sauƙi. Shi yasa yake ta kaucewa sanar da mutane. Amma zai bi shawararta. Idan an gama bikin Taj da kamar sati ɗaya da kan shi zai faɗawa iyayensa.
*
Mota Sajida da Fadila su ka rako Hamdi bayan an rufa mata wani net ja wanda dama an faɗa musu da shi za ta fara shiga. Sai an yi kamun za a cire mata. Haka aka rufe motar gabanta yana matsanancin faɗuwa.
A hankali yake tuƙi cikin nutsuwa. Ƙamshin da take yi ya kwance duk wani notin arziƙi na kansa. Yana son yi mata maganar abin da ya faru amma yana jin nauyin hakan. Kamal ya ce ya bata haƙuri. Amma idan kuma ya bata ta sake yi masa maganar da wancan yanayin zai dawo fa?
Tsoron da yake ji bai kai nata ba. In ka cire gaisuwar da tayi masa a gaban su Sajida bata sake ko da ɗaga kanta ba. Kwata kwata bata yarda da bakinta ba. Yanzu dai lafiya ƙalau su ke tafiya. Idan kuma tayi magana irin kalaman nan dake fita da kansu su ka bar harshenta fa?
Kowa kama bakinsa ya yi. Da Salwa za ta ga yadda aikinta ya yi tasiri a wajen nan da ta daka tsallen ƴan bori ta dire don murna.
Shirun damunsa ya yi ya kunna musu rediyo. Tashar farko da ya samu ya bari. Aka yi dace ko rashinsa domin kuwa a daidai lokacin mai tallan maganin gargajiya ce take ta kwararo bayanin maganin basir.
(Wato shi fa basir idan yaci jikin magidanci sai kaga ko kukan jarirai an daina yi a gidansa. Cikinsa kullum a ƙulle tamau kamar yarinya tana koyon ɗaurin zani. Da shi da matarsa babu maraba. A jaraba maganin nan domin kawo ƙarshensa. Akwai mai tsiro, da mai jini.)
Cikin kujera Hamdi ta shige saboda tsabar kunya. Mai magani ta cigaba da ɓaro zance mai nauyi. Aka barta da satar kallon Taj. Ɗan duniya da ya fahimci kunya take ji sai ya ƙara volume. Can sai cewa yayi
"Nagode Allah ni dai ƙalau nake. Masu fama kuma Allah Ya yaye musu."
Shiru tayi tana ƙifta idanu. Gara yayi mata waƙoƙinsa akan wannan magana.
Kallonta ya yi ya saki murmushi. Wani irin jindaɗi da nutsuwa yake ji a ransa. "Ko kina da shi in saya miki..."
"Innalillahi..." ta kalle shi babu shiri ta yaye lulluɓin.
Numfashi ya ja da ƙarfi da su ka haɗa ido. Tayi masa kyau ba kaɗan ba.
"Ni lafiyata ƙalau wallahi."
A daidai lokacin mai maganin ta zaɓi ɗora zancenta da dawowa kan mata.
(Na dawo gareku matan gida. Ina da magunguna sahihai waɗanda mu ka gada tun kakanni. Maganin sanyi da magungunan mata masu gigita maigida.)
Hannu ta kai za ta kashe rediyon ya damƙe shi yana murzawa a hankali.
"Don Allah ka canja."
"Shhh...an zo wajen naku. Bari mu ji."
"A ji me?" Ta tambaye shi looking horrified.
(Mace sai ta bari sanyi ya gama cinye mata jiki. Sai miji ya mayar da ita bora sannan za ta fara neman magani. Ina mai fama da ƙaiƙayin...)
Hamdi ta dube shi kamar tayi kuka. "Allah idan baka kashe ba zan iya yin kuka."
"Allah Ya baki haƙuri. Daga taimako?"
"Ba na so." Ta turo baki.
Soyayyarta da ta kwanta wucin gadi ta dawo masa sabuwa fil. Ba ƙaramin kewar wannan Hamdin yayi ba. Yana son faɗa mata amma sun riga sun iso gidan Alh. Lurwanu. Inda zai ajiyeta Amma ta faɗa masa bayan ya shiga ciki da motar. Yana hango masu rakata wurin zamanta su Zee da su Firdaus.
"Wanne zan saya miki? Kin dai ji ance mace bora take zama idan bata sha ba."
Tsuke bakinta tayi. Sai da ya buɗe lock za ta fita ta yi magana a hankali yadda babu mai ji cikin ƴan rakiyarta.
"Nafi ƙarfin zama borar gida."
"Za ki maimaita wannan maganar nan da saturday."
"Allah Ya kaimu" ta faɗi sannan ta ƙifta masa ido don tsokana.
A tunaninta za ta samu guduwa ne a lokacin. Sai gashi su Firdaus sun dage sai sun yi musu hoto kafin a shiga da ita ciki. Fitowa yayi daga motar ya tsaya a gefenta.
"Kai Uncle Taj. Irin wannan hoton tun zamanin su Mama. Ku ɗan ƙara matsowa mana."
Hamdi bata ankara ba taji ya janyota kusa dashi. Hannunsa ɗaya a tsakiyar bayanta. Jin kamar za ta faɗi sai ta ɗora nata hannuwan a kafaɗunsa.
"In miki waƙa?" Ya ce a saitin kunnenta. Hakan ya bada style na hoton masoyan da su ka yi nisa da ƙaunar juna.
Ta san tsokanarta yake yi shi yasa tayi dariya. A haka aka ɗauki hoton. Ya yi kyau sosai.