Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 55
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 55: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 55. "Jar uba! Kin ga kira Ɗandaudun nan ki haɗa mu kawai. " Baba Malam ya…
3,353 words
"Jar uba! Kin ga kira Ɗandaudun nan ki haɗa mu kawai. " Baba Malam ya nuna kansa yana jijjiga jiki "Ni za a ha'inta? Ɗiyar tawa za a feɗe daga zuwa ibada? Dama can ban yarda yana da kuɗin kai Jinjin Saudiyya ba. Matsiyaci mai tafiyar mata. Ina yi masa kallon wanda ko ƙuda ba zai iya kashewa ba ashe ja'irin ƙodar ɗiyata zai sayar. Allah Ya isa Habibu!"
To Inna Luba dai babu bakin kare Abba Habibu domin kuwa bata san gaskiyar me yake faruwa ba. Ana haka gida ya kaure da tsine-tsine da zagin bawan Allah Abba Habibu sai ga wani ɗan saurayi cikin jikokin Amarya. Inna Luba ta miƙa masa wayarta ko zama bai yi ba.
"Ya'u maza lalubo min lambar Sajida ka kira."
Ya'u ya yi abin da ta ce ba tare da tambayar komai ba duk da mamakin da ya cika masa zuciya. Kiran na shiga ya miƙa mata wayar sai dai kafin ta ankara Malam ya karɓe ya manna a kunne yana masifa.
"Maza-maza ki yiwa ubaki waya ki ce ya kira ni yanzun nan."
"Baba Malam me a ka faɗa muku?" Sajida ta fahimci ba lafiya ba "don Allah ka tsaya nayi maka bayani."
"Ƴal ƙwal uba har ki na da bayanin da za ki mani? Me ya hana ki neman mu kafin yanzu tunda da alama kin san komi" ya yi ƙwafa "wato kun haɗa kai da baban ku za a kawo muku kuɗin jini ku wanki biyar ku tsoma biyar, ni da na san zafin haihuwarta kuma a barni da kukan rashin ɗiyata. To wallahi ba ku isa ba. Nemo shi ki ce masa lallai a mayar mata da ƙodarta."
Sajida ta sake kwantar da murya "Baba Malam ka yi haƙuri. Ba abin da ka ke tunani bane. Yaya taimako tayi da ceton rai."
"Da ƙodarta? Ke Sajada, kada ki raina min wayau mana don kawai kin ga ina rayuwa a ƙauye. Tun Kaka da Kakanni ban taɓa jin an cire sassan jikin wani an dasawa wani ba. Zancen nan bai yi kama da wanda hankali zai ɗauka ba."
Haƙurin ta sake bashi ya ji haushi ya surfa mata zagi daidai wa daida. Ya ce kuma ta saka a ranta cewa Yaya na dawowa zai maka Abba Habibu a kotu a raba auren su. Jin haka Inna Luba ta karɓe wayarta ta ce da Sajida tayi maza ta nemi Abbansu.
"Idan bai kira ni ba to nima zan bi shawarar Malam." Ta katse kiran.
Hankalin Sajida ya tashi sosai. Ranar kwanan su Taj biyu da tafiya Madina ta kira ta sanar da Abba Habibu yadda su ka yi da su Baba Malam. Murnar sauƙin da su Yaya ke samu sai ta koma ciki domin kuwa nasa hankalin ba ƙaramin tashi yayi ba. Alh. Hayatu ya yi Allah wadai da halin surutun wasu mutanen.
"Wani lokacin sai ka yi tunanin akwai masu ɗokin zama ƴan yaɗa labari mara daɗi. Suna rawar jikin zama farkon waɗanda za a ji mummunan labari daga bakinsu. Banda haka wane irin rashin nazari ne zai sa a kira tsohuwa a tayar mata da hankali irin haka?"
"Yanzu ta ina zan fara? Ta yaya zan yi musu bayanin da za su fahimta?"
Abba Habibu cikin damuwa, Yaya kuma tana ta kuka. Tausayinsu ya kama Hajiya, musamman da ta tuna rayuwar ɗanta ce ta janyo mu su.
Jikin kowa yayi sanyi. Sun kira su Inna Luba amma ko kusa Baba Malam bai bata wayar ba. Shi kaɗai ya dinga faɗa kai ka rantse tunda Yaya ta taso bai taɓa juya mata baya ba. Maganganunsa duka ana ji domin faɗa yake yi iya ƙarfinsa. Har cewa Yaya ya yi ta tabbatar ta karɓi takardarta kafin su dawo. Hajiya dai sai da tayi kuka mai isarta. Yanayin ɗakin ya koma wani abu daban a tsukin lokacin.
Ana haka sai ga kiran tawagar Madina. Dama kullum sai sun kira an gaisa. Hajiya na karɓa ta ce a bawa Yaya Kubra wayar. Sai da ta fara gargaɗinta akan kada maganar da za su yi ta fita musamman zuwa kunnen Hamdi sannan ta tambayeta shawara.
"Ke ce likita Kubra. Me ya kamata mu yi? Ta ina za mu ɓullo mu su ta yadda za su fahimci girman taimakon da Yaya tayi har ma su yaba mata?"
"Hajiya turo min numbar da zan same su."
"Bari na karɓa sai na turo miki. Amma don Allah ki kiyaye."
Kallo su ka bita da shi har ta tura numbar sannan tace musu su duka babu mai ilimin da zai iya yin bayanin da su Inna ba za su ɗauka son zuciya ba.
"Mu bata dama tunda ɓangaren aikinta ne. Na san Kubra, za ta yi abin da ya dace."
*
Gidan Baba Malam fa babu lafiya. Inna Luba kwanciya tayi zazzaɓi ya rufe ta yayinda maƙota su ke ta zaraf-zaraftu a ƙofar gidan ana ta zuwa jaje da ganin ƙwaf. Amarya ce ta fice fit ta fesawa waɗanda ta san za su tayata yaɗawa. Kafin wani lokaci gari ya ɗauka. Abin ne da mamaki ace mutum ya bayar da ƙoda sukutum kuma yana nan da rai.
Waya na ringing Inna Luba ta tashi da sauri ta ɗauka. Yaya Kubra ta gaishe ta a ladabce sannan ta buƙaci Innar ta haɗa ta da matashi ko matashiya idan akwai a kusa.
"Yarinya ko me za ki ce ki faɗa min kawai."
"Don Allah ki yi min wannan alfarmar Inna. Ki taimaka."
Ba don ta so ba ta fito tsakar gidan. Cikin sa'a tayi kiciɓis da Ya'u. Har yanzu bai koma gidansu ba tunda ya san me yake faruwa. Rigimar kakarsa Amarya da Inna Luba ba sabgarsa bace. Yana ɗasawa da kowa a gidan.
"Inna kina buƙatar wani abu ne?" Ya matso kusa da ita da sauri.
"Gashi" ta bashi wayar ta koma cikin ɗakinta.
Ya'u ya saka waya a kunne ya ce "hyalo?"
Kai tsaye Yaya Kubra ta bijiro masa da buƙatarta bayan ta gabatar da kanta kuma taji daga ɓangarensa. Yadda take magana kaɗai ya yi masa kwarjini don jikinsa har rawa yake wajen amsa mata.
"Aiki ka ke yi ko karatu?"
"Aiki ne. Ina koyarwa a wata pravet a nan kusa da mu."
"Masha Allah. Mal. Ya'u nawa ne albashin ka tsakani da Allah?"
"Et fife (8,500) ne." Ya amsa mata cikin basarwa. Ba ya so tayi tunanin shi ɗin cima zaune ne.
"To zan baka dubu ashirin a yau in sha Allah idan buƙata ta ta biya."
Gigicewa yayi sosai yana ta doka murmushi ba ji ba gani. Ta gama da shi da tunaninsa kaf.
"Me ki ke so nayi?"
"So nake ka samo min waya mai yin bidiyo call na whatsapp."
"Shike nan?" Ya tambayeta da mamaki.
"Ƙwarai kuwa. Idan an samo ka bani lambar in saka data domin wayar za ta iya ɗaukar lokaci."
Ya'u baki har kunne don farinciki ya ce "wayata tana yi sai dai bani da data sannan wassof ɗin ma ya yi ispiya."
"Wannan layin?"
"Eh."
Cikin minti biyar Ya'u yaga 25G. Gani yayi abin kamar wani mafarki da zai iya tashi kodayaushe. Shi da ya saba saka datar naira ɗari zuwa ɗari biyu sa'i da lokaci ina zai kai wannan? Ya yi updating komai da sauri sannan da kansa ya kira. Dr. Kubra Hayatu tayi masa wani irin kwarjini. Ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta sannan ya kaiwa Inna Luba wayar. Kafin a fara jawabi Baba Malam da Amarya suma sun hallara. Ya'u yana gefe Yaya Kubra ta zauna tayi mu su gwari-gwari game da ciwon Kamal, zuwan Yaya asibitin, bayar da ƙodar da ma zuwan Abba Habibu.
Inna Luba tayi kuka babu adadi ba. Muryarta duk ta dashe.
"Yanzu ƴar nan kina da tabbacin rayuwar yarinyar nan ba za ta tawaya ba?"
"In sha Allahu babu abin da zai biyo baya sai tarin alkhairi. Addu'a da kulawa kawai take buƙata."
Baba Malam kuwa cewa ya yi "Idan gudan ƙodar ta sami matsala fa?"
Yaya Kubra ta jinjina tambayar don ta san da wuya a rasa mai yi. "Komai na Allah ne Baba. Addu'a da kulawa kaɗai za ku iya yiwa Yaya. Sanin gobe kuma sai Allah maɗaukakin Sarki. Abu guda nayi imani da shi, Allah ba Ya taɓa barin wanda Ya fawwala Masa al'amuransa ya taɓe. Mu kyautatawa Allah zato, in sha Allahu babu nadama a cikin sadaukarwar Yaya."
"Allah Ya sa ƴar nan. Allah Ya dawo mana da ita lafiya."
Yaya Kubra ta tausayawa Inna Luba matuƙa. "Inna na san Yaya a ƙalla za ta yi wata a ƙasar nan kafin ta sami sahalewar shiga jirgi daga hukumar lafiya. Saboda haka ki fara haɗa jaka. Zan yi magana da ƙannena ma za mu ji yadda za ayi a samar mi ki passport da visa."
"Allahu Akbar. Ni ɗin?" Ta kalli Baba Malam "wai Saudiyya zan tafi. Ikon Allah. Allah Buwayi gagara misali. Ni dai Lubabatun ko wata ƴar nan?"
Yaya Kubra ta sha dariya kafin su gama waya. Tana kuma ankare da fuskar Baba Malam. Yaƙe kawai yake yi.
Alhaji ta kira ta tura masa lambar Ya'u ta ce ya kira ya haɗa su Yaya da Innarta. Haka kuwa aka yi. Sun ji daɗin ganin juna. An dai sha koke-koke da addu'o'i. Har Kamal sai da su ka gaisa da shi. Ya yi musu godiya sosai da alƙawarin zuwa har gida idan ya dawo in sha Allah.
***
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah SWT. Yau kimanin sati uku kenan da yiwa Kamal dashen ƙoda. Sauƙi ya samu sosai domin duka an sallamo su daga asibiti. Likitoci dai sun hana su barin ƙasar domin suna buƙatar kulawa sosai har na tsahon wata biyu zuwa uku.
"Ina ganin gara na kama mana gida kawai. Zaman hotel ba zai yiwu ba" Alh. Ya ce da matansa suna zaune duka su huɗun tare da shi a ɗakin hotel.
Inna ta ce "Hakan ma shawara ce, amma kafin nan ya kamata a san masu zama don a kama ɗan daidai. Sauran yaran nan su zo su koma gida haka nan."
"Kamar kin shiga zuciyata akan raguwar nan. Mata sun baro mazajensu sun tare a asibiti ayi ta hayaniya kullum" cewar Mama.
"Kamawa fa tayi." Umma mai ɗan sauƙin ta ce tana murmushi.
"Tunda dai suna samun lafiya mu kanmu sai mu ragu. Ko kuwa Alhaji?"
"Wannan shawarar ku ce. Ni dai ƙafata-ƙafar Habibu da iyalinsa." Ya gyara zama yana sauraron su.
Hajiya aka bawa dama. Ta zauna ta gama lissafinta ƴan uwanta su ka yi na'am. Umma za a bari tare da Bishir. Sai kuma Taj da Hamdi saboda zamanta kusa da Yaya yana da mahimmanci. Mubina ma babu inda za ta je. Sauran kuwa Alhaji ya ce da kansa zai faɗa musu su shirya nan da kwana uku su za su tafi. Sannan akwai wanda zai nema a samar mu su gida.
"Dr. Hadifi ya ce yana son ganin mu ni da Habibu. Idan mun dawo zan yi magana da su."
*
Bakin Abba Habibu ya kasa rufuwa bayan fitar Dr. Hadifi daga ofishinsa inda ya barsu su yi shawara kafin a bashi amsar batun da ya zo da shi.
"Habibu ba ce wani abu mana."
Abba Habibu ya girgiza kai "wallahi bani da abin cewa. Ni dai abin ya yi min girma. Anya zan karɓa kuwa?"
Alh. Hayatu ya ce "me zai hana? Roƙa kayi?" Ya yi gyaran murya "ba ka ganin kamar wata dama ce daga Allah SWT?"
"Har na isa a bani abu makamancin wannan?"
"Kada ka yi saɓo mana. Kowane bawa da arziƙinsa Allah Ya ke halittarsa. Kuma rabon mutum baya taɓa wuce shi. Ko dai ka je da ƙafarka ko ya biyo ka har inda kake."
"Haka ne. Allah Ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi."
"Amin amma don Allah ka yi shawara mai kyau."
Abba Habibu ya yi murmushi "Zan yi istihara in Allah Ya yarda."
* Zuwa yamma kowa yaji abin alkhairin da ya sami Abba Habibu. Dr. Hadifi ya yi masa kyautar gidan abinci sukutum a nan cikin birnin Jeddah. Tsohon ginin na Kawunsa ne ya saya ashe zai yi masa amfani. Abinnda Yaya tayi ya burge shi matuƙa, sai kuma ya tuna a hirarsu Abba Habibu ya ce ya taɓa sana'ar abinci a nan.
A hoto ya nuna musu gidan. Kusan komai na kayan aiki akwai, gyaran da za a yi kaɗan ne sai kayan abinci da za a tanada. Yayi masa alƙawarin yi musu igama shi da Yaya da duka ƴaƴansu. Sannan zai yi masa gyare gyare da kuma zubin kayan abinci na farko kafin ciniki ya kankama.
"Ku buɗe Nigerian restaurant wanda yake serving abincin ku na gargajiya." Ita ce shawarar da ya bashi.
Kamar haɗin baki duka shawararzu guda. Ya karɓa. To dai ya karɓa ɗin ranar da ragowar masu tafiya za su wuce. Ba su tafi ba sai da su ka je aka ga waje aka sanya albarka.
A gida ma ƴan uwa da su Zee anata murna da rawar jiki.
"Ki bar tunanin tafiya dai kina da aure. A daure a koyi larabci saboda idan na dawo zai yiwu na daina jin Hausa."
"To nima ai ba yanzu za ayi biki ba sai na kai level 4."
Daga cikin ɗaki Anti Zinatu ta ɗago murya "to uwar iya. Ke da yanzu ki ke jarabawar gama sakandire kike kiran level 4 saboda sallamamme ne ya aure ki? To bari iyayen naki su dawo naji ko da yawunsu ki ke wannan saɓon mai girma. In baki yi wasa ba wallahi ranar asabar zan ce da Baballen ya zo ku tafi."
Hankalin Zee tashi yayi tana neman yin kuka. Halifa kuwa dariya harda ƙyaƙyatawa.
***
Godiya da kyautatawar da Ahmad ya yi wa Zahra ba a cewa komai. He truly appreciated kulawar da ta bawa Mami duk da irin zaman da su ka yi a baya. Da ya fito daga wajen Mamin ne ya yi mata zancen Salwa.
"Babanta ne ya damu wai naje naga gidanta."
"Hakan ne ya kamata dama. Ba fa a canjawa tuwo suna."
"Ina ki ka baro amala da fufu? Ko duk ba ƴan uwan juna bane?"
Tayi dariya "ba zan yi musu da kai ba. Don Allah ka ɗauki matsayinka na babba ka wakilce kowa ka je ka ganta. Babu mamaki ma kaga ta sauya. Aure ai ba wasan yara bane."
"Allah ko? Shekararki nawa ne a ciki tuna min."
"Lokaci ɗaya mu ka yi da kai." Ta zolaye shi.
*
Da yamma Ahmad ya kira Salwa ba don ya so ba. Ita kuwa da azama ta ɗauka don ta fidda ran sake ji daga gare shi. Gashi tana jin kunyar zuwa gidansa. Alh. Usaini har gorin dangi yayi mata. Bata yi shawara da kowa ba ta kira Anti Zabba'u. Ai kuwa ranar taga tashin hankali. Irin haukan da su ka yi a gidan Ahmad su ka kwatanta a nan. Alh. Usaini ya zo ya gani ya ci musu mutumci la'ada waje daga su har ita. Banda Mami ta jawo musu ai da yanzu dangi sai sum ture na uwa da uba. Kai ba don abin da tayi ba hatta iyalin Alh. Hayatu sai sun fitar da ita kunya.
Purewater ta ɗauko guda ɗaya ta sako akan plate ta zo ta ajiye a gaban Ahmad. Ya bi ta da kallo ita da ruwan ya watsar.
"Ɗauke abin ki ba ruwa na zo sha ba."
Kunyar taji ta ce "Ko na fita na siyo maka mai sanyi? Ko zoɓo?"
"Zauna."
Zaman tayi tana godiya ga Allah da bai nemi hakan ba don ko sisi bata ajiye ba. Sadakinta ma ta nema ta rasa a cikin gidan. Ta san wanda ya ɗauka amma a yanzu tsoron tada maganar take yi.
Ahmad ya sami damar ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. Abin tsoro. Auren da bai fi wata guda ba duk ta ƙare tayi baƙi sai idanu a cikin loko kamar mujiya da haƙora gayau. Falon da ta ajiye shi babba ne irin wanda kowacce amarya za ta yi farinciki da mallakarsa. Fitilu na alfarma, POP ceiling da dukkan wani abu da zai sa ace gida ya haɗu akwai shi. Abin da babu shi ne funiture da electronics. Kuma da alama har cikin ɗakuna da kitchen haka abin yake. Shima a yanzu akan tabarma yake zaune. Ɗakin kwananta ma tabarmar ce. A cikin ɗakin Alh. Usaini kuma katifar maigadi ya ɗauko bayan mahaifinsa ya kira maigadin ya ce ya bar aikin gidan.
"Salwa wannan rayuwar ce ashe take jiranki shi yasa ki ka kasa kwantar da hankalinki akan rashin samun biyan buƙatar zuciyarki ko?"
Ta ina za ta fara faɗa masa tayi nadama amma a lokaci irin wannan da bata da amfani? Yanzu ta gane cewa idan so cuta ne da gaske haƙuri magani ne. Da ta haƙura da Taj da tuni Mami ma bata gamu da hatsarin nan ba. Everything would have been fine. Rayuwar gidan Alh. Usaini babu daɗi ko kaɗan. Har yanzu bata gabansa, hakan bai dame ta ba kamar yadda ta zame masa wajen huce haushi idan ya fita bai samo komai ba. Mahaifinsa bai barshi da komai ba sai gidan nan albarkacin auren da ya yi. Duk inda yake ajiya a banki ya sa an rufe masa da dogon gargaɗi akan kada ya kuskura ya tada maganar.
"Na san irin wadaƙar da kayi min da dukiyata. Idan zan bi kayana na tabbata baka da kuɗin biyana saboda haka magana ta mutu a tsakaninmu. Duk ranar da ka dawo mutum ni kuma nayi maka alƙawarin dawo maka da komai naka. Idan ba haka ba kuwa sai dai ka jira gado in na riga ka."
Yanzu rayuwarsa ta koma bibiyar abokai da tsofaffin yaransa yana maula. Wataran a dace wataran kuma a wulaƙanta shi. Da ya gaji ne ma ya goranta mata rashin gara da kayan ɗaki. Ita kuma saboda ɗanyen kai ta kira Anti Zabba'u. Ranar anyi sa'a ƙanwarsa ta zaga ta bayan idon iyayensu ta aiko masa da kaji da jallof ɗin shinkafa ta gaske. Kafin ya dawo daga wajen abokinsa sun cinye tas. Ita kanta Salwa bata ko ɗanɗana ba. Tana ta magiyar kar su taɓa aka rasa mai sauraronta ma. Ɗan uwa aka ce rabin jiki. Ahmad ya tausaya mata sosai. Kayan ɗaki da electronics babu abin da bai tanadar mata ba amma ta watsa masa ƙasa a ido.
Suna zaune ya danne fushinsa yana ta yi mata nasiha tana ta kuks sai ga Alh. Usaini. Takalman namiji kawai ya gani ya yi jifa da ledar hannunsa ya zare belt ya afka musu. Salwa na ganin shi ta tashi ta tsaya a gaban Ahmad ta bubbuɗe hannuwa da ƙafafu ta kare shi. Ai kuwa belt ta sauka a jikinta ta gantsare don azaba. Ya sake ɗagawa karo na biyu Ahmad ya miƙe. Kwarjini da cikar mutumtakarsa su ka sanya Alh. Usaini yin laƙwas kamar dafaffen alayyahu.
Ahmad ya riƙe belt ɗin tare da hannunsa ya nuna masa Salwa.
"Duk abin da za ka yi, musamman wanda ya shafi mu'amala da mutane kaji tsoron Allah. Da kai da ita da gurɓatacciyar rayuwarku ku ka haɗu amma hakan ba yana nufin da ita za ku ƙare har ƙarshen rayuwa ba in kun so."
Ficewa yayi ko waige babu. A waje yaci karo da ledar da Alh. Usaini ya yar. Taliya ce leda ɗaya sau mai, maggi da kayan miya na naira ɗari biyu. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Yanzu Salwa ake ciyarwa a haka? Lallai kowa yaƙi sharar masallaci zai yi ta kasuwa.
Ya koma gida cike da damuwa. Ya kira Abban Salwa akan maganar kayan ɗaki ya ce ya rabu da ita. Darasi yake so ta koya a cikin auren nan. Hujjojin da ya bashi duka ya gamsu da su. Duk da haka washegari ya tura ƴar ƙurƙura gidan shaƙare da kayan abinci.
"Idan da kuɗi a wayarka don Allah ka bani aro na kira Yaya Ahmad nayi masa godiya."
Tsaki ya banka mata ya tashi ya fita da sauri ya bi bayan mai ƙurƙurar nan da gudu. Sai da ya kusa ƙarshen layi ya tsaya. Yana faman haki ya ce ya taimaka masa da numbar wayar wanda ya aiko shi. Mutumin ya karanto masa ya kwafa. Da numfashinsa ya daidaita ya kira shi.
"Dama godiya na kira nayi maka."