Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 57

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 57

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 57: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 57. Yaya da Abba Habibu dariya su ka yi. Kamal ya fita ya shiga mota su…

1,215 words

Yaya da Abba Habibu dariya su ka yi. Kamal ya fita ya shiga mota su ka tafi gida da Taj da yake gidajensu babu nisa da juna. Mubina tana gida laulayi ya make ta amma ta gama shiri Hamdi kuma ciki ya tsufa sosai. Haihuwa ko yau ko gobe.

*

Kukan Hamdi na huɗu kenan yau saboda Taj ya ce ba za ta je dinner ba. Da ya shigo kallon juna su ka yi kowa ya ɗauke kai. Yana fitowa daga wanka da gangan ya leƙo falo.

"Taso ki fito min da kaya."

"Suna kan gado."

"Turare fa? Wanne zan saka?"

Ta sake kawar da kai "Na fesa a jikin kayan"

"Body spray fa?"

"Akwai akan dressing mirror." Ta san jan magana ne kawai tunda abubuwa ne da yake yiwa kansa.

Ya koma ya shirya cikin ankon su na shadda shi da su Kamal. A gabanta ya tsaya ya cika mata hanci da ƙamshi mai daɗi.

"Menene ne kuma?" Ta ce da muryar kuka.

"My goodbye kiss."

Da kumburarrun idanunta ta harare shi "na ajiye a ƙofar gida."

"Wannan kuma ba ki isa ba. Ki min kawai na tafi."

"You are looking for my trouble." Ta tura baki tana jan hanci.

"Yep."

"Wai me nayi maka ne?"

"Kin kasa kallona saboda kina fushi ki ce nayi kyau."

Satar kallonsa tayi ta ce "kayi kyau."

"Ko ke fa. To tashi ki shirya mu tafi."

Maganar a bazata ta shiga kunnuwanta. Ta tashi da ƙarfinta ta rungumo shi tana dariya.

"Da gaske kake?"

"Idan naƙuda ta taho ki tabbatar kin riƙeta tunda rigima ta sa ba ki son zama a gida."

Da dariya Hamdi ta ce "ni fa ba bikin ne ya dame ni ba. Ƴan matan da za su ji ka burgesu nake son na hana samun dama. Ka sanni da kishi."

Taj ya tuntsire da dariya. Ya zauna ya ce mata nan da minti shabiyar idan bata fito ba zai tafi. Da sauri ta dinga komai. Ta fito a minti ashirin da biyu. Taj yana zaune yana waya. Hannunta ya riƙe su ka fita daga gidan tare.

* Biki yayi biki domin ya sami halartar mutane da dama cikin ƴan uwa da abokan arziƙi. Ƴan uwan Yaya da ƴaƴansu sun zo daga Batsari tare da Inna Luba. Ya'u ya zama na hannun daman Yaya Kubra domin har ta mayar da shi makaranta. Amma da su Anisa harda Hajjo su ma sun zo. Ƴar ficika da matarsa ba a barsu a baya ba. Haka dangin Alh. Hayatu da na matansa na kurkusa duk sun zo.

Ahmad ya taho da Zahra sannan ya ce Salwa lallai sai ta zo saboda shi bai ga amfanin ƙauracewa mutane ba. Idan ana haɗuwa ko yaya yau da gobe za a iya yafe mata.

To ashe Ummi ma da kishiyoyinta harda maigidan Kofar Ɗanliti su ma sun taho. Hamdi ta tako da ƙyar take ɗaga ƙafa taji kamar da mutane a gefenta. Ta juya hagu ta haɗa ido da Salwa gayauna. A ɓangaren dama kuma Ummi yangaura. Kowacce ta lalace ta fita hayyacinta. Su ukun suna yiwa juna kallon kallo su ka tsinkayi muryar Taj daga bakin ƙofar hall ɗin.

"Ke da na ce ki jira ni a mota in fara sama miki wurin zama? Na zo na ɗauke ki?"

Salwa da Ummi su ka bi shi da kallo. Ya fi Taj ɗin da su ka sani cika, kyau da ɗaukar ido. Aure ya karɓe shi kamar yadda ya karɓi matarsa. Ko me su ka ji a ransu ba su furta ba.

"Ka zo ka tayani tafiya dai."

Taho wa ya yi Hamdi ta saƙale hannu a waist ɗinsa saboda support su ka dinga takawa tare har su ka ɓacewa ganinsu. Sai su ka sake kallon juna, kowacce ta buga tsaki. Za su fara cacar baki sai Ummi ta kula Alh. Usaini yana tahowa. Yadda Salwa ta fige shi har ya fi ta. Wata muguwar dariya ce ta suɓuce mata bata sani ba. Kamar daga sama taji muryar Kofur.

"Ummi ban hana ki dariya irin wannan ba?" A gefensa hagu da dama kishiyoyinta ne.

"Wai, sannu fa." Salwa ta ce sannan ta rama dariyar da tayi mata.

*

A falon gidan Abba Habibu, shi ne da Alh. Hayatu su ke hira irin tasu ta manya. Hirar yawanci ta iyalansu ce da abubuwan da su ka shafi rayuwar yau da gobe.

Can dai Alh. Hayatu ya ce "ni kuwa Habibu akwai abin da nake sha'awar ci amma na kasa faɗawa iyalina tunda ban saba ba."

"To ya aka yi ka san kana so tunda baka ci?"

"Ka san jikoki akwai kyauta. A baki aka zo aka bani rannan da aka yi. Si ka tayar min da kwaɗayi amma ban isa na nemi ƙari ba kada na zama abin surutu a gidan."

Abba Habibu ya miƙe yana dariya "ban yi ritaya ba har yanzu. Ya sunan sa in dafa maka?"

"Wainar fulawa" Alh. Hayatu ya faɗa yana wani basarwa don kada Abba Habibu yayi masa dariya. Bai tsira ba kuwa don sai da ya yi masa dariyar sannan ya shiga kitchen.

Bayan minti talatin Alh. Hayatu ya ɗora babbar rigarsa a saman kujera wai kada ta ɓaci da manja. Ya zauna a kan kafet yana cin wainar fulawa yana jindaɗi sai ga wayar Kamal sun wai wuce asibiti da Hamdi shi da Mubina da Taj. Iyayensu sun biyo bayansu.

Ya kalli plate ɗin ko rabi bai ci ba kamar kada ya tashi don wannan tafi wadda aka yi a gidansa daɗi. Sai da ya ƙara loma guda sannan ya tashi su ka tafi asibitin. Suna shiga Mubina na fito musu da jariri.

Abba Habibu ya ce a miƙawa Alh. Hayatu. Yana karɓa sai cewa ya yi "wainar"

Abba Habibu ya yi saurin cewa "Wai ina wa?"

"Wai ina maigidan nata?" Alh. Ya wayance.

"Gamu nan fa Alhaji."

Ya juya ashe sun wuce kowa a wurin bai sani ba. Farin kaya mai tonon silili Inna ce ta fara cewa

"Mene ne wannan a gaban rigarka Alhaji?"

"Ina babbar rigarsa za ki ce" in ji Mama.

Hajiya ta ce "Ƙamshin manja nake ji kamar wainar fulawa."

Alh. Hayatu da Abba Habibu su ka soma kame kame duka wajen ya kaure da dariya.

Basu bar asibitin ba sai da aka fito da Hamdi kowa ya ganta lafiya. Alh. Hayatu ya miƙa mata jaririn da amarya Zee ta ƙanƙame bayan iyaye sun gama saka masa albarka. Ya miƙawa Hamdi bayan ta zauna akan gado.

" Hamdi ga Habib Tajuddeen Hayatu. Allah Ya raya shi bisa sunnar Ma'aiki SAW. Allah Ya sa ya yi koyi da kyawawan halayen mai sunansa."

"AMIN" kowa ya amsa da farinciki.

Abba Habibu da bai taɓa zaton wannan karamcin ba ya rasa me zai ce sai kawai ya dinga murmushi yana godiya ga Allah da Ya nufe shi da ganin wannan rana.

Alhamdulillah bata gushe daga bakinsa ba har ya kwanta yana tunanin rayuwar duniya mara tabbas. Ace har ya yi ƙimar da za a yi masa takwara?

"Allah na gode Maka. Ya Rabbi Ka ƙara shiriya da albarka ga iyalanmu da mu kan mu. Ka raba mu da bin hanyar taɓewa. Ka dawo da ɓatattun cikin mu hanya madaidaiciya. Amin"

HAMDAN KATHIRAN ƊAYYIBAN MUBARAKAN FIHI. Ya Allah Ka yafe min kurakuran da su ke ciki. Ka sa mu amfana da darrusan. AMIN

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull