Kenza eBookz

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 7

Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 7

Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 7: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 7. Ɗokin da ya kama shi tunda aka yi sanarwar jirgi zai sauka nan da…

3,368 words

Ɗokin da ya kama shi tunda aka yi sanarwar jirgi zai sauka nan da mintuna kaɗan ya bashi mamaki. Belt ɗin da aka ce fasinjoji su ɗaura ya gyara gami da leƙa tagar jirgin. Garin Kano yake gani da tsakar rana ƙarfe biyu da rabi. Tsirarun bishiyoyi da yalwar ciyayin damina sai gine gine marasa tsayi ba kamar inda ya baro ba. Tayoyin jirgin na dira ƙasa sabon yanayi ya baƙunce shi na farinciki da tarin fargaba. Uwayensa da ƴan uwa tun a waya su ke nuna farincikinsu. Alhaji ne damuwarsa. Zai karɓe shi ko kuwa yanzu ma zai cigaba da nuna masa ƙyama kamar wanda yake aikin saɓon Allah?

*

Kafin kowa ya kula wata matashiya dake tsaye tare da iyalan Alh. Hayatu Sule ta hango Taj ta cikin ƙofar gilas. Kyakkyawan saurayi ne wanda duk hangen mace indai ta same shi ta sake ɗaga ido neman wani dole a sanyata a sahun marasa wadatar zuci. Yana kama da ƴan uwansa amma akwai wani abu dake tattare dashi wanda ya bambanta shi dasu da take iya gani. Ba hasken fata bane domin wasu cikin ƴan uwan nasa sun fi shi haske. Haiba da cikar halittarsa su ne suka fi komai ɗaukar hankalinta. Tana can duniyar saƙe saƙe bata kula da yadda ƴan uwan nasa da ƴaƴansu su ka bar wurin ba domin tararsa sai daga baya.

Idanu kansu su ka dawo ganin yadda ake pasin-pasin wajen rungumar Taj. Gashi taron mata don Ahmad da Kamal ne kaɗai maza in ka cire jikokin gidan da ba wani sabo suka yi dashi sama da waya ba. Bishir da Abba su na makaranta.

"Aunty Salwa mu je mana."

Wani yaro ne ya yi maganar yana jan hannun matashiyar budurwar da Taj ya sacewa zuciya farat ɗaya. Murmushin jin kunyar kanta tayi ta kama hannun yaron su ka matsa kusa dasu. Yaron ya saki hannunta ya koma wajen Ahmad yana cewa ya ɗaga shi zai ga Uncle Taj.

"Daddy ni bai ganni ba. Ɗaga ni sama."

Kamal ne ya ɗaga yaron ya miƙawa Taj. Ya karɓe shi ya rungume yana sumbatar kumatunsa.

"Babana da kansa."

Yaron ya girgiza kai "Uncle Taj sunana Hayat."

"Ba Hayatu ba?" Taj ya ce da alamun mamakin da yasa yaron saurin cewa "Hayat yafi daɗi."

Dariya kowa yayi sannan Ahmad ya ɗan turo budurwar nan gaba.

"Ga Salwa ku gaisa."

Taj ya sakar mata murmushi domin kuwa ƙanwar yayansa Ahmad ce da su ka haɗa uwa. A yanzu haka sakamakon karatu da ya kawota Kano daga Bauchi garin da mahaifiyar tasa ta sake aure shi ne take zaune a gidansa. Shekararta ta biyu kenan a Kano kuma iyalin Alh. Hayatu har matansa basu nuna mata wani abu da zai sosa zuciyarta ba. Ƙanwar ɗansu ita ma ƴarsu ce.

Shi Ahmad matarsa ɗaya da yara biyu. Hayat da ake kira da sunansa bisa umarnin Alhaji sai jaririyar da ko arba'in ɗinta ba ayi ba mai sunan Mama wato Aisha.

Ɗunguma su ka yi a motoci huɗu su ka nufi gida. Mazan motarsu ɗaya su kaɗai. Kamal ya yiwa Taj bayanin cewa sun canja shawara zai zauna a gidan Ahmad har lokacin komawarsa.

Jikinsa a sanyaye ya tambaye su "Alhaji ya ce kada na zauna masa a gida ne?"

"A'a" Ahmad ya faɗi da sauri.

"Yaya ka faɗa masa gaskiya mana." Cewar Kamal dake tuƙi "ɓoyewar bata da wani amfani."

"Faɗa min me ya ce Happiness."

Tiryan tiryan kuwa Kamal ya faɗa masa yadda Alhaji yaje ɓangarensu har ɗaki ya ce yaga saƙon Taj na tahowa buɗe gidan abinci. Ba zai hanasu mu'amala da ɗan uwansu ba amma indai da niyyar cigaba da saɓa masa ya dawo ya nemi wurin kwana.

"Amma ya amince ka shiga gidan ka gaishe da su Hajiya. Kawai dai kada ka bari ku haɗu."

"Zan zauna a hotel."

Dukkaninsu kallonsa su ka yi. Ba kuma don abin da ya ce ba, yadda muryarsa ta fito kai ka san ba ƙaramar dauriya ya yi ba. A shaƙe take da wani irin rauni daga zuciyarsa.

"A gidana za ka zauna. Tun jiya nasa Salwa ta gyara maka ɗaki." Ahmad dake baya ya zura hannu gaban motar ya ɗan bubbuga masa kafaɗa.

"Ba zan zauna na takura iyalinka ba. Infact mutumcina ma zai zube. Kawai bamu taɓa haɗuwa ba sai da aka koreni daga gida for the second time."

Dariya Kamal ya yi "zaman hotel ɗin ba matsala bane amma ba mutumcin aljihunka bane gaskiya a garin da kake da gidan ƴan uwa sama da hamsin da za su so zamanka tare dasu."

Kamar shi ya kar zomon, Taj ya ɗaure fuska ya ce masa "kawai ka faɗi abin da yake ranka. Kana tsoron kada naje ace na fara bin mata ko?"

"Ba a ji mutuwar sarki a bakina ba, amma dai kai da kake kan tsini idan ka ƙara da kwanan hotel ban san yaya za ku kwashe da Alhaji ba."

"Allah ni ba ɗan isk* bane. Saboda tsoron kada Alhaji ya yi min baki watarana na lalace ko girlfriend na kasa yi." Taj ya amsa defensively.

"Daga budurwa sai lalacewa Taj?" Cewar Ahmad, shi da Kamal su na dariya.

Shi kuma Kamal ya ce "dama me za kayi da busassun turawan nan da ba su da gaba da baya?"

Haɓa Taj ya riƙe yana kallonsa kafin ya ce "Yaya kaji irin zancen banzan da Happiness yake yi ko? He is long overdue for marriage."

"Da za ku yi auren maybe da ka samu daidaitawa da Alhaji."

Hirar tasu sai ta koma ta dacewar Kamal da Taj su nemi mata su yi aure haka nan. Da haka su ka isa gida. Sai dai kafin maigadi ya buɗe musu gate motar Alhaji ta tsaya a bayan tasu.

"Alhaji ne" Ahmad ya faɗawa Taj.

Zuciyarsa ya ƙarfafa ya fita daga motar duk da tunin da yayunsa ke yi masa akan gargaɗin Alhajin na baya son ganinsa. Da sassarfa ya isa bakin motar da gilasanta duka baƙaƙe ne. Ba a sauke ko ɗaya ba a ciki amma ya tabbatar daga cikin ana ganinsa. Direba ke tuƙin motar amma da dishi-dishi yana iya hango Alhaji zaune a baya. Ya taka har bakin tagar ɓangaren nasa ya durƙusa cike da girmamawa.

"Sannu da zuwa Alhaji."

Tun a hanya jikinsa dama ya bashi zai ga ɗan nasa. Tunaninsa ne ma ya hana shi gama uzurin da ya fitar dashi. Yanzu da yake ganinsa kewar Taj ɗin ta mamaye zuciyarsa. Idanunsa su ka tara ƙwallar da yake jin abin kunya ne a ganshi da ita. Saboda haka bai ɓata lokaci ba wurin umartar direbansa da ya yi ribas su bar wurin.

"Alhaji ka daure ka saurari yaron nan don Allah."

"Koma na ce!"

Direba ya so yin musu Alhajin ya manta da dattijantakar mutumin ya daka masa tsawa. Wannan yasa shi danna accelerator bayan yasa giya a ribas da ƙarfi. Ƙura kuwa ta tashi ta baɗe Taj da yake durƙushe har lokacin bai motsa ba.

Ba shi ya tashi ba duk da magiyar su Kamal da wasu cikin matan da su ka riga su dawowa daga airport. Anyi a idonsu ne saboda an buɗe gate. Kuma dama Kamal na yin horn su ka firfito tare da iyayensu.

Ahmad ne ya ɗaga shi zai shiga dashi gidan ya cije ƙafarsa.

"Mu je gidan naka."

"Kaga su Umma fa a tsaye. Mu ƙarasa ku gaisa sai mu tafi."

Kai a sunkuye Taj ya girgiza kai.

"Wallahi ba zan shiga gidan nan ba sai ranar da mai shi ya kirani ciki da kansa."

Motar ya kama zai buɗe Kamal yayi saurin danna lock da muƙullin hannunsa.

"Kada kayi taurin kai. Don Allah ka shiga ciki."

Kai Taj ya ɗaga ya hango Salwa a tsaye tare da sauran. Bai yarda ya haɗa ido da kowa cikin matan gidan ba ya ƙwala mata kira.

"Salwa..."

Gabanta ya faɗi, zuciyarta tayi wani irin bugu. Sai kuma wani irin ɗumi mai daɗi ya lulluɓe mata jiki da ta tuna sunanta kaɗai Taj ya ambata a wannan yanayin da yake ciki. Ƙafafunta kusan da ikon kansu su ka ƙaraso da ita gabansa.

"Kai ni gidan Yaya a rickshaw (haka ake kiran adaidaita sahu a India)."

Alamun rashin fahimta ya gani a tare da ita ya nuno mata guda da ya shigo layin nasu.

Kai Ahmad ya girgiza domin hanata sannan ya umarci Kamal da buɗe motar. Da kansa ya tura Taj baya ganin ƙanin nasa ƙiris yake jira ya saki ƙwallar da ta rufe masa idanu.

"Kai shi gida zan taho."

Haka kawai ya ce da Kamal ya buɗe gaba ya ce da Salwa ta ɗauki Hayat su bi shi. Suna tafiya shi da sauran suka koma ciki.

"Korarsa ya sake yi?" Umma ta tambaya da kukanta.

"A'a. Ku shirya mu je gidana ku gan shi."

"Me ya faru Ahmad?"

Mama da Hajiya duka kuka su ke yi. Inna kuwa jingina tayi da ƙofar shiga gidan ta runtse idanunta. Da yake duk da mayafi su ka fito Ahmad buɗe motarsa da ya bari a gidan ya yi ya ce su shiga.

"Alhaji zai yi faɗa Ahmad."

Da mamaki mai haɗe da ɗimbin takaici Mama ta kalli Inna da tayi maganar baki buɗe.

"Sau tari damuwar uwa da jajircewarta na taimakawa wurin ragewa ƴaƴa raɗaɗin hukuncin uba. Kina tsammanin akwai riba idan duka ku biyun kun juya masa baya? Ko kuwa kina ganin yin hakan wata gwaninta ce da Alhaji zai yaba?"

Umma dama tafi kowa zafi kuma maganarta indai akan gaskiya ne ba kasafai take taunata ba.

Jiki ba ƙwari Inna ta ce "ba haka bane."

Umma ta ce "to yaya ne? Sama da shekara goma rabon da ɗanki ya sanya ki a ido zahiri. Banda ma Allah Yasa Takwara (da yake haka su ke kiran juna da Amma) jajirtacciya ce da tuni ɗannan ya bi duniya. Uwa da uba a raye amma kun bar masa wawakeken giɓi mai wuyar cikewa. Baku san ku yabi ƙoƙarinsa ko kuyi masa faɗan kuskure ba."

"Kiyi haƙuri don Allah" Inna ta ce tana kuka sosai.

"Magana ce ta gaskiya. Kin goyi bayan miji kun mayar da yaro marayan ƙarfi da yaji. Yau ko ɗan kafin Fatiha ya kawo muku gida wannan hukuncin ya yi tsauri, balle girki. Mene ne aibun girkin nan ne? Har mamakin ki nake yi idan kina sha'anin gidan nan kamar babu abin da yake faruwa."

"Jamila ya isa haka don Allah. Na tabbata tana da dalilinta na yin duk abin da tayi tunda ita tayi naƙudar Taj. Ta fi mu son sa." Hajiya ma ta gwaɓa tata maganar.

Kukan Inna ya sake tsananta da wannan rashin fahimta da abokan zamanta su ka yi mata. Ita fa tun lokacin da taga auren Mama yana girgiɗi a dalilin Taj hankalinta ya yi mugun tashi. Balle da aka zo sulhun nan ta fahimci ashe su Hajiya ma dake gidan sun daina girki. Wannan dalilin yasa ta sauke dukkanin tijarar da ta tanadarwa Alhaji. Domin tana da tabbacin muddin ya sallameta akan Taj su ma za su gwada masa rashin goyon baya. Ƙarshenta cikin fushi aurensu ya sami matsala. Indai ba butulci ba kuwa irin zaman da su ke yi a gidan bata jin ya kamata ta yi musu sakayya irin wannan.

Zafin da taga sun ɗauka ne ya bats damar yi musu wancan bayani yadda za su fahimceta.

"Kuna ganin rayuwar Taj za ta yi albarka idan sanadinsa gidan nan ya wargaje? Fushi irin na Alhaji nayi imanin sallamarmu duka lokaci guda ba zai yi masa wahala ba. Sai dai ya yi nadama daga baya. Sannan gabaɗaya yaran gidan nan da wuya su sake yiwa ɗan uwansu kallon mutumci. Da farin gashinmu a ka ace muna zawarci."

Allah Sarki. Tana rufe baki Umma ta rungumota.

"Ki yi haƙuri Abullen Alh. Hayatu. Shaiɗan yaso amfani da ɓacin raina ya haddasa mana fitina."

"Sunan da ki ka kira ni dashi na mene ne kuma?"

"Na ƙaunar rigimammen tsohon nan mana."

Dariya su ka ji an kwashe da ita. Shaf sun manta da ƴaƴansu dake wajen a tsaye. Kowa da jan ido an sha kuka suke dariyar daidaitawar iyayen nasu. Da wannan kuma babbar ƴar gidan Yaya Bintu ta sanar da ƴan uwanta cewa babu masifa da za su bari ta shiga gidan sama da rabuwar kawunansu. Don haka kowa ya shirya abin da zai iya domin taimakawa Taj. Haɗin kansu kaɗai zai iya sassautawa mahaifinsu haƙƙin ɗansa da yake ɗauka.

Zaman lafiya aka ce yafi zama ɗan sarki. Alhaji bai san cewa duk cikim alkhairansa na duniya yadda ya gina gidansa shi ne mafi girman arziƙinsa ba. Gashi yana neman ɓata abin sa da hannunsa.

Motar Ahmad su ka shiga ya kaisu gidansa. Sai ga Taj ya manta da dukkanin damuwarsa da ya ganshi tsakanin uwayensa.

***

Abba ya maimaita zancen da yaji daga Vice Principal yafi a ƙirga a zuciyarsa bayan sun gama waya. Abin ne bambarakwai wai namiji da suna Hajara. Ta yaya ma za a ce Hamdi tayi dambe har ta kai rashin zuwansa akan matsalar zai iya jawo mata kora? Hamdi ce fa. Yarinyar da ko a cikin ƴan uwanta lokacin ƙuruciya da wuya a kawo ƙararta.

Damuwar da su ke ciki shi da Yaya akan matsalar tashinsa da aka yi daga wurin sana'a sai ta zama ba komai ba. Fatan wayewar gari kawai yake domin yaje ya ji me yake faruwa. Sai dai kuma hantsi na soma leƙowa yaji wani irin tashin hankali. Da hankalinsa ya riga ya san yadda yaran ke kunyar nuna shi musamman ita Hamdi. Shin za ta yi maraba da amsa kiran nasa ko kuwa? RAYUWA DA GIƁI 8

Batul Mamman💖

***

Zazzaɓin gaske ne ya kama Ummi tun bayan ta saurari wayar Vice principal da mahaifinta. Aikin gama ya riga ya gama. Bayan ya ajiye wayar wani irin kallo ya yi mata ya jinjina ƙarfin halinta. Sannan ya ƙara tabbatarwa mace abar tsoro ce komai ƙanƙantarta.

"Wannan mutumin shi ne mahaifinki Ummi?"

Kai a ƙasa ta ce "eh."

"Wanda yake zuwa kuma ya kuke da shi? Kuma me yasa ki ka zaɓi faɗin gaskiya yanzu?"

Shiru tayi babu amsa tunda Hamdi ma taƙi magana me zai sa ta fara?

Rai a ɓace ya ce "To kuwa ki kwana da sanin cewa yau ce ranarki ta ƙarshe a makarantar nan. Don ban ga wani dalili da zai hana a kore ki gobe ba ko da kece mai gaskiya. Sannan dole zan kira shi domin a warware komai gaban mahaifin naki."

Yanzu ma kasa cewa komai tayi sai faman saƙe-saƙen neman mafita. Sannan a gefe guda babu irin ashar ɗin da bata saukewa Hamdi ba. Da farko ta san kawai jindaɗin samun mai yi mata bauta a makaranta tayi da sanin sirrin Hamdi. Yanzu kuwa wata irin tsana ce da za ka ji komai ma za ka iya yiwa mutum take ji akanta. Har lokacin bata saduda ba don tana jin da Hamdi tayi mata biyayya ta bata ruwan nan da bata ga wannan lokacin ba. Haɗuwarta da Baba Maje gobe ba ƙaramar tarzoma zai tayar ba.

"Ki tashi ki fice min daga office nace."

Tsawar VP ta dawo da tunaninta inda take. Ta miƙe za ta fita sai kawai wani tunani ya zo mata. Guntun murmushi ta saki wanda har ga Allah sai da ya VP ɗin tsoro da shakku akanta.

Wurin ƙawarta konace babbar ƴar korarta Widad taje da saurinta. Sun gama nasu punishment ɗin na yau sai kuma washegari da ake sa ran samun ruwa. Za su wanke banɗakunan makarantar kaf har na malamai. Ga kuma sharar harabar makaranta da cire ciyayi.

Widad na ganinta ta tashi zaune daga kwanciyar gajiyar da tayi. Ummi ko kallon arziƙi bata yiwa ciwon dake babban yatsan Widad na ƙafa wanda taji a wurin faɗan ɗazu ba. Kuma ta gan shi sarai amma ba shi ne a gabanta ba.

"Bani wayarki in kira Uncle B"

"Kuna can aka zo inspection ɗin bazata tun bayan an nuna wayarki a wajen principal. Yau wayar da aka fitar daga ɗakin nan tafi ashirin."

Muguwar harara Ummi ta jefeta da ita sannan ta yatsina fuska ta ce mata "banza, me yasa ko a pant baki ɓoye ba?"

"Korarmu aka yi waje bamu san dalili ba. Sannan aka yi searching ɗinmu da ɗai-ɗai." Widad ta amsa tana mai ɓoye zafin zagin da halin ko in kula da Ummin ta saba nuna mata.

Plan ɗinta na farko ya faɗi tun kafin ta aiwatar. Dama niyarta ta faɗawa sugar daddy ɗin nata da take kira Uncle B idan an nemi numbarsa kada ya yarda ya zo. Shawara ta biyu kawai za ta ɗauka. Idan an zauna gobe kawai ta tada aljanu kuma duk yadda za ayi da ita kar ta yadda ta dawo daidai sai an koma gida. In ya so ko kasheta za ayi gara ayi a can.

***

A hanyarsa ta zuwa tasha cikin adaidaita sahu Abba ya kira ƙaninsa a waya. Hankalinsa ne sam bai kwanta da zuwa makarantarsu Hamdi ba. Yana son kare martabar ƴaƴansa daga dukkan abin da zai iya janyo musu raini daga mutane. Ya tuna wani lokaci da Yaya Hayatu kamar yadda yake kiran Alhaji yayi masa wata magana a baya.

"Habibu gaba nake jiye maka. Lokacin da za ka ji kunyar nuna kanka a wasu wuraren saboda kana ganin kamar darajarka bata kai ba. A lokacin ilimi ko rashinsa, talauci ko arziƙi ba su ne za su zame maka shamaki ba. Wannan mazantakar da kake gudu da Allah Ya karramaka da ita ce za ka so a baka aro ko na awa guda ne."

Bai manta yadda ya murguɗa baki bayan wucewar Alh. Hayatu ba. Ya doka cinya harda tofar da yawu.

"Aniyarka ta bika. Sa idawa, ana ruwa kuna ƙirgawa." Ya nuna ƙafarsa "wannan sayyara da Allah Ya bani babu inda ba za ta shiga ba sha Allahu."

Ga ire iren ranakun sun zo. Ina ma ana mayar da hannun agogo baya. Da ya juya lokaci ya canja komai banda auren Jinjin. Matar da ta rufa masa asiri ta kuma bashi ƴaƴa mafi soyuwa a gare shi.

Gaisawa su ka yi da ƙanin nasa da girmamawa sannan ya faɗa masa halin da yake ciki a kunyace.

"Wallahi Yaya Habibu ka ganni a asibiti wani maƙocina ne babu lafiya. Daga shi sai matarsa ga yara ƙananu ta taho dasu. Basu da kowa a nan sai mu maƙota. Yanzu haka yayansa dake Zaria yana hanya. Tun asuba nake nan."

"Ahhh, yi zamanka Abdulƙadir. Bari kawai naje."

"Ka daina ɓoye kanka daga rayuwar yaran nan. Yau in dukkaninmu babu sai kai kaɗai shikenan sai ace zuri'armu basu da uba saboda abin da ya wuce?"

Yayi maganar ne saboda ya saba ji daga yaransa cewa ƴaƴan yayan nasa suna kunyar alaƙarsu da shi. Bai ga laifinsu ba Fisabilillah. Amma kuma Allah da Ya haɗa alaƙar Shi Ya san yadda zai tafiyar da al'amura. Tayasu ɓoye kansa ba dabara bace tunda duk lalacewa da uba ake ado.

Abba bai sake neman kowa ba ya tafi makarantar. Anyi sa'a yau shadda ya sanya ruwan madara, riga da wando harda hula. Da ya shiga makarantar bayan tafiyar minti arba'in tafiyarsa ya fara ƙoƙarin gyarawa. Sannan da zai tambayi masu gadi ofishin principal ya daddage ya kumbura murya. Amma kunne da idanu masu lafiya babu yadda za ayi su kasa fahimtar me ake son ɓoye musu. Basu dai nuna a fuska ba guda ya nuna masa hanyar office ɗin. A can gefe inda ake ajiye motoci ya ga wata kamar ta Baba Maje. Amma da yake baya tare da nutsuwa bai tsaya ƙare mata kallo ba.

***

A rayuwa babu abin da yafi tashin hankali kamar a samu wani ya san sirri a kanka wanda baka so a sani. Kuma in anyi rashin sa'a ya dinga amfani da wannan damar wurin cusgunawa rayuwarka. A shekara shidan da Hamdi tayi a makarantar nan bata taɓa shiga matsanancin hali ba sai da Ummi ta fara blackmailing ɗinta. A jiya da abu ya fito fili waɗanda su ka sami ganin bidiyon nan su ka labartawa waɗanda basu gani ba, sai taji zuciyarta wasai. Abin ya matuƙar bata mamaki. Tayi zaton in an sani an tsokaneta za ta iya yin kuka. Sai gashi babu wanda ya tunkareta tunda aka ga abin da ta yiwa Ummi da kuma maganar da ta yaɓawa wata Metiron bayan ta dawo ɗaki.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull