Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 31

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 31

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 31: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 31. Meenal tana gama wayar ta zauna ta ɗora waya da…

3,354 words

Meenal tana gama wayar ta zauna ta ɗora waya da dadironta suna ta shan soyayyarsu don tana ƙara tabbatar masa babu rabuwa tsakaninta da duk wani abokin holewarta don ta yi wani aure, babu abin da za a fasa. Zaman da ta yi ta san duk ƙwawar hajia dole ta gaji ta haƙura domin ta san za take ta tunanin bata gama wayar ba.

Hajiya kuma sai jera hamma take don da yanzu a gida ne da ta fara haramar cin abincin rana amma yanzu babu hali bata ma cikin nutsuwa da kwanciyar hankali an barta tana ta tangaririya a titi tun da sanyin safiya tana zuwa wajen malami tare da kashe naira dubu gomar magani bayan gashi shi kansa maganin ba a karɓa ba bare ta saka ran Meenal ɗin za ta yi amfani da shi.

Suna gama wayar sai kiran Mominta ya shigo hakan ya sa ta ɗauka cike da farinciki suke waya Momi ta ce

"Ta gaban goshi fatan dai babu matsala" Meenal ta ce

"Momi ki bar batun matsala ko a mafarki ai tun da dai ni ce ƴarki to kin yi bakwana da matsalar damuwar ƴa mace a gidan aurenta don kin san babu wanda zan yarda ya yi awon gaba da ƴancina a gidan miji" Momi ta jinjinawa ƴarta tana ƙara bata ƙarfin gwiwa da jaddada mata kar ta kuskura ta bada fuskar da za a rainata a gidan aure!.

Meenal ta ce

"Momi ni dai zan yi iya iyawata don ganin ba a tozarta ni ba duk da na san wani lokacin duk ƙoƙarin mutum na gujewa natsala sai ta afka masa sannan matsaloln gidan aure ba kidahumanci ne yake kawo su ba ko rashin wayo, sai dai ya danganta da wanda ka dace da shi a matsayin abokin rayuwa ko kuma suruka da dangin miji, duk da akwai matan da suke bayar da kansu suka sakin jiki a musu kowane cin kashi duk da cewa mace ƴar biyayya ce amma ba ce ta bada fuskar da za ta zama baiwa ko kuma abar wulaƙantawa ba" Tun da ya fara bayani Momi take jinjina mata daga na ta hau faɗin

"Kar ki kuskura ki ragawa Hajiya na faɗa miki daga ita har ɗanta ki koya musu karatun ta nutsu don na ga da sauransu a karatub duniya sun ɗauka don kina ƴata za su ci kashi a kanki ko su juye kowace bola a kanki to ba haka take ba"

Meenal ta hau ba mahaifiyarta labarin yadda abubuwa suka wakana tsakaninta da Hajiya da Nasir har ma da zuwan Hajiyar gidan ta kawo mata magani wai bata cikin hayyacinta sai dai bata faɗawa Momi wayar da ta yi a gaban Hajiyar ba.

"Magani Meenal hauka ake za ki karɓi magani a wajen wani barw ki yi amfani da shi, karki manta ni da Hajiya tif da taya muke hakan ba zai hana ta tarwatsa ko farraƙa tsakaninki da ɗanta ba don son zuciya irin nata kin sani bata ƙaunar a ɗanɗani arziƙin ɗanta ta fi son koyaushe daga ita sai ƴaƴanta don haka tana iya karɓo maganin da za ta rage miki matsayi a wajensa don kar yake kyautata miki, ko kuma ta yi maganin da za ki koma kina mata biyayya kamar vaiwa ta taka ki yadda ta so kamar yadda suka mayar da wannan uwar gidan marar ƴanci da galihu a wannan gidan"

Meenal ta ce

"Momi dama ina sane ba zan yarda ma na yi amfani da shi ba, sai faman faɗi take wai bana hayyacina ta fi so in ci gaba da ƴasƙantar da kai irin yadda nake nuna mata kafin ya aureni bata san kawai shigo shigo ba zurfi ba ne"

Momi ta ce

"Ai na san kin haifu a cikina gwara ki nuna mata shayi ruwa ne, sannan ki nuna mata tsakanin zuma da maɗaci akwai bambanci, kuma dole ne ki bambanta mata tsakanin aya da tsakuwa banda zubar da girma mai za ta je yi gidan yara a ranar farko ga ƙawayenki nan bata tunanin za a rainata duk son abin ɗanta ya rufe mata idanu""

Meenal ta ce

"Ai da ni take zancen sai na gasa mata aya a hannu in shayar da su ruwan mamaki in bata kauda idonta ba sai na bayar da darasi a kanta yadda uwayen miji za suke barin matan ƴaƴansu su sake da mijinsu, ni ba zan lamunci cin mutunci ba ni babu wanda zan ragawa ko ita matar tasa sai ta san da zamana" Suna cikin haka Meenal daga wutsiyar ido ta hango Hajiya ta leƙo kanta cikin ɗakin, da sauri ta yi sallama ta kashe wayar ta nufi wajen tana faɗin

"Hajiya dama baki tafi ba?" Wata ajiye zuciya da har sai da Meenal ta ji ita Hajiya ta yi a fili kafin ta ƙaraso tana faɗin

"Ƴata Meenal baki karɓi magani ba ina na samu damar tafiya, kuma bakya tunanin ƙawayen can naki su yi aika-aika a store da kika basu mukullin?" Hajiya ya faɗa don jikinta sai yake bata kamar za su yi sata a store ɗin ko su yi almubazzaranci don ta ga ita Meenal ɗin bata ma damu ba da mukullin da ta basu.

Ɗan yatsina fuska ta yj ta ce

"Hajiya bari na miki gwari gwari yadda za ji fahimta, wallahi summa tallahi rass nake babu wani fitar hayyaci idan kuma akwai wani abu da kike so in tabbatar miki ki yarda za ki iya faɗar abin da kike so na faɗa miki, sannan kuma mukullin store ɗin ne sai an bi mutum don an bashi aika-aika a kan abinci sai kamce wasu ɓarayi to ni ko ɓarawo in ya saci abinci gani nake ba sata ba ce tun da idan ya ci ma maganin yunwa ya yi kuma za ka samu ladan sannan ai abinci kashinsa za a yi ba kadara ba ne da za ake alkintawa"

Tsabar mamaki Hajiya kallon Meenal kawai take dakyar ta yi yaƙi da bakinta ya iya furta

"Abincin ne ba kadara ba Meenal baki san mace ana so ta zama mai adana dukiya da komai na miji ba yanzu idan abincin ya salwanta a taron nan na amarcinki sai fa Nasir ya sake fafutukar kawo wani ai a tausayawa miji, sannan da kike batun ɗaukan abinci ba sata bane ai duk abin da mutum zai ɗauka in har ba nashi bane kuma ba a bashi ba sunansa sata k...

Meenal hannu ta ɗagawa Hajiya wanda ya sa ta dakata da maganar cike da mamakin hannun da ta ɗaga mata tamkar wata sa,arta sai kawai ta ji ta ce

"Hajiya ya kamata kisan inda dare ya miji karki manta nan gidan mijina ne ina da damar yin komai, sannan ba huruminki bane da zaki baro naki gidan sabodan zubar da girma ki zo kina bin diddigin abin da yake faruwa a gidan ɗanki sannan shi Nasir ɗin ai tun da kika ga ya yi aure ya shirya tarɓar kowace buƙata dole ta nemo idan babu kuma wallahi summa tallahi babu mai mini shamaki da abinci ko wani abu a gidan mijina, yadda kike taƙama ɗanki ne haka nake taƙamar mijina ne na ma fiki iko da shi yanzu" Furucin Meenal na yanzu ya sa Hajiya ta yi tsai tana lura da yanayin maganar ta a nan ta fahimci cewa tabbas a hayyacinta take babuwwasu alamu na fitar hayyaci a tare da ita kawai tsabar rashin kunya ne da fitsara hakan ya nuna ba ma sai ta ɓata loakci wajen cewa Meenal ta yi wani abu da zai nuna tana hayyacin ta hakan ya sa a zafafe Hajiya ta ce

'Wallahi ƙarya kike Meenal! Babu wanda zai yi iko da Nasir sama da ni"

Meenal ta kalle ta ido cikin ido ta ce

"Kina musu da hakan?" Bata jira amsar Hajiya ba ta ce

"Idan kin musa ki zo ɗakin nan da daddare akwai wata shegiyar rigar bacci da nake da ita da kuma shu,umar humra mai tada kan maza zan saka rigar in shafa humrar zan faɗa wa Nasir ya zauna a wuri ke kuma ki ce ya tashi in zai bi umarninki mu gani!." Wani salati da Hajiya ta kwasa sai da ya so ba Meenal dariya son ta lura Hajiya ta shaƙi takaici kuma abin ya ɗaure mata kai Meenal ta murmusa ta ce

"Ki saka takalmanki ki koma gidanki sannan ki ɗauke idanu a kan lamuran gidan nan idan kina son kanki da girma da arziƙi in ba haka ba wallahi takaici sai ya kusa kasheki" Tana gama faɗar hakan ta fito falo ta bar Hajiya tsaye kamar ta saki ihu tana fitowa falon ƙawayenta suka hau mata kirarin amarya har da masu mata waƙar amarya da Ali Jita ya yi wa amarya. Suna ta abin su Hajiya tana bedroom tsaye da jaka maƙale a hamata ƙullin magani guda biyu a hannu, waiwayawa ta yi ta kalli ɗakin ta ƙare masa kallo sai ta hangi gajeran wandon Nasir da rataye saman ƙofar banɗakin juyowa ta yi ta fito falon ko kallon tarkacen ƙawayen Meenal na falon bata yi ba ta yi waje don zuwa lokacin ma Meenal ɗin ta yi tsakar gidan.

Sadiya tana alwalar azahar a famfo Meenal tana tsaye wajen ƙawayenta da suka ɗakko kayan abincin a store suna nuna mata, suna cewa abincin da yawa tana faɗa musu dama fa ba wai za a kai gidansu ba ne yau kawai ta faɗa ne don ta cusawa Hajiyar haushi. Fitowar Hajiya daga falon Meenal za ta saka takalmi ya yi daidai da shigowar Nasir da ya kinkimo silindar gas yana tafiya a ɗan duƙushe alamar mutum ya ɗaga abu mai nauyi bayansa wasu matasa ne guda uku suna ɗauke da katan ɗin lemo coca cola biyu mirinda ɗaya sai fanta biyu.

Hajiya tsabar yadda ta ruɗe da ganin lemukan da ya siyo ga gas tana tunanin kenan dai maganar Meenal ta zama zanen dutse sai da ya aikata, a ƙwaƙalwarta tana ƙiyasin kimanin nawa aka kashe a hakan ta saka takalminta ɗaya nata ɗaya kuma na wata daga cikin ƙawayen amarya sannan kowanne ba ƙafarsa ba ce.

Kiran sunan Nasir take Sadiya da ta gama alwala dariya tana neman ƙwace mata da ta ga ƙafar Hajiya ta yi saka takalmi kamar ƙafar ƙananan yara sannan takalman daban-daban ne uwa uba yadda ta tikce tana kiran Nasir.

Nasir faɗi yake

"Ina zuwa Hajiya" Ya yi hanyar kicin ya daidaita musu silindar a jikin gas ɗin, tsakar gidan kuma samarin nan suna tambayar inda za su ajiye lemukan Meenal ta yi karaf ta ce

"Ku kai ƙofar wancan ɗakin" Ta faɗa tana musu nuni da ɓangarenta sannan ta hau ƙwalawa wasu daga cikin ƙawayenta ta ce su karɓa su saka a frige har tana musu tsiya wai sun zauna a ɗaki ba za su fito su yi aikin abincin ba. Suna faɗin sai sun ci wani abu hakan ne ya ankarar da saƙon su da Nasir ya bari a mota.

Yana zuwa gaban Hajiya ya sassauta murya ya ce

"Hajiya kin ga ƙafarki kuwa?" Hajiya wacce duk takaici ya ishe ta ta san Nasir da izza da nuna isa a kan Sadiya amma yau ta ga ya zama kamar wani sauna sai abin da aka ce masa. Sadiyar da ko kuɗin magani ba a bata idan bata da lafiya haka ma idan Kalifan bashi da lafiya suna idon a bata kuɗi duk ƙanƙantarsa sai gashi wata ta zo rana tsaka za ta kawo wargi a lamarin aljihun Nasir ɗin duba da yadda ya siyo komai da aka faɗa babu musu.

Tana ganin yadda ta yi masanyan yakalmi kuma ba ƙafafun bane sai ta juya da sauri don kar a lura bata san Sadiya ta gani ba hatta Meenal ma ta gani kawai dai ta ce a zuciyarta

'Kaɗan kika gani wallahi mu zuba mu gani' Nasir kuma kafin Hajiya ta ɗakko takalmin ya juya ya fita matasan yaran nan suna biye da shi da suka fita ya basu ɗari biyu su raba, bayan motar ya buɗe ya ɗakko manyan ledojin da aka yi take away na snacks da drinks masu sanyi haka ya shigo gidan da ledojin riƙi-,riƙi.

Meenal ganin Sadiya ta baro wajen famfo sai ta aikawa Sadiya harara kuma Sadiyar ta gani amma ta yi kamar bata gani ba Meenal kuma a zuciyarta ta ce

'Ina nan zuwa kanki kema'

Hajiya kuma tana sako takalmi ta ga babu Nasir kafin ta gama tambayar kanta ina yake sai gashi ya shigo da ledojin wannan Meenal ta nufi inda yake ta tare shi tana aika masa sannu, haɗe da miƙa hannu ta maƙalo bayansa suke tafiya inda shi kuma yake ta kaucewa alamar kunyar Hajiya amma Meenal ta ƙi sakin sa har da saka ɗaya hannunta ta sumbaci hannun nata ta kai masa saman nasa bakin. Hajiya kallo ɗaya ta musu ranta ya ɓaci ga ƴanmatan nan su Safiyya a kicin sai ƙaran kwanuka take ji alamar hada-hadar girki waau suna yayyakan kabeji so take ta ce masa ya yi taka-tsan tsan da mukullinsa sannan ya matse hannu da aljihu amma kuma ta kasa tsayawa saboda yadda Meenal ta ƙaƙabe masa.

Hanyar waje ta yi tana faɗin

"Nasir ka zo waje ina son ganinka" Sadiya da tun da ta koma ɗaki ta laɓe a labule tana kallon dirama, komawa kan kujera ta yi ta kwanta tana ta dariya Kalifa yana taya ta duk da bai san dariyar mene ne take yi ba.

Meenal tana ganin Hajiya ta fita ra sake shi, ta karɓi kayan sai kuma ya juya ya fita don amsa kiran Hajiya, ko da ya zo ƙofar gidan ya same ta tsaye tana riƙe da ƙugu ga kuma jaka a rataye sai kai komo take bata ma san ya zo wajen ba sai da ya kira sunanta da sauri ta waigo tana faɗin

"Nasir mu shiga cikin mota maganar nan ba ƙarama ba ce akwai gagarumar matsala don da alama abubuwa sabbi za su kunno cikin rayuwarmu da muke lallaɓawa" Ta faɗa bata jira cewarsa ba ta buɗe gaban motar ta shige cike da rashin fahimta ya shiga mazaunin direba tun bai gama zama ba ta shiga faɗin ya rufe ƙofa rufewa ya yi sai kuma ta ce

"Nasir akwai matsala wallahi" Cike da faɗuwar gaba ya ce

"Allah ka mana maganin matsala, Hajiya matsalar mene ne?" Idanunta da suka kaɗa suka yi jawur saboda ɓacin ran abubuwan bazatan da ta ƙunsa daga Meenal ta ce

"Nasir Meenal ce matsala" Cike da rashin fahimta ya ce

"Meenal kuma?"

Hajiya a faɗa ce ta ce

"Meenal mana bari na faɗa maka abin da baka sani ba tana cikin hayyacinta babu wani jifanta da aka yi ta tabbatar min da hakan da bakinta da alama yarinyar nan zaɓen tumun dare muka yi Nasir wallahi bata da ƙudurin sa ya wuce ta rusa mu ta faraƙa mana dangi, ka ga kai kaɗai ne gatanmu ni da marayun Allahn nan su Husna yanzu wannan yadda daga juya zuwa yau take saka ka ɓarin kuɗi kuma Nasir ko musu baka yi duk abin da ta lissafa sai ka siyo sannan uwa uba ka ɗauki mukullin store ka bata" Ɗan dimmm ya yi sai kuma kafin ya ce wani abu ta ce

"Wallahi so take ta mallake ka ka fi ƙarfina ta mamaye gidan nan don haka dole ka tashi tsaye ka zama namiji ka matse bakin aljihu ka ƙwace mukullin store karka sake bata ita ma kake tsakura mata abincin kamar yadda kake tsakurawa Sadiya wallahi da ni take zancen dankalin ma an fasa aiko mata can za kake zuwa kana ci kamar yadda ake yi wa Sadiya kuma a gobe ba sai jibi ba Meenal za ta fara ɗora tukunyar tuwo, kuma gawayi za take hurawa wannan gas ɗin dole a kai min gidana ko ka je ka aiyar da shi amma ba a gidan ɗana ba" Tun da ta fara maganar yake kallonta ya mayar da hankali kanta yana sauraro da nazarin ta inda zai fara wannan gagarumin faɗan da take son kwasowa don ya lura Meenal ba kanwar lasa bace kuma ba za ta lamunci wannan abubuwan da aka zana ba kenan da sauran rina a kaba.

Baki ya buɗe zai yi magana sai dai ƙaran ƙwanƙwasa ƙofa da aka yi shi ya dakatar da shi daga furta komai, daga shi har Hajiya suka juyo don ganin mai bugawa sai dai wanda suka gani tsaye ya basu mamaki ba kowa ba ne illa Meenal da take tsaye riƙe da tsantsa hannunta ɗaya riƙe da wani ƙaton kwando, ganin sun maido da kallonsu kanta ta saka hannu ta buɗe ɓangaren da Hajiya take haɗe rai ta yi ta ce

"Na gama jin duk abin da kuka ce dama tun da na ga kin ce ku je wajw kuma na san halinki shi ya sa ban yi ƙasa a gwiwa ba na biyo bayanku na laɓe a zaure ina kallonku ta jikin tular ƙofa, kuna shigewa na zo jikin ƙofar na tsaya amma kasancewar hankalinku ba ya wajena babu wanda ya ganni har na koma na ɗakko kwando na dawo, don haka abin da nake so da ke Hajiya ki dakata da wannan faɗan don wallahi ba za ki iya ba, kuma ba za ki ci gabala ba kawai ki sakar mini" Hajiya baki sake take kallon Nasir ganin bai yi kataɓus ba wajen tsawatarwa Meenal a zafafe ta ce

"Nasir ya ka tsaya kamar sauna kana jin abin da ta ce?" Kafin Nasir ya ce wani abu Meenal ta ce

"Ina shawartarki Hajiya da ki cire ido da hannunki a gidan ɗanki shi ne kima da mutuncinki don wallahi ko ana mutuwa ana falkowa ba zan taɓa ɗora girki a gawayi ba, sannan mukullin store daga yau ya bar hannun Nasir in kin ga ya taɓa mukullin store to tabbas kayan abinci ya siyo za a saka a ciki, abu na gaba ba uwar miji yanzu babu ruwanki da aljihun ɗanki a kan lamarin gidansa tun da matar mutum ita take ɗauke ɗawainiyarsa ta cikin dare don haka ta cancanci a mata komai shin in ba matarsa ba waye zai ɗauke masa wannan ɗawainiyar? Don haka ni nake kwana da miji kuma ni zan yi iko da abina ba wai a mini iko da shi ba ikonki ya tsaya iya ke da shi...

Hajiya ta hankaɗa ƙofar ta sako ƙafa waje tana nuna Meenal da yatsa ta ce

"Wallahi ƙaryar rashin kunya kike da a ce na san haka kike da Nasir bai aure ki ba"

Meenal ta ce

"Daga baya kenan wai an yi sadaka da karuwa, to ai duk ɗaya an ce da karuwa hayo gado yanzu ma lokaci bai ƙurw miki ba za ki iya saka ya warware igiyar" Nasir da ya buɗe baki zai yi magana sai ya ji kansa ya sara hakan ta sa ya zuba musu na mujiya, domin cikin maganin da ta saka da dare har da mallaka ciki.

Hajiya ta ce

"Daga na gidan uwarki zan je, in mata bayanin yadda kika sauya halinki a kwana ɗaya, ai ni ƙawar uwarki ce ko wannan kaɗai kya duba"

Meenak ta ce

"Ai in dai tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ke baki duba dangantakar ba kike mini taka haye?"

Tsaki kawai Hajiya ta yi don ta hango yadda za ta magance wannan matsalar

Meenal kuma ta rausayar da kai tare da zumɓura baki tana wani shagwaɓe fuska cikin muryar ɓaci ta ce

"Zumana wannan kwandon gidan Hajiya za ka kaini zan kwaso dankali, su Safiyya suna son sakawa a miya ƙwan ma za su yi amfani da shi, ka ga sai a kwaso kayan duka in ya so gobe in za a yi break fast ɗin sai su Husna su zo su yi in ɗauka musu na Hajiya ka ga ni ba zan iya aiki ba jikina ciwo yake" Ta faɗa tana yin farrr da idanu, Hajiya tsabar mamaki na ganin Meenal ko kunyarta bata ji ya sa ta kasa magana, da sauri ta juya don ta ga abin da Nasir ya yi kawai sai ta ga ya saki baki yana murmusawa.

Kafin ta ce wani abu Meenal ta ce

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull