Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 53

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 53

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 53: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 53. Tunanin tsakaninsu da Jidda ta yi komai zai rushe…

585 words

Tunanin tsakaninsu da Jidda ta yi komai zai rushe shikann Jidda za ta zama ta san cewa su ba masu ƙaunarta ba ne tun da har ga shi za ta zo har cikin gidanta a lokacin da ba ta nan don kawai ta cim ma manufarta, ta san shikann kuma Jidda ba za ta sake yarda da su ba, ƴar soyayyar ƙaryar da suke nuna mata za ta daina yarda da ita ba ma lallai ta sake sakin jiki da su ba bare har su zo inda take su cika ƙidirinsu da mafufarsu a kanta!.

Ibrahim handle ɗjn ƙofar ya kama ya buɗe ƙofar Aliya da take bayan ƙofar gabanta yana dukan lugude ta yi tsuru tsuru. Shi kuma ko ɗakin ma bai kalla ba ya dai buɗe ɗakin ne hankalinsa ma ba a wajen yake ba don ya waiwaya bayansa ne, ko mai ya tuna sai ya ja ƙofar ya rufe a juya tare da buɗe ɗaya ɗakin ya shiga. Aliya komawa ta yi ta jingina da bango tana sauke ajiyar zuciya a fili har lokacin ƙirjinta yana tsananta bugu kamar zuciyarta za ta fito.

Yana shiga ɗakin ya kwashe kofin da ya fashe ya zuba a kwandon sharar da yake cikin ɗakin daga can gefe wanda babu komai a ciki sai tissue. Saurin saka kayansa ya yi yana son tafiya airport ɗakko su Jidda. Yana ɗaura agogonsa ya tsiyaya maltinar a kofin da ya sake ɗakkowa da ya sauka ƙasa. Kai ya kafa ya sha ya ajiye tare da miƙa hannu zai ɗakko wayarsa da ta ɗauki ruri yana dubawa ya ga Mummy ce hakan yana bashi tabbacin sun dira. Sai dai kafin ya ɗauka mararsa ta murɗa masa da wani irin ƙarfi, fuska ya yatsina yana kai hannunsa ya dafe mararsa a take ya ji komai ya sauya wata irin buƙata ce da bai taɓa ji ba ta mamaye ilahirjn jikinsa ji yake idan ya ƙara wasu mintuna bai samu biyan buƙatarsa ba tamkar numfashin sa zai bar jikinsa gabaɗaya idanunsa sun rufe mafita yake nema ta ko ina.

Aliya da ta gama kallon abin da yake faruwa ta ƙaramar tular jikin ƙofar hannu ta saka domin buɗe ƙofar ɗakin da yake ciki, ɗankwalin da yake jikinta ko mazaunai bai rufe mata ba. Tana shiga dama ya ba ta baya sakin ɗankwalin jikinta ta yi ya faɗi ƙasa kafin ta fara taku ta nufe shi tana wani malmalƙwashewa kamar macijiya!.

A can ƙofar gida su Jidda ne da Mummy, jidda da Mummy a baya sai Daddy wanda yake gaba direba yana tuƙawa. Sun yi ta kiran wayar Ibrahim bai ɗauka ba kuma shiru bai zo ba, hakan ya sa Daddy ya kira direba ya je ya ɗakko su. Mai gadi ya wangale musu get suka shigo Jidda ta fito daga motar Mummy tana cewa ta gaishe shi wataƙila bacci ya yi. Ga magriba ta gabato. Mai gadi yana ta mata sannu ta amsa lokacin su Mummy motar su ta har ba zuwa titi. Riƙe da akwatin ta ta tura ƙofar ta shiga tare da mayarwa ta rufe tana tunanin abin da ya hana Ibrahim zuwa ɗakko su bayan ta san ya san lokacin da jirginsu zai sauka.

*Ni ma dai maman afrah a nan na dasa aya, don gabaɗaya turka-turkar ɓangarorin nan uku ta sha min kai, domin samun cigaban labarin bar ƙarshe 500 ne shiga group za a biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay, sai a tura min shaidar biya ta lambata 09025576222 idan na kammala littafin complete docment 800*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull