Kenza eBookz

Sakon so complete Novel - Chapter 16

Sakon so complete Novel - Chapter 16

Sakon so complete Novel Chapter 16: Sakon so complete Novel Chapter 16. Hajiya kadaine a falo da Maman Aneesarh ahankali tace “ina yinin ku” murmushi…

2,729 words

Hajiya kadaine a falo da Maman Aneesarh ahankali tace “ina yinin ku” murmushi Hajiya tayi tace “sannu da zuwa” Aneesarh data gani taduka tadauka tana murmushi tace “zomuje dakina” murmushi Mamanta tayi tace “wanan saita batamiki daki wlh da barna” murmushi tayi tace “dan Allah kibarni natafi da ita Allah ina sonta” Maman Aneesarh tace “shikenan kuje” wucewa sukayi sama Abee yashigo shima gaida Hajiya yayi, Hajiya tace “sannu da zuwa Imrana” ahankali Maman Aneesarh tace “sannu da zuwa Yaya” Gyadamata kai yayi yawuce sama, Maman Aneesarh takalli Hajiya tace “Hajiya Ya Imrana is so nice towards this girl” Hajiya tace “Imrana has always being nice to kowa, banbancin Babba mai hankali kenan da kananun yara samari, Lujain is just like Kausar kozai wulakantata bazai iyaba dan kaman diyar cikinshi ne bazai iya imagining wani ya wulakanta mai Kausar ba, nasan Imran dina dudda bayason Auren nan bazai taba cutar da ita kokuma yaga abin cutarwa yabari ya cutarda ita ba” Maman Aneesa tace “saisa yasata a makaranta mai tsada ko su Kausar ba makarantan turawan nan sukayi ba” Hajiya tace “inba irin makarantan nan ba awanne za’a sata yarinyar da fuskanta ya zagaye yanar gizo so kike kullum adinga dukanta ta tsani makaranta gabaki daya taki fita” ahankali Maman Aneesarh tace “Hajiya ni tausayi yarinyar ke bani koda zamuso zamansu da Ya Imran tayaya zata fara kula da Ya Imran? Babu abinda ta iya wannan saidai shi yakula da ita ai” Hajiya tace “daga next week duk idan tadawo daga makaranta zan dinga sata tana shigowa kitchen kuna koyamata abu daya biyu haka harta kware” kallonta Maman Aneesarh tayi tace “Mama kinason auren su ne?” Hararanta Hajiya tayi tace “kin isheni da tambaya amman abu daya zan fadamiki babu Babba dazai cemiki yanason mutuwan aure duk Auren da aka daura fatanmu shine yadaure har abada, idan zamansu tare Alkhairi ne Allah yahada kansu kullum shine addu’a na”. ***

Olusay ke tuki suka shigo estate din, horn yayi gaban gidan gateman yabude musu suka shiga ciki Olusay yace “wow gidan yay kyau wlh Man” yadan kalleshi ganin yana cikin IG, karasa parking yayi ganin Mandawari baima saniba yasa gently yakai hannunshi yadaura akan shoulder nashi hakan yasa dasauri Mandawari yakalleshi yace “ohh harmun shigo”? Olusay yace “kanachan kana kallon hoton stalker naka yaza’ayi kasani” kallonshi Mandawari yayi, ahankali Olusay yace “can I talk to you Man I am serious”? Dan yatsine fuska yayi yana cire sitbelt yace “what”? Dan jim Olusay yayi dan baisan how he’s going to take the magana ba ahankali yace “first of all Muhammad I don’t know your reason na sayan gida right next to gidan da stalker dinka ke aure, nabiyu you saw everything mezakayi da matan aure yarinyar data Riga tayi aure? Thirdly kasan your Mom bazata taba bari ka auri yarinyar that went viral online hakaba, and nahudu kariga kayi loosing chance dinka da bakin wulakanci for the past how many years yarinyar nan namaka magana wulakancinka yahanaka kulata sai yanzu bayan an mata aure ne zaka fara sonta what’s all this Man? Mezakayi da wannan yarinyan kanada thousands of mata har yan film dake sonka sai wannan da aka mata unfortunate Marraige din nan zaka wani fara so” shiru Mandawari yayi saikuma chan yace “you want an honest answer?” Gyadamai kai Olusay yayi ahankali yace “I buy this house triple amount na gidan nan because of the girl dan wasu harsun sayi gidan nakara kudade, sannan kai kanka you just call the marriage unfortunate one kawai anyishine dan ayi blocking mutane from saying shit akan honest mistake datayi well koma Iskancin tayi da mutumin I know he must be the one to force her dan that girl love only me, and again what made you think Mom harta isa tagayamin ga wanda zan aura ga wanda bazan aura ba bayan ita taje tayi aurenta da Dad dina yarasu? She have no right over me, lastly kowa yarinyan nan ta aura I don’t bloody care she belongs to me! Just me, watch and see how I win my girl and shape her to abinda nakeso that fat everything she will loose it, idanma takasa dakaina zan kaita amata tummy tuck” dan murmushi yayi yace “how is my welcoming party going”? Tabe baki Olusay yayi yace “I know how stubborn you are just be careful, mijin yarinyan nan is not our mate that’s number one tsoho ne, nabiyu kuma he’s a soldier, a retired old soja” dan dariya Mandawari yayi yace “that’s more of the reason why I want to save her, mezatayi da tsoho dakeda yaran dasuka girmeta? She’s to young and fresh for him, bata sonshi ni kadai takeso, just sit back and watch how I open her eyes and show her the world” “hmmmm” Olusay yace da mamaki yabude mota yafito shima Mandawari yafito Olusay yace “ni bantaba ganin mutum irinka ba yarinyar dabaka nuna mata so bamaka kulata” dan tsaki yayi yace “leave me alone please, kaji da kanka” taba yaciro yakunna yanasha Olusay yawuce ciki abinshi, saida yagama sha ya yarda karan ya shiga ciki.EPISODE 2️⃣8️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram; https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Wuraren magrib tabude kofanta tafito tana daure dawani pink towel a kirji rikeda Aneesarh datai bacci Kausar tagani dazata shiga dakinsu dasauri tace “inane dakinsu Aneesarh”? Kallonta Kausar tayi saikuma tamata pointing dakinsu Aneesa wucewa tayi tashiga Maman Aneesarh naciki tace “laaa tayi bacci” gyadamata kai tayi tana kallon wayan Maman Aneesarh dake kan gado, karban Aneesarh tayi ta kwantar da ita sannan ta tashi takalli Lujain dake kallon wayan tace “Ya akayi Lujain”? Ahankali tace “dan Allah na ari wayanki nakira Gwaggo na”? Dan murmushi tayi tace “to dauka kije ki kirata” wani kalan tsalle tayi cikeda farinciki tace “nagode Mom Aneesarh” daukan wayan tayi da gudu tafita tana saka number Gwaggo data haddace aciki tai dialing tabude kofan dakinta tashiga daidai wayan na ringing Gwaggo tadauka cikeda ihu yanda take waya tace “hello” dan murmushi Lujain tayi dayasa hawaye yataru akan idanunta murya chan kasa tace “Gwaggo” cikeda ihu Gwaggo tace “jama’a muryan Lulu nakeji”? Gyadamata kai Lujain tayi kaman jira take tawani kalan fashe da kuka itama Gwaggo fashewa tayi da kuka tace “wlh inda badan Babanki nina haifeshi ba da tuni na tsine mishi, tun Washegarin ranan da aka kaiki gidan miji naji ina baran iya rayuwa bakiba, ranan kasa bacci nayi nayi nayi da Babanki yakawoni gidanki yaki da asussuba kafin natashi yake fita baya kara dawowa sai dare bayan nai bacci, keto ya isa daina kukan hakanan kinji” gyadama Gwaggo kai tayi ahankali, murya chan kasa tace “Gwaggo dan Allah kizo kitafi dani gida” Gwaggo tace “namiki alkawari ko ana ha maza ha mata sainazo kafin satin nan yakare nadubaki kinji daina kukan kinashan maganin dana daddaka miki nasa miki a akwati”? Turobaki tayi ashagwabe tace “ni baram sha…..” daidai lokacin aka bude kofan dakin Abee ne yana tsaye sanye da kananun kaya riga da jean sun mishi wani kalan kyau sai kamshi yake ganinshi yasa dasauri tace “Gwaggo bye bye” takatse wayan dasauri tana zaro idanu, wani kalan kallo yamata tareda mikamata hannu alamun tabashi wayan, tashi tayi ahankali tazohar gabanshi sannan tabashi wayan yajuya yafita.

Koda akai magrib Abee zamanshi yayi a masallacin danjin ta’aleem da akeyi kan zamanta kewa da hakkoki mutane, saida aka gama tass malam yabada daman tambaya daga baya wani yadaga hannu hakan yasa Malam yace “yi tambayanka” dan sosa gemunshi yayi sannan yakalli Malam yace “Malam ni sonake nasan hukuncin tsofaffin dake auremana yammatan mu” duka jama’an masallacin juyowa sukayi suna kallonshi yahade rai banda Abee dake duba littafin hannunshi, Malam dake kallonshi yace “ban gane tambayanka ba yan samari” dan yatsine fuska Mandawari yayi yace “yanzu saikaga tsofaffi misali irinku malam na auren mata dakun haifesu kusan sau biyar mukuma yara mekukeso mu aura me atambayata dabaka ganeba”? Sai alokacin Abee yadago kanshi dan tambayan sounds so disrespectful to Malam dan Malam ba karamin mutum bane, shima Mandawari kyar idanunshi akan Abee, yanda yake kallon Abee yasa Abee ya gyara idanunshi akanshi, gyaran murya da Malam yayi a speaker yasa Mandawari ya janye idanunshi dagakan Abee dake kallonshi kyar yakalli Malam, Malam yace “shidai aure na farko Halas ne yan samari, dudda dai bansan mesa kayi irin wannan tambayan ba dan ba darasin mukeba amman dai abinda nasani shine wacce baraka iya aura ba aduniyan nan shine wacce take muharamman ka, idan kuma ana maganan Auren yara ne annabin mu Annabin Tsira Muhammad tsarki yatabba agareshi ya auri Yar yarinya Aisha kuma mu koyi mukedashi, jama’a atashi sahu” tashi sukayi akai salla ana idarwa Abee yafito dan yanada business meeting dazaiyi a zoom by 9, harya zo zaishige gida yaji ance “Yallabai” chak Abee ya tsaya saikuma yajuyo ahankali, Mandawari ne yataho tareda Olusay dayay hanyar gate nasu, jallabiya ce ajikinshi yakaraso gaban Abee hannu yamikamai yace “kasanni”? Wani kalan kallo Abee yamai tsaf yaganeshi from the first glance dayamai a mosque, hannu Abee yakawo zai bashi kaman jira Mandawari yake with so much disrespect and humiliation yajanye hannunshi yarugume hannunshi a kirji, hannunshi Abee yakalla daya kaimai su gaisa dake nan acikin thing air ahankali yaja hannunshi ya maida jikinshi yazubama Mandawari idanu, baisan mesaba jiyayi gabanshi yafadi amman daurewa yayi with so much courage yace “you took something that belongs to me Mr Imran, kuma na tabbata fada da kananun yara irinmu dazaka iya yara damu is not ur thing dan haka I come to tell you in peace ka saki babe dina daka daura lokacin da abin nan yasameku I wasn’t in Nigeria yanzu nadawo I want my woman back I want to marry her” wani kalan kallo Abee yamai saikuma yay folding hannunshi akirji yana kallonshi, Mandawari yace “yanzu ma nasameka ne namaka magana out of respect inba hakaba” anatse Abee yace “mezakayi”? Kallonshi Mandawari yayi yace “I will defame you! I will scatter everything you’ve ever stood for” dan murmushi Abee yayi iya lips nashi sannan yajuya yawuce anatse wani abu Mandawari yaji ya tsayamai awuya kaman yabishi ya chakamai wuka sai yanzu daya tsaya gaban Abee face to face kawai yaji yawani tsaneshi wani kalan mugun kishi nacinshi dan ko kadan mutumin doesn’t look old gashi he’s so handsome gashi so neat kayan dayake jikinshi tundaga kan slippers na kafanshi are designers, kamshin dayake koshi dayake takama yafi kowa using turare baikai Abee kamshi ba, wani kalan dunkule hannu yayi yadaki iska sannan yajuya yawuce gida, akan benci mai gadi yasami Olusay zaune Olusay na ganinshi yamike tsaye yace “Man nasanka to be stubborn tun muna yara, but idan kasan kazo anguwan nan ne to make trouble ni zan tattara nabarmaka gidanka, this man baida any business to do with you and yet you want to make trouble dashi akan mene ubanme yamaka eh” cikeda ihu Mandawari na tafarfasa yace “he stole my woman from me abinda Yamin kenan” cikin sauri Olusay yace “woman din dabaka taba cema kanaso ba or respond to her messages, this is not good Man, trust me this is not good at all” hannu Olusay yakai zai tabashi wani kalan bugemai hannu yayi yawuce ciki yana tafarfasa tsayawa Olusay yayi so worried Kodai yakira Mom yafada mata abinda ke faruwa ne amman yay haka Man will never forgive him, shi yasan Man always view her message dan shinema yafadamai about Lujain amman baitaba fadamai yana sonta ba saima wulakanci dakin kula yarinyar, saida wannan sex tape da news na aurenta ya yada social media shine fa tundaga ranan Mandawari yafara having sleepless night. ***

Falonsu yashiga da sallama chan kasa Musty yagani da Harun sunacin tuwo, Hajiya kadai yagaida yamusu mugun kallo yawuce sama, Hajiya tace “kudai kuna kokari da wannan abokin naku” tashi Musty yayi yace “cigaba daci Harun bari najawoshi ya sauko kasa” daidai Abee na zama gaban desk nashi Musty nashigowa ciki yace “waikai tunda kayi auren nan nakasa gane kanka” wani mugun kallo Abee yamai yace “I told you Musty, kasanni Musty banson aure let’s not even go there idan wata ne maybe I can even manage Auren na zauna not Auren little girl like this da dan karamin yaron saurayinta zai tareni this night yana threatening dina, what is all this rubbish what kind of mess kuka sani ciki haaa? At this stage some stupid small boy da aka haifa jiya jiya zaizo yatareni yanamin maganan banza can you imagine”? Yanda Abee ke magana zakasan he’s really pissed hakan yasa Musty yace “wait Imran I don’t understand me kake cewa? Waya tareka wani boyfriend kake magana”? Cikin dan ihu kadan Abee yace “her boyfriend dashine the reason behind abinda yasa taje toilet na maza mana taxauna tana kallon live video nashi Muhammad Mandawari” shiru Musty yayi yana kallon Abee dan shi dama dayashigo anguwan dazu Hamza ke fadamai sunyi neighbor wani footballer baima tsaya jin waye ba sabida Hajiya daketa kwalamai kira, one thing da Abee ya tsana to the core arayuwanshi is raini ya tsani raini da rashin kunya, dafe kanshi yayi saikuma yadago yace “how far about the tracking dasu Abdul keyi idan bazamu iyaba zan turama contact dina number a USA cus I can’t wait for all of this shit to be over narabu da yarinyar nan data shigo rayuwana tahanani kwanciyan hankali I am tired Musty I am tireddd” yay maganan yana kabar da keys na motanshi da wayanshi dake kan desk din kasa, dasauri Musty yazo yadafashi trying to calm him down yace “calm down Imran, fushinka is not good for you and kowa dake tareda kai, calm down please” dan ajiyan zuciya Abee yasauke ahankali Musty yace “what happen tell me” kaman Abee bazaiyi magana ba saikuma yafadamai komi shima Musty baci ranshi yayi yace “I don’t care koshi waye what gave him the gut dazai tare soja yanamai magana anyhow, lemme go and lock him up wlh sainai uselessing kafafuwan nan nashi na kwallo ” Musty yazo zai wuce dasauri Abee yarikeshi yace “common mu yarane dazamu biye musu, he’s just a child let him be please, is not easy karasa abinda kake so cikin dare daya to some extend I understand how bittered he’s” dasauri Musty yace “her grandmother told me baitaba kulata ba all this childish crush Lujain kemai” yatsine fuska Abee yayi yace “that’s non of my business, I’ve taken care of her, nasata a school da babu wanda zai bully nata, nayi securing waec nata and neco I am just waiting waiting for the whole thing to be over nagaji” yay maganan ahankali, murmushi Musty yamai yace “ya isa tashi muje falo muci tuwo tare” yatsine fuska Abee yayi yace “baran ci ba” Musty yace “Allah saikaci” badan yasoba yatashi yabishi suka fita falo tare, sai wajajen 11 sukabar gidan hakan yasa yarufe ko’ina yawuce sama ko dakin da Lujain keciki bai kalla ba.EPISODE 2️⃣9️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram; https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Around 1 tafarka daga bacci sabida mugun yunwan datakeji rabonta dacin abinci tun lunch dataci a school shima ba sosai ba taci, yanda Mandawari yagaya mata tacika kiba taje tarage kiba kafin takulashi yadameta tayi alkawarin zata rage kiba, barata dingacin abinci sosai ba, kulolin abincin da aka kawomata jiya da daddare takalla amman taki zuwa wajen, kife cikinta tayi ahankali tanajin yanda cikin ke sokanta amman tadaure tana lumshe idanu, ganin yaki denawa yasa ta tashi tadauki bottle water tabude tasha sosai sannan takara kwanciya tana shafa cikinta da hannunta dake cizonta cikin wani kalan murya tace “wayyooo cikina wauyooo” juyi kawai take akan gado sai wajajen 3:00 bacci yay awon gaba da ita, 4:30 Abee yafito, tada kowa yayi saida yatada Kausar yace “jeki tashi yarinyar nan” gyadamai kai Kausar tayi tawuce tafita shima Abee yafita yasauka kasa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull