Sakon so complete Novel - Chapter 20
Sakon so complete Novel Chapter 20: Sakon so complete Novel Chapter 20. Vibration yatadata a bacci datakeji kaman a kunnenta bude idanunta tayi ahankali…
3,296 words
Vibration yatadata a bacci datakeji kaman a kunnenta bude idanunta tayi ahankali tana dube dube saikuma chan ta hango waya akarkashin gado nakawo haske yana vibration hannu Gwaggo tasa tace “waya manta da wayanshi adakin nan gashi sai kira ake” tashi tayi tafice rikeda wayan dake vibrating bude kofa tayi daidai Abee da dawowanshi kenan daga sallan la’asar a masallaci yahayo saman ganin Gwaggo yasa ya sunnar da kai kasa ahankali yace “ina yini Gwaggo” murmushi Gwaggo tamai itadai bakaramin kima da mutuncin shi take ganiba tace “kaga Imrana bansan ko Binta ko Kausar bane sukabar wayansu ba bacci fa nake naji giririrriii natashi shine naga waya akarkashin gado anata kira itakuma tana bacci balle nabata takawo musu gashi katayani basu bari naje nai salla tunda wayan yatadani” ahankali Abee yakarbi wayan daidai number da akai saving da Mandawari na kira Gwaggo kuma tajuya takoma daki tareda maida kofa tarufe Abee yadade yana kallon wayan harta katse daidai nan kuma yaga hoton Mandawari ajikin screensaver, yakai kusan 2min yana tsaye awajen kallon wayan yake yaji zuciyanshi nawani kalan tafarfasa dayarasa dalilli kafin ahankali yafara tafiya yawuce dakinshi, Binta IPhone 14 take amfani dashi, kannenshi da yaranahi dukan su 13 pro max garesu har Kausar Wanan ne kawai 12 agidan nan, yana shiga dakinshi ijiye wayan yayi kan desk yawuce yafada bayi.
Wuraren 5 tafarka ita kadaine adakin amman tana iyajin muryan Gwaggo anan falon sama tana zuba sai waka takema jikokin gidan su Aneesarh, gently ta tashi zaune tanajin ciwon cikin nadawo mata sabo fresh, sauka tayi dagakan gadon ahankali tawuce bayi wanka tayi da ruwa mai zafi sosai tafito daure da towel shiryawa tayi tsaf tadauki wani simple gown mai spaghetti hand anytime take period she don’t use to feel comfortable at all takurama rayuwanta yake ba kadan ba dan batason saka pant naturally, kuma batason zama da kaya, feffesa turaruka tayi tana kallon kulolin abincin dake dakin amman bakinta baya mata dadi daga kanta tayi tabi dakin da kallo idanunta ne suka sauka kan agogo 15min after 5, wani kalan zaro idanu tayi tamike tsaye dasauri tai wajen gado taleka zata ciro wayan da dazu tacire daga jaka ta tura karkashin gado amman bata gani ba, tashi tayi dasauri taje ta dayan side din gadon tana leka karkashin gadon amman bata ganiba jin anbudo kofa yasa dasauri ta dago Gwaggo ne, zaro idanu Gwaggo tayi tace “ke ciwon cikin keneman sakaki shigewa karkashin gado, zokisha magani mijinki yasayo miki kici abinci” shigowa Anty Binta tayi tace “sannu Lujain kinji Zokisha magani” girgixakai Lujain tayi tafashe da kuka tace “ni naji sauki basainasha magani ba” Gwaggo tace “hakafa take sainai da gaske yarinyar nan keshan magani, ballo maganin kigani Binta” ballo magungunan Anty Binta tayi guda hudu ne tana gani Lujain tawani kalan fashewa da kuka mikewa tsaye tayi dawani kalan gudu tabude kofan tafita daidai Abee dake waya yazo zai wuce wani kalan fadawa jikinshi tayi one two three Abee yay tangal tangal, baya Abee yayi kaman zai fadi saikuma yay sauri yay standing on his feet waya na kunnenshi still yabita da kallo yanda ta rirrikeshi ta kulle idanunta gam danta dauka fadi zatayi ana hello hello awayan da Abee yake yakasa cewa komi hakan yasa gently tadago kanta jin hello da akeyi hada idanu sukai da Abee dake mata wani mugun kallo dawani kalan sauri tafita daga jikinshi takoma baya, Anty Binta da Gwaggo dasuka fito dasauri Gwaggo tace “yauwa Imrana kaga magani take guduwan mawa haka hartanacin karo dakai gashi mugun ciwon ciki take” kallon Anty Binta dake rikeda maganin da ruwa a hannunta yayi babu alamun wasa a muryanshi yace “bata tasha” mikamata Anty Binta tayi tace “gashi” karba tayi ahankali tana wani kalan shagwababben kuka daga Abee har Gwaggo da Anty Binta kallonta suke, Anty Binta sai murmushi take dan gown din datasaka yamata wani kalan kyau shape nata yafito sosai, ruwa tasaka abaki sanan tadau daya zata saka Abee yace “drink all” gyadamai kai tayi ahankali takara sautin kukan datake Gwagho tace “aisai kiyi nagode ma Allah da yanzu inada maganin ki” watsa maganin tayi abakinta tana yunkurin amai Abee yace “don’t you dare” hadiyewa tayi tana batarai tawuce tashige dakin dasauri Abee yawuce yasauka kasa abinshi, abinci taci badawani yawaba dan bakinta badadi gabanta sai faduwa yake tarasa ta yanda zata tambayi Gwaggo wayan haka taja bakinta tayi shiru tun cikin namata ciwo harya daina.Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram; https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
EPISODE 3️⃣7️⃣
Bayan salla isha’i ta tashi daga kan gado tanajin dariyan Gwaggo dan turobaki tayi tarasa ganekan wajenta Gwaggo tazo ko wajen yan gidan nan tana gama bata tea yanzun nan takara fita, wanka tawuce tashiga tadade abayin tafito shiryawa tayi tsaf bayan ta shafa mai ta feffesa body spray tasaka wani rigan bacci orange yana nan kaman t-shirt a iya knees dinta kanta babu dankwali saitayi kaman wata Cinderella, sake tsugunnawa tayi taleka karkashin gadon tana kara duba wayan Mandawari but still bata ganiba, wuraren 10:30 Gwaggo tabude kofa tashigo dakin ganin yanda Lujain take daddaga filoli da bargo tana neme neme yasa Gwaggo tace “nashige su mehaka kika juyamin daki wai mekike nema haka kinbar mijinki shi kadai adakinshi ke kina nan tun dazu yatafi ya kwanta” turo baki tayi tazauna ganin bakin gadon tai tagumi ganin bataga wayan ba, karasowa dasauri Gwaggo tayi gabanta takama hannunta tareda mikarda ita tsaye tace “yo wai ke wace kalan yarinya ne Lulu iyye? Oya wuce kitafi dakin mijinki” turobaki tayi tace “ni anan nake kwana” baki Gwaggo tasaki saikuma tamata dakuwa kaman zata tsokale mata idanu da sauri ta kulle idanunta Gwaggo tace “aida kin barshi bude kiga yanda zan tsiyaye miki wayan nan idanuwan magen naki tunda bakida hankali, wuce kitafi dakin mijinki” akufule Lujain tace “ni bansan dakinshi ba Gwaggo kumani ki kyaleni” hararanta Gwaggo tayi kawai ta finciki hannunta tayi waje da ita tana masifa tace “da girmana billahillazi barakisa nayi abun kunya ba nazo gidanku inaji ina gani kizonan ki kwana dani barakije ki kwana da mijinki ba” duk yanda Lujain ke turjewa kin sakinta Gwaggo tayi har gaban dakin Abee kai tsaye Gwaggo tabude dakin tareda wurgata ciki itama tana shigowa Abee dake zaune gaban study yadago kanshi yakallesu yanda Lujain ke makema Gwaggo kafada alamun barata zauna anan ba Gwaggo ta washe baki tana kallon Abee tace “Imrana zan lallasa matar nan naka akanme sabida taganni barata kwana dakin mijinta ba sai wajena, kibiyoni kiga abinda zan miki” Gwaggo tawuce tafita tareda rufomusu kofan tsayawa wajen tayi chak kanta akasa hawaye ya gangaro daga idanunta takai hannayenta tanajan riganta kasa she’s so uncomfortable, Abee cigaba da abinda yakeyi yayi batare daya kara bata second look ba, gajiya tayi da tsayuwa ganin kafafunta na neman rikewa ta tsugunna ahankali akasa saikuma tazauna awajen kaman marainiya tarasa abinda kemata dadi, wuraren 11 tafara gyangyadi awajen.
12 daidai Abee yagama aikin dayakeyi tass yakashe computer sannan yajuyo ahankali yadaura idanunshi akanta gabaki daya atakure take tana gyangyadi kanta na lilo awahale. “Kee!” Wani kalan mugun firgita tayi tabude idanunta dasauri tareda mikewa tsaye tana kallon Abee awani kalan tsorace, mikewa tsaye yayi ahankali tareda zuba hannayenshi acikin aljihun wandon dake jikinshi yafara tafiya yana tahowa inda take, batasan mesaba wani kalan faduwa gabanta yashigayi yawani kalan cika mata idanu yamata mugun kwarjini kasa jure kallon dayake mata tayi dawani kalan sauri tasauke kanta kasa, karasowa yayi gabanta ya tsaya chak hannunshi zube a aljihu yana wani kalan kallonta, tunda take bata tabaganin mutumin dayamata rumfa kaman yanda Abee yamata ba ganin yanda ya tsaya daf da ita ko Baba baya mata rumfa haka, hakanan jikawai tayi kafafunta sun kasa daukanta, dukewa tayi awajen dasauri tana wasa da yatsunta, kallonta yayi cikin kakkausar murya yace “stand up!” Babu musu ta mike tsaye kirjinta nawani kalan bugawa babu kakkautawa bata tabajin kalan faduwan gaba datakeji ayanzu ba wani kalan zati da kwarjini Abee yakedashi da ita kanta bazata iya bayani ba, ganin yanda takasa dago idanunta takalleshi yasa strictly yace “look into my eyes!” Dago idanunta tayi tadaura akan nashi kasa cikakkun 3secs tayi ganin kalan kallon dayake mata zata sauke idanubta kasa azafafe yace “don’t you dare!” kafeta yayi da idanu yana tura hannunshi cikin aljihu yaciro wayan Mandawari tareda nunamata wani kalan ijiyan zuciya tasauke saida yaji saukan numfashin akan fuskanshi gashi ya tsareta da idanu bayako kyaftawa daburcewa tayi daburcewan dabata tabayiba tunda tazo duniya kawai fashewa tayi da kuka, yatsanshi yakai kan lips nashi hakan yasa tawani kalan hadiye kukan tass, anatse yace “kuka nace kimini”? Girgixamai kai tayi tanawani kalan sauke ijiyan zuciya gwanin ban tausayi, ganin yanda take numfashi kaman zata shide yasa ya sassauta murya ahankali Yace “what did I say?” Adaburce tace “kace wayan waye wannan?” Tsareta da idanu yayi alamun yana jiran amsa, lips dinta har rawa suke kaman an jonamata electric shock tace “Maa…….Man…….d…..wari yab……b……bani” tafada dukta burkice, wani irin kallo dayamata yasa taji cikinta ya murda batasan lokacin datace “a school din nan yakawomini” wani irin kallo Abee yamata yace “ina jinki” kuka ne a muryanta sosai amman yahanata yi in that crying tone tace “ina aji security guy yazo yace Yayana nakirana I thought kaine naje naga shine, he asked me yanda akai auren mu, saiya bani wayan yace zai kirani and he’s inviting me to his welcoming party, da……daz….zu ma yaaaaa…..kir……rani” Abee jiyayi kaman ta watsamai garwashin wuta azuciyanshi, nunata yayi da yatsa yace “listen here girl babu abinda zanyi dake, I don’t consider you my wife one bit, ko anjima aka kama yaron nan I will be sending you back to your father’s house batare dana bari kin kara koda kwana daya agidan nan ba, but listen here dagayau don’t ever bring wani abu that belongs to wani namiji into my house kinajina” gyadamai kai tayi dasauri tana tagwayen ijiyan zuciya idanunta na mugun kyalli sabida yanda suka cikada hawaye, cikin zazzafan murya Abee yace “nine nace you can live anyhow and talk to duk wanda kikaga dama and that same me yau na janye! Inhar kina gidan nan kina zama karkashina karki kara kula wani, idan kika kara koda kallon that small boy saina baki mamaki kinajina” gyadamaikai tayi dasauri tace “eh naji” cikin fushi sosai Abee yace “just sit and be praying akamo mutumin nan so that you will get out of my life forever nagaji dake! I am tired of you! Pray akamoshi sabida narabu dake only then you can do duk abinda kikaga dama and talk to duk wanda kikaga dama Imran doesn’t care! Understood” gyadamai kai tayi dasauri, hakan yasa yawuce fuuuuu yafada bathroom nashi, wanka yayi yafito sanye da kayan dayashiga dasu bayin yana fitowa yabude kofa yashiga dakin closet nashi yadan jima aciki sannan yafito dawasu pj dark blue ajikinshi yana wani kalan kamshi hannunshi rikeda wani babban bargo batare daya kalleta ba yace “jeki kwanta akan gado” dan dago kanta tayi takalleshi ganin yay kan dogon couch din wajen yana shirin kwanciya yasa ta tashi ahankali tai kan gadon har wani tsoron hawa gadon take, gadon fes fes bedsheet din fari kal amike kaman ba’a kwana akai, kaman wacce bata bata ganin gado ba tahaukai ta kwanta gadon nawani kalan kamshin turarenshi, bargo taja ta lullube sabida yanda dakin keda sanyi, kashe wutan dakin akayi hakan yasa ahankali tasauke ijiyan zuciya tareda lumshe ido.Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram; https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
EPISODE 3️⃣8️⃣
Hakanan jitayi baccin yaki zuwan mata tarasa sukuni bakaramin damuwa ne aranta ba, yace zai saketa dazaran gaskiya ya bayyana amman kuma yahanata magana da saurayinta mai sonta wanda zai aureta dazaran sun rabu, duka maganganunshi dawomata suke, wani kalan kukane yazo mata taushe bakinta tayi da bargon data lulluba dashi tadinga kuka, tarasa farincikin ta rana daya kawai sabida wani mugun shairi dawani mutum yahada mata, dudda Babanta baida kudi Babanta atampopi yake saidawa akasuwa gidansu babu Ac kaman wannan, gidansu is not mansion kaman wannan, babu motoci agidansu kaman irin manyan motocin gidan nan but she has always been a happy person, kometakeso takeci, Baba nadadewa kafin ya yanka musu kaji but Gwaggo koda yaushe tana cikin yanka mata kaji tana soyamata, dudda lokacin Mandawari baitaba kulata ba ko amsa messages nata still she’s always happy, she’s always at each she sleeps peacefully clinging to Gwaggo so tight, but rana daya she lost everything she lost her sweet life, kunya da tsoron fita take, zaman aure take dabama tagane kan Auren ba, zama take a inda batasan kowaba, Mandawari da sunan shine kullum acikin sallolinta biyar finally Allah yahadata dashi he loves her so much har yana bata iPhone IPhone dabata taba rikewa a hannu ba, but Mandawari yabata yay yay inviting nata but she couldn’t show up duk sabida wannan kaddararren auren duk dan sabida wannan shairin da aka mata, Allah kadai yasan yanda Mandawarinta yake fushi da ita yanzu ina zatasa kanta taji dadi, babu abinda kemata dadi aduniya, cikinta ne taji yadaurenata kanta na sarawa, lallashin kanta tasomayi juye juye tadingayi akan gadon tarasa abinda kemata dadi aduniya, daga baya tashi zaune tayi gashi wutan dakin akashe abinda yakara kara mata damuwa kenan, yaye bargon tayi ahankali tasauke kafafunta sama dudda dakin ba duhu mikewa tayi ahankali tana shafa bango kaman mayya tana kokarin locating bayin dataga yashiga dazu, jin ta taba kofa yasa ahankali ta murda kofan tabude wani kalan farin bayine tsaftaccen gaske ita har tsoron shigama tafara dan karta mai datti da bayin ganin yanda hasken bayin ke shigowa cikin dakin yasa tadan juya atsorace takalli kujeran dayake kai ya lullube fuskanshi kadaine ke waje dasauri tashige cikin bayin tareda maida kofan ahankali tarufe, tana kalle kalle, wanke fuskanta tayi da ruwan sanyi takalli fuskan nata a madubi idanubta sunyi jajir sun kumbura sabida kuka, bayin tabida kallo ganin bataga towel ba wani drawer mai bala’in kyau datagani takai hannunta har rawa yake tabude towels tagani kusan guda 10 farare tass anmusu wani kalan rolling ninki sotake tadauka tadaura amman yanda taga an gyarasu awajen yasa tsoro ma yahanata tabawa, bayin tashiga kallo tana kallon sabulan wankanshi kadai kusan 13, different shower gel na maza, da scrubs dakuma set na bubble bath, abubuwan dayake dashi ko ita batadasu bayin sai kanshi yake bude kofan tayi ahankali tafito ta maida tarufe tana daddafa bango tawuce takoma gadon ta kwanta ahankali tacigaba da rolling still takasa bacci sai wajajen 2:30 bacci yay awon gaba da ita.
Tashi Abee yayi ahankali ya zauna dan all this while ba bacci yakeba yan addu’a yayi 3 dot as usual yatashi yawuce bayi alwala yayi yafito yahau kan dadduma yafara salla har zuwa 4:00 yanakan dadduma sannan yatashi bayi yashiga wanka yayi yafito da pj dinajikinshi yawuce closet nashi shiryawa yayi cikin wani jallabiya fara kal da hula sai kamshi yake zubawa yafito ko kallon gadon baiyiba dan yasan ba salla takeba yabude kofa yafito tada mutanen gidan yayi suka wuce masallaci.
Wuraren 6 tabude idanunta ahankali tanabin dakin da kallo daya kunna wutan ciki, gently ta tashi zaune kaman wacce ta tuna wani abu saikuma ta yaye bargo tasauka daga gadon dasauri tana kallon zanin gadon ganin bata batamishi ba yasa harwani ijiyan zuciya ta sauke, agurguje tashiga gyara gadon dan amike taga bedsgeet din kaman ba’a kwana akai, maida bargon shima tayi ta shimfida yanda tasameshi sannan tajuya tana bin dakin da kallo dakin komi white kar kar sai kamshi kaman kada kafita shi karan kanshi dakin nauyin kallo yake mata kaman mai dakin naciki, kaman yana kallonta daga wani waje wucewa tayi tafita daga dakin dasauri tawuce dakinta tabude kofa tashiga babu Gwaggo adakin ko ba’a fadamata ba tasan tasauka kasa ne bayi direct tawuce brush tayi tai wanka tafito tasake shiryawa tsaf wani gown tasaka very simple mai ruwan ganye daya tsayamata a guiwa sannan ta feffeshe jikinta da turare tasake kwanciya agado tanajin wani sabon ciwon ciki dan rabonta da magani tun wanda tasha jiya, bude kofan dakin akayi Anty Binta ne murmushi tayi ganinta sanye da gown idan tasaka kaya saitayi daban saita kara kyau, karasa shigowa dakin tayi da katon tray tace “sauko kiyi breakfast kisha magani bari nakawo miki atampopinki da aka gama dinkawa jiya daman sabida bakida lafiya ne nan baki ba” tana ijiye tray akasa tawuce tafita, saukowa tayi ahankali tazuba shayin a cup tana kallo, bude kofa Anty Binta tayi tashigo dawani katon ghanamasgo dan anan telan ta lodo kayan bin Anty Binta tayida kallo data wuce gaban wardrobe nata tashiga jera kayan itakuma ahankali tadauki tea ta shanye tasss, takasa cin daidai da kwai kawai babu abinda kemata dadi ko kadan dawowa wajen Anty Binta tayi tadauki magungunan ta tashiga ballo mata tace “ga maganin kisha tundadai yauma baraku hadda ba sai kuma next week ke ba lafiya Kausar kuma wai bazata ita kadaiba saikace da chan ba ita kadai ke zuwa ba” tabe fuska tayi ganin maganin da Anty Binta ke bata, Anty Binta tace “wlh ko kisha kona fita nakira miki Yaya Imran daman yadawo” hannu tamika mata dasauri kaman zatai kuka tace “ai zansha” runtse idanu tayi tasha kaman zatai amai da sauri Anty Binta tabata tea tasha sannan ta tashi zatahau gado Anty Binta tace “sauka kizauna bakisan babu kyau dazaran mutum yaci abinci Ya kwanta ba, baida kyau sannan yanasa kiba, yanasaka katon ciki, medically kuma yanasa abinci yadawo maka har hanci tashi muje falo ki gaida su Hajiya saiki dawo ki kwanta tunda bakida lafiya” Gyadamata kai Lujain tayi tamike tsaye ahankali tareda saka slippers zata fita Anty Binta tabita da kallo yanda manyan hips nata ke shaking a rigan are way too sexy, wani kalan crazy sexy shape ne da Lujain babu abinda batadashi all this chubby orobo fine yaran nan she’s just one, gashi su Harun da Musty duka abokanen Ya Imran na falo idan akwai one thing datasani kan Ya Imran lokacin tun Mamansu Kausar na raye shine yanada bakin kishi dudda dai Lujain bawai sonta yake ba kokuma yadauketa matsayin mata bane still bazaiji dadi tafito falo haka gaban abokanenshi ba babu ko dan kwali gatada gashi duk wanda zai kalli kitson shukun kanta saiya kara sabida yanda yay kyau bakin kiston duksun warware ma tsabagen santsi sunyi coils, “Lujain” Anty Binta takirata dasauri ganin harta bude kofa, juyowa tayi Anty Binta takalleta tace “zoje dauki hijabi kisaka” Gyadamata kai Lujain tayi takoma tashiga cikin dakin tana tafiya ahankali Anty Binta na kallonta dan bata saka bra ba yau ko singlet dinma bata saba rigan kawai tadaura ajikinta Anty Binta tace “maisa baki son saka bra Lujain batun yau na lura ba bakison nonon ki zasu zube ba” karasa saka hijabin tayi tareda lankwaye kanta murya chan kasa dan yau ko magana ma bason yinshi takeba tace “ni damuna yake” yanda tai maganan Anty Binta takalla saikuma tai murmushi tace “muje” mamaki kawai take da har yanzu Abee bai farason Lujain ba she’s damn adorable, yanda yake abubuwa ashagwabe, her expression, dan karamin pink lips nata, kumatunta are just so sweet and too cute to watch, she just wish inama Allah zai bata diya Yar chubby haka kaman Lujain daba karamin dadi zataji ba.