Sanadin caca book 1 complete - Chapter 18
Sanadin caca book 1 complete Chapter 18: Sanadin caca book 1 complete Chapter 18. A galabice na shigo gidan,na dawo daga makaranta,kai neman ilimi kam…
3,283 words
A galabice na shigo gidan,na dawo daga makaranta,kai neman ilimi kam akwai wuyah. Uniform na fara cirewa sai naji wayar da goje tabani tana ƙara,tunda ya tafi bai taba ƙiraba,iyah Tunga kawai na taba ƙira yakawo mana kananzir. Ɗauka nayi naga two missed call,goje?? Ni nayi zaton Tunga ne ma ya ƙira. Tunda ya tafi hadda cewa sati biyu zayyi,abu ana shirin yin wata amma bai dawo,mai kuma zai ƙira yace. Dama yana raye kalau kenan. Ɗagawa nayi tareda yin sallama a hankali,yanayin dana ji muryarsa ne yasakani maida hankali kan abin zai ce,idan ba kunnena ne ya samu matsala ba toh nishi naji yana yi. "Hello Sumaimah kin....ajinahh?" "Ehh ina jinka mai yasameka,wata matsalarce ta faru?" "Kinga ki tsaya ki saurareni,kinsan wannann dutsen mai kogo na bayan gari?" "Ehh ....eh nasani" "Toh kizo ki sameni a wajen,ki tahomin da abinci da kuma kaya,yawwa sannan ki je chemist zan turo miki sunan wasu magunguna ki tahomin dasu,sannan karki sanar da inna komai" Daga haka ya kashe wayar,wani bugawa kirjina yayi,yayinda kaina yafara lissafomin abubuwa da dama,shin mai ya sameshi yake cikin kogo,shida yayi tafiya.. Kayan na cire a gurguje na nufi inda abincin mu yake. Ɗiba nayi a kula na saka a kwando da,hijabi na zura na fita daga gidan da sauri.. Akan hanya chemist ɗin yake,magungunan daya faɗamin nasiya,harda auduga,plaster da kuma bandaji acikin abinda ya turo ɗin, ciwo yaji,shine abinda yafara zuwa kaina lokacin dana siya abubuwan. Pure water na siyah a ɗaya shagon,daga nan na nufi inda yayi min kwatance. Da ɗan tazara wajen da cikin gari,dan haka saida na taka kafin na isa.. Ina shiga wajen na sameshi a kwance akan kayansa,gefensa kuma akwatine da tarin auduga duk jini a jikinsu,idonsa a rufe yake yana kallon saman kogon,inda bashi yayi kwatance ba zan iya cewa bashine bane,don babu wannan gashin fuskar dana sanshi dashi,sannan yayi fari ya rame kaman bashi ba.. Numfashi yake fitarwa hankali ma wahala. Ban lokacin dana isa wajensa ba da sauri,bayan na ajiye kwandon danazo dashi.. Tsugunnawa nayi a gabansa ina ƙare masa Kallo,fuskata ɗauke da damuwa ƙarara,na tunanin shin wanne irin mummunan abune yasameshi haka,sannan kuma yaushe? Buɗe shanyayyun idanuwansa yayi ya ɗora akaina masu kama dana majinyaci. Nima kallonnasa nake da nawa idanuwan wanda suka cika da ƙwallah,fatar bakina nakeson na buɗe nayi masa tambaya,amma sai rawa suke sun kasa bani haɗin kai. Hannunsa ya ɗakko zai kawo wajen fuskata,amma abinka da dama tsoronsa nake,saina ɗan ja da baya. Murmushi yayi tareda rufe ido a hankali yakuma buɗewa,dimple ne ya lotsa a gefen kumatunsa,dama yanada wannan abin a fuskarsa,amma ba wanda yasani saboda gashin fuskarsa,yanzu daya aske sainaga kaman wani mutum daban aka ajiyemin. Ashe farace fuskartasa kamar jikinsa,saidai bakinsa yayi duhu bakaman sauran fatar jikinsa ba,saboda shaye shayen dayake. "Duk da ina cikin wannan halin amma tsorona kikeji,shin mai zan iya yimiki a yanayin danake uhm?" Tari ya fara yana runtse ido,ban san lokacin dana tallafo kansa zuwa jikina,dama gani Allah yayini banson naga mutum a halin jinya. Bare irin wannan,tsayawa yayi da tarin tareda saqala hannayensa ya riƙo kunkumina gam,wanda nasan ciwon dayake jine yasakashi yin hakan,a nanne nima na kulada bandejin dayake cikinsa wanda yayi jajur dashi da jini. "Sannu sannu,wayyo please ka tsaya barinaje na ƙira mai chemist ɗinnan,wataƙila zasu iya taimakawa" Ƙoƙarin zare jikina nayi domin na tafi,amma sai naji yasake ƙanƙameni sosai.. Magana yafara cikin gajiyayyar murya. "Ahahh kada ki ƙiramin kowa,banason kowa yasan halinda nake ciki....kin kawomin abinda na buƙata?" "Ehh dukka na taho dasu" "Uhm barina dashi ki gyaramin wajen,jikina ba ƙarfi bazan iya dakai na ba" "Niiii ban ban....iya ba bazan iya gyara wannan ciwon ba" "Uhmm zaki iyah mana ko baki iya ba zannunamiki yanda zakiyi,ba wani abune mai wuya ba,taya zaki ƙira kanki matar goje idan kina tsoro uhmm?" Nidai kurmiya na koma da zancennasa. Saboda kallonsa nake kaman bashi ba. Tallafah masa nayi ya jingina da jikin dutsen,jikinsa har rawa yakeyi saboda zafin ciwo. A hakan kuma yasaka hannu ya sunce ɗaurin ciwon,wanda matar data kawoshi wajen tayi masa. Lokacin da yagama suncewar saida na rufe idona saboda yanda wajen yayi jawur kaman ɗanyen nama. "Ohh bazaki iya gani ba,taya kuma zaki iya wankemin idan kika kasa gani?" "Ya akayi ka samu wannan ciwon haka,a wajen satar ne koh" Nafaɗa cikeda jin haushin yana satar,koda yake yaudarar kaina nake,zaman danayi dashine a wannan watannin nafara manta waye shi. "Uhm a wajenne wani soja ya soka min wuƙa,ina faɗuwa dana bude ido nasamu kaina a wajennan tareda abinda muka je sata ɗin. Sannan ba sata ce wacce kika sani ba,abune na sirri da mutanena ma basu sani ba,shiyasa nace miki kada ki faɗawa kowa ina wajennan ,saidai in yayi yawane ki faɗawa Tunga kinji" Ɗaga kaina nayi tareda fitowa masa da abubuwan dayace na kawoɗin,naga yanda yake maganar na fahimci lamarin mai tsaurine. Kaman yanda yafaɗa shine yake nunamin yanda zanyi har muka gama rufe ciwonnasa,gumi kuwa ya haɗashi shirkif saboda wahala. "Gashi sai wahala kakeji,da baka jeba da haka bata faruba" "Uhm to hakane,amma ni nasamu da sauƙima,tunda abokan aikina kusan duk sun mutu,wanda sukeda rai ma suna hannun ƴan sanda. Wannan akwatin in zaki tafi gida ki tafi dashi ki boyemin,zan kaiwa ƙungiya idan na warke" "Kace tacemaka yanada muhimmanci,amma meyasa zaka kaiwa barayi,bayan kasan hakan yanada hatsari,dan Allah karka sake komawa wajensu,duk da cewar kaima........uhm ....amma dai kafisu kasaka hakan a ransu" "Me kikeson fada kika fasa,nima bana kirki bane koh?" "Ahah nidai bance ba amma dan Allah karka koma,inna bataso" Hannunsa yasaka na dama ya ballamin akan goshina,nima sai a sannan nakulada yanda na zage inata surutu.." "Ya karatunki,daga gani dawowarki kenan bakici abinci ba..ɗebomin naji ko zan iya ci" Ɗan murmushi nayi ina shafa goshinnawa,kafin na ɗebo abincin. Miƙamasa plate ɗin nayi amma naga ya kafeni da ido yaƙi ƙarba.. Har na fara tunanin ko bayason jallof ɗin taliyar,saikuma naga ya buɗemin baki,wato so yake na ciyar dashi kenan. Ɗiba nayi a cokalin cikeda kunya nakai bakinsa,ba kunya kuwa shi ya karba yafara ci. Shuru wajen yayi sai numfashinmu kawai,baici da yawa ba ya min alamar ya ƙoshi. "Naƙoshi bani ruwa,sannan ki cinye sauran,dan naga yunwa kikeji" Ikon Allah tun ɗazu yake cewa yunwa nakeji,yaushe yafara kulada ni haka?. Maganin dana taho dasu na miƙa masa ya balla,kafin na bashi ruwa ya kora dasu. Bayan mun gama cin abincin alwala nayi na sallahr la'asar nazo na shimfiɗa ɗankwalina,yana kallona harna idar da sallahr,Addu'o'i nayi kafin na juyo na kalleshi.. "Amma tsawon wannne lokaci kayi a kwance" Ɗaga min kafaɗa yayi tareda cewa. "Bansani ba,kawai dai abinda nasani shine ranar 23 ga watana march ne aka sokeni da wuƙa" Zaro ido nayi tareda rarrafowa kusada shi,kenan satinsa guda a sume? "Sati guda kenan kayi a kwance,dan yau talatinne ga wata" "Uhm zai iya yiyuwa,kuma da alama wadda takawoni nan wajen har asibiti suka kawoni" Yafaɗa yana nunamin hannunsa,inda aka saka masa canular,kaman ma yau aka cireta a jikinsa,kuma wajen akwai takun sawun takalmin mace,harda robobin lemo da ledar cakes. "Amma wacece haka in tana cikin tawagarku meyasa ta ajiye maka akwatinnan,inaga bataso ka kaiwa kungiyar nan taku" Dan haka kawai naji banaso ya koma wajensu. "Hhhhh da alama bakyaso na koma aikina,amma ke ruwanki ne,dan kinga bana iya komai shiyasa har umarni kike bani ko" "Ahah ba haka bane kayi haƙuri" Koƙarin tashi nake shirinyi daga wajen,sai kuma naga ya kamo hannuna gam ya riƙe,idonsa ya rufe yana jijjiga kan cikin sauri. "Ciwon kaina wayyo kaina yana shirin tsagewa ahhhh,bansha wiwi ba,kibani wiwi ɗina......." Tambayata yake,amma da alama kuma badani yakeba,sambatune kawai na ciwo. Hannayena na saka a gefe da gefen kannasa na riƙe,Addu'o'i nafara karantowa na neman sauƙi,hannunsa yasaka yana ƙoƙarin ture hannuna,tareda ƙara sautin ƙarar dayakeyi. Yayinda nikuma na riƙe gamm na dawo yi ma a fili,kasancewar jikinsa babu alamar ƙarfi yasa ya kasa ture hannunnawa. Can bayan kaman wasu mintuna naga yatsaya da jijjiga kan,ina dubawa naga yafara bacci daga zaunen,gyara shimfiɗin danaga anyi masa da kayansa nayi,tareda kwantar dashi a wajen. Tashi nayi na tsaya ina kallonsa,daga yanda yake maganar kaman daman ya san da ciwon kan kuma ya daɗe yanayi. Dannima na sha ganinsa a ɗakinsa ya riƙe kai,kenan shiyasa yake shaye shayen. Har yanzu na gagara fahimtar sa,kowacce rana sainaga wani abu sabo dan gane dashi. Kayan abincin na ɗauka domin komawa gida,zanje na dawo kada inna inna taka bananan. Karare na gona na ɗakko nayi ta jerawa saida na rufe wajen tass kafin na tafi. Ina shiga gidan muka haɗa ido da inna,tun kafin nayi magana ta jefomin tambaya.. "Kekuma daga ina haka kikadawo,ɗazu naji motsinki ina tashikuma na bakyanan" To anan gizo yake saƙar ,shin mai zan faɗawa inna,gashi yace kada na kuskura tasani.Wata dabara ce ta faɗomin. "Umm uhm inna dama wata ƴar ajinmu ce a islamiyya batada lafiyah,kuma ba ƴar garinnan bace zuwa sukayi,shine to na kai mata abinci.....sannan inaso na zauna mata kafin ta warke,tunda bakowa wajenta" "To ikon Allah,dama rashinnaka a garinnan ba daɗi,kin kyauta sosai saki faɗawa shi mijinnaki a waya" "Ehh na tura masa message yace ba matsala,yace yana gaisheki ma wajen aikinnasu ne ba a kiran waya ne" "To shikenan ba matsala ina amsawa,zan shiga anguwa anyi matar ɗan marka ta haihu" "To saikin dawo inna a gaisheta" Daga nan tabar zancen,dan dama ita macece da bata matsamaka sai tasan mai kake,musamman idan tasan abu kake boye mata. Kuɗin na ɗauka a cikin wanda Tunga ya kawomana. Kasuwa na tafi na siyo hanta da kuma alayyahu,dama duk wani abunda nake buƙata. Farfesunta nayi masa da ɗan romo na juye a kula,saikuma shayi dana haɗa na zuba a flask. Wanka nayi lokacin rana ta kusa faɗuwa. Pillow na ɗauka da sallaya sai butah,a cikin jakar da aka kawomana kayannan na saka su,saikuma kwandon kayan abincin. Lokacin dana ɗauki hanyar wajen ba sawun mutane sosai,Allah ya taimakeni dana ɗebi ƴan kallo an ganni da kaya nayi bayan gari. Yanda na rufe wajen haka naje na sameshi,saida na ture kararen kafin na shiga. A kwance yake yanda na tafi na barshi yanata bacci,da alama maganin dayasha akwai mai saka bacci a ciki. Ban tsasheshi ba,dana ajiye kayan hannuna wajen na fara gyarawa. Na ɗebe dattin da wanda suka kawoshi wajen suka zubar,da kuma audugar da sukayi ta goge ciwon dasu,harda wanda muka cire muma ɗazu. Shimfiɗa sallayar nayi gefe,kasancewar wajen rairayine,awakin mutanene masu kwana a jeji suke shiga wajen da daddare,kokuma almajirai idan suka iyo itace su tsaya su huta.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977 Auwal Sadiya First bank
Ko katin mtn ta nan 09035784150
VTU ta nan 2347068390570
Shaida kuma ta nan 09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[27]
Basan ya tashi ba saida naji maganarsa tukunna. "Yaushe kika dawo?" Cikin magagin bacci yake maganar. "Uhm ban daɗe ba sosai,sannu ya jikinnaka" "Da sauƙi kawai zance,miƙomin ruwa nasha,bakina bushewa yakeyi akai akai" Ruwan na ɗauko na bashi,lokaci guda ya zuqe guda biyu,Wannan wanne irin shan ruwane haka,na faɗa a raina. "Ga abinci yakamata kaci" "Mts banajin yunwa, bar abinci nan,ki ƙiramin Tunga kice ya kawomin ajiyata danayi a jeji" "Ba abinci bane haka,nayine saboda ina tunanin ko jikinka yana buƙata,sannan a halinda kake ciki bai kamata ka zauna da yunwa ba" Ganin bai sake cemin komai bane yasa na jawo kular dana zo da itan,farfesun hantar na tura masa gabansa,na manta banzo da plate ba.. Matsawa kusada shi nayi ina bashi a baki,daga yanda yake karba ma tabbatar yanayimasa daɗi sosai,dan saida ya kusa cinyeshi tass. Kofi na ɗakko bayan yagama na zuba masa shayi shima mai zafi. "Yaushe kika waɗannan abubuwan haka?" "Lokacin dana koma gidane,saidai kayi haƙuri na fita zuwa kasuwa da kaina,dama inason na faɗamaka saikuma na manta." "Uhm bakomai nagode da kulawarki,bani maganin can nasake sha naga har dare yafara" Bayan na miƙomasa yasha ruwa na zuba a buta nima nayi alwala nai sallahr magriba,kaman ɗazu yana kallona har na gama. Sake zuba wani ruwan nayi nazo inda yake,kallon tambaya yakemin ganin na miƙamasa hannu yabani nasa hannun. "Kawo hannunka alwala zanyi maka,yakamata ka rama sallolin da ake binka,tunda ka ɗan samu sauƙi" "Taya kike tunanin zan iya sallah a haka?" "Indai kana cikin hankalinka to zaka iya yin sallah,domin a kowanne yanayi mutum yake ba'a ɗauke masa sallah,saidai idan baya cikin hankalinsa. Ance idan bazaka iya a tsaye ba ka jingina,in shima bazayyi ba ka zauna,in ya gagara ka kwanta ka kalli gabas,in shima bazayyiyu ba toh zaka iya yi a duk yanda ka tsinci kanka. To haka ma wajen yin alwala,in jikinka bazai ɗauki ruwa ba saikayi taimama da ƙasa,idan itama bazaka iya da ita ba to saika shafi jikin gini mai tsarki kayi dashi. Toh a wannan bayanin kaga kai zaka iya yin alwala kuma kayi sallah a zaune" Bayan gama bayanin bai ce komai ba,amma ya miƙomin hannayensa na fara yimasa alwalar. Cikin nutsuwa nake yimasa alwalar har na gama tsaff. Rigar dana zo da itah na taimaka masa yasaka,yanda bazata shafi ciwon ba,kafin na juyashi ya kalli gabass,magriba yafarayi wacce ake binsa kafin ya fara da rama sallahr asuba tun sanda aka jimasa ciwo. Daki daki yake bin sallahr ina zaune ina kallonsa,daga baya daya gaji sai na koma ta baynasa ina tallafamasa. Muna daɗe a haka har akayi sallahr isha ya tsaya da ramakon yayi,ganin yana haki yagaji yasa ya tsaya dayi sai ya huta tukunna. A bayansa nake ya jingina dani,saiji nayi ya kwanto akan cinyata,kallon fuskata yakeyi,yayinda nima na sunkuya ina kallonnasa,mun daɗe a haka idonmu a sarƙafe dana juna,saida naji hannunsa akan fuskata kafin na dawo zahiri.. Magana yafara a cikin wata murya da banyi tunanin yanada itaba. "A ɗan zamana dake kin taka wata rawa a rayuwata,ko yaushe cikin juyewa kike da narasa taya zan misaltashi. A lokacin danake son naga kin sake dani saiki ɗankware jikinki,lokacin danazo yimiki barazana kuma saiki dake,idan nayi laushi kuma sai zama jaruma,a yau kaɗai kinyimin abinda ban taba tunani ba,kin zamemin hannun a sanda na rasa nawa,kin zamemin ƙafa da tawa taƙi aiki,kin zauna dani a wannan dokar dajin da babu kowa a ciki saini kaɗai. Tun farkon da mahaifinki yabani ke a matsayin fansar kuɗina naga rashin dacewarsa nayin hakan,shiyasa na nesanta kaina dake,a tunanina hakan zaisa kiyi rayuwarki yanda kikeso,naƙi shiga rayuwarki saboda nasan nida ke bamu dace ba ko kaɗan,amma sai naga duk wannan koƙarin danake yatafi a banza,ke koyaushe so kike ki cusa rayuwarki cikin tawa. Wannan ƙasa da kan da kike idan kina gabana,da kuma neman izinina a duk wani lamari na rayuwarki shine yayi babban tasiri wajen karya zuciyata,har tasaka na ajiye komai na ɗauki nauyinki batareda nasani ba. Saboda tunda nake babu wanda yazo da kansa yanemi izinina akan abu,saidai na bashi dakaina in kika ɗauke Tunga. Sannan tun kina zuwa inda nake ina jin kin takuramin,har yazamo idan banganki ba sai zuciyata tayi ta kewarki. Sumaimah bansan mai kikayimin a rayuwata ba amma dai shigarki kinyi nasarar share wani a fili a ciki kin mamayeshi yazamo naki. Ciwon kan dana tashi a rayuwata bansan lokacin dana faraba,bai taba dainawa ba indai ba shaye shaye nayi ba sai yau,kuma dama yakan tashi ne idan na bijirewa umarnin da zuciyata tabani,saikashi yau kin karanta min wani abu naji ya tafi batareda nasha komai ba" Tunda yafara magana ban ɗauke idona ba daga kan fuskarsa,shin anya kuwa gojen danasanine yake waɗannan kalaman,meyasa yau ɗaya naga wata nutsuwa a tattare dashi,babu wannan zazzare idon da kuma cije cijen baki..wannan gashin daya maidashi dodo duk babu shi. Kar a ji haushina idan nace yayimin kyau fiyeda mutane dayawa a garinnamu. Hannuna nasaka akan nasa wanda yake kan fuskata,tareda sakin wani murmushi da bansan ma'anarsa.. "Duk abinda kake faɗan nayi aikata a rayuwarka banice nabaka wannan matsayinba,Allah ne dakansa yabaka a matsayinka na mijina,ni kawai umarnin da aka bani na nayi maka biyayya,kada nayi wani abun batareda saninka ko kuma yardarka ba,sannan na kyautata maka na kasance sassanyar inuwar dazaka zo ka hutas da gajiyarka,na kasance tamkar dare wajen rufe sirrinka,sannan na kulada kai da dukiyarka harma da dani kaina idan baka nan.....domin aljannata tana ƙarƙashin ƙafarka,sai nayi hakanne Allah zai bani izinin shiga" A yanda nake kallon idanuwansa lokacin danake faɗomasa wadannan Kalaman,naga Abubuwa da dama wanda wasu bazan ce mesuke nufi ba. Kawai naga yashiga mamakin,shin dama ashe yanada irin wannan matsayin a rayuwar wani,kaman nasan mai yakeson faɗa na cigaba da bayanina. "Tabbas hakane kanada wannan matsayin a rayuwata tsawon lokacinnan,koda wasu zasu gujeka suyi nesa dakai. Ni kaiɗin jigona ne,kuma mahaɗin rayuwata,wanda rayuwata ta riga ta ɗinke da taka tun lokacin da ɗauramin igiyoyin aurenka a kaina,shiyasa duk abinda zakayi wanda bai dace ba zaifi yimana ciwo nida inna sa'banin sauran mutane" Hawayen daya zubo acikin idona ne ya sauƙa akan kumatunsa,sai sannan ya ƙifta ido,da ya tsaya tamkar wanda ya daskare a cikin ƙanƙara. "Shin dama har haka na shiga rayuwarki,nayi tunanin dan an ɗaura aure ban kulaki ba bakomai,to idan harda waɗannan haƙƙunan da suke kanki wanda dole saikinyimin kenan nashiga rayuwarki dayawa,na rabaki da rayuwar da kike hankalinki kwance idan babu ni a ciki..kinmin abubuwa da dama,dan haka banaso ki cigaba da zama kina amsa sunan matar mutum kamanni,musamman daya kasance kinada ilimi mai yawa da kuma sanin yakamata,zalunci ne na ajiyeki a cikin rayuwata...zan sake..........". Kiff bansan lokacin dana rufe masa baki ba ina jijjiga kai. "Karka fara faɗin wannan kalmar,dan Allah karka furtata a gareni,da lokacin daka aka kawoni gidanka ne ka faɗaminsu zanyi farinciki da jinsu,amma a yanzu dana fahimce ka bana fatan jin wannan kalmar daga gareka,karka faɗesu ka fiddani a cikin rayuwarka" "To amma meyasa naga......" "Saboda na hango wata rawa danake son takawa a rayuwar taka,hmmm bazaka sani bane amma kanada wani hali da mata zasu zaga mazaje dayawa basu samu mai irinsa ba,duk da sunaso su samu ɗin. Kai tamkar zinarene a cikin duhun dare,rana bata haskashi na ballantana a gane wanne irin haske yake ɗauke dashi.....koda babu hasken rana ka bani dama nazamo fitilar dazata haska shi,ta yanda kaikanka zaka hango irin hasken da kake ɗauke dashi......dan Allah ka yarda dani,sannan ka bani damar ragamar kulada rayuwarka,kar nesanta ni daga gareka,ta hakanne zamu gano inda matsalar take kuma mu gyara.....ni har cikin zuciyata na amince dakai a matsayin mijina,kuma bana fatan naga ranar da zanyi nadama da ƙiranka da wannan sunan" Magana nake kawai ina kwararowa abinda yake cikin zuciyata,duk da yanda muryata ke rawa saboda yanda maganganun suka tabani. "Tunda nake ban taba yin alaƙa da wata mace ba bayan inna sai ke,a da hakan haushi yake bani,amma d kaɗan kaɗan nakejin wani abu na mannani da rayuwarki. Yanzu ma dakikaji na faɗa bawai son raina bane,saidan zanyi hakanne saboda ke,amma tunda kinji kingani ra'ayinkine zaki zauna tareda ni. Nikuma namiki alƙawarin bazan taba guje miki ba,kuma zan kyautata miki na faranta miki daidai yanda zan iya,sannan kaman yanda kika buƙata nabaki jan ragamar dukkan lamurana" "Naji daɗin maganar ka kuma nagode,nima kuma nayi maka alƙawarin Inshaallah bazakayi danasanin yarda dani ba" Shuru ne ya ratsa tsakaninmu,saikuma naga ya jare hannunsa daga fuskata yana riƙe kai. A yanda na kula kaman irin abinda yayi jiyane,hakanne yasa na ɗauke hannunsa na mayeshi da nawa. Addu'o'in danayi jiya na neman sauƙi nafara karanta masa,wanda yawanci sunayen Allah ne da yayi umarnin a ƙirashi dasu,sai fatiha da kuma su QUL guda uku. Maimaita masa nashigaba dayi bayan naji yayi shuru ma,a haka har nima bansan lokacin da baccin ya ɗaukeni ba anan zaune.
___***___