Sanadin caca book 1 complete - Chapter 21
Sanadin caca book 1 complete Chapter 21: Sanadin caca book 1 complete Chapter 21. Tun wayewar safiyar Sumaimah take neman goje a asibitin bayan ta tashi…
491 words
Tun wayewar safiyar Sumaimah take neman goje a asibitin bayan ta tashi amma shuru bata ganshi ba,har rana tayi inna tazo itada ƙaninta,abin yabawa kowa mamaki sosai. "Inna banga mijina ba ya bata inna,wasu sun ɗaukemin shi bai tashi na ganshi ba,shin wanene yake shirin rabani da mijina innaa... Inna kice su dawomin dashi,ban taba cewa ina sonshi ba,ina so na nuna masa soyayya innaaaaaaa ahhhhh" Tunda safen Sumaimah take jin wani abu yana hawanta,amma bata san menene har zuwa yanzu daya ci ƙarfin ta faɗi.. Abu goma da ishirin,ga batan goje ga kuma faɗuwar Sumaimah,cikin asibitin aka maidata da gaggawa,kowa a zatonsa rashin ganin gojenne yasakata yin haka,amma ana gwadata aka gano tanada shigar ciki na wata uku,ga kuma jininta ya hau saboda tension ɗin data sha a kwanakinnan. Dan haka asibitin suka Kwantarta ta samu hutu tukunna.. "Mairo wai yaronnan anya kuwa ba hankalinsa ya dawo ba shiyasa ya tafi,dama ina kince baisan komai nasa ba sanda kuka tsinceshi,hatta sunansa baya tunawa?" Kawu ya faɗa ƙanin inna mairo,zatayi magana kenan sukaji muryar Sumaimah a bayansu. "Inna shin mai kunnuwana suka jiyo kina cewa,dama bake kika haifi goje ba,to su waye suka haifeshi,daga ina yake? Shin menene asalinsa,danginsa da kuma sunansa ma. Inna dan Allah ki faɗamin,inna gudan jininsa ne a yanzu a cikin cikina,nayi saton na sanshi kuma na fara fahimtarsa,ashe ba haka bane,taya zayyimin irin wannan nisan a lokacin da mukeda buƙatarsa haka?" Zubewa Sumaimah tayi a wajen tareda rushewa da wani zazzafan kuka.....
Toh fah Jama'u anan fa littafi na ɗaya zai dasa ayah,tunda malam goje kam ya koma ga rayuwarsa ta ainihi,da alama bai san wani shafi ma da aka rubuta Sumaimah a cikinsa ba a rayuwarsa ballantana ya duba..........
Nagode nagode nagode da kuka biyo a sannu a cikin wannan littafi na SANADIN CACA Book 1 .......masu buƙatar son jin cigaban labari inda wasan zai fara sai su antayo min 300 na zuba a asusuna nasha mai mu cigaba da tafiyah,inda zaguji amsar waɗannan tambayoyin.
#shin dama ashe goje shine Ahmad?.
#waye sanadin shigarsa rayuwa a matsayin goje?
#wacece Madeena da Ahmad ya ambata lokacin daya farfaɗo?
#Wa kuke zargi da yimasa wannan tuggu?
#Ina labarin akwatin da aka bawa goje,Ahmad baisan dashi ba?,sannnan waye shugaba na biyu dana ɗaya na kungiyar BC?
#Allah sarki Sumaimah shin ya zatayi,wacce ƙaddara ce zata sake haɗata da,wannan miji nata wanda bai san da ita ba sam?.
#Irin waɗannan buhuhhunan cakwakiyah dana tafka anya ni SADI-SAKHNA zan iya warware su kuwa?
#domin jin zan iya ko bazan iya ba miƙomin 300 da fari tukunna tanan 3131951977 Auwal sadiya First bank 😊😊😊
Ko kuma ku tuntubeni tanan 0903578415
SADI-SAKHNA ce dai wacce kuka sani mai GIDAN GANDU da kuma BAƘAR AYAH ,wanda yasansu yasan tsarina......
Muhaɗe a littafi na biyu,ni nayi nan da ikon rabbis samawati,Allah ya yafemana abinda mukayi ba daidai ba.
Bye.........
MEENA VIP GROUP HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on +234 7014979567 WhatsApp ONLY