Sanadin caca book 1 complete - Chapter 5
Sanadin caca book 1 complete Chapter 5: Sanadin caca book 1 complete Chapter 5. Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15…
2,176 words
Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[07]
Butar hannunta ta ajiye tana kallonsu,sune kuma da gaske,tayiwa kanta wannan tambayar. "Gaji kune da asubar nan haka,mai ya faru kukayi wujiga wujiga haka?" Bude baki tayi zatai magana ƴar ta ƙarama ta rigata,tunda su ba ciwo a jikinsu. "Yaya ce tayi soyayya da Alhaji,shine wasu sojoji sukayiwa su baba duka suka jefarmu a bola" Kunya ce takama su kaman zasu nutse a wajen. Saurin wayancewa inna mairo tayi,musamman ganin yanda gaji ke kallon ƴar tata farida kaman zata cinyeta ɗanye. "Ohh to Allah ya tsare gaba,yanzu kuzo ku zauna,barina fito daga banɗaki na haɗamuku ruwan wanka kuyi mamatsa jikinku." Cije baki gaji tayi,so take tayi magana amma kuma tana tsoron kar inna mairo ta hana su ruwan kaman yanda tayi niyya. Kafin gari ya waye duk sun wanke jikimsu sun sanja kaya wanda inna mairo ta ɗauko musu a sashennasu,dan ko ɗakinta basu bariba tun asubar,bare su taka cikin gidan suga mai ya sauyah. A daren tayi musu abinci mai sauƙi sukaci,hankalinsu ya dawo kansu. Da safe kuma tasiyo musu burofen da masu shago suka buɗe.
Gaji ce tafito daga ɗakin tana kallon gidan,babu abinda ya sauya a cikinsa,saima fess da yayi kaman bashine sansanin shirgi ba lokacin da suke nan. Ƙofarsu ta nufah domin taga mai ya sauya,tun kafin ta ƙarisa tajiyo kukan saniya,abinne yabata mamaki,saniya kuma a ƙofarsu?. Turus tayi ganin kewayen ƙofar tata cikeda abincin saniyar da kuma kashinta,wajen sai kace kewayen dabbobi. Cije baki tayi tareda ƙiran sunan goje da ƙarfi har ƙasan maƙoshinta. "Gojeeeeeee!!!" "Na'am" Taji ya amsa a bayanta. Wani dum ƙirjinta ya doka saboda firgici,dan batayi tsammani yana gidan ba kuma ya jita,tafaɗa ne kawai yanda zuciyarta tafara tafasa. "Miye kike ƙwalamin wannan ƙiran kaman zaki ƙare min suna daga dawowarki iyeee" Diriricewa tayi tana inda inda,in a lokacin bayane zata iya maida masa magana,amma yanzu gani tayi gabaɗaya ya sauya mata,jikinsa ya sake murɗewa,gashin bakinsa sun sake tsayi,ga wani uban tabon yankan wuƙa a dantsensa na dama. Ji tayi kaman wani zaki yana tunkarota" "Uhm dama dama bakomai bane,kawai gani nayi ka maida mana ƙofar kamar kewayen dabbobi daga tafiyarmu" "To wa yace ku tafi ɗin,sanda kuke nan na tasheku na saka ta ne,ina saida kuka tafi yawon maularku tukunna,kunje kun saida musu hali sun koroku rana tsaka,mutane sun zaman zamansu zaku dawo ku damesu. In nan ba inda zanje kuma ban sanja ba,duk wanda ya damu mutane ko ya nemi neman rigima,saina yanke masa wata gaba ta jikinsa,daga ke har mijinnaki da kuma tarin tsiyar ƴaƴan ku" Muryar inna mairo yaji,hakanne ya tsaya da yiwa gaji tatass wacce take gabansa,tana jinsa amma babu dama ta rama sai yace zai bugeta kokuma yasaka ta a kewayen karnukansa. "Kai goje kaine fah bakada gaskiya anan wajen,saboda kai kasaka musu dabba a ƙofarsu,sannu kuma tayi magana kace ba madu ba bukar. Kaje ka sunce saniyarka ka maidata inda take da,wato gefen ƙofar ka,ni banga mai zakayi da saniya ba ma" "Kyauta tace ta farko dana samu sanadin ƙarfina da ƙwazo nah,idan na ganta tana tunamin dani jarumine,dan haka babu inda zan kaita anan zata zauna a gidannan. Tunda kinyi magana zan turo Ragarus ya ɗauketa a wajen" Cikin tafiya ta izzah ya nufi hanyar waje,wani baƙin kare yana binsa a baya.. Sai bayan ya fice tukunna gaji ta saki wani numfashi data riƙe tun ɗazu. "Uhhh nina manta ma da wannan basamujen yana gidan,gabaɗaya mutum sai murɗewa yake kaman wani dodo...abinnan yana cimin tuwo a ƙwaryah,kaf cikin yarana babu wanda yake ɗaga cikin plastic na ruwa saboda lalaci,amma shi kalleshi har tanki ma zai iya ɗauka. Narasa mai yakika yimasa yana yaro ya zama haka,kaima da ka sani ai da kayiwa yaranka,waɗannan masu kama da agwagin" Oh gaji har yanzu kina nan da ɗabi'arki ta zagin ƴaƴan ki,koma dai ya suke ai sune naki,kuma su Allah yabaki" "Ehh zakice haka man saboda naki jarumine,nawa kuwa ƴaƴan nasan in kinshiga ɗaki dariya kike musu,kin gansu kaman buta" Kasa riƙe dariyar ta inna mairo tayi,wanda hakan ya ƙara ƙular da gaji tazo har wuyah. "Kinga ya isa haka ni bazan biyeki ba,kujira yaxo ya daukemuku saniyar ku gyara muhallinku ku koma" "Mee kashin saniyar tasa na wata da watanni mu zamu gyara masa,zancen banza ma kenan,jakunan ku kuka maidamu keda shi komai,yanda kuke da iko da gidannan fah muma haka mukeda iko dashi" Jijjiga kai inna Mairo tayi cikeda takaici,ta dawo ai za'a cigaba daga inda aka tsayah. "Nina fara gajiyah da mitarki gaji,in sun dauke saniyar ku jirashi yazo ya gyara muku wajen,kuce sai ya tattare kashin tunda saniyarsa ce tayi" Yawu gaji ta haɗiye muƙutt,saboda tasan inna Mairo gatse tayi mata,hakan bazai taba faruwa ba.
__***__
A zaune take a gaban wuta ta haɗa gumi sharkaff tana suyar awara,gabadaya hankalinta yana wajen,buƙatar ta ta gama soye uban taragon awarar dayake gabanta. Dama sana'arta ce tun tale-tale kowa yasan ta da ita. Atika ce ta shigo ƙofar da sauri daga wajen inna Mairo take,kana ganin yanda take zumuɗi kasan gulma ce take cinta a rai. Ɗaga kai gaji tayi ta kalleta tareda mikamata wata awarar wacce ta suyah. "Hungo dan Allah atika zubawa farida Ta ɗari biyu ta kaiwa wani a waje,sannan kema kizo ki kintsa ki tafi wajen tallen ki,kuma maza ki hanzarta kada a gama siyan na kowa a bar naki yayi kwantai mana. Kince nayi miki da ƙwai nayi miki,amma tun ɗazu sai yada kai kike kinƙi tafiyah" "Ohh gaji zan tafi dai,yaushe ma ranar tayine wai,wani abu fah nazo dashi nake son na faɗamiki. Wai kiji ashe Goje aure zayyi?" Tsayawa ta juya awarar tayi tareda juyowa tana kallon Atika,alamu duk sun nuna bata yarda da abinda tace ɗin ba" "Ke bana son ƙarya,kaff garinnan wacece zata auri wannan dodon,in zakiyi ƙarya ma kiyi wacce kunne zai yarda da ita" "Wlh gaji da gaske nake,kuma gobe nema ɗaurin auren,gashinan inna Mairo ta gyara ƙofar gojen,kuma yanzunan aka kawo mata saƙo,kayane a ciki sabi na mata ta siyah wai na Amaryar ne" "Ke ƴar nan,ƴar gidan wanne shashan ubanne zai bawa goje ƴar sa,kalan ya danneta sai ƴaƴan hanjinta sun fito nan take?" "Uhm ai bakiji ma abinda naji bane jiya a wajen talle,har nunamin itama akayi,gata kyakykyawa da itah,ƴar gidan Mijin su inna rammah ce fah ƙawarki,wai a wajen caca dasukayi da goje ya cinyeshi,shine da bashida kuɗi yabashi ita" Sakin baki gaji tayi tana kallon atika kaman ta samu TV. "Duk yaushe haka ta faru a garin bansani ba uhm,barina gama suyar awarar nan zanje gidan naji komai ai" "Ko kuma ki bari sai da daddare ba,kinga babu wanda zaisan kinje,ni labarin naji wai ƙawar indo ce ma nan maƙwantanmu" "Wai tagamu da ƙaddara,muma da muke gida ɗaya dashi muke ganin takanmu balle ita mai zama dashi? Amma kuwa Mairo bata kyauta ba,duk ana wanann zancen bata faɗawa malam ba,saboda sun rainashi basa ganinsa a uban goje koh? Bari kuwa ya dawo da faɗamasa yanda ake ciki,duk wacce za'ayi ma ayi" Tafaɗa tana cigaba da suyar ta.
___***___
[Sumaimah a mahangar gani]
A zaune nake ina tilawar qur'ani,yau wacce rana banje talle ba,tunda akayi auren masu zuwa tallen ban taba fashi ba sai yau. Ban san na saba da zuwan tallen ba sai yau,dan jina nake duk wani iri tun safe,na rasa ma mai zanyi a gidan. Abinci dama banice nakeyi ba su suke kayansu,iya abincin siyarwar ammi kawai nake sai shara da kuma wanke wanke wani lokacin,saboda duk mai abinci burinta ta gama ta kwasa da yawa itada ƴaƴan ta. Wannan mummunar al'adar dasu ce yasa na huta kokuma nace na tsira daga yi musu girki. Bayan nagama karatun shuru nayi ina tunani,inason yin karatu mai zurfi,amma nasan hakan bazai taba yiyuwa ba,musamman ta muka taso a gidan da babu wanda ya damu da wani abu wai shi ilimi. Alamar takun sawun mutum naji,hakanne yasa na buɗe idona,Asiyah ce a tsaye akaina tana min kallon marar daraja. "Wai kizo inji ammi tana nemanki" Kawar da idona nayi akan ta tareda cewa. "Kice ganinan zuwa" Bata sake cewa komai ba tabar wajen,tafiyar ta bani da kallo,bansan lokacin da dariyah da kubcemin ba. Tafiya take tana turo kunkumi baya,ƙirji kuma gaba,wanda yake kaman allo babu komai a jikinsa,dan ko ƙirgen danginma bata fara tukunna. Hmm nace a raina tareda cewa....'in kikayi haƙuri ma nono kam zai fito miki har ki rasa yanda zakiyi dashi indai kinyi gado. Dan ammi Allah yayi mata arziƙin nono har cinyarta suke tabawa,inda tanada ƙiba da za'ayi mutanennan ne masu nonon su yafi girman ɗansu idan suka haihu,amma kasancewar rayuwar tada tsinci kanta sai yazaman basuda girman sai tsayi,in bata saka riga ba sai suyita rito kaman igiya.... Kunkumine dai da ƙyar ki samu,dan kaff ƴan ɗakinnasu a shafe suke ta baya. Kawar da wannan marar amfanin tunanin nayi na tashi zuwa wajen ƙiran da akayi min. Yanzu nagama kuwa tunanin yanda take,ina shiga ɗakin da ɗaurin zani a kunkumi na sameta,tana goge tsakar daƙin dan ba laifi tanada ƴar tsafta,shiyasa nake sallah a ɗakinnata da rana hankalina kwance. "Ammi gani,Asiyah tace kina ƙirana" Ɗagowa tayi ta kalleni saikuma tace. "Ohhh ehh haka,zauna barina gama wannan goge gogen tukunna,ai takaicinnan ya isheni,ace bakada ƙaramin yaro,amma ko yaushe kana cikin goge fitsarin yaran wasu can" Ban tofah komai ba a cikin sababin da takeyi,sai zama kawai danayi ina jiran ta kaman yanda tace. Bayan ta gama wata leda ta miƙomin baƙa da kaya ciki. Mamaki ne ya cikani,ban yi ƙasa a gwiwa ba na tambayeta. "Ammi wannan kuma na menene" "Mairo ce ta kawo ɗazu wai kayanki ne" "Mairo kuma...." "Innar goje" Tayi saurin katseni,dan tasan konayi nazari akan sunan bazan ganota ba. Saurin a jiye kayan nayi kaman wanda suka ƙona ni,kuma hakane ƙona ni sukayi a zuciyata. Hannu na ɗora akan ƙirjina ina ƙoƙarin hana zuciyata fitowa daga cikin ƙirjinnawa,dan naga kaman hakan take ƙoƙarin yi. "Sumaimah yakamata zuwa yanzu kin fara kwantar da hankalinki,domin razanar da kike ko shiga ƙunci bashi zai hana a fasa ba,koda an fasa kaiki gidan goje to babanku bazai iya biyan kuɗin dayake binsa ba,karki manta in akwai kuɗin goje a wajenka to duk bayan wani lokaci ƙaruwa yake har sai sanda ka biyashi,in kuwa kaki biyansa to ranka yake ɗauka a matsayin kuɗinsa. Kinga kuwa in kinga an fasa aurennan to saidai ya ɗauki ran sa kenan a matsayin kuɗinsa,shin zaki iya zuba ido ya kashe mahaifinki ne kina ganin kuma zaki iya cetonsa?" Shuru nayi ina saurarenta,zancenta gaskiya ne duk da kuwa ina jiyo son kai a cikinsa,da ƴar ta ce za'a kai gidan goje bazata bari ba,saidai uban kowa ma ya mutu a gidan. Amma ni ji yanda take zaromin bayani dallah dallah saboda na amince,tafi kowa sanin kuma inna shiga gidan nima bazan fito da rai ba a hannunsa,saidai kuma ya zanyi dama kullum amfani ake da sanyin rai na da kuma karayar zuciya ta,ga kuma bugu da ƙari banida gatan dazai tsayamin a wannan cutarwar da ake shirin yimin. Kaman yanda ta faɗa kuma bazan iyah guduwa ba ya kashe mahaifina,duk da baya yimin abinda uba ke yiwa ƴaƴan sa,amma shiɗin mahaifina ne bazai kuma tashi daga wannan matsayin ba har abada. Gashi kuma shikaɗai ya ragemin a duniyah,bansan ƴan uwan mahaifiyata ba ko ɗaya,tun ba ƴar nan bace a yawon ci rani ya aurota,bayan yayi mata ƙarya kala kala ta yarda ta biyoshi garinsu,duk da taga ba haka bane amma ta zauna dashi,saidai mai hakan bai isaba saida matansa suka kasheta. Wannan zaluncin har ina? Kukane ya kubcemin wanda ammi take ganin na auren goje ne,amma va haka bane,abubuwan da suka haɗu sukayimin yawa na shekara da shakeru nake son na rage zafinsu da kukan. Bata rarrasheni ba bata kuma hanani ba,saima tashi datayi tabani waje tana min kallon tausayi,bazanga laifinta ba don tayimin iya ƙoƙarinta a matsayinta na mariƙiyata,kuma ina yabama ta bazan taba mantawa da halaccinta ba har abada,koma mai zanji tayimin a baya,matsayinta danake gani na mahaifiya bazai taba bacewa daga kan idona ba. Kayan na ɗauka cikin sanyin jiki na nufi ɗakinmu wanda zuwa gobe zan barshi na tafi wata rayuwar,ban taba kawowa barin gidan a wannan lokacin ba,dudu zancen auren bayyi sati ba da farawa,gashi gobene ɗaurashi uhmm rayuwa mutum yana nasa Allah ma yana nasa..
Wayyo nikam har banaso gobe tayi na rubuta auren Sumaimah da goje,ku kanku kunsan bata dace dashi ba kohhh........duk mai wata idea to muhaɗu a commen secition toh🤣🤣🤣
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977 Auwal Sadiya First bank
Ko katin mtn ta nan 09035784150
VTU ta nan 2347068390570
Shaida kuma ta nan 09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[08]