Sanadin caca book 2 complete - Chapter 22
Sanadin caca book 2 complete Chapter 22: Sanadin caca book 2 complete Chapter 22. Basuja lokaci sosai ba suka isa garin su Sumaimah Dabagayi, A baƙin ƙofar…
1,349 words
Basuja lokaci sosai ba suka isa garin su Sumaimah Dabagayi, A baƙin ƙofar gidansu sukayi parking,dan ko gidan su gaji basuje ba,taje can ita tasani aniyarta ta bita. Sumaimah ce da Deejah suka fara shiga gidan,shaddace a jikinsu iri ɗayah maroon. Deejah na riƙeda hannun Sayyid saikuma Sumaimah tana riƙeda jakarta. Tun a bakin ƙofah da sukayi sallama matan gidan suka fara riƙe baki,duk wanda yaganta ya ganeta sai koma ƙofarsa fesawa,kafin wani lokaci gidan ya cika famm da mutane. Ammi ce tayi ƙarfin halin cewa. "Sumaimah nake gani ni ƴasu,dama Musbahu yace mana zakizo,amma bai faɗi ranar ba,ashe wai goje ogansu ne a wajen aiki. Ikon Allah Allah mai yadda yaso. Wannan yarinyar fah kaman..... "Deejah ce baki ganeta bane?" Turo baki tayi jin yadda suke mata kallon kaman ba ita ba. "Deejahhh mai cin kazata dai koh" "Kiji inna rammannan in kazace saina baki kuɗin goma ma" "Bani kam ko kuɗin koko banida shi ki bani kinji" Dariyah tayi tana sosa jiki kaman mahaukaciya sabon kamu. Ganin kallon dasu Sumaimah sukeyi mata yasa ammi yimusu alamar kansu ya kuncene. Sallama hajiyah maryam itama tayi a cikin gidan. Anan ammi ta shimfiɗamasu tabarma suka zauna. Yaro aka tura ya ƙira ya ƙira malam uwaisu a bakin masallaci,dan yanxu ba aikin yi nan ya koma zama da dattijan anguwa. Yana shigowa turus yayi yana kallon su Sumaimah. "Wannan kamar......." "Baba nice ya kake ya rayuwa?" Kuka ya kece dashi tareda zama a ƙasan wajen. "Sumaimah ki yafeni da abinda nayimiki, na tuba nayi nadama nayi nadama" "Baba kadaina cewa haka komai ya wuce,sanadin caca yasakani cikin ha'ula'i amma kuma yasaka sanadiyyarsa na gamuda abokin rayuwata,muna fatan masuyi a yanzuma su daina." "Ina wuni malam uwaisu ya gida?" "Lafiya kalau ko kece....." "Nice mahaifiyar goje yanda kuka sanshi kenan" "Ahah anty Meerah kece koh?" Shuru tayi tana kallonsa,a tunaninta dai baisan sunan ba kuma wannan sunan? Zainab ce kawai take ƙiranta dashi. Tashi yayi daga wajen ya nufi dakinsa,can sai gashi da wani hoto ya miƙawa hajiyah Maryam. Zaro ido tayi tareda cewa. "Zainab a ina ka samu hotonta,wanda muka ɗaukane a graduation" "Itace ai mahaifiyar Sumaimah dama bansan garinta ba da asalinta taƙi faɗamin har ta koma ga mahaliccinta" Kuka hajiyah maryam ta dungayi tana fadin. "Rashin riƙe maganata ne yajawo komai,dama duk neman da muka miki kina raye?,Allah ya jiƙanki yamiki rahama. Sumaimah ashe ke ƴata ce bansani ba,ke ƙanwar Neelah ce uwa ɗayah. Wannan zainab ce ƙanwar Muhammad baban Ahmad,kuma mahaifiyar ki" Lokacin data gama bayanin sai sannan kowa ya fahimceta,Sannan kuma kowa ya gane irin haɗin da Allah yayi wanda bamai iya irinsa saishi. A ranar an taso da abubuwa da dama da suka wuce,ciki kuwa harda labarin ummah ta da baba ya dunga bayarwa. Ashe ni ƙanwar Neelah ce,ikon Allah. A sashen yah Musbahu aka sauƙi Ahmad dakuma driver,bayan munci abinci shiga wajennasa nayi. Yana zaune da waya a hannunsa yana dannawa. Sallama nayi ya ɗago ya kalleni. "Ummin twins ya gajiyar jiki dai?" Fadawa nayi jikinsa ya riƙeni kaman jira yakeyi dama. "Nagaji amma ba sosai ba,idan baka komai inaso muje na nuna maka wani waje" "Is not fair ma,meyasa ban tuna komai bane har yanxu?" "Miye kake sauri,likita yace zaka tuna ai muje na nuna maka wani waje,inkuma bakaso toh" "Inaso muje" Mota muka shiga mu biyu,nuna masa hanya nake har muka iso anguwar tamu ta da,alama nayi masa ya tsaya kana na fitah. Wata daba na nufah inda na hangi su yawancin ƴan kungiyarsa ne a wajen,hadda Tunga yanata surutu na siyasa. A raina nace mai hali baya sanjawa. Sallama nayi musu,a ciki Tunga ne kawai ya ganeni,bayan mun gaisa alama nayiwa Ahmad akan ya ƙariso. Kallonsu yake da alama bai sansu ba,yayinda su kuma suke masa kallon mai kama da goje. Ganin hakanne yasa nagane dole nice mai share tantamar nan. "Tunga kaida sauran ga goje,kaikuma gasu tunga wanda kukayi ta gwagwarmaya tare" Tun kafin na ƙarisa Tunga ya riƙe hannunsa kaman zayyi kuka. "Ogah oga ina kashiga mukayi ta nemanka" Murmushi yayi tareda yimusu takaitaccen bayani. Haƙiƙa yanda aka bashi labarin sudin suwaye a wajensa abune da bazai manta ba. Kuɗi ya basu tareda address dinsa na abuja kan suzo su sameshi zai Sama musu aiki. Nima naji daɗin abinda yayi sosai,domin sun cancanci hakan a wajensa. Bayan ya gama dasu hannunsa narike muka nufi hanyar zuwa jeji,da alamar mamaki a fuskarsa amma baice komai ba har muka isa bakin kogon da bazan manta ba. "Bazan taba manta wannan wajen ba,anannne naji abinda yake cikin zuciyarka gameda ni,ananne muka shirya a matsayinmu na ma'aurata,a nanne nayi jinyarka lokacin da duniya babu wanda yasan hakan saini da Tunga. Kuma shine sanadin shiryuwarka ka fita daga ƙungiyar BC." Shiga mukayi cikin kogon na tsugunna a inda mukayi ajiyah. Ganin ina bude wajenne ya tayani muka buɗe. Akwatin daya sato a daren na fito dashi na bashi. "Wannan fah" "Abinda kake tunanin ƙungiyar BC sun sace,kaine kayi rai a tafiyar,Sannan baka kai a ganka ba Neelah ta kawoka nan wajen a ranar tayi maka maganin gaggawa ta tafi. Nice na kulada kai harka warke. Na rufe sirrin inda abin yake ban faɗawa kowaba,tunda Allah yasa munzo wajen yau gashi na dawo maka dashi,saikayi yanda ya dace dashi" Buɗewa yayi yaga babu abinda ya sauya a ciki. Kallon so da ƙauna yakeyimin kowacce tayi aikin jarumta. "Nikuwa mai zance dake yake wannan baiwar Allah na abinda kika min a rayuwata?" "Kace Allah ya barmu tare cikin farin ciki,aminci da kuma ƙaunar juna har ƙarshenmu" "Wannan yana cikin Addu'a ta a kullum" Rungumeni yayi ina dariya shima yana Murmushi....ohhh ina son mijinah.
Bayan munje naso na kwana biyu amma Ahmad yaƙi,saboda inaso na zaga danginnamu, duk da a baya basu nunamin ƙauna ba,amma badansu zanyi ba ai. Haka ina gani mukayi kwana ɗaya muka kamo hanyar dawowa, zuwa gidana kuma cikin dangin mahaifiyata,wacce yanzu nasan asalinta.
Bayan shekara biyu da haihuwar ƴan biyuna dukka mata, Maryam da zainab wanda ake ƙiransu Islam da ilham. Dukkansu babu mai kamata,Neelah islam ta iyo,ilham kuma hajiya Maryam har jikin. Cikin ƙoshin lafiyah na rainesu har na yayesu,lokacin kuma Sayyid yashiga makaranta,wanda yadawo hannuna da zama. Dan so nake nayi masa tarbiyyah yanda ya kamata bata iyayen zamani ba. Bayan yayennasu makaranta na shiga Jami'a,zan karanci Qur'anic science,dan inada burin sanin ilimi a fannnin,a lokacin ne nayi planing na haihuwa,soyayya kawai muke sha nida mijina Sannan kuma ina samun lokaci na yarana sosai.
****
Ina faka motar dana kasheta shigowa cikin gidan nayi,da islam naci karo ta dawo daga sashen inna larai,wandonta ya jiƙe da fitsari,jijjiga kai nayi dam takaci,magana saita siyarka amma tana fitsari a wando. "Daga ina kike islam?" "Gujin inna nake Unni" "Ina ɗayar taki?" "Tana bacci gujin inna" "Kekuma kina yanda kikaga dama koh,yayah fah yana gidan Ummee ko wajen inna " "Bashu dawoba da abbah" "Hmm wuce to muje nacire miki wannan wandon" Saida na gyara mata kafin nashiga kitchen a gurgune,ina cikin yi naji muryar Ahmad a falo shida yaransa. Jallop ɗin taliya nayi na fita da itah. Sannu da dawowa nayi masa kafin na juya zan shiga ɗaki.. "Hayatee ke bazaki ci abincin bane zaki tafi yau?" "Ahah banajin yunwa beb wanka ma nakeson yi,kuci abincinku kada ya huce" "Ahha baki isa ba dawo ki zauna,banason zama da yunwa,zona baki a baki" Zaro ido nayi bayan na zauna a gefensa,ganin zai bani kunya a gaban yara na saka hannu mukaci tare. Kallonsa nake yanda yake sakawa su ilham abincin a baki. A raina nace Alhamdulillah da wannan baiwar da dddaɗar rayuwa.
Nima sainace ALHAMDULILLAH a fili tareda ajiye alƙalaminah. Kuyi haƙuri ta katse littafin a haka,banida zabine exam ta matsoni. Da fatan zaku fahimta. Kowa in bai masa ba yasake maimaita ƙarshen a kundin hasashensa😁.
Godiya ga dukkan makaranta,musamman masu binsa yana da'irar rubutu na gode da kasancewa dani nagode sosai. Taku a kullum SADI-SAKHNA ke muku sallama da BISSALAM. sai mun haɗu a wani sabon littafin wanda babu rana a yanzu gaskiya. Saboda sabuwar rayuwa na shirin tunkarata ta aure,ina barar addu'ar ku Allah yasa yazomin da sauƙi. Nagode.
THAMMAT BIHAMDULLAH......✍🏼