Sanadin labarina complete novel - Chapter 11
Sanadin labarina complete novel Chapter 11: Sanadin labarina complete novel Chapter 11. Da sauri ta shiga goge hawayen da bata san ainahin na menene ma ba,…
4,491 words
Da sauri ta shiga goge hawayen da bata san ainahin na menene ma ba, ta mike tabi bayan aunty zuwa bangaren Baban, suka shiga da sallama ya amsa yana kallon Jiddan da kanta yake a kasa tausayin ta na kamashi
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (22)
***A k'asa ta zauna daga farkon falon, Aunty kuma ta zauna daga gefen Baban, kallon tausayi yake wa Jiddan dan sai da ya gama kallon ta sosai sannan ya shiga bayani cikin salon da yasan zai wanke kansa ya kuma wanke Baffa, sannan ya samu ta karbi abinda suka zo mata dashi, nasiha sosai yayi mata akan rayuwa sannan ya kawo maganar auren, wanda ya sakata jin Abu ya tsirga mata tun daga sama har k'asan kafafunta, ta kalmashe kafar cikin son rage abinda take ji din duk da bata san menene ba.
Dukkan maganganun da Baban ya fada mata sun yi matukar tasiri a gareta, ba zata iya taba kin Ya Tariq ba, tunda har ya fito daga tsatson Baba, mutumin da yake da girma da k'ima a idanun ta. Tana kyautata masa zato, tana fatan yayi halin Baban ko da ba dukka ba. Maimakon ta koma dakin ta, sai tayi bangaren Yaya dan tasan idan ta keba kanta toh dole tunane tunane zatayi tayi, gwara tazo ko ta rage daren.
***Tunda suka bar kofar gidan su Jidda yake kwance a dakin Farouk, kamar wanda ruwa ya cinye haka yake ta kwanciya, babu abinda ya saka acikin sa, sai wani irin suya da kirjin sa yake, babu yadda Farouk be yi dashi ba, akan ya saka ko da wani abu ne a cikin sa, amma yaki sam. Sallah ma da kyar ya tashi ya hada azahar da la'asar haka magriba da Isha. Kansa na tsakankanin kafafuwansa bayan ya idar da sallar Farouk ya sake shigowa, ya dube shi a in da yake zaune ya girgiza kai,ya kira sunan shi, be amsa ba sai dagowa da yayi ya kalle shi
"Bro dan Allah man up mana, ka tashi muje wajen Safeera muyi mata magana, may be ta iya convincing Jiddan, ni nayi mamaki ma wallahi, na zata kace bata da saurayi ko?"
"It's too late, Jidda bata so na, nasan kuma ko shekara dubu zan bata ba zata taba so na ba, na gani a cikin idon ta. Dama nayi ma kaina alkawari idan har tayi rejecting dina ba zan takura mata ba, zan hakura da ita. You can't force anyone to love you."
"Amma kuma you can try your best to win their heart, kayi saurin given up."
"Ba zaka gane ba, inaji a raina ba zan iya cigaba da rokonta ba, har kusan kasa na kai ina rokon ta, and she said no, me kake so nayi?"
"Fight for your love mana, don't be a looser, ka bata time ta kara tunani sosai, dama kamar kayi rushing abun, kaga fa akwai yarinta akan su, kila ma bata san menene soyayya ba, she's just nervous."
"Kasan kiyayya? Ita na gani a cikin idanun jidda, na hakura, bata so na ba zata kuma taba so na ba."
"Shikenan, Allah ya mana zabin alkhairi, karka wahalar da kanka toh, eat something, kalli yadda ka koma, mom ta kira wayar ka na daga nasan tana jiran ka."
"Muje ka sauke ni, ba zan iya cin komai ba."
"Ko tea ne kasha dan Allah "
"Zan sha idan na koma."
"Ok muje toh."
Hannu ya mika masa ya tashi, yayi kamar zai fasi sai da Farouk ya tallafe shi, sannan ya taimaka masa zuwan wajen motar.
***Yadda Mama taga rana haka taga dare, kamr ta jawo gari ya waye haka taji. Ana idar da sallah aka kaita airport ita da Safiyya sai securities biyu, kafin tara tana Kano, kai tsaye doshi part din Baban lokacin ko tashi be ba, Aunty na falon tana hade masa wasu takardu waje daya, knocking akayi, ta tsaya da abinda take cike da mamakin wanda zai knocking a part din Baban dan ko Usman baya biyo ta bare tace shi ne. Wajen kofar taje ta dan leka ta jikin dan opening din dake jikin kofar bata ga kowa ba, sai tace waye
"Matar gidan ce."
Rass! Gaban ta yafadi jin muryar Maman, ta tabbata ba zuwan lafiya bane musamman da tunda tatafi idan ba sallah ba, babu abinda yake kawo ta, murda key din tayi ta bude kofar, ta matsa baya da sauri ta shigo ciki.
"Sannu da zuwa." Tace ganin tana mata kallon sama da kasa, bata amsa ba, sai jan dogon tsaki da tayi cikin bacin rai tace
"Munafuka algunguma, muguwa maci amana, saboda ke bakar makira ce, shine kika san yadda kika yi, kika shiga kika fita kika sa aka kakabawa Tariq gwanjon yarki, bayan yadda kika kakabawa mahaifin su kula.da ita, wato dan ina kyale abubuwa ina dauke ido shine har kika samu damar hada wannan shirmammen auren wanda bashi da maraba da auren gangan a waje na."
"Haba Maman Fauwaz, kamar yadda kika ji labarin auren nan wallahi haka naji, bani na hada ba, Yaya ce ta hada kuma nima kaina ba wai inaso bane."
"Dallah rufe mana baki, ai ke babu kalar munafuncin ki da ban sani ba,zanzo kanki bari na gama da shi."
Sai tayi fuuu ta bude bedroom din Baban ta shiga. Zuciyar Aunty ce ta shiga yi mata zafi, ta gaji ta gaji da cin kashin da aunty take mata, ta gaji da tozarcin ta, tana kyale ta ne ba wai dan tana tsoron ta ba, sai duk dan a zauna lafiya, ta amsa tayi laifi a lokacin da ta auri Baba amma ya zatayi da kaddararta? Shikenan ace abu yaki ci yaki cinyewa? Ta kai karshe a wannan karon sai dai duk abinda zatayi tayi amma ta daina bin ta. Kin fita tayi daga dakin kamar yadda take yi a baya, ta cigaba da aikin da take tana jiyo hayaniyar Maman sama-sama.
**Tunda ta shiga dakin ta saka Baba a gaba tana banbanmi, me kulata ba, yana jinta duk abinda zata fada ta fada aure dai ya riga ya dauro, kuma tunda har Jidda ta amsa masa da ta amince shikenan, bashi da matsala da kowa dan yayi wa Yaya abinda take so. Duk yadda Mama taso tunzurashi sam yaki bata hadin kai, cigaba da danna wayar sa yayi rabin hankalin sa na kanta rabi na wayar. Kamar kunnen sa ne yake masa gizo sanda yaji maman na cewa
"Duk wadda ta tsara hada auren nan wallahi ban yafe ba, ko wacece ta cuce ni."
Sai ta fashe da kuka ganin Baban ya ki kulata, saukar mari taji akan fuskar ta, baban dake tsaye yana huci a gabanta ya nuna ta da dan yatsa
"Duk abinda zaki fada a kaina ko kan mahaifin jidda ko Halima ko ita Jiddan duk ki fada ba zan hanaki ba, amma a hir dinki kika sake sako mahaifiyata, dan dukkanku albarkacin ta kuke ci, kuma wallahi wallahi wallahi, kinji na rantse ko? Idan har kika ce zaki daga min hankali akan dan na yiwa Tariq aure, wallahi sai na nuna miki kuskuren ki,kuma ko da wasa kika kira Tariq ko kika saka yaran nan suka kirashi da maganar wallahi sai mun samu babbar matsala."
"Naga sam baki san kaddara ba, ba kuma ki isa ki ce zaki fadi magana akan Yaya ba, baki isa ba wallahi."
Wajen da ya mareta, ta rike cike da tsananin mamaki, tunda suke da Baba, be taba ko da daga mata murya ba, bare har yakai ga taba lafiyar jikin ta,komai take so tun daga zamanin kuruciya har gobe shi yake mata Ko kwakkwaran motsi ta kasa yi daga wajen da take tsaye, ta san shi sarai bashi da sauki idan har yayi fushi, bare fushi irin wannan da bata taba ganin yayi ba. Ficewa yayi ya barta a dakin,ya samu Aunty a falo ganin yanayin sa ya sakata yin shiru dan da har zatayi magana, har ya kai kofa sai ya juyo yace.
"Ku fara shirye-shiryen tarewar ku a wannan satin."
Daga haka ya saka kai ya fice, be jira yaji ko ta amsa ko bata amsa ba. Kasa fitowa Mama tayi daga dakin saboda tsabar kunya, a mareka kishiya tana ji ai ba karamin zubar maka da mutunci bane, a tunanin ta Auntyn zata fita bayan Baban ya tafi, taji shiru shiru, sai kawai ta yanke shawarar fitowa, ta fice fuuu, bata ko dubi part din Yaya ba, ta fada mota, dan dama a chan main house dinsu aka sauke Safiyya, saboda haka chan ta koma, ta samu Hajiya Babba da maganar, da duk abinda ya faru da abinda Baban yace, shawara ta bata akan ta bar komai har zuwa dawowar Tariq din, dan suna da yakinin ba zai taba amincewa ba.
Da daddare suka koma, ta tattaro su ta fada musu abinda Baba yace akan maganar fadawa Tariq din, dama Safiyya da Fauwaz ne kawai suke magana dashi, kuma wajen kwana uku kenan ma basu yi magana ba, dama kuma Fauwaz ba zai fada ba dama Safiyya ce itama tunda aka yi maganar ba zata fada ba.
***Mom na zaune a falo Isma'il ya shigo, yana tafiya kamar wanda zai fadi,
"Innalillahi, me faru?"
Tace tana yin wajen sa, a cikin kujerun falon ya zauna yana jujjuya kansa da yake masa wani irin mahaukacin ciwo, Safeera dake kan dinning tana dinner ta taso da sauri, tazo ta durkusa a gabansa tana tambayar
"Ya Isma'il me ya same ka?"
Da kyar ya bude bakin sa, da yayi masa nauyi yace
"Jiddaaa."
"Me ya samu Jiddan?"
"Ba...ta..so..na."
ya fada a rarrabe saboda tsabar yadda yake ji, ga yunwa da ta hadar masa ta sake taimakawa wajen rashin kuzarin sa.
"Kirawo min Dr Aminu Safeera, yi sauri yazo ya duba shi, wannan abu har ina, dama wallahi kamar nasan za'a yi haka, naji tsoron ganin yadda kake son yarinyar nan, kalle ka yau daya Ismail, akan soyayya ka koma kamar wanda yayi jinyar shekaru?"
Jujjuya kansa yake, Safeera ta kirashi ta dawo gaban Ya Isma'il din cike da tausayin sa, ita kanta ta hango faruwar hakan dan tasan Jidda, tasan idan har bata son shi ba zata taba barin shi yayi ta fama ba, zata fada miki ne kai tsaye, sannan kuma ba zata taba sauya raayinta ba.
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (23)
***Kafin isowar Dr Aminu, zazzabi me zafin gaske ya rufe shi, sai rawar sanyi yake saida aka kashe AC falon da duk wata na'urar sanyi me alaka da wajen, daki ya taimaka masa ya kaishi ya kwanta,sannan ya hau examining nashi, ya gama ya rubuta masa magani sannan ya daura masa drip saboda yadda jikin sa yayi weak gashi babu komai da ya saka a cikin sa, fita yayi yaje ya kawo magungunan yace a bashi idan ya tashi ya sha, sannan yayi musu sallama ya tafi. Jigum sukayi a dakin nasa cikin yanayin rashin jin dadi har Daddy ya dawo ya same su. Baya hada yaransa da kowa da komai, shiyasa Mom na kiran sa ya taho gidan ba dan ya gama abinda yake yi din ba, a dakin suka tare gaba daya sai Safeera ce da ta soma jin bacci mom tace taje ta kwanta. Dakin ta, ta shiga maimakon ta kwanta sai ta dauki wayarta duk da kusan sha daya na dare ne, ta kira Jiddah wadda take kwance tana ta juye-juye, tana ganin kiran taki dagawa dan bata san me Safeeran zata ce ba haka itama bata san amsar da zata bata ba. Da safe ya tashi da dan kwarin jikinsa saboda drip din da yasha, Daddy ya gani a dakin yana kallon sa, ya taso da sauri yazo gaban gadon nasa,
"Isma'il, ya jikin naka?"
Yace ba tare da yasan dalilin ciwon nasa ba dan Mom bata fada masa ba, dan yatsine fuska yayi kadan sannan yace
"Naji sauki Daddy."
"Toh Allah yakara sauki, bari naje na shirya, ka tashi kayi sallah, sai a kawo maka breakfast saboda ka kara samun kwarin jikin naka, zazzabi bashi da dadi."
"Tohm, dan Allah amma Daddy inaso na tambaye ka wani abu."
"Ina jinka." Ya tsaya da shirin barin dakin da yake
"So nake a matso da tafiyar karatun nan, ko cikin next week ne."
"Me yasa? Da kace baka shirya ba, an samu change of plan ne ko me?"
"Eh Daddy, yanzu inaso natafi,as soon as possible, please Daddy."
"Ok, ba damuwa ka bari ka kara samun sauki, sai muyi maganar fixing date din."
"Ai na warke, please Daddy."
"Shikenan, ka same ni a falo idan ka gama."
"Nagode."
Tapping bayan sa yayi, ya fita shi kuma ya fada toilet. Tun last two months Daddy yake masa maganar masters da zai fara, ya dinga jan abun saboda ya samu Jidda idan yaso suka daidai ta, sai ya tafi tunda ba yawa just two years ne be ma kai ba, har yaje ya dawo lokacin ta shiga university ta fara karatun ta itama, that was his plan, sai gashi komai ya ruguje a cikin yan awowin da ba su gaza ishirin da hudu ba. Ganin haka ya saka shi yanke shawarar tafiya kawai tunda hatta admission yana dashi a hannu da komai, visa kawai zai yi applying wadda yake saka ran in a week ma zata zama ready, babu amfanin zaman sa tunda har Jidda ta k'i shi, bashi da amfanin cigaba da zama gwara yaje ya amfani lokacin da yake dashi.
***Duk da Jidda taga kiran Safeera kuma ta sake gani ma da safe amma ta kasa kiran ta, bata so ko kad'an su samu matsaala, ta san kuma d'aga wayarta a lokacin zai iya zama matsala tunda ta san a yadda Ya Isma'il ya fita ta kuma tabbatar da sun san abinda ya faru. Aunty ce ta shigo daga part din Baba, ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, a yanayin da taga Mama zata iya komai dan ganin auren nan ya baci, bata so jiddah ta shiga matsala ko kad'an musamman a irin wannan karancin shekarun nata, dama dai duk abinda ta guda kenan, dan dai su iyaye maza basa bawa ire-iren wadannan abubuwan muhimmanci ko kadan, tayi mamaki da har Maman ta dauko kafa tazo, har kuma suka samu sabani da Baba akan hakan wanda ko lokacin aurenta da Baban basu samu irin wannan matsalar ba dan Mama mutum ce me matukar kissa da iya takunta a wajen Baban dan duk wuya bata taba bari yaga aibun ta, amma kuma a yadda ta kasa dauke idon ta akan wannan auren ne ya sakata sake tsorota da lamarin. Wayar Jidda ce ta sake kara a karo na uku tun shigowar aunty, ta kalle ta cikin son neman karin bayani tace
"Ki daga mana ana ta kiranki kina ji."
Yadda Auntyn tayi sounding yasa ta gane ranta a bace yake, daga wayar tayi sannan tace
"Hello Safeera."
Wani kallo Aunty tayi mata, sai ta tashi sum-sum-sum ta bar falon zuwa dakin ta, girgiza kai kawai Aunty tayi,ta shige daki itama ta hau tunanin yadda zasu fara hada kayayyakin da zasu bukata a chan din dan ba komai zasu dauka ba.
***Shiru jiddah tayi tana sauraron banbamin masifar da Safeera take akan kin daga wayarta bayan tasan dole ne ta kira ta, sai da ta gama tas duk da bata sako maganar Isma'il din ba sannan tayi shiru Jiddan ta bata hakuri
"Bana kusa da wayar ne, kiyi hakuri."
"Ko dai kika ki dagawa ba, kar nayi miki maganar Ya Isma'il."
"Ba haka bane ba fa."
"Toh me? Ni dai ban ce miki dole ki so shi ba, babu dole ai a soyayya, dama kiran ki nayi muyi wata magana amma shikenan."
Ta wayance kawai dan bata ga amfanin dawo da maganar baya ba, ita da kanta Jiddan idan taga ta share zancen zata saki jikinta har ta bata labarin abinda ya faru.
"Dan Allah fada min, wacce maganar ce?"
"Ah ai kuma shikenan, idan kin matsu kina so kiji ki kirani da kanki."
"Toh zan kiraki, kinsan me ya faru? I'm clueless gaba daya, bansan ma wanne irin tunani zan ba."
"Oya,tell me ina jinki."
"Uhm... Jiya aka daura min aure."
"Wait what!!!" Ta fada da dan karfi dan yadda maganar tayi shocking dinta
"Kamar ya? Ban gane ba, aure kuma, da wa?."
"Ya Tariiiiq."
Dip Safeera ta dauke wuta, kamar bata kan wayar, sai da ta ja wasu yan sakanni sannan tace
"Yanzu dama all this while jidda kinsan yayanki za'a aura miki amma kika ki fada min,haka kika dauki friendships dinmu? Baki yi trusting dina ba ko? Shikenan nagode."
Ai kafin Jiddah tayi magana ta katse kiran, ta kalli wayar ta girgiza kai kawai, me neman kuka ce dama aka jefe ta da kashin awakai, dama zuciyar Safeern a kusa take da abinda ya faru tsakanin su da Ya Isma'il, sai kuma katsaham tace mata an daura mata aure bayan dah tana dan da hope din ko aka kara turawa Ya Isma'il din ya samu kanta, duk da tasan Jidda kaifi daya ce tun basu kai yanzu ba,idan tace yes toh babu abinda zai sakata dawowa tace no, haka ma vice versa. Sanin cewa sarai ko ta kirata ba zata daga ba, ya sakata tura mata sakon text message, tayi mata bayanin abinda ya faru a takaice, ta ajiye wayar daidai lokacin Aunty ta kwalo mata kira, da saurin ta, ta amsa ta fita dan ta lura sarai Auntyn a wuya take akan maganar auren nan. A daki ta sameta ta fito da kayan wardrobe dinta gaba daya, tana ware su,zama Jiddan tayi ta shiga tayata, anan take fada mata maganar tafiyar, shiru tayi dan bata kuma san kalar sabuwar rayuwar da zasu fada ba, tun bayan komawar Maman Abuja aunty ta samu yancin kanta, bata da wata damuwa dan idan ba sallah da akayi ba suka zo babu wani abu da yake hada su waje daya, shima har a gama hutun sallar su tattara su koma ba wani zama Maman take a gidan ba,kullum cikin fita take.l shiyasa yanzu take hasaso irin zaman da za'a yi, gata kuma, wanne irin tarbar Maman zata yi mata? Shin zata taba karbar ta kuwa a matsayin matar Baban danta? Toh wai me da sanin ta kuwa akayi auren nan? Sai ta tuna da sunan bararojin da ta taba kiran ta dashi cikin son nuna kaskancin ta, ajiyar zuciya ta sauke, dan tasan tabbas akwai kalubale babba a gabanta, amma koma menene tana rokon Allah ya duba ta, ya kawo mata sauki. Suna aikin Aunty na kokarin nuna mata rayuwa da kalubalen da yake cikin rayuwar aure, taana ji tana kuma daukar komai a kanta, har suka kammala aikin taje ta zuba abinci ta koma dakin ta, taci sannan itama ta hau ware kayan nata, tana daukar wanda zata bukata ta. Hakan ya jata har yamma dan sai da ta hada komai kaf dan zataje tayi kwana biyu a gidan su kafin ranar tafiyar da zata dawo ana I gobe. Sai da ta gama tas sannan ta dauki wayarta, taga reply din safeera, tayi murmushi kawai ta sake tura mata wani,
_"Wednesday zamu koma Abuja."_
Sakon na shiga ta biyo shi da kira, ta dauka tana murmushi dan tasan wata masifar ce
"Nima wallahi dazu na san da tafiyar." Tayi saurin cewa tana dariya
"Allah Jidda ko? Yanzu dan Allah shikenan tafiya zakiyi ki barni? Ni kadai ga Ya Isma'il shima tafiya zai,haba dan Allah."
"Zamu zo sallah fa, ko weekend nasan ba wai mun tafi gaba daya bane, ni ma ba son tafiyar nake ba, kinga achan zamu fara school ni da Amira shiyasa ma."
"Ai shikenan, zan shigo gobe."
"Ok Allah ya kaimu, sai kinzo."
"Amin, bye."
"Bye."
Maimakon ta ajiye wayar sai ta samu kanta da shiga photos din wayar, ta bude hotunan sa, tana dubawa,tana tuna wai mijin tane,an daura musu aure, bata san me take ji game da hakan ba, kawai tasan tana jin ta at ease, bata da wata damuwa ko fargaba a zuciyar ta. Ba kamar idan taga Isma'il ba, ba kuma kamar ace Isma'il aka aura mata ba, ta tabbatar zata iya bori akan hakan. Ya Fauwaz ne ya kirata, tana dagawa ya hau yi mata kirari
"Kaga amaryar Ya Tariq, kaga amaryar Captain Tariq, kaga amaryar international pilot, eh Masha Allah, ban taba ganin perfect couples irin ku ba, kun yi matukar dacewa, da za'a bada award za'a iya baku award din perfect couples of the year."
Dariya take tunda yafara maganar,
"Kai Ya Fauwaz." Tace farin ciki na mamaye zuciyar ta
" Allah da gaske Jiddo, auw Aunty Jidda."
"Na shiga uku, nice Auntyn?"
"Emana, kin zama matar Big B, ai dole ace miki Aunty."
"Kai dai Ya Fauwaz ka iya tsokana wallahi."
"Allah ba tsokana bace, da gaske nake. Har Allah, Allah nake ya Tariq ya dawo yaga amaryar sa, nasan ji zai yi kamar an tsunduma shi a aljanna."
"Hum umm." Tace tana giggling
"Toh ya ake ciki?"
"Alhamdulillah wallahi."
"Toh Masha Allah, dama nace bari na kira matar yaya, kar ya dawo yace mun bar masa mata babu kulawa."
"Ya Fauwaz ko?"
"Na barki lafiya toh."
"Nagode."
Wani irin dadi ne ya rufe ta, dan ba karamin dadin kalaman Fauwaz taji ba, ya bata kwarin guiwa sosai wanda har ta soma hasaso rayuwar ta anan gaba kad'an. Murmushi tayi tana lumshe idanun ta, ta furta a hankali.. Matar Ya Tariq
***Washegari da wuri Safeera tazo, suka shige daki suka shiga hira, har kusan azahar sannan ta je ta kawo musu abinci suka ci sukayi sallah, sannan Safeeran tace zata tafi dan Mom ma da kyar ta barta tazo dan dai tana son duk abinda suke so ne, mayafi ta yafa ta rakota gate in da driver gidan su yake jiranta. Hakurin abinda ya faru tsakanin ta da Ya Isma'il ta bata dan duk yadda taso dauko maganar da suna ciki Safeeran taki yarda da ta dauko maganar sai ta goce da ta sake daukowa sai ta shashantar da maganar ko ta nuna bata ma ji ba. Yanzun ma tsaki tayi kawai ta harare ta,ta shige mota. Part din Yaya ta wuce ta sameta kafarta na mata ciwo, ta dauko maganin da ake shafa mata, ta shafa mata a kafar sannn ta zauna tana rage mata zaman kadaitar. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (24)
***Kwanan ta biyu a gidansu, Baffa yayi mata nasiha da kashedi sosai akan abinda ya faru, ya kuma ja mata kunne sosai akan kar yaji kar ya gani, duk a tunanin sa zata bijire, be san da gaske take son abun. Wuni tayi ranar da tazo a gidan Saude wadda akayi bikin ta da kaka, bata samu zuwa ba lokacin suna examz, gashi hadda tsohon cikin ta, sun sha hira suka tuna da sannan ta dawo da la'asar sakaliya. Iya Lami nata haba-haba da ita,ta share ta kamar bata san Allah yayi ruwan ta a gidan ba, dan ko kad'an bata son matar dan babu kalar azabar da bata gana mata ba, akwai wani duka da tayi mata har yanzu da ragowar shatin dukan a gadon bayan ta abunka da fara. Shiyasa taki sakin jiki da ita sam bare ma su zauna suyi doguwar magana. Ranar da zata tafi Aunty ta turo aka dauketa, dan ta karasa abubuwan da bata karasa, dan da safe zasu tafi washegari. A tsakar gidan Yaya ta tarar dasu ana ta fama da Yaya tayi tsalle ta dire babu shegen da zai sakata shiga jirgi, idan kuwa akace dole toh ta fasa tafiyar, duk yadda Fauwaz da yazo yaso ya fahimtar da ita sam taki fahimta, kamar ma a tsorace take da al'amarin, gashi a wannan yanayi na insecurity babu yadda za'a yi a barta ta shiga mota, haka kuma a barta ita kadai ma matsala ce.
"Yaya menene?" Tace tana matsawa kusa da ita
"Yawwa gwara da Allah ya kawo ki, kiji dan wulakanci wai jirgi zamu hau idan zamu tafi."
"Eh Yaya, ba bata lokaci nan da nan zaki ga anje."
"Aikuwa banga uban da ya isa ya sakani hawa jirgi ba wallahi."
"Har Baba?" Fauwaz yace yana dariya
"Ko Kaka ne, ehe."
"Ah abun azimun ne, bari na kira Baban da kansa yayi miki magana, kila shi yayi convincing dinki."
"Duk ma me zakayi kayi, na gama magana."
"Muje ki zauna Yaya, ki daina yawan fada kina tada hankalin ki dan Allah."
"Toh yaran nan ne duk hanyar da zasu birkita min lissafi sun santa, ina dalili za'a ce dole sai na hau jirgi? Ai ba dole bace Habujan ko? A kyale ni dan Allah.".
Sai ta fara tari da karfi, saurin tallafa mata jiddah tayi, ta mika mata ruwa tasha tarin ya lafa, zata cigaba da sababi Jidda tayi saurin cewa
"Kiyi shiru karki sake tarin, ba in da zaki a jirgi, a mota zamu tafi ni dake sai su suyi ta hawa jirgin su."
"Yawwa toh idan hakan ne na amince."