Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 13

Sanadin labarina complete novel - Chapter 13

Sanadin labarina complete novel Chapter 13: Sanadin labarina complete novel Chapter 13. "Tam, zan taimaka maka, amma ka bani sati uku ayi shagalin bikin…

4,412 words

"Tam, zan taimaka maka, amma ka bani sati uku ayi shagalin bikin nan a gama, ni nasan yadda zan bullowa al'amarin dan nima ba wai inason auren naku bane, tunda kuma kace baka so ai an gama."

Kallon ta yayi a cikin ido, ta gid'a masa kai alamar eh, ta gimtse fuska kamar gaske,

"Shikenan tom, dan Allah kiyi yadda zakiyi."

"Dole na, yanzu dai ka kwantar da hankalin kar Babanku yace baka masa biyayya ba, ka barmun komai a hannu na, Kaje yanzu ka huta ka kwanta."

"Nagode Yaya, nagode sosai."

"Karka damu yiwa kaine."

Tace tana dariya

Fita yayi ta bishi da harara sannan ta rufo kofar ta

"Ja'iri zaka yi bayani ne, idan ma aljanun suka zugo ka daidai nake da su wallahi."

Yana fita yaji zuciyar sa ta dan yi sanyi, maimakon ya wuce bangaren su sai ya juya zuwa part din Auntyn dan yana so yaje yaga yarinyar da tsaurin idonta har ya kai ta yarda a hada su aure, sai ya nuna mata iyakar ta, da matsayinta dan shi ba sa'an ta bane, tukunna ma nawa yarinyar take? Dole ya koya mata hankalin da zata je ta samu Baba da kanta tace ta fasa. Knocking yayi a kofar da dan karfi, shiru ya sake kwankwasawa sai ya gwada turawa, ta bud'e ya shiga yana kallon falon da yake a share neat sai kamshin turaren wuta da yake tashi me sanyin kamshi, shak'ar turaren yayi ya kalli katotuwar television din dake tayi ita an kunna cartoon network. Aunty na part din Baba dan yau itace da gidan, shiyasa shirun yayi yawa masu aikin kuma duk sun wuce bq, tunawa da yayi da babu abinda yasa a cikin sa yasa shi tunawa da abincin da yaji kamshin sa dazu. Tana tsaye a kitchen sanye da doguwar sakakkiyar rigar bacci me dan kauri, kanta babu ko dan kwali tana tsaye gaban microwave tana warming abincin da akayi dazun don shi wanda Fauwaz ne kawai yaci sai Aunty da masu aikin. Tun da ta dawo daga wajen su dazun aunty tace a kai masa sai ta doje tace baya nan sun fita, har magriba Aunty ta sake tambayar Fauwaz yace eh ya dan fita be dawo ba, har ta gaji tace a saka a fridge kawai ta tafi part din Baban. Yunwa ce yanzu ma ta taso ta, bayan ta shaki kukan ta, ta koshi ta gode Allah, taji ciwo fiye da tunanin me tunani, amma ba zata taba bari ko Amira taga weakness dinta ba, dazu ma haka Fauwaz ya sake kiranta amma ta nuna masa babu komai, duk da deep down she's hurt, very hurt da ta kasa iya daukar abun, da kunnenta taji yana ikirarin ba zai so ta ba, tayi masa siranta da yawa, ba ajin sa bace. tabbas duk abinda ya fada haka ne, amma kuma zuciyar ta, ta k'asa karbar gaskiyaar yafi karfin nata, shiyasa har abun ya tsaya mata a ranta sosai. Kashe microwave din tayi, ta dora abincin akan dan madaidacin tray ta saka ruwa da lemon kwakwar da duk shi akayi wa. Zuciyar ta ce ta sake karyewa tana kokarin daukar abincin, sai ta dora kanta akan kitchen cabinet din ta sake sakin kuka me cin rai. Kitchen din ya nufo, da niyyar ya duba abincin ko zai samu, sai yaji kamar shasshekar kuka k'asa -kasa, da dan saurin sa ya karasa kofar, ya hangi bayan ta, kanta a duk'e tana fidda sautin kuka irin me taba ran duk me saurare. Gashin kanta idanun sa suka sauka akai, ya bud'e baki cike da mamakin tsawo da bakin sa, yana tsaye ta ware hannun ta, ta jawo tissue dake gefen daman ta, ya bi dogayen zarara-zararan hannayen nata da kallo, sun sha kunshi baki da ja me matukar kyau da daukar hankali abinka da farar mace. Yana nan a tsaye ta gama share fuskar ta, ta jefa tissue din a dustbin ta daga kanta sama tana kokarin maida ragowar kukan da yake taso mata, sannan ta sauke ta dauki tray din a hannun ta, ta juyo idanun ta suka shiga cikin nasa, yana tsaye a jingina da jikin kofar yana kallon ta, irin kallon wacece ke? Irin kallon da ya fara yi mata ranar da ya fara ganin ta. Duk da ya chanja yayi kiba da haske fatar sa ta murje, amma be sauya mata ba, shi din ne dai na ranar farkon nan, idanun sa a shanye kamar me jin bacci, kallo daya biyu tayi masa, sai kalaman sa suka shiga dawowa mata daya bayan daya, da sauri ta sauke kanta k'asa zuciyar ta na harbawa, da sauri da sauri, daga kafar ta, tayi daga wajen da take tsaye, tazo ta gifta ta gefen sa, har jikin ta na gogar nasa dan yadda ya cinye kusan fiye da rabin kofar. Juyowa yayi ya bita da kallo, har ta shige dan corridor din da zai kaita dakin ta, tana shiga tayi saurin dire tray din ta saka key a kofar, ta durkusa a wajen tana sakin kuka.

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (26)

Tana tsaye a gaban mirror taji shigowar motocin alamun sun dawo, gaban ta ne ya fadi cikin ta yayi wata irin murdawa, ji tayi kamar tana bukatar shiga toilet amma tasan irin wannan yanayin ne da mutum yake tsintar kansa when he's nervous. Tafin hannun ta ne taji yana mata wani iri sai kuma tafi kafarta, samun waje tayi ta zauna da sauri tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ta dan dan mintuna a haka kafin ta tashi ta karasa shiryawa cikin sabon kayan ta riga da skirt, ta yafa madaidacin chantilly akan kayan nata, ta feshe jikin ta da turare me sanyin kamshi, wanda baya hawa ka.

***Kafafunsa ya zuro sanda suka iso cikin gidan nasu, idanun sa na kan gidan da yanayin tsarin gine-gine wanda yayi saurin banbance kowanne,.

"Ina wajen Mama?"

Yace bayan ya fito daga motar, da hannu Fauwaz ya nuna masa, yana kokarin bawa yaran dake harabar gidan masu kula da gyaran compound din da duk aiken gidan jakunkunan Tariq din dan kai mishi su part dinsu.

Takawa ya shiga yi zuwa part din Maman wanda tuni su Maryam sun isar mata da labarin isowar sa, tana tsaye a tsakiyar falon ya turo kofar ya shigo, ta saki baki ganin wani irin chanjawa da Tariq din yayi. Murmushi ya sakar mata yana karasa ciki da dan saurin sa, ya russuna ya gaida Maman bata san lokacin da ta rungume shi ba.

"Welcome home son, sannu da hanya."

Ta sake shi tana fada, sai kuma tace ya zauna, ya zauna bayan ya dan kalli falon. Gaishe ta ya sakeyi sannan sukayi maganar bayan rabuwa, ta saka aka kawo masa ruwa da juice yasha ruwan kawai tace sauran abincin suna chan a part dinsu aka jera masa, mikewa yayi yana zuwa hannun sa a cikin dogon wandon sa yace zai je ya huta zai shigo anjima. Har kofa ta raka shi cike da jin dadin ganin sa. Yana fita suka hadu da Fauwaz ya gama shigar masa da kayan, ratayo kafadar sa yayi ya yi maganar a hankali

"Rakani na gaida Aunty, sai Yaya daga nan ina so na huta dan wani banzan transit mukayi a Ethiopia wanda yayi draining baki daya energy dina."

"Wai, matsalar kenan dama, ina zamu fara zuwa?"

"Wajen aunty, dan Yaya idan naje surutun ta nasan zai kara min ciwon kai, kaga ina fitowa sai naje na huta gaba daya."

"Allah ya dawo damu ai, kai da Yaya ai kamar Tom and Jerry, Jidda ce kawai daidai da ita ta iya lallaba ta wallahi."

"Jidda?" Ya kira sunan kamar me tunani, sai kuma yace

"Ohh, that slim girl?"

Dariya ya bawa Fauwaz,be bashi amsa ba saboda karasowa part din Auntyn da sukayi, suka shiga Fauwaz na gaba yana bin sa a baya yana nazarin part din shima, kamshin abinci ne ya daki hancin sa, irin kamshin da be taba jin irin sa ba, lumshe idon sa yayi ya bude sanda Auntyn ta fito fuskar ta cike da fara'a tana masa maraba, murmushi yayi ya amsa sannan suka dan taba hira, yace zai dawo ya mike sai kuma ya tsaya

"Aunty wannan kamshin abincin, inason naci"

"Naka ne ai, tunda dan kai Jidda tayi."

Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, sai kuma ya kada kansa alamun ok, sannan yace

"Zamu ci dadi."

"Sosai, jiddah expect ce in dai girki ne."

Ya Fauwaz ya kara dan duk ya sake samun hanyar convincing dinsa. Gid'a kansa yayi, yace suje suka fita sai part din Yaya, wadda ta cika tayi fam dan tunda tasan sun shigo take zurara ido a hanya amma dan wulakanci sai yaje ya gaida uwarsa sannn zai zo wajen ta. Suna shigowa ta tsuke fuska kamar ba jiran shi take ba, kallon fuskar ta yayi sai ta bashi dariya ganin yadda tayi kicin kicin da fuska ita a dole tayi fushi, fushin da be san na menene ba.

"Ai da ma baka zo ba, tunda sai ka gama gaida iyayen ka zaka zo waje na."

"This woman and her wahala."

Yayi maganar a kasan makoshin sa, ya zauna a gefen kafarta yace

"Yi hakuri bazan kara ba."

"Dama ba laifi kayi ba..." Tace kunya kuma sai ta kama ta yadda tayi masa bayan dawowar sa kenan

"Mun same ku lafiya?"

"Alhamdulillah, Allah ya kaddara saduwar mu, na zata fa da sai mun mutu zaka zo taaziyya."

"A ah, ban isa ba." Yace yana murmushi

"Ikon Allah, ashe dama kana murmushi, dama dan uwanka yana murmushi kai." Ta kalli Fauwaz tana rike haba

"Dariya ma har da kyalkyalawa."

"Ah lallai magani yayi aiki, dole na kira Malam na sake godiya, ya kuma sake aiko maka da wani rubutun."

"Ai naji dadin maganin nan Yaya, nagode sosai."

Yace yana biye mata dan ya gano da dadewa wahalar da kansa kawai yayi da ya kasa fuskantar halin Yayan

"Ba komai ai yiwa kai ne, ka dai samu daddad'an labarin bikin ka wajen ita uwar taku ko?"

"Biki? Wanne biki Yaya?"

"Bari Yaya zan masa bayani kinji?"

"Wanne biki ake magana Fauwaz?"

"Muje part din mu, muyi magana."

"Ok." Yace a sanyaye, ya tashi suka fita, ita dai Yaya ko a jikinta, murnar ta kawai take tasan kuma duk tsiyar Tariq din ba zai taba kin jiddaa ba.

Suna shiga part din nasu Fauwaz yayi wa Jidda text wadda take rufe a daki tun shigowar su wajen Auntyn har suka fita, tana jiyo echo din muryoyin su amma ta kasa fitowa

"Kawo ruwa part dinmu jiddah." Ta karanta text din, sai ta mike tana sake kallon kanta a mudubi, kafin ta fito ta shiga kitchen ta dora ruwa akan tray tare da cup ta fita zuwa part din su Fauwaz din.

Ransa ne yayi kololowar tun kafin ma Fauwaz ya gama maganar, ya dakatar dashi ba tare da ya gama fahimtar abinda ma yake nufi ba, abu daya kawai ya tsaya ya fuskanta shine ana so a hada shi aure da figaggiiyar yarinyar nan jidda, be ma ji karshen bayanin ba, bare yaji har ma an daura musu auren shekara daya kenan. Hannu yasa ya dakatar da Fauwaz din ta hanyar cewa

"Ya isa!!!"

“Ya Tariq amma…” Fauwaz yace zai cigaba da bayanin

“Look fauwaz, ba zan iya auran yarinyar nan ba, tayi min kankanta da yawa, plus bata cikin spec dina gaskiya. Bana so mace ta cika siranta da yawa, plus she’s young. Very very young da rainon ta zanji ko da aiki na!?”

“I know, amma when last kaga Jidda? When last ka ganta face-to-face?”

“Ba zan iya tunawa ba, infact na manta kamar ta ma baki daya ni. So it’s better kaje ka sanar da Yayah, ba zan iya ba gaskiya, gobe goben nan zan koma in da na fito, daga dawowata? Haba!”

“Calm down and give it a second thought, karka yanke shawara base on abinda ka sani a baya, jiddan da ka sani shekara biyar baya ba itace wannan Jiddan ba! Ka daure ka ganta.”

“Fauwaz!”

Sai ya mike tsaye

“Kana bata bakin kane kawai, ba zan iya ba gaskiya, ba zan daukar ma kaina abinda na san ba zan taba iyawa ba.”

Mikewa shima yayi, yana girgiza masa kai, zai yi magana ya daga masa hannu

“Bana son sake jin komai. Ya isa haka nan, ba zan taba iya soyayya da ita ba, bare har ta kai ga maganar aure! Never!!!

****Tray din ruwan da yake hannun ta ne yake neman subucewa, tayi saurin rike shi hawaye na saukowa a kuncin ta, ya zatayi da auren sa da yake kanta? Ya zatayi da rayuwar ta yanzu kenan? Innalillah wa inna ilaihi raji’un. Ta shiga maimaitawa. Takun takalmin sa ne ya iske ta, tayi saurin matsawa jikin dan corridor din dake jikin dakin ta makale, fuskar sa a hade take tsaf, yana cikin shigar farar tshirt wuyan sa sakale da necktie navy blue sai dogon wandon chinos dake sanya a jikin sa. Dogo ne sambal, kuma giant na ajin karshe, zuwa yayi ya wuce ta, ba tare da ya lura da ita ba, tana jin kiran da Ya Fauwaz yake kwala masa amma yayi biris kamar be ji ba. Ya wuce kansa a gaba cikin yanayin da ta kasa hange ko hasashen sa. Ji tayi tamkar kafarta ba zata iya daukar ta ba, duniyar na juya mata, shekara guda kenan tana dauke da igiyar auren sa, igiyar da ta raba ta isma’il me tsananin son ta da kaunar ta, ta zabi zaman dakon jiran shi, duk da bata da yakinin abinda zata tarar daga gareshi. Zuciyarta tayi nisa a kaunar sa wanda har take jin bata da wani katabus idan har babu shi. Me yasa zuciyar ta, ta zalunce ta? Me yasa ta sakata kaunar wanda baya son ko ganin ta? Lallai zuciyar ta, ta zalunce ta zalunce mafi girma.

Zaman dirshan tayi a wajen, cup din da ruwan kowanne yayi nasa wajen, Fauwaz ne ya fito, ya ganta a wajen, yanayin da take ciki ya tabbatar masa da lallai taji maganganun su, durkusawa yayi a gabanta cikin yanayin tausayinta, dan yasan yadda take son Ya Tariq, kuma yasan sune ummul abaisin gina mata soyayyar shi a cikin zuciyar ta, shi da Amira sune suka bata hope, suka dora ta akan turbar da a yanzu shi kansa be san da wanne irin baki zaiyi amfani wajen gyara matsalar ba.

“Jiddah.”

Ya kira sunan ta cikin yanayin da shi kansa yasan abinda zai fada bashi da wata maana, dago manyan dara-daran idanun ta tayi, wanda a kullum suke cike da wani haske me kyawun gaske, sai dai a yanzu sun rine sun koma wasu iri na daban, tamkar ba su.

“Nasan kinji komai da muka ce, bansan me kuma zan ce miki da zai karfafa miki guiwa ba, amma na miki alkawari sai Ya Tariq ya kawo kansa wajenki, begging you on his two knees akan ki taimaka masa. Nayi miki wannan alkawarin, sai ya sauke duk wata izza da yake ji, sai ya ajiye duk wani self respect nasa, ya nemi soyayyar ki.”

Girgiza masa kai tayi, ta mike tana karkade jikinta, ya taimaka mata ya dauki tray din yana leka fuskar ta da ya kasa gane ainihin abinda yake faruwa a cikin zuciyar ta

“I’m so sorry Jidda.”

Murmurshi ta sakar masa wanda yake dauke da abubuwa masu yawan gaske, ta shiga takawa zuwa cikin gidan, gefen ta ya tsaya suke jera yana rike da tray din, suka shiga cikin gidan zuwa part din antyn, a saman madaidacin fridge din dake falon ya ajiye tray din ita kuma tayi saurin shigewa dakin ta, tana shiga ta kulle kofar ta jingina da bayan kofar zuciyar ta na bugawa da karfi da karfi

“Ina son ki Jiddah, ina son ki fiye da yadda nake son kai na, dan Allah ki ceci rayuwata ki so ni ko da kwatan son da nake miki ne.”

“Kayi hakuri isma’il, ba zan iya ba, ba zan iya ba.”

“Shikenan Jidda, shikenan sai watarana!”

Kalaman Isma’il na karshe kenan, anya ba alhakin sa bane zai fara bibiyarta? Anya? Ashe haka kake ji idan wanda kake so ya furta maka kalmar baya son ka? Haka isma’il ya ji? Mutumin da ya so ta tun tana yar kauyen ta? Ya so ta tsakani da Allah ba dan wani abu da ta mallaka a jikin ta ba, anya bata cuci kanta da rayuwar ta ba?

Dafe kanta ta yi da yake barazanar tsinkewa, ta lallaba zuwa gaban mudibi ta tsaya tana sake kallon kanta da kanta! Duk in da ake so mace ta kai a haduwa da cika ta san ta kai, amma sai dai kash!

ZAFAFA BIYAR!!!

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300) BIYU (400) UKU (500) HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR ZENITH BANK 2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼 [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (29)

***Bin Baban yake a baya ran Baban a bace har zuwa wajen motar sa, dama mantuwa yayi ya dawo har ya ji maganar da Maman take, bude masa murfin motar akayi ya shiga, sannan yace Tariq din ma ya shigo driver kuma ya fita ya jira su a waje.

"Yanzu ni zaka watsawa k'asa a ido Tariq? Na nema maka auren yarinyar nan yau shekara guda, mahaifin ta ya bani wuk'a da nama, haka yarinyar da ba haifan ta nayi ba, ta karbi abinda nazo mata da shi sai kai? "

"Ba ki nayi ba Baba, na karba hannu biyu wallahi, nagode Allah ya saka da Alkhairi ya kara girma."

"Idan har ba k'i kayi ba, wacce irin magana naji kuna yi da mahaifiyar ka?"

Shiru yayi dan baya son fadin laifin Maman, girgiza kai Baba yayi yace

"Shikenan, kar naji kar na gani, ka fara shirye-shiryen daukar matarka."

"In sha Allah Baba,kuma dan Allah ayi wa Mama uzuri,zan yi kokarin fahimtar da ita in sha Allah."

"Mahaifiyar ku bata son gaskiya Tariq, uzuri nayi mata sau nwa ma, amma shikenan, kuyi magana da ita, Allah yayi maka albarka."

"Amin." Ya amsa, sannan ya fita daga motar driver ya shigo, yaja suka fice daga gidan tare da motocin DSS dake bin bayan Baban.

Wajen wasu kujeru ya nufa ya zauna, baya son wannan matsalar ta shafi zaman iyayen sa, dan haka ya zama dole ya karbi yarinyar ko da na wucin gadi ne, dan ba zai so akanta iyayen sa su dinga samun sabani ba. Yana zaune a wajen Fauwaz ya fito ya hango shi, sai ya taho ya zauna a gefen sa, dan be yi tunanin Tariq din yana gidan ba. Suna zaune iskar wajen na kada su, ta fito rike da hannun Usman da wata warmer madaidaciya, mayafi ta saka ta rufe kanta amma kana iya hango duhun gashin kanta, fuskarta fayau duk da k'asan zuciyar ta babu dadi, bata lura dasu ba, tafiyar ta kawai take kai tsaye zuwa part din Yaya, idanun sa akanta Fauwaz na ankare dashi, mikewa yayi ya nufe ta, ya kira sunan ta, waigowa tayi sai ta saki fuskar ta

"Ya Fauwaz.."

"Na'am, kin daina buyan?"

"Dama ba buya nake ba fa."

"Me kike?" Yace yana mika mata hannu, ta bashi warmer din hannun ta, mika masa tayi suka jera tana masa bayanin dalilin ta, wanda jin ta kawai yake amma ba wai ya gamsu bane.

"Kinga Ya Tariq chan ya kafe mu da ido,kar ki juya just pretend kamar baki ganshi ba."

"Dama ban ganshi ba ai, me yasa zai kafe mu da ido?"

"Oho." Ya d'age kafada yana murmushi, share zancen tayi suka shige wajen Yayan yana kallon su, kamar ya tashi yaje ya kwankwashi kan Fauwaz haka yaji, ya rasa me yasa amma yadda yaga suna magana da murmushi yasa duk yaji haushi ya tik'e shi, cigaba da zama yayi a wajen har ranar da tayi saura ta karasa mamaye wajen, zafin ta ya bige shi. Mikewa yayi yana zura hannayen sa cikin aljihun wandon sa, yabi bayansu zuwa part din Yayan dan zuciyar sa ta gaza hakuri sai yaje yaga abinda yake faruwa.

Dariyar Yaya ya jiyo har da kyalkyalawa tun kafin ya ida shiga ciki, daidaita fuskar sa yayi zuwa yanayin da ya saba a ko da yaushe, ya shiga da sallama amma ciki - ciki,dakatawa Yaya tayi da dariyar dama video take kallo a wayar Fauwaz na abin dariya.

"Malam Badamasi an karaso?"

Tace tana dariya, dariya Fauwaz yayi Jidda kuma ta dauke kanta zuwa wani shashen falon, zama yayi yana zaro hannun nasa yana kallon wajen da take zaune, kallon kallo Yaya sukayi wa juna ita da Fauwaz kafin su kwashe da dariya, dariyar da ta saka Tariq din tsarguwa.

"Ina kwana?" Yace

"Lafiya lou wallahi, kamar yadda ka ganmu ni da mutanen amana ta."

"Ke bakya gaida mutane ne?"

"Wai Jidda, ai bata son yawan magana kasan, kuma dai idan jinin ta be hadu da na mutum ba, bata masa magana ko Jidda?"

"Haka ne kuwa." Fauwaz yace,

"Ok yayi kyau ai, ni dai Yaya karki manta da alkawarin da mukayi."

"Ina zan manta? Ka jira lokacin dai."

"Shikenan." Yace yana maida kansa jikin kujerar , mikewa jiddah tayi, ta gyara yafen mayafin ta, ta ce

"Yaya zan dawo anjima."

Jan numfashi yayi ya sauke da sauri, yadda muryar ta, ta doki kunnen sa. Hada ido sukayi, tayi saurin janye nata tayi hanyar fita da dan saurin ta. Kundin tunani ya fada bayan fitar ta, sai ya mike kawai be ce uffan ba, ya fice daga shashen. Tafawa Yaya sukayi da Fauwaz,

"Kaga mutumin ka ko?"

" Wallahi Yaya, ke ai legend ce kinsan ta kan tsiya, wallahi ya Tariq ya fara bani tausayin dan yadda yake jin kansa da miskilanci jiddah oga ce, kuma tana da gudun zuciya tunda taji da bakin sa yana furta wannan maganar zaa sha wuya kafin ta dawo daidai."

"Su karata chan, idan suka tare zasu daidaita kansu, mu dai muyi iya yinmu mu hora shi sosai, sauran mu barwa jiddaa su karata."

"Kin san ta kan tsiya Matar nan."

"Dani yake magana ai, kunno min kallon nan na cigaba."

"An gama ranki ya dade."

Kunna mata yayi yace zai je ya dawo yanzu, yana fita ta sa hannu ta jangwale kallon gashi bata iya ba, haka tayi ta tabe-tabe har tazo kan video da yayi mata a airport da za'a chanja ta daga mota zuwa jirgi, a cikin jirgin har zuwa gida. Salati ta rafka wayar saura kiris ta subuce daga hannun ta, sai gashi ya dawo yana shigowa ta damke masa hannun riga

"Ni zaka yaudara? Wayyo Allah."

Sai ta fashe da kuka

"Menene Yaya? Me ya faru?"

"Ubanka ne, wallahi sai yazo da kansa ya raba ni da kai yau, sai da nace maka bana so, bana so, amma saboda ka raina ni..."

"Wai menene Yaya?" Ya yi dabara ya zame rikon da tayi masa ya karbi wayar sa,

"Waye ya saka ni a jirgi? Waye idan ba kai ba? Waye?"

"Auw wai magaanar jirgi ne Yaya? Yaushe kika shiga ni bansan zancen ba."

"Video din menene a wayarka? Ni zaka rainawa hankali?"

"Video ni? Yaushe akayi? Bansan maganar me kike ba fa Yaya."

"Idan yazo sai kayi masa bayani, ita Jiddan zTa shigo ne wato har da ita za'a hada baki a kassara min rayuata?"

"A ah fa, ba laifin jiddaa, tunda dai kin riga kin ga video din ba amfanin boye miki, maganin bacci na baki aka saka ki a jirgin."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Wayyo ni Hajara, ni kake so kaga baya ko? So kake ka kashe ni, na shiga uku na lalace Wayyo."

Gwalo yayi mata, ya fice da sauri tana kiran sa ya gudu yana dariya. Kuka ta shiga yi wiwi tace Usman yaje ya kira mata Anty, yaje zai gasu sun dawo tare da saurin ta, tana zuwa tace ta kira mata Baba yazo yanzu yanzu Fauwaz yana son ganin bayanta, duk yadda Aunty taso ta tsaya suyi magana ta fahimci me ke faruwa amma kemaimai taki sai kuka take tana fece hanci, Baba yadda Aunty ta iya dole ta kira Baba be dauka ba dan dama yace suna da meeting, hakuri ta dinga bawa Yayan har ta samu ta lafa da rikicin, ta lallaba ta, ta zauna taje ta kawo mata kunun ta tasha ta kunna mata kallo, sannan ta samu ta bar maganar kafin Baba ya dawo.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull