Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 22

Sanadin labarina complete novel - Chapter 22

Sanadin labarina complete novel Chapter 22: Sanadin labarina complete novel Chapter 22. Amira tace tana hararar ta, tsayawa tayi taki motsawa jin tarin…

4,499 words

Amira tace tana hararar ta, tsayawa tayi taki motsawa jin tarin Jidda a bayan ta, ba'a taba humiliating dinta irin yau ba, kamar an dasa ta a wajn haka ta kasa motsawa, sai da Amira ta fizgi hannun ta sannan ta iya daga kafarta guda daya sannan ta motsa dayar. Wuce su yayi yana kokarin daidaita fushin da yake ciki, ya nufe ta ganin duk ta tsorata da yanayin sa. Ji tayi kawai yayi hugging dinta da sauri yana sauke ajiyar zuciya, kafin ya ja hannun ta su bar falon ba tare da ya sake bi ta kan su Amira ba.

Tun a mota Salman ta dinga rusa kuma Amira bata tanka mata ba, dama tun ranar farko taso ya Tariq din ya kore su amma ya kyale su, ita tana ta danna waya bata ma lura da falo Salman ta fito ba, ta dauka ma tana toilet ashe yar iskar yarinya wai tarar Ya Tariq din tazo,lallai bata san waye shi ba, su kansu da suke ciki daya basa zama tare dashi haka ba mayafi bare har suyi wata banzar shiga sam basu taso da wannan rayuwar ba, akwai limit a komai idan aka cire ma Ya Fauwaz da Ya Safiyya babu Wanda a cikin su Ya Tariq din yake wata doguwar magaana dasu bare har su samu fuskar raina shi, ita Amira da yake ma itace karama kuma akwai tazara sosai a tsakanij su tsoron sa ma take ji shiyasa bata so zuwan su gidan ba, shima kuma yasan ba zata so ba amma ya zatayi da Mama? Tun farko basu iya cewa Maman a ah ba a komai tace tunda dama ba tarbiyya bace, shiyasa har Ya Tariq din baya ketare maganar ta sai dai a irin case din yanzu na jiddah da kuma ko waye tasan hakan zai yi tunda dai tsanar da tayi ma Jiddan ba ta da wani kwakkwaran dalili. motar na gama parking Amira ta fice ta wuce part din Yaya dan ma kar su Mama su cikata da tambaya dan yau tasan akwai rikici a wajen Aunty Nafi akan shalelen ta, dan bata sani ba ma ko kafin fitowar ta daga daki Ya Tariq din ya dan mammari fuskar ta. Tunda suka shiga dakin ya zauna be ce uffan ba, tana ta satar kallon sa yayi nisa a tunani, he looked disturbed kamar akwai wani abu bayan abinda ya faru yanzu da ya dame shi. Ji tayi duk ta damu da damuwar sa dan tunda tazo gidan bata taba ganin damuwa karara kamar haka a fuskar shi ba. Kasa sukuni tayi, ta taso tazo gabansa ta zauna ya kalli babban dan yatsan kafar tata sannan ya kalli fuskar ta, sai ya zamo ya zauna a kasan kan carpet din da ke gaban gadon ya kama hannun nata

"Sun daina ciwon?"

Yace bayan ya hadiye yawun da ya taru a makoshin sa, gid'a masa kai tayi, ya lura tana son yin amfani da kanta wajen amsa tambayar da amsar ta dari bisa dari.

"Kafar fa?"

"Da sauki."

"Basu daina ba ko? Raguwa ciwon kawa yayi."

"Eh."

"Owk sannu."

"Uhumm."

"Shine baki fada min Salma ce ta zubar da man da kika zame ba ko? Yanzu idan da tsautsayi kika karye fa? Ko wani abu worst than this ya faru? Shikenan sai kiyi shiru?"

"Bana son ranka ya baci ne, shiyasa kawai na kyale, tunda Allah ya kiyaye ma."

"Karki kara irin wannan, babu amfanin zaman mu da ita in dai cutarwa zata shigo ciki."

"In sha Allah ba zan kara ba."

"Good."

"Shikenan?" Tace ganin be saki ran nasa ba har lokacin, girgiza mata kai yayi yadda take yi yace

"Ba shikenan ba."

"Ok." Tace a sanyaye.

"Ciwon ya daina?" Ya sake tambayar ta bayan be dade ta tambayar ta ba

"Kad'an yake yi."

"Ok ."

Sai ya mike tsaye ya hau rage kayan jikin sa yana jin yadda zuciyar sa ke neman yi masa ingiza me kantu. Tashi tayi ta fice ganin yana neman cire kusan dukka kayan jikin nasa a gaban ta, tasan kila ya manta tana nan shiyasa . Chanjawa yayi ya fito falon ya zauna bayan ya jona system dinsa ya bud'e ta ya fara aiki akanta Wajen goma na dare suna zaune shi yana ta aiki a system din ita kuma tana kwance a gefen sa tana kallon film bacci na fizgarta, wayar sa dake ta side din ta tayi kara, hannu ya miko mata still idon sa na kan system din ta mika masa ya daga ba tare da ya kalli number din ba, ya kuma sata a handsfree

"Hello Captain." Muryar mace ta ratso cikin wayar ta dire a kunnen Jidda da gaban ta yayi wani irin faduwa

"Wa ke magana?" Yace yana maida hankalin sa akan wayar

"Yasmin ce."

"Yasmin?"

"Don't tell me baka gane, ohh my God yanzu Tariq ka manta Yasmin?"

"Sorry, ya akayi?"

"Lord! Kana nan dai yadda na sanka, ba abinda ya chanja daga classy Tariq din da na sani who's always ignoring me "

"How are you? Ya komai?"

"Fine sha, sai dai missing dinka ka tafi ba sallama, yanzu ka kyauta kenan?"

Kallon gefen Jidda yayi yaga ta tashi zaune, tana gyara dankwalin kanta da ya sabule mata, sai kuma ta mike ta shige ciki yana kallon ta.

"Sorry Yasmin, nagode sai anjima."

"Wait..." Kit ya katse ya mike yana rufe system din yabi bayan ta

Tana zaune hawaye na tsere a kan kuncinta, kishi da haushin wadda aka kira da Yasmin ya cika mata zuciya har take jin kamar numfashin ta nayin sama-sama, da gaske take kishin sa musamman akan wannan unknown Yasmin din da take jin kamar tayi daidai ta dace da spec din Ya Tariq din. Turo kofar yayi ya shigo tayi saurin sa bayan hannun ta, ta share fuskar ta, amma duk da haka ya ganta.

"Jidda, are you ok? Menene? Why are you crying?"

"Ba komai."

"Fada min, ciwon ne?" Girgiza masa kai tayi tana jan kukan da ke taso mata

"Come here." Ya jawota jikin sa sai kawai ta fashe da kuka, kukan da ya saka shi gaba daya yaji yayi loosing control dinsa, dama tun dazu yana ta kokarin hana zuciya da gangar jikinsa, amma sai gashi jidda na neman ballo ruwa, rarrashin ta ya ke yi amma sam taki yin shiru, dago ta yayi daga danna fuskar ta da tayi a kirjin ta, ya hade bakin su waje daya ya shiga kissing dinta da sauri da sauri. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (47)

Malama's Citadel 08035625833 Zaria kaduna state Original Ayu oil Infection and Cleansing set na maza da mata Tsumi Tightener Matsi me kyau Kaza Tsarki herbs

***Saurin hadiye kukan da take tayi ganin gaba daya Ya Tariq din ya chanja mata zuwa wani daban, yana yi mata wasu abubuwan da kwakwalwarta ya gaza dauka, gigicewa tayi ta hau kokarin tashi take ya hanata yana girgiza mata kai

"Please Jidda, dan Allah."

"Dan Allah kayi hakuri."

Jikinta ya hau rawa kaamar mazari, ba zai iya ba, ba zai iya hana kansa ba, amma yayi alkawari zama cool, ba zai cutar da ita ba,gyara mata zama yayi a jikin sa yana shafa mata kanta,

"Shsss, kiyi shiru kinji?, ba zai ciwo ba, I promise ba zai ciwo ba."

"Dan Allah kayi hakuri " Ta cigaba da kuka tana cigaba da son tashi, sake matse ta yayi yana cigaba da bata hakuri, har ya samu ta nutsu, tallafo fuskar ta, yayi yana kallon cikin idon ta. Motsa bakin sa yayi a hankali yace

"Ina sonki Jidda!"

"I love you so much, har bansan yawan son da nake miki ba, bansan yaushe ba, kawai na samu kaina in love with you, you possess all the qualities da nake son mace, i was foolish at first da na fadi abubuwan nan, and it's just my hallucination, ke nake so, only you, and you alone."

Ajiyar zuciya ta sauke tana boye fuskarta a tsakanin kirjin sa. Kansa ya daga sama yayi murmushi yana ciro ta daga chest din nasa yace

"Allow me to show you how much I love you,I promise to be a gentle man."

"Tsoro nake ji." Tace idon ta na ciccikowa

"Comman karki kuka, ba wani abu bane ba, pleaseeee."

"Kin amince?"

Yace yana murza mata tafin hannun ta a hankali, da ka ta amsa masa duk da zuciyar ta kamar zata bud'e ta fito saboda tsabar tsoron da take ji. Murmushi ya sakar mata yana lumshe idon sa

"Thank you Jidda!"

Yace yana gyara mata kwanciyar, kulle idon ta tayi gaba daya kukan na cigaba taso mata, tana jin kamar tace bata amince ba, kaamar tace ta fasa ya kyale ta, sai dai kash!

Babu irin duka da yakushin da batayi masa ba, ta dinga kiran Baffa, Aunty har Amira sai da ta kira tana neman agaji amma ko a jikin sa, be masan tana yi ba, sai jaddada mata irin son da yake mata yake da bata gane ko mai sai bakar azabar datake ji har cikin kwakwalwar. Duk da da gaske a hankali ya tafi da ita amma still ta sha bakar wahalar ,irin wadda bata taba tunani ko hasashe ba, bata san haka abun yake ba, bata kuma san yadda zata misalta ba. Kukan ta cigaba da yi amma k'asa-k'asa, sai jan ajiyar u yayi wajen ta tayi saurin matsawa tana rokon sa cikin muryar ta da ta dashe sosai saboda tsabar kuka.

"Dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya ba."

"Ba abinda zan miki I promise, I'm sorry."

Rungume ta yayi ta cigaba da kukan yana jin ta, hannun sa na saman kanta yana shafawa a hankali, be san da wanne baki zai amfani wajen bata hakuri ba,sai kawai yayi shiru ya cigaba da shafa kan nata har ya samu tayi shiru sai ajiyar zuciya da take jerawa, rungume ta yayi kam-kam yana jin kamar ya bude zuciyar sa ya saka ta a ciki. A hankali bacci ya soma daukar ta, sai kuma zazzabin da ya dawo ya sake rufe ta, gyara mata kwanciyar yayi ya zare jikin sa a hankali ya mike ya nufi toilet yana jin kansa yayi masa nauyi sosai, ya dan jima a ciki ya fito yana goge jikin sa da towel, ya shinfida abun sallah bayan ya zura doguwar jallabiya ya dan karo fan din sannan ya tada sallah. Rara'a biyu yayi ya zauna yayi addu'a sosai sannan ya godiya Allah bisa niimar da yayi masa duk da ya saka san ransa bayan zabin Allah shine babba zabi mafi dacewa. Motsi yaga tana yi ya mike da sauri ya isa wajen ta, yana kallon yadda take ya mutse fuska alamun rashin jin dadi, tausayin ta yake ji gaba daya da dana sanin abinda ya aikata mata, yaso ace ba yanzu ba, yaso ace sai sun kara shakuwa sosai, amma kuma babu yadda zai. Rike ta yayi ta daina motsin ta cigaba da baccin a wahalce, jikin ta zafi sosai kamar wuta, so yake ya taimaka mata ya rage mata zafin jikin amma baya so ta tashi a gigice dan duk ta riga ta tsorata dashi. Magungunan ta yaje ya dauko yazo ya ajiye a bedside ya hau gadon a hankali yadda ba zata tashi ba, ya kwanta a bayan ta ba tare da ya hada jikin sa da nata ba, ya leko fuskar ta ya gyara mata gashin ta da ya hargitse ya bazo har saman fuskarta. Wajen asubah ta farka ta ware idon ta akan shi sai abinda ya faru ya dawo mata, da sauri ta sake matsawa daga kusa dashi, ta sakko a hankali daga gadon tana ya mutse fuska ta shiga toilet, karar bud'e kofar toilet din ce ta tashe shi, ya kalli bangaren datake kwance ganin bata nan yasa ya tashi da sauri ya bi bayanta ya bud'e toilet din da turo shi kawai tayi bata rufe ba. Tana tsaye tana hawaye ya shigo, ya riko ta yana kiran sunn ta

"Jidda?"

"Menene? Akwai abinda yake miki ciwo ne?"

Daga kanta tayi tana jan kukan,

"I'm sorry dan Allah kiyi hakuri."

"Ni ka fita." Tace tana cigaba da kukan,

"Taimaka miki zan, zaki ji sauki."

"Um um ni bana so."

"Kiyi hakuri dan Allah, ki bari na taimaka miki kinji?"

Noke kafardar ta tayi,

"Shikenan, shikenan zan fita, I'm sorry."

Sai ya juya ya fita ya ja mata kofar, ya cire bedsheet din ya saka a gefe ya dauko wani a closet ya saka sannan ya dawo ya tsaya a jikin kofar yana jiran ta fito, ta dade sosai har ya fara tunanin komawa ciki amma sai gata ta fito tana jan kafar ta, yayi saurin tarar ta, ya kai ta ta zauna a gefen gadon ya dauko towel ya hau goge mata kanta.

"Sanyi."

Tace tana kankame jikin ta, saurin kashe komai yayi ya bud'e kayan sa,ya dauko mata jallabiyar sa, ya saka mata sannan ya taimaka mata ta kwanta, kumburarrun idon ta ya kalla ya girgiza kai lokacin aka soma kiran sallar asubah, alwala yaje yayi yazo yace ta tashi suyi sallah, ta mike tana kin kallon sa ya bata Hijab ta saka har lokacin sanyi take ji sosai sukayi sallar sannan ta koma ta kwanta ya lullube ta ya fito zuwa kitchen ya hado mata tea me kauri ya dawo dakin ya tashe ta zaune tasha sannan ya bata magungunan ta,tasha suma sannan ta koma ta sake kwanciya, bata dade ba baccin ya sake dauke ta. A gaban gadon saitin fuskar ta ya durkusar da guiwowin sa yana kallon kyakkyawar fuskar ta da tayi ja saboda tsabar kuka, saman dogon hancin ta ya kai hannu wajn wani ja ya taba kad'an yana girgiza kansa, a yadda take fitar da numfashin ya tabbata taji jiki sosai, dama kuma ga ciwon targaden da ya dinga kokarin hana kanshi akan hakan amma be san me ya hau kansa ba, ya kasa hakura bayan yasan tana bukatar tayi healing yazo ya kara mata wani ciwon akan wanda take fama, be kyauta ba sam, kuma zata iya yi masa wani irin kallo. Hannun sa ya kai ya shafi gefen fuskar ta.

"I love you Little Jiddah."

Sai yayi kissing dinta a saman goshin ta, sannan ya mike ya fita daga dakin ganin rana ta fito sosai.

***Wayarsa dake yashe akan kujera tun sanda Yasmin ta kirashi ya ajiye be saka bi ta kanta ba ya dauka ya ga missed calls da yawa, da sauri ya cire lock din ya shiga call log ya tarar da 15missed calls daga Yasmin sai 5 daga Mama sai Fauwaz guda biyu. Duk da dama yasan Mama zata kirashi amma be yi tunanin har missed calls haka ba, kiran ya bi yana kishingid'a a saman kujerar yasa hannun sa yana shafa saman kansa dake masa ciwo sama-sama. Bata dauka ba har ta katse ya sake kira nan ma no answer sai kawai ya ajiye wayar yana tunanin yadda zasu kwashe da maman yana kuma fatan ta fahimce shi ko yaya ne. Wani tunani ne yazo masa sai ya sake daukar wayar ya kira Fauwaz bugu daya ya daga.

"Ya Tariq ina ka shiga?"

"Fauwaz, bacci nayi na bar wayar a falo naga miss calls din Mama da yawa, hope lafiya?"

"Ba kalou ba wallahi, akwai babbar matsala."

"Toh! Me ya faru?"

"It's a complicated case wallahi, ni dai da zaka zo gidan yanzu kawai."

"Jidda bata jin dadi ba zan iya barin ta ba, she needs me."

"Ayya, Allah ya bata lafiya, kaga Maman ma gasu nn sun fito ita da Aunty Nafi da Salma, bari naji zan kiraka."

"Ok, kace wa Maman na kirata bata daga ba."

"Okh ." Yayi hanging yana nufar wajen su,

"Mama,fita zakuyi?"

Wani kallo tayi masa ya sunkuyar da kansa k'asa dan yasan halin da Maman take ciki ba karami bane ba

"Tariq be kiraka ba?"

"Ya kira, ya kira ki ma baki daga ba."

"Good, idan ma yayi hakan ne dan kar mu hadu ni yanzu zanje har gidan nasa na same shi."

"Gida kuma Mama? Why not ki bari yazo, za'a iya solving issue din nan ba sai kinje ba."

Kallon shashen da Aunty Nafi da Salma ke tsaye tayi ranta ya kara baci idan ta tuno da abinda Salmar tace wanda tasan sharri ne kawai tayi wa Tariq din kuma da tainakon Nafin da tasan haka zasu yi mata da tun farko bata yarda da shawarar Nafin ba.

"Ina Sam?" Tace tana share maganar Fauwaz din, da sauri ya karaso ya duka ya gaishe ta,

"Muje."

"Mama bari na kaiku."

"Zaka iya biyo bayan mu, ku shiga muje."

Tace wa aunty Nafi ta shiga ita,zagaya wa sukayi Salma ta shige chan baya, security daya ya zauna a gaba sai Mama da Aunty N a tsakiya. Da sauri Fauwaz ya nufi wajen motar sa ya shiga yana kiran Ya Tariq din a waya amma sam taki shiga, key yayi ma motar ya bi bayan su yana cigaba da gwadawa.

Yana kwance a falo lokaci zuwa lokaci yana lekawa ya dubo Jiddan amma sai yaga tana bacci, sai ya dawo. Har bacci ya soma daukar sa yaji ana knocking a chan kofar main entrance din, Godiya ce ta fito daga kitchen taje ta bud'e sai ya mike ya fito daidai lokacin da Mama, Aunty Nafi, Salma sai Fauwaz dake bayan su suka shigo, da kallo ya bisu irin kallon mamakin nan, kafin ya karaso yana nazarin fuskar Maman da take a hade tamkar an mata mutuwa.

"Mama? Welcome."

"Ina ka ajiye wayar ka nake da kiran ka?"

"A falo na barta."

"Good, zauna." Tace tana nuna masa wajen zama ya zauna a darare duk jikinsa yayi sanyi dan be san dalilin zuwan nasu ba

"Salma, maimaita abinda kika fada mana ni da mamanki."

"Na'am?" Tace tana kallon TARIQ din da itama shi yake kallo

"Kiyi magana mana ba kallon sa zaki tsaya yi ba." Aunty Nafi tace tana tamke fuska

"Dama, dama ya Tariq ne."

Saukar da kai Mama tayi wani irin abu na taso mata tun kafin Salman ta yi maganar da ta gigita ta, ta kuma hanata bacci a daren jiya ko runtsawa bata yi ba.

"Muna jinki."

"Dama shine ya ke taba ni yana min wani abu shine jiya da ya dawo ya fara min wata irin magana ni kuma nace bana so sai ga jiddah nan ta fito shine ya kore mu yace mu bar masa gida."

Wajen sakwanni biyar maganganun nata suka dauka kafin su kai sakon zuwa kwakwalwar Tariq wanda ya kura mata ido kawai ya kasa furta ko kalma daya.

"Kaji abinda tace?"

Mama tace cike da kunya da takaicin hali irin na Nafi

"Ya Tariq kana ji kuwa?"

Fauwaz yace ganin kamar be san me ake cewa ba. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (48)

A hankali yanayin fuskar sa ya shiga chanjawa zuwa tsananin bacin rai, cikin kankanin lokaci kamannin sa suka sauya ya koma tamkar wanda be taba dariya ko murmushi ba a rayuwar sa, kallon yarinyar yake yana jin zai iya kakkaryata ya zubar a wajen idan har ya biyewa zuciyar sa.

"Baka ce komai ba." Mama tace tana kallon sa

"Me zai ce? Bashi da abin cewa ai, ni wallahi an cuce ni wallahi an cuci rayuwa ta."

Anty Nafi tace tana fashewa da kukan munafurci, be ko kalli in da take ba, ya cigaba da kallon Salman ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa dan kallon nasa ya fara bata tsoro, ba ita ba har Anty Nafin tsoro ya shige ta ganin yadda kirjin sa yake dagawa.

"Tariq!!!" Mama ta kwala kiran sa, ya juyo a nutse yana kallon ta tar,

"Na'am Mama."

"Baka ji me Salma tace ba?"

"Naji Mama." Yace yana kokarin daidaita calmness dinsa

"Amma ba zaka ce komai ba?"

"Bani da abinda zan ce Mama, in dai har wannan dakikiyar kazamar kuchakar yarinyar nan zata zauna ta tsara wannan maganar kuma ku zo dan tabbatarwa, bani da abinda zance akai."

"Tariq karka yi kokarin chanja maganar nan, kasan dai Salma ba zata maka karya ba ko?" Anty Nafi ta fada ganin kamar yanayin da yake ciki ya sassauta

"Da mahaifiyata nake magana ban sa dake ba!"

Yace mata a fusace, da karfi. Tsit tayi bata kuma cewa komai ba, ya maida hankalin sa kan Mama ya cigaba da magana

"Idan har yarinyar nan ta kara minti daya a gidan nan wallahi wallahi sai na ajiye alaka da komai na kakkaryata na zubar a wajen nan,."

"Saboda baka son gaskiya ko? Wallahi ba zan yarda dake ni sannan a hanani kuka ba, wallahi mahaifin ka zan gyayawa, ko ka auri Salma wallahi ko na fada masa, kunsan dai dan siyasa ne baya so sunan sa ya baci ko?"

"To hell with you!" Ya dake mata tsawa

"Ki fadawa duk wanda zaki fadawa wallahi, I don't care!"

"Fauwaz, take them out."

"Calm down Ya Tariq."

"Su fita nace!"

"Tashi Nafi, ma karasa maganar a gida." Mama tace tana kallon yadda yake huci

"Dole ya auri Salma wallahi dan ba zai lallata min rayuwar yarinya kuma yazo yace ba zai aure ta ba."

"Muje."

Tashi tayi tana cigaba da kumfar baki, Jidda da tun dazu take jin muryar sa a sama ce ta lallabo ta fito sanye da rigar sa sai yar hular da ta rufe gashin kanta,sun tashi kenan ta fito kallo ya dawo kanta, da sauri ta juya zata koma a tunanin ta basu ganta ba, sai jin Fauwaz tayi ya kira sunan ta

"Aunty jidda."

Tsayawa tayi ta juyo cikin matsananciyar kunya ta karaso falon ta duk'a kad'an tace

"Ina kwana?"

A gajarce Maman ta amsa tana kauda kanta dan kallo daya tayi wa Jiddan ta gano wani abu, Anty Nafi ta gaisar amma bata amsa ba sai Salma da ta banka mata harara, suka fice daga falon ya rage saura Tariq din da Fauwaz, zama Tariq din yayi yana tallafe kansa da hannayen sa biyu.

"Ya Fauwaz ina kwana?"

"Lafiya lou Jidda, pls ki kula da Ya Tariq bari na dawo."

Sai ya juya shima ya fice daga falon ya same su har sun shiga mota.

A gaban sa tayi kamar kneel down tana kallon hannun sa da ya tallafe fuskar sa dashi, hannu tasa ta kama hannun nasa ya dago idanun sa da suka rini sukayi jajawur ya zuba mata tsoro ya kamata ganin yadda suka koma.

"Ya kike jin jikinki?" Ya fada muryar sa a dashe kamar wanda yasha wani abu

"Naji sauki."

"Ok."

"Baka da lafiya ne?"

"I'm furious Jiddaaaa."

Sai ya saka hannu ya jawo ta jikin sa, ya rungume ta ko zai samu saukin abinda yake ji.

Fauwaz ne ya dawo ciki sannan ya cikata yana gyara mata jikin rigar

"Jeki ciki kinji? Karki damu."

Jiki a sanyaye ta shige ciki ya kalli Fauwaz yana tashi tsaye

"Ya za'a yi Ya Tariq? Menene abun yi? Kasan irin wannan sharrin issue ne very complicated, sannan kamar bata sunan mutum ne, hatta Baba idan abun nan ya fita sai sunan sa ya baci sosai duk da ba gaskiya bane."

"Fauwaz I don't care duk abinda duniya zata ce wallahi, this is a great lesson da ya kamata Mama ta dauka, da tun farko ba'a turo yarinyar nan gidan nan ba, ya hakan zata faru? But sai ta biyewa Anty Nafi which ita da kanta tasan how evil that woman is, duk saboda kishi, kishin da bashi da maaana bare tushe."

"But Aunty Nafi zata iya aikata komai to tarnish your reputation in dai har bukatar ta zata biya."

"Har abadah wallahi, kuma in dai ta cigaba da pushing akan maganar nan wallahi sai na bata mamaki ita da ballagazar yar ta."

"Calm down dan Allah, don't frustrate your self mu zauna a samu solution."

"Ba wani solution Fauwaz, tunda hakan suke so hakan za'a yi, muga wanda zai fasa ni dasu."

"Amma idan suka samu Baba da maganar fa? Kana ganin zai yarda?"

"I can't say ko zai yarda ko bazai yarda ba wallahi, ni dai tunda nasan ban aikata ba shikenan." Yayi maganar yana yarfa hannun sa gefe daya cikin bacin rai

"Nasan kana cikin bacin rai."

"Very! Kasan yadda sharri yake kuwa? Sharri irin wannan? ba zaka gane ba."

"I totally understand, nasan yadda kake ji, it's not easy amma kayi hakuri dan Allah, mu bi komai a sannu wasu matan are cunning yadda baka taba tunani, shaidan haka suke wallahi."

"Allah ya kyauta."

"Amin ya Allah, inaga bari naje duk yadda ake ciki zan fada maka."

"Ok thank you." Ya mika masa hannu sukayi musabiha sannan ya tafi shi kuma ya cigaba da zama a wajen ya kasa mikewa bare ya shiga ciki.

***Tunanin abinda ya kawo Maaman take tunda ta koma duk da taga Salma ta kuma san kila akan abinda ya faru jiya ne amma kuma ai be ci ace har sai Maman sunzo da kanta ba, bacin ran dake fuskar Ya Tariq din yasa ta tabbatar akwai matsala babba, wanda ta alakanta da yadda Maman bata son auren su. Shiru shiru be shigo ba gashi bata son komawa ko basu gama maganar ba, zama tayi ta cigaba da jiran sa har ta gaji ta shiga wanka tana fitowa ta ganshi yana duba wasu takardu, dagowa yayi ya kalle ta kad'an ya cigaba da abinda yake yi, wucewa tayi ta dauki kaya a closet ta saka daidai lokacin ya fice daga dakin ya dauki system dinsa ya fara yi mata processing visa!

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*

5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull