Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 11

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 11

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 11: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,481 words

Tun daga nesa TAIMIYYAH ta hangi Sani zaune tare da Baba mai-gadi.Ta cigaba da takawa a hankali har ta isa bakin gate ɗin,ta gaisar da su suka amsa a lakoci guda.Tana shirin fita daga gate ɗin ta jiyo muryan Anty Laurat na ƙwalla mata kira.Sai tai tsaye tana jiran ƙarisowan Laurat ɗin, "Anty Laurat gud morning." Cewan TAIMIYYAH da murmushi saman fuskanta a lokacin da Laurat ɗin ta ƙariso wajen.Anty Laurat sai ta aikawa TAIMIYYAH da harara tana faɗin "Ban amsawa wallahi,yanxu TAIMIYYAH don rashin kirki jiya kashe wayanki kika yi duk roƙon da bawan Allahn nan ya yi akan ki barta a kunne? Ni yanzu ya kirani yana min ƙorafi wai har yanzu ma ya yi ta neman line ɗin naki a kashe.Shine fa nace masa bari inzo inga ko lafiya,haba TAIMIYYAH ya da haka please?" Anty Laurat ta kai ƙarshen maganan idanunta akan TAIMIYYAH da ta wani narke fuska.Kafin tayi magana cike da shagwaɓa tana faɗin "Anty ni fa bansan me zance masa bane idan ya kira.Shiyasa na kashe wayan kuma dama ni bana kwana da waya a kunne." "Kin kyauta to,yanzu sai ki kunna tun da gashi ya damu ya na son yai magana da ke.Please! ki kunna wayan kafin ku isa skull ɗin,ni bari in koma dama shi ya fito dani,da yake jiya ya amsa numberta kafin ya wuce.Sai kin dawo bye." Cewan Laurat tana juyawa ta koma inda ta fito,ta bar TAIMIYYAH na taɓe baki ta juya ta fara takawa don fita daga gate ɗin.Tuni Sani ya fita har ya tada motan shiyasa tana isa bakin motan ta buɗe gidan baya ta shiga.Sani ya ja motan suna barin layin,ko kaɗan kuma TAIMIYYAH ba ta yi tunanin zata iya kunna wayan ba kaman yadda Anty Laurat ɗin ta roƙo.

__________

Suhailah ce zaune ita da qawarta ko ince aminiyarta Zubaida.A cikin falon gidan da ke sama a nan su kai masauki. An cika gaban Zubyn da kayan motsa baki,wacce a kallon farko za kaiwa Zubyn ka san cewa irin ƴan duniyan matannan ne masu buɗewan ido.Baƙace ɗik sai dai tana da matsakaicin kyau,da kuma dirin jiki me kyau.

Suhailah ta aje cup ɗin hannunta data shanye lemun Chivita,tana faɗin "Zuby yanzu kina ganin idan Maleek ya jaji bo aure ban gama shiga uku na lalace ba kuwa? Ina cikin matsanancin tashin hankali Zuby.Burina a yanzu bai wuce in samu ciki ba.Amma ga abinda likita ke faɗi wai haihuwan ma zan iya rasa ta baki ɗaya.Zuby nayi nadaman fara shan magungunan hana ɗaukan ciki.Kece duk kika bani wannan gurgun shawaran,ga shi ina shirin shiga masifan da bansan ta yadda zan iya tinkiransa ba.Ko kaɗan bana hango wasa a idanun Maleek,da gaske yake yi akan son haihuwa zai iya auro wata macen.Ba tare da yayi la'akari da halin da zan iya shiga ba, ki sanar da ni miye mafita yanzu?"

Yadda Suhailan tayi maganan hankali a tashe,yasa Zuby aje cup ɗin hannunta da ta cika da lemu ta shanye.Ta miƙa hannu ta dafa kafaɗan Suhailah tana faɗin "Calm down babbar Yarinya! Nifa ban ga wani abin ɗaga hankali har haka ba.Ki bari ku je can Egypt ɗin kiji me likitocin can zasu faɗi.Kuma maganan ya ƙaro aure to sai me tunda ba a kan ki kishiyar za ta zauna ba.Kuma in banda abinki idan ya auro wata ai tamkar ya auro ta don samun cikar burinsa na samun haihuwa ne kaɗai.Ba wai don zai yi mata soyayya irin yake miki bane,kinga ashe soyayyar dai tana gareki ne.Ni abinda nake so da ke ki koyi iya kissa da zaman duniya Suhailah.Ki zama mace me wayo da iya janyo hankalin miji,ki kwantar da kai ki dinga masa duk abinda ya ke so.Amma ko kaɗan ki daina nuna damuwanki akan abinda ki ka aikata,domin ba zamu dawo da hannun agogo baya ba.Ki nuna masa ko auren zai yi za ki goyi bayansa,in yaso idan matar ta haifa masa ɗan sai kiyi kissan yadda riƙon ɗan zai dawo hannunki.Kin ga zaki ƙarisa janyo hankalinsa kanki ke ɗaya.Daga shi har Hajjah ki nuna musu kin amshi ƙaddara ko da ance ba za ki haihu ba kin amince Maleek ɗin ya sake wani auren."

Zuby ta kai ƙarshen maganan tana wani kashewa Suhailah idanu,wacce ita kuma jikinta gaba ɗaya yai wani irin sanyi da kalaman Zubaidan.Wani sashi na zuciyanta na gaya mata tabi shawaran aminiyan nata,sai dai tsananin soyayar da take wa Maleek da kishinsa me zafi da take yi.Bata ji zata iya gani tana raye ya auro wata mace har ta iya dannewa ta nuna rashin damuwanta.Ta tabbar idan har zanen ƙaddara ya zanawa Maleek ƙarin auren wata mace bayan ita.To tabbas za'ai bikin tana gadon asibiti ne a kwance.

Suhailah ta dubi Zubyn cikin ido kafin ta soma faɗin "Zuby baki zo da shawaran da zan iya ɗauka ba a wannan karon.Domin har yau kin kasa gane wani irin zafin kishi na ke dashi akan Maleek ba.Taya kike iya tunanin zan iya rintse ido in kalli wata mace,a matsayin kishiyata har ta haifa masa ƴaƴa ba ni ba?Ba zan iya ba Zuby idan ko har na iya to ki tabbatar da zan kwanta ciwon da zai iya zama ajali na! Ina ma Maleek wani irin so me wuyan bari, sannan baki san waye Maleek a iya kula da mace bane musamman a shinfiɗa.Tabbas da sam ba zaki kalli idanuna ki bani shawaran wai in goya masa baya ba." Yadda Suhailah ta kai ƙarshen maganan hawaye na cika idanunta,yasa Zuby taɓe baki tana jifanta da wani irin kallo.Can ƙasan zuciyanta kishi da takaicin Suhailan ne kwance sosai,amma ganin Suhailah ta zubo mata ido yasa ta sakin murmushi tana faɗin "Suhailah shiyasa na ke faɗi miki kanki baya ja har yanzu.Sunan kinyi boko ne kawai amma sam baki da buɗewan ido,irin na matan zamani da suka san kan duniya.Baki san miye kissa da iya zaman duniya ba,yanzu fa kike tambayan mafita amma na kawo miki mafitan da zata anfane ki,kina kawo min zancen kishi da wani so.Ubanwa ya gaya miki dama akwai macen da aka taɓa mata kishiya da son ranta? Babu wannan macen duk wacce kika ga anyi mawa bata so aka yi.Amma hakan baya hana matan da suka iya bariki kwantar da kai har su cika burikansu ba tare da an gano haƙiƙanin manufan da ke zukatansu ba.Kin riga kin aikata abinda ya janyo miki illa,kina tunanin da Maleek ya ƙaro aure da rashin yardan ki,ba gwara ya ƙaro da yardan ki ba? Ko banza idan kishiyan ta shigo za ta shigo ne don kawai ta haifa masa ɗa,ba wai don zai yi mata so irin wanda ke ya ke miki ba.Daga lokacin da zata haifa masa ɗan,ke kuma a lokacin zaki sake kwantar da kai a baki riƙon ɗan.Kin ga babu me zargin ki sai ma tausayin ki da zai kama zuciyan Hajjah har ta goya miki baya wajen a baki riƙon ɗan.Daga kuma lokacin da ɗan yazo hannunki kece zaki raine sa irin yadda kike da burin ya taso.Amma yanzu idan kika bari kishi ya rufe idanunki har ƙaddara ta zana masa auren wata kina nuna zafin kishi da shirme to zaki ɓata goma ne ɗaya bai gyaru miki ba.Sannan idan baki aje son jiki da sakaci kin kama mijinki da kyau ba duk wacce za ta shigo cikin ruwan sanyi za ta gama da zuciyan mijinki.Ta kuma samar da abinda ke kika kasa samarwa.Yanzu ki bani lambansa zan taya ki bashi haƙury akan cewa kinyi nadaman abinda kika aikata,sannan zan sanar da shi laifi nane duka domin nice na baki shawara ba tare da mun san hakan zai iya janyo kowace irin illa ba.Ke kuma da zaran ya diro gari ina so yaga canji,ki tarairaye shi da kyau tare da samar masa dukkanin nutsuwa.Ko a fuska kada ki sake ki nuna masa cewa abinda likita ya faɗi yana damunki.Nuna masa za kiyi kin barwa Allah komi,ina fata kin fahimce ni?"

Zubaida ta ƙare maganan da jefawa Suhailah tambaya.Wacce ta zubawa Zubyn idanu kaman me son gano gaskiyan dukkanin kalaman Zubyn akan fuskanta.Ta gyaɗa kai kafin ta buɗe baki tana faɗin "Na gane Zuby gaskiya kin fini sanin kan duniya,kuma kanki yafi nawa ja.Tabbas hakan za a yi har Hajjah bazan sake nuna mata damuwa ta ba.Zamu bi su a duk yadda suke so.Koda auren zai ƙaro akwai plan ɗin mu a ƙasa.Idan kuma Allah yayi ikonsa na samu cikin ma kin ga shikenan komi yazo cikin sauƙi.Amma fa zanyi yaƙi me girma kafin in iya duk waɗannan abubuwan da kika zano." Suhailah tayi maganan murya a maraice,Zuby da har wani ajiyan zuciyan samun nasara ta saki,tayi saurin kamo hannun Suhailah tana faɗin "Karki ji komi za ki iya Suhailah sai dai baki sakawa zuciyanki cewa zaki iyan ba.Yanzu dai bani lambar ranshi ya daɗe ɗin,da zaran na isa gida zan zauna in tsara masa kalaman da zai gamsu da shi.Ai indai muna tare kisa wa ranki baki da sauran wani matsala.Irin wannan daula da kike ciki kina fantamawa,yaushe zan miki fatan wani abu ya raba ki da Maleek ɗin ki.Gashi kuma kina sakar mana muna dangwala ta ina zamu bari wani abu ya shige gabanki da zai baki matsala?Ki sawa ranki duk wacce za ta shigo to tamkar za ta zo bautan haihuwa ne ke kuma kina amshe ƴaƴan,kin ga kenan ke ce da riba ba ita ba.Aikin ki kawai ki cigaba da gyara kanki da jikinki,kina samar da nutsuwa a zuciyansa.Wata kuma tana aikin ɗaukan ciki tana haifewa,komi nata na yin ƙasa ke kuma na ki yana gyaruwa hhhhh.....!" Ta kai ƙarshen maganan tana bushewa da wani irin dariya na ƴan duniya,ita kuma sakarya Suhailah na tayata,lokacin da take karantowa Zuby numbern Maleek ɗin,har wani rawa zuciyan Zubyn ke yi wani abu na kewaye zuciyanta.Tana gama kwashe numbern tsaf tai saving da suna *My M.Ado* Suhailah sam bata san ko da wani suna qawar nata dake a matsyin bazawara tai saving numbern mijinta ba.Zuby ta cigaba da tsarawa Suhailah kalamai son ranta,bata bar gidan ba sai data tabbatar Suhailah ta hau kan duk wani gadan zare da take ɗaura ta akai.Sannan Suhailan ta haɗa mata sha tara na arziƙi cike da leda ta raka ta har bakin gate.Sukai sallama tana ji a zuciyanta bata da aminiya me sonta irin Zubaida Halliru. Koda ta dawo cikin gida kai tsaye wayanta ta ɗauka ta shiga neman layin Maleek ɗin,amma har wayan yai ringing ya katse bai ɗauka ba.Hakan yasa Suhailah aje wayan tana gyara kwanciyanta cikin seater ɗin.Ƙwaƙwalwanta na tariyo mata dukkanin yadda sukai da Zubyn da shawarwarin da ta bata.Ta lumshe ido tana fata kada ma Allah ya jarabceta da rashin samun haihuwan,bare har Maleek ɗin ya auro wata mace bayan ita.Sai dai can ƙasan ranta na gaya mata in kuma abinda bata so ɗin ya kasance to tabbas yadda duk Zubaidan ta tsara mata haka za ta bi...........✍🏻

_Ni dai Ɗansabo cewa na yi anya Suhailah na da man kai kuwa? 😁 amma bari dai mu cigaba da bibiyan su don ganin yadda wasan zai kaya._

Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻

https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb

*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*

*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

--------

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

*Bank Transfer* *Airtime Transfer*

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️

©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

*Page 25*

_______Lokacin dasu TAIMIYYAH suka fito wajen bakin gate,tun daga nesa idanunta ke hango mata mutum tsaye jingine da jikin mota,ya harɗe hannuwansa a ƙirji tare da kafowa ƙofar fitowa gate ɗin wajen idanu.

A cikin daƙiƙa kaɗan ƙwaƙwalwanta ya bata tabbacin cewa Naseer ne.Domin kallo ɗaya taiwa fuskansa ta gano hakan,don kamanninsa ne data gani a daren jiya kwance akan fuskar sa.Tayi saurin furta "Ya Allah!" A bayyane lokacin da ya fara takowa yana kusanto su.Zee tayi saurin duban TAIMIYYAH tana faɗin "Lafiya Namcy?" Sai dai kafin TAIMIYYAH taba Zee amsa har ya ƙariso wajen da sukai tsaye.Hakan yasa TAIMIYYAH ta gagara bai wa Zee amsa,sai kawai ma ta dafe ƙafanta ta fara tafiya don barin wajen.Hakan yasa Nass da ya ƙariso daf da Zee ɗin ya saki murmushi yana faɗin "Salamu Alaikum!" Zee ta ɗaga idanunta ta sauke a kansa tana amsa sallaman da ya yi,kafin ya ɗaura da faɗin "Qawar mu ko zaki taimakeni mu je ki taya ni rarraso waccar qawan taki please?"

Yadda yai maganan cike da magiya yasa Zee sakin murmushi kaɗan tana faɗin "Eh mu je badamuwa." Daga haka suka rufawa TAIMIYYAH baya wacce har ta kai bakin titi, tana tsaye daga gefe guda.Ta jingina da jikin wani ƙarfe don jin daɗin tsayuwa sabida laluran ƙafanta.Lokacin da su Zee suka iso wajen qamshin turarensa na AZZARO WANTED,ya fara sanar mata da isowansu wajen.Sai ta yi saurin haɗe fuska cike da zunɓuro baki take duban Zee dake faɗin "Haba Namcy ya da haka kuma? Zaki taho babu ko jira to ai gashinan na biyo ki,ga baƙo nan kuma ki ji da shi please!"

Cikin murya me cike da shagwaɓa TAIMIYYAH ta kai dubanta kan Nass tana faɗin "Ina yini." Ya saki kyakykywan murmushi yana jin wani irin relief! Daga jin muryanta kawai da yayi a yanzu.Idanunsa a kanta sosai yake faɗin "Ba zan amsa ba Baby,sabida gaba ɗaya yau kin tashi hankalina,kin kuma shiga hakkin zuciyata ta hanyar hana mata dukkanin sukuni.Har sai yanzu dana bayyana a gaban ki sannan na samu nutsuwa,kin kyauta kenan eyim Luv?" Ya ƙare maganan cikin wani irin salo daya saka Zee murmusawa tana duban yadda TAIMIYYAH ta wani kwaɓe fuska kaman zata saki kuka,ita sai abin ma yaso bata dariya,amma ta maze tana kallon wannan drama da ake bugawa.Shi ko Nass ganin TAIMIYYAN taƙi amsa shi sai ya ɗaura da faɗin "To Baby tunda ba za ki magana ba mu ƙarisa ki shiga mota in sauke ki a gida please! Don ba zan so wannan ranan ya cigaba da taɓa min ke ba.Please! qawarmu kisa baki ko ke zata miki magana." Ya ƙare maganan yana maida dubansa kan Zee cike da magiya.Zee ta saki murmushi tana matsawa kusa da TAIMIYYAH sosai,cikin ƙasa ƙasa da murya ta ke faɗin "Qawata ya da shariya haka kuma,miye laifin wannan Handsome guy ɗin daya mato a kanki? Please mu ƙarisa in raka ki kawai ki shiga ku wuce,kin ga mutane sai kallo mu mutane suke.Amma fa gaskiya kinyi Babban kamu Namcy." Zee tayi maganan cike da tsokana,a karon farko da TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta masu tsananin haske ta saukewa Zee wani hararan daya sa Zee ɗin kwashewa da dariya.Ta sake ƙasa da murya yadda Nass daya matsa gefe ya basu wuri ba zai ji ba,ta furta "Wayyo Qawata wannan harara ai sai ki sa in suma,afuwan please karki gwalesa mu je ku wuce please!"

"Amma Zee kin san ba mutunci bane aga mace a motar saurayi.Me zance idan wani a cikin ƴan gidan mu yaga na sauka a motar sa?Duka fa ban san ko shi waye ba,a jiya ɗaya da haɗuwan mu fa,kawai sai yau a ganni a motarsa gaskiya bazan iya ba.Ki je kawai ki san me zaki faɗi masa ya kama gabansa." TAIMIYYAH tai wa Zee maganan cikin ƙasa da murya itama,kuma sosai Zee ɗin ta fahimci me TAIMIYYAN ke nufi.Don ko ita bata ɗauki shiga motan saurayi a mutuncin ƴa mace ba,har gara gara ma idan ansan da shi a gida,an kuma yar je masa ixinin zuwa zance,Zee ta gyaɗa kai cike da gamsuwa tana faɗin "Na fahimce ki ina zuwa.Bari naje na san me zan sanar masa."

Daga haka Zee ɗin ta nufi wajen Nass dake faman danna waya,ya ɗago yana duban Zee ɗin bayan ya amsa sallaman da tayi masa,ya furta "Mu je ne ta amince Friend ɗin mu?"

Zee ta murmusa kaɗan tana faɗin "Ayyah! Abokin mu kayi haƙuri a she ta riga tayi da me kawo ta cewa ya zo ɗaukanta.Kaga kuma babu daɗi a ga kaine ka sauke ta hakan zai iya zama abin yi mata faɗa a gida.Kayi haƙury next time insha Allah ba zamu gwale ƙoƙarin ka ba."

"Alright! Babu damuwa,amma fa ba haka naso ba gaskiya.Kuma ina roƙon alfarma don Allah ki rarrasar min ita kice ta kunna wayanta da zaran ta isa gida.Wallahi na azabtu haka nan a taimaka min a kunna wayan." Cewan Nass cike da magiya idanunsa na kan TAIMIYYAH da tayi tsaye a inda take ko da wasa bata waiwayo in da suke tsaye shi da Zee ba.Ya ɗauke idanunsa daga kanta lokacin da Zee ɗin ke bashi tabbacin zata sanya TAIMIYYAH ta kunna wayan.Su kai sallama da Zee ɗin ya juya zuwa wajen motar sa, ita kuma Zee ta nufi wajen TAIMIYYAH tana zayyane mata yadda tayi da Nass ɗin.Ta ƙare maganan da faɗin "Don Allah Namcy ki bashi dama ki sauraresa ki ji da wacce ya zo? Ni dai a haka yayi min wallahi kaman zaiyi hankali.Ga shi kyakykyawa ga iya Dressing gaskiya gayen ya haɗu.Da alamu kuma masu gidan rana sun zauna masa.Ki dubi fa motar da yake hawa gaskiya kun dace da juna, ki bada kai kawai qawata mu sha biki nan bada jimawa ba."

TAIMIYYAH wannan karon ma harara ta aika wa Zee ɗin,tana faɗin "Wallahi baki da mutunci wato in bada kai,lallai ne ni kam tsoron ma bashi dama nake yi don da alamu zai yi baƙin naci,da takura ni kuma bani son hakan.Dadai ace ma yazo a me lalura irin tawa ne wataƙil dana bashi space kaɗan in ga ko zan iya gwada ɗanɗana ya soyayyan ta ke.Amma wannan sai ina ga kaman yafi ƙarfin me lalura iri na,gurguwa dani a ganni da wannan ke kinsan sai anyi da ni an kuma ga zaƙewata da yawa."

TAIMIYYAN ta ƙare maganan cikin wani irin sanyin murya,me cike da rauni da ya motsa zuciyan Zee sosai.Taji ƙarin ƙaunan TAIMIYYAN da tausayinta na sake kama ruhinta.Ta dubi TAIMIYYAN da kulawa sosai take faɗin "Ayyah! Qawata don Allah ki daina irin wannan maganan.Kada kiyi saɓo ko butulce ma ni'imomin da Allah yai miki,ke dai kawai ki bashi dama Allah ya fimu sanin yadda ki ke,shi kuma ya san me yasa ya jefo miki shi cikin rayuwanki a hakan.Kin ko ga yadda nake hango tsantsan ƙaunar ki cikin idanunsa kuwa? Gaskiya bana ji wannan guy ɗin da wasa ya zo.Da alamu da gaske ya kamu da son ki Namcy.Ki cire duk wani tunani mara kyau ki bashi dama ki kuma cigaba da Addu'a shi Ubangiji ya fimu sanin hikimansa na barin ki a yadda kike,ki godewa Allah TAIMIYYAH naki laluran ma mai sauƙi ne,wanda suka fiki nakasa ma Allah ya basu mijin aure bare ke da Ubangiji yai ma baiwan halitta me fisgan hankali."

Zee bata bar TAIMIYYAH cewa komi ba,ta cigaba da faɗi mata kalamai na ƙarfafawa,da kawo mata misalai na nakasassu kala kala.Wanda kuma sun yi aurensu a hakan ba kuma guragu suke aure ba da yawan su.Har Zee ta tarewa TAIMIYYAN abin hawa ƙarfafata take yi akan ta daure taba Naseer dama.TAIMIYYAH ta jinjina kai a lokacin da suka isa bakin Napep ɗin, ta shiga ta zauna tana yiwa Zee godia,me Napep ɗin ya tashe mashin ɗinsa suka harba bisa titi.TAIMIYYAH ta daɗe tana jin tasirin kalaman Zee na keta zuciyanta,har tana ji cewa za tai ƙoƙarin ganin ta fara sauraran Nass ta ga da wacce ya zo? Sun iso layin su TAIMIYYAH na jinta a gajiye sosai.Ga kanta dake ɗan mata ciwo sama sama,a haka ta fito tana zuge jaka ta baiwa Me Napep ɗin kuɗinsa,ta juya tana nufan gate ɗin shiga gidan,ta ƙaramin ƙofa inda ake shiga ta nufa bayan ta tsaya ta gaida Me gadi sai ta nufi hanyan isa Sasan su.Sam bata kula da Motar Guggo Bilki da suka iso garin a yau ba,ta nufi cikin Sasan su bakinta ɗauke da sallama.Yasmeen budurwar ƴar Guggo Bilki wacce za suyi sa'an juna da su TAIMIYYAN.Itace ta fito a guje tana wa TAIMIYYAH sannu da xuwa.Da wani irin murna TAIMIYYAH ta washe baki tana duban Yasmeen data ƙariso ta rungumeta take furta "Wash! Yasmeen sai ki yarda ni ai,kin ga yadda kika narka uban ƙiba kuwa, sannunku da xuwa." Yasmeen ta saki TAIMIYYAH tana faɗin "Sannu Sis TAIMY,kin ji yadda na ƙosa ki dawo kuwa,wayyo nayi missing zuwa Zaria irin sosai ɗinnan.Duk na ƙagu mu iso in sanya ki cikin ido na."

"To ai gashi kin sanya ni a idanun naki,ni ma na yi kewanki My Headache.Yanzu shikenan bani da sauran hutu sabida sani magana da zaki dinga yi." TAIMIYYAH tayi magana tana sakin dariya ganin yadda Yasmeen ta cuskune fuska,su ka ƙarisa falon Iyah da sallama idanun TAIMIYYAH na sauka akan Guggo Bilki.Ta ƙarisa gareta tana faɗawa jikinta tana faɗin "Oyoyo Guggo na sannu da zuwa." Guggo Bilkisu ta rungume TAIMIYYAH tana faɗin "Oyoyo! ɗiyata sannunki da dawowa,kin ga yadda kika koma wata baturiya,me Iya wai take baki ne kullum kike sake zama wata kaman baturiya?" Iyah dake kallon su murmushi yaƙi barin fuskarta sabida murnan zuwan tilon ƴarta mace sai cewa tayi "Babu abinda nake bata ni,tsabar dai kwanciyan hankali ne da hutu da take ciki yasa take ƙara kyau da cika kullum.Amma ja'iran a hakan bata ko so ayi zancen kauda ita,ki duba min yadda kullum take ƙara wani cika ƙirji kaman ya fashe,amma wai bata son zancen aure." Guggo da Yasmeen ne suka kwashe da dariyan zancen Iyah,hakan yasa TAIMIYYAH kwaɓe fuska kaman zata saki kuka take faɗin "Kai Iya! Kai Iya! Ni wallahi kinsa min ido da yawa a gidannan,kawai ki fito fili kice kin fara gajiya dani ko kin daina sona." TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana tashi daga jikin Guggo Bilki.Iyah ta aika mata harara tana faɗin "Kya dai ji da shi,ba ɗaya cikin duk abinda kika lissafa,zancen aure ne dai sai anyi miki har sai kinyi zuciya kin tsayar da mijin,ja'ira kawai shagwaɓaɓɓa."

TAIMIYYAH ta miƙe fuu...! dafe da ƙafanta ta fara takawa ta nufi ɗaki.Tana jiyo su Yasmeen na mata dariya kafin Yasmeen ɗin ta biyo bayanta zuwa ɗakinta.Ta tadda TAIMIYYAH na cire kayan jikinta zata shiga toilet watsa ruwa,xama tayi daga bakin Bed tana faɗin "Haka kike kwasan Drama da tsohuwar can Sisi?" TAIMIYYAH ta sake kwaɓe fuska tana faɗin "Rabu da Iyah kawai ke dai Yasmeen,wallahi ta saka min ido komi maganan aure,ita ko tsoran a wulaƙanta mata ni bata yi.Ni gurguwa ina naga ta wani xancen aure in ba irina zan aura ba." Yasmeen ta zabga ma TAIMIYYAH harara tana faɗin "Bismillah! Zaki fara ƙonan rai ba,da anyi maganan aure ki fara kiran kanki gurguwa.Ke kaza da kaza,to wallahi wannan karon zamu hau sama in baki daina min banzan zance irin haka ba.Allah sa ke kika fi ko wace mace gurgunta sai mun aurar dake sai dai mijin bai zo ba."

Yasmeen ta ƙare maganan tana sake tsuke fuska.TAIMIYYAH sanin halin Yasmeen na ɗaukan zafi yasa ta sakin murmushi tana faɗawa toilet abin ta,tafi kowa sanin Yasmeen ta tsani tana kiran kanta gurguwa.Shiyasa basa shiri dasu Zuhurah sosai,sabida yadda suke kiran TAIMIYYAH gurguwa,hakan yasa in dai Yasmeen tazo hutu basa ma yin duk iskancin da suke wa TAIMIYYAN.Don sosai Yasmeen ke gwaɓa musu ba daɗi su ma,don haka nema basu damu Yasmeen ɗin ta zo garin ba.A cewan su bata ƙaunar su yadda take ƙaunar TAIMIYYAH,ita kaɗai take so.

Lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga wanka,har lokacin Yasmeen na ɗakin.Tayi kwance akan gadon TAIMIYYAN,tana faman kallon hotunan girke-girke kala kala acikin wayan TAIMIYYAH.Da yake ita ba gwanar sanyawa waya code bane don gani take ita kaɗai take rayuwanta a sasan Iyah.Bata da me zuwa yace zai dinga mata taɓe taɓe a wayan,shiyasa sam bata sanya ma wayan Code ba.Ta wuce wajen kayanta direct tana ciro doguwar Riga mara nauyi na shan iska ta saka,ta juyo kenan don yiwa Yasmeen magana wayanta dake hannun Yasmeen ya fara kuka.Sai Yasmeen ɗin ta tashi daga kwance ta zauna tana miƙowa TAIMIYYAH data iso bakin gadon wayan tana faɗin "Ungo wani number ne ke kira." TAIMIYYAH ba tayi magana ba ta amsa wayan tana receiving ta kai wayan kunni bakinta ɗauke da sallama.Daga ɓangaren Nass har wani ɓoyayyen ajiyan zuciya ya sauke lokacin da sassanyar muryar TAIMIYYAH ta isa ga kunnuwansa.Ya lumshe ido yana faɗin "Ranki ya daɗe ina fata banyi gaggawan kira ba,na kasa samun nutsuwan zuciya ne hope kun isa gida lafiya?"

TAIMIYYAH data kai zaune a bakin gadonta,ta ɗan lumshe ido da taɓe baki tana faɗin "Lafiya lau,amma yanzu abinci zan ci, in babu damuwa later sai mu yi magana please!"

Naseer daga ɓangarensa,ji yayi ina ma suna kusa ne yana kallon yadda ƙaramin bakinta ke furta kalaman.Ya sauke ajiyan zuciya yana faɗin "To Baby zan barki kici abinci,amma sai kinyi promise ɗin cewa kina kammalawa zaki min ko da flashing ne saina kira.Inba haka ba kici abincin ina tare da ke ni bazan gaji ba,sai na dinga sauraran yanayin taunan Babyna.Hakan ya wadatar da ni." Yadda yayi maganan cikin wani irin salo na jan hankalin me sauraransa,yasa TAIMIYYAH rufe ido kaɗan tana jinjina rigima da wayo irin na Nass ɗin.Aahankali tayi magana cikin low voice ɗinta take faɗin "I will call u insha Allah bye!" Daga haka tayi cuting call ɗin tana maida wayan Silent,ta aje bisa Bed tana miƙewa ta bar ɗakin,tuni dama Yasmeen ta fita ta bata waje tunda ta fara amsa wayan,hakan kuma ba ƙaramin daɗi yaiwa TAIMIYYAN ba.Wajen cin abinci Direct ta nufa ta samu Yasmeen ta zuba tana ci itama,da alamu tun da suka iso bata kula taci abincin bane sai yanzu.TAIMIYYAH tayi joining ɗin Yasmeen suna cin abincin tare, har su ka cinye wanda Yasmeen ɗin ta ɗiba.Suka ƙara wani suna ci jefi jefi suna taɓa hiran yaushe gamo har suka kammala cin abincin,su ka tattarro zuwa cikin falon Iyah,inda Guggo Bilki da Iyah suka buɗe babin hira.......✍🏻

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY

Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Readers Also Read