Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 13
Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 13: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…
4,426 words
TAIMIYYAH ta taɓe baki tana faɗin "To ai da kema an je da ke kawai unguwar baki dawo ki dame ni ba." Yasmeen ta saki dariya tana faɗin "Ai ko yanzu kina iya maidani can,ƴar rainin hankali kawai.Ina sha ba missn ɗina kika fara ba na ga har da min 2 misscall, irin indawo da wuri ɗinnan." Yadda Yasmeen ta ƙare maganan da kashewa TAIMIYYAH idanu,yasa TAIMIYYAN sakin dariya sosai tana faɗin "Wannan Babyn wallahi ƴar duniya ce ke."
Kafin Yasmeen tace komi kiran Nass ya shigo wayan TAIMIYYAH.Wannan kuma shine kira na biyu a yau ɗin da yayi mata, don kafin ta fita skull ma sun yi waya da shi,ta wani narke face da taɓe baki irin zai takura ta ɗinnan.
Ganin kiran zai yanke yasa ta ɗagawa da kai wayan kunni.Tana amsa sallamansa da sweet voice ɗinta, da ke sake narkar da Zuciyar Nass ɗin.
"Baby hope kin dawo lafiya,ina fata dai ranan yau bai taɓa min ke ba?" Cewan Nass ɗin bayan ya amsa gaisuwan da TAIMIYYAH tai masa.TAIMIYYAH ta wani narke murya tana faɗin, "No bai taɓani sosai ba kam,cox around 12 ma na shigo gida." Yadda tai maganan tana wani shagwaɓa yasa Yasmeen da ta zuba mata ido kwashewa da dariya.Murya can ƙasa ƙasa ta furta "Wow! Shegiya luv ta fara aikinta wallahi,duk mutum ya gama cika baki wannan uwar shagwaɓan sace zuciyan duk ta mecece?" Ta ƙare maganan tana sakin dariya cike da tsokana.Ita ko TAIMIYYAH sai faman danno mata harara take,ba daman kulata tunda Nass ɗin yana mata magana.
Sun daɗe sosai da Nass ɗin suna waya.Yana faman zuba mata hira,da gaya mata kalamai na sace zuciya.Daga ƙarshe sukai sallama akan cewa sai ya sake kira zuwa anjima.
TAIMIYYAH bayan ta sauke wayan daga kunni ne,ta dubi Yasmeen tana faɗin "Wallahi Yasmeen kin shiga uku da sanya ido,in banda gulma ma miye na wani zama ki tasa ni gaba da kallo, har ki ga me nake yi."
Yasmeen ta saki dariya tana faɗin "An zauna ɗin,nima course nake so inyi, kona samu in iya irin wannan shagwaɓar da zan sake sace zuciyan Aliyu na." Suka saki dariya a tare lokacin da Yasmeen ta kai ƙashen maganan,kafin su rankaya su fito zuwa falon Iyah don yin Lunch.
Suna cin abincin ne suna hiran su kaɗan kaɗan.Sunyi nisa cikin cin abincin, Zuhurah da Anty Laurat suka shigo ɗauke da abincin Iya.
Direct wajen cin abincin suka nufo suna aje kulolin abincin daga gaba kaɗan.TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta tana dubansu kafin ta furta, "Sannunku Anty Laurat."
Laurat ta saki murmushi tana faɗin "Yauwa sannu Besty,ashe kin dawo skull ɗin koda yake yau Friday, na manta da wuri ku ke tashi." Ta ƙare maganan tana zama kusa da TAIMIYYAN.Ita ko Zuhurah sai ta samu kusa da Yasmeen ta zauna suna magana, ba tare da tabi ta kan sannnun da TAIMIYYAH tai musu ba.Yasmeen suka gaisa da Laurat,tana musu tayin cin Dambun da a kallo ɗaya Laurat ta ji ya shiga ranta.Hakan yasa ba ta wani ɓata lokaci ba wajen ɗaukan spoon ta fara ci,daɗin Dambun dana sauces ɗin da akai masa na ratsata. Ita ko Zuhurah cewa tayi bata ci ,sabida ita ƴar gaye ce ba ta cin Dambu.Shiyasa ma ta baro wajen cin abincin ta nufi cikin falo don gaida Iyah,wacce ke zaune ta kunna TV tana kallon tashar Saudi Sunnah. Da sakin fuska ta amsa gaisuwar jikanyan nata tana faɗin "Yau an ga daman shigowa gaida ni kenan,ya uwar ta ku?"
"Lafiya lau Iyah,ai dama ke ɗin ce baki son muna shigowa.Sai kice wai muna hantaran TAIMIYYAH,kaman wasu yara ai yanzu an girma Iyah." Cewan Zuhurah tana hararan Iyah ƙasa ƙasa.Iyah dake kallonta kar! Ta aika mata daƙuwa tana faɗin "Ungu nan mutumiyar banza,kin harari Zuwairah ne ba Iyah ba.Kuma da kike faɗin kun girma ina girman yake tunda baku fasa ci mata fuska da kiranta da gurguwaba,daɗin abin dai kuma mata ne.Ina jiye muku randa Ubangiji zai nuna muku isar sa da ikonsa,shashashai kawai marasa tunani.Inma banda sakarci ku taso tare gunin sha'awa, lokaci ɗaya don uwar ku na muku huɗuban tsiya,sai ku biye tata ku watsar da haɗin kan da kuka ta so da shi.A ce Sadeeq ne kawai me hankali a cikinku da bai biye ta uwar na ku, tunda shi yasan abinda ya ke yi.To ku dai bi a hankali ni gaskiya na ke faɗa muku,ku da kuke ganin ba'a jarabce ku da nakasanba ba wai kun fita bane.Haka Allah yaga dama ya bar ku, itama kuma bawai baya son ta bane da ya mayar da ita hakan.Ni dai ina muku nasiha da ku haɗa kai ku so juna kuyi zumunci a tsakanin ku,idan kuma baku ji ba akwai ranan da za ku yi nadama yana zuwa." Daga haka Iyah ta maida hankalinta kan TV. Bata sake bi takan Zuhurah da ke wani kumbure kumburen fuska ba,daga ƙarshe ma ta koma can ƙarshen kujeran falon ta zauna tana danna waya. Dawowan su TAIMIYYAH cikin falon yasa Zuhurah maida hankalinta wajen Yasmeen suna hira.Ita kuma TAIMIYYAH suna hiran su da Anty Laurat, akan wani online class da zasu shiga, na koyan yadda ake haɗa Graphics.
Su Zuhuran sun daɗe sosai a Sasan Iyah, don har Guggo Bilki ta dawo suna nan,sai da aka kira la'asar sannan suka bar Sasan Iyah.
*Around,8:45Pm.*
Su TAIMIYYAH ne zaune gaba ɗayansu suna yin Dinner.Bayan ita da Yasmeen sun dawo daga gaida Baba Sani,da ya dawo ɗazu da Magriba.
TAIMIYYAH ita ce tai sarving Iya da Guggo Bilki tuwan shinkafa miyan taushe.Wanda aka wadata miyan da naman kan sa,da zallan tsokar kaza sai qamshi yake.
Bayan ta gama zuba ma su Iyah, ita sai ta zuba Rice and Stew da aka kawo daga Sasan Baba Sani.Ta zabga uban haɗin Salad da ya rinjayi rabin shinkafar da ta zuba ɗin.
Yasmeen kuwa ita tuwan ta zuba tana ci,kaman su Iyah. TAIMIYYYAH kaɗai ce dama bata faye son tuwan Rice ba sam!
Sunyi nisa cikin cin abincin,sallaman Yah Sadeeq daga can ƙofan shigowa falo ya katse musu ɗan hiran da suke yi.Iyah ce ta ɗaga murya tana amsa masa sallaman, da bashi izinin shigowa.
Lokacin da ya iso cikin falon tuni qamshinsa na turaren BENTLEY ya gama isowa hancin TAIMIYYAH.Ta ɗaga manyan idanunta tana kallonsa a lokacin da yake ƙarisowa har wajen da suke cin abincin,ya samu wajen zama kusa da Guggo Bilki yana gaisheta.Ta amsa cike da kulawa tana faɗin "Su Sadeeku an zama magidanci auren kawai ya rage,gaskiya ayi a fito min da suruka haka nan." Ta ƙare maganan cike tsokana,shi ko Yah Sadeeq ɗin sai ya maida dubansa wajen da su TAIMIYYAH ze zaune yana amsa gaisuwan Yasmeen,kafin ya baiwa ya mai da wa Guggo Bilki martani da faɗin "Soon zan fito da ita Guggo Bilki ku dai kawai ku taya ni addu'a." Ya ƙare maganan yana maida hankalinsa wajen Iya ya gaida ta,ta amsa da kulawa kafin muryan TAIMIYYAH ya ratsa kunnuwansa tana faɗin "Yah Deeku sannu da zuwa ina yini." Sadeeq ya ɗaura manyan idanunsa akanta yana faɗin "Lafiya lau Baby ya skull?" TAIMIYYAH ta dubesa tana bashi amsa da "Lafiya lau Yah Deeku." Sai dai kafin Yah Deekun yace komi wayan TAIMIYYAH ya fara haske alamun shigowan kira,sai tayi saurin duban screen ɗin wayan don ganin waye me kiran? Idanunta suka sauka akan sunan da tai saving da NASS,sai kawai ta ɗauke kai ta basar da kiran har ya yanke ba ta ɗaga ba.Lokacin da wani kiran ya shigo dai-dai da sallaman Megadi ne daga bakin ƙofa,Yasmeen ta amsa sallaman Baba Megadin tana tambayansa ko lafiya? Kansa tsaye ya furta "Ranki ya daɗe baƙon TAIMIYYAH ne ya iso yana waje,shine yace don Allah na isar da saƙo ya kira bata ɗaga ba,a shigo da shi kaman wancan lokacin?" Iya tayi karaf ta amsa da faɗin "Eh! Kace ya shigo sai ka aje musu kujeru kaman yadda ka yi wancan karon." Tukur Megadi ya amsa da "Angama Hajiya." Daga haka ya bar wajen don zuwa ya aiwatar da umurnin Iya,daga cikin falon Iyan kuwa Yah Sadeeq ne ya zubawa TAIMIYYAH idanu babu ko ƙiftwa,zuciyansa na wani irin gudu da baisan dalili ba.Ita ko TAIMIYYAH tai ƙasa da kai takaicin duniya na rufeta na yadda Nass zai zo bai sanar mata ba,bayan sunyi waya har sau uku a yau ɗin,ta kasa kallon kowa sabida kunyan da ya mamayeta.Muryan Iya ne ya shiga kunnuwanta inda take faɗin "Maza tashi ki je kinyi wani zaune kaman mara gaskiya,Yasmeen rakata ku je in kun gaisa sai ki dawo ki ɗaukar masa ruwa da lemu." Iya tayi maganan cike da bada umurni,hakan yasa daga Yasmeen har TAIMIYYAN suka miƙe simi simi Suka nufi hanyan ɗakin TAIMIYYAN,Sadeeq ya bi bayan TAIMIYYAN da kallo tamkar idanunsa za su faɗo ƙasa,tuni yaji wani irin duhu na mamaye zuciyansa,bai kuma cewa komi ba ya miƙewa ya bar falon.Daga Iya har Guggo Bilki da tausayin Sadeeq ɗin ya kama su ka bi shi da ido,Iya na faman taɓe baki.Guggo Bilki ta furta "Allah sarki! Da gaske Sadeeq soyayyar TAIMIYYAH ya yi masa kamu me kyau,da alamu dannewa kawai yake don yasan hakan shine mafita tunda uwarsa ba ta so,wallahi tausayi yake bani sosai Iya." Iya ta sake taɓe baki tana faɗin "Sai haƙury Bilkisu don ni tausayinsa ba zai rufe min ido ayi abinda zai zo ya cuci baiwar Allah ina ji ina gani ba,don yadda Zuwairah ke nunawa yarinyar ƙiyayyah tun tana ƙarama abin bana lafiya ba ne.To kin ga ina zan yadda in ɗaure gindi ayi haɗin zumunci su haɗu da uwarsa da qannensa suna cusguna mata,o'o'oh! Gara kowa Allah ya haɗa shi da dai-dai shi." Iya ta ƙare maganan tana tashi ma ta barwa Guggo Bilki wajen,don ita sam bata ma son ana ɗakko maganan wai Sadeeq na son TAIMIYYAH.
Sanye da dogon Hijab TAIMIYYAH ta fito kalan Coffee da ya haske fuskarta.Ita kuma Yasmeen ta yane kanta da babban Veil hannunta riƙe da wayanta,suka wuce Guggo Bilki suka nufi can wajen Nass,wanda tuni ya jima da shigowa cikin Compound,yana zaune bisa ɗaya daga cikin fararen roba guda biyu da Tukur ya aje,bayan ya sanya farin tebur daga tsakiya idan za'a iya aje abin motsa baki akai.
Tunda su TAIMIYYAH suka fito daga Sasan Iya,idanun Nass ke kan TAIMIYYAN yana kallon yadda suke jerowa da juna cikin nutsuwa,salon tafiyan TAIMIYYAN na motsa zuciyansa matuƙa.Tare da jin ƙarin ƙaunar ta da tsa-tsan tausayinta na sake ratsa jinin jikinsa.........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 28*
__________Lokacin da su TAIMIYYAH suka ƙariso wajen.Nass ne yayi saurin tashi yana janye ɗaya kujeran baya TAIMIYYAH ta zauna,yana faɗin,
"Ran Babyna ya daɗe, barkan ku da fitowa.
Yasmeen ta saki murmushi tana gaida Nass,ya amsa da sakin fuska sosai,sai lokacin TAIMIYAH ta saci kallonsa.Yana sanye cikin wata Light Brown Wagan-bari,da ya yi masa matuƙar kyau.Kansa sanye da hulan ƙube daya zauna akan sosai,sai qamshin AZZORO WANTED,ke tashi a wajen.
Yasmeen komawa tayi cikin gida bayan sun gama da Nass ɗin,don kawo masa lemu da ruwa,kaman yadda Iyah tace.
Har Yasmeen ta kusa isa bakin ƙofan shiga Sasan Iyah.ta jiyo muryan Yah Sadeeq na kiran sunanta. Hakan yasa ta waiwaya tana hangosa daga can wajen parking space na gidan.Yana tsaye ya jingina da jikin motarsa,sai ta juya tana takawa zuwa wajen nasa. Ta tsaya daga gefen damansa tana faɗin ,"Yah Sadeeq kaine anan,gani tuh."
Ya ɗaga manyan idanunsa da suka sauya launi.Yana kallon Yasmeen ɗin cikin ido yake faɗin,
"Waye wancan Guy ɗin Yasmeen,tell me yaushe ta fata sauraransa?"
Ya yi maganan cikin very low voice,daya sanya Yasmeen saurin dubansa.Ya aika mata harara yana faɗin "Amsa zaki bani ko kallona zaki tsaya yi?"
"Kayi haƙury Yah Sadeeq,ni ma bansan yaushe ya fara zuwa ba,amma dai bana jin sun kai 2 weeks da haɗuwa." Yasmeen tayi maganan tana gujewa sake duban fuskarsa.Shi kuma ya wani sauke numfashi a hankali yana faɗin "Aright! go."
Daga haka bai sake cewa komi ba.Ya buɗe front seat na motansa ya zauna,yana me jingina jikinsa da jikin seat ɗin sosai,tare da maida idanunsa ya lumshe.Zuciyansa na sake ɗaukan wani irin zafi da suya,gaba ɗaya soyayyan TAIMIYYAH da yake ƙoƙarin adanawa ya binnesa can ƙasan zuciyansa ne ya taso baki ɗaya.
Don a yanzu gaba ɗaya wani irin zazzafar soyayyarta haɗi da kishinta me tsananin zafi yake ji.Irin wanda bai taɓa tunanin zai ji ba.
'Yaushe TAIMIYYAH ta fara soyayyah ba tare da ya sani ba.A ina ta haɗu da gayen kuma shin tana son shi kenan,da har ta bashi daman zuwa wajenta taɗi?"
Waɗannan tarin tambayoyin ne suka haɗu suna amsa kuwwa! A tsakar kansa.Ba ya ji kuma zai iya rintsarawa a daren yau ba tare da yaji amsa daga bakin TAIMIYYAH ba.
Yasmeen kuwa bayan ta baro wajen Yah Sadeeq ɗin.Tana tafe ne tana mamakin yadda duk ya wani birkice daga ganin TAIMIYYAH da wani.Don ita ta ɗauka cewa tunda ya haƙura da TAIMIYYAN idan ya ganta da wani bazai ji komi ba,har ta kai Sasan Iyah mamaki bai bar zuciyanta sukuni ba.
Direct kitchen ta nufa ta ɗauki madaidaicin Tray.Ta ɗaura ruwa biyu da Juice ɗin 5alive Babba guda ɗaya,sai ta ɗauki Glass cup guda ɗaya ta ɗaura akai,sannan ta fito don zuwa ta kaima su TAIMIYYAH.
Ko da ta kai ta aje TAIMIYYAH taso Yasmeen ɗin ta tsaya a wajen,amma fir Yasmeen taƙi tayi komawanta Sasan Iyah. Nass ya cigaba da zubawa TAIMIYYAH kalaman Luv masu ratsa zuciya.A lokacin ne kuma yake sanar mata cewa gobe zai wuce Kd ne,daga can kuma ran Sunday ya wuce Abuja. Dama hutu ya ɗauka na 2 weeks gashi kuma hutun ya ƙare.Dole Monday zai shiga office, ita dai TAIMIYYAH jinsa kawai take tana amsa shi da eh! ko umm!
Ya ɗauki a ƙallah awa ɗaya da wasu mintuna kafin yai mata sallama don wucewa gida.TAIMIYYAH ta miƙe tsaye tana ɗan dafa kujeran da ta tashi,idanunta a ƙasa take faɗin "To Allah ya kiyaye ya tsare hanya agaida su Mama."
Yadda take magana cikin sanyi da wani irin narke murya,ba ƙaramin motsa zuciyan Nass yake ba.Ya tsura mata ido yana sake ganin yadda kalan Hijab ɗin da ta sanya yai mata kyau matuƙa,ya zura hannu cikin aljihu yana faɗin,
"Thank u Luv,za su ji insha Allah,sai dai please ki bar wayanki a kunne, ina isa gida zan kira muyi gud night call, kafin inyi bacci kinji Baby Luv?" Ya ƙare maganan cikin narke murya,yana ji kaman kada ya tafi ya bar wannan kyakykyawar halittar da ta gama sace zuciyansa. Sai dai babu yadda ya iya haka ya aje mata kuɗin daya ciro daga aljihunsa,a saman Tray ɗin da Yasmeen ta aje,yana faɗin "Baby gashi nan ba yawa ki sayi Recharge Card."
Duk iya magiyan da TAIMIYYAH tayi akan ya ɗauki kuɗinsa, sam bai saurareta ba.Tana ji tana gani ya bar wajen ya nufi hanya isa gate,idanunta biye da bayansa tana kallon yanayin tafiyansa abin birgewa.
Zama tayi bayan ta ga fitansa,tana tunanin yadda za ta yi da kuɗin daya aje.Daga ƙarshe haka ta miƙe tana ɗaukan Tray ɗin da hannu ɗaya,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta mara lafiyan,ta fara takawa don komawa cikin gida.
Sai dai ko taku biyar bata yi ba qamshin turaren BENTLEY ya fara isowa hancinta.Tayi saurin ɗaga manyan idanunta tana duban Yah Sadeeq daya ƙariso inda ta yi tsaye cak! Sai ta lumshe ido tana ji tamkar ta saki Tray ɗin dake hannunta. Don wani irin faɗuwan gaba ne ya ziyarce ta da bata san daliliba.Kafin tayi wani motsi sai hannuwansa ta gani akan nata hannun da ke riƙe da Tray ɗin da ta ɗakko.Cikin wani disashshan murya yake faɗin,
"Muje part ɗina ina son magana da ke."
Daga haka yai gaba abinsa,hannunsa riƙe da Tray ɗin da ya amshe daga hannunta.Sai ya bar TAIMIYYAH da bin bayansa da kallo,tana rasa yadda zata yi,don haka kawai take ji ba ta son binsa. Sabida ko bai faɗi ba ta san akan Nass ne zai titsiyeta ta faɗi masa lokacin da fara tsayawa zance da shi.
Ganin ya dakata daga tafiyan tare da waiwayowa yana dubanta.Yasa TAIMIYYAH fara takawa tana bin bayansa,har suka isa ɓangarensa,ya saka key ya buɗe ƙofan shiga falon nasa,yana ja baya kaɗan tare da nuna mata hanya alamun ta shiga.TAIMIYYAH jiki a mace ta raɓa shi ta shige,ya rufa mata baya hancinsa na shaqo sassayan qamshin da ke fita a jikinta,ya maida ƙofan ya rufe ba tare da ya saka key ba.
Daga hannun kujeran da ke facing ƙofan shigowa falon nasa,TAIMIYYAH ta ɗan ɗosana mazaunanta. Kanta a ƙasa tana wasa da zoben azurfa dake yatsanta na hagu.Sam ta kasa kallonsa sai wani irin bugawa zuciyarta keyi ba bu ƙaƙƙautawa,shi ko Yah Sadeeq kallo ɗaya yai mata ya gane ba ta cikin nutsuwa.Hakan yasa shi sake haɗe fuska yana faɗin "Malama zama sosai za ki yi,ko nan ɗin baƙon kine da zaki wani zauna a hannun kujera kaman na ce zan cinyeki?"
Ya kai ƙarshe maganan cikin masifan da baima san zai iya ma TAIMIYYAN ba.Abinda ya sake tsorata TAIMIYYAH tayi saurin kallonsa,idanunta suka shige cikin nasa idanun,sai tayi saurin ɗauke kanta hawaye na taruwa a idanunta.Ta gyara zama sosai a cikin seatern muryanta na rawa take faɗin "Yah Deeku please! Bacci nake ji don Allah ka barni na koma gida." Wani harara da Sadeeq ɗin ya jefa mata yasa TAIMIYYAH saurin kauda kanta daga dubansa.Ji take yi tamkar ta saki kuka kawai ko zai barta. Amma memakon hakan sai gani tayi ya taso ya dawo kujeran da take kai na 1 seater ga zauna. Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi lokacin da taji hannuwansa duka a jikinta,ya ɗaga ta cak! Ya zaunar saman hannun kujeran,shi kuma ya zauna daga ciki sosai yana crossing duka leg ɗinsa. Hannuwansa riƙe da nata yana zuba mata manyan idanunsa.Da suka daɗe da canza launi ,sabida azaban kishin Nass dake cin zuciyansa,yayi magana cikin wani murya very low,
"Zaynab sanar dani waye shi? A ina ku ka haɗu kuma yaushe har ki ka ba shi zuciyanki?" Sadeeq ya watsawa TAIMIYYAH tambayan.har lokacin yana riƙe da hannunta bai saki ba,yanayin da yai masifan ɗaga hankalin TAIMIYYAH da jefata cikin ruɗu.Don kusancin na su da juna yayi yawa matuƙa.Kuma yau ɗin shine karon farko da hannuwan Sadeeq ɗin suka ratsa jikinta,shiyasa gaba ɗaya ta firgice,daga zuciyanta har gangar jikinta rawa suke. Matsanancin tsoro da fargaba ya hana ta duban idanunsa.Saima kuka da ta sakin masa da ƙaramin sauti,cikin muryan kukan take faɗin,
"Yah Deeku please ka sakeni zan gaya maka koma me kake son ji please!"
Ta ƙare maganan tana kuka sosai,hakan yasa Sadeeq sake hannunta,yana zuba mata mayun idanunsa,yake faɗin,
"Ina jinki Zaynab."
TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya,tare da sanar da shi komi.Tun daga randa Nass ɗin ya fara zuwa gidan,har kawo wayan da su ke yi da yadda Iyah ta matsa sai ta fita,duk bata ɓoye masa komi ba.Ta ƙare maganan da faɗin "Yah Deeku ni Allah ba ni ce na janyosa ba,kuma ina sauraransa ne sabida bana so Iyah tai fishi dani.Baba kuma yaga kaman naƙi jin maganansa na cewa infito da wani,amma ni sam babu ma Soyayyah a lissafina, sai karatu kaima kasani ai,amma kayi haƙury in ranka ya ɓaci please!"
Yadda take bashi haƙury tana kuka ne ya sake karya zuciyan Sadeeq.Wani irin soyayyanta ya motsa masa wanda har ya kasa controlling kansa,ya janyota jikinsa baki ɗaya ya rungumeta.Abinda ya tsaida bugun zuciyan TAIMIYYAH cak! Jikinta ya ɗauki wani irin rawa,kafin ta fashe masa da kuka lokacin da take jin kansa bisa kafaɗunta.Yana sauke wani irin numfashi kaman wanda yayi gudu,gaba ɗaya qamshin turarensa ya gama cika kafofin hancinta.Cikin muryan kuka take faɗin "Yah Sadeeq don Allah ka sakeni,kasan dai haramun ne hakan da kayi ko? Pleas......" Maganan TAIMIYYAH ya maƙaleni ne lokacin da Sadeeq ya sake shigar da ita jikinsa sosai,yana ƙoƙarin haɗe bakinsu waje ɗaya.Gaba ɗaya huɗuban da sheɗan ke masa ne ke aiki,don burinsa bai wuce yayi duk abinda zai bashi relief ba.Sai dai kukan da TAIMIYYAH ta saki me tsananin ƙarfi ne yasa shi janye fuskansa daga gareta,yana maida kansa ya kwantar bisa kafaɗunta,dukkaninsu jikinsu rawa yakeyi bama kaman TAIMIYYAH, da ke ji numfashinta na yin sama. Cikin wani irin murya Sadeeq yake faɗin "Zaynab bansan ta yadda zan sanar dake nakasa cire soyayyanki daga cikin zuciyata ba.Bansan cewa duk iya ƙoƙarin da nake na danne feeling ɗina akanki shirme nakeyi ba,sai yau da dana ganki da wani namiji bani ba.Please! Zaynab mu ture duk wani ƙiyayyan da Umma ke miki,ki amince in samu Baba Sani in gaya masa muna son junanmu.Nayi miki alqawarin kare ki daga duk wani cutarwa ko tsangwama.Domin bazamu zauna anan ba bare har Umma ta ganki tai miki abinda ranki zai ɓaci,please Zaynab ki amince dani bazan iya kallo wani namiji ya aureki alhali ni zuciyata na azabtuwa da soyayyarki."
Sadeeq yayi maganan har lokacin TAIMIYYAH na jikinsa,yai mata wani irin runguma da ta kasa kwacewa.Kuka kawai takeyi me tsuma zuciya,amma Yah Deekun da alamu sam hakan baya damunsa.Cikin kuka take faɗin "Ka sakeni tuh sai muyi magana Yah Sadeeq please!"
Bai yi musu ba ya saketa tai baya tana zamewa ta sauka daga kujeran.Kaman yasan shirin da takeyi na son ta gudu,sai yayi saurin riƙo hannunta yana tsareta da rinannun idanunsa.TAIMIYYAH tayi saurin faɗin "Yah Sadeeq don girman Allah ka barni in tafi lokaci na tafiya,zamuyi magana gobe nayi maka alqawari." TAIMIYYAH tayi maganan cike da magiya,dukkanin jikinta rawa yake burinta bai wuce ta ganta a Sasan Iyah ba.
Kafin Sadeeq ɗin yace wani abu aka buɗo ƙofan shigowa falon nasa haɗe da yin sallama.Muryan Zuhurah ce ta shigo kanta tsaye tana sauke idanunta akan su TAIMIYYAH.Ta wani waro ido tsananin mamaki na cika zuciyanta,tuni TAIMIYYAH taji maranta yai wani irin ƙullewa,tana jin lokacin da fitsari ya zuba cikin pant ɗinta.Tsabagen yadda ta ruɗe da ganin irin kallon da Zuhurah ke jifanta dashi.Da ƙarfin gaske ta kwace hannunta daga nasa hawaye masu tsananin zafi na sake ɓalle mata.Dukkanin jikinta babu inda baya rawa sabida tashin hankali,shiko Sadeeq rinannun idanunsa ya ɗago ya sauke akan Zuhurah dake tsaye daga bakin ƙofan,ta zubo musu ido.
Yayi magana cikin ɓacin rai yana faɗin "Uban me kika zo yi,da zaki shigo min ɗaki ba tare da an baki iziniba,sabida ke daƙiƙiyace ko?" Ya ƙare maganan da dakawa Zuhurah tsawan daya sake ruɗa TAIMIYYAH ta sanya masa kuka.Zuhurah ko ta wani kyaɓe fuska tana faɗin "To ai Umma ce tace inzo in kira mata kai,don ta kira wayanka har sau uku baka ɗaga ba."
"Get out! Stupid kawai,idan kinje kuma ki gaya mata cewa kinga wani abu,kiga idan ban ɓaɓɓalaki ba!" Yah Sadeeq ɗin yayi magana a fusace idanunsa akan Zuhurah data juya da sassarfa tana barin ɗakin.TAIMIYYAH da gaba ɗaya ta rasa inda zata sanya kanta,itama sai miƙewa tayi tana saurin dafa ƙafatan zata fara tafiya,amma sai Yah Deekun yayi saurin isowa wajenta yana kama hannunta.Ta ɗago manyan idanunta da hawaye suka kasa daina zuba,cikin muryan kuka take faɗin "Kaga abin da ka janyo min ko Yah Deeku? Yanzu Allah ne kaɗai yasan abinda zata je ta gayawa Umma,shikenan na shiga uk....." Hannun da Sadeeq yakai bakinta yana faɗin "Shihhshhhh..!" Shiya katse TAIMIYYAH daga ƙarisa maganan data faro,cikin low voice yake faɗin "Babu abinda zai faru Zaynab calm down please! Muje in rakaki,amma ki sani duk abinda na faɗi da gaske nake yi.Bazan iya haƙura da soyayyarki ba Zaynab,don haka ki fara koyawa zuciyanki yadda za ta so ni,ki kuma dakatar da wancan gayen bana son in sake ganin ku tare."
Yadda ya ƙare maganan cikin wani irin murya,ya tabbatarwa da TAIMIYYAH cewa duk abinda yake faɗi da gaske yake yi,sam babu alamun wasa ko kaɗan.Ita dai TAIMIYYAH burinta kawai ta ganta a Sasan Iyah shine kawai samun nutsuwanta,don haka sai kawai ta gyaɗa masa kai ba tare da tayi magana ba.
Hannunta cikin nasa suka fito daga ɗakin nasa,kobi ta kan Tray ɗin lemu da ruwan TAIMIYYAH bata yi ba,bare har ta tuna da wani kuɗin da Nass ɗin ya bata.Sai da Sadeeq ya ga shigan TAIMIYYAH cikin Sasan Iyah,sannan ya juya yana nufan hanyan Sasan su,don amsa kiran Ummansa.
TAIMIYYAH dake tafiya cikin wani irin slow motion,gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake.Zuciyanta na tsananin bugawa da tsoron abinda zai je ya dawo,don tasan tabbas sai Zuhurah ta sanar da Umma cewa ta ganta a wajen Sadeeq.Ba kuma zata rage komi akan yadda idanuwanta ya gane mata su sarƙe da hannun juna ba,har ta shiga cikin falon Iyah bakinta ɗauke da sallama,zuciyanta babu nutsuwa sam.Da idanun Guggo Bilki ta fara cin karo lokacin data sanya kai cikin falon,sai tayi saurin yin ƙasa da kanta tana takowa cikin falon.Tana shirin gota su ta wuce muryan Iyah dake zaune tare da Guggo Bilkin ya shiga kunnuwan TAIMIYYAH ,Iyah na faɗin "Sai yanzu ne ya tafi Naseerun?" TAIMIYYAH bata jiyo ba ta gyaɗa kai kawai tana yin gaba,domin bata son yin magana bare Iyah ta gano akwai matsala.Daga Iyah har Guggo Bilki suka bi bayan TAIMIYYAH da kallo,Iyah na faɗin "Anya lafiya Bilki,naga duk tayi wani sanyi ne gashi ta jima bata shigo ba." Guggo Bilki ta dubi Iyah tana faɗin "Lafiya lau Iyah,ai kinsan dama bata so fitanba,watakila daɗewan da yayin ne ya bata haushi."
Iyah sai ta saki rai tana faɗin "Hakane fa kuma,to shine kuma tabar min faranti a waje sabida taɓara,to ai sai ki kira Yasmeen ta je ta ɗakko min."
TAIMIYYAH kuwa tana shiga ɗaki toilet ta nufa direct.Yasmeen dake kwance akan gado tana kallo a System ɗin TAIMIYYAH,sai tabi bayan TAIMIYYAN da kallo kawai.
Lokacin da TAIMIYYAH ta fito kan gadon ta nufa tana aje Hijab ɗin data cire shi tun a toilet.Tayi kwance kawai tana lumshe idanunta ba tare data kula Yasmeen dake ta faman binta da kallo ba,ganin haka yasa Yasmen danna pause tana ture System ɗin gefe ɗaya.Ta matsa kusa da TAIMIYYAH da tayi rub da ciki tana faɗin "TAIMIYYAH lafiya,meyafaru?"
TAIMIYYAH kaman jira take Yasmeen tayi magana sai kawai ta saki kuka,tana gayawa Yasmeen ɗin abinda duk ya faru a part ɗin Yah Sadeeq.Sai dai ta ɓoye mata cewa ya rungumeta,ta taƙare maganan da cewa "Yasmeen bansan da wani fassara Zuhurah zatai min ba,ban kuma san iya abinda zata gayawa Umma ba.Sannan bansan me zan cewa Iyah ba idan ta tambayeni yadda akayi har na biye masa naje ɗakinsa,ni dai Yah Sadeeq na son jefani cikin masifa Yasmeen."