Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 15

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 15

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 15: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,440 words

Daƙyar ta lallaɓashi ya yo wankan ya fito,ta taya shi ya shirya cikin farar jallabiya suka fito zuwa falo.Suhailah ce ta isa wajen dining ta fara sakko da kulolin data shirya masa abinci,tana jera su a ƙasan carfet don ba koda yaushe yake cin abinci a sama ba.Fovourite Food ɗinsa tai masa na tuwan semo miyan ɗanyar kuɓewa,wanda ta wadata shi da naman shanu da ganda aciki.Sai haɗin chicken salad da yaji salad cream da kayan haɗi,sai qamshi ke tashi lokacin data ke zuzzuba abincin cikin plate. Idanun Maleek ne ke yawo a jikinta ko'ina,tunda ta fara kai-kawo na kwaso kayan abincin,har zuwa yanzu data gama zuba masa abincin cikin plate.Da kanta ta ciyar da shi itama tana ɗan cin haɗin salad ɗin kaɗan-kaɗan. Bai wani ci tuwan da yawa ba sabida dare ne baya son cika cikinsa da abu me nauyi sosai,shiyasa yafi cin salad ɗin da ɗan yawa sosai,kafin ya kauda kai alamun ya ƙoshi,hakan yasa Suhailah aje plate ɗin ta tsiyaya masa ruwa da lemun Pineapple da tayi masa,sai ya amshi cup ɗin lemun ya fara sha da kansa.Ganin hakan yasa Suhailah tashi ta nufi ɗakinta don sauya kayan jikinta,ta maida wata fingilwan Vest wacce tsayinta da kaɗan ya wuce guiwa.Babu komi a jikinta illa Vest ɗin kaɗai,wacce ba ta da maraba da ba-bu sabida yadda tabi fatan jikinta ta lafe,tare da bayyana duk wani suran jikin Suhailan.

Lokacin data sake fitowa falon samun Maleek ɗin tayi yana kallo.Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akanta,yana jin wani irin feeling na taso masa,na zallan sha'awan ta da ya tara.Domin sati biyu har da kwanaki biyu ba wasa bane a wajen lafiyayyan namiji kamansa,don haka baƙaramin tara sha'awanta yayi ya adana a ƙasan zuciyansa ba. Don haka a yanzu da take gabansa sai komi ya kwance masa,Suhailah ko tun daga nesa ta hango yadda ya kasa ɗauke idanunsa akanta.Shiyasa tana ƙarisowa sai tayi masauki a laps ɗinsa,tana kwantar da kanta a ƙirjinsa murya can ƙasa take faɗin, "Sweet wannan kallon fa?"

Maleek da ya sauke ajiyan zuciya me ƙarfi sai ya aje remote ɗin dake hannunsa,yana sake shigar da ita cikin jikinsa sosai.Gaba ɗaya qamshin da ke tashi a jikinta sake kwance notikan sha'awanta sukeyi akansa,ya cusa kansa tsakanin wuyanta yana faɗin, "Wife ina tsananin buƙatarki oya muje Bed ki bani magani." Daga haka ya miƙe da ita ajikinsa,yana takawa kaman ya ɗauki Baby suka wajen kayan kallon da ke aiki,ya yi anfani da hannu ɗaya wajen kashe kayan kallon.Ita dai Suhailah sake maƙalƙalesa tayi tana faman bashi kiss a saman face,har suka isa ɗakinsa yai mata masauki akan tsakiyan gadonsa,yana sakkowa ya nufi toilet don wanko bakinsa.

Lokacin daya fito kai tsaye light off yai musu yana nufan kan gadon,tare da janyo Suhailah zuwa jikinsa. wacce ta cire masa rigan jikinta gaba ɗaya sabida sauƙaƙa masa wahalan cirewa......

To sai in ce asuba ta gari Maleek Ado tunda na ga,wannan karan da soyayya ka dawo lol.

____________

Tun misalin takwas da rabi na safe,TAIMIYYAH ta gama shirinta tsaf na zuwa haddah.Sanye take cikin riga da plain zani na wata atamfar Chiganvy,kalan Green da akaiwa adon manyan zane da Milk and Red kaɗan,ɗinkin yayi mata kyau sosai tare da zama ajikinta ɗas! Fuskanta kaman ko yaushe babu komi akai sai man leɓe,yau ko kwallin ma bata sanya ba.Cikin sauri-sauri take komi don bata ma so Yasmeen ta motsa ta ganta,wacce take kwance tana baccinta sadidan.Ta ɗauki dogon Hijab ɗinta na skull ɗin ta sanya,tare da nufan wajen takalmanta ta zura flat shoe me hanci, don sune irin takalman da take iya tafiya dasu.Qur'aninta ta ɗauka tana fitowa zuwa falo,ganin babu kowa yasa TAIMIYYAH nufan ɗakin Iyah,sai dai nan ɗinma Guggo Bilki ce kawai akan gadon Iyan tana bacci.Jin motsin ruwa daga bayi yasa TAIMIYYAH gane cewa Iyah wanka ta shiga,sai kawai ta juyo tayi fitowanta don tafiya makarantan.

Daga waje suka haɗu da Ladi ta fito daga ɗakinta.TAIMIYYAH ta gaisheta tana faɗin, "Saina dawo Babah Ladi,idan Iyah ta fito kice mata sauri na ke yi na wuce,kuma a aje min abin kari na saina dawo zan karya." Babah Ladi ta amsa da faɗin, "To ƴar gidana adawo lafiya,zan sanar da Iyan Allah bada sa'a da ilimi me anfani."

TAIMIYYAH da tai gaba ta amsa da "Ameen." Tana fitowa daga Sasan Iyah ta nufi Compound na gidan,tana fata kar ta haɗu da kowa har ta bar gidan.Cikin sa'a kuwa bata haɗu da kowan ba sai Tukur da suka gaisa ta fice abinta.Tana tafe ne zuciyanta na tariyo mata abinda ya faru tsakaninta da Yah Deeku a daren jiya.Ta wani ɗan lumshe ido ta buɗe hankalinta na kan hanyan da take bi,sanyin safiyan na kaɗa Hijab ɗinta yana ratsa jikinta.Har ta isa makarantan bata bar tunanin da wani ido zata kalli Zuhurah ba,ba kuma ta san ta yadda za ta yi ta iya dakatar da Nass ba, kaman yadda Yah Sadeeq ɗin ya buƙata.

A round 10:30am aka tashe su daga skull ɗin,TAIMIYYAH suka jero da wata ƴar ajinsu me suna Bilkisu.Suna tafe suna magana akan yadda waliman yayensu zai kasance,wanda bazai wuce nan da wata biyu ba zasu kammala haɗe haddansu baki ɗaya.Sun zo dai-dai kwanan da TAIMIYYAH za ta nufi hanyan gida sannan sukai sallama da Bilkisun.Sai ya zamana TAIMIYYAH ita kaɗai ke takawa zuwa cikin layin nasu,kanta a ƙasa take tafiya kaman yadda ta saba.Wani irin ciwan kai take ji na ɗan taso mata kaɗan-kaɗan,ta kuma san hakan baya rasa nasaba da fitowan da tayi bata karya ba,har ta ƙariso gida bata haɗu da kowa data sani a layin ba.

Lokacin da ta sanyo kanta cikin compound ɗin gidan,tun daga nesa idanunta suka hango mata Baba Sani da Yah Sadeeq a tsaye suna magana.Hakan yasa tafiyanta ya sake komawa very slow,don sam bata so haɗuwa da Yah Deeku ba sam,so tayi har ya gama weekend ɗinsa ya koma ba za ta bari su sake haɗuwa da juna ba.Babu yadda ta iya haka ta karya kwana zuwa wajen da suke tsayen,don ta san dole za su ga wucewanta,kuma gashi dama bata je sun gaisa da Baban ba ta tafi haddah.

"Salamu alaikum! Ina kwana Baba."

Cewan TAIMIYYAH lokacin data ƙarisa gabansu Baba Sanin,tana me tsugunawa har ƙasa ta gaida shi.Ya amsa da matuƙar kulawa yana faɗin "Zainab har kin dawo daga haddan,ya dai tabbata ke kaɗaice ke maida hankali,waɗancan shashashan basama zuwa kenan? Aiko zanci ƙaniyansu sosai." Baba Sani yayi maganan cike da nuna ɓacin rai,ita dai TAIMIYYAH na tsugunne.Sai daya kai aya sannan ta miƙe tana satan kallon Yah Sadeeq,da take jin tasirin idanunsa ajikinta.Don tunda ta ƙariso wajen jikinta ya bata kallonta yake yi,ta gaishe shi cikin sanyin murya tana juyawa ta fara takawa don barin wajen,ba tare data jira ya amsa ba.

Tana dafda shiga Sasan Iyah ta jiyo muryansa yana faɗin "Wait! Zaynab." Sai TAIMIYYAH ta tsaya cak! Har ya ƙariso inda take,sannan ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa,yana sanye da riga da wando ne irin masu kaurinnan na bacci,da alamu ko wanka baiyi ba kenan. Ta ɗauke idanunta daga gare shi lokacin da yake matsowa daf-da ita sosai,har tana jin saukan numfashinsa akan face ɗinta.Abinda yasa tai ɗan baya kaɗan tana sake dubansa da fuska a shagwaɓe. Shi kuma sai ya saki ƙaramin smile yana faɗin "Matsoraciya miye na wani saurin yin baya kaman kin ga dodo,wato shine kika kashe waya tun jiya ko?" Ya jefawa TAIMIYYAH tambayan idanunsa akanta yana kallon yadda ta sake wani narke fuska,kafin ta dubesa tana faɗin "Ni mantawa nayi ban kunna ba,sabida da wuri na tafi Haddah."

Yadda TAIMIYYAN tayi maganan cike da shagwaɓan daya riga ya santa da shi,yasa shi sake matsowa gabanta sosai,cikin ƙasa da murya yake faɗin "Alright! Jiya kin manta baki ɗauki kuɗin da saurayinki ya baki ba,ki ka barmin a ɗakina saura kaɗan in yayyagasu sabida kishi." Ya ƙare maganan yana wani tsuke fuska alamun har zuciyansa da gaske kishin yake ji.TAIMIYYAH tayi saurin dubansa tana sake kwaɓe face take faɗin "Kai! Yah Deeku to ba kaine duk ka janyo hakan ba,ni har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwan cewa Zuhurah ba za ta sanar da Umma a yadda ta gammu jiya ba."

TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan komi yana dawo mata,shi ko Yah Sadeeq sai ya tsura mata ido yana ji tamkar ya sake rungumanta ajikinsa irin na jiyan,ya wani lumshe ido ya buɗe akan fuskan TAIMIYYAN.Yana ɗan sakin smile yake faɗin "And so what! To idan ta faɗi Baby, Zina ta ganmu muna yi ko babu kaya a jikinmu ta ganmu?" Yah Sadeeq ɗin yayi maganan yana ƙoƙarin su haɗa ido da TAIMIYYAH. Amma sai TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke kai,wani uban kunyan maganan da Yah Deekun ya ɓaro na lulluɓeta.Bai bari tace komi ba ya sanya hannu a aljihunsa yana ciro kuɗin da Nass ya bata jiya yana miƙa mata,ta sanya hannu ta amsa amma taƙi bari su haɗa ido har lokacin.Cike da kishi yake faɗin "Ki tabbatar Iyah kika ba kuɗinsa ta aje masa,kar ki sake ki anfani da su kinji na gaya miki Baby." Yayi maganan bilhakki idanunsa akan TAIMIYYAN data ɗan zumɓuro baki,kafin ta furta, "Ai da ma ita zan ba ni bance zan kashe ko sisi ba,kuma ma ai shine ya aje yai tafiyansa,amma tunda ya bani nace masa bazan amsa ba." Tana kaiwa ƙarshen maganan ta juya zata bar wajen,amma sai Sadeeq yayi saurin riƙo Hijab ɗinta.Saura kaɗan hannunta ya goce akan guiwanta da take dafe dashi,tayi saurin sake dafe ƙafan me laluran.Tana ɗago manyan idanunta ta sauke akan Yah Deekun,ya wani haɗe fuska yana faɗin "Shine zaki tafi na ce na gama magana dake ne?"

"Yah Sadeeq don Allah ka saki Hijab ɗin to,kada wani ya fito ya ganmu.Yinwa nake ji ban karya ba na fito don Allah ka barni in ƙarasa ciki please!"

Yadda tai maganan kaman zata sanya masa kuka,yasa ya sake mata Hijab ɗin yana faɗin "Alright! Baby jeki ki karya amma ki kunna wayanki zamuyi magana."

Kai kawai TAIMIYYAH ta gyaɗa masa tana juyawa ta shige,shi kuma Yah Sadeeq ya juya ya nufi part ɗinsa,zuciyarsa ba sake cika da soyayyan TAIMIYYAN,da yake ji kaman ƙara shi akeyi a zuciyarsa kullum.

Da sallama TAIMIYYAH ta shiga falon Iyah,idanunta na sauka akan Yasmeen da Guggo Bilki da ke zaune cikin falon.Luggage ɗin Guggo Bilkin ne agabanta tana shirya kaya,TAIMIYYAH ta ƙarisa wajen tana gaida Guggo Bilkin.Ta ɗago tana amsa gaisuwan TAIMIYYAN kafin ta ɗaura da faɗin "TAIMIYYAH shine kika tafi makarantan baki ko tsaya kin karya ba,zaki ci faɗan Iyah kuwa don sai mita take yi tun ɗazu." TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Iyah kenan,dama na san za ta yi faɗa kam.Guggo Bilki wai da gaske tafiya zakiyi yau ɗin? Gaskiya zamuyi kewa."

TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da nuna irin missing ɗin da za su yi na Guggon nasu,don babu ruwanta da hayaniya akwai ta da sauƙin kai sosai. Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin "Aike wallahi baki da kirki, kin san za kiyi sammakon fita makaranta amma baki tasheni ba,ki kai tafiyanki."

Yasmeen ta ƙare maganan tana zabgawa TAIMIYYAH harara.Kafin TAIMIYYAN tace komi Iyah ta fito daga ɗaki,hannunta riƙe da wayanta ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin "Kin kyauta fita babu karin safe,bayan kin san kina da ulcer." Iyah tayi maganan cike da mita tana hararan TAIMIYYAH data cire Hijab ta aje saman kujera,kafin ta dubi Iyan tana faɗin "Allah baki haƙury Iyah,sauri nake yi amma kin san bana fita ban karya ba ai.Ina kwana mun tashi lafiya?" Ta ƙare maganan da gaida Iyah,wacce ta amsa tana faman taɓe baki,hakan yasa Yasmeen sakin dariya tana faɗin "Iyah wallahi wajenki TAIMIYYAH ke course ɗin iya harara da shagwaɓa,ke ma da alamu lokacin ƙuruciya kin taɓa shagwaɓa son ranki." Yasmeen ta ƙare maganan suna kwashewa da dariya ita da TAIMIYYAH,Iyah ta aikawa Yasmeen daƙuwa tana faɗin "Kin ci gidanku ƴar nema." Guggo Bilki dai na jinsu tana dariyan draman su Iyah da jikokin nata da bai ƙarewa.TAIMIYYAH ce ta nufi wajen cin abinci don karyawa,koda ta gama sai ta wuce ɗaki tana ɗaukan wayanta ta kunna. Haka kawai take son jin muryan Nass ɗin,don tasan yayi ta kiran wayan da safe ya jita a kashe.Aiko wayan na gama Booting saƙonni suka fara shigowa.Sai ta nufi inbox ɗin don karantawa,biyu daga MTN ne sai guda ɗaya daga Nass ɗin,ta buɗe na Nass ɗin tana karanta tsararrun kalaman daya turo mata na gud morning text.Wanda baya fashin turowa duk safe.Daga ƙarshen saƙon yai mata ƙorafi akan ya kira wayanta a kashe,amma idan ta ga saƙonsa ta kira shi please!

TAIMIYYAH ta saki smile a lokacin data gama karanta saƙon,tana nufan call log tayi dialling number ɗinsa.Yana fara ringing zuciyanta ya shiga bugawa,har zuwa lokacin da yai cuting call ɗin ya biyo bayan kiran.Sai ta gyara zamanta daga bakin Bed ɗin lokacin da sassanyar muryansa ya shiga kunnuwanta.Ta gaida shi cike da salonta dake sake narkar da zuciyanta Nass ɗin.Sun ɗauki kusan 15minutes suna waya kafin suyi sallama,Nass ɗin na sanar da ita tuni har ya isa Kd ma.

Bayan TAIMIYYAH ta aje wayan sai ta miƙe tana cire kayan jikinta.Ta maida wata doguwar riga mara nauyi,sabida bata faye son zama da kaya masu nauyi idan tana zaune a gida ba.

Yasmeen ce ta shigo ɗakin lokacin da TAIMIYYAH ta ɗakko System ɗinta zata kunna.Yasmeen ɗin ta sauke idanunta akan TAIMIYYAN tana faɗin "To Malama sai ki tashi ki fito mu raka Mamie don yanzu zata wuce." TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta tana duban Yasmeen take faɗin "Yanzu da wuri haka,kai ita ko Guggo da-dai ta bari sai gobe kawai." Yasmeen ta jefa mata harara tana faɗin "To Abbah bai ga dama ba,yace yau-yau yake son ganin ta koma gida,nima da ƙyar ya amince in ƙara one week."

Tare da TAIMIYYAN suka fito zuwa falon Iyah,dukansu sanye da Hijab a jikinsu.Tuni Guggo Bilki har an kai Luggage ɗinta mota,Driver ɗin da zai tuƙata zuwa Kanon ma iya so ashe tun safe.

Har da Ladi me aiki aka rankaya zuwa wajen compound ɗin gidan,don yiwa Guggo Bilki rakiya wacce ta nufi Sasan Baba Sani don yi musu sallama.TAIMIYYAH da Yasmeen dai na tsaye jingine da jikin Motar Guggo Bilkin basu bi ta Sasan su Umman ba,mintuna kaɗan sai ga Guggo Bilkin sun fito tare dasu Zuhurah,sunyo mata rakiya har zuwa wajen mota.Ta shiga motar su TAIMIYYAH na ɗaga mata hannu,har Motar ta bar cikin compound ɗin suka juya don komawa cikin gida.

Zuhurah ce tayi saurin biyo bayansu tana kiran sunan Yasmeen.Hakan yasa su TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan suna jiran ƙarisowan Zuhuran,koda ta iso idanunta akan TAIMIYYAH yake wacce tayi saurin ɗauke kai,don bata son ma su haɗa ido da Zuhurah.Tuni Zuhuran ta gane abinda yasa TAIMIYYAH take ɗauke mata kai,sai ta saki murmushi kawai tana faɗin "Yasmeen yau fa Ameeru zai iso,shine nace me kike ganin zamu shirya masa na tarba?"

Yasmeen da idanunta ke kan Zuhurah,sai ta juya tana nunawa Zuhurah TAIMIYYAH tana faɗin "Ga wacce zaki tambaya nan,don ita ce gwanan sanin abubuwan kwaɗayi da Girkunan zamani."

Zuhurah da takaicin maganan Yasmeen ɗin ya ɓata ranta,sai ta maze bata nuna ba.Sai ma tayi taku biyu tana tsayuwa daga gefen da TAIMIYYAH ta juyar da kanta,murya can ƙasa yadda bama lallai Yasmeen data zama a gefen Zuhuran taji me zata iya faɗiwa TAIMIYYAN ba.Zuhuran ke faɗin "Ya da ɗauke kai ƴan matan Yah Sadeeq,ko kuma karuwansa zan ce? Don naga alamu ya gama amshe budurcin tunda har kike kai kanki garesa kina bashi kayan daɗin har ɗaki.To ya? Zaki taimaka ki samarma saurayin nawa abinda zamu tarbe shi da shi ɗin ne Babyn Yah Deeku?"

Zuhurah ta ƙare maganan tana sakin dariyan iskanci.Tuni TAIMIYYAH ta gama muzanta da jin kalaman da Zuhurah ta jefeta da shi,kalmar karuwa data jingina ta dashi yafi komi ɗaga hankalinta.Tayi saurin ɗago kanta don ganin ko Yasmeen ta ji abinda Zuhuran tace,amma cikin sa'a sai ta ga Yasmeen ɗin tama yi nesa dasu tana amsa waya.Hakan yasa TAIMIYYAH sauke manyan idanunta da suka fara tara ƙwallan baƙin ciki a kan Zuhurah,tana faɗin "Zuhurah ni kike kira da karuwan Yah Sadeeq,sabida kawai kin ganmu riƙe da hannun juna?" Tai tambayan tana ji hawayen da take son dannewa na son kwacewa su zubo akan fuskanta.Zuhurah ta dubi TAIMIYYAN tana sakin dariyan rainin hankali take faɗin "To da wacece ke? Karki rainawa kanki wayau mana,ko daga yadda na ganshi a wani susuce nasan magiya yake miki lokacin,yana so ku shiga daga ciki ya jisa ajikinki,ke kuma kina wahal dashi irin sai ya gama shiga uku kafin ki bashi abinda ya saba karɓa,ni dama na san soyayyan da yake miki ba banza ba.Jikin yake so da can ƙasan tunda an sakar masa komi yaji daɗi shiyasa yake nacin ki zama mallakin nasa baki ɗaya,kuma wallahi idan kikai wasa kaman na sanar da Umma abinda na gani."

Zuhurah na kai aya TAIMIYYAH tayi saurin juya baya dafe da ƙafanta ta fara tafiya.Kuka take son yi amma ta danne tana jin wani irin tashin hankali na rufto mata,ga tsananin zafin kalaman da Zuhurah tai mata na ƙona zuciyanta.Tana jin Yasmeen data biyo bayanta na kiran sunanta,amma ko waiwaye bata yi ba, don burinta kawai ta isa ɗaki,ko zata kwanta tayi kukan dake neman kwace mata.Cikin Sa'a babu kowa a falon Iyah hakan yasa ta nufi ɗaki,tana faɗawa kan gado ta saki kuka me ƙarfin gaske.Dukkanin jikinta rawa yake na tsananin shiga ɓacin rai,domin ba'a taɓa jifanta da munanan kalamai irin wanda Zuhurah ta jefeta da su a yau ba. Kalamai ne mafiya munin saurare musamman daga bakin ɗan uwanka na jini. Har Yasmeen ta ƙariso bakin gadon TAIMIYYAH kuka take yi me asalin motsa zuciya.Daƙyar Yasmeen ɗin ta ciyo kan TAIMIYYAH ta sanar da ita yadda su ka yi da Zuhurah,ta ƙare maganan cikin muryan kuka tana faɗin "Yasmeen shikenan na shiga uku idan har Zuhurah wannan sharrin zata ƙulla min a wajen Umma.Wallahi hannuna kawai ta ga ya riƙe,baya ga haka bata ganmu muna komi ba."

TAIMIYYAH takai ƙarshen maganan tana sake rushewa da kuka.........✍🏻

Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:05 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️

©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

*Page 31*

___________

Umma ce zaune a cikin Bedroom ɗinta,ta tasa Sadeeq a gaba tana zazzaga masa ruwan masifa,akan cewa lallai ya fita a harkan Gurguwan yarinyar nan TAIMIYYAH.

Ta inda take shiga bata nan take fita ba,shi dai Yah Sadeeq yai ƙasa da kansa yana sauraranta,ba tare da ya tari nunfashinta ko sau ɗaya ba.Umman ta ƙare maganan da cewa "Aure zan maka tunda abin naka ya fara zama iskanci,ka fara saka Gurguwa a ɗaki kana kwanciya da ita sabida asara,in banda abinka in ma iskancin zaka yi ka rasa wanda zaka kula sai Gurguwa,Musaka! To tunda ka kasa fito da zaɓinka ni zan zaɓo maka yarinya dai-dai da ajinka,ƴar gidan qawata Hajiya Hadeeza za ka je ka nema.Tana nan da budurwar ƴa kyakykyawa me dirin jiki,ita ma fara ce ƙar kaman waccar Musakar,don haka sai ka shirya wata satin idan ka dawo Weekend za ka ku ga juna,sunan yariyar Nadeeya."

Umma ta kai ƙarshen maganan tana ɗaura idanunta akan fuskan Sadeeq ɗin,wanda ya haɗe fuska babu annuri ko kaɗan.Zuciyansa tafasa kawai yake yi yana ji da ba Umma bace ke masa wannan maganan,tana aibanta TAIMIYYAH a gaban idanunsa,tabbas da wata can dabam ne ba abinda zai hana shi nuna mata fushinsa.

Amma da yake Uwa ce hakanan ya danne ɓacin ransa,yana faɗin "Umma ni bana son wani haɗe-haɗe zan zaɓo matar aure da kaina,don Allah kada ma ki yi wa Anty Dijen maganan." Ya kai ƙarshen maganan cike da roƙo,Umma da ke kallonsa baki buɗe ta dalla masa harara tana faɗin "Ai ko baka isa ba Sadeeq,wannan umurni ne nake baka ba wai shawaran ka nake nema ba,don haka na gama magana,kana dawowa wata satin za ka ku ga juna final!"

Daga haka Umma ta miƙe ta bashi waje tana jan tsaki tsuuuw....! Hakan yasa Sadeeq bin bayanta da kallo,zuciyarsa na matuƙar sake ɗaukan zafi.Tuni idanunsa sun yi mugun kaɗawa ya miƙe yana ji tamkar ƙafafunsa ba zasu iya ɗaukansa ba,ya rasa da wani ɓacin ran zai ji,na Iyah da itama tai masa tatas a daren jiya akan lallai ya fita daga harkan TAIMIYYAH,ko kuwa da rigiman da Umma ta ɗauko yanzu na cewa zata haɗa shi da ƴar aminiyanta Anty Dije? Har ya fito falo bai san taƙamaimai inda yake jefa ƙafafunsa ba.

Lokacin da ya iso tsakiyan falon ne idanunsa ya sauka akan su Zuhurah.Take Brain ɗinsa ya tuno masa cewa Zuhuran ita ce silan duk wannan masifan da ake son jefa Zuciyarsa a ciki,sai ya nufi inda take yana damƙota tare da kifa mata lafiyayyen marin da ya ɗauke jin ta da ganin ta na wasu ƴan daƙiƙu.

Zuhurah da komi yazo mata a bazata ta ƙwallah wani uban ihu,wanda ya janyo hankalin su Umma da Anty Laurat da ke ɗaki,suka fito a guje don ganin meke faruwa.

Umma sai tai turus a tsaye tana kallon yadda Sadeeq ya dage yana jibgan Zuhurah,yana zuba mata masifa akan duk munafunci da cin mutuncin da tai wa TAIMIYYAH a jiya.Umma ganin zai raunata mata ƴa yasa ta isa wajen da sauri.Ta ɗaga hannu zata ɗauke shi da mari Anty Laurat da ta ƙariso wajen, tayi saurin shiga tsakiyansu tana faɗin, "Umma kiyi haƙury,Yah Sadeeq oya bar nan wajen please!"

Babu musu Sadeeq ya juya ya bar Sasan a fusace tamkar zai tashi sama.Zuhurah da Umma take riƙe da ita sai ta sake sakin wani uban ihu tana faɗin "Wayyo kafaɗata Umma ya karya ni!"

A rikice Umma ta zaunar da ita tana faɗin "Ke don ubanki bansan jafa'i,kar ki tara min mutane cikin Sasa,ya karya miki kafaɗa ne zaki xauna a haka? Ki yi shiru ki bar ni da shi saina saɓa masa,ba dai duk akan waccar Gurguwan yake yi ba,to zanci ubansa very soon!"

Umma ta ƙare maganan a fusace,tana juyawa ta bar Zuhurah da su Anty Laurat,wacce ita abinda Yah Sadeeq ɗin yaiwa Zuhurah ba ƙaramin birgeta ya yi ba.

A can ɓangaran Sasan Iyah kuwa,TAIMIYYAH ce zaune ita da Zee wacce ta kawo mata ziyara a yau.An cika gaban Zee ɗin da kayan motsa baki,sai hira suke yi har da Yasmeen da ke zaune daga gefe tana sanya baki cikin hiran.

Wayan TAIMIYYAH ne ya shiga ringing,ta ɗaga wayan tana miƙewa don barin wajen.Ganin Nass ne me kiran sabida kunyan amsa wayansa ta ke ji a gaban mutane,daga Yasmeen har Zee suka bi bayanta da kallo suna sakin murmushi.

Ta ɗauki tsayin 15 minutes sannan ta fito ,Zee ta dube ta cike da tsokana ta ke faɗin, "Qawata da alamu dai wannan Nass ɗin ya ci mu da yaƙi, ya yi nasaran sace zuciyar ki, dama ni na san da ƙyar zaki iya tsallake tarkon sa,don Guy ɗin ya haɗu kun kuma dace da juna,Allah dai ya tabbatar da alkhairy a tsakaninku."

Yasmeen ce ta amsa da "Ameen." Su na cigaba da tsokanan TAIMIYYAH wacce ta narke musu da shagwaɓa akan su daina tsokananta ita ba wani Soyayyan da take wa Nass ɗin.

Yasmeen ta danna mata harara tana faɗin, "To ai dukkanin reaction ɗinki akansa ya gama fallasaki yarinya,kowa ya ji yadda kike narke masa ya san kin kamu wallahi,don haka mu bawani gulman da za a mana a tuh!"

Zee ta saki dariya sosai bayan Yasmeen ta dire magananta,idanun Zee ɗin cikin na TAIMIYYAH take faɗin "Qawata kawai ki saki an riga an ci ki da yaƙi." TAIMIYYAH ta aikawa Zee ɗin harara tana faɗin,

"To na ji ƴan saka idanu a ɗakko wani topic ɗin a aje wannan." Daga haka suka shiga wata hiran har Iyah ta dawo daga anguwan da ta fita,ta tadda Zee ɗin da take jin labarinta a bakin TAIMIYYAH.Zee ta gaida Iyah cike da ladabi tana faman yi mata sannu da zuwa,Iyah ta amsa da fara'a sosai cikin Zuciyanta tana yaba nutsuwan Zee ɗin.

Sai around 3pm Zee ta tashi tafiya,Iyah ta bada sinƙin Sabulu me tsada na wanka da turare aba Zee ɗin.Ita kuma TAIMIYYAH wani Ɗan-kunni da sarƙa me kyau,da take aje da shi bata taɓa amfani da shi ba,shi ta ɗauka ta haɗa Body Mist me Qamshi,cikin turarukan da Abie ke aiko mata za ta baiwa Zee ɗin.Har bakin gate ita da Yasmeen su kaiwa Zee rakiya,sai faman godia Zee ɗin take yi lokacin da TAIMIYYAH ta bata ledan da suka zuba mata sha tara ta arziƙin.

Sai da suka ga Zee ɗin tayi nisa da tafiya,sannan suka juyo zuwa cikin gida.Yasmeen nata yaba kirkin Zee ɗin da hankalinta,hakan kuma yai wa TAIMIYYAH daɗi a rai,ta ji Zee ɗin ta sake shiga Zuciyanta musamman da Iyah itama take ta yaba nutsuwan Zee ɗin.

__________ *After One Week*

A cikin sati ɗayannan da ya biyo baya,abubuwa da yawa sun faru.Ciki har da yadda Soyayya me ƙarfi ya ƙullu tsakanin TAIMIYYAH da Naseer,wanda ke can garin Abuja wajen aiki amma kullum suna maƙale da juna a waya.

Sunyi wani irin shaƙuwa ta ban mamaki,ta yadda ɗaya baya iya yini guda sur! Bai ji muryan ɗan uwansa ba.Hatta da yin vid call da TAIMIYYAH ke ƙorafin bata so,yanzu ya fara zame mata jiki don duk dare kafin su kwanta sai sunyi vedio call da Nass ɗin.

Ita dai Yasmeen na ganin ikon Allah,tare da tasa TAIMIYYAH da tsiya kala kala.Gefe ɗaya kuma tana jin daɗin yadda TAIMIYYAH ta saki jikinta da Nass ɗin suna kwasan Soyayyah.Zuhurah da mutuminta Ameeru ɗan mutanen Bauchi itama luv suke bugawa ba kaɗan ba,don da gaske son shi take yi da dukkanin Zuciyanta.Tuni har maganan ya je kunnin Baba Sani,ya kuma ce a gayawa Ameerun ya turo manyansa su nema masa izinin fara zuwa zance,duk a bakin Anty Laurat su TAIMIYYAH ke jin hakan.

Yau ya kama Saturday tun safe su TAIMIYYAH ke shirin tarban zuwan Abie,wanda ya kira wayan Iyah tun daren jiya ya sanar da ita zai ƙariso Zarian bayan ya tsaya a Kaduna an ɗaura auren da zai kawo sa garin.

Qanwar Ummie da suke Cousine ne za'ai wa aure shine Abie ɗin zai zo ɗaura aure,ita Ummie da su Nahar tun Thursday ma suka biyo jirgi zuwa Kaduna.TAIMIYYAH haka kawai take jin duk ta ƙosa tayi ido biyu da Abie,sabida ya kwana biyu bai shigo garin ba,sai dai su gaisa ta waya wani zubin su yi vid call.Shiyasa yau ɗin daya sanar zai zo gaba ɗaya farin cikinta ya kasa ɓoyuwa,gefe guda kuma tun tashinta da safe take fama da faɗuwan gaba,sai ta dinga nanata kalmar Hasbunallahu wani'imalwakil! Shine ta ɗan samu sauƙi.

Readers Also Read