Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 18
Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 18: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…
4,469 words
Daga can wajen Compound ƙaton parking space ne,da aka adana manyan motoci sabbi dal guda huɗu.Hatta sabbin Drivers da aka bashi daga Office sunanan ready suna jirane kawai su tare a gidan, su fara aikinsu don muƙamin da aka bashi ba ƙarami bane.A kwai BQ me ɗauke da 2 Bedroom da single falo,sai ƙaramin Kitchen daga cikin corridor,sai toilet da ke manne jikim kowani Bedroom.
Kwanansu biyu a garin Abujan suka biyo jirgi zuwa Kano,daga Kano Yusuf driver ɗin Maleek ya ɗakko su zuwa Zaria.
____________
*Zaria.*
Yau kwanakin su Abie goma sha biyar kenan da barin gidan duniya.Su TAIMIYYAH sun ɗauki dangana tare da komawa harkokinsu na yau da kullum,don har TAIMIYYAH ta cigaba da zuwa Computer Training ɗinta.Sai dai har lokacin ba za a ce alhinin mutuwan ya sake su baki ɗaya ba, sabida gaba ɗaya TAIMIYYAH ta koma wata irin shiru-shiru mara son yawan magana sosai ba kaman daba. Duk yadda Iyah da Yasmeen ke ƙoƙarin ganin ta koma kaman da abin yaci tura.Sai Iyah ta maida kai wajen yi mata addu'an samun ƙarin dangana,daga ɓangaren Ummie kuma takaba ya fara nisa,itama kuma ba laifi ta dangana.Sai dai ita ma ta sake zama mara son magana kullum cikin tunani da mafarkin mijinta da ƴaƴanta ta ke.Iyah har lokacin ba ta fasa sa ana mata rubutu tana sha ba,tana kuma ƙoƙari matuƙa wajen ganin Ummien ta samu nutsuwan zuciya.
Daga ɓangaren Soyayyar Nass da TAIMIYYAH kuwa kullum daɗa samun cigaba ake yi.Don wani irin zazzafan soyayyar Nass ɗin ne yai mata mugun kamu,wanda har abin ke bata tsananin mamaki ta yadda bata iya cikakken awa biyu bata ji muryarsa ba,sabida yadda ya saba mata da yawan kira. Bai cika zuwa Weekend ba sai duk bayan Sati biyu,shiyasa rabon su da ganin juna a zahiri tun ranan da yazo yai mata sallama zai wuce Abuja kwanaki goma sha uku kenan baya.Tun daga lokacin bai sake shigowa garin ba sai gobe Friday ne yake saka ran shigowa,don an kwantar da Mamarsa ma a asibiti ciwan Sugar ɗinta ya tashi yau kwana biyu kenan. Shi yake gayawa TAIMIYYAH hakan a jiya da suke waya da daddare,har yana sanar da ita idan ya shigo dole zai ɗauke su ita da Yasmeen su je duba Mamar tasa.
Ita dai TAIMIYYAH jinsa kawai tayi a lokacin,amma sam ba ta tunanin za ta iya binsa su je gaida wata Mamarsa.
"TAIMIYYAH ki zo in ji Iyah."
Cewan Yasmeen data shigo cikin ɗakin dawowanta daga kasuwa kenan,don ita TAIMIYYAH ta shiga Skull a yau ɗin shiyasa basu tafi tare ba.TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Yasmeen ɗin tana cewa, "Yaameen har kin dawo,Allah dai yasa kin samu siyo wiffing cream ɗinnan da cocoa powder."
Yasmeen data aje jakan hannunta ta dubi TAIMIYYAN tana faɗin, "Hmm! Na siyo amma da ƙyar wallahi don komai yayi tsada sosai , duk abinda ka taɓa sai ka ji ya ƙara kuɗi wannan tsadan rayuwa dai kullum gaba ya ke yi TAIMIYYAH,ni wallahi abin har tsoro yake bani fa."
Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana sake jinjina irin yadda kullum ka je kasuwa,sai ka tadda ƙarin hauhawan farashin kayayyaki.TAIMIYYAH ta miƙe tsaye tare da dafe ƙafanta me laluran tana cewa, "Hmm! Ke dai Allah yasa mu dace kawai,amma abin sai Addu'a Allah dai ya kawo mana ɗauki,bari in je wajen Iyan." Daga haka ta fara takawa don barin ɗakin lokacin da Yasmeen ke amsa Addu'ar da tayi da,
"Ameen."
"Iyah gani Yasmeen tace kina kirana."
TAIMIYYAH tayi maganan lokacin da ta iso wajen Iyah da ke zaune a falo tana irga wasu kuɗi.Iyah ta sauke manyan idanunta akan TAIMIYYAH tana faɗin, "Eh dama waɗannan kuɗin zaki tayani irgawa,don ni ina yi ina daburcewa na rasa gane ko nawa ne duka kuɗin."
TAIMIYYAH ta zauna kusa da Iyah tana kwashe kuɗin daga gabanta ta fara irgawa tana cewa,"Ke dai Iyah irgan kuɗi wahala suke baki waye ya kawo miki kuɗi haka masu yawa?"
Iyah ta ɗan taɓe baki tana faɗin, "Kuɗin hayan gidana ne na Samaru ɗazu Kallamu ya kawo kinsan ai lokacin amsan kuɗin yayi."
"Oh..! Hakane fa na manta wallahi,kice mun yi kuɗi yau zaki siyan mana rousted fish mu ɗanci ko?"
Cewan TAIMIYYAH cike da tsokana,Iyah ta harareta tana faɗin, "Ai bakinki ne fish ɗin,ki gama irga kuɗin dai sai ayi magana koma me za'a siya,Allah ya ji ƙan wanda ya siya min gidan yasa suna kyakykyawan matsayi,su da iyayenmu baki ɗaya da suka rigamu gidan gaskiya."
Iyah ta kai ƙarshen Addu'ar wani abu na motsawa a zuciyarta,tunawa da tayi da Abie don shine ya siya mata gidan yace a zuba ƴan haya,ta dinga samun kuɗin shiga duk ƙarshen shekara.Banda jarin kuɗin da ya bata a hannu tana ɗan siyan irin su Barkono da waken Suya idan farashinsu ya hau an samu riba sai a siyar a sai wani.
TAIMIYYAH ta amsa da "Ameen." Itama zuciyarta na motsawa da wani irin kewa me tarin yawa na Abiee ɗin,har ta kammala irga kuɗin babu wanda ya sake magana a cikin su.Ta baiwa Iyah kuɗin tana sanar da ita adadin yawan su,kafin ta tashi ta koma ɗaki tana kwanciya tayi lamo a kan gado,haka kawai ta ji tana son jin muryan Abie ɗin nata.Hawaye suka fara zarya a fuskarta suna sauka bisa pillow,amma bata damu data share su ba. Yasmeen ce ta ƙariso bakin gadon ta zauna tana faɗin, "Haba TAIMIYYAH wai don girman Allah sai yaushe ne idan kin tuno su Abiee zaki daina kuka sai dai kiyi musu Addu'a? Don Allah ki sanyawa Zuciyarki cikakkiyar dangana,idan kin tuno su kiyi musu kyakykyawar Addu'a ne ita suka fi buƙata ba yawan kuka da sanya damuwa a rai ba.Gashi nan shiyasa har yau baki maida jikinki ba duk kin bi kin rame ba kamar da ba,ina sha kinma Yah Sadeeq alqawarin daina kuka duk idan kin tuno su yace kiyi musu addu'a ne don haka yanzu zan kira shi in ce gaki nan kina ta faman kuka."
Jin abinda Yasmeen ɗin tace yasa TAIMIYYAH saurin kai hannu tana share hawayen ta dubi Yasmeen da face ɗin tausayi kafin ta fara faɗin, "please! Yasmeen kar ki kira shi na bari wallahi,yanzu ma na kasa controlling tears ɗin ne shiyasa."
Yasmeen da tausayin TAIMIYYAH ya cika Zuciyarta sai ta gyaɗa kai tana faɗin, "Naji ba zan kira shi ba amma don Allah ki daure ki daina irin haka Baby Sis ɗina kinji ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana ɗan sakin ƙaramin murmushin yaƙe jin sunan da Yasmeen ɗin ta kira ta da shi tamkar wata ƙaramar Baby.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:06 PM] +234 703 769 7050: *35*
Yau ya kama Friday tun misalin sha biyu da rabi TAIMIYYAH ta dawo daga Computer Skull.Lokacin data shigo gidan ta samu Yasmeen na Sasan Baba Sani don haka kai tsaye kayan jikinta ta cire ta nufi toilet don watsa ruwa.Duk da anyi ruwa da safe bai hana rana ƙwallarewa ba,shiyasa ɗan tafiyan da sukan yo daga cikin Class zuwa bakin gate ya gajiyar da ita,shiyasa da ta dawo tafi gane ta ɗan watsa ruwa sannan take jin daɗi.
Ta fito wankan kenan Yasmeen ta shigo ɗakin hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano.TAIMIYYAH ta dube ta tana faɗin, "Yasmeen me kuma kika samo a Sasan Baba Sani?" Yasmeen ta aje kwanon a saman drawer tana faɗin, " Awara ce Mero me aiki tayi ya bani sha'awa shine na amso a ɗanyenta,zan soya da kaina da Egg in masa sauce.
TAIMIYYAH ta furta, "Wow! Aiko ni ma zan ci wallahi,na rabu da cin Awara ma ni kam."
Kafin kowa ya sake cewa komi wayan TAIMIYYAH ya fara kiɗa,tuni ta gane Nass ne sabida a yanzu ringing ɗin data sanya masa na daban ne.Don haka ta ɗauki wayan tana faman narke murya basu wani jima suna magana ba ta aje wayan tana duban Yasmeen take faɗin, "Yasmeen Nass fa ya dage sai ya zo ni kuma ina tsoran wannan karon suyi arba da Baba Sani,ga Yah Deeku ma duk yau ɗin za su shigo weekend."
Yasmeen ta saki murmushi tana duban TAIMIYYAH take faɗin, "Waya ce miki zasu dawo yau? Lagos fa za su wuce don haɗo abubuwan Abiee da suke can,sabida za a fara zaman rabon gado don sauke masa nauyi,ina ga bama a gobe zasu dawo ba sai zuwa jibi,haka na ji Iyah suna waya da Baba Sanin bayan kin fita Skull ɗazu da Safe."
TAIMIYYAH sai ta tsaya tai shiru tare da faɗawa duniyan tunani, 'Yanzu har za a fara maganan raba gado?" Ta tambayi kanta da kanta tana jin wani abu na son tokare mata maƙoshi, jikinta a sanyaye ta nufi wajen kayanta tana ciro rigar da zata saka.
Doguwar riga ce ta ciro na wata Atamfar Java Holland me kyau.Kalan red and black da akai wa ƙananun zane da kalan golden and green colour,ɗinkin free gown ne da ya yi mata mugun kyau,kaman yadda kalan ya haska farar fatarta.
Ta ɗaura ɗankwalin kayan tana ɗaukan Turarenta ta fesa kaɗan ta aje kwalban tana maida dubanta akan Yasmeen da ke ta faman bin ta da kallo,ta aika mata harara tana faɗin, "Wannan kallon fa Yasmeen sai kace baki taɓa gani na ba."
Yasmeen ta saki murmushi tana faɗin, "Ke baki ga yadda ki kai kyau bane shiyasa,daga nan har zuwa lokacin da Nass zai zo karki sauya wannan shigan please,wallahi kayan sun amshi jikinki sosai Masha Allah!"
TAIMIYYAH ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, "Ke dai Yasmeen ba dama ne wajen iya ziga mutum,ni tashi mu je ki soya Awaran mu ci tun kafin Babah Ladi ta gama girki in ji Awaran ya fita kaina."
Daga haka suka fito tare da Yasmeen ɗin zuwa Kitchen,bayan sun ma Babah Ladi da ke ta suyan Waina sannu da aiki ne sai suka fara hidiman gabansu.Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala suyan Awaran wanda suka wadata shi da egg,ya ji haɗin Sauces ɗin Albasa sai qamshi ke tashi duk ya cika kitchen ɗin.
Bayan sun ɗibarwa Babah Ladi ne suka juyo sauran cikin plate su ka nufo falon Iyah,in da suka samu Iyan a zaune tana faman zuba Sugar a cikin bokitin Nonon da za a yi sadaka da shi haɗe da Waina, idan an gama soya Wainar. Ta ɗago tai wa su TAIMIYYAH kallo ɗaya tana faɗin, "Dama na san wannan qamshin da ke ta zuwar min har nan kune kuke wani abin kwaɗayin.Yanzu Awaran ce ba za a ci ta hakanan ɗinta ba sai an mata wannan haɗin lallai kam!"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe face tana duban Iyah take cewa, "Iyah ai yanzu duk haka ake yi,anfi iya ci da yawa idan akai irin wannan haɗin,bari dai a baki naki ki ci ki ji yadda yake."
Iyah tayi saurin girgiza kai tana faɗin, "ku ci abinku lafiya ni kam bada ni ba."
TAIMIYYAH su kai dariya suna cin abinsu hankali kwance,bayan sun kammala ne Yasmeen ke sanar da Iyah Nass zai zo zuwa anjima.Kuma gobe idan Allah ya kaimu zasu je su duba Mamarsa da aka kwantar a Asibiti, kamar yadda yake ta magiyan su tambayi Iyan izini tun yau.
Iyah ta ɗaga kai ta dubi Yasmeen ɗin da ke mata bayani tana cewa, "To sannu sarkin iya tsari me kaifin baki,ita Zainabun bata da baki ne halan? To duk ba wannan ba ni a gaskiya bana son irin wannan sakarcin,wai saurayi ya fara ɗaukan budurwa yana kaita wajen danginsa tun kafin ai aure ko magana me ƙarfi ya shigo,hakan ba mutuncin ƴa mace bane sam.Amma yanzu tunda ana maganan rashin lafiya ce ta uwa kuma shine ya roƙi ku tambayeni izini,to zan amince amma da zaran kun yi mata sannu ku kamo hanya ku dawo gida.Ban amince daga dubiyan ku bishi ko'ina ba kunji na gaya muku! Don hakan ba mutunci bane sam, ku dinga riƙe martaban ku na ƴaƴa mata,wayewa duk idan bata musulunci bace halaka ce,don haka ku kula kuma shine karo na ƙarshe, dama ke Zainab ina son in gaya miki tunda na ga kun fuskanci juna kina sonsa to zuwa wata satin sai ya zo ya samu Babanki Sani,in yaso sai ya turo magabatansa a zo a yi magana a san da zamansa."
TAIMIYYAH da tunda Iyah ta fara magana tai ƙasa da kanta,sai yanzu ta ɗago ta dubi Iyan cike da shagwaɓa take cewa, "To Iyah zan sanar masa Insha Allah! Kiyi haƙury nima wallahi bana son zuwa duba wata Mamarsa,shi ne ya matsa da maganan ita kuma Yasmeen ta amsa cewa zata tambayeki,don ni kai tsaye na sanar masa ma ba za ki amince ba."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana ƙin yarda su sake haɗa ido da Iyah,ganin haka yasa Iyah cewa, "Karki damu tunda uwarsa ce sai ku je ɗin,amma daga haka bazai sake cewa ki bishi ko'ina ba,don ma ga Yasmeen ɗin dai za ta yi muku rakiya da ace ke da shi ne kaɗai bama zan taɓa amincewa ba sam."
Daga haka suka kulle babin wannan maganan,suka ɗakko maganan zaman rabon gadon da za a fara idan an gama tattara abinda Abie ɗin ya bari.Jikin TAIMIYYAH duk sai yayi sanyi hankalinta ya sake tashi,tana jin wani irin kewa me tsanani na danne zuciyarta.
Ganin mood ɗinta ya sauya gaba ɗaya yasa Iyah kawar da maganan,ta hanya sanya TAIMIYYAH ta tashi ta kai Nonon da Iyan ta gama sanyawa Sugar zuwa Kitchen.Daga nan ta duba idan Babah Ladi ta tara Wainar da yawa,sai su fita ita da Yasmeen su haɗo kan almajiran da za a baiwa Sadakan Wainar da Nonon.
Hakan ko akayi su TAIMIYYAH suka fita kiran almajiran da kusan duk Friday sukan taru a ƙofar gidan.Don sun saba amsar sadaka a Sasan Iyan,mussamman idan Waina ko tuwan shinkafa aka yi. Sai da suka gama raba ma almajiran sadakan tas sannan suka dawo ciki suka nufi ɗakin su don ganin lokacin sallan Zuhur ya yi.
*5:35pm*
Motar Nass ne ta faka a ƙofar gate ɗin shiga gidan su TAIMIYYAH.Ya fito sanye cikin shigan manyan kaya riga da wando na shadda,anyi masa ɗinkin zamani da ya dace da Matashi kamarsa,wanda ya san daraja da ƙiman iya saka kaya.Kalar shaddar Milk ne daya haska shi sosai fuskarsa cike da annuri yake takawa zuwa bakin gate ɗin ya buga. Tukur Mai-gadi ya buɗe suka gaisa yana faɗin, "Ranka-ya-daɗe barka da isowa." Nass ya saki murmushi yana faɗin, "Barka dai Malam Tukur ya ƙoƙari."
"Lafiya lau wallahi barka da isowa,bari a sanya maku kujerun zama kafin Gimbiyar ta fito." Cewan Tukur yana nufan inda zai ɗakko fararen kujerun zama ya aje ma Nass ɗin.Nass yabi bayansa da kallo yana me zaro wayansa ya shiga kiran line ɗin TAIMIYYAH.
Basmah wacce ta fito daga Sasan su zata fita can ƙasan layinsu,sai idanunta suka hango mata Nass da ke magana da TAIMIYYAH a waya yana sanar da ita gashinan cikin Compound ya iso.Tayi saurin gyara zaman gyalen jikinta tana wani gyara takun ta cike da yanga,sanye take cikin Riga da Skat da suka fidda suranta. Idanunta akan Nass yake har ta ƙariso inda yake tsaye tai masa sallama ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akanta,yana amsa guisuwanta da faɗin, "Basmah ko,ina fata kina lafiya?"
Basmah ta wani kashe murya cike da iyayi take faɗin, "Lafiya lau Bro bari na kira maka Yah TAIMIYYAN kafin na wuce ko." Daga haka ta juya don zuwa Sasan Iyah ta kira masa TAIMIYYAH,ba tare data jira Nass ɗin ya sanar da ita cewa TAIMIYYAN ta san da isowan nasa.
Tana sanya kanta a ƙofar shiga Sasan ita kuma Yasmeen na fitowa,hakan yasa saura kaɗan suyi karo Basmah ta ja baya tana faɗin, "Ayyah! Yah Yasmeen saura kaɗan mu gwabza karo,wai na zo sanar da TAIMIYYAH cewa guy ɗinta ya iso."
Yasmeen tayi wa Basmah wani sakartaccen kallo tana faɗin, "Okey! Ai tuni ta san da isowan nasa Basmah,yanzu ma wajensa na nufa kafin ta fito." Daga haka Yasmeen ta ɗaure fuska tana yin gaba abinta ta bar Basmah da bin bayanta da kallo,tana wani taɓe baki ta juyo itama don tafiya inda za ta.
Lokacin da Basmah ta fita wajen gate ɗin gidan nasu idanunta akan haɗaɗɗiyar motar Nass suka fara sauka.Tayi tsaye cak! Tana bin motar da kallo zuciyarta na wani irin kaɗawa,ta cigaba da tafiya tana ƙarewa motar kallo cikin Zuciyarta take cewa, 'Taɓɗi! Yanzu wannan motar tasa ce,shine duk haɗuwarsa da ajinsa ya rasa wacce zai so sai Yah TAIMIYYAH,wacce take gurguwa musaka shi ko me zaici da ita? Alhali ga ƴan mata kamarta lafiyayyu da basu da nasakan komi a tattare da su." Ta cigaba da tafiya zuciyar na raya mata wasu tarin lamura, da take ji dole ma tayi anfani da basirarta wajen karkato da hankalin wannan Zuƙeƙen saurayin zuwa gareta. Har ta kai gidan su Zeenah wata qawarta anan ƙasan layin, zuciyarta bata bar ta sukuni ba.Don gaba ɗaya Nass ya tafi da dukkanin nutsuwarta,sai yau ne ma ta sake ƙare masa kallo ta ga haɗuwarsa sosai.
Allah Sarki ita ko TAIMIYYAH suna can suna shan luv ɗinsu da Nass ɗin,bayan ta fito ta same shi zaune shi da Yasmeen. Isowan TAIMIYYAH wajen yasa ta basu waje ta je kawo ma Nass ɗin lafiyayyen samosa da meat pie ɗin da sukai masa haɗe da lemun Abarba da yaji Kwakwa da Madara. Koda ta kawo bata sake zama ba ta koma cikin gida ta basu waje don TAIMIYYAH ta sake da Nass ɗin sosai,wanda gaba ɗaya tun isowan TAIMIYYAH wajen ya wani rikice sai faman bin ta da azababban kallo yake. Gyale ta yafa yau ba Hijab ba hakan yasa tai masa kyau sosai fiye da kullum.Shiyasa ya kasa ɗauke idanunsa akanta har abin ya dinga bama TAIMIYYAH haushi, ta ji dama bata biyewa Yasmeen ta fito sanye da gyale ba.
Sun ɗauki a ƙallah awa ɗaya da rabi kafin yai mata sallama yana aje mata sabbin kuɗi wai ta sayi credit.Babu yadda TAIMIYYAH bata yi akan ya ɗauki kuɗinsa ba amma fir! yaƙi,sai ma rigiman da ya kafa mata akan cewa sai tayi masa rakiya bakin gate. Hakanan ba don ta so ba ta raka shi sukai sallama da juna,ta juyo don komawa cikin gidan bayan ta tsaya ta ɗauki kuɗi da tray ɗin abinda Yasmeen ta kawo,wanda kaɗan ya ci ya bar sauran.
Lokacin data isa ciki a falo ta aje tray ɗin hannunta tana nufan ɗakin Iyah don bata kuɗin hannunta ta aje.Faɗa sosai Iyah ta yi ma TAIMIYYAH akan amso kuɗin da tayi har sai da TAIMIYYAH ta fara mata alamun za ta yi kuka sannan Iyah ta amsa kuɗin ta adana.
"Yah Zuhurah kin ko ga motar da Guy ɗinnan me son Yah TAIMIYYAH yake hawa? Gaskiya wallahi guy ɗinnan ya haɗu ƙarshe....Sam bai ma dace da Gurguwa kamar Yah TAIMIYYAH ba.Gaba ɗaya ya gama tafiya da zuciyata Allah ya sani na kamu da son sa farat ɗaya kuma sai na san yadda nayi ya zama mallaki na.Don baxan bari ina ji ina gani ya auri wata gurguwa can musaka,alhali na gani na ƙyasa sam hakan bazai taɓa yiwuwa ba."
Zuhurah da tun fara maganan Basmah ta zuba mata ido,sai yanzu da Basman ta kai aya sannan ta dube ta cikin ido tana faɗin, "Basmah kinsan me kike faɗi kuwa? Snatching ɗinsa za ki yi ko me kike nufi da waɗannan kalaman?"
Basmah ta wani watsa hannuwa baya tana faɗin, "Yadda kika faɗin shi za a yi snatching idan nayi aiba kaina farau ba,wallahi Numbern sa zan sata in gwada sa'ata,idan an dace shikenan sai labari ya canza,shi ma banda abinsa me zai ci da gurguwa? Duk abinda yake nema a jikinta nima ina da shi kyau da farar fata kawai zata nuna min."
Yadda Basmah ta kai ƙarshen maganan tana wani jujjuya jiki yasa Zuhurah kwashewa da dariya dai-dai kuma lokacin da Umma ta fito,tana duban Zuhurah take faɗin, "Dariyan me kuke yi haka kaman wasu taɓaɓɓu?"
Zuhurah sai ta sake kwashewa da dariya,cikin dariyan take sanar da Umma komi,sai Umman ta xauna tana faɗin, "Ke Basmah da gaske kike yi motar da yake hawa har ta fi ta Sadeeq kyau? To ɗan gidan uban waye ta rakito tana gurguwa musaka da ita,anya ko ba Iyah ke shige da ficen da take nemowa Yarinyar can maganin farin jini ba? Ana kulle idanun Samari su daina ganin nakasan Yarinyar in banda haka ina hakan zai yiwu kana lafiyayye ka auri me nakasa."
Umma tayi maganan tana jin wani abu na tokareta a ƙirji.Basmah tayi saurin faɗin, "Sai ma kin ga haɗuwan guy ɗin Umma,wallahi bazai yiwu ace kamansa ya kawo kansa wajen musaka gurguwa wacce sai da taimakon dafa guiwa take iya tafiya a duƙe,ni dai yanzu da gaske na ke sonsa ya kama Zuciyata Umma,kuma idan ma muka zuba ido ta aure shi ai mune da kunya tunda kin hana ya Sadeeq ya aure ta, to kuma kawai sai a ga ta samo wanda ya fi Yah Sadeeq ɗin komi ai mun ji kunya kenan Umma."
"Ƙwarai maganarki a kan hanya ta ke Basmah,idan har na zuba ido ta auro wanda yafi Sadeeq na ji kunya,sai Iyah ta zuba ruwa a ƙasa ta sha,don haka idan har da gaske kina son sa kiyi ƙoƙarin sato numbarsa a wayanta,sauran bayanin duk zan kitsa miki shi,ke inma bazai so ki ba to sai dai kuyi biyu ba bu,amma In Sha Allah ba za ta auri wani mutum me daraja ba sai musaki ɗan uwanta,shegiyan yarinya me kama da Aljanu."
Zuhurah data saki baki tana duban Umma sai cewa tayi, "Umma yanzu sai ki goyawa Basmah baya tayi ƙwacen saurayi,ni aganina hakan duk bai taso ba,ku ma tsaya ku ga yadda tarayyan nasu da shi zai kaya mana,ku ka sani ma ko jikinta take bashi yana anfana da shi tunda har ta iya sakewa ya Deeku ya kwashi rabonsa waye za ta ki baiwa kanta,tunda ta san da wuya ta auru ku kuna ganin kyawun da take ƙarawa na banza ne? Ni hatta cikar ƙirjinnan ban yadda ba hannun maza yaji ba yake ƙara bunƙasa." ( _Allah ka raba mu da sharrin maƙiyi,readers wannan irin sharri da Zuhurah kewa TAIMIYYAH na lafiya ne kuwa? Dole ka nemi tsari daga sharrin maƙiya,duk wanda baya son ka babu abinda ba zai iya yi ma na ɓatanci ba arayuwa,sai dai mu ce Allah ya sakawa Baiwar Allah TAIMIYYAH_ 😰).
Umma ta dubi Zuhurah tana cewa, "Oho! Koma dai mene ne tunda ƴar uwanki ta kamu da sonsa ai sai ki mara mata baya tai iya yinta wajen janyo hankalinsa.To wai ma yaushe kika fara sonta da har za ki ji tausayinta? Ke abin sonki ne ta auri wanda yafi Yayanki komi,waya sani ma yafi har Ameerun da kike taƙama da shi tunda ba a ma san ɗan gidan uban waye ba,yanzu haka irin ƴaƴan attajiran garin nan ne ma waya sani?"
Zuhurah sai taji maganan Umma ya soki Zuciyarta,wani kishi da tsanan TAIMIYYAH na taso mata,tare da wani tsoro me tsanani tana ji kada fa maganan Umma ya tabbata Nass ɗin yafi Ameerun ta,aiko da ita da kanta zata iya ƙullawa TAIMIYYAN makircin da ba za ta auri Nass ɗin ba,tayi saurin haɗe face tana faɗin, "Don Allah Umma ki daina wannan fatan,hakan ma ba zai taɓa kasancewa ba,Ameeru fa Babansa har Muƙamin ɗan Majalisan Jiha ya yi a baya,kin san ko sun tara arziƙi ba kaɗan ba."
Umma ta danna ma Zuhuran harara tana cewa, "To shi ma sai ki bari mu san ko shi waye ɗin,kuma ta ina zamu sani ba tare da Basman ta saci number ɗinsa mun fara bibiyansa ta waya ba."
Dukansu su kai na'am da maganan Umma,sun daɗe suna tattauna yadda za a yi Basmah ta sato Number ɗin Nass a wayar TAIMIYYAN,daga ƙarshe Zuhurah ce ta basu tabbacin su bar komi a hannunta zata samo numbern cikin ruwan sanyi.Daga haka suka rufe maganan zuciyoyinsu cike fal da ƙyashi da hassadar yadda TAIMIYYAH ta fi su tarin abubuwa masu yawa alhali tana matsayin gurguwa musaka da suke ganin ita ɗin bakomi bace.
_To masu karatu ya ku ke ganin wannan Cakwakiyan za ta kaya? Su Umma za su yi nasaran raba soyayyan data riga ta ƙullu tsakanin Nass da TAIMIYYAH ko kuwa wata ƙaddarance za ta raba? Sai ku cigaba da bibiyan yadda rayuwar TAIMIIYAN zata kasance.......✍🏻_
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
#Ɗansabo ce # [12/14, 10:06 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*38*
__________Suhailah ce zaune tana kallo a cikin makeken falon nata da ke down-stair. Daga gefenta ƙaramin Bowl ne da aka ciko shi da milky cin-nin wanda tayi ordering daga wajen BAMS,wata shahararriyar me yin Snacks a nan gaban layinsu kaɗan.Gefe guda kuma kwalin Hollandia Milk ne da cup wanda ta cika da milk ɗin tana korawa da cin-cin ɗin kaɗan-kaɗan.
Wayarta da ake kira yasa ta ɗauke ido daga kan makeken smart TV ɗin ta mayar kan wayar, tana duba sunan me kiran ganin sunan Bala Mai gadi ne, yasa ta ɗaga wayar ta kai kunni.