Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 20
Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 20: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…
4,456 words
Fitowan TAIMIYYAH zuwa main-parlor ɗin yayi dai-dai da shigowan big bros ɗin su Yasmeen ɗin me suna Emran.TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa lokacin da shima idanunsa ke sauka akanta.Sai ta ɗan saki fuska sosai tana cewa, "Sannu da zuwa Yah Emran ina yini." Emran ya amsa a taƙaice da faɗin, "Lafiya lau Sis barka da xuwa." Daga haka bai sake cewa komi ba ya nufi hanyar da zai kaishi kitchen.
TAIMIYYAH tabi bayansa da kallo tana taɓe baki,don batun yau ba ta san shi ɗin miskili ne na gaske. Sam baida hayaniya da kula mutane fuskarnan kullum a cuskule yake. Memakon ta zauna a falon ma sai kawai ta yanke shawaran komawa ɗakin Yasmeen tai kwanciyarta tana ɗaukar wayarta ta hau online. Yasmeen data shigo ta ganta a kwance sai ta nufeta tana cewa "Ke yada kwanciya a ɗaka kamam wata baƙuwa,ki tashi mu fita falo mana ga su Yah Anas can sun shigo ku gaisa."
TAIMIYYAH sai ta tashi zaune tana taɓe baki take cewa, "Ni rabani da wani fita falo wannan Yah Emran ɗin yaita ma mutane kallon banza.Baki ga fa dana gaida shi yadda amsa gaisuwan a wani wulaƙance,shi dai akwai baƙin hali wallahi."
Yadda TAIMIYYAH tayi maganan tana faman kwaɓe fuska yasa Yasmeen sakin dariya tana faɗin, "Ke sai kace baki san hali ba TAIMIYYAH da har zaki wani damu don ya yi miki hakan,shi fa kowa ya san halin miskilncinsa.Shiyasa gashi nan ko budurwa ya kasa yi har ansawa Yah Anas rana ashe ina can Zaria,amma shi kin ga ko budurwa bana ji yana da ita,don Allah ki tashi mu je falo nasan ma bazai zauna ba ya fita abinsa zuwa part ɗinsu."
Ba don TAIMIYYAH taso ba haka tabi Yasmeen suka fita xuwa falon.TAIMIYYAH da fuskan mutumin nata Yah Emran ta fara cin karo,yana nan zaune babu wani inda ya je. Sai ta haɗe fuska tana ɗauke kai daga duban sashin da yake zaune.Ta ƙarisa kusa da kujeran da Yah Anas ke zaune wanda tun fitowan su TAIMIYYAH yake sakar mata murmushi,kafin ya riga ta da faɗin "Wow! Sis barka da xuwa yau wace rana Iyah ta barki kin shigo Kano,welcome dear Sisi." TAIMIYYAH itama sai ta sakar masa murmushinta me kyau tana faɗin," Thank u Yah Anas na sameku lafiya,ashe kuma an sanya lokaci to Allah ya sanya alkhairy yasa za a yi muna raye,kace kafin inbar gari za a kaini inga irin zaɓen da kai mana ta Sis in-law."
Anas ya saki dariya yana faɗin, "Karki damu Sis kisa a ranki kin ganta kin gama."
TAIMIYYAH ta maida masa martanin dariyan da yayi ƙasa-ƙasa.Tana maida dubanta kan ɗaya Yayan su Yasmeen ɗin me suna Ahmad tana faɗin, "Yah Ahmad ya kake?"
Ahmad da idanunsa ke kan TAIMIYYAH ya amsa da faɗin, "Lafiya lau aina ɗauka ba za ki gaishe ni bane sai Anas kawai kika sani." Yadda yayi maganan yana hararanta yasa duka suka saki dariya a tare.TAIMIYYAH na faɗin, "Sorry ai abin step by step ake bi,yanzu ba gashi mun gaisa ba ashe kananan dai kuna buga kishi da juna da Yah Anas ɗin."
Ahmad ya sake aika mata harara yana faɗin, "To ya za a yi kinsan saƙo da saƙo ai." Suka sake sakin dariya TAIMIYYAH sam bata sake duban inda Yah Emran ke zaune ba.Wanda ya harɗe ƙafa gaba ɗaya hankalinsa na kan TV amma kunnuwansa na jiyo masa duk abinda akeyi cikin falon. Hiransu suka yi sosai da su Yah Anas ɗin,Yusuf ne kawai baya nan wai yayi tafiya tare da wani Cousine ɗinsu xuwa Niger.Sai da aka kira Sallar Magriba sannan suka watse,mazan suka nufi masallaci su kuma su TAIMIYYAH suka shige ciki don yin nasu sallar.
Kwananta biyu da zuwa Kanon ta ware sosai a gidan Guggo Bilkin.Tana jin daɗin yadda ƴan uwanta su Anas ke ji da ita,don duk idan zasu dawo daga wajen aiki shi da Ahmad sai sun shigo mata da Ice Cream da su Shawarma. Yah Emran ne kawai babu ruwanta da shi daga gaisuwa sai gaisuwa ke haɗa su. Yasmeen ta kan fita zuwa can gidan da za su yi bikin cousine Sis ɗin tasu.Kasancewar gidan babu nisa da gidan su Yasmeen ɗin layi ɗaya ne ya raba su,shiyasa da ƙafa ma Yasmeen ke zagayawa ta je.
Ita dai TAIMIYYAH ko sau ɗaya bata taɓa bin Yasmeen ɗin ba don ita sam bata son shiga cikin mutanen da bata saba dasu ba.Guggo Bilki tayi mita akan su dinga zuwa ana shirin bikin da su tare, amma TAIMIYYAH tayi biris taƙi zuwa.
Yauma tun safe Yasmeen ta gama shiri bayan sun karya kumallo.Ta sanar da TAIMIYYAH cewa zata fita zuwa gidan Babansu Lawal ɗin,don yau Thursday za a yi lalli.
TAIMIYYAH da ke daga kwance sai kawai ta sake gyara kwanciya tana faɗin, "Yasmeen ni wallahi bana son shiga mutanen da ban sani ba.Dama mun saba da Amaryar ce sai na je to amma ban santa ba itama ba sanina tayi ba,kawai sai aganni ana nuna ni ana cewa waccar gurguwan kuma daga ina?Gaskiya ba za ni ba ni ko ranan yinin ma ni kaɗai zaku bari a gidan don ba zuwa zanyi ba."
Yasmeen data gama jin haushi ta ballawa TAIMIYYAH harara tana cewa,"Ai ke kina da damuwa wallahi TAIMIYYAH.Inba haka ba miye na kawo wannan maganan,don Allah ki taso muje kema ai miki lallin mana,ko ja ne zai miki kyau sosai wallahi."
Da ƙyar ta ciyo kan TAIMIYTAH ta yadda zata bita itama ai mata lallin amma a hannu kawai.Ta tashi ta shirya cikin wata doguwar rigan atamfa da ɗinkin yabi jikinta sosai.Kamar yadda kalar atamfar me duhu ya haske farar fatarta,ta sanya Hijab irin me kamar riga ɗinnan,wanda zaka zura hannuwa kai ta sabgarka babu takura. Suka fito sai faman zuba qamshi suke yi.Sallama sukaiwa Guggo Bilki wacce taji daɗin yadda yau TAIMIYYAH ta yadda zasu fita zuwa gidan Bikin da Yasmeen. Tayi musu a dawo lafiya suna jerawa da juna suka fice daga gidan.
"TAIMIYYAH bari kawai mu ƙarisa bakin layin shigowa nan zamu sama Ɗan-sahu,sai mu hau ya zagaya damu layin gidan Baba Lawal don gaskiya zan wahal dake idan nace mu taka a ƙafa."
Yasmeen tayi maganan idanunta akan TAIMIYYAH da ke dafe da guiwar ƙafarta suna takawa a hankali.Lokacin da suka ƙarisa bakin titin basu wani daɗe ba suka tare Napep suka shige,ya zagaya dasu xuwa gidan Baba Lawal ɗin,suka sauka Yasmeen ta biya shi kuɗinsa suka shige zuwa cikin gidan.
A falon gidan suka tadda Anty Kareema matar Baba Lawal tare da wasu baƙi.Suka gaisheta ta amsa da fara'a idanunta akan TAIMIYYAH take cewa, "Yasmeen ina kika samo kyakykyawar budurwa haka,ko itace naji kina cewa kun zo daga Zaria tare?"
Yasmeen ta saki murmushi tana faɗin "Itace Ummah sunanta TAIMIYYAH,bata son shiga mutanene yanzu ma da ƙyar ta amince ta biyoni,Kausar ɗin na ɗaki ne?"
Anty Kareema dasu Yasmeen ke kira da Ummah,ta dubi Yasmeen ɗin tana bata amsa da cewa, "Allah sarki wallahi kyakykyawa da ita,Kausar na daga ciki ku ƙarisa mana na san ai sun gama shiri gara kuje wajen lallinnan da wuri." Daga haka su Yasmeen suka wuce zuwa don ƙarisawa ɗakin ƴan matan gidan.Anty Kareema da baƙuwarta suka bi bayan su TAIMIYYAH da kallo baƙuwar na cewa, "Oh! Yarinya kyakykyawa da ita amma ta nakasa wannan da ba gurguwa bace da anga zallar diri da kyawun halitta,wallahi sai naji duk tausayinta ya kamani."
Anty Kareema ta jinjina kai tana cewa, "Ke dai bari Raliya kin riga ni da baki ne,wallahi yarinyar ta birgeni a ganin farko,haka Allah ke ikonsa."
Duk wannan maganganun dasu Anty Kareema ke yi akan kunnin TAIMIYYAH ne.Wacce ke bin bayan Yasmeen a hankali zuwa ƙoafr shiga ɗakin ƴan matan,don haka akan kunninta sukai maganan. Ta shige cikin ɗakin daga ƙarshe tana jin wani iri cikin zuciyarta.Ire-iren waɗannan maganganun da bata rabo da jin su suna ɗaya daga cikin abinda yasa bata faye son shiga mutane ba.Sabida yawan tanka kyawunta da tausayawa Nakasanta da mutane ke yawan yi,wanda hakan na taɓa zuciyarta da jefa mata rauni da tausayin kanta da kanta.
Lokacin da suka shige cikin ɗakin ƴan matan wanda su biyu ne ma suka rage ba su yi aure ba.Yasmeen ce ta nunawa TAIMIYYAH gefen gado tana cewa, "Ga waje TAIMIYYAH zauna,Kausar ga TAIMIYYAH na janyo muku ita yau zamu tafi Lallin tare."
Daga Amarya Kausar har ƙanwarta me suna Firdausy suka zubowa TAIMIYYAH idanu.Firdausy na riga Kausar da faɗin, "Sannu da zuwa TAIMIYYAH,Yasmeen gaskiya ƴar uwar taki kyakykyawace ga sunanta unique, sam ni ban taɓa jin mace da suna TAIMIYYAH ba."
TAIMIYYAH ta sakar musu murmushi suka gaisa cikin fara'a, Yasmeen na cewa Feedoh, "Haka kowa ke cewa bai taɓa jin sunan ba a wajen mata.Kuma asalin suna TAIMIYYAH mata aka fi samawa don ko Abul Barakat da Abul Abbas da ake ce musu Ibnu TAIMIYYAH.Toh su TAIMIYYAN sunan wata kakarsuce na can sama amma macece,sai dai a wajen su labarabawa ba kowanne irin mutum suke kira da suna TAIMIYYAH ba.Sai wanda ya shahara da ko dai kyau ya zama mutum kyakykyawaneshi na buga misali,ko kuma irin budurwarnan wacce take da kyawawan ɗabi'u da iya zama da mutane me haƙury sosai to sai su kirata da suna TAIMIYYAH.Amma galibi bakasafai suke kiran mutum TAIMIYYAH ba se wanda yake da siffofi da ɗabi'u masu kyau abun yabo."
Yasmeen ta kai ƙarshen bayaninta,tana sakin murmush ganin irin hararan da TAIMIYYAH ke aika mata. Kausar ta furta, "Wow! kice idan na haifi ƴata mace kyakykyawa zan sanya mata suna TAIMIYYAH kuwa,sai in mata fata ta taso da dukkanin siffofi ababen yabo.Yadda za ta cika sharuɗan cinye suna TAIMIYYAH,don wannan Sis ɗin taki Yasmeen da alamu ita ta cinye sunan,don ga kyau nan ga kuma alamun nutsuwa a tare da ita."
Yasmeen ta saki dariya ita da Feedoh suna haɗa baki wajen faɗin, "Amma wannan Amarya baki da kunya tun kafin ma a ɗaura har kin fara zancen haihuwa,eh lallai gara ayi-ayi mu miƙaki tun kafin kifi ƙarfin mu."
Wannan karon har da TAIMIYYAH aka saki dariya,kafin su Feedoh su kammala shirinsu Kausar ta kira wanda zai kaisu wajen yin Lallin. Lokacin da suka fito jere da junane su Kausar suka kula da yanayin tafiyar TAIMIYYAH.Suka gane ashe gurguwace me laluran ƙafa,take suka ji wani tausayinta ya kama zuciyarsu,Feedoh tai ƙasa da murya tana cewa Kausar, "Wayyo Yah Kausar dubi yadda sai ta dafe guiwa take iya tafiya,ina ma Allah bai jarabceta da laluran ƙafa ba,wannan ai da baƙaramar haɗaɗɗiyar mace za a yi a wajennan ba.Sabida Allah ya bata kyau da dirin jiki,dama shiyasa ake cewa ɗan Adam tara yake bai cika goma ba.Duk abinda kake taƙama da shi sai an rageka ta wani fannin toh ita dai da gurgunta aka jarabceta,amma fa wannan matar manyace gaskiya akwai body da kyau masha Allah."
Kausar ta jinjina kai tana faɗin, "Wallahi kuwa Feedoh,Allah dai yasa mu dace amma naji tausayinta ya kama zuciyata."
TAIMIYYAH dai tayi gaba abinta bata san wainar dasu Kausar ke toyawa akanta ba.Don lokacin da suka fito wajen motar wanda zai kai su kiran Zee ya shigo wayar TAIMIYYAH.Don haka tai receving call ɗin tana kaiwa kunni lokacin da Yasmeen ta buɗe mata murfin back seat ta shige ta zauna.Itama Yasmeen da Kausar back seat ɗin suka shiga sai Feedoh ne ta kame agaba. Yellow yaja motar suna barin layin,har lokacin TAIMIYYAH na amsa wayar Zee dake bata labarin tayi sabon Saurayi.
Lokacin da suka isa gidan Lallin Amarya Kausar ita aka fara yiwa ja a ƙafa.Sannan akaiwa TAIMIYYAH a hannu don tace bata son baƙi iya ja kawai za a mata. Da ƙyar su kausar suka ja ra'ayinta ta yarda ai mata har da ƙafafu. Basu san ita TAIMIYYAH kunyan yadda zata buɗe ƙafarta aga ɗaya yafi ɗaya girma shi ke hanata yin Lalli a ƙafa ba.Ko zata yi tafi yarda ta siya salataf na yanka ta manna abinta tayi da kanta. Amma hakanan ta miƙa ƙaramar ƙafar aka zana mata.Su Kausar na ta satan kallon ƙafafun nata suna jin wani tausayinta da kaɗaita ƙuduran Allah cikin zukatansu.Don banda Allah wa zai yi hakan gaka mace har mace kaman TAIMIYYAN amma gashi Allah ya jarabceta da Nasaka na ƙafa ɗaya. Lokacin da aka gama zanawa duka ƙafafun ba ƙaramin kyau Lallin yayi ba,tun kafin ma ya kama a cire.Ita dai TAIMIYYAH na zaune bata wani sanya musu baki a hiran da suke,zuciyarta na can wajen tunanin Nass wanda har yanzu ta kasa yakice tunaninsa daga zuciyarta sai dai bata zauna waje ɗaya ba.
Basu baro gidan Lallin ba sai huɗu na yamma.Zuwa lokacin TAIMIYYAH ta gama galabaita da yinwa,don sam taƙi cin duk abinda aka siyo musu a gidan Lallin. Sai data ga yinwa zai halakata sannan taiwa Yasmeen raɗa suka tsaya a wani shago aka amso mata Hollandia Milk da Buns ta ci a motar. Lokacin da suka iso gidan su Kausar juyin duniya anyi TAIMIYYAH ta shiga ciki suyi sallolin da ke kansu amma taƙi. Ta kafe ita kawai su barta Yellow driver ya sauke ta a gida,ita Yasmeen ɗin ta dawo daga baya.
Hakanan su Yasmeen suka bar TAIMIYYAH ta tafi Yellow zai sauke ta a gida. Suna isa TAIMIYYAH ta sauka ta shige ciki.Tun a waje ta hango motar Yah Emran dama shi huɗu yake baro office ya dawo gida daga wajen da yake aiki.
Ta isa cikin gidan tana ji kanta har wani ciwo yake mata sabida rashin cin abinci akan lokaci. Tunda tai sallama taji babu motsin kowa a falon kawai sai ta nufi ɗakin Yasmeen kai tsaye. Tana shiga tai wurgi da Hijab ɗin data cire akan Bed ta nufi toilet ta yo wanka tare da ɗauro alwala ta fito. Idanunta ta zuba akan yatsun hannunta da jan lallin ya kama juwur abin sha'awa,tana kallon irin kyawun da lallin yayi a yatsun hannunta. Da sallolin da ke kanta ta fara bayan ta idar ne ta canza rigar jikinta zuwa wata doguwar rigan ta shan iska mara nauyi.Kalar rigan pich ne sai ya ƙara fito da hasken fatar ta,bata sanya hula a kanta ba sai ta bar gashinta dake ɗaure da Ribbom a tsakiyar ka.
Ta fito don zuwa ɗakin Guggo Bilki ta sanar da ita ta dawo ta kuma nema abinci. Sai dai tana sanya kanta cikin corridor ɗin shiga ɗakin Guggo Bilki idanunta ya sauka akan takalman Yah Emren,dake xube daga bakin ƙofar shiga ɗakin.A hankali amon sautin muryar Guggo Bilki ya fara shiga kunnuwan TAIMIYYAH. Jin Guggo Bilki ta ambato sunanta yasa ta jan birki daga bakin ƙofan.Ba tare da tayi yinƙurin shiga ɗakin ba,haka kawai taji tana son jin dalilin kiran sunanta cikin hiran Guggo Bilki da Yah Emran ɗin........✍🏻
*Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku* *.To ga dama ta samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.* *Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻
*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,* *Turaren wuta dinta kuwa Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji, Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night, Bukhur, Alajab.*
*Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline.* *Harma da su atamfofi, less, shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .*
Za ku sameta a Garin Kano ta wannan adireshin:- No:221 sarari koki quaters.
Ko ku nemeta a garin Kaduna a Unguwar kanawa.
ga handle ɗinta na Instagrm kamar haka👇🏻 @ Ruuscollections
Ga kuma lambar wayarta don kiranta kai tsaye 👇🏻
07025393114 [12/14, 10:07 PM] +234 703 769 7050: *Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku.* *To ga dama ta samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.* *Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻
*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,* *Turaren wuta dinta kuwa akwai Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji, Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night, Bukhur, Alajab.*
Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline
Harma da su atamfofi, less, shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .
Zaku sameta a Garin Kano ta wannan adireshin:- 221 sarari koki quaters.
Ko ku nemeta a garin Kaduna a Unguwar kanawa.
ga handle ɗinta na Instagrm kamar haka👇🏻 @ Ruuscollections
Ga kuma lambar wayarta don kiranta kai tsaye 👇🏻
07025393114
*36*
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na ranar asabar ɗin, su TAIMIYYAH suka gama shirin zuwa gaida Mum ɗin Nass. TAIMIYYAH na sanye ne da wani haɗaɗɗen Egyptian Abaya kalan navy blue wanda akai ma adon zane a wuya da hannun rigar da pink and black colour.Ba ƙaramin kyau TAIMIYYAH ta zuba ba musamman da tai rolling veil ɗin abayar ya zagaye beautiful cute face ɗinta,sai ta fito tamkar wata balarabiyar ƙasar Marocco. Fuskarta Powder ne kawai ta shafa sai man leɓe me taushi idanunta kuma ta zizara musu kwalli, tare da gyara baƙin gashin giranta da Brush ɗin kwantar da gira. Daddaɗan ƙamshin body mist da turaren GIORGIO PINK data yi anfani da su ke tashi a jikinta duk ta yadda ta motsa.
Ta ɗaga manyan idanunta masu tsananin haske ta dubi Yasmeen wacce ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar gown na Material. Ɗinkin ya zauna a jikinta sosai tare da yi mata kyau sai ta ɗauki gyalen da ya shiga da kayan ta yafa bayan ta sanya manyan ɗan-kunni da suka ƙarawa kwalliyan fuskarta armashi,itama daddaɗan ƙamshi ke tashi a jikinta.
"Yasmeen ni fa wallahi kunyan zuwa dubiyan nan nake ji,gani nake yi kaman idan ya nuna ni yace ni ce Budurwar tasa zan muzanta ne a gabansu idan suka ga ni ɗin gurguwa ce."
Yadda TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan cikin rawar murya yasa Yasmeen da ke aje man leɓen dake hannunta saurin duban TAIMIYYAH tana faɗin, "Kin ga matsalarki ko TAIMIYYAH yanzu don Allah miye na sanyawa zuciyarki wannan banzar tunanin? Please kar ki ɓatan rai tun bamu kai ga fita ba,sai me don ke gurguwace? Ina sha ba shi ya kawo kansa wajenki ba ko kece kika janyosa ta ƙarfi ya zo gareki?"
Ganin yadda ran Yasmeen ya ɓaci yasa TAIMIYYAH faɗin, "Allah baki haƙury almasifatu daga gaya miki abinda ke raina sai ki hauni da masifa,to shikenan na bari bazan sake cewa komi ba har mu je mu dawo."
"Da dai yafi miki mutunci." Cewan Yasmeen tana zabgawa TAIMIYYAH harara kafin TAIMIYYAH tayi magana kiran Nass ya shigo wayarta.Sai ta ɗaga kiran tana kai wayan kunne,tsayin seconds ta ɗauka kafin ta furta, "Okey gamu nan fitowa yanzu Insha Allah."
Ta sauke wayan daga kunni tana duban Yasmeen take cewa, "Yasmeen gashi can a waje har ya iso."
Yasmeen sai ta nufi wajen takalmanta tana faɗin "Okey fara yin gaba kafin in ɗakko ledan kayan dubiyan ko?"
"A'a Yasmeen ni dai mu fita tare kawai,wani irin in fara yin gaba ya tsareni da wannan mayen kallon nasa." TAIMIYYAH tayi maganan tana sake kallon kanta a jikin mirrow ɗin ɗakin nasu,ita da kanta ta yaba da kyawun da Abayar yai mata a jiki sosai. Ta nufi wajen takalminta kalan blue black samfurin ALDO Flat.Ta zura ƙafarta a ciki take kalan ya haske farar ƙafarta. Wayarta ne kawai ta ɗauka tayi gaba tana fitowa daga ɗakin ta nufi ɗakin Iyah,ta sanar da ita cewa Nass ɗin ya ƙariso yana waje.Iyah ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan TAIMIYYAH tana me yaba kyawun da tayi kafin ta furta, "To shikenan Allah kai ku lafiya ku gaida me jikin kuma ku dawo da wuri kada ku yarda daga asibitin ku je ko'ina na gaya muku."
"Insha Allah Iyah,sai mun dawo."
Cewan TAIMIYYAH tana juyowa ta fito falo dai-dai lokacin da Yasmeen ta fito daga ɗaki hannunta riƙe da ƙatuwar leda,wanda sukai siyayyan kayan dubiyan da zasu kaiwa Mum ɗin Nass ɗin.Ita ma ɗakin Iyah ta nufa tai mata sai sun dawo ta fito suka jera da TAIMIYYAH suka fito daga Sasan.
Kamar yadda TAIMIYYAH tai ta Addu'an kar su haɗu da kowa a waje.Cikin sa'a ko babu kowa a wajen Compound ɗin har suka fice daga gate ɗin,bayan sun gaisa da Tukur da ke musu adawo lafiya.
Tun daga nesa Nass ya kafawa TAIMIYYAH idanu wacce ke tahowa hannunta dafe da guiwar ƙafarta,tana takawa cikin nutsuwan da Allah ya halicceta da shi. Gaba ɗaya shigar Abayar jikinta ya gama tafiya da zuciyarsa shiyasa har suka ƙariso wajen motar ya kasa ɗauke idanunsa akanta. Ya fito da sauri yana buɗewa TAIMIYYAH mata front seat ta shiga ya maida murfin ƙofar ya rufe, yana komawa da baya ya rufewa Yasmeen murfin side ɗinta itama,sannan ya zagaya ya shiga mazaunin Driver ya tashi motar.
Sassanyar ƙamshin turaren AZZARO WANTED dana jikin su TAIMIYYAH ne ya haɗe da sanyin AC ɗin cikin motar ya bada wani irin lafiyayyan ƙamshi me motsa zuciya.Nass ya ɗaga idanunsa ya sauke akan Gimbiyar tasa yana faɗin, "My luv irin wannan kyau da kika yi ai sai kisa in kasa yin tuƙin da karsashi.Gaskiya kice zan je na ƙara jibga yawan Abayoyi cikin kayan lefe tunda na lura kyau suke yi a jikin Baby na ba kaɗan ba."
TAIMIYYAH da kunya ya rufeta sai tayi saurin kauda face daga gefensa tana kallon gefen hanya murmushi na Blushing saman face ɗinta,ba tare da iya cewa komi ba hakan yasa Nass ya cigaba da tsokanarta tana faman jin kunya. Yasmeen na musu dariya,har suka isa Asibitin AL-MADINAH da ke cikin GRA zaria.
Haka kawai TAIMIYYAH taji jikinta yayi mugun sanyi lokacin da Nass ya tsaida motarsa.Gabaki ɗaya sai tana ji tamkar kar ta shiga cikin asibitin, don bata san wani irin tarba zasu samu daga ahalin Nass ɗin ba idan sukai ido biyu da ita suka ga ita ɗin gurguwace. Yasmeen ne data kula da sanyin da jikin TAIMIYYAH yayi ta ƙariso wajen da take tsaye tana me kama hannunta ta riƙe,murya can ƙasa take faɗin, "Malama don Allah ki saki ranki kinga yadda kika wani kwaɓe fuska ne miye haka kike son yi Sis?"
"Yasmeen wallahi tsoron shiga nake yi bansan wani irin tarba zamu samu a ciki ba,gaba ɗaya ƙirjina bugawa yake yi wallahi." TAIMIYYAH tayi maganan dai-dai lokacin da Nass ya ƙariso inda suke tsaye yana faɗin, "Bismillah luv mu je ko."
Yayi gaba suna biye da shi a baya har zuwa ɗakin da aka kwantar da Mum ɗin nasa a ciki.Zuciyar TAIMIYYAH babu abinda yake yi sai bugu,suka sanya kai bakinsu ɗauke da sallama. Yasmeen ita ce a gaba biye da Nass sai TAIMIYYAH daga bayansu,har suka ƙarisa ɓangaren da Nass ɗin ya nufa.
Mutane uku suka samu a zaune daga kan ɗaya gadon da ke ɗakin,wanda babu Patient akai da alamu Mum ɗin nasa ne kaɗai mara lafiyan da aka kwantar a ɗakin.
"Sannunku da zuwa Naseer da baƙi kake tafe ne haka,ince dai surukar tamu ce aka kawo yin dubiya?Sannun ku da zuwa ƴan mata ku ƙariso ga wajen zama."
Cewar wata Farar mata ƴar gayu dake zaune daga gefen mara lafiyar. Ta ƙare maganan tana nunawa su TAIMIYYAH kujerun roba biyu da babu kowa akai. Yasmeen ta janyo musu suka zauna suna gaida mutanen da ke zaune a ɗakin,wanda duk manyan mata ne babu sa'ar su ko ɗaya.
Mahaifiyar Nass dake daga zaune akan gadon an jingina mata pillow ta baya don jin daɗin zama.Ta ɗaga kai tana zubawa su TAIMIYYAH idanu lokacin da suka isa bakin gadon tare da durƙusawa suka kwashi gaisuwa da yi mata sannu da jiki. Ta amsa da sakin fuska idanunta akan Nass lokacin da su TAIMIYYAH suka koma wajen zamansu,ta buɗe baki tana cewa , "Auta wacece Surukar tawa a ciki?"
Nass da fara'arsa ya nuna mata TAIMIYYAH dake faman yin ƙasa da kai cike da jin kunya yana cewa "Gata nan Mum baki ga sai faman yin ƙasa da kai take yi ba tana jin kunya,da ƙyar fa nai convincing ɗinta ta zo sabida ta cika kunya."
Tunda Nass ya fara magana yana nuna TAIMIYYAH cewa itace zaɓin nasa fara'ar da ke kan fuskan Hajiya Hajara ya ɓace ɓat.... Dukkanin sauran ƙawayenta dake ɗakin suka tsurawa TAIMIYYAN idanu kaman masu son gano wani abu akan fuskarta, kafin muryan Mum ɗin Nass ya karaɗe kunnuwansu lokacin da take faɗin, "Kana nufin gurguwan itace yarinyar da kake sanar min ka samu matar aure Naseeru? Anya ko kanka ɗaya da zaka rakito gurguwa alhali kana lafiyayye baka da wata Nasaka,duk ƴan matan da ke yawo a gari lafiyayyu idanunka bai gane maka su ba sai musaka? To badani za a yi wannan haɗin ba sam! Ni duk ga zato na waccar itace yarinyar ai.To tun wuri ka rabu musu da ƴar mutane ta samu dai-dai ita ta aura,don bazan taɓa yarda ka auri gurguwa ana zaune ƙalau ba,tun farko ma meyasa baka sanar min da cewa me lalura ka kwaso ba?"
Hajiya Hajara ta jefa masa tambayan idanunta akan Nass wanda tuni zufa ya fara jiƙe rigarsa. Ga wani mashahurin tashin hankali da ya taso masa,iya muzanta yana jin ya gama yinsa a yau agaban su TAIMIYYAH.Wacce tuni itama jikinta ya ɗauki wani irin rawa,idanunta har sun fara fitar da hawaye tsabagen yadda take ji ta gama muzanta. Yasmeen da ranta ya gama ɓaci sai kawai ta miƙe tana kama hannun TAIMIYYAH ta miƙar da ita tsaye.Sannan ta ɗaga idanunta ta sauke akan Mum ɗin Nass da bakinta ya cigaba da faɗin kalamai na rashin ilimi akan TAIMIYYAH.Yasmeen ta soma furta cewa, "Allah ya ƙara lafiya mu zamu tafi,Allah ya huci zuciyarki Mama,TAIMIYYAH ba itace ta ga Naseer tace tana so ba,dama shine ya kawo kansa amma daga yau ta barshi bari na har abada Insha Allah, Allah ya baki suruka lafiyayya wacce ba gurguwa ba itama ƙaddara ce ta mayar da ita haka ba itace ta zaɓi kasancewa a gurguwan ba."