Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 22

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 22

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 22: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,375 words

_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_

*40*

TAIMIYYAH ta sake jingina da jikin bangon corridor ɗin,ta yadda zata iya jiyo maganganun da su Guggo Bilkin ke yi da kyau.Kunnuwanta suka cigaba da jiyo maganan da Guggo Bilki keyi inda take cewa Emran ɗin,

"Emrana ka ga ita ɗin ƴar uwarka ce ta jini,duk wacce zaka je ka auro a waje barin ita TAIMIYYAR ce.Kaine nake ganin duk kafi sauran zurfin tunani da hankali,kuma kaine baka fito da matar aure ba ka tsaya shiririta,Anas ya samu mata haka Ahmad shima magana yai nisa,shiyasa nake ganin kaine ya dace ayi wannan haɗin zumuncin da kai,gadai ta nan ka ganta babu abinda ta rasa kuma nakasanta ba abinda zai kawo cikas bane don ka aureta,don babu abinda bata iya yi da kanta,Zaynab tana da tarin nutsuwa da baiwa masu da yawa da zaka ji daɗin kasancewa da ita.Abbanku kansa yayi na'am shi ya bani ƙwarin guiwan in tinkareka da maganan don aji ta bakinka,ko kuwa ka samu wata ne bamu sani ba?"

Emran wanda ke zaune kusa da Mamien tasu,ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta,cikin tsananin mamakin dukkanin kalamanta ya fara cewa, "Yanzu Mamie don kawai ban fito da mata ba daga zuwan Yarinya sai ki fara irin wannan tunanin,arasa wacce za a ce na aura sai gurguwa,musaka Mamie? Gaskiya bazan iya aurenta ba da dai ace ba gurguwa bace yarinyar ta haɗa duk wasu abu da nake so a jikin mace,amma tunda tazo a gurguwa gaskia Mamie bazan iya aurenta ba,haba abokaina ai dariya zasu yi min,ace duk matan garin nan da sauran wurare in rasa wacce zan aura sai gurguw......"

"Ya isa haka Emrana!" Guggo Bilki ta katsesa cikin fishi me tsanani kafin ta cigaba da faɗin, "A gabana Emrana,a gabana zaka riƙa aibanta ƴar uwarka don kawai tana da nakasa? Miye aibun kasancewarta gurguwa kai me lafiyayyun ƙafafu?Ko kana tunanin ka fita gata ne a wajen Allah da ya barka a yadda ka ke, ita ya jarabceta da zama gurguwan? To shikenan tunda abin naka yazo da iskanci da rashin mutunci abar zancen gaba ɗaya,amma kasani nan da watanni uku kacal ka fito da matar aure,sakarai kawai miskilin banza da wofi, da ina maka kallon wanda yasan abinda yake yi ashe kai ɗin baho ne,duk matar da zaka je ka rakito ɗin ba baki zan maka ba Emrana,amma ba za ka taɓa samun me nagarta da kyakykyawan hali irin TAIMIYYAH ba.Amma ka je kai nazari ka kuma sake fuskantar halayyar TAIMIYYAH tunda ga ta nan tana nan tare damu har nan da zuwa sati ɗaya,idan ka ji kana da ra'ayi zan fi kowa farin ciki tashi ka bani waje."

Guggo Bilki ta kai ƙarshen maganan tana saita masa hanyar fita daga ɗakin.Fuskarta har lokacin a ɗaure yake don maganganun da Emran ɗin yayi ya ɓata ranta. Emran ya zube daga gabanta yana cewa, "Mamie kiyi haƙury na ga ranki ya ɓaci,ina gaya miki gaskiyan abinda ke zuciyata ne amma zan duba inyi tunani kiyi haƙury please...!!"

Iyah abinda TAIMIYYAH ta ji kenan tayi gaggawar juyawa tabar wajen,wani irin yanayi na ɓacin rai da takaici na lulluɓe zuciyarta. Itace yau ake wa wani talla yana gudunta don tana matsayin gurguwa? Wasu hawaye masu tsananin zafi suka cika idanunta,haushi da tsanan Yah Emran ya dira a zuciyarta farat ɗaya.Har ta isa wajen dining ɗin gidan zuciyarta suya yake yi matuƙa,hatta da Guggo Bilki haushinta take ji sosai a ranta,tana ayyana me zaisa tai mata haka?Meyasa zata tallata ma Emran ita har ya samu chance na aibanta nakasanta? Ta kai hannu tana share hawaye masu zafi da suka kwaranyo daga idanunta,bata so sam ta nuna wani alama na cewa taji zancen nasu shiyasa tayi matuƙar ƙoƙari wajen danne zuciyarta.Cike da ƙarfin hali ta zuba abinci kaɗan ta fara ci,sabida yadda yinwa ya dameta kuma bata so ulcer ɗinta ya motsa. Akan idanunta Yah Emran ya fito daga ɗakin Guggo Bilkin, sai dai shi sam bai kula da ita ba,sabida bai kallo sashin dining ba har ya fice daga falon.Ba a ɗauki lokaci ba sai ga Guggo Bilki itama ta fito,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta aje spoon ɗin hannunta,tana ɗaukan cup ta zuba ruwan juice kaɗan ta shanye.

Guggo Bilki ta ƙariso wajen dining ɗin tana cewa,"TAIMIYYAH dama har kun dawo ne shine ban ji motsin ku ba,ina Yasmeen ɗin take ita?"

TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Guggo Bilki,tana ƙirƙiran murmushi a saman face ɗinta, lokacin da take baiwa Guggo Bilki amsa da cewa, "Aiko na dawo bada jimawa ba Guggo Bilki,yinwa ce ta haukatani na yo nan banje na sanar miki mun dawo ba,Yasmeen tana can gidan zuwa anjima zata dawo tace."

Idanun Guggo Bilki akan Lallin da suka zanu a kyawawan yatsun TAIMIYYAH,lokacin da take faɗin, "Shiyasa kice ban ji shigowan naku ba muna ɗaki da Yayanku,aiko Lallin yayi kyau TAIMIYYAH ina fata har a ƙafa akai miki ko?"

TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Aiko su Yasmeen sun matsamin da mita Guggo Bilki hakanan na bada har ƙafafun akayi kin gani ma."

Ta ƙare maganan tana ɗago ƙafanta me lafiyan ta nunawa Guggo Bilki Lallin.Guggo Bilki tabi zanen da yai raɗau a farar ƙafar TAIMIYYAN tana cewa, "Kai Masha Allah,Lalli yayi kyau kam ai sun ƙware sosai indai a iya lalli ne."

TAIMIYYAH ta saki murshi yaƙe kaɗan tana cewa, "Ai nan Kano ƙarshe ne wajen iya Lalli Guggo Bilki,mu Zaria babu ƙwararru sosai gaskiya kaman nan,duk da cewa ba laifi yanzu ana ta samun wanda suka iya amma basu kai nan ɗin ba gaskiya."

TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana miƙewa tsaye,don so take kawai ta jita a ɗaki daurewa kawai take yi wajen kula Guggo Bilkin,amma maganganun Yah Emran ne kawai ke kai kawo cikin zuciyarta. Guggo Bilki ta bi TAIMIYYAH da kallo lokacin da take ƙoƙarin wuce ta xuwa ɗaki TAIMIYYAN na cewa, "Guggo Bilki zan je na huta kaɗan kafin yamma ta ƙarisa yi,wallahi na gaji ne sosai zaman gidan Lallinnan."

"To shikenan TAIMIYYAH a huta lafiya,ai zaman kunshi akwai gajiyarwa shiyasa nima ban damu da yi ba sam." Daga haka TAIMIYYAH tayi wucewarta zuwa ɗaki.Guggo Bilki na bin bayanta da kallo da yanayin tafiyarta,wanda sam ita bata hango aibu a cikinsa da har Emran zai ce wai idan ya auri TAIMIYYAH za ai masa dariya ba,ta jinjina kai kawai kalamansa na sake ɓata zuciyarta.

TAIMIYYAH ko tana shiga ɗakin Yasmeen kwanciya tayi akan gado,ta me lumshe idanunta kalaman Yah Emran na dawo mata inda yake cewa, " _Da dai ace ba gurguwa bace Mamie ta haɗa duk wasu abu da nake so a jikin mace."_

'Kenan shiyasa take yawan kama shi yana satar kallonta?" TAIMIYYAH tayi tunanin hakan cikin xuciyarta,tana sake jin zafin dukkanin kalamansa.Ta lumshe idanunta tana me jin kaman tai tsuntsu ta ganta a gaban Iyah,gaba ɗaya sai taji zaman Kanon ma ya gundureta. Amma sai dai bata son ko Yasmeen taji maganan bare har Guggo Bilki ta gane tai musu laɓe, har ta ji zancen su da Emran ɗin,don haka dole ta daure ta kai iya kwanakin data ambata zata yin. Tana me shan alwashin ko gaisuwa ba zai sake haɗa ta da Emran ɗin ba.Dama haka kawai ita jininta bai haɗu dashi ba, girmansa kansa da miskilancinsa sam bai mata ba.

Ta cigaba da kwanciya tunanika kala-kala na kutsowa cikin kwanyarta.So take yi ta gano ko ita ɗin tana da wani laifine wajen zamantowarta gurguwa? Amma har ta gama tunaninta bata gano hakan ba. Abu ɗaya kawai ta sani shine Allah haka yaso ganinta,kuma babu wanda zai fi ta son ta kasance cikin lafiyayyu marasa nakasa,amma bata da yadda zata yi tunda haka Ubangiji ya jarabceta ya so ta da kasancewa.Kuma tana masa godia tunda ya bata tarin baiwa da ni'imomi, wanda zata iya alfahari da kanta a hakan. Ta kai hannu ta share hawayen dake saukowa daga idanunta, zuciyarta na sake shiga ƙunci a duk sanda ta tuno cewa masu ƙinta duk sabida kasancewarta gurguwace suke gudunta.Ta tuno da irin cin fuskar da Mummyn Nass tai musu a asibiti, wani irin ƙunci ya cigaba da danne zuciyarta har bata san sanda ta sanya kuka ba. Ta cusa kanta a cikin pillow tana kuka sosai har sai da ta gaji don kanta,sannan ta ɗago kai tana share hawayenta.

A kuma dai-dai lokacin Yasmeen ta shigo ɗakin,kallo ɗaya tai wa TAIMIYYAH tayi saurin ƙarisowa cikin ɗakin tana faɗin, "Lafiya TAIMIYYAH kika kunshe ke kaɗai a ɗaki kina kuka,meke faruwa ne?"

TAIMIYYAH tai ƙasa da kanta tana yamutse fuska take faɗin, "Yasmeen kaina ne da cikina ke ciwo,ina ga sabida yadda na wahala a gidan kunshinnan ne banci abinci ba,ni kinsan ciwan kai na ɗaga min hankali dana nemi magani ban gani anan ɗaki shine nayi ta kuka abina."

Baki sake Yasmeen take duban TAIMIYYAH tana jinjina shagwaɓarta.Don ita har ga Allah ta kama da gaske hakan ne,tunda dai tasan babu kowa da zai ɓata ran TAIMIYYAN a gidan, bare ta kawo cewa ko wani abin akai mata.Ta buɗe baki tana faɗin, "Eh! Lallai ke wannan matar shagwaɓarki har ta yi yawa,kawai ki fita kiwa Mamie magana abaki magani shine sai ki wani zo ki kunshe a ɗaki kina kuka,bari inje in samo miki maganin a ɗakin Abbah ki sha." Daga haka Yasmeen ta juya don zuwa ɗakkowa TAIMIYYAH maganin,ita kuma TAIMIYYAH sai ta miƙe dafe da guiwar ƙafarta ta fara takawa ta nufi toilet don wanke face ɗinta,idanunta har yaji-yaji suke sabida kukan data sha.

Lokacin data fito daga toilet ɗin har Yasmeen ta kawo mata magani haɗe da table water ta aje akan bedside. Hakan yasa TAIMIYYAH zama daga bakin gadon, tana ɗaukan paracetamol ɗin ta ɓalli guda biyu ta kai baki tana korawa da ruwan ta shaye.Ta aje goran ruwan tana cewa, "Yasmeen gobe kuma me zaku yi,hala dai Angon ustaz ne shiyasa ban ji kince za a yi wani bidi'a a bikin ba?" Yasmeen ta murmusa lokacin da take aje wayarta akan madubi.Ta juyo tana fuskantar TAIMIYYAH sosai kafin ta fara faɗin, "Aiko dai babu abinda za su yi daya wuce walima gobe da ƙarfe huɗu za a tafi MIEMAH a can za a yi walimar.Ina fata dai zaki mana tunda walimace dai a ci a tashi ba wani abu za a yi ba."

TAIMIYYAH ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, "See ur mouth like kece walimar,to bari mu gani kila in je kila kuma ba za ni ba,nifa ban son shiga mutanene kema kin sani."

"Sai aljanu kike son shiga ko?" Cewan Yasmeen tana ballawa TAIMIYYAH harara. TAIMIYYAH bata san lokacin data kwashe da dariya tana cewa, "Ki rifa min asiri da jinnu,Allah yai mana tsari dasu abar zancen zani Insha Allah shikenan ko?"

Wani hararan Yasmeen ta sake aika mata tana faɗin, "Eh shikenan kin tsira tunda kin miƙa wuya za ki ɗin." Daga haka suka dasa hiran bikin har aka kira sallah kowacce ta ɗauro alwala don bada faralinta.

Da daddare ƙememe TAIMIYYAH taƙi fita falo zaman hira yadda suka saba zama dasu Yah Anas.Abincin ma nan ɗaki tasa Yasmeen ta kawo musu suka ci tare. Guggo Bilki data shigo tana tambayan dalilin da zasu ƙi fitowa falo,sai Yasmeen ta bata amsa da cewa TAIMIYYAH ce bata jin daɗi,amma ta sha magani,sai Guggo Bilkin tai mata sannu tana juyawa ta bar ɗakin.

Washegari ƙarfe huɗu da rabi su TAIMIYYAH suka isa wajen walimar. TAIMIYYAH ta gama haɗuwa cikin wani ubansun Abaya kalar Dark Gray da yaji adon zane da cream colour. Duk inda ta wulga ƙyalli take yi cikin kayan,fuskarta babu kwalliya komi amma tayi mugun kyau. Tana ji mutane da yawa na gulmar kyawunta a wajen,suna kuma tsegumi akan kasancewarta gurguwa.Shiyasa tunda ta samu waje ta zauna bata kuma motsawa ba har aka tashi daga walimar.

Lokacin da suka iso gida ana ta kiran sallar magriba.Suna sanyo kansu cikin gidan kenan sukai arba dasu Yah Anas zasu fita zuwa masallaci. TAIMIYYAH ta ja baya don basu hanya lokacin da Yah Anas ke faɗin, "Wow! Kin ga yadda kika zama wata balarabiya kuwa Sis,gaskiya shigar Abaya tana miki kyau Sister." TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin, "Kai Yah Anas banda ziga fa."

Anas ya saki dariya yana cewa, "Ba wani ziga fa,da gaske shigar yai miki kyau TAIMIYYAH."

TAIMIYYAH ta ɗago face don yiwa Anas magana, sai idanunta suka shige cikin na Yah Emran da yai tsaye yana faman ƙare mata kallo. Tayi saurin fara takawa don barin wajen tana cewa Anas , "Thank u Yah Anas sai kun dawo."

Tuni Anas yayi gaba abinsa ba tare da TAIMIYYAN ta sani ba. Emran daya tsaya kaman wanda aka dasa.Yabi bayanta da wani irin kallon ƙurilla yana sake jinjina baiwar kyawu da Allah yayi wa TAIMIYYAN. amma

Sai dai kasancewarta gurguwa yasa yake jin bazai taɓa iya bata zuciyarsa ba.Wani tunani ne ya haska cikin kwanyarsa sai ya juya da sassarfa don fita daga gidan, jin za a tada sallah a masallacin dake kusa dasu inda suke sallah anan.

TAIMIYYAH dai bata san ma yana yi ba,don ita haushin kallonta da ya tsaya yine ma ya kamata.Ta dinga mita a zuciyarta ita kaɗai akan me zaisa ya tasata da kallo haka kaman wani ɗan iska.

A fili ta furta, "Mutum sai shegen girman kai da baƙin hali,ga shegen kallon matan tsiya kaman maye." Ƙasa-ƙasa tai maganan iya kunnuwanta,shiyasa Yasmeen da ke gefe tana cire Abayar jikinta sam bata ji me TAIMIYYAN ta faɗi ba.

Yau ɗinma da lokacin yin Dinner yayi TAIMIYYAH ƙin fita tayi.Sai ta fake da cewa Yasmeen zata ɗan yi tilawa ne sai zuwa can anjima zata ci abincin. Hakanan Yasmeen ta fita ta bar TAIMIYYAN a ɗaki wacce ta ɗakko Qur'ani ta fara karantawa.Bata bar karatun ba har sai da Yasmeen ta shigo hannunta riƙe da ledan gasasshen nama ta ajewa TAIMIYYAH tana cewa, "Gashinan inji Yah Anas kuma Guggo Bilki tace kiyi maza ki bar karatun haka ki fito kici abinci,don ta kula da gangar kike ƙin fita falo yanzu."

TAIMIYYAH sai ta aje Qur'anin tana duban Yasmeen take faɗin, "To sarkin karaɗi ai dama yanzu zan fita ɗin don na fara jin yinwa,ɗakko naman muje dashi can ɗin sai muci kilama shi kawai zan ci in sha madara ya wadaceni."

Yasmeen ta saki dariya tana cewa,"Ai nan kika fi kauri dama, kwaɗayi da son cin nama kamar wata kura,duk Iyah ce ta sangartaki haka wallahi,yarinya sai shagwaɓa kamar wata babyn goye."

TAIMIYYAH ta juya ta bankawa Yasmeen harara tana faɗin, "Na dai ji wani ma ya koyi shagwaɓar idan zai iya mana." Daga haka suka jera da juna zuwa falon.Sun samu babu kowa su Yah Anas ɗin sun kama gabansu zuwa part ɗinsu. Guggo Bilki kuma da alamu tana ɓangaren Abbah,sai kawai su TAIMIYYAH suka baje naman suna ci a tsakiyar falon saman carfet. Yasmeen ce ta ɗakko musu kwalin Hollandia milk cikin fridge ta haɗo da cup suka zuba madaran suna korawa da shi,suna cin gasasshen naman da yaji kayan haɗi sai qamshi kawai ke tashi. Koda suka kammala TAIMIYYAH ta riga Yasmeen isa ɗaki don kwanciya bacci,ita Yasmeen ta tsaya kallo sai wajen 11:30pm ta shigo lokacin tuni TAIMIYYAH ta jima da yin bacci.

Washegari ya kama ɗaurin aure da yini baki ɗaya.Duk iya yadda Guggo Bilki ta matsama TAIMIYYAH akan ta tashi ta shirya su fita zuwa gidan bikin tare amma ta ƙi,dama ita Yasmeen tun safe ta bar gidan bayan ta tashi TAIMIYTAH su wuce tare taƙi tashi.

Hakanan Guggo Bilki ta fice zuwa gidan bikin ita kaɗai.Sai ta bar TAIMIYYAH da masu aiki dake can baya suna hidimansu. Ita kam TAIMIYYAH ko ajikinta ta gwammaci tayi zamanta ita ɗaya, data je gidan biki ta shiga taron jama'a daga me cewa Allah sarki dubi gurguwa sai masu yaba kyawunta. Ko wanka bata tashi yi ba sai wajen 12 na rana.Gidan yai tsit babu kowa don har mazan duk suna wajen reception tunda ɗaurin auren sha ɗaya na safe ne,shiyasa babu motsin kowa sai su Ramma masu aiki kuma duk suna ta can baya.

Lokacin da TAIMIYYAH ta fito wanka tana ɗaure ne da towel da tsayinsa ya zarce guiwanta.Ta nufi wajen madubi tana jan stool ta zauna don fara shafa mai.

Tana tsaka da shafa man aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.Sam ita bata damu ba ta cigaba da shafanta tana cewa, "Yasmeen kin dawo ɗaukan wani abu hal....."

Maganan ta ya katse ne a lokacin da idanunta suka bango mata wanda ke tsaye daga bakin ƙofa ta cikin mirrow.

Yah Emran ne ta hango tsaye ya zubo mata manyan idanunsa yana kallonta babu ko ƙiftawa.

TAIMIYYAH take ta ji wani matsanancin faɗuwar gaba da takaicin yadda ya risketa babu kaya ajikinta.Ta rintse idanunta tana rasa ma me zata yi,ita dai ba zata iya tashi a haka ta nufi wajen da Hijaban sallansu yake ba.Sai ta gwammace ta cigaba da zama a hakan tunda a zaune take da a ce ta tashi neman abun rufa ya ganta daga ita sai towel. Ta buɗe idanunta a lokacin da ya gama sanyo kansa cikin ɗakin tare da maida ƙofan ya rufe.Ya murza key yana zaresa daga jikin ƙofar ya cilla a aljihun dakakkiyar farar shaddar gezner dake jikinsa.

Ganin hakan yasa TAIMIYYAH dubansa a firgice tana faɗin, "Lafiya Yah Emran zaka shigo ɗaki babu neman izini,baka ga a halin daka sameni bane? Please ka fita ka bani waje zan shirya tunda kai ba muharramina bane."

Yadda TAIMIYYAH take magana cike da zallar ɓacin rai,jikinta har wani rawa yake na tsananin tsoro yasa Emran sakin wani makirin murmushi. Idanunsa na cigaba da bin jikinta da wani mayen kallo.A hankali ya fara takowa zuwa inda take zaune ba tare da ya bi umurninta na fita daga ɗakin ya bata waje ba.Ganin yana tahowa wajenta ne ya sake jefa zuciyar TAIMIYYAH cikin matsanancin fargaba da tsoro.Ta kai hannuwanta duka biyu tana sarƙesu a ƙirjinta tare da maida idanunta ta rintse,tana nanata kalmar Innalillahi daga farkonsa har ƙarshe.........✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:10 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*

*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_

*41*

Emran ya cigaba da takawa zuwa wajen da TAIMIYYAH ke zaune idanunsa akanta,ya tsaya daga bayanta yana kai hannuwansa duka ya dafa kafaɗunta.

Jikin TAIMIYYAH ba inda baya rawa lokacin da ta ji saukan hannuwansa a kafaɗunta. Tayi saurin buɗe ido tana kallonsa ta jikin mirrow ɗin, jikinta na rawa hawaye na fara wanke fuskarta. Emran shi kuma ya juyo da ita gaba ɗaya suna fuskantar juna.TAIMIYYAH ta ware idanunta tana magana cikin rawar murya tace, "Yah Emran please miye hakan kake yi,don girman Allah ka fita ka bani waje,baka ga babu kaya a jikina bane daga ni sai towel,ko kai bakasan haramcin yin hakan bane?"

Yadda take magana cikin nuna zallan fusata yasa Emran kai hannu ya bige bakinta da ƙarfi.TAIMIYYAH ta saki kuka tana ture hannunsa daga jikinta,ta yinƙura don ɗakko Hijab ko wani abu ta suturta jikinta da shi,sai dai tana ƙoƙarin tashi daga kan stool ɗin Emran ya kai hannu ya ɗagota gaba ɗayanta zuwa jikinsa. Kafin tayi wani yinƙuri ya kai bakinsa bisa kunninta yana faɗin, "Ashe baki da kunya ni kike wa tsawa haka? To bari in tabbatar miki da cewa bani da ilimin sanin haramcin." Yadda yayi maganan yana ƙoƙarin kai ɗaya hannunsa kan towel ɗin dake ɗaure a ƙirjinta yasa TAIMIYYAH buɗe baki zata saki ihu...Kamar yasan shirinta kawai sai ya kai bakinsa ya rufe bakinta ruf! Take bugun numfashin TAIMIYYAH ya tsaya cak! Jikinta ya ɗauki wani irin rawa.Hakan yasa Emram ɗagata gaba ɗayanta ya kai kan gado,har lokacin bakinsa na manne da nata, ƙamshinsa na turaren SAUVAGE DIOR gaba ɗaya ya gama buɗe hancin TAIMIYYAH. Ta kai hannu ta fara dukan ƙirjinsa da yai mata rumfa da iyakan ƙarfinta,amma Emran bai yi ko gezau ba har sai da yayi nasaran tura harshensa cikin bakinta,cikin sa a TAIMIYYAH ta samu ta gantsara masa cizon daya sa shi sakinta babu shiri.

Tayi wani irin hantsalawa gefe guda tana damƙo zanin gadon dake shinfiɗe ta rufe jikinta,wani matsanancin kuka na ƙwace mata har lokacin jikinta rawa yake kaman mazari.

Emran da yai tsaye yana bin ta da kallo, zafin cizon da taiwa harshensa na ratsa shi,sai ya saki ƙwafa yana binta kan gadon baki ɗaya ,ya damƙota ita da zanen gadon data cimimiye jikinta da shi. Ya fara ƙoƙarin zaro ta daga cikin zanin gadon yana cewa, "Allah yau tunda kika cijeni sai na nuna miki cewa ni ɗin ba kanwar lasa bane."

Cikin kuka TAIMIYYAH ke masa magiyan yayi haƙuri ya barta amma ina...! Sam bai saurareta ba sai da yayi nasaran rabata da zanin gadon da ya zama sutura a gareta. Ganin towel ɗin dake ɗaure a jikinta na son kwancewa, yasa TAIMIYYAH kai hannu ta damƙesa tana sakin kuka me sauti,dukkanin jikinta na sake ɗaukan rawa, zuciyarta tamkar ta fashe sabida baƙin cikin wannan tozarci da Yah Emran ke shirin aikata mata.

Hannunsa ya kai yana kamo siririn ƙafarta mara lafiyan ya riƙe a hannunsa, yana kallon yadda zanen jan Lallin da akai mata ya zauna a farar ƙafartata.Ya cigaba da bin ko'ina na jikinta da kallo sha'awanta na sake fisgar zuciyarsa,musamman da yaji yadda jikinta ke da wani irin laushi. Cikin disasshiyar murya yake faɗin, "Zaynab kina da kyau da diri daya kamata ace na mallakeki,sabida kin mallaki duk abinda nake so a jikin mace,cikas ɗaya ne zai hanani amincewa da ƙudirin Mamie wannan laluran ƙafar daya mayar dake gurguwa.Ba don hakan ba da gudu zan amince na aureki ko don in more albarkatun jikinnan naki da kyau,amma ko a yanzu bazan iya barinki ban ɗanɗana koda kaɗan bane naji yadda daɗinki yake ko Babe?"

Yana maganan ne duka hannunsa na yawo a jikin TAIMIYYAH,wacce ke faman rasgar kuka jikinta na cigaba da ɗaukan rawa ,kaman wacce zazzaɓi ke shirin kamawa. Kalaman Emran suka haɗu da tsananin ƙunan da zuciyarta ke yi suna neman tsaida gudun numfashinta. Ta saki wani gigitaccen ihu a lokacin da taji ya fisge towel ɗin jikinta yayi jifa da shi.

Emran ya kai hannu ya danne bakinta yana ƙoƙarin haɗata da jikinsa ,amma hannun da TAIMIYYAH tasa ta kai mishi wani nushi a ciki yasa shi sakinta babu shiri,yana me ɗauketa da wani gigitaccen mari da hannu ɗaya.Wanda ko kaɗan TAIMIYYAH bata ji zafin marin ba, ta yinƙura tai wani irin tsalle sai gata a bakin toilet. Jikinta na wani irin kakkarwa ta buɗe ƙofan ta shige tana murza key.Dai-dai lokacin da Emran da ke dafe da cikinsa ya ƙariso wajen yana cizon yatsa. Har lokacin hannunsa ɗaya dafe yake da cikinsa,don bada wasa naushin ya shigesa ba,wanda ya haifar masa da ɗaurewar mararsa a lokaci ɗaya.

Yana jiyo kukan da TAIMIYYAH ta saki daga cikin toilet ɗin,ya juya yana takawa a hankali ya isa bakin ƙofa. Da hannu ɗaya ya yi anfani wajen ciro key ɗin dake aljihunsa ya buɗe ɗakin ya fice.Zuciyarsa na cike da ɓacin rai da jin zafin yadda bai samu nasara akan TAIMIYYAN ba. Yaso koda kaɗan ne ya murji jikinta koya rage zafi koda ace bai shigeta ba,sai gashi ta shammacesa da wannan nushin ta kufce masa. Ya cije lips ɗinsa yana girgiza kai cike da takaici,har ya fice daga falon hannunsa ɗaya na riƙe da cikinsa, ya nufi ƙofan fita daga sashin baki ɗaya zuwa nasu part ɗin.

TAIMIYYAH dake cikin bayi tana rasgar kuka tana jin lokacin daya fice daga ɗakin.Hakan yasa ta fitowa da hanzari ta nufi ƙofar ɗakin ta kulle tana me barin key ɗin a jikin ƙofar. Kuka take yi sosai jikinta kuma bai daina ɓari ba,ta faɗa kan gadon Yasmeen tana sake rushewa da wani sabon kukan.Bata taɓa tunanin Yah Emran ɗin tantitin ɗan iska bane sai yau da yake ƙoƙarin tazartata,duk don kasancewarta gurguwa da yake ganin zai iya cin banza akanta. Hankalinta taji ya yi mummunan tashi, gaba ɗaya sai taji hankalinta ya koma gida,zaman Kanon ya isheta hakanan,ba kuma taji zata iya wuce gobe bata ganta a gaban Iyah ba.

Ta share fiye da mintuna talatin tana rasgar kuka kaman ranta zai fita. Da ƙyar ta iya tashi tana layi dafe da ƙafarta me laluran ta nufi toilet tana me sakarwa kanta shower,ruwa me sanyi na ratsa tsakiyan kanta yana gangara a jikinta.

Ta jima a durkushe ruwan na jiƙe dukkanin jikinta,kafin ta ɗauro wani towel ɗin ta fito daga bayin,jikinta na ɗaukan wani sabon rawar kamun zazzaɓi. Ta isa wajen kayanta ta zaro wata riga mara nauyi ta saka, ko bra da pant bata tsaya sakawa ba ta naɗe akan gado tana sake ɓallewa da kuka. Nan da nan jikinta ya ɗauki matsananci zafi kanta na wani irin ciwo.Ta janyo wayarta da ƙyar tana kiran layin Yameen,bugu biyu Yasmeen ta ɗauka. Da ƙyar TAIMIYYAH ta iya ce mata, "Yasmeen don Allah ki dawo gida banda lafiya." Daga haka tayi jifa da wayar ba tare da ta tsaya kashewa ba,sai Yasmeen ce tayi hanging up daga ɓangarenta.

Ta dubi ƙawayensu da suka cika ɗakin da suke zaune ta miƙe tana cewa, "Friends ku bani awa ɗaya zan je gida na dawo TAIMIYYAH ce bata jin daɗi Firdausy."

Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana duban Feedoh,kafin ta ɗauki mayafinta don fita lokacin da Feedoh ke cewa, "Ayyah..! Ki gaisheta please, zuwa anjima zan zo nima idan muka gama da jama'a,Allah ya bata lafiya."

Yasmeen ta amsa da "Ameen." Tana saurin ficewa daga ɗakin ta nufi waje,lokacin data fito daga gidan Baba Lawal sai taci mugun sa a wani mai adaidaita ya sauke wata,kawai sai ta shige tana sanar masa cewa can layin zai zagaya da ita.

Readers Also Read