Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 31

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 31

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 31: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,465 words

Maleek Ado ne zaune daga cikin falon Hajjah,isowar sa garin kenan ko mintuna goma bai yi ba.

Daga gefensa Hajjah ce zaune tana amsa call, shi kuma yayi zaman dirshan a gabanta. Lokacin da ta kammala amsa wayar ne ta sauke idanunta akan Maleek ɗin tana cewa, "Abdulmaleek lafiya dai na ga baka da walwala ko duk gajiya ce?"

A.Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah yana sake ɓata fuska,ya buɗe baki kaman me yin raɗa yana cewa, "Wallahi Hajjah na gaji ne, satinnan gaba ɗaya har ya ƙare ban samu wani isasshen hutu ba,ai dai ta tayamu da addu'a amma wannan muƙami da aka bani ji nake tamkar in ajesa,gaba ɗaya harka da ƴan kudu akwai haɗari, an sanya min ido sosai a wajen Hajjah."

Yadda yayi maganar cike da rauni yasa Hajjah dubansa da fuskar tausayi tana cewa, "Kayi haƙury Maleek shi ɗaukaka ya gaji haka,duk wanda Ubangiji yai wa wata baiwa ko ɗaukaka to fa kullum rayuwarsa na cikin jarabawane kala-kala,matuƙar akwai imani a zuciyarsa.Don haka kayi haƙury ka daina zancen cewa kamar a amshe muƙamin daga gareka,hakan tamkar butulcewa Ubangijin da ya baka ne.Addu'a kuma kullum cikinsa muke ba dare ba rana,muna kuma da yaƙinin Allah na jinmu kuma zai amsa mana,babu abinda zai faru zaka rabu da su lafiya da izinin Ubangiji,yanzu dai ga abinci can an shirya maka a dining idan kaci sai ka huta da kyau,don ina da wata muhimmiyar magana da nake so mu tattauna da kai,shiyasa kaga na ƙagu ka zo garin don mu tattauna gani ga gaka."

Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan tilon ɗan nata Maleek Ado,wanda ya wani sake shagwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro.

Cikin muryansa me cike da ƙasaita yake faɗin, "To Hajjah bari inci abincin amma a kira Lubah tazo ta sauko su nan ƙasa bazan hau dining ba."

Hajjah ta ciri murya ta kira Lubah don ta zo tai masa duk yadda yake so ɗin.Cikin ƙanƙanin lokaci Lubah ta iso cikin falon ta zube a gaban Maleek ta kwashi gaisuwa,hannu kawai ya ɗaga mata alamun ya amsa, sannan ta tashi ta fara ɗakko kulolin abincin ta jeresu nan tsakiyar carfet.

Tana kammalawa ta wuce ta basu waje,yayi saura daga Hajjah sai shi a cikin falon. Da kansa ya zuzzuba abinda yayi masa cikin abinci kala uku da aka shirya masa. Hajjah ta miƙe tana dubansa tace, "Ai ɗazu mun yi waya da Suhailah tana so ka wuce muku da garin kunu idan zaka juya,Allah yasa jiya Babah Rabi ta kammala tankaɗesa ya yini a rana, tunda anci sa a anyi ban iska ba ai ruwa ba."

Maleek ya dubi Hajjah kawai ba tare da yace komi ba har Hajjan ta shige ɗaki.Ya cigaba da cin abincinsa lokaci-lokaci ya kan amsa kiran da ke shigowa wayarsa, a haka har ya ƙare cin abincin ,ya tashi daga wajen ya koma kan seater ya zauna.

Lokacin da Hajjah ta fito daga ɗaki samun sa tayi yana ta faman amsa waya da harshen Nasara. Ta ƙariso tana zama cikin seatern da ke facing ɗinsa, hankalinta na kan TV da ke ta faman aiki cikin falon,har ya kammala amsa call ɗin yana sauke ganinsa akan Hajjan yake cewa, "Hajjah ina so a sake yin garin ɗan-wakennan wanda akai mana yayi daɗi sosai,sai dai kinsan Suhailah da kyuiyan yinsa ina ga shiyasa bata sanar miki ya ƙare ba ko?"

Hajjah ta dubesa da murmushi saman fuskarta tace, "Aiko bata faɗi ba amma tunda sai zuwa jibi zaka wuce za a yi Insha Allah."

Maleek ya jinjina kai yana faɗin, "Okey Hajjah thank u,Allah ƙara muku tsawancin kwana me anfani."

"Ameen Maleek ku ma Allah ya cigaba da yiwa rayuwarku albarka ya kawo zuriya masu albarka."

Maleek ya amsa da cewa, "Ameen."

Hajjah ta kirayi sunansa kai tsaye kafin ta sake zama so serious tana cewa, "Abdulmaleek ina buƙatar dukkanin nutsuwarka anan,don abinda zan sanar da kai yana da matuƙar muhimmanci a wajena."

Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah,yana ganin yadda taci serious yasan lallai duk abinda take so su tattauna me muhimmanci ne kamar yadda ta faɗi.Sai ya nutsu sosai tare da maida dukkanin hankalinsa kanta yana cewa, "Ina jinki Hajjah Bismillah."

Hajjah ta jinjina kai tana me farawa da bashi labari tun daga kan kaɗe TAIMIYYAH da sukai da mota, har kawo aminci da zumuntar da ya shiga tsakaninta da su.Ta ƙare maganan da cewa, "Maleek ba wani abu nake so ba illah kai min alfarma ka je ka ga Zainab TAIMIYYAH,idan har ka ji tayi maka zaka iya zama da ita a matsayin mata,zan so ka nemi aurenta.Wannan shi kaɗai ne ƙarshen alfarman da nake ji zaka sake min arayuwa ka faranta zuciyata har in cigaba da alfahari da samun ɗa kamarka.Kai kaɗai na mallaka a duniya da zan iya iko da kai in kuma roƙi alfarma kayi min ba tare da raina ya ɓaci ba,na so a ce Ubangiji ya bani wani ɗan wanda bai taɓa aure ba don in saka shi ya aure ta amma Allah kai kaɗai ya mallaka min."

Hajjah ta ɗan dakata kaɗan tana duban fuskar Maleek Ado, wanda ya zuba mata ido yana sauraren dukkanin kamalamanta. Sai Hajjah ta kasa gane wani yanayi yake ciki, don shi yana cikin irin mutanen da suka iya riƙe kansu,duk iya yadda zance zai girgiza zuciyarsa zai yi wuya ka gane hakan akan fuskarsa.Hakan yasa Hajjah cigaba da cewa, "Maleek TAIMIYYAH gurguwace kuma marainiya da ta rasa uwa da uba,amma ta mallaki tarin abubuwan da duk namijin da yasan kansa zai yi alfahari da samunta a matsayin matar aurensa,Mahaddaciya Qur'anice me tarin nutsuwa da hankali,wacce ta samu tarbiyyah me kyau daga kakarta na wajen uba,wacce ta raineta tun tana taumman goyo,don haka ina so a gobe ka wanke ƙafa ka je ka ganta,dukkanin abinda zuciyarka ta yanke akanta ka zo ka sameni ka sanar dani."

Maleek da ke sauraren Hajjah yana dinga nanata kalmar gurguwa cikin kwanyansa kafin ya ɗaga manyan idanunsa yana kallon fuskar Hajjar,Yayi karfin halin fara faɗin, "Shikenan Hajjah zan yi duk yadda kika ce, amma Hajjah wannan karon kuma da gurguwa kika ga na dace?"

Hajjah ta dubi Maleek cikin ido, tana hango ruɗanin da kamalamanta suka jefa zuciyarsa a ciki.Ƙarfin hali kawai yayi wajen amsa mata buƙatarta ba tareda yayi mata musu ba,don abune da bai taɓa yi ba bata taɓa sanya kara ya tsallake ba,shi ɗin me tarin biyayyane akan dukkanin abinda ta nuna tana so.

Ta jinjina kai tana cewa, "Maleek karka bari kalmar gurguwa ya jefa wani abu a cikin zuciyarka,don kai da ita duka a wajen Ubangiji ɗaya kuke,bai jarabeta da zama gurguwa don baya ƙaunarta ba,kamar yadda kai da kake lafiyayye ba zaɓinka bane,shine ya so ka kasance a haka,don haka abinda za ka fara dubawa da tambayata shine, 'me ya ja hankalina akanta har nake sha'awar haɗa jini da ita? Wannan amsar kuma kai ne zaka baiwa kanka ita, bayan ka je kun yi ido biyu da TAIMIYYAH.

Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan Maleek, tana jifansa da wani irin murmushi.Ya lumshe idanunsa yana jin wani abu na dokawa a cikin kansa,kalmar gurguwa da suna TAIMIYYAH na amsa-kuwwa cikin kwanyansa da ƙarfin gaske.

Ya buɗe idanun nasa yana sauke su akan Hajjah,cikin son ɓoye dukkanin ruɗanin da ya shiga yake cewa, "Shikenan Hajjah za a yi yadda kika ce,a kullum mu masu biyayyah ne akan duk abinda kuke so."

"Allah yayi maka albarka Maleek,Allah kuma ya baku zuriyar da zasu bi ku kamar yadda ku ke min biyayyah,ban yi maka tayin zuwa ka ga TAIMIYYAH don in tirsasaka aurenta akan dole ba,duk abinda ka ji a zuciyarka idan ka haɗu da ita ka sanar dani Maleek,kuma ina so ka je a matsayin kaine ka kai kanka gareta,sam bana so su san ina da alaƙa da kai har sai ka ji cewa tayi maka,kuma idan ka tashi zuwa kada ka je a motar da zai nuna matsayinka,ina fata ka gane duk yanda nake nufi?"

Maleek ya jinjina kai cike da gamsuwa yake cewa, "Na gane Hajjah,bari in shiga daga ɗaya bedroom ɗin in kwanta ina buƙatan hutu zuwa la'asar."

Daga haka ya wuce Hajjah zuwa ɗaya ɗakinta wanda Suhailah ta zauna lokacin tana gida....✍🏻

#Ɗansabo ce#

#Ɗansabo ce"[12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*54*

Kwanciya yayi tare da lumshe manyan idanunsa,maganganun Hajjah na dawo masa daki-daki.Ko kaɗan baccin da yayi tunanin zai iya yi bai samu yi ba,sai ma tarin tunani da suka dabaibaye kwanyarsa.

Haka ya cigaba da kwanciya time to time ya kan amsa call ɗin da ya ga zai iya ɗagawa,a haka lokaci ya ja ƙwaƙwalwarsa na cike da tarin tunanin yadda zai fuskanci gobe. Bayan ya dawo daga masallaci sallar la'asar ne yayi wa Hajjah sallama, akan zai je wajen wani aminin mahaifinsa ya gaishe shi,daga can kuma zai wuce gidansu na GRA a can zai kwana.

Hajjah tayi masa fatan Allah tsare tare da jaddada masa maganar zuwa Gyallesu a goben,kamar yadda ta roƙi alfarma ya kuma amsa mata.

___________

TAIMIYYAH da Iyah ne a zaune suna hiran su cikin falon Iyan,daga gefe ɗaya Babah Ladi ce ta maida hankali kan kallon wa'azin da ake haskawa a tashar ManaraTV.

TAIMIYYAH na sanyene cikin wata free gown na atamfar Chiganvy Gold,kalar atamfar red and black ne da ya yi matuƙar yi mata kyau tare da haske farar fatarta.Sallamar Zuhurah da shigowarta cikin falon Iyah,ya sanya TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Zuhran,wacce taci uban ado kamar zata biki. Fuskarnan ya sha make-up ,kamar yadda kayan jikin natasuka fidda shape ɗinta sosai a waje,ta ƙariso cikin falon tana gaida Iyah daga tsaye.

Iyah ta dubeta tana amsa gaisuwan a dake,Zuhurah ta ɗaura da faɗin, "Iyah dama Ameeru ne zai shigo ku gaisa yanzu."

Iyah ta dubi Zuhurah cikin ido kafin ta furta, "To madallah." Daga haka bata sake cewa komi ba har Zuhurah ta juya ta fice,ba tare da tace wa TAIMIYYAH kanzil ba.

Tsam TAIMIYYAH ta miƙe tana ɗaukar wayarta don shigewa ɗaki,amma sai Iyah ta dakatar da ita tana cewa, "Koma kiyi zamanki Zainab,kema ke gansa ku gaisa ai."

TAIMIYYAH ta buɗe baki cike da shagwaɓa tace, "Kai Iyah nina ce miki ina son ganinsa? Ni dai da kin barni na yi shigewata ɗaki."

Kafin Iyah tace komi sallamar su Zuhurah ya karaɗe bakin ƙofar shigowa falon,hakan yasa TAIMIYYAH sake ɓata face.Iyah ta amsa sallamar tana basu umurunin shigowa cikin falon,suka shigo Zuhurah na kan gaba Ameerun na biye da bayanta.

Ya zube ya kwashi gaisuwa wajen Iyah wacce take binsa da kallo tun shigowanrsu. Ta amsa gaisuwar Ameeru cike da fara'a, tana tambayarsa iyayen nasa,ya amsawa Iyah idanunsa a kan TAIMIYYAH dake zaune cikin kujeran dake facing ɗinsa.

TAIMIYYAH ta buɗe baki ta gaida shi cikin sanyin muryarta,ya amsa yana sake binta da wani irin kallo na ƙurillah.Hakan yasa ranta ya sake ɓaci da hanata tafiya da Iyah tayi,Iyah ta sanya Babah Ladi ta kawo masa lemu amma sai ya miƙe yana cewa tafiya zai yi.

Hakan yasa Iyah yi masa fatan alkhairy,ya isa wajen da take zaune ya aje mata kuɗi masu yawa,duk kuma yadda Iyah tayi da shi akan ya ɗauke kuɗinsa ƙi yayi. Hakanan Iyah tayi masa godia da sanya albarka,suka fice Zuhurah na biye da bayansa kamar jela.

Suna fita TAIMIYYAH ta miƙe tayi shigewarta ɗaki,don bata ma so Iyah ta ɗakko wani zance akan Ameerun, wanda ita kallon farko da tayi masa sam bai kwanta mata ba.Bata kuma hango dacewarsa da ƴar uwar nata ba sam,amma sai tayi musu fatan alkhairy cikin zuciyarta,tare da addu'an Allah yayi mata zaɓi itama mafi alkhairy cikin nata rayuwar.

Har suka zauna cin abincin dare TAIMIYYAH taƙi tanka Iyah akan zancen Ameeru,wanda Iyah ke ta faman mitan ita dai yaron yai mata kama da irin mazannan marasa kamun kai.TAIMIYYAH sai tayi murmushi kawai tana cewa Iyah, "Ke dai Iyah kiyi fatan alkhairy kawai tunda dai an riga an sanya lokaci,kuma ita shi ta ga yayi mata,shi take so kin ga kenan koma ya yake tana son kayanta."

"Hakane kuma Zainabu,miye nawa a ciki yaran da basa ganin ƙimarka da darajarka a matsayin wacce ta kawo ubansu duniya,ai sai suyi tayi Allah bada sa a ya sanya alkhairy."

TAIMIYYAH tayi saurin amsawa da, "Ameen." Tana ɗaurawa da faɗin, "Iyah ya maganar xuwa gidan Mamar Gonan Ganyen?"

Iyah tayi saurin duban TAIMIYYAH tana cewa, "Oh! Ni Iyah wallahi kaman kinsan abinda nake ta tunani a raina kenan,ina ga za mu zuwa sati me xuwa Insha Allah,so nake yi ki ɗan yi ko irin cake ɗinnan na ƴan takaddu da Doughnut ɗinnan me laushi sai akai mata ko baƙi ta dinga ba."

TAIMIYYAH ta jinjina kai tace, "To shikenan Iyah Allah shi kaimu lafiya,sai ayi mata ai tunda weekend ne za mu Insha Allah."

Daga haka suka cigaba da hira da Iyah,har sai da agogo ya buga ƙarfe tara sannan TAIMIYYAH tayi wa Iyah sai da safe,ta shige zuwa ɗakinta.

Bata kwanta ba sai da ta gama karanta sabon novel ɗin da ta siya me suna NAHUCE,na Sumayyah Abdulƙadir Takory, (Gwanata kenan a kaf marubuta littafan Hausa,Allah ya ƙara ɗaukaka Anty Takory).

Bayan ta kammala ne ta miƙe ta ɗauro alwala ta zo ta kwanta,tana jin wani irin shauƙi na kewaye zuciyarta,bata jima da kwanciya ba bacci ya saceta ba tare da ɓata lokaci ba.

___________

*GRA,Zaria.* *09:48am*

Maleek Ado ne zaune cikin falonsa na ƙasa yana karin kumallon safe,wanda Hajjah ce ta shiryo abincin Shehu ya kawo masa.

Yana cin abincin ne suna vid call da Suhailah,wacce ke ta faman narke masa wai bata da lafiya,ta tashi da zazzaɓi ne gashi tace masa bata ma sha magani ba.

"Please wife ya isa haka kukan,ki tashi ki sha magani idan bai yi ba,ki wuce asibiti da driver kin ji ko?"

A.Maleek yayi maganar idanunsa akan face ɗin Suhailah,ta sake zararo hawaye lokacin da ta yaye duvet ɗin da ta rufe jikinta dashi.Take kuma fingilwan rigar da ke jikinta ya bayyana,hakan yasa Maleek sake manna idanunsa bisa allon screen ɗin wayarsa,yana kallon yadda ƙirjinta ya bayyana sosai a waje.Yayi magana cikin low voice yana cewa, "Baby kina son sani a damuwa ne ko? Bayan kinsan a matse na taho nan ɗin,kin yi tsarki ne?"

Suhailah dake duban face ɗin Maleek ta share hawayen da ke zuba,tana gyaɗa masa kai tace, "Yes my Maleek ɗazu na yi wanka,goben za ka dawo ko sai jibin?"

Maleek ya ɗan lumshe idanunsa sabida yadda Suhailah ke son kunna shi,gaba ɗaya ta riga ta san lagonsa babu abinda ke saurin tada sha'awarsa kamar ya ga breast ɗinta a waje.Ya buɗe idanun ya sauke akan inda yake ɗaukar hankalinsa,sannan ya buɗe baki yace, "No sai jibi daga wajen meeting zan ƙariso gida,na sanar miki zamuyi meeting da Minister jibi,please wife ki tashi ki je ki sha magani."

Maleek yayi maganar yana haɗe face yadda Suhailah ba za ta yi masa musu ba,ta kuwa ɓata fuska tana dubansa tace, "Korata kake yi Baby bayan nima nayi missing ɗinka."

"Suhailah kina son in shiga wani hali ne alhali bama kusa bare in rage zafi,please ki je ki sha magani za mu yi waya anjima kaɗan, yanzu nima wanka zan yi akwai baƙin da zan gani kafin na wuce zuwa gidan Hajjah."

Daga haka ya kashe wayar kawai don yasan idan ya biye mata za ta yi ta kunna shi ne kawai,Ya cigaba da cin abincin yana jin kewarta me yawa na lulluɓe zuciyarsa.

Lokacin da ya kammala cin abincin direct sama ya nufa,ya since kayan jikinsa ya wuce zuwa toilet don yin wanka. Koda ya fito cikin sauri-sauri ya shirya cikin manyan kaya da suka amsa jikinsa,ya feshe jikinsa da tutaren AMOUAGE daddaɗan ƙamshinsa ya cika ɗakin.

Kiran wayarsa da akayi yasa shi isa inda ya zube wayoyin nasa,ya ɗauki wanda kira ya shigo ciki ya kai kunni. Maganar minti ɗaya yayi ya aje wayer yana nufan wajen wata drawer, ya ciro kuɗaɗe masu yawa ya zura cikin aljihu,sannan ya kwashi wayoyinsa ya fito don sauka zuwa falon ƙasa inda zai gana da mutanen da ke jiransa.

Da wani mutum da zai ba kwangilar kai abinci gidajen marayu ya fara ganawa,ya sallameshi bayan ya turo masa kuɗi ta account.Daga nan ya fara ganawa da mutanen da ke jiransa daga waje,yana sallamansu da kuɗi kamar yadda ya saba,in dai ya shigo gari aka san yazo to shikenan fa bai da sauran sukuni,mutane ƴan maula da masu tarin matsaloli ne za su yi ta zuwa,shi kuma baya gajiya da bayarwa.Shiyasa shi ma tunda Ubangiji ya yi masa arziƙi bai taɓa gajiya da bayarwa ba,kuma Allah bai taɓa nuna masa ranan da za a zo a tsaya masa yace ya rasa abin badawa ba.

Bai samu kansa sai kusan ƙarfe ɗaya na rana,shiyasa bai ma tsaya cewa zai jira yin sallah a masallacin da dake jikin ƙaton gidan nasa ba,ya wuce kawai don zuwa gidan Hajjah.

Kafin ya ƙarisa cikin Gonar Ganye ɗin sai da ya tsaya ya samu jam'i a masallacin dake bakin titin shiga kwanar gidan Hajjah ɗin. Bayan an idar ne ya ƙarisa zuwa gidan Hajjah yayi horn mai gadi ya buɗe masa gate ya shige. Sai lokacin da yake tinkaran entrance na shiga cikin gidan,zuciyarsa ta tunasar da shi alqawarin da ya yiwa Hajjah na zuwa ya ga gurguwarta.Wani abu ya taɓa zuciyarsa yana jin gaba ɗaya jikinsa na mutuwa,don tun daren jiya yake neman hanyar da zai iya sillewa Hajjah amma ya rasa,ya riga ya amsa mata zai je ɗin dole ne kuma ya cika wannan alqawarin.

Ya samu Hajjah tare da wasu baƙi biyu lokacin da ya shiga,hakan yasa suna gaisawa da baƙin ya wuce zuwa cikin ɗakin Hajjah.

Akan gadonta ya zauna yana aje wayoyinsa,ya wani lumshe ido yana furzar da iska daga bakinsa,kafin ya ɗauki wayarsa ɗaya ya shiga neman layin Suhailah.

Bugu biyu ta ɗaga wayar ya fara da tambayarta jikinta,yayi ɗan jim kafin yayi magana cikin isarsa da ƙasaita yace, "Alright! Sai ki shirya ku wuce zuwa asibiti,ki yi haƙury Suhailah bana son wannan kukan kina ɗagamin hankali,zan dawo gobe na fasa kaiwa jibin okey."

Ya sake yin jim kafin yace, "Okey sorry zai tafi Insha Allah,ku dai je asibitin in kun isa ki kirani bye Allah ya baki lafiya."

Daga haka ya yi hanging up yana maida idanunsa ya lumshe,dai-dai lokacin da Hajjah ke sanyo kanta cikin ɗakin.Ta sauke idanunta akan Maleek ɗin tana cewa, "Maleek lafiya dai?"

A.Maleek ya buɗe manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah,kafin ya ɗan saki murmushi kaɗan yana cewa, "Lafiya lau Hajjah,Suhailah ce ke son dagulamin lissafi zazzaɓi take yi taƙi kuma shan magani sai kuka,kin san halin ciwanta da raki da shagwaɓar tsiya,yanzu nace lallai su wuce asibiti tunda ga driver nan a gidan."

Hajjah ta zauna bakin gado tana cewa, "Subhanallah! Allah ya bata lafiya,ai Suhailah ita ciwanta ban haushi ne da shi,bata son sha magani to ina ko za a samu sauƙi da sauri,gara dai ka matsa mata su je asibitin a duba ta,zazzaɓin ake tayi ko'ina sai dai fatan Allah yaye wahala kawai."

Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Hakane Hajjah,karki damu na sanar mata su wuce asibitin yanzu,da zaran sun isa za ta kira ni,akwai fura ne a fridge Hajjah?"

Hajjah ta dubesa tana gyaɗa kai take cewa, "Akwai bata da yawa amma,mu je daga falo sai Lubah ta ɗakko maka,baƙin sun tafi ai."

Suka fito tare da Hajjah zuwa cikin falon nata,ta ciri murya ta kira Lubah tare da bata umurnin ɗakkowa Maleek Furan da bata da rabo da shi cikin fridge.Lubah ta kawo furan ta aje tana kwasan gaisuwa,kafin ta miƙe ta bar wajen tana jinjina halin tilon ɗan Hajiyar,wanda suke gulmarsa akan cewa ya cika miskilanci,sai dai yana da kyauta don suna dafa kuɗaɗe duk idan zai wuce sai ya musu rabon kuɗi.

"Abdul-maleek ina fata kana sane da zancenmu na jiya,ƙarfe nawa ka yanke shawaran za ku je ɗin? Ga dai Shehu driver nan da shi zaku don shi ya kaini gidan,amma kamar yadda na sanar maka bana so ka je da babbar motarka,sabida wasu dalilai don haka a ɗauki ƙaramar motata ta da,wacce ke aje cikin rumfa yanzu sai a sanar da Shehu ya fito da ita ya goge,so nake ka je ka ganta ido na ganin ido ba,ba sai da daddare ba."

Maleek dake sauraren Hajjah ya jinjina kai yana cewa, "To shikenan Hajjah duk yadda kika ce haka za a yi."

Yadda yayi maganar very low yasa Hajjah gane Maleek na cikin damuwa,amma sai ta share ta dubesa tana cewa, "To bari a sanar da Shehun ya fito da motar zuwa la'asar idan kun yi sallah ba sai ku je ba kawai,ko akwai inda zaka ne?"

Maleek yayi saurin girgiwa Hajjah kai ba tare da yayi magana ba,sai ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta ta shiga kiran Shehu,don sanar masa ya ciro motar ya goge."

Duk Maleek na zaune yana jin abinda Hajjah ke cewa har ta kammala wayar.Ta dubi Maleek da yayi shiru ba shi da alamun tanka ta,ta murmusa kaɗan tana cewa, "Maleek ka kwantar da hankalinka bafa dole zan maka akan Yariyar ba,cewa nayi kawai ka je ku ga juna,duk abinda ka ji game da ita ka sanar dani,idan tayi maka ka kuma ji a ranka za ka iya zaman aure da ita zan fi kowa farin ciki,idan kuma ba tayi maka ba zan maka dole ba,sabida ina mata son da bazan so ta auri wanda baya son ta ba,ko wanda zai ji a ransa an tirsasa shi ne ya aureta don tana da lalura,don haka ka sanya zuciyarka a inuwa."

Maleek ya dubi Hajjah yana murmushi kaɗan,sabida yadda yake mamakin duk duniya ita kaɗaice wacce take karantar abinda ke zuciyarsa ko bai furta ba.Ya yi magana cikin shagwaɓe murya kamar ƙaramin yaro,yana cewa, "Hajjah cewa nayi hankalina ya tashi dama?"

Hajjah ta zabga masa harara tana cewa, "Bansani ba ɗan rainin hankali." Maleek ya saki murmushi me faɗi a wannan karon,ba tare da yayi magana ba amma.

Kiran Suhailah da ya shigo wayarsa yasa shi ɗagawa cikin sauri,suka jima suna magana kafin ga miƙa wa Hajjah wayar.

Hajjah tayi wa Suhailah ya jiki suka ɗan jima suna magana,sannan Hajjah ta miƙawa Maleek wayarsa.

Bayan ya gama da Suhailah a waya ne aka kawo masa lunch nan tsakiyar falon Hajjah.

Da kansa ya zuba abinda zai ci cikin abinci kala biyun da aka shirya a gabansa.Yana cin abincin ne amma hankalinsa na kan yadda zai je ya ga gurguwar Hajjah. Zuciyarsa na hasaso masa ko wace irin gurgurwace Hajjah ke nufi? Don bata sanar da shi yanayin yadda TAIMIYYAH take tafiya ba.Shiyasa yake ji duk ya ƙago ya je shi ma ya ga wacece wannan gurguwar data sace zuciyar Hajjah,har take so ta ɓallo masa rigimar da bai san ta yadda zai iya ɗauka ba,don koda yake ma Suhailah zancen ƙarin aure bai yi tunanin Hajjah za ta iya jajibo maganar aure nan kurkusa ba.

Har ya kammala cin abincin ya kasa samun nutsuwar zuciyarsa,shiyasa abincin ma bai wani iya ci da yawa ba.

Hajjah dake zaune duk tana kula da yanayinsa, sai tayi murmushi kawai tana dubansa cikin ido tace, "Maleek yanzu har ka ƙoshi kenan ka ke nufi?"

Maleek ya shagwaɓe face tare da tsukesa yana cewa, "Na ƙoshi Hajjah kin san yau banyi karin safe da wuri bane,amma anjima ina so amin farfesun Kifi asa yaji sosai da garlic."

Hajjah ta jinjina kai tana cewa, "To Allah ya kaimu anjiman za a yi."

Daga haka sai Hajjah ta kamo wani zancen me muhimmanci suka shiga tattaunawa akai. Basu tashi daga cikin falon ba sai da akai kiran sallar la'asar,sannan Maleek ya tashi ya fice don gangarawa zuwa wani ƙaramin masallaci,wanda ke gaba kaɗan da gidan Hajjah.

Ita kuma Hajjah ta shige ciki don gabatar da sallar itama,zuciyarta cike da addu'an Allah ya jefa son TAIMIYYAH a zuciyar Maleek ɗin.

Lokacin da Maleek ya dawo masallaci sai ya sanar da Hajjah cewa zasu wuce,zuwa gidansu gurguwanta.Hajjah ta jefa masa harara tana cewa, "Kul! Na sake jin kalmar gurguwar nan,sunanta Zainab TAIMIYYAH sai ka zaɓi na faɗi aciki ba ka kirata gurguwaba."

Maleek ya taɓe baki yana cewa, "Hajjah wai yaushe kika fara son wannan Yarinyar har haka ne?"

Hajjah ta sake manna masa harara tana cewa, "Babu ruwanka da wannan kai dai kawai ku je Allah haɗa zukatanku ni shine fata na."

Maleek ya juya ya fice daga falon Hajjah,yana jin zuciyarsa na wani irin dokawa da addu'an da Hajjah tayi daga ƙarshe..........✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*55*

Lokacin da Maleek ya fita har Shehu ya gyara parking cikin tsohuwar motar Hajjah na da,wata baƙar Vibe wacce har yanzu da kyanta ba wai tayi wani abu bane.

Shehu ya buɗe masa back seat yana masa barka da fitowa,Maleek ya shiga ya zauna yana amsa Shehu a taƙaice.

Shehu ya rufewa Maleek murfin motar tare da zagayawa ya buɗe driver seat ya shiga,ya tada motar suka nufi wajen gate. Bilya ya buɗe musu gate ɗin yana musu fatan dawowa lafiya,zuciyarsa cike da mamakin yau kuma ubangidan na su ƙaramar mota yake jin hawa.

"Shehu Gyallesu muka nufa,gidan wannan Yarinyar da Hajjah tace kun kaɗeta da mota kwanakin baya."

A.Maleek ya yi maganan lokacin da suka hau kan kwalta,Shehu ya jinjina kai cike da nuna gamsuwa yace, "An gama ranka-ya-daɗe Hajiya ta sanar dani."

Daga haka motar ya ɗauki shiru kafin kiran Suhailah ya shigo wayar Maleek,yayi receiving call ɗin yana jingina da jikin seat ɗin sosai don ya ji daɗin amsa wayar.

Readers Also Read